Sashe 12
Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kyaleni da ita Aliyu, ita don bata da kunya don na amshi wani shegen dari biyar a hannunta kusan shekara daya knn sae ta aiko a karba, maxa kice kuma ta baki canjin dari biyar ki mayar min," khadija har ta fita inna ta kwalo mata kira ta dawo fuskarta a daure tace "wae meye ne inna," inna tace "kije ki kira min inteesar ynxun nn," ta fice daga falon Aliyu ya daka mata tsawa baki ji me tace maki bne "ta leko tace naji ae," snn ta wuce, bayan kmr minti goma inteesar ta shigo falon tana rike da kugunta daga bakin kofa tana kallon inna tace "gani inna," Aliyu dake xaune yana shan fura ya juya yana kallonta, inna tace "to bakin kofar xan xo in same ki," inteesar ta shigo ta xauna gefenta da kyar, sae bin ta da kallo Aliyu yake, tace "me xan maki inna bacci fa nake, inna tace "kai haba, to shiga ki kwanta in kin tashi ma yi maganan," inteesar ta mike xata shiga daki, inna tace "lah baki ga Aliyu bne, naga baki gaidashi ba," inteesar ta juya tana kallon inda yake, har lkcn kallonta yake, yyi murmushi ya ci gaba da shan furarsa yace "ni na isa ta gaishe ni," inteesar ta dan yi tsaki ta shige daki abinta, inna tace "to Allah shi kyauta," hira Aliyu ya kwanta gefen inna yana mata tana biye masa muryarta har waje, sae ka rantse kace ba Aliyu bne, duk inteesar na kwance a daki tana jinsu, rabon da Aliyu ya tsaya suyi hirar arxiki da inna har an manta, yace "ni fa inna yunwa nake ji kin wani hada ni da fura," tace "lah me xaka ci toh," yace "jollof rice nake so da farfesu," da sauri tace "to bari in je in maka," ta mike tsaye tana gyara dankwalin kanta tace "yo nayi ma wasu bnxa ma bare kai," ta fice tana kwala ma kursum kira taxo ta hura mata gawayi, don bata gane gas acewarta bata lkci ne. Aliyu ya juya yana kallon kofar dakin kmr ya shiga ya fasa, yana ta danne dannen wayarsa amma lkci lkci yakan juya ya kalli kofar dakin, inteesar taji shirin yyi yawa, wata xuciyarta tace ta leka taga ko yana falon, a hankali cikin sanda ta isa bakin kofa ta dan bude labulen a hankali tana lekensa, shima ya juya knn yana kallon kofar dakin xuciyarsa na son ya shiga, suka hada ido, ta sake labulen da sauri yyi murmushi bae dae ce komai ba, ganin xuciyarsa ta kasa hakura da shiga dakin kuma baya so ya shiga yasa ya mike da sauri ya fice daga falon yyi sashinsa. Ko da inna ta shigo falon tana kiran inteesar ta fito ta ci abinci da xafinsa, da sauri ta fito kmr jira take, taga inna kadae ne xaune falon, tace "wae ni kika ma girki," inna tace "aa Aliyu nayi ma," inteesar tace "to ina yake," inna tace "ae ni da kaina na kai masa yana kwance a dakinsa yaron kirki." inteesar bata ce komai ba ta dauki furan da ya rage ya rufe ta shiga sha, inna tace "ke dae kin banu da kwadayi, naki ne," ko kallonta inteesar bata yi ba ta shanye ta ajye kofin, snn ta fara cin abincinta, ta gama cin abinci knn, khadija ta shigo dakin tace "wae ina furan ya Aliyu" inna tace ahaf gata nn ta shanye khadija tayi tsaki ta juya ta fice. Karfe tara inteesar tayi ma inna sae da safe tayi sashinsu, har ta wuce bangarensu Aliyu ta dawo tana lekan ko yana nn ko ya tafi, ita dae bata ga alaman ya tafi ba kuma bata ga alaman yana nn ba, ta karasa bakin kofar a hankali da yake basu kunna bulb din wajen ba ta durkusa tana lalube ko xata ga takalminsa, dae dae nn aka bude kofar Haisam ya fito, daga ita har shi sae da suka tsorata. Ashe Aliyun ma na kallonta daga bayanta ya fito daga bangaren Hajiyarsa knn. . Haisam yace "me kike yi a nn Inteesar," ta ji kmr ta nutse wajen don kunya ta fara kame kame, Haisam yyi dariya yace "to ae baya ciki ya fita sae dae in xaki shiga ki jirasa," kmr xata yi kuka tace "wayyo ni ya Haisam abu na ne ya fadi nke nema," bata jira me xae ce ba ta juya da sauri xuciyarta a dagule xata bar wajen ta kusan cin karo da Aliyu dake tsaye har lkcn yana kallonta, gabanta yyi mugun faduwa, tabi gefensa da sauri xata wuce ya rikota, Haisam dae yyi gaba abinsa yana dariya, ta buge masa hannu ta daure fuska tace "meye hka malam," dariyarsa mai kyau yyi snn yace "me kike bukata daga gare ni da kika biyo ni," ta fashe da kukan takaici tace "waye ya biyo ka, Allah ya isa na, da'alla ka sake ni na wuce don naxo neman abu na shine na biyo ka," dariya ya dinga yi har da buga bango yace "ae nine abun naki, ni kika xo nema 4 sure na sani," ta fixge hannunta xata bar wajen yyi saurin rikota ya bude kofar falon ya ja ta suka shiga, kuka ssae take yi kuma na takaici, ka kyaleni ya Aliyu bana son hka, yyi murmushi ya rufe kofar falon da key ya karaso bayanta ya tsaya a hankali yace "am srry fateema, i also feel...." sae kuma yyi shiru ta juya tace "ka bude min kofa in fita nace maka," bae ce mata komai ba ya dauketa sae bedroom yace "ki bari in gaisa da yarana," kuka ta dinga yi tana jin haushin kanta ita kam har ga Allah ganinta kawae tayi a bakin kofar bata san ya aka yi ba, ya rufe kofar dakin ya xaunar da ita kan gado yana kallonta ya durkusa gabanta yace "its High tym mun fahimci juna fateema," cikin tsawa tace "wace fahimta kuma, ka bude min kofa in fice daga dakin nn" yyi murmushi ya kauda kansa yace "ok," snn ya mike ya bude mata kofar dakin da sauri ta fita, ya bi ta baya ya bude mata na falo ma ta fice, snn ya mayar da kofarsa ya rufe. Ko barin wajen bae yi ba ta fara buga kofar da sauri, ya bude yana kallonta ta shigo falon da sauri tace "momy xata gan ni" yace "a ina," tace "wucewa take," bae ce komai ba ya xauna kan kujera, ita ko tana tsaye bakin kofar sae leke leke take, ta kai minti kusan goma a hka snn yace "to ki xauna mana," ta juya ta galla masa harara tace "ina ruwanka da tsayuwata," yyi murmushi ya dauke kansa bae sake cewa komai ba har ta gama tsayuwarta ta bude kofar ta fice, ya sauke ajiyar xuciya, shi kam baxae iya tsayawa rokan karamar yarinyar nn ta koma gidansa ba ta ci gaba da raina sa ba, duk da abun yana damunsa but ya gwammace yyi ta damunsa din. Kullum sae Aliyu ya xo gida da daddare duk dan sbda inteesar amma baya nunawa, ita kuwa idan bata gansa ba har bata jin ddi, tayi ta sintirin xuwa gun inna knn, ta rasa me ke damunta kan Aliyu, gashi ko sun hadu kallon arxiki bata yi masa bare gaisuwa, shi kam sae dae ya bita da kallo, tun ran da inna tayi mata maganan komawa gidanta ta balbaleta da masifa bata sake yi mata ba. Cikinta ya shiga wata na shidda amma bbu me yi mata maganan komawa gidan mijinta, Yau tana xaune falon inna ya shigo da daddare, inna na bakin famfo tana wanke robobinta, ya xauna yana kallon inteesar dake xaune tana shan watemelon, kallo daya tayi masa ta dauke kanta, ya sauko gabanta ya xauna yana kallonta, tayi kmr bata san da shi ba tana ta shan kankananta, ya shafi cikinta ta buge masa hannu tace "meye hka," bakinsa ya daura an nata yana kallon cikin idonta, gabanta yyi mugun faduwa ta rufe idonta da sauri ya shiga kissin din wuyarta, tayi baya xata fadi ya tallabota da sauri snn ya kwantar da ita a hankali ya shiga shafata ta kasa hanasa, ganin idan ya ci gaba da hkn baxae iya hkura ba yasa ya dago ta yana kallonta da kyar yace "fateema," ta daga kai tana kallonsa ita ma da kyar don gaba daya yanayinta ya canxa, ya kauda yace "meyasa kike walakantani hka ne kike cutata," tayi tsaki bata ce komai ba, ya ci gaba "kiyi hkuri ki koma dakin ki, ni nayi maki alkawarin baxa a sake jin kan mu ba," tace "ae bani kadae bace matarka da xaka damu kanka a kaina, kuma ni bana sonka" yyi murmushi yace "karya kike yarinya ga sona nn ina hangowa cikin idonki, ni dae ne bana sonki i only need yhu badly, amma xanyi kkri naga na koyi sonki sbda kids dinmu" ta fashe da kuka ta mike tsaye tana kallonsa tace "ka yaudari kanka idan kayi tunanin ina sonka, uwar me xanyi da wanda baya ganin mahaifiyata da gashi ma dae tukun, i hate yhu Aliyu," ta juya da sauri ta shige dakin inna tana kukan takaici, wae he only need her dama tasan kawae don ya dinga biyan silly bukatarsa yasa yake son ta koma gidansa. Ya sauke ajiyar xuciya ya mike ya fita daga falon, inna tace ina xaka" yace ina xuwa inna, sashinsu inteesar ya nufa, yyi sallama can kasa ihsaan ta amsa ya bude kofar ya shiga falon, momy na xaune tana feed din ihsaan, ya nemi gu ya xauna kansa a kasa ya gaisheta, ta amsa da "qlau," yyi shiru na kusan minti biyar tana ta harkan gabanta, a hankali ya fara magana yace "wajen ki na xo momy," ba tare da ta kallesa ba fuskarta a daure tace "ni kuma . Aliyu ya dan yi shiru snn yace "dama so nake don Allah ki taimaka kiyi ma Fateema magana ta koma dakinta, don xata fi jin maganarki," momy tayi masa wani mugun kallo tace "lallai ka cika mara kunya, kasan da warce kke magana kuwa, to fice min a falo tun kan na baka mamaki," ya sunkuyar da kansa ya dan yi murmushi bbu