Sashe 2
Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inteesar tayi shiru a dan tsorace bayan ta hadiye maganin tana jiran jin me xata fara ji a jikinta, har na kusan minti goma bata ji komai ba hkn yasa ta mayar da hankalinta ga TV dake ta aiki shi kadae tana kallo, taji ta fara jin bacci amma har lkcn bata ji ko da ciwon kai a jikinta ba, hkn yyi mugun daga mata hankali, tace na shiga uku kar dae cikin baxae xube ba, ta dauko magungunan ta shiga balla su kuma xata sha yanda ta sha daxu hankalinta a tashe, ta ciro su knn ta jawo kofin ruwanta xata sake korawa taji wani matsanancin ciwo a mararta da bata taba ji ba, tayo waje da ido a tsorace gabanta na faduwa, a hankali cikinta ma ya fara ciwo ya hade da na maran, tunda take bata taba jin irin wnn ciwon a jikinta ba, kankame cikinta tayi ta shiga mutsu mutsu daga xaunen da take tana buga tiles da hannunta, taga xama ya gagareta ta kwanta kasa tana rike da cikin tana juye juye, ita nn tana ga xata iya jure ciwon har ya gama cikin ya fita, da marar ta yyi wani irin murda mata ta daura hannu a ka taji kmr mutuwarta ce ta xo, bata san lkcn da ta fasa wani axababben ihu ba tana rike da cikin, lkci daya ta hada xufa, ta shiga kwala ihun axaban da take ji a gigice, a tare Aliyu suka fito da Safeena ya karasa kusa da kofar a rude ya murda yaji a rufe, bubbuga kofar ya shiga yi yana kiranta, ta fashe da wani matsanancin kuka da kyar tace "wayyo mutuwa xanyi ya Aliyu," ya koma daki a rikice ya shiga neman spare key, safeena kam da gudu ta koma dakinta ta dinga tsallen murna shknn ta sha ruwan, ya karaso jikin kofar jikinsa na rawa ya bude kofar ya afko cikin dakin yana kalle kallen inda xae ganta, can kusa da gado ya ganta kwance tana juye juye ya karasa gabanta da sauri ya durkushe ya dago ta a rude yana tambayarta me ya faru, kasa cewa komae tayi sae juye juyen da kawae take a hannunsa, a rikice ya shiga cewa "don Allah kiyi min magana fateema me ya same ki," duk da mugun axaban da take ji hannunta na rawa ta shiga tura kwalin magungunan karkashin gado tana mayar da numfashi da kyar wae kar ya gani, ya lura da abinda take, ya rike hannunta da sauri yana kallon kwalin yace "meye wnn," girgixa masa kai ta shiga yi tana neman xamewa daga jikinsa ya daga kwalin tabs din yana kallo baki bude, a rude ya jefar ya shiga cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un meye wnn," wani ihun ta kuma fasawa ta kankamesa tace "wayyoo ya Aliyu, cikina, mutuwa xanyi wllh," yana jijjigata cikin tashin hankali ya shiga cewa "ki gaya min shi kika sha fateema?" kasa cewa komai tayi sae jujjuya kanta da take cikin axaba, ya ga farar takardar scan din dake gabanta ya dauka da sauri hannunsa na rawa ya bude, jefar da takardar yyi ya fixgota cikin mugun tashin hankali yace "wayyo fateema ki gaya min magungunann nn kika sha? Plss kiyi min mgna," a rude yake maganar, ita ko da kyar ta shiga gyada masa kai tana jawo numfashi kmr me shirin suma, ya dafe kansa yana kallonta yace "nashiga uku, oh my God," saketa yyi da sauri ya fice daga dakin, ta dinga ihu tana birgima cikin axaban ciwo tana kiran Abbanta, ya dawo dakin da sauri rike da allura, kwance ya ganta cikin jini, yyi wani kara a rude ya jefar da alluran hannunsa ya karaso kusa da ita da sauri yace "ya salam, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, fateema fateema" kuka take ssae tana juye juye kmr ranta xae fita jini sae malala yake ta kasanta, ya dagota ya kai mata wani wawan mari a gigice ya shaketa yace "kika kashe min yarana, yhu kill my kids" ta kankamesa tace "wayyo mutuwa xanyi na shiga uku," wani marin ya kuma kai mata ya dagota ya buga ta da bango, tunda take bata taba ganin yanayin da Aliyu ya shiga ranan a tare da shi ba, idonsa ya kada yyi jajur muryarsa na rawa yace "ki gaya min ubanwa ya baki maganin nn, wani asibiti kika je," ya wurgar da ita ya buga bango da hannayensa biyu yace "ya salam," juyowa taga ya sake yi ta fara kkrin fita daga dakin ya fixgota ya shaketa yana huci yace "me yarana suka maki kika kashe su fateema," ta rike hannayensa biyu cikin kukan tashin hankali tace "no plss kayi min rae ya Aliyu cikina xae kasheni," bugata yyi da bango da karfi ya fice daga dakin tasan be gama da ita ba, tayi karfin hali ta rarrafa ta fito daga dakin da kyar tana neman inda xata safeena ta fito da sauri ta ja ta suka shige dakinta ta rufe kofar da sauri, inteesar ta xube kasan dakinta tana mayar da numfashi har lkcn jinin dake xuba jikinta bae tsaya ba . Aliyu ya fito kmr wani mahaukaci daga dakinsa ya shiga nata a rikice bae ganta ba, ya fito ya shiga buga kofar Safeena da karfi ganin trace din jini tun daga kofar Inteesar har nata, alamar nn inteesar ta shiga, cikin tsawa yace "baxa ku bude min kofar ba" cikin sanyin murya Safeenah tace "haba dear ka sa ma xuciyarka ruwan sanyi mana, so kke kayi kisan kai, ka bar ta da halin da take ciki mana xaka dinga dukanta kuma," ya daka mata wani raxanannen tsawa yace "na rantse da wanda numfashina ke hannunsa idan ban hada dake ba kada Allah ya bani abinda yake nema, baxxa ki bude min kofa ba" ya karasa maganar yana huci, ta bude baki da mamaki tana kallon kofa, A'aaah lallai abun babba ne yau, to fa, ta dan tabe baki tace "to ni ko sae dae kar ya baka, don baxan tsaya hka kawae ina ji ina gani ka kashe yar mutane gabana ba," bae sake cewa komai ba ya juya da sauri kmr xae tashi sama ya koma dakinsa yana huci, inteesar kam na durkushe dakin sae kuka take tana juye juye kmr ranta xae fita, kila karshenta ne ya xo yau, gashi har lkcn jini bae tsaya mata ba sae bulbulowa yake, duk kayan jikinta ya baci da jini hka ma dakin safeena, safeena ta dauko Zaninta da sauri ta mika mata a xuciyarta tana cewa "yau ai sae dae jininki ya tsiyaye ki mutu yarinya baxan bude kofar ba bare ya taimaka maki," inteesar ta kasa karban xanin, sae cewa take mutuwa xanyi, safeena tace "baxa ki mutu ba," key suka ji Aliyu ya saka a kofar, Inteesar ta fasa ihu jikinta na rawa taji kmr ta sume ynxu ta samu saukin abubuwan dake faruwa ynxu "wayyo kayi min rae ya Aliyu wlh yau mutuwa xanyi, don Allah kaji tausayina" ya afko dakin rike da kwalin tabs din da ta sha yana huci, idonsa ya koma jajur kmr gauta, kanta yyi ya fincikota da karfi ya dago ta, muryarsa na rawa yace "wllh wllh baki gaya min wanda ya baki magungunan nn ba, sae na kashe ki kema yau," jikinta na rawa ta shiga girgixa masa kai hawaye na bin kuncinta, ya shaketa da karfi, cikin tsawa yace "baxa ki gaya min ba," ta yo waje da ido a tsorace, da kyar muryarta a shake tace "xan gaya maka," ya watsa mata mari yace "uban me kike jira," ta fashe da wani matsanancin kuka ta juya tana kallon safeena tace "ita ce ta kaini aka bani," Safeena ta yo waje da ido ta dafe kirjinta tace "na shiga uku yarinya xata min sharri, a ina kika ganni," cikin kukan Axaba Inteesar tace "ita ce ya Aliyu, ka tausaya min cikina kasheni xae yi wllh," a hankali Aliyu ya saketa ta sulale kasa ya juya yana kallon safeena da ta xama kmr mara gskyar gske, duk ta rude, sae rawa bakinta yake ta kasa cewa komai, ta fashe da kuka tace "wllh wllh sharri tayi min Aliyu, a ina ta gan ni yau da har xan kai ta a bata magani," wani kara yyi ya karasa kusa da safeenar kmr xaki ya shaketa hawaye cike idonsa yace "ku ka kashe min yarana, me suka maku safeena," bae jira me xata ce ba yyi wani irin buga kanta da bango ya saketa yana huci, sae ga jini, a hankali ta sulale kasa ta fadi sumammiya a wajen, juyawa yyi bae sake ganin Inteesar ba a dakin . Inteesar na fita daga dakin dama falo ta sauko tayi hanyar kofar fita waje da sauran karfinta don dk jikinta yyi weak, tana isa tsakiyar falon jiri ya debeta ta xube kasa ta kasa tashi kuma, dae dae nn shima ya sauko kmr an hankadosa ta fasa wani gigitattcen ihu ta fara kkrin mikewa tsaye amma ta kasa cikin kuka ta dinga cewa Noo plss ya Aliyu ka tausaya min," ganin ya yo kanta ne yasa ba tare da ta shirya ba ta sulale wajen sumammiya, ya xube gabanta ya kife kansa kan tiles cikin tashin hankali yace "Nooo" da kyar ya dago kansa yana kallonta hawaye kwance fuskarsa, ya dagota ya rungumeta muryarsa na rawa yace "y fateema, meyasa xaki min hka, me yaran nn suka yi maki kika gwammace ki kashesu, y?" ganin har lkcin jini bae tsaya mata ba yasa ya dauketa da kyar ya haura sama da ita ya bude dakinsa ya kwantar da ita yana tunanin me xae mata, duk wata baseera ta bace masa kmr ba likita ba ya rasa yanda xae yi da ita sae bincika ruwan allura yake ya rasa wanne ma ya kamata yyi mata, da kyar ya jawo wayarsa jiki ba kwari ya shiga neman nmbr wani abokinsa doctor yaji a kashe, ya kira Dr maryam ma yaki shiga, hkn yasa ya kira nmbr faruuq bugu daya ya daga, da kyar ya iya cewa "plss faruuq ka taho gidana ynxun nn i need yhu help," ya katse kiran ya ajiye wayar har lkcn inteesar na jikinsa, ko minti sha biyar bae cika ba faruuq ya iso gidan