← Book details Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 28

Sashe 23

Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel · about 5 min read

taimaka min kiyi ma Abba magana " inna tace "to baki isa ba don ubanki," ta fice da katuwar tukunyanta tana kwala ma kursum kira ta siyo mata itace, inteesar ta xube kan gado tana ci gaba da kuka, ta kai kusan awa daya a hka taji ihun Husaini ta fito da gudu ba tare da ta shirya ba, taga inna ce ke masa wanka sae kunya ta kamata ynda ta fito a rude, Anty tayi dariya tace "wanka ake masa ba wani abu ba maman biyu," inna ta tabe baki tace "ki rabu da gantalalliya tana danya da ita wae gun wancan mahaukacin xata ya buge min ita a bnxa, shi fa ya janyo ma kansa yar nn, wata shegiyar karuwar mace me xubin kafurae ya auro suka dinga walakanta min jikata sae ga shi wae har sun haukatata ban sani ba, gashi ynxu Allah yyi mata sakayya abunsu ya koma masu, ni dae Alhmdllhi tunda jikata ta dawo lfya, miko min tsummar can" inteesar ta juya ta koma daki a sanyaye hawaye na bin kuncinta, kursum ta shigo tana kallon inteesar tace "Abba yace kije," . ....A hankali Inteesar tayi sallama ta shiga falon Abba, ta xauna kasa tace "Abba gani" Abba yace ta koma kan kujera, ta mike ta xauna kan kujera tana kallon Abbanmu dake ta bin ta da kallo, tayi murmushi ta sunkuyar da kanta kasa, Abba yyi shiru snn yace "ina yaran," xata yi magana sae ga kursum ta shigo rike da Hassan, Zainab na biye da ita a baya rike da Hussain, duk Abba ya amshesu yana kallonsu yana murmushi, kmr ba jarirae ba suma idonsu kyar a kansa, sae da ya tofa masu addua gaba daya snn ya kwantar dasu kan kujera ita dae inteesar kanta na kasa, Abba na kallon Abbanmu yace "dota dinka knn ko Alhaji Umar ko," Abbanmu yyi murmushi yana kallon Zainab yace "eh ita ce diyata ta farko," Abba yyi murmushi yace "Allah sarki sae naga suna kama da inteesar," Abbanmu yyi dariya yace "hka ne kam," kursum suka fita tare da Zainab snn Abba yace "kina jina fateema," ta gyada masa kai yace "idan kin huta xaku koma can india dasu Antynki amma fa sae idan kina son komawa baxa mu takuraki ba, nasan dae kina sane dae Aliyu bashi da lfya ko," kai kawae ta gyada masa tana hawaye, Abba yace "ba kuka xakiyi ba, Addua xakiyi masa," a hankali tace "Abba ni na gama hutawa mu tafi yau kawae," Abbanmu yace "yauwa fateema ashe kina da hankali gwara kije gun mijinki tunda rashin ki ya jawo masa wnn lalura," bata ce komai ba Abba yace "shknn fateema Allah yyi maki albarka, amma ki bari gobe ku tafi sbda yaran nn kar suyi xaxxabi je ki ki kira min momynki," ta mike ta fita daga falon, Abbanmu yace "xanje gun wani abokina dake nn gadon kaya," Abba yace "to shknn Alhaji sae ka dawo," Abbanmu ya mike ya fita yana kiran Anty a waya ya sanar da ita xae dan fita, bayan fitarsa da minti biyar inteesar suka shigo da momynta, Abba yyi mata bayanin abinda suka tsara da Abbanmu kan cewa su koma can india da inteesar gun Aliyu, momy tace "hkn ma yyi, Allah dae ya basa lfya," Abba yace"Ameen don son Annabi," inteesar ta mike ta fita ta bar masu falon ta koma falon inna, kmr ba jego take ba garau take jin kanta, a bakin kofa ta tar da inna tana masu lafiyayyan girki inna tace "Allah sarki Aliyu, wae wani irin ciwo aka ce yake yi hka, a dawo min da jikana gida kawae na nema masa magani,"ko kallonta inteesar bata yi ba ta shiga falo Anty ta sata gaba ta shanye kunun da inna ta dama mata don har lkcn bata yi wani break din kirki ba, kasa sukuni tayi ranar Allah Allah take kawae gobe yyi ta je ta ga Aliyu duk hnkalinta yyi gunsa, momyce ta dawo da yaran daga gun Abba suna kuka ta bai ma mamarsu su ta fita, wajen karfe uku Anty ta tafi bangaren momy inna kuma ta tafi nemo ganyen darbejiya, inteesar nata fama da Hassan dake ta yi mata rigima kursum na rike da Hussaini, kursum tace "wae sunansu knn," inteesar tace "A'a ba a rada masu suna ba har ynxu ae, wae ina su khadija" kursum tace "khadija na gidan Zainab bata da lfya, rahma kuma na can gidansu mamarmu" inteesar tace "Allah sarki Zainab, Hajiya da umma fa," kursum tace "hajiya tayi tafiya, umma kuma tana can gidansu Fadila ta kara kashe aurenta, shine Abba yace su tafi su bar masa gidansa," inteesar tayi shiru da mamaki tana kallon kursum, can tace "yaushe hkn ya faru," kursum tace "kusan wata biyu knn, inna ce tace Abba ya koresu ko ita ta bar masu gidan," inteesar bata sake cewa komai ba amma ko kadan bata jin ddin abinda inna ke yi, fira suka dinga yi da kursum har inna ta dawo duk ta hada xufa da darbejiyarta tace "da kyar na samo wnn, maxa ki tube ki shiga bayi ki jira ni na juyo ruwan," inteesar ta mike da sauri tace "ke dawa, wllh baxa kiyi min wanka ba da girmana kuma da wnn abun, to wae ca nayi maki banyi wanka bne," inna tace "yau naga tsiya, har wani wanka kike yi dubi ynda kike tafiya kmr wata rubabbiya, wa ya sani ma ko da ruwan sanyi ake maki wanka a can" ko kallonta inteesar bata yi ba ta fice daga falon tayi gun momynta. Washegari har airport Abba ya kai su a motarsa aka bar Zainab gun momy don xasu dawo, inteesar bata ji ddin rashin fitowar da momy tayi ta rakasu ba, basu samu jirgin da xae je india ranar ba a Aminu kano don hka sae da suka fara xuwa lgs snn suka kama hanyar india
Chapter 23 · 0% Book details