Chapter 9
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites*
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
09… Ilham?!” Ya kira sunanta da mamaki.
Rage tsayinta tayi a gabansa kada yanzu ya miƙe ya haɗa kanta da bango, ta amsa da “Na'am ya Hashim”
“Menene wannan farau-farau ɗin? Shine abinda zanci?”
“Abinda muke dashi kenan a gidan, maggin ma fita nayi na karɓo bashi a shago.”
A hasale yace “bana son rainin hankali, yanzu fah ina jinki kina daka a waje..”
Tayi saurin amshewa da “Maggin ne yayi tauri saida na saka a turmi na faffasa, gashi nan na barbaɗa maka.” ta ƙarashe tana matse baki saboda murmushin da yake niman ƙwace mata, ta ɗan ji sanyi a cikin zuciyarta da tayi mishi hakan.
Saidai yanda ya yunƙuro ya sanya tayi saurin ja da baya tana kare fuskarta da hannuwanta a tunaninta marinta zai yi.
Hasken da ta gani yasa ta sauƙe hannun ta buɗe ido, sai ganinshi tayi ya ɗaga labule yana saka takalmin shi daga bakin ƙofa, ko waiwayenta bai sake ba ya sake mata labulen yayi gaba.
Tana sauraron takun shi har ya ƙarasa ya wangale ƙofar dake jikin gate ya dawo ya kunna mashin ɗin shi ya hau ya bar mata gidan, a ranshi yana jinjina girman wulaƙancin da zai yi mata. Bai yi niyyan siyan shawarman jiyan nan ba, ya faɗa ne kawai saboda daɗin zance, amma duk yanda ake siyarda shawarma da safiyar nan a garin kaduna sai yaje ya nemo.
Taɓe baki tayi ta miƙe da farantin shinkafar a hannunta, rufe mishi zatayi idan ya dawo sai ya ɗauka yaci, bai ajiye cefanen da zatayi miya ba balle ta damu kanta ta ɗauko hanya tun daga asibiti ta zo ta tuƙa masa tuwon dare.
Bata da lokacin sake yin wanka, sai kawai ta ƙarasa kimtsawa ta mayar da hijabinta da tayi sallah dashi, ta cire wayanta daga jikin caji ta kulle gidan bayan ta ɗauki abubuwan da zata buƙata ta miƙa key ma maƙwabtansu idan ya dawo bata nan ta san zai tura yara su karɓa masa.
Idan tayi sauri kuma har zata samu isa asibitin ta bawa su Khausar abin karyawa kafin ta tafi wurin Hajiya Surayyah Kagarko, ta san khausar ɗinma ta gaji don zaman ba na daɗi bane, idan tana son tafiya gida babu damuwa tunda gari ya waye, ai ma tayi mata ƙoƙari, kuma itama tana fatan ba daɗewa zata yi ba zata dawo jikin yaronta.
A hanya ne kiran Khausar ɗin yake shigowa wayarta, ta ɗauka tunda ita ba kati take da shi ba gashi ta ƙure limit ɗin bashinta.
“Aunty Khausar ayi haƙuri gani nan zaki ganni nan da ƴan mintina” tace da sautin murmushi bayan ta kara wayan a kunne.
“Lah Aunty Ilham ki bari kawai ki fara zuwa wurin su kada kiyi latti, za'a kawo mana abin karyawa yanzu daga gida nida Muftee”
Ta kalli kwanon dake ƙulle a cikin laida mai fari da baƙi da ta rungume. “Allah sarki Khausar kiyi ma umman ku godiya sosai don Allah”
“babu komai Aunty sai kin dawo, Allah ya bada Sa'a” da haka ta katse kiran daga bangarenta.
Wannan ya bawa Ilham damar kasancewa a cikin A&I Support Organisation da karfe 9:23 na safiya, rungume da envelope a hannu ɗaya kwanon abinci a ɗayan.
Da murmushinta ta gaida receptionist ɗin jiya, shima ya amsa mata da murmushin kana ya sanar da ita cewa hajiya Surayyan bata shigo ba tukunna amma yau ya bata matsuguni a ɗaya daga waiting chairs ɗin wurin ta jira isowarta.
AC ɗin wurin yana ratsata take fatan Allah yasa yau ta taho a kan alkhairi.
…..
Fitowa tayi rataye da jakarta, ta zura ƴar makullinta a cikin raminsa ta murɗa shi sau biyu ta garƙame ƙofar ɗakin, sannan ta juyo ta kalli tsakar gidan tana gyara zaman yalwataccen mayafinta.
Ƙarfe 8 da rabi na safiya amma yanda ta dawo ta same shi a daren jiya har yanzu ma a haka yake kaca-kaca kaman babu mutane a gidan, ga shinkafar da yara suka ci suka zubar tun jiya da rana har ya bushe a wurin.
“Hudah! Hudah!!” Ta kira cikin ɗaga murya.
Jin ba'a amsa ba ta mayar da kiran zuwa “Ameerah! Zakiyya! ɗaya a cikin ku tazo”
Yanda kasan bayan ita babu wani mai ji da magana a gidan, ko samun mai faɗa mata idan ma basa kusa ne ba'ayi ba. Sai ta ƙarasa ɗakin dake gefen nata ta ɗaga labule tare da yin sallama domin ƙofar ɗakin a buɗe yake already.
Matar dake zauna a jikin socket ɗin da ta jona dutsen guga, ta baza darduma da kaya a kai tana gogewa ta amsa mata sallamar.
“Ina kwana Maman Ameerah, ina su zakiyya?” ta haɗa mata gaisuwan da tambayar wuri guda lokacin da idanunta suka sauƙa a kan Ameerah dake kishingiɗe a kan dogon kujera hannunta riƙe da remote ɗin TV tana kallon Series, da ta san Aunty Surayyan leƙowa zatayi da ta tashi ta gudu cikin ɗaki don ai taji kiran taƙi amsawa, babu wanda ya isa ya saka ta aiki da safiyar nan.
Tace “Ameerah Gidan nan babu mutane ne kuka bar tsakar gida tun jiya da datti ba zaku saka tsintsiya ku share ba kuna ƴammata?”
Saurin miƙewa zaune tayi tana kare kanta ta hanyar faɗin “Yau fa Zakiyya ce mai dutyn shara da wanke-wanke aunty Surayyah, nawa sai jibi idan Hudah tayi gobe, ai kinsan ni bani ƙin yi.”
“Ina Zakiyyan?”
“Ta tafi Makaranta, kuma ta san itace zata yi ta tsallaka ta tafi”
“Toh yanzu sai ta dawo kenan za'a share gidan?”
Da mamakinta sai cewa Ameerah tayi “Ai zuwa ƙarfe biyu za'a tashe su, daman na faɗa mata haka zata dawo ta same shi yanda ta bari”
Aunty Surayyah ta tsaya kallonta galala, mahaifiyarsu da tayi kaman bata ɗakin sai a lokacin ta buɗe baki tace “Ai itama tace ba zatayi bane saboda kema baki yi naki ba jiya, sai kananun yaran nan ne na saka su suka tattara wurin sama-sama kafin su wuce Islamiyya”
Ta turo baki cikin ƙunƙuni tace “Toh umma ba wunin asibiti ba muka yi ba jiyan a jikin Kiki?. ko sai in dawo daga asibiti da almuru kuma in kama shara don Allah”
Aunty Surayyah dai ta sake musu labulen ta bar kofar ɗakin amma maganganun da suke musaya a tsakanin su bai bar shiga kunnenta ba, a inda maman Ameeran ke cewa.
“Ai da kin yi da safen babu wanda zai ce miki kiyi shara da daddare, gashi kin jawo min magana har ɗaki ina zaman zamana”
Allah sarki mahaifiyar Abdulhameed, ita kawai ta tuna a lokacin, da irin zaman da suka yi da ita shekaru 30 baya.
Kaman yanda rana yake fitowa yake faɗuwa babu fashi haka itama ta ɗauki hidiman gidan a wuyanta ko ruwa ko iska bai saka ta fasa ba, domin koda ta riga ta tsaftace gidan idan aka yi ruwan sama ko iska mai karfi ya shigo da datti sai ta sake fitowa ta share, saboda a rayuwarta bata son ƙazanta bata jin daɗin zama a cikinta shiyasa ta ɗaura ma kanta alhakin gyarawa a kowani lokaci.
Amma hakan bai saka ta iya tsallake ma zagi da cin fuska daga mazauna gidan ba, suna iri-iri babu wanda ba'a kiranta dashi, da wanda bata ganewa saboda Hausan ta bai yi ƙwari ba daga farko harda wanda zai yi daidai da iliminta.
Gashi ta haɗu da tsangwaman uwar miji don mahaifiyar su bata sonta ko kaɗan kasancewarta inyamura, har kafurta ta anyi saboda gani suke yi musuluncinta bai cika ba tunda bata bin Al’adun malam bahaushe.
Ba da son ran mahaifiyar su Muhammad ya auro Amina ba sai don iko da mahaifinsa ya nuna a kanta lokacin, shiyasa ta bada dama ma kannensa suka rainata matuƙa gaya, bayan Muhammad ɗin Shine babba a gidan baki ɗaya.
Idan tayi sharan haka za'a ɓata ta sake sharewa, a ci abinci a tara mata wanke-wanke kamar ƴar aiki, tukunyar abincinta kuwa kaman na runduna, a ciki da ƙwaryan ƙannen shi maza har lokacin da take ɗauke da tsohon cikin Abdulhameed a jikinta.
Sannan ita kanta Surayyan bayan ƙananun sharri da munanan ƙazafi da ta dinga binta dasu har dambe sun taɓa yi a lokacin ƴammatancin ta a gidan.
Tana da tabbacin hakkin Amina shi ya hanata jin daɗin Zaman Aure, ga kishiyoyi da suka kusan kasheta da asiri, tayi ta dogon jinya kaman ba zata rayu ba, har ta ƙare ta haƙura da auren baki ɗaya, tunda har ta gama zaman gidan mijin na shekaru goma bata taɓa ko ɓatan wata ba bayan kishiyoyinta suna haihuwa lafiya lau, kaman gasar haihuwar ma suke yi duk shekara saboda mijin su yana da rufin asiri sosai.
Sai kuma gashi kafin ta kaiga niman yafiyar Amina Allah ya ɗauki ranta ba tare da ya bari sun sake ganawa ba. Itama mahaifiyarsu da ta fara assasa abun gashi Allah ya ɗauketa ya bar Abdulhameed ɗin da basu saka shi ma a cikin lissafi a lokacin.
Shiyasa ta zaɓi ta ƙare sauran rayuwarta wajen kula dashi da kyautata masa ko Allah zai tausaya mata ya yafe mata kura-kurenta ba sai an isa filin ƙiyama ya tsayar da ita a gaban shi tare da Amina ba.
Ba don haka ba da ba zata zauna a gidan har ƴaƴan cikinta su taso suna abinda bai dace ba kuma bata da bakin magana ba, amma yanzu sune masu gida tunda ba da daɗewa ba Abdulhameed ya saka kuɗi ya mallaka ma ubansu gidan, ita alfarma yayi mata ya bar mata ɗakin da ya kasance na mahaifiyarta ta cigaba da zama dukda ya biyata kuɗin shi hannu da hannu.
Juyawa tayi zuwa ɗakin mai gidan a yanzu, Yayanta Muhammad, ta same shi zaune a parlour mahaifiyar Hudah tana zuba mishi abinci a plate.
“Ina kwana yaya” ta gaida shi tana zama a gaban shi a saman tsohon carpet ɗin dake baje kan tiles din dake walwalin sabunta yana ɗaukan ido. Gidan sabone dall Abdulhameed bai shekara biyu da yi musu renovation ba, a lokacin da ya sayi gidan maƙwabtan su zai fitar da nashi ɓangaren daban saboda Ikram, saboda bata samun kulawan da ya dace a tare da su, sai ya saka aka rushe gidan gaba ɗaya aka ɗaga sabon gini na zamani amma haka mahaifin shi ya dawo da tsoffaffin kayan ɗaki saboda a cikin ƴaƴansa da ƙannensa an rasa wanda zai canza masa carpet ko kujera koda mai sauƙin kuɗi ne, suna jira saidai shi Abdulhameed ɗin yayi.
Gyaɗa mata kai yayi saboda be kai ga haɗiye ƙosan da ya tura a baki ya kora da kunu ba. Ta juya wurin maman Hudah ta gaidata tana amsawa ciki-ciki saboda wani dalilinta.
“Yaya nace an kwantar da yarinyar Abdulhameed a asibiti jiya, ta faɗi ne ta samu rauni a hannu, duk munje asibitin mun dubota a jiyan”
Saida ya ƙarasa tauna ya haɗiye, yabi ya sake kurɓan kokon shi, sannan ya dubeta a tsanake. “Wata yarinya kenan Sharmama?”
“Yarinyar shi Ikram jikar ka”
Ƙosai guda biyu ya sake ɗauka a hannunshi ya tunkari bakinsa dasu yana faɗin “Ni ai cikin Jikoki na babu mai suna Ikiram” ya cusa ƙosan a baki ya fara taunawa yana kallonta kaman mai niman ƙarin bayani da gaske.”
“Haba yaya, sau ɗaya kawai, ko text kayi mishi a waya ka tambaye shi jikinta, zai ji daɗi Wallahi saboda ya damu sosai”
Sai ya girgiza kai yana murmushi, ya haɗiye ƙosan ba tare da ya kora ba, kana ya gyara zama ya jingina da jikin kujeran bayansa .
“Sharmama abun duniya ba zai taɓa rufe mun idanu na karɓi abinda yake ba daidai bane. Ban amshi wannan al'amarin ba lokacin da Abdulhameed baya da komai, ba zan karɓa ba don kawai Allah ya kawo mishi wadata.”
Cikin yanayin damuwa tace “Yaya wannan maganar ta wuce ai”
“ke kinsan ba mai wucewa bane, idan kuma na bari ya wuce a wurina yaya kike so in taya shi bayani a wurin Allah tunda na bashi goyon baya da nakasar shi yaje ya haifo mun ƴar gaba da fatiha ya kawota ƙarƙashin kulawana”
Ta kalli maman Hudah da tayi kaman an mannata a wurin da super glue ta kasa tashi ta tafi, sai ta shiga zuba wani ƙosai da kokon tana turowa gaban Aunty Surayyah don kawai ta cigaba da zama ta saurari gulma.
Akwai abubuwan da ta so ta tunasar dashi da yawa, yawan nasu laifukan a wuri Allah da ma hakkin Amina da ɗanta Abdulhameed dake wuyan su, amma sai ta fasa saboda maman Hudah, tace “wannan tsakanin shi da ubangiji ne, bamu san menene matsayin shi a wurinsa ba, idan yaga dama sai ya yafe masa. Amma ita Ikram menene laifinta? Haka zata girma ta fara fahimtar ita wacece daga wurin mu? Kada muyi sanadin rayuwarta ya shiga garari don Allah”.
Ta lura da yanda kalamanta suka shiga jikinsa amma sai yayi ƙarfin halin taɓe baki, ya karkaɗa mata hannu ta tashi ta bashi wuri.
Haka yake da tsananin kafiya da ƙi faɗi, tana fatan dai ba zai bari lokaci ya sake ƙure masa ba a wannan karon ma kafin ya juyo ya fuskanci gaskiya.
Kitchen ta koma ta ɗauki kwandon abincin da ta haɗa na asibiti kafin ta koma tayi wanka ta shirya. Ta so tayi ma mutanen gidan tayin zuwa asibitin sai ta rage musu hanya amma dake ranta a dagule yake sai kawai ta saka kwandon a seat ɗin baya ta shiga ta tada mota ta bar gidan.
A waje take haɗuwa da ƙanin Abdulhameed ɗin na uku Mukarram, ta tsaya suka gaisa sai ya buƙaci su tafi asibitin tare bayan ta sanar da shi can ta nufa.
Izini tayi mishi ya shiga seat ɗin gaba suka ɗau Hanyar Medi-plus hospital.
.
.
.
Da shigar su ɗakin da sallama suka hango shi tsaye rungume da Ikram wanda ta lafe a kafaɗar shi tana ƙananun kuka, shi kuma sai aikin jijjigata yake yi yana shafa bayanta kaman wata jaririya.
Yana ganin Aunty Surayyah ya sauƙe numfashi. “Aunty taƙi cin abinci tana ta kuka” yayi magana kaman zai fasa Ihu.
Ƙarasawa tayi ta karɓeta dukda yarinyar tana da zuri amma haka ta ɗauketa tunda mara lafiya ce.
Mukarram dai ya ajiye basket ɗin abinci ya koma gefe yana kallo.
Aunty Surayyah ta ɗago fuskar yarinyar da take nan fara tass, gashin kanta da parking ɗinshi ya warware mai tsananin laushi ya sauƙo har saman fuskarta.
“sorry Kiki kina son indomie?”
Girgiza kai tayi idanunta a rufe tana ƙara kukanta na shagwaɓa.
“Eggs fah? Na kawo miki banana ma.” Tayi maganan tana murmushi don haka yarinyar ta buɗe fararen idanunta ta zuba mata su.
Ƙarasawa jikin gadon ɗakin Aunty Surayyah tayi ta ajiyeta sannan ta shiga buɗe abubuwan da tazo da su ta fara zuba mata farfesun kaza da romo mai ɗan yawa kana ta tsoma soyayyan ƙwan a ciki tana yanyanka komai da cokali daidai bakin Ikram ɗin.
Tana kallonta saida ta gama ta dawo gefenta ta zauna zata fara ciyar da ita saboda hannunta sannan ta kawar da kai tana noƙewa.
“Uhm-uhm.. Daddy nake so ya bani”
Aunty Surayyah ta miƙe, tunda dai zata ci ai shikkenan.
Abdulhameed ne ya maye gurbinta a gefen Ikram ɗin yana bata abincin a baki yana bata chivita orange da ya tsiyaya mata a cup ta kora har saida ta kawar da kai ta ƙoshi tana ɗan ƙaramin gyatsa lokacin ta kusan cinye abinda ke cikin bowl ɗin kafin ya ajiye ya bata ruwa ta sha.
Sai a lokacin ma ya lura da Mukarram dake zaune a bakin ɗayan gadon dake ɗakin, aunty Surayyah kuma tana ta kimtsa musu wurin.
Mukarram yayi mishi jinjina da hannu kawai yana ƙaƙalo murmushi. Da mamakinsa sai Abdulhameed ɗin ya mayar masa martani domin har cikin ransa ya ji daɗin ganinsa.
Ikram na jikinsa yana shafa kanta a hankali Aunty Surayyah take masa bayanin abubuwan da zasu wakana a safiyar yau na rabon magunguna da zasu yi ma marasa lafiya, sai kayan abinci da kuɗin jinya ma masu ɗauke da manyan cututtuka masu wuyan magancewa irin su cancer, sickler, Aids da sauran su, sai kuma wheel chairs da hearing aids ga masu nakasan ji da tafiya harda test da za'a yi wa masu ciwon zuciya kyauta duka a bisa tallafin da suka karɓo daga gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu ciki harda World health Organisations WHO. Kuma bayan sun gama shirya yanda komai zai tafi wa’inda suka ɗora a kan abun da masu saka ido akan tabbatar da wanzuwar shi cikin gaskiya da amana jiran lokaci da umarni kawai suke yi su fara aikin su.
“Mun yi meeting da su sosai jiya kuma duk wani bayani da iyaka da ya kamata ayi musu nayi musu”
Ya jinjina kai “Komai yayi, Allah yasa mu fara lafiya mu gama Lafiya”
Ta amsa da “ameen” tana ajiye wayan da take karanto masa sauran tsare-tsaren da ta ƙarasa a daren jiya, sannan ta miƙe don lokaci ya tafi.
“Na gode Aunty Sharmama” ya furta ba tare da ya kalleta ba, idanun shi a kan ikram da ta fara gyangyaɗi. don haka babu amfanin amsawa tunda ba zai san ta amsa ɗin ba, sai kawai ta fice daga ɗakin Mukarram da ya samu ya karya yayi tamm cikin abincin da suka zo dashi ya rufa mata baya.
….
Tana zaune har 10:22am, har sanyin AC ɗin ya fara mata yawa kafin Aunty Surayyah ta iso.
Ilham tayi saurin miƙewa tana gaidata.
“Oh kece, biyo ni office” ta wuce ciki bayan ta karɓi wasu takardu a wurin receptionist.
Suna tafe Ilham tana ƙarewa cikin Organisation ɗin kallo. Ko ina fess ga shiru mai sanya nutsuwa da kukan tsuntsaye mai daɗi, sai ofisoshi da yawa a jejjere kuma a jikin kowanne akwai shuke-shuke da fulawowi, ga wasu matasan bishiyoyi da suka yi rumfa ma tsakiyar wurin ko ina abun sha'awa har suka shiga office ɗin Hajiya Surayyah mai ƙamshin daɗi Saboda turaren office na Bakhoor by Seemah(08021689184) da take yawan amfani da su.
“Zauna Malama” ta bawa Ilham matsuguni bayan ta zaga table ɗinta ta zauna itama. “Ki sanar dani me yake tafe dake?”
Ilham tana rawar jiki ta ciro takardun dake cikin envelope ɗin ta miƙawa hajiya Surayyah, ta saka hannu ta karɓa tana dubawa kafin Ilham ta fara mata bayani.
“Daman yarona ne, sickler ne, ciwon nashi ya tashi sosai muna kwance a asibiti, kuma babu kuɗin magani Hajiya, alluran da ake masa ba zamu iya siya ba, shine nake roƙon tallafinnan da aka ce za'a bayar dan Allah a taimaka a saka damu, dan girman Allah Hajiya” ta saka hannunta daya cikin ɗaya tana ƙanƙan da kai cikin roƙo.
Hajiya Surayyah ta nisa tana kallon Ilham, kafin kalmar da ta san Ilham ɗin ba zata so jin shi ba ya fito daga bakinta.
“Kiyi haƙuri.”
```````
Seemahwrites ✨