← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 26 OF 30

Chapter 26

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 16 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

Wattpad and Arewapen @Seemahwrites

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


26…. Rayuwa tana da wani hanya na ba ma ɗan adam mamaki, mamaki a kan kanshi. Sai kaga mutum ya daɗe yana burin zuwan wani dama ko lokaci saboda abinda yake so ya aiwatar a cikinsa, amma idan lokacin ya riske shi sai ya gagara aiwatar da abinda yake buri, saboda wannan daman babu ita, ko kuma yanayin ya sha banban da tunaninsa.

Kaman yanda ta daɗe tana kokwanto a kan A Moher, sai gashi a yanzu ko kallon shi ta kasa yi da tunanin dake ranta, nashi kallon ma ta fara kasa jurewa, wanda yana tsananta shi ba da wani nufi bane sai don ya fahimci komai da kowa da idanunsa.

Amma ita kunya take ji, ba kunyar shi kawai ba.
Harda kunyar kanta.

Shi da take tsammanin zai zamo abun Allah sarki a nan gaba, sai gashi ko da Allah ya tauye masa wani ɓari na jikinsa amma ita ce ke nima a ƙarƙashin sa.
Kuma ya gane ita wacece, ya bayyana mata hakan. Haka kuma yanayin da yake kallonta da shi a cikin idanunsa kafin ko bayan nan bai canza ba, yana kallonta ne kaman ɗaya daga cikin miliyoyin mutane da Allah yake haɗa hanyar su da taka a tsawon rayuwarka.

Ta banbance hakan ne da yanda ta ga yake kallon wa'inda suke da muhimmanci a rayuwar shi, kaman Kiki da Aunty Surayyah, yana Kallon su ne da zuciyarsa a maimakon idanuwa.

Babu kusancin da ya wuce abinda yake kawota gidan a tsakanin su, daga ranan da awara ya bayyama mata shi wanene kuma sai ta ɗauki matakan ƙara nisanta kanta da shi.

Banda ranan da ta makara saboda tuyan masa yana da ɗaukan lokaci, da safe kafin ya fito zata gama shirya musu abun karyawa a dining table ta zuba ma kiki nata ta bar wurin, tun da ta lura cin abincin da ya fara hucewa ba damunsa yayi ba, ko ta zuba da zafi ma sai ya jira ya huce ya fara ciyar da kiki kafin ya kai nasa bakin.

Haka da yamma idan ta gama yiwa Kiki abinda ya dace zai dawo ya samu abincinsa, kuma kafin ya gama ci ya huta ta gama na dare saidai tayi masa sallama ta wuce.

A bisa roƙon Aunty Surayyah ta nimawa Kiki kayan Fulani na talent show ɗinsu.

“Daman babanta bafulatani ne?” Ilham ta samu kanta da tambaya don Abdulhameed bai yi mata kalan Fulani ba, Hausa ma idan yana yinta kaman wanda ya koya ne kawai saboda zama cikin hausawa.

“A’a yace wai mahaifiyarta ce bafulatana”

Ta ji maganar a wani iri, kaman itama Aunty Surayyan bata da tabbacin yaren matar da suka zauna da ita a gida ɗaya, duk da ma zuciyarta ta daɗe tana tambayar mahaifiyar Kiki tana ina ne a halin yanzu? amma bata bari tambayar ya iso kan harshenta ba. Ta fi dai kyautata zaton mutuwa tayi, ko hala rabuwa suka yi, domin bayan a kan zancen kayan fulanin bata taɓa jin wani a cikin su ya ambace ta ba.

Akwai gidan da ake bada hayan kayan fulani a unguwan su, kuɗin da Aunty Surayyah ta bata kuma ya kai a siya sabo harda canji, shiyasa ta ba ma matar kuɗin kawai tace ta taimaka a siyo ma Kikin harda sarƙa da awarwaron murjani, ƙwarya, ludayi da kuma faifayi.

A weekend ta karɓi kayan ta wanke ta goge mata tare da kayan Hashim da ya tara da ma nata saboda yanzu bata samun lokaci sai weekends ɗin, sai kuma na Muftee da na Ihsan.

Gajiyan wanki da gugan yasa da wuri ta kwanta ranar asabar bayan ta ajiye ma Hashim taliya da manja da yaji.

Fitsari ya tashe ta ƙarfe ɗaya na dare, ta kunna tocin wayanta tana haskawa saboda nepa sun ɗauke wuta, ta ci karo da kwanon abincin a inda ta ajiye mishi, da ta shiga ciki ma gado yana gyare tsaff, mai birkitawa da juye-juyen danna wayarsa baya kai.

Ta kaikaita murfin abincin kada yayi tsami ta gyara tayi kwanciyarta don ya sabar mata da haka, bata da ƙimar da ko wani uzuri ne ya riƙe shi ya kirata ya sanar da ita, balle ma idan wani abun ne yake yi shi ya sani, bata da nutsuwar da zata saka damuwar shi a cikin kanta, bata jin kishin Hashim a ƙirjinta ko me zai yi, gargaɗin da tayi ma Khausar ma Saboda ita ne, saboda ta san ba kowace mace bace zata iya irin zaman da take yi.

Da asuba kuwa da zata shiga yin alwala sai gashi nan kwance cikin wata sabuwar shadda yana ta minshari, ga sabon hula da takalmin da ya cire su a inda ya jefar da babban rigan kayan, sai takardan cupcake da takeaway ɗin da ya gama cinye abun ciki har ƙashin saida ya tattauna cokali kawai ya bari, sai goran soft drink. har tayi shirin fita asibiti kuma bai farka.

Ranan talata ya kama ranan da za'a yi talent show ɗin su Kiki, kuma kowani yaro ana bashi pass guda uku ne na iyayen shi biyu da sibling ɗaya idan an fi haka yawa kuma saidai ku bada kuɗi ku siya wani pass ɗin.

Sai gashi guda ukun da aka bayar ma Abdulhameed ya rasa yanda zai yi da su, Kiki bata da kowa sai shi, kuma shima tun da ya rasa Nne yake jin shi kaman bayi da kowa, sannan mura mai zafi ya kama Aunty Surayyah ko A&I bata iya zuwa ba ranan Monday, ba zai so ace Kiki ne kawai bata da familyn da zata nuna ma sabbin ƙawayenta da malaman su ba.

Da ya samu shiga yi mata ya jiki bayan ya dawo daga sallan asuba ta amsa da “Jiki da sauƙi Abdulhameed, tun jiya ma naso na karɓi pass ɗinmu, toh ciwon kai ne ya hana ni fitowa”

“Har zaki samu zuwa Aunty Sharmama?”

Cike da ƙwarin guiwa tace “In sha Allahu, mura ce fa kowa yana yi, zan sha magani in saka takunkumi ai ba zamu barka kai ɗaya ba.”

“Guda biyu ne” yayi maganan yana mata kallon tambaya.

Cikin fahimtar abinda yake nufi tace “zamu je da duk mai niyya, ko mu biyu ma mun isa idan ta fito mu tafa mata, kada ka damu”

Ita ta saka shi ya shiga ya gaida mahaifinsa kafin ya koma ɓangaren sa.
Yanda ya sauƙa a kan guiwowin shi, har ya miƙe ya juya ya tafi Mahaifin shi bai ɗago ya dube shi ba, balle ya sani ko ya amsa gaisuwan ko bai amsa ba.

Itama Aunty Surayyah da ta gama ƙoƙarinta kowa a gidan ya dinga kawo mata uzurin da zai hana su zuwa sai ta dawo wurin Ilham dake goge kwanukan da ta gama wankewa tana jerawa a dish rack da kitchen cabinet.

“Ilham kina ganin zaki iya zuwa ma Ikram talent show din da za'a yi a makarantarsu”

Da hanzari ta amsa da “Eh Hajiya, zan je” murmushin jin daɗin tayin da aka mata ya bayyana a kan fuskarta, ta dunƙule farin kitchen towel ɗin a hannunta ta tana fara'a sosai.

“Toh ba sai kin sake ɗora abinci ba, idan kin gama abinda kike yi sai ki zo ɗaki na mu shirya kada mu makara”

Ta gyaɗa kai tana amsawa da “toh hajiya”

Bata fara tunanin zuwa da kayan jikinta ba saida ta je ta samu Hajiya Surayyah cikin dogayen rigunan saudiyya masu manyan mayafai ɗinnan orange colour da fari-fari a jiki. Sai agogo, abun hannu da zobe da ta jera a hannunta amma tayi ma Ilham kyau ba na wasa ba. Ana ganinta da Hajiya Surayyah a haka a waje za'a gane ƴar aikinta ce, wataƙil ayi tunanin ma ba a birni ta faro rayuwarta ba saboda yanda rayuwa ya maida ita.

“Na duba miki kayan da zai yi miki saboda babu lokacin da za'a je nema miki koda abaya ne saidai wannan, amma shi bayi da hijabin da zai shiga da kalan, saidai gyale, amma babba ne. Idan an gama sai ki tafi da su gida ki cigaba da sakawa”

Bata jin tana da wani zaɓi ko ta cewa a kan abubuwan alkhairin da Aunty Surayyah bata gajiya da mata, kuma bata ba ta damar tsayawa ta ɓata lokaci wurin mata godiya ba ta umarceta ta sauya kayan jikinta zuwa wanda ta bata sannan ta zaɓo mata sarƙa da ɗan kunne, takalminta ne aka yi rashin sa’a yayi ma ilham yawa sosai, duk da skirt ɗin kayan ma saida ta hauro da shi har cikinta kafin tsayin yayi mata kuma saida a aka kame kunkumin da clip Saboda a tsayi da garin jiki ma Aunty Surayyah tayi mata fintinkau.

Sai Aunty Surayyah ta kira Mukarram ƙanin Abdulhameed dake zama a shagon siyar da takalma yana samun na kan shi, tace ya nema mata baƙin takalmi size 38 ya ba ma masu delivery su kawo yanzu.

Saboda tsananin daɗewan da tayi rabonta da kafa ɗauri da ƙyar ta samu ɗankwalin yayi mata yanda take so a kanta, kaman ba ita bace ko biki suka je a family haka ƴammata da ma matan Aure zasu yi ta layi da ɗankwalayen su a hannu idan suka ga irin wanda tayi a kanta.


Da Ilham ta ɗan goga powder da man leɓe ta yafa gyalen sai taga ta fito daban, kaman Fidelan Maama da Taa, wanda duk wani abun kwalliya ko na yayi idan suka gani sai sun siya mata saboda tayi farin ciki, saboda ado yana sakata farin ciki sun sani, kuma sun bata goyon baya da aljihun su.

Duhun fatar yana nan, canzawar kamannin yana nan, amma ta daɗe bata ga ita da kanta tayi ma kanta kyau ba sai yau.

Aunty Surayyah ta kalleta daga sama har ƙasa lokacin Mukarram ya kawo takalmin da kan shi, da yaji inda zasu je sai yace shima zai bi su idan babu damuwa.

“Kinga yanda kika fito?. Masha Allah”

Ilham ta kasa danne Murmushinta saboda ta san ba daɗin baki bane zalla.

“Murmushin ki yana da kyau”

Tace lokacin da Abdulhameed ya rufo gidan ya ƙaraso ya same su a jikin mota.

Daga nesa ya hangota tana murmushin, bai sake kallonta ba har ya zo ya wuce su yana faɗin “mu je” tunda ya san zasu ji shi, amma ya ɗan yi mamakin ganin da ita zasu tafi.

Mukarram ne ya shiga mazaunin driver, Abdulhameed a gefen shi. A gidan baya kuma Aunty Surayyah ce zaune a bayan seat ɗin mukarram Ilham tana bayan na Abdulhameed.

“Mukarram kashe AC ɗinnan kafin mu isa ina yoyon hanci” cewar aunty Surayyah tana maƙala takunkuminta tun lokacin jin yanda motan ya ɗauki ɗari.

Mukarram da Ilham suka murmusa jin abinda tace, Abdulhameed kuma bai san me aka ce ba sai ganin glass ɗin window suna sauƙa kawai yayi.

Ya juya yana kallon mukarram ko wani matsalan ne sai yayi masa nuni da Aunty Surayyah da babban yatsar shi a baya don haka ya juya yana kallonta.

“Lafiya dai?” ya tambaya ganin takunkumi a fuskarta.

Saida ta sauƙe tunda ba zai ji abinda zata faɗa ba kafin tace “Kada in yi na yara ne a samu mai kora ni gida, shiyasa nace a kashe AC ɗin”

Dariya ya kufce wa Ilham, ta mayar da kanta jikin windown gefenta tana yi shi kuma sai ya amsa ma Aunty Surayyah da “Allah ya sawaƙe” kawai ya juya ya fuskanci gaban shi tare da ɗora guiwar hannun shi dake maƙale da agogon fata a daidai inda sleeve ɗin baƙar rigar jikin shi ta tsaya a jikin windown da aka buɗe, ya ɗan dafe kan shi.

Suna taɓa hira sama-sama a tsakanin su ukun banda wanda bai san me ake cewa ba ma, har suka isa ƙofar hall ɗin da za'a yi show din, suka nemi masu siyar da pass aka siya ma Mukarram kafin suka shiga ciki.

Suna jin ance masu cultural dance zasu shigo suka daɗa mayar da hankali. Abdulhameed, Aunty Surayyah da Mukarram suka saita Cameran da zasu yi recording Ikram.

Sai kuma ita dake zaune a can baya saboda bata son ɗaya daga cikin su ya lura da ita Musamman shi Abdulhameed ɗin da kan shi.

Kiki suna shigowa kan stage ta fara baza idanu saida ta hango daddynta ta ɗaga mishi hannu tana dirin murna, har saida ƙwaryan kanta ya kusan faɗowa malamar su tayi saurin riƙewa.

A lokacin da suke yin rawar kuma Ilham ta ji inama itama tana da waya mai yin video da ta ɗauka ta ajiye.

Da suka gama aka yi musu tafi sosai, wa'inda suke gaba da su suka zo suka gabatar da nasu category ɗin kafin aka zo bada kyauta ma wa'inda suka yi shura a cikin kowanne. Saidai su ƴan Nursery duka an basu kyauta don haka kiki ma ta samu.

An yi hakan ne maganin rikicin ƙananun yara kuma yayi aiki, don da murnanta ta fito aka fara ɗaukan su a hoto.

“Ayi mun da Mimi”

Ta ƙaraso jikin Ilham ta riƙeta.
Sai Ilham ta sunkuya ta ɗauketa a hannunta ayi musu hoton a haka.

“Kun shirya?”

Mukarram ya tambaya yayinda ya saita cameran wayan Abdulhameed a kansu domin yafi fito da hoto.

Kiki ta jingina kanta a jikin na Ilham a lokacin da ya ɗauka ya sake wani a take, sai mamaki ya bayyana a idanun Ilham a na farko a na biyu kuma murmushin jin daɗinta ne ya fito.

……
6:06pm

“Sannu Filiyan” Ilham ta ƙaraso inda Ihsan ta kifa kanta a jikin gadon Muftee, shi kuma yana shafa mata kan a hankali da hannun shi mai maƙale da Canular.

Ta miƙe zaune jin muryar yayarta daman ba barci tayi ba, hannunta yana kan mararta dake ciwo sosai sai faman cije baki take yi.

“Ko zamu je wurin likita mu roƙe shi ya rubuta miki magani ne mu siyo, ko yayi miki allura?” ta tambaya cike da kulawa.

Ihsan ta girgiza kai “A'a dan Allah, idan na sha burufen ma zai bari, period cramps ne”

likitan dake on duty a lokacin har sun yi exchanging numbers Saboda yanda ya matsa mata, kuma idan ya kirata wani lokaci tana ɗagawa, sai yanzu kawai su je wurin shi ace tana period ya bata magani?.

“Toh mu je in siya miki maganin sai ki tafi ki huta ni zan kwana a nan”

Ihsan tana cikin zafin ciwo amma saida ta tambayeta game da suturar da ta gani a jikinta duk da Ilham ta mayar da hijabinta a kai ta saka gyalen da takalmi a cikin laida, ta labarta mata duka abinda ya faru kafin su rabu sannan ta dawo ɗakin yaran.

Nurse ta gani riƙe da hannun Muftee mai canular tana tsirga mishi ruwan allura a ciki.

Ta ƙarasa da sassarfa tana cewa “Nurse an yi mishi alluran shi fah!”
Ihsan ta jaddada mata hakan kafin ta tafi.

Ko arziƙin kallo Ilham bata samu ba saida ta gama abinda take yi sannan ta juyo tayi mata kallon hadarin kaji a daƙile tace “malama zaki gwada mun aiki na ne?” Ilham tayi shiru bata amsa ba har ta bar wurin.

“Mimi yaushe zamu je gida?” Muftee ya tambaye ta lokacin da ta zauna a gefen shi yana shigewa jikinta.

“Likita yace mun kusa in sha Allah, kayi ta addu'a ka ji, bari na zuba maka abinci”

Ta fito d takeaway ɗin haɗaɗɗen shinkafa da coleslaw da kaza ta buɗe musu suka ci, daman souvenir biyu aka bata har da na Abdulhameed da yace bayi buƙata shine ta ba ma Ihsan ɗaya ta tafi da shi, ga su samosa da springrolls, donut da cupcake duk a ciki da suka yi matuƙar daɗi, ta duba sticker ɗin dake manne a jikin containern ba don tana da kuɗin siya ba sai don ta ga sunan wanda Allah yayi wa baiwar iya small chops har haka.

Ummee’s Baking Empire (UBE) ta gani da lambar waya kamar haka 08173775170 kuma abin mamaki location ɗinta a kano ne, kenan tun daga kano aka yi ordern su har KD? Ko da yake inganci da daɗin shi ya biya buƙata sosai.

Basu daɗe da cin abincin ba Muftee ya fara mata gyangadi, ta zaunar da shi a jikinta kada ya kwanta cikinsa ya ɓaci, sai kuwa ya tashi mata da safe babu wani kuzari a jikin shi.

Abun har ya fara bata tsoro ganin ko magana baya yi sai wani nishi kaman wanda aka dannewa ƙirji.

“Ibrahim. Ciwo ne kake ji?”

Ya lumshe idanun shi ya buɗe ya sake lumshewa, tsoro ya ƙara kama ta.

“Muftee, yaya ne?”

Still ba amsa.

A hargitse ta ƙarasa tayi ma Nurses ɗin da suke cikin ward ɗin magana. Kuma da wanda tayi mishi allura jiya ta sake mishi sai gashi har abinci ya ci ya sha kunun gyaɗa kafin Ihsan ta dawo ta karɓeta ita kuma ta tafi.

Saidai ta riga da ta makara.

Ta makara a laraban da ya canza ƙaddarar rayuwarta gaba daya.

Ta makara a laraban da bai nuna kyawun da juma'arta zata yi ba.

Da taje gidan ta samu Kiki saboda an basu hutun kwana ɗaya su huta bayan taron da aka yi jiya, amma Abdulhameed har ya tafi wurin aiki sai Aunty Surayyah ta tarar don itama muran ba wai ya saketa bane.

Wajajen Goma da rabi wayan Ilham ya shiga ruri, har yayi na farko ya tsinke bata ɗauka ba kasancewar a kitchen take barin shi ita kuma ta raka Kiki toilet.

Da ta koma jikin wayan ganin missed calls guda 12 daga Ihsan, 5 daga Maama, 20 daga Aliyyu sai 15 daga Addah Iman yayi matuƙar tsorata ta.

Abu ɗaya ta kawo ma ranta.
Muftee ne ya rasu.

Amma kiran yaya aliyyu da Addah Iman fah?, Abinda ya faru ya fi haka girma tabbas.

Kiran Ihsan na 13 ne ya shigo wayan tayi saurin ɗauka, sai kuka kawai ta ji Ihsan tana yi ba tare da tace komai ba.

A take taji zufa yana yanko mata, kirjinta ya shiga dukan uku-uku, fargaba mai tsanani ya rufeta.

Ta fito parlo da sauri zata bar gidan idanunta suka sauƙa a kan Kiki.

Sai ta rasa yaya zata yi da yarinyar.

“Kiki zo mu je wurin Aunty Surayyah ki zauna kafin in dawo”

Ta kalleta tana turo baki “ina zaki je?”

Bata kulata ba ta ruƙo hannunta suka fita ta jawo ƙofar kawai domin babu key a jiki, ta ƙarasa da Kiki har jikin ƙofar da zai sada ta da ɗaya ɓangaren gidan sannan ta sake ta.

“Je ki wajen Aunty Surayyah maza, yanzun nan zan dawo”

Ta ga yanda yarinyar ta kwaɓe fuska tana shirin kuka amma sai ta juya kawai da sassarfa ta bar gidan.

Bata sani ba ashe kiki biyota tayi. Mai gadi sai yayi tunanin tare suke kuma ba da nisa zasu je ba don haka bai dakatar da ɗaya daga cikin su ba har suka fice ya rufe ƙofa.

Cikin Sa'a Ilham tana fita ta samu napep, ko faɗa mishi inda zata je bata yi ba ta shiga suka fara tafiya, idan ma ba hanyarta suka nufa da wacce take cikin napep ɗin ba sai ta sauƙa a bakin hanya ta shiga wani.

Gudun da zuciyarta ke yi, da kuma hayaniyar da ƙwaƙwalwarta yake wajen canko mata abinda ya faru ya saka har suka wuce bata lura da Kiki dake ƙarasowa jikin napep ɗin ba.

Tana ganin sun tafi sun barta kuwa ta fara kuka.

Kafin wani a unguwan ya jiyo kukanta wata baƙar mota mai bakin tinted tayi parking, farar matar dake sanye da baƙin shades a idanunta ta fito daga mazaunin driver ta zagayo ta tsaya a gaban Kiki da murmushi a fuskarta.

“I finally got to see you my Little angel” ta zare gilashin idanunta kana ta miƙa ma yarinyar hannu. “Zo, zo na kaiki wurin Daddyn ki”

Babu musu Kiki ta kama hannunta, matar ta share mata hawayen idanunta sannan ta ɗauketa ta saka a cikin motar dake ƙyallin sabuntaka ta saka mata seatbelt sannan ta zaga ta shiga suka bar unguwar.


````````````
Seemahwrites ✨


ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
Chapter 26 · 0% Book details