← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 13 OF 30

Chapter 13

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites*

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)

Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


13…. “However, A faɗa mata bana son wasa, bana son fashi, bana son latti, bana son ƙazanta and I absolutely don't tolerate anything that will harm my daughter, kada tayi saken da ko ƙwaro ne zai cije ta under her watch.”

Da zuciyar shi ɗaya yayi maganan amma sai ya ga Aunty Surayyah tayi murmushi tana gyaɗa kai.

Da ace Abdulhameed kaman sauran maza yake haka ma Kiki kaman sauran yara take, da ta faɗa mishi duniyan nan gabaki ɗayanta ƴar haƙuri ne.

Abinda yake nima a wurin Nanny da babu abinda ya haɗa ta da ƴar shi bayan albashin da za'a dinga biyanta duk wata, ko uwar da ta tsuguna ta haifa masa yarinyar ba zata iya ba.

Amma sanin wanene shi da irin gwagwarmayar da yayi a rayuwa tun da ƙananun shekarun shi yasa zata cigaba da mishi uzuri ta bi shi a yanda yake har lokacin da komai zai wuce kaman bai taɓa faruwa ba.

“Yaushe zata fara zuwa?” ya tambaya lokacin da suka yi parking a gaban ɓangaren shi, ya sake ɗaukan Kiki a hannun shi wanda iskan mota yasa ta koma barci.

“Ban kirata ba tukunna, na fara niman amincewar ka ne, but I'll call her now”

“Okay, thank you so much Aunty sharmama”

Bayi gajiya da mata godiya, kuma yana jin kamar duk godiyan da zai yi mata bai isa ba, don haka zai cigaba da mata godiyan ne koda hakan zai nuna mata irin darajar da take dashi a idanunsa.

“Babu komai” tace tana juya kan motan ta koma office.

Kwana huɗu kawai amma sai yake ganin gidan yayi mishi ƙura sosai. Ya kwantar da kiki a kan gadon shi sannan ya fita zuwa store ɗin kitchen ya ɗauko tsintsiya da mopper.

Babu ɓata lokaci ya shiga yin shara, ya ƙwalƙwalo ko ina ya zuba dettol a ruwa yayi mopping, ya bi ya ɗauko napkin ɗin goge-goge.

Ko ina shiru, duniyar shi ta riga da ta saba da wannan shirun, don ya manta da yanda hayaniyarta yake baki ɗaya.

Amma yanzu tunani daban-daban ne suke karakayya a cikin kan shi, saboda kwanan nan yana yawan mafarkin Ikram da tunaninta.

Ikram mahaifiyar ƴar shi Ikram kaman yanda ya mayar ma abinda ta haifa sunanta saboda hakan ne kawai daidai.

Ya kwana biyu yana Tunanin gaskiyar da ba kowa ya sani ba bayan su uku, sai kuma Ubangijin da ya halicce su duka.

Ya kuma ɗau Alƙawarin ba zai taɓa bari Kiki tayi rayuwa irin ta mahaifiyarta ba. Zai yi iya ƙoƙarin shi a matsayin shi na uba wajen ganin ya kareta daga dukkan cutarwa.

Kafin wani lokaci ko ina yayi fess sai kamshin air fresheners dake tashi. Yayi musu ordern abinci, ya koma ɗakin shi da Ikram ke kwance ya shiga bathroom yayi wanka da ruwa mai zafin da ya narka duk wata gajiyan dake tattare da shi kana ya shirya cikin navy blue shirt da dogon wando fari tass.

Tunanin yanda Kiki zata ɓata mishi wandon da abincin da zata ci yasa ya canza ta zuwa gajeren wandon khaki, in yaso idan suka gama sai ya cire ya mayarda wanda yayi niyyan sakawa tun farko.

Da abincin ya iso saida ya jirata ta tashi da kanta lokacin ma biyu ta gota.
Da yunwa ta farka kaman wanda aka yiwa yasa a ciki, kuma saida ya yanka mata apple taci bayan ta karya kafin su baro asibitin, sai suka fita dining ya fara bata abincin a baki kafin ya shiga da ita ya wanke ta tass itama.

Daɗewan da yayi bai koma jikin wayan shi da ya ajiye ba yasa yaci karo da saƙonni barkatai lokacin da ya ɗauka.

A ciki har da missed calls guda biyu daga wani number da yayi saving da “Excellency”

A take yanayin fuskar shi ya sauya.

…..

Zaune take a waje da sanyin safiya, tana wankin kayan shi da ya gaji da ganinsu a zube ya siyo sabulu ya bata, sai gashi yazo zai kunna mashin ɗin shi zai fita daga gidan ba sannu ba madallah, ko kallo bata ishe shi ba, don kallon nata ma ɓacin rai yake ƙara masa.

“Baban Muftee”

Ta miƙe tana tsane hannunta daga ruwan kumfan.

“Yaya akayi kuma? Kina ganin dai wurin aiki zani ko!” Ya tambaya yana muzurai kada taga daman tambayan shi wani abu ganin ya sayi sabulun wanki.

Shima yanzu haka kuɗin yake nima, da zata bashi karɓa zai yi yayi mata godiya, dan albashin ya ƙare tass tun wata bai je ko ina ba saboda hidiman da ya saka a gaba.

Sai ta sunne kai tana mutstsuka hannun nata cikin fargaba tace
“Daman Filiyan ce zata zo mun gobe”

Yamutsa fuska yayi “wacece Filiyan?” ya tambaya kaman da gaske bai sani ba.

“Ƙanwata Ihsan” ta bashi amsa.

“ƴar Jamila?”

Gyaɗa kai tayi amma bata amsa ba, don yanda Maama take mata matsayin uwa, kuma ta riƙi ɗan shi a matsayin jikar ta, ya kamata ace ta samu girmamawa daga gare shi.

“Toh yanzu niman izini kike yi ko kuma sanar dani kike?”

“Ɗan zaman asibitin ne zata taya ni na wani lokaci tunda bamu san zuwa yaushe zasu sallame mu ba.”

“Idan dai izini na ake nima toh ban yarda ba, idan kuma gidan naki ne ai sai tazo mu gani Ilham” Ya faɗa yana nuna ta da key din mashin ɗin shi, ya ja dogon tsaki ya kama hanyar shi ya fita yana mitar da ta zame masa jiki.

Ta dai jishi amma har duniya ta naɗe bata jin zata iya hana Ihsan zuwa inda take, kuma taimakon da zata mata Hashim ɗin bai nemo wanda zata mata irin shi ba. Ko babu komai zata samu lokacin da zata cigaba da ƴan sana’o’inta a cigaba da samun na rufin asiri, tunda gashi ta samu kanta a zamanin da mata su ke kula da kansu a gidan aure.

Ƙarasa wanke kayan tayi tass ta dauraye su, wasu saida ta shanya a jikin garu, saboda yawa igiyan shanya bai ɗauke su duka ba.
Ganin ba damina bane tayi shirinta na tafiya asibiti idan ta dawo sai ta kwashe lokacin sun bushe don idan ta Hashim ne saidai su kwana a wurin.

Bashin Ƙarago ta karɓa taje musu da shi asibitin suka sha tare da kunun sadaka ita da Muftee suka yi tamm, amma tun a nan ta fara tunanin dabaran da zata yi su samu na abincin rana, gashi ɗan abinda sauran suka tarfa mata cikin kayan tallafin da suka samu har ya ƙare daman ba yawa.

Ta yi tagumi tana kallon matar dake canza ma jaririyarta da bata da lafiya pampers, ga yarinyar ƴar ficiciya, har oxygen aka saka mata duk abun tausayi. Wayanta dake gefen Muftee ya shiga ruri, tayi saurin ɗauka kada ƙaran shi ya damu majinyatan dake ward ɗin, ta ma manta ne da ta iso bata saka a silent ba.

“Hello” tace bayan ta ƙara a kunnenta ganin babu suna a kan lambar, ma'ana bata yi saving ba.

“Malama Ilham ina kwana, Surayyah Kagarko ce”

Tsugul ta miƙe tsaye kaman wanda aka tsikara da allura. “Ina kwana Hajiya!”

Ta amsa da “lafiya ƙalau. Zaki iya zuwa ki same ni yanzu? Kaman yanda nayi miki alƙawari wani abu ne ya samu amma ba irin wancan bane”

Hannu ta saka ta kare bakinta cikin tsananin farinciki, tayi ƙoƙarin daidaita kanta tana faɗin “gani nan zuwa yanzu Hajiya, na gode, na gode sosai”

“Saii kinzo” Hajiya Surayyah ta katse kiran, Ilham sai ta shiga hamadala ma Ubangiji, don duk abinda za'a ce maka ya samu in sha Allah alkhairi ne duk da ma bata san menene ba tukunna.

Zata ɓata lokaci idan tace zata tafi da ƙafa, dan haka ta roƙa aron naira ɗari uku a wurin matar da suka fi shiri da ita a ward ɗin.

Har ta danna kiran Khausar ya shiga, mai ta tuna sai ta katse kiran, kawai tace ma mutanen ward ɗin su ɗan saka mata idanu a kan Muftee dan Allah bari ta je ta dawo.

“Mimi ki siya min minti” shine abinda yace mata da zata tafi.

“In sha Allah yaron Mimi” ta sake mishi murmushi, suna daga ma juna hannu ta tafi.

Babu ɓata lokaci sai gata a cikin A&I Support Organization, kuma kai tsaye aka kaita ofishin Hajiya Surayyah, ta rage tsayinta ta gaida matar mai mutunci sannan ta zauna a kujeran da ta nuna mata.

“Kaman yanda na faɗa miki ba tallafi bane irin wancan, aiki ne na samu mai kyau shine zan miki tayin shi idan zaki iya”

Aikatau shima ba baƙonta bane, tayi aiki a gidajen masu kuɗi saidai idan jikin Muftee ya kwantar dasu a asibiti na tsawon lokaci tana komawa sai ta samu an kawo wata a madadinta a bata haƙuri.

“In sha Allah zan iya Hajiya, a ina ne?”

“Toh ai baki ji wani irin aiki bane ba” Aunty Surayyah ta faɗa da murmushin ganin ɗokinta, sai ilham ma ta murmusa ta gyara zama tana sauraron ta.

“Aikin raino ne, yarinyar ɗan yayana, ta kusan cika shekaru huɗu”

“Na kwana ne Hajiya?” ta tambaya damuwa yana maye gurbin farincikin da take ciki, kada ace zata sake ganin samu ta ga rashi ne.

“A'a daga safiya ne ƙarfe 7 zuwa 5 na yamma a ranakun mako, kuma banda weekend”

Ta ɗan yi jigum tana tunani. Yaya zata yi da Muftee yanda bata da mai zama mata a jikinsa? Filiyan zata zo amma hutun ta na ƙarewa zata koma BUK.

“dubu dari ne albashin” muryar Hajiya Surayyah ya ratsa dodon kunnenta.

Ta waro ido tare da dafe ƙirji “Dubu ɗari Hajiya?!”

Aunty Surayyah ta jinjina kai. “Shiyasa na kira ki saboda alƙawarin da nayi miki”

Tana jujjuya kai tace “zan iya hajiya, in sha Allahu zan iya”

Koda aikin dubu biyar zuwa goma ta samu indai kuɗi zasu shigo hannunta zata yi, balle aikin dubu goma sau goma.

“Amma bayi da Mata a halin yanzu, saidai duk a gida daya muke rayuwa ɓangarensa ne kawai daban, kuma da kin zo kin shiryata ta tafi Makaranta shima zai fita aiki sai ki samu fili ki kimtsa gidan, idan an tashe su zaki je da driver ku ɗaukota ki sake mata wanka ki bata abinci, toh yana dawowa zaki iya tafiya gida abun ki.”

“Zan yi hajiya, wallahi zan yi, yaushe ake so na fara zuwa?”

“ko gobe ma, ina kina da mai zama miki a jikin yaron ki?”

Ta ɗan sosa ƙeya ta cikin hijabinta “A dan yi mun alfarma zuwa jibi Hajiya, ƙanwata zata zo daga kano zata taya ni”

“Shikkenan Allah ya kaimu jibi ɗin. Idan kin shirya sai ki kira ni in yi miki kwatancen gidan.”

“In sha Allah Hajiya, Nagode fah, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma”

Bata bar A&I ba saida naira dubu biyu a cikin purse ɗinta kamar wancen ranar.

Saboda farin ciki bata bari ta koma asibitin ba Ta kira Maama ta sanar da ita. A yanda tayi ta mata addu'an Allah yasa ya zame mata alkhairi ta bata shawaran ta kula ta riƙe amana kuma Ilham taji ɗauka.

“In sha Allah Maama na, zan kiyaye”

“Yauwa Fidela, hidiman yara kuma saida haƙuri, dukda kema kina dashi amma ba zaki haɗata da wanda kika saba dashi ba, kuma sai kin bata matsayin ƴa a wurinki kafin ta ɗauke ki a matsayin uwa sai kuji daɗin zaman. Kada ki dinga duba kuɗin da zaki na samu kinji? Amana ne aka baki wanda Allah zai tambaye ki a kanshi ranan ƙiyama, dan haka kiyi ƙokarin cika shi da zuciya ɗaya. Allah ya kaɗe fitina”

Saidai abinda Ilham bata sani ba shine; kamar yanda kuɗin aikin nan yake da yawa haka ma wahalar shi, haka ma ƙaddarar da zata datse mata farin ciki ta saka ta zubar da hawaye mai tarin yawa.

Yanzu dai abinda ya rage shine yanda zata sanar da Hashim, dan idan ya samu labarin kudaɗen da zasu fara shigo mata shikkenan zai sake janye jikinsa daga sauƙe hakkokin da suka rataya a wuyan shi, na Muftee da ita kanta.
.
.
.
Banbanin da ya shigo yana yi ne ya saka ta tsumewa a daƙin har saida ya ƙaraso ciki, ya sameta durkushe da dutsin guga a hannunta tana danne kayan shi da ta wanke da safe.

“Kina jina kika yi mun banza ko? Mara godiyan Allah!. Har ki samu wacce zata ɗaura ma kanta dawainiyar ki kice mata bakya so? Ina saboda nace kada Ihsan tazo mun gida ne nima zaki raba ni da ƴan uwana?”

Ta dora dutsen a kan kifaffen kwanon samira sannan ta miƙe tsaye.

“Idan zancen khausar kake yi da tazo cemun tayi tana da wurin zuwa shine nace ta tafi kawai, daman bisa kuskure ma na kirata, amma ban yi tsammanin zata haɗa mun munafurci a wurinka ba”

Marin da ya ɗauketa da shi yasa saida tayi baya saboda ya shammaceta, ƙafarta ya ture dutsin guga da samiran, garwashin ciki ya zube a saman tiles din wurin.
Raɗaɗi ya ziyarci fuskarta a inda yatsun shi suka sauƙa da kuma dunduniyar kafarta.

“Yaya Hashim, yau a kan Khausar ka mareni?. Khausar din da nice na jawota jikin mu?”

“An mare kin. Idan kina da ƙarfin ramawa bismillah. Kuma dan Allah wata tazo mun gida ta gani, dukkan ku sai na baku mamaki tunda na lura ba fasawa kika yi ba, toh mu cigaba da zubawa mu gani waye zai kwashe.”

*Washegari*

Ƙarfe 12 da rabi na safe Ihsan ta sauƙa a garin Kaduna, Ilham kuma ta shirya mata dambun tsaki da jollop ɗin taliyan murji na manja da wake, ya ji daddawa kaman yanda ta san Ihsan ɗin tana so.

````````

Seemahwrites ✨

.
Chapter 13 · 0% Book details