Chapter 11
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites*
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
11…. Malam Mahmoud Ibrahim Baniza. Manomi ne wanda tun a zamanin samartakan sa ya gwada yana sha'awar noma, sai mahaifinsa Ibrahim Jen ya yanka masa fili a cikin gonan shi ya bashi iri a matsayin jarin da yakan bawa kowani ɗan shi idan zai fara sana'a ya duƙufa aikin gona. Da ya samu Allah ya saka masa Albarka sai gashi kaka tana zagayowa yayi Aure da ƴar maƙwabtansu mai suna Amina.
Watan Amina tara cuss a gidan shi ta haifa masa ɗa namiji wanda yaci sunan mahaifin shi Ibrahim, wata shekarar tana sake zagowa ta sake haifan Namiji mai suna Umar.
Ganin bajintan da Mahmoud yayi a ranar sunan umar ya kusa yafi wanda yayi a haihuwar Ibrahim ya sanya ƴan suna tsokanarta a lokacin da suke ɗaga zannuwan da ya kawo mata cikin sabon akwati haka ma kayan jariri.
“Amina Allah ya sake dawo damu baɗi muga abin arziƙin da yafi wannan kinji?!” Shine abinda ƴan gidan su Mahmoud da sauran abokan arziƙi suke faɗa tana murmushi daga ƙuryar gado.
Saidai koma bakin su ne ya kamata bata sani ba Amma ba'a rufa shekara ba ta sake haihuwar ƴarta mace wacce suka sakawa Sahura, saidai daga haihuwarta lafiya ya gagari Amina.
Haka suka dinga ziryan asibiti daga Jen zuwa cikin taraba kuma tayi jinya sosai kaman ba zata tashi ba har saida ta koma gidansu.
Mahmoud kuma Ya kaiwa mahaifiyar shi Sahura ruƙon yaran a lokacin, a ganin shi ɗawainiya ne zai yiwa iyayen Amina yawa idan ya ɗebi yara har uku ƙanana ya kai musu bayan suna fama da jinyar ƴar su, sai gashi ƴan uwa sun saka shi a gaba da zuga na ya ƙara aure ya samu wacce zata riƙe masa yaran da amana, mahaifiyar su girma ya kamata ba zata iya raino ba.
Da ƴar ƙanwar mahaifiyar shi aka haɗa su mai suna Dijengala. Suka saka auren wata guda kacal daman iyayen Dijengala a shirye suke su mata aure miji kawai ake jira kuma an samu.
Amma Mahmoud ya rasa yaya zai yi ya sanar da Amina da iyayenta.
Kullum idan yaje dubata sai ya buɗi baki zai yi maganar auren, idan yaga yanda take kallon shi cikin azaban ciwo tana cije baki rike da cikinta ko tana washh sai yaji ya kasa.
Saida za'a shiga satin bikin da yaga babu sarki sai Allah yake faɗa mata. Bata ce komai ba har ya tashi ya tafi amma ranar ɗaurin aure a asibiti yayiwa Mahmoud saboda Amina da akewa aiki a ciki.
Kuma daga nan shikkenan ta fara samun sauƙi a sannu. Dijengala bata haura wata biyu a gidan ba ma Amina ta dawo kan yaranta don jikinta yayi kyau sosai.
Haka akayi zaman da daɗi da dambe sai gashi Amina ta sake samun wani cikin, Dijengala shiru, Amina ta haifi ɗanta namiji da suka sakawa Usman.
A ranar suna, wannan karon ba Mahmoud bane yayi bajinta, saboda ƴan kuɗaɗen shi sun ƙare a kan auren Dijengala da kuma rashin lafiyan Amina. Kayayyaki aka kawo masu kyau da tsada tun daga garin kano.
Sai a lokacin itama Amina take jin cewa ashe ma wani Alhaji dake siyan amfanin gonansa yayi wa takwara, shine yaji daɗi ya zuba musu kaya haka harda kuɗi ya baiwa Mahmoud kyauta.
Abinda ya tsayawa Dijengala a rai kenan bayan watanni itama Allah yasa ta samu ciki, tun daga nan ta duƙufa da addu'ar Allah yasa namiji zata haifa kuma da ta haifa ɗin saida ta tursasa Mahmoud ya sanya mishi Usman shima, amma abinda take nima ɗin bai samu ba don kafin saƙo ya kaiwa alhajin tafiya ta kama shi kuma bai dawo ba sai bayan watanni huɗu.
sai ya zamo Usman sun yi biyu a gidan kuma suna linzami idan ka kira kowannen su zai amsa, don haka aka koma cewa ɗan Dijengala Ussy.
Da Amina ta sake haihuwar mace Halima sai ta rufe haihuwa saboda yanayin jikinta. Dijengala kuma ta ƙara da Rabi'u wanda ake kira da Rabe sai Aliya da Laweeza.
Rasuwan mahaifin Mahmoud ya kawo zancen rabon gado wanda a ciki harda gonan da Mahmoud ɗin yake samun abinda yake ci da iyalansa ya biya sauran bukata na rayuwa, kuma yana da ƴan uwa da yawa, har su 17 a wurin mahaifin su.
Suka yanke shawarar kada a siyar da gonan, a barshi ma Usman yana biyan su kuɗin haya amma sai yaƙi amincewa gudun matsala da ɗaukan hakkin wa’inda zancen bai kwanta musu ba danne su aka yi.
Aka ɗauki gona aka sayar aka bashi rabon shi na gado ya nausa Kano wurin Alhaji Usman niman arziƙin shi a can.
Kaman da wasa ya fara gini a Jakara a filin da uban gidan shi Alhaji Usman ya siyar mishi daga gefen gidan shi, ya dawo da iyalan shi ciki.
Lokacin da Alhaji Usman zai tashi a Jakara ya koma sabon ginin da yayi sai Mahmoud ya shawarci ƴan uwan shi da suke ɗaki ɗaya da su haɗa kuɗi su sayi gidan sai su dawo kano da zama su shiga harƙan kasuwanci. Suka aminta da zancen ganin yanda shima samun shi ya ƙaru don haka suka tattaro ƙwan su da ƙwarƙatan su suka dawo gidan da aka san shi da gidan Baniza a yau.
Kuma har suka kafu a garin Kano yaransu suka girma suka mallaki hankalin kansu basu taɓa bari wani bare ya shiga cikin zuriar su ba, sun gwammace su koma Jen su sama ma yaran su abokan rayuwa.
har manyan ƴaƴan Malam Mahmoud suka yi aure aka zo kan Usman a wannan tsarin ake.
Usman ya fito ya shaida musu akwai wacce yake so Jamila kuma bafulatana ce, a ranan irin marukan da ya ɗiba a wajen mahaifiyar shi Amina saida ta kwana tana ciwon hannu. Amma dake soyayyar tazo da zafi sai gashi ya tubure a kan ra'ayinsa babu shiri aka nimo yarinya a dangi mai suna Aisha aka aura masa sai shiga ɗakinsa kawai yayi bayan ya dawo daga interview ɗin niman aiki yaga mace a lullube.
Fatattakan Aisha yayi waje ya rufe ƙofar shi ya kwanta haka aka dinga bugawa Sahura da sauran ƴan uwan shi suna sababi ko a jikinsa har suka gaji suka kama Aisha dake kuka wiwi suka mayar da ita ɗakin mahaifiyar shi.
Saidai abu kaman almara sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci Aisha ta fara tara masa zuri'a, ta haifa masa Abubakar, Iman, Ahmad sai Aliyyu daga nan ciwon ƙoda ya sakata a gaba kafin Allah ya ɗauki ranta bayan ta Haifi Amina wacce akewa laƙabi Ilham da shekaru biyu.
Sosai mutuwar Aisha ya taɓa Usman, daman shine mafaɗaci fiye da ƙanin shi Ussy don shi babu ruwan shi Rabe nema yake taɓa rashin ji. Amma haka ya dawo sukuku abin tausayi kaman shima maraicin yake yi tare da yaran shi.
Bai sake dawowa cikin zaamar shi ba saida ƙaddara ta sake haɗa shi da Jamila a shagon yayan shi Umar tazo siyan yadin Hijabi shi kuma yaje shan iskan yammaci a wurin.
Daga nan suka sake jamewa, musamman da yaji duk bayan tsawon lokacin nan bata yi aure ba, sai yake ganin kaman sanadin shi ne hakan ya faru don duk shi ya kora mata maneman ta. Aka tada tsohon zuma ya sake mata alƙawarin aure wanda ta jishi ne kawai amma ta san abu ne da ba zai yiwu ba.
Usman ya samu magabatan shi da zancen Auren Jamila don mahaifin su ya rasu a tsakanin nan. Daga farko basu aminta ba suma amma ganin yanda ya matsa yasa suka ce yaje ya nemi amincewar Mahaifiyarsa.
Dake matar Mutum kabarin shi, Jamila ta shiga ɗakin Usman sai dai ba na gidan Baniza ba, Bayan sharaɗin da suka kafa mishi na cewa bayi da matsuguni a gidan har sai ranar da ya rabu da Jamila.
Bayan auren ko gaida mahaifiyar shi yaje yi sai ta juya ta bashi ƙeya ya gama bada hakurin shi ya tashi ya tafi, takwaranta Ilham ma da ta samu labarin Jamilan ta karɓeta zata riƙe tace a daina kawo mata yarinyar.
Saidai ganin shekara ta zagayo babu alamar Usman zai saki jamila sai ma tsohon ciki da take dashi yasa mahaifiyar shi yanke shawarar ta saka shi ƙara aure da ta bar Jamila tayi nasara a kan su, suka aura mishi Shafa’atu.
Bai so Shafa kaman yanda ya samu kansa da son Aisha ba saboda bata da hali, amma haka yake haƙuri da ita alfarmar mahaifiyarsa da take ci.
Da Jamila ta haihu sai ta zaɓi ta sanya ma yarinyarta suna Ihsan don ta faranta ma Usman Saboda ta lura mahaifiyar Ilham duk sunan yaranta mata daga I ya fara na maza kuma daga A.
Shafa ganin ta fara haihuwa da yara maza sai kanta ya ƙara faɗi, ɗanta na farko aka saka mishi Mahmoud shiyasa ake kiranta da maman baba, a lokacin da Jamila wato Maama kaman yanda yara suke kiranta ta haifi ƴarta na biyu wanda taci suna Islam shima namiji shafa ta sake haifa, sai a haihuwa na uku suka yi kunnen doki wajen haihuwan maza dukkan su, yaron Maama yaci sunan mahaifinta Ahmad amma dake akwai wani ahmad ɗin a gidan sai ta zaɓi ana kiran shi da Jawad daga nan haihuwan ya tsaya mata.
Khausar kuma ƴar kawu Rabe ne ƙanin mahaifinsu da suke uba ɗaya dashi wato ɗan Dijengala, so cousins suke da Ilham da Hashim. samun aiki da babansu yayi a wani kamfani a kaduna yasa ya tattaro iyalansa daga gidan Baniza ya dawo dasu kaduna sai gashi sun zamo ma Ilham zallan ƴan uwan da take dasu a kurkusa dukda ma su khausar ɗin sun jima a nan.
*****
“Aunty Ilham bari na tafi, sai gobe ko jibi zan dawo” muryar khausar ɗin ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.
Cikin sanyin jiki tace “toh Aunty khausar nagode”
Ta langabar da kai “ayyah babu komai fah”
“Ki gaida su mama” ta miƙe zata raka ta sai taga Hashim ma ya juya zai tafi.
Ta bude baki zata yi magana yayi saurin katseta da “zan ajiye ta ne in wuce gida in huta, tasowata kenan daga aiki na gaji”
Abinda ya ƙara bata mamaki shine basket ɗin da Khausar tazo dashi sai gashi ta ɗauka zata tafi dashi.
“Daman kada Mu bari a jikin mashin ne mu koma mu samu babu shiyasa muka shigo dashi, amma zan kawo miki naki gobe Aunty Ilham, wannan na yaya Hashim ne ya kira maman mu yace a zuba mishi yana jin yunwa” ta koro bayani kaman wanda aka tambaye ta.
“Muje da’alla muna ɓata lokaci” cewar Hashim yana ciki-ciki da murya kaman wanda yayi ajiyan miliyoyi a asusun bankin sa.
Ilham Sai ta hangame baki kawai tana kallon bayan su yanda suka jera kafaɗa da kafaɗa har suka bar ward ɗin.
`````````
.
Seemahwrites ✨