Chapter 15
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)
Wattpad and Arewapen @Seemahwrites
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
15… Ilham ta miƙe zata bi bayan shi Ihsan ta ruƙo rigan jikinta, tana tilasta mata maido da hankalinta da ya gama tafiya uwar ɗakin da Hashim yake ciki zuwa gare ta.
“Menene?” Ta tambayi Ihsan da ta ƙura mata idanu, tana riƙe da ita kuma bata ce komai ba.
“Mun gama kitson ne?” Ta tambaya tana shafa rabin kan da yake har yanzu a tsefe da ɗaya hannunta.
“Baki ga baban Muftee ya dawo bane? Zan dawo in ƙarasa miki ai”
“Kina dai ganin maghriba ta gabato, kuma Maama ta sha mana faɗan kitso ko tsifa da Almuru, kuma ba zan kwana da rabi da rabin kai ba gaskiya.”
Danƙwale tayi mata “kin ci gidanku Filiyan. Ba nayi miki zancen Almurun ba ki bari sai gobe kika ce a fara a haka? Ai nace yanzu zan dawo”.
Ta ƙwace riganta daga riƙonta, ta karasa jikin ɗakin tayi sallama kana ta ɗaga labule ta shiga tsoro yana daɗa mamaye zuciyarta.
Yanzu idan Hashim ya sake jaddada mata hukuncin shi a kunnen Ihsan fah? Koma ya zo ya koreta a gidan da kan shi, Ina zata saka kunya da nauyin Maama?.
“Sannu da dawowa” tace tana tsaye daga bayan shi a lokacin da yake cire riga ya jefa mata a kan gado idan taga dama ta ɗaga.
Bai kulata ba ya shiga kunce mazargin wandon shi, shima ya zame shi a ƙasan wurin ya tsallaka shi ya raɓata ya wuce hanyar ban ɗaki.
Ganin haka Ilham ta fita ɗauko mishi dambun tsakin da Ihsan bata ci ba, ta saka a kan tray da jug ɗin ruwa a gefe ta dawo ɗakin.
Ko idan ta bashi zai huce ya hakura da nunawa duniya irin zaman da suke yi.
Tana da tabbacin ba baƙon abu bane a wurin duk wanda yake kusa da su amma sirri komin kashin sa sirri ne, ko da ita bata da rabon hankalinta ya kwanta tana fatan kada damuwarta ya cigaba da damun zuciyoyin Ihsan da Maama.
Ganin toilet ɗin a wanke ga sabon sabulu yasa ya yanke shawarar yin wanka bayan ya gama abinda ya shigar da shi.
Tana zaune a gaban tray ɗin bayan ta tattara kayan da ya watsar Ya fito sanye da gajeren wandon da lokacin canza shi bai yi masa ba tukunna don sai yayi kwana huɗu zuwa sati yana maimaitawa, idan ɗoyin shi ya fara shiga masa hanci tukunna yayi tunanin lokacin canza wani yayi.
Tayi tsammanin zata samu sauƙin shawo kan shi idan yaga kwanon abinci, amma ko kallo bata ishe shi ba haka ya wuce zuwa akwatin kayan shi da ta jera a gefen ghana must go ɗinta, wanda na lefenta ne ya mallake tun bayar da ta siyar da wardrobe ɗinta tayi jinyar Muftee da kuɗin.
Yana jin yunwa amma gidan su Khausar ya nufa da sunan lallashi, ya san kuma zasu tarbe shi da abinci mai rai da lafiya shiyasa bai kula tsiyan dake cikin samiran Ilham ba, ya shirya cikin jamfa ruwan goro ya kafa hula.
“Baban Muftee abincin fah” ta tambaya ganin yana shirin fita.
“Kiyi yanda kike so dashi tunda ban Isa da gidana ba Ilham”
Hararan da ya watsa mata tare da wucewa ya hanata sanar da shi aikin da ta samu na raino wanda zata fara zuwa gobe.
Ya fita parlourn da sallama a bakinsa inda Ihsan ke zaune ta lulluɓe kanta da mayafin kayanta tana danna waya. Yayi tunanin zata gaida shi yanzu amma kaman bata san da halittar shi ba saida ya zo fita yaji tace “Uhm”.
Tuƙuƙin baƙin ciki yazo ya tsaya mishi a wuya kuma babu yanda ya iya da ita, don idan yana dukan Ilham yana kwana lafiya yana tsoron Ihsan da idanunta ke a tsakar ka tsaff sai ta iya ramawa.
Amma duk zai yi maganin su ne ita da Ilham ɗin.
“Wallahi baki da kunya yarinyar nan” Ilham ta girgiza kai tana komawa matsuguninta a bayan Ihsan.
Ta yatsina baki tana kashe wayan ta ajiye. “Wallahi ina da kunya nikam, marasa mutunci ne bani gani da gashin ido.”
Ilham ta fisgo gashin kanta bayan ta zame mayafin “dalla rufa mun baki, ko baya aure na kin san dai yayan ki ne”
Jin Ilham ta saka kibiya tana tsaga gashinta yasa ta koma ƙunƙuni kawai kada ta soke ta da shi idan ta cigaba da magana.
Da suka gama Ihsan ne ta fara miƙewa ta shiga banɗakin yin fitsari tare da alwala amma da ta haɗu da ajiyan Hashim da aroma ɗin shi ya cika banɗakin babu shiri ta fito.
“Kambu Aunty Ilham kashe ni kuke son yi?”
Ilham ta tsaya da alwalan da take yi a bakin rariya.
“Lafiya?”
“Haka kuke amfani da toilet ɗinku? Toh gaskiya ba zan iya ba motan dare zan bi in koma kano.”
Da sauri Ilham ta miƙe tunawa da Hashim ya shiga banɗakin bayan ta wanke kuma ta san halin shi.
Bata ce komai ba ta wuce ciki tana jin Ihsan na faɗin “Haka kawai ana zaman lafiya? Ni ba haka ake ba a garin mu wallahi” kunya ya hana ta tankawa saida taje ta tsaftace banɗakin ta bar ƙofa a buɗe iska ya kora warin kafin ta ce Ihsan ta shiga.
Kuma dake da gajiya a jikin Ihsan kafin Hashim ya dawo gidan har tayi barci a parlor inda Ilham tayi musu shimfiɗi a ƙasa, daman ta saba da kwanan parlour idan tana gudun kada takaicin Hashim ya ƙarasa ta, sai yau yayi mata daɗi ganin gata ga rabin jikinta.
Kiran sallan asuba ta tashi, ta shiga hidiman hura wuta da sharan tsakar gida kaman kullum saboda ta samu tayi sammakon zuwa asibiti.
Sai gashi Ihsan tana gama karatun Alqur'ani da azkhar ɗinta itama ta fito ta saka mata hannu don haka babu ɓata lokaci suka gama suka soya doya a matsayin abun karyawa, ba don Ihsan ta so ba aka zuba ma Hashim.
Kuma har suka ci suka fita bai farka ba kasancewar yau Lahadi.
Asibiti suka fara zuwa su biyun. Ta tambayi wacce ta yarda zata dinga duba mata jikin Muftee yanda ya kwana, ta tabbatar mata da sauƙi kafin ta kira Hajiya Surayyah tayi mata kwatance ta tafi ta bar shi da Ihsan.
….
8:51am
Mai gadi ne ya wangale mata gate bayan ta sanar dashi wurin wacce tazo.
Bata tsaya mamakin irin girma da kyawun gidan ba ganin kuɗin da suka ce zasu dinga ɗauka suna bata duk wata. don haka ta kutsa kai cikin ƙaramin ƙofar da ta gani a buɗe ta shiga.
akasin yanda ta samu harabar gidan ta waje ƙal-ƙal, tsakar gidan kaca-kaca yake, ga taliya da shinkafa a barbaje kaman wanda aka zubawa kaji, ga miyan kuka da aka zubar a wurin har ya bushe ba'a samu mai saka ruwa ya wanke ba, ƙudaje kaman a gidan gandun ƙauye.
Ta buɗe murya ta sake sallama ganin babu kowa a tsakar gidan, sai wata budurwa ta fito daga kitchen hannunta rike da farantin da indomie da wainar ƙwai yake tururi a kai.
“Baiwar Allah daga ina?” Cewar Hudah”
“Ina kwana” Ilham ta fara gaidata, kana ta ɗora da “nazo wurin Hajiya Surayyah ne”
Hudah ta kalleta sama da ƙasa tana yatsina baki sannan tace “Babu Hajiya Surayyah a gidan nan”
Bata rufe baki ba ƙofar ɗakin aunty Surayyah ya buɗe ta fito sanye da farin hijabi har ƙasa. “Malama Ilham bismillah” shine kawai abinda tace ma Ilham da ƙaramin murmushi a saman fuskarta ko inda Hudah take bata kalla ba.
Itama Hudan ta buga tsaki ta bar wurin kafin Ilham ta iya jan ƙafarta zuwa inda ɗakin yake.
Saida ta shiga ciki taga girman shi, gashi ko ina ya wadata da hasken lantarki ga sabon fenti da yake nan ƙal ba kaman na tsakar gidan ba da yara suka zane shi da chalk da gawayi. Sai Hajiya Surayyah ta ƙara burgeta ganin kaman yanda ta haɗu a karan kanta muhallinta ma ya haɗu, banda ƙamshin turaren wuta mai daɗin da yayi mata kama da wanda Maama take yawan amfani dashi na Bakhoor by Seemah (08021689184).
Ta fara dauko mata ruwan gora mai sanyi a fridge ta ajiye a gabanta, kana ta zauna a kujeran dake kallon inda Ilham ke zaune a saman carpet.
“Sannu da zuwa Malama Ilham”
“Ina kwana Hajiya, yaya aiki” ta gaidata tana ƙasa da kai cikin girmamawa.
“Lafiya Alhamdulillah. Yaya jikin yaron ki”
“Da sauƙi Hajiya”
“Masha Allah. Bari a kawo miki abun karyawa”
Tayi saurin girgiza kai “ A'a na karya kafin na fito Hajiya, Nagode”
Hajiya Surayyah ta gyaɗa kai “Toh madallah. Yanzu kafin in nuna miki inda zaki fara aikin akwai abubuwan da nake son jan hankalin ki a kai”
Ilham ta gyara zama ta bata dukkan hankalinta, don bata son ta baɗa ma hajiya Surayyah ƙasa a idanu bayan ta zaɓi ta taimaka mata.
“Na farko sai kin yi haƙuri Malama Ilham…”
Haƙuri.. Haƙuri… ta daɗe tana jin kalmar nan daga bakin mutane daban-daban.
Kuma a kowani lokaci akwai nauyin da kalmar yake tafe da shi.
Na farko da aka faɗa mata a ranar da aka ɗaura mata aure da Hashim ne, kuma ya zo mata da baƙin ƙaddarar da har yanzu take cikin duhun shi ta gagara kuɓuta.
Na biyu an faɗa mata shi a ranar da ta rasa bangon jinginan ta, ranar da mahaifinta ya bar duniya, kuma daga nan ta san ainihin abinda ake nufi da maraici.
Na uku shine ranar da likita ya miƙo mata takardar genotype ɗin Muftee da yake rubuce da harafin ‘SS’. Kuma daga nan ya fara rashin lafiyan da Allah ya barwa kansa sanin ranar da zai samu sauki.
Toh wannan shine karo na huɗu.
Daga bakin Hajiya Surayyah Kagarko.
Kuma bata san da me yake tafe ba, amma tana fatan yazo mata da sauƙi.
“... Yarinyar da zaki kula da ita tana da lalurar ji don haka tana bukatar kulawa ta musamman, shiyasa sai kin yi haƙuri sosai kin kai zuciya nesa. Ki tausaya mata kaman yanda kike tausayin naki yaron, Yanda kika durƙusa a kan guiwowin ki kina magiya a kan rai da lafiyan shi yasa naga dacewar ki da wannan aikin, saboda tana buƙatar kulawar uwa irin ki. Don Allah ki jata a jiki Ilham kuma shima mahaifinta sai kin yi haƙuri da shi saboda ita kaɗai gare shi kuma laluran su kusan iri ɗaya, kin san kurame da faɗa. Bani tunanin akwai wani abu mai tsayi ma da zai ke haɗa ki dashi amma idan an kai ga haka ki kalle shi ki bashi hakuri ni sai ki sanar dani a shawo kan lamarin kin ji ko?”
Ilham ta jinjina kai ta amsa ta “in sha Allah Hajiya” tana jin nauyin ƙirjinta na raguwa jin girman Haƙurin bai kai sauran na baya ba.
In sha Allah zata iya, indai a kan Muftee ne babu abinda ba zata iya ba.
Hajiya Surayyah ta ɗora da “Masha Allah. Sai kuma a kula da tsafta, da aiki mai kyau dan Allah banda amaja. Kiyi girki daidai gwargwadon da zai ishe ku kema ki ci ki ƙoshi, a dinga gyaran ɗakinta da gidan kullum duk wani abinda ake buƙata kuma kai tsaye ki zo nan ki same ni idan lokacin aiki ne kuma ki kira ni a waya.”
Shima ta amsa da “toh Hajiya”
Sannan Aunty Surayyah tace su je ta zaga da ita ko ina a ɓangaren, ta nuna mata abubuwa kafin su Kiki su tashi daga barci tunda yau weekend babu makaranta babu aiki.
Tana tafe Ilham na binta a baya, tunanin dattin dake tsakar gidan tsaye a ranta tana ji dama zata bata minti goma zuwa sha biyar zata share shi ta wanke tass ko zai yi mata yanda take so.
Har suka isa ƙofar flat ɗin kafin ta ajiye tunanin ta ɗago ta dubi ƙofar shiga, lokaci guda taji ƙirjinta na bugawan taraddadin abinda zata riska a ciki a lokacin da Hajiya Surayyah ta murɗa hannun ƙofar ta tura.
Ya kai hannu zai buɗe ƙofar daga ta ciki kenan yaga ana turowa daga waje, don haka ya matsa baya yana jiran ƙofar ya gama buɗewa idanun shi a kan mai shigowa.
Kaman yanda yayi tsammani Hajiya Surayyah ya fara gani don ita kawai ke da lasisin shigo mishi part kai tsaye a cikin gidan.
Amma da idanun shi suka mata kallon sakwan biyu sai suka fahimci ba ita kaɗai bace, A hankali kuma suka ɗaga daga kanta suka sauƙa a kan wacce ke tafe tare da ita.
ILHAM.
```````````
Seemahwrites ✨
ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a turo shaidan biya ta 09039206763