← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 30

Chapter 10

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

Arewapen & Wattpad @Seemahwrites

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


10… ƙirjinta yayi mummunan bugawa, a lokacin duk wani lissafi da ta gama haɗawa a cikin kanta na yanda abubuwa zasu yi mata sauƙi da take zaman jiranta a reception ya shiga warwarewa.
Ta zame daga kujerar da take zaune tana tura shi baya domin ta samu isasshen wurin da zata sauƙa a kan guiwowinta yayinda hawaye suka fara gudu a saman fuskarta.

“Hajiya don girman Allah. Na roƙe ki Hajiya dan girman zatin ubangiji..” ta shiga roƙo da magiya tana kuka shar-shar.

Miƙewa Hajiya Surayyah tayi da sauri ta zaga teburin ta nufo Ilham dake roƙonta tana kuka kaman ranta zai fita. Ta yi ƙoƙarin ɗagata ta mayar da ita mazauninta na farko Amma yanda jikin Ilham ya ɗauki rawa ya ƙara bata tausayi.

Kuma bata yarda ta miƙe ba, a ganinta idan ta miƙe kafin buƙatarta ya biya gani Hajiya Surayyah Kagarko zatayi kaman tana da wani zaɓin bayan wannan.

Tabbas Hajiya Surayyah ta tausaya mata, kuma ta yarda da duk bayanan da tayi mata amma Ilham ba ita bace ta farko. Mata da suke cikin yanayi irin nata suna da yawa a faɗin Nigeria, kuma suna samun da yawa wa'inda suke zuwa gare su da ƙoƙon bara irin nata a kullum. Suna iya ƙoƙarinsu ne kawai amma sun kwana da sanin cewa ba zasu taɓa iya yiwa kowace uwa maganin damuwarta ba saidai su rage na ɗan wani kaso daga cikinsu, amma idan suka ce kukan kowacce uwa da ta tsaya a gabansu zasu share toh nauyin zai rinjayi kafaɗunsu ne, aikin su zai koma babu tsari kaman yanda aka saba yi a ƙasar, saboda dole su koma bangaren masu kawo koken su a maimakon wa'inda suka duba suka ga cancantar a basu taimako.

“Malama Ilham tallafin da kike magana a kai yanzu haka rabo yayi nisa, tun ƙarfe 9 da rabi suka fara kinga babu yanda za'ayi in saka ki. Kiyi haƙuri zuwa wani jiƙon in sha Allah zan yi ƙokari na tabbatar kin samu”

Gaba ɗaya gaban hijabinta ya jiƙe da hawayen da ke ɗiga a kai da kuma zufan dake tsatsafowa a jikinta kaman ba ɗazu ne take rawar ɗari a reception ba saboda AC “Hajiya ki dubi girman Allah, kaman yanda ya taimaka miki Hajiya dan Allah ki taimaka mana, Wallahi bani da yanda zanyi, na gama iya ƙoƙarina, abinda mara lafiyan zai saka a bakin shi ma wani lokaci gagara na yake yi”.

Hajiya Surayyah ta lumshe idanunta. Duk lokacin da taji rayuwa tayi mata ƙunci ko kuma kaɗaici ya lulluɓeta irin wa’innan mutanen take tunawa taji sanyi a ranta

“Shikkenan naji tashi” tace da Ilham, sai kuwa ta miƙe ɗin tana share hawaye don tayi tunanin ƙoƙon bararta za’a amsa.

Ta koma jikin jakarta da ta shigo dashi ta zaro saɓɓin ƴan dubu-dubu guda biyu ta dawo ta riƙe a hannunta na hagu sannan ta miƙawa Ilham wayarta dake hannun dama.

“Gashi saka min lambar ki, nayi miki alƙawarin da wani abu ya tashi ko ba irin wannan ba zan san yanda za'a yi a maƙala ki a ciki. Koda a cikin satin nan ya samu zaki ga kirana in sha Allah”

Da alama ta ƙure gwajin sa'ar ta, kuma tunda ta ƙwanƙwasa ta sake ƙwanƙwasawa babu ƙara toh ba zata samu karɓuwa ba, daman Hajiya Surayyah alƙawarin sauraronta tayi mata jiya kuma ta saurareta ɗin.

Sai ta ɗauki dangana ta rubuta mata lambar tana yi tana jan hanci, ta mayar mata da wayar bayan tayi saving da ‘Amina Usman Jen’.

Dubu biyun da Hajiya Surayyah ta ɗauko ta mayar hannunta na dama sannan ta miƙa ma Ilham “gashi kiyi kuɗin mota, sai kinga kira na”

Ta rage tsayinta kana ta saka hannu bibbiyu ta amsa tana zuba godiya kaman wanda ta bata dubu goma, hakan ya ƙara ma Hajiya Surayyah tausayinta, don saida ta rakata har reception suka sake sallama tana kallonta ta ɗauki laidan da kwanonta yake ciki ta rungume tare da purse ɗin da ta saka dubu biyun a ciki da kuma envelope ta sake musu godiya ta fita bakin hanya niman mashin, a ranta tana sarewa don ta san idan hidima suka sha kan hajiya Surayyah ba zata tuna ta kirata ba, ta bata tabbaci ne kawai don taji sanyi a ranta kuma taji ɗin, in sha Allah hanyoyin Allah da yawa suke.

Khausar ta fara hangowa zaune a kujera da isarta pediatric ward ɗin, tana juya abu a cikin kofin roba tana magana da dariyar dake bayyana wushiryarta. A lokacin da idanunta ya shiga cikin na Ilham dake ƙarasawa jikin gadon su kuma sai ta taɓa ƙafar yaron dake zaune a saman gadon tana cewa “Muftee ga Mimin ka”

Yaron yayi saurin juyowa ya kalleta a lokacin ta iso wurinsu tana ɗora murmushin dole a kan fuskarta. “Babana ka tashi? Ina kwana”

“Mimi ina kwana. Jiya inata jiran ki har nayi barci Mimi”

Ya ɗan kwaɓe fuska yana kallonta.

Sai ta bishi da kallon tausayi, ga canular maƙale da ɗan hannunshi, ramar da yayi ya nuna har a fuska. Ganin ƙasusuwan ƙirjin shi kaman babu tsoka a zagaye da su kuma na yawan saka ta zubar da ƙolla.

Amma yanzu sanye yake da tsohuwar rigan sanyin da ta siya mishi a gwanjo last year, dake shi ɗaya ne kacal kamar tsoka a miya saidai a cire a wanke yasa duk kalan rigan yabi ruwa.

“Ina kwana Aunty Ilham” Khausar ta gaidata da faffaɗan murmushi a saman fuskarta.

Ilham ta ɗaga idanunta daga kan Muftee ta dawo dasu zuwa ga khausar a inda take ganin kunun gyaɗa ne a cikin kofin don gashi fari tass.

“Lafiya Aunty Khausar, yaya gajiyan ki? Na gode fah, na gode sosai Allah ya biya ki da gidan aljannah ya baki miji na gari”

Khausar ta duƙar da kai a kunyace tana amsawa da ameen.

Saida Ilham suka gaisa da sauran majinyatan dake ward ɗin suna gwada mata kayan alkhairin da aka ajiye musu niƙi-niƙi, wasu har sun fara tafiya da kayan abincinsu gida, tayi musu murna ta dawo jikin gadon yaronta.

“Aunty Ilham ina kin samu muma sun saka mu?”

Ta numfasa ta girgiza kai kawai, sai ta samu wuri ta ajiye kwanon da tazo dashi, ta zauna a gefen Muftee tana zura hannu ta cikin rigan shi taji ko jikin shi da zazzaɓi.

“Ga abinci ko zaku ƙara ne” tayi maganar tana kallon Khausar wanda ta girgiza kai har yanzu murmushi bai bar fuskarta ba.

“Da abun daɗi muka karya wanda In-law ɗinki ya kawo mana, ko Muftee nah?” Ta ƙarasa tana jijjiga ƙafar yaron, ya ɗan yi dariya mai sauti.

Har cikin ranta Ilham take jin daɗin yanda Khausar take taya ta son Muftee, “iye, shine sirikin nawa bai tsaya mun gaisa ba?”

“Ai ko shigowa bai yi ba Aunty Ilham, daga waje ya tsaya saboda yayi lattin zuwa wurin aiki. Amma yace da yamma zai dawo ya duba jikin Muftee ɗin” tace tana miƙewa da kofin hannunta ta ajiye, ta ƙarasa saman drawern asibitin ta dauko wata farar laida mai tambarin wani wurin shawarma ta miƙa mata.

“gashi kema mun ajiye miki naki”

Ta karɓi laidan ta buɗe tana leƙawa, ɗan gutsurin shawarma ne naɗe a cikin takarda, ga ƙamshin dake shiga hancinta yana sakata haɗiyar yawu don ta daɗe bata ci wannan abun ba. “har dani Aunty Khausar? lallai wannan siriki nawa dole inji dashi.”

Ta ciro ta gutsura, daɗi yana ratsa duk wata kusurwa na bakinta zuwa jijiyoyin kanta har maɗiga, daman bata karya ba, dan haka ta koma gutsiran shi kaɗan-kaɗan kada ya ƙare da wuri, Khausar kuma tana baiwa Muftee kunun da ta samu ya huce a baki suna taɓa taɗin yanda abubuwa suka kasance a asibitin da kuma A&I.

Ƙarfe sha biyu Khausar tayi mata sallama zata je tayi wanka, kuma zata kawo saurayinta ya gaida Ilham da yamma kaman yanda tayi mata alƙawari.

Ilham tayi mata godiya sosai kuma taƙi barinta ta tafi saida ta karɓi kuɗin napep kuma ta biyata ɗari biyun da ta karɓa aro jiya, ya rage a cikin kuɗin da Hajiya Surayyah ta bata sauran naira dubu da ɗari uku.

…..

Da misalin ƙarfe uku na yamma Hajiya Surayyah ta koma Medi-plus kai ma Abdulhameed abincin rana, Saboda saida ta koma ta dafa abincin da kanta, domin sa’ilin da ta koma gidan ta samu abincin da tace maman Hudah ta zuba na asibitin bata zuba ba.

Haka ta yayyafa ma zuciyarta ruwan sanyi bata ko kulata ba ta ajiye mayafi ta shiga kitchen tayi jollof rice a gaggauce wanda yaji kifi da yawa sai kuma cabbage da Cucumber da ta yayyanka a ɗan bowl ta lulluɓe da farin laida. tayi wanka ta saka dogon riga da hijab sannan ta fita ta kai masa abincin.

Yana zaune a kujera ya ɗora Ikram a cinyar shi yana riƙe da tab ɗin da take kallon Omar and Hanna da hannu ɗaya, ga hearing aids wato Na’urar taimakawa sauraro maƙale a kunnuwanta dukka biyu. ɗayan hannun shi kuma yana riƙe da wayan da yake ƙoƙarin rubuta saƙo.

Bai san da shigowarta ba dukda tayi sallama, har saida Ikram ɗin ta taɓa shi ta nuna Aunty Surayyan sannan ya juyo ya dube ta.

“Good Afternoon” yace da ita yana ajiye wayan.

“Afternoon Abdulhameed, yaya mai jikin?”

Sai ya leƙa fuskar Ikram yana tambayarta “How are you feeling Kiki?”

Ta ɗago ta dubi Aunty Surayyah tana kwaɓe fuska. “Har yanzu da zafi hannun”

“Kiyi haƙuri, zai bari a hankali.”

Sai ta gyaɗa kai tana mayarda hankalinta kan cartoon ɗinta.

“Yaya aiki Aunty?” Abdulhameed ya tambaya yana maido da hankalin shi gareta.

Ta ajiye basket ɗin tana amsawa da “alhamdulillah, an gama rabon yau cikin nasara in sha Allah, sauran na gobe shi kuma babu yawa daman”

“Masha Allah, sannu da ƙoƙari”

Ta amsa da yauwa, ta zuba mishi abincin tare da ƴar shi a dalilin sun saba ci a plate ɗaya. Amma shi kaɗai yaci shinkafar, haka ya ɓata hannunshi wajen cire ma Kiki ƙayan kifin yana bata a baki, har saida ta koshi kafin yaje ya wanke hannunshi a sink ɗin toilet ya dawo ya saka spoon ma shinkafar da ta gama sanyi, da taimakon cabbage ɗin kai ya samu yaci da ɗan yawa.

“Sun yi muku zancen sallama kuwa?” Aunty Surayyah ta tambaya bayan wani lokaci.

“Yes, but I asked them to extend it. Na fi son sai jikinta ya ƙara kyau tukunna. Ki cika mun casual leave a office please”

Ta cika mishi casual leave ta miƙa ma wane kuma tunda daman office dinshi ne suke processing?. Amma sai ta amsa shi da toh kawai suka cigaba da tattaunawa sama-sama har aka kira la’asar, da ya fita masallaci yin Sallah sai ta shiga da Kiki toilet ɗin ɗakin ta kunna ruwan zafi tayi mata wanka cikin kiyaye ɗaurin hannunta.

Saida ya dawo bayan ta shirya ta cikin riga da wando baƙaƙe ta tufke mata gashin kanta sannan take sanar dashi zata wuce gida ta huta dan tabbas akwai gajiya a jikinta.

Ta ɗauki basket ɗin da ta kawo abincin safe tana masa sallama, sai yace kawai ta bar abincin dare zai yi order, ya sake mata godiya.

“babu komai. Allah ya ƙara sauƙi, saida safe”

Har ta juya ya sake kiran sunanta.

“An sama mata wata Nanny ne? Because when I resumed work zasu dinga tashi a school ni kuma ban koma gida ba.”

Ta jinjina kai “za’a samu kafin nan in sha Allah. Criteria da ka zana ne kawai zai yi wahalar samun wacce ta cika shi duka, yawanci sai ƴammata dake zuwa daga ƙauye ake samu sai kuma Christian mothers”


Ya girgiza kai “Kiki is still young Aunty Surayyah, akwai abubuwan da yaro ba'a koya mishi a makaranta sai a wurin uwa, Islamiyya karatu kawai zasu koya mata amma aiki da shi sai a gida, so idan na ɗauki Christian ba zata samu wannan ba. And sanin zafin yaro sai wacce ta haifa itama taji, I won't tolerate anyone maltreating my child please”

Ta sani, shiyasa ya haƙura da nannies guda uku da aka taɓa samarwa Kiki.

Ta farkon yarinyace da ba zata wuce shekaru 15 ba, tayi ƙoƙarin kula da ita sosai amma bata iya girki ba, kuma kikin ba komai take iya ci ba koda taje ta karɓo mata a cikin gidan, watarana ma sai ace mata babu. Gadan-gadan Ikram ta fara zabgewa ga yawan rashin lafiya shiyasa ya sallameta.

Ta biyun kuma Christian ce da ta dan manyanta tana da wasu yaran ma. Saidai ba'a ɗora sati ba Aunty Surayyah taji Ikram tana kiran Jesus sama jesus ƙasa ko tuntuɓe tayi saidai kaji tace “Jesus!” A maimakon ta ambaci sunan Allah, ai Aunty Surayyah bata ma bari Abdulhameed ya fahimta ba ta sallame ta.

Haka ma ta ukun da ya taɓa dawowa ya samu tana ɗaɗɗauke masa fuskar yarinya da mari wai ta zubar da abinci a ƙasa, kaɗan ya rage ta kwana a station, saida Aunty Surayyah tayi kaman zata je ƙasa tana roƙon shi kafin ya yarda ya haƙura.

Shiyasa yanzu da yace baya son makamantan su ta fahimta.

“Za'a cigaba da dubawa in sha Allah.”

Ya sake yi mata godiya sannan ta buɗe kofar ɗakin ta fita. Bata bar haraban asibitin ba sai ga alert na 200k ya dira a account ɗinta.

….

Ƙarfe huɗu daidai Khausar ta kira ta sanar ma Ilham suna ƙarasowa tare da saurayinta amma har wajajen biyar shiru. Haka ta canza ma Muftee kaya ta gyara wurin don yazo ya gansu fes-fes.

Tana cikin waya da Maama ta hango fuskar Hashim yana tunkaro ta, Hashim da tun washegarin ranar da aka kwantar dasu bai sake tako kafar shi asibitin ba shine take hangowa sanye da kayan da ya fita dasu ɗazu da safe a jikin shi, bayan sa kuma Khausar ce riƙe da basket ɗin abinci.

“Aunty Ilham” Khausar ta wuce shi ta ƙaraso jikin gadon da fara'a tana ajiye kwandon abincin a ƙasa.

Gaban Ilham ya yanke ya faɗi!.

Mijinta Hashim, da Khausar?... Kai ina?!.

Tayi tsammanin duk wanda Khausar ɗin take soyayya dashi sananne ne a wurinta don Ahalin Baniza basa auren bare, amma tunda Khausar ɗin bata taɓa ambatan sunan shi ba hala bata san shi bane, ko itama zata yi irin na Taa ɗinsu da ya kafa record ɗin wanda ya fara auren bare kuma wata ƙabila daban lokacin da ya auro Maama, kuma daga kan shi ba'a sake ba.

Muryar Khausar ne ya katse mata tunani “kinga na daɗe ko? ina ta tsaye ban samu abun hawa bane kuma ni bana hawa mashin shine na haɗu da Baban Muftee ya kawo ni”

ajiyar zuciyan da tayi a lokacin ya ɗarsa mata kwokwanton kishin Hashim take yi ne dama? ko kuma kasancewar Khausar ce yarinyar da yake kulawa abin bai mata daɗi ba saboda kusancin da ke tsakaninsu?.

Amma koma menene yanzu ta wanke mata zarginta daman ta san hakan da kamar wuya kawai shaiɗan ne yaso sakata waswasi.

“Allah sarki. Toh ina In-law ɗin nawa?” Tace tana ɗaga idanunta daga kan Hashim don bai kula halittarta ba sai wucewa da yayi ya ɗauki Muftee a hannun shi yana masa magana.

Khausar ta murmusa itama tana ɗaga idanunta daga kansu ta mayar kan Ilham. “Sai wani lokaci yace, yau ɗin wani abu ne ya taso masa”

“Allah sarki. Toh Allah ya nuna mana”

Ta amsa ta Ameen, sai ta matsa jikin Hashim tana saka Muftee dariya shima Hashim ɗin yana biye mata dukkan su uku suna ƙyalƙyalawa an bar Ilham rakuɓe a gefen gado kamar itace baƙuwa a duniyarsu.

*Kabilar Jenjo*

Ƙabila ce da ake kiran mutanenta da Jenjawa, ƙabila ce mai daɗaɗɗen tairhi wato tsohuwar ƙabila da ake samunsu ta yankunan arewa maso gabashin Nijeriya Musamman Adamawa da Taraba state.
Masana na kallonsu ne a matsayin kabila mai tsohuwar al'ada da harshen kanta saboda sun mallaki yare da suke magana da junansu da ita.

Ƙabila ce masu tarin zaman lafiya, sun kuma kafu ne ta yankin Karim Lamido LGA a karkashin karamar gari da ake kira JEN, Dukda akwai kauyuka da dama da jenjawa suke zaune tare da Yaruka daban daban kaman su Fulani, hausa da sauran kabilu.

Kusan duka jenjo kusan kowa ya san kowa ne saboda yadda abubuwansu kan wakana a tsakaninsu kaman aure da sauransu, sannan sun kasu kashi uku akwai Christians akwai Musulmai akwai kuma masu bautan dodo.

An fi sanin jenawa da Noma, kamun kifi, saƙa da kuma kasuwanci.
Ana kiran yarensu da jenjo language ko a ce yaren jenjo.

Suna da daɗin zamantakewa amma kuma mafadata ne wa’inda ba'a taɓa su su kyale, suna da haɗin kai ta yadda ko faɗa ne wani jenjo ya zo ya tarar ana yi da ɗan uwansa jenjo zai shiga sai an gama dambatuwa tukuna ya tambayi dan uwan me ya haɗa faɗan?

Kowa ya san kowa saboda rashin yawansu hakan ya sa suke da kyamar aure daga waje ko wata kabilar a kokarinsu na kare harshensu da al'adarsu.

````````
Seemahwrites ✨

.
Chapter 10 · 0% Book details