Chapter 16
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)
Wattpad and Arewapen @Seemahwrites
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
16…. A karatun da ake musu a Islamiyya, akwai babin da idan aka zo ita da ƙawayenta sai su jawo wuyan hijabinsu su rufe fuskarsu suna dariya ƙasa-ƙasa. Shi kuma malamin da yake warware musu zare da abawa kan hukuncin da addini ta yanke a kan wacce ta taka wa’innan matakan suna mishi kallon ɗan Iska.
Sai gashi bata iya dariya ba lokacin da ta taka mataki na farko wanda ke tabbatar mata na biyu ma yana tafe wata rana.
Maama ne ta zaunar da ita ta jaddada mata daga wannan lokacin an buɗe mata littafin ayyuka, duk abinda tayi mai kyau ko akasin shi za'a cigaba da rubutawa har zuwa ranar da zata koma wurin mahaliccinta, makomarta kuma zai kasance bisa sakamakon da ta samu a wannan littafin.
Haka ta wuni jikinta sukuku, tana kwance tana juya maganganun Maama da na malamin su a kanta.
Zata iya cewa daga Ranar da ta fara jinin Al’ada rayuwarta ya fara canzawa. Kaman labarin da aka gama karanta babi na farko aka miƙa zuwa na biyu kai tsaye.
Wasu ɗabi’unta na banza ko na shirmen ƙuruciya Maama ce ta sakata ta sauya su ta hanyar Nasiha da gargaɗi, wasu kuma a karan kanta ta ji ya kamata ta bari.
A cikin sauyin da ya sameta lokaci guda ba tare da tayi tsammani ba kuma harda shi.
Harda A Moher.
Daga ranar da tayi masa magana a kan shan Sigari bata sake ganin shi ba.
Kullum suka zo wucewa suna hira kaman ko yaushe, sai ta samu bakinta da yin shiru idanunta kuma su tafi zuwa inda suka saba ganinsa yana zama amma babu shi babu dalilinsa, Sai abokinsa da wasu matasan da suka maye masa gurbin A Moher.
A hankali kuma ta fara mantawa dashi, rayuwa ta cigaba da tafiya har ta taka mataki na biyu wanda shine aure.
Amma a yau da ta saka mai kama da A moher a cikin idanunta, sai take sanin ashe akwai wani ɗan ƙaramin gurbi da zuciyarta ta tanada masa a cikinta, wanda ke cike da ƙwaɗayin sanin yanda rayuwar shi ta kasance bayan rabuwar su.
Ko yanzu yana ina?
Ya bar shaye-shaye?
Da idanunta take yiwa Abdulhameed wa’innan tambayoyin duk da ta san bayi da amsar su.
Shima ya kasa cire nashi idanun cikin nata, a cikin kan shi yana jinjina ma lamarin ƙaddara wacce bata gajiya da baiwa ɗan Adam mamaki a kan yadda take tafiyar da rayuwar shi.
Ilham ce tsaye a gaban shi.
Ilham da ya barta a rayuwar shi na baya.
Itace ƙaddara ta sake ɗaukowa ta kawo mishi.
“Abdulhameed wannan itace sabuwar Nannyn Ikram, Sunanta Ilham.” Aunty Surayyah tayi magana jin shirun yayi yawa sai tayi tunanin ita ya kamata ace ta gabatar da su ma juna.
Abdulhameed!.
Ta maimaita sunan a cikin kanta.
Bata taɓa sanin ainihin sunan A Moher ba, haka ma bata san menene ma'anar A moher ɗin ba, ita dai ta san ta kira shi da sunan ya ɗago ya dubeta. Amma yau sai taji dama ace koda sau ɗaya ne ta taɓa jin ainihin sunan shi da zata iya banbanta shi da na wannan.
Ilham tayi ƙoƙarin ɓanɓare idanunta daga cikin nashi ta rage tsayinta tana gaida shi.
Bai kaiga amsawa ba wayar shi yayi vibrating a aljihun wandonsa don haka ya ciro yana dubawa.
Saƙon Excellency ne kaman yanda yayi tsammani don shi ya ɗaga shi da sanyin safiyar nan duk da gajiyar dake cin jikinsa, bayan sun gama karaɗe gari tare da Kiki jiya har wurin taran dare driver na ta yawo da su, shiyasa yaso yayi barci sosai ya samu hutu yau kafin gobe ya koma aiki tunda leave ɗin da ya ɗauka ya ƙare.
Cikin seconds ya rubuta reply “on my way” ya tura sannan ya maido dubansa ga Aunty Surayyah.
“I'm in a rush, please take care of Kiki, idan na dawo we’ll talk Aunty Sharmama”
Ya raɓa ta gefen Ilham ya wuce ba tare da ya bari idanun shi dake cike da tarin tambayoyin yanda aka yi rayuwarta ta sake tsayar da ita a gaban shi sun sake shiga cikin nata ba.
“Muje ko?” Muryar Aunty Surayyah ta dawo da ita daga kamanta muryar shi da take yi da na A Moher. Sun so suyi kama, amma akwai wani zaƙi a bayan muryar A Moher wanda babu a cikin Muryar Abdulhameed.
Sai wani amo da idan ya shiga kunnenka duk yawa da ƙarancin shekarunka, walau mace ko namiji dole sai ka waiwayo ka kalle mai shi, shiyasa itama ta bi bayan shi da kallo har ya nufi motar da driver ya fito musu da shi harabar gidan.
Gyaɗa ma Hajiya Surayyah kai tayi sannan ta shiga binta sau da ƙafa.
Suna shiga parlorn sanyi AC ya buge ta, ta shiga juye-juye tana baiwa idanunta abinci.
Komai na parlorn Fari ne da ruwan ƙasa mai haske sosai, daga kan labulaye, kujeru, carpet, center table ga wasu manya manyan windows da suka baiwa hasken rana damar shigowa sosai dukda gilasan a rufe suke.
Babu datti ko ƙazanta ko ƙanƙani, komai yana tanade ne a wurinda ya dace har throw pillows ɗin kujera suna jere reras kaman ba parlorn namiji ba.
Suka wuce parlorn zuwa kitchen bayan Aunty Surayyah ta gama mata bayanin yanda zata ke gyara shi a kullum.
Sun daɗe a kitchen tana gwada mata yanda ake tanada komai kaman yanda Abdulhameed yake so da kuma inda kayayyakin da zata dinga abinci da su suke, ta shigar da ita har store ɗin dake haɗe da kitchen ɗin a inda Ilham ta ga kayan abinci kaman a shago, kaman ta ɗauka ta kai nata gidan suyi ta ci tare da Muftee.
Hajiya Surayyah tana tsaye a kanta ta shiga sharan gidan da take ganin a share yake amma abinda aka sata shi zata yi babu musu, har ɗakin Ikram suka je saidai babu yarinyar a ciki sai tarin kayan wasanta da duk gidan masu kuɗin da ta taɓa aiki bata taɓa ganin kamar su ba. Ɗakin babba ne a karan kansa amma tarukucen ciki ya saka girman nashi ya ragu sosai.
Suma kayan wasan haka ta gyara musu zama bayan ta share ɗakin ta shiga ta wanko banɗakin dake haɗe dashi.
Ta saka mopping mist ta goge gidan har kitchen banda ɗakin da aka ce Mata na Mahaifin yarinyar ne. sannan ta shiga haɗa musu abun karyawa.
Aunty Surayyah ta taya ta da wasu abubuwan kasancewar yau ne rana na farko kuma Ilham ɗin bata san kan cimar mutanen gidan ba, suna aikin tana mata ƙarin bayani har suka gama, lokacin ƙarfe sha ɗaya ta gota.
Suna fitowa daga kitchen zasu jere abincin a kan dining sai ga kukan Ikram na daga Fitowa daga ɗakin Abdulhameed.
Aunty Surayyah ta bar Ilham ta ƙarasa, ta wuce ɗakin da sassarfa sai gata ta fito da wata sangamemiyar budurwa a hannu, don wannan tafi Muftee ɗinta kumari nesa ba kusa ba.
Bata gama mamaki ba sai gashi ta iso inda take tsaye ta saka mata yarinyar dake kukan sakalci a hannu. Suka kalli juna ita da farar yarinyar kafin ta buɗe ƙaramin bakinta ta saka ihun da ya saka Ilham rintse idanu, sauran ƙiris ta sake ta a ƙasa aunty Surayyah tayi saurin saka hannu ta karɓeta.
“Kiki Aunty ce da zata dinga miki wanka tana baki abinci”
Zillon da take yi tana birgima yasa itama Aunty Surayyan ta sauƙeta a ƙasa kafin ta faɗo.
Kaman jira take yi ta kwanta tana bori kukan yanzu harda hawaye tana kiran Daddynta.
Aunty Surayyah ta kalli Ilham wacce jikinta yayi sanyi tace “sai haƙuri fah Malama Ilham, a hankali zaku saba in Allah ya yarda”
Ta haɗiyi miyau tare da durƙusawa a kan guiwowinta ta shiga lallashin Kiki saidai kaman wanda take ƙara Volume haka suka sha fama da ita na wurin minti 30 kafin da ta gaji tayi shiru don kanta, shima taƙi zuwa wurin Ilham firr sai Aunty Surayyah ce ta ɗaura ta a cinya ta bata abinci tayi mata wanka, Ilham ta dauko kaya aka saka mata.
….
ABDULHAMEED
Ya ɗauki kusan minti uku yana jira bayan ya turawa Excellency saƙon isowarshi kafin wani mutum ya fito sanye da ƴar shara da hula dara a kan shi, yayi masa iso cikin gidan.
Yayi tunanin su biyu zasu gana kaman yawancin lokutan da Excellency yake zaɓan suyi magana cikin sirri, amma a yau sai ya ci karo da baƙin fuskoki guda uku zaune a manyan royal chairs dake zagaye da babban parlourn.
A tsanake ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya don ya san da su waye zai zauna a ƙasan inuwa guda.
Ya gane fuskar mutum ɗaya a cikin su bayan yayi masa kallo na biyu amma sauran yana da tabbacin bai taɓa ganin su ba a rayuwarshi.
Wanda ke Hakimce a dogon kujeran dake kallon ƙofa ya ajiye tumbinsa ɗan dadai ya yafato Abdulhameed ɗin da hannu sannan ya bubbuga space ɗin dake gefensa ma'ana ya zo ya zauna.
Kan shi ya kulle gaba ɗaya, amma bai bari hakan ya nuna a fuskar shi ba ya ƙarasa ya zauna da ƙwarin guiwa.
Excellency yayi murmushi yana kallon mutanen dake parlourn, su kuma nasu duban na kan Abdulhameed ko zasu gano Abinda ke tattare da shi na musamman.
“Wannan da kuke gani shine tsanin da zamu haura zuwa ga nasara in sha Allah” cewar Excellency ba tare da ya bari Abdulhameed ya fahimci a kanshi suke magana ba.
Ɗaya a cikinsu ya gyara zama cikin rashin fahimta yace “Excellency, ga wa’inda suka goge a mulki suka daɗe ana damawa da su a siyasar ƙasar nan bamu riƙe su ba sai wani saurayi guda ɗaya rakk?”
Ya gyara zama a kujeran yana shafa gashin bakinsa murmushin kan leɓen shi yana ƙara faɗi, idanun shi a kan Abdulhameed da ya saka hankalin shi gaba don burin shi su gama abinda zasu yi su watse, Excellency ya sanar dashi dalilin kiran da yayi mishi na gaggawa ya samu ya koma wurin Kiki, shiyasa bai ma saka hankalin shi ya karanci abinda suke cewa ba.
“Baku san me nake hangowa game da shi bane. Su wa’inda kuke magana a kan su idan muke je musu da buƙatar mu ba zasu bamu goyon baya ɗari bisa ɗari ba har sai sun tabbatar sun kwashe kaso mai girma a cikin tafiyar nan, amma wannan sai yanda nayi da shi, wannan alƙawari ne a tsakanin mu.”
Mutumin da ya shigo da Abdulhameed ya dawo da tray mai ɗauke da ruwan gora a hannunsa ya ajiye a gaban shi sannan da hannu yayi mishi alaman ya zuba ya sha ruwan.
Yayi hakan a maimakon ya zuba masa da kan shi ne saboda ya isar ma sauran mutanen wurin saƙon Excellency na dalilin da yasa ya zaɓi yayi amfani da shi.
Saboda Nakasarsa.
…..
Zuwa Azahar daga ita har Hajiya Surayyah jikin su yayi laushi saboda yanda kiki take walagigi da rayuwar su, ta yi nan ta yi can, ta ce tana son kaza sai an yi mata tace ba shi ba. Gashi ko kallon arziƙi Ilham tayi mata sai ta saka ihu tana niman Daddynta.
Don haka Ilham ta shafa ma kanta lafiya ta tafi ɗakin da Aunty Surayyah tace zata iya hutawa a ciki tayi alwala tayi sallah Sannan ta wuce kitchen ta daura sanwan abincin Rana lokacin ƙarfe biyu ta kusa.
Shinkafa basmati ne tayi jollop ɗinsa ya sha carrot, green beans da peas tunda ta gansu a wadace a cikin fridge.
Tana yayyanka Albasa round-round zata zuba a kai lokacin ya kusa nuna sai ga Aunty Surayyah ta shigo.
“Ina fatan ba a kan abincin zaki saka wannan albasan ba Ilham”
Ta tsaya da yankan ta ɗago idanunta da suke tsiyayan hawayen yajin da albasan ke da shi tana jan hanci tace “a kan shi ne hajiya.”
“Ai Ikram bata cin yankakken Albasa, kuma tare suke cin abinci da babanta, ki bar shi a haka kawai”
Ita kuwa ina fasalin Jollop rice babu albasa a kai? Amma babu mai niman ra’ayinta don haka ta amsa da toh. Sai ta ajiye albasan a gefe ta ƙarasa girkin ta zuba musu a food flask ta kai dining.
Hajiya Surayyah ma ta saka mata a plate dukda bata tambaya ba amma ita san ya kamata ganin yanda suka wuni tare a cikin gida.
Da zata ci sauran wanda rage a tukunyan sai ta zuba albasan duka ta ci kayanta tana santi, sannan ta wanke komai a take a take ta kimtsa kitchen ɗin tass tana yi tana lissafin yanda zata kasafta Naira dubu ɗari nan da kwana talatin a cikin kanta.
Fitowarta daga kitchen ta hange su zaune a dining shi da Ikram, plate ɗin shikafan da ta dafa a gaban su yana ta cire carrot da green beans ɗin da ta zuba a ciki yana mayarwa gefe saboda kiki ta ce bata so.
Ta taɓe baki ganin samun wuri irin na ɗan Adam gashi ita tana niman kayan gina jikin ma mara lafiya amma bayi samuwa.
Bata ga Hajiya Surayyah a parlorn ba don haka ta ƙarasa kusa da table ɗin ta durƙusa kana ta gaida Abdulhameed da “Ina wuni”
Bai ji gaisuwan ba, har saida yaga alaman mutum a gefe kafin ya ɗago daga abinda yake yi, ya juya ya dubeta.
“Sannu ko” Muryar shi ya sake shiga kunnuwanta yana sanyata lumshe idanu tare da buɗe su a kan hannayenta dake bisa cinyarta, har yanzu da damshin ruwan da ta gama aiki da shi a jikin su basu gama bushewa ba.
Ta amsa tana sake gaida shi.
Ya ga dai alamun tana magana amma bata kallon shi.
Ya ajiye cokalin hannun shi ganin hankalin Kiki ya koma kan TV dake nuna kids show da ya saka mata, kuma ta ɗan ci abincin da yawa.
“Look at me”
Bata san da ita yake yi ba, muryar tashi ce kawai ta sanya dole ta ɗago ta kalle shi amma sai ta samu shima ita yake kallo.
“Amina Usman Jen.” Ya kira cikakken sunanta.
“Are You married?”
````````````
Seemahwrites ✨
ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a turo shaidan biya ta 09039206763