Chapter 21
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)
Wattpad and Arewapen @Seemahwrites
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
21… Ya riƙe Na’urar guda biyu a hannun shi na hagu da dama. A hankali ya kai jikin kunnuwan shi, ya tusa a cikin ramin kunnen saboda ƙanƙantan shi ya shige sosai yanda ba za'a iya hango shi daga waje ba sai an saka lura.
Komawa yayi ya jingina bayan shi da jikin kujeran da yake zaune a kai, yana ji a jikin shi wannan karon ma ba zai yi aiki ba, amma zuciyar shi tana faɗa mishi ba haka ba, yana jin kaman the result will be different this time, kaman daga wannan, rayuwar shi zata koma yanda take kafin Accident ɗin da ya sauya komai.
Ya kai hannu ya danna makunnin abun sannan ya zauna yana jira.
Ya cigaba da jira..
saidai shiru.
Shiru babu komai, ko da wannan ƙaran da yake ji a duk lokacin da ya gwada.
Hasken da wayar shi yayi ya rushe fatan da ya samu na cewa na’urar tayi masa aiki, shirun ɗakin ne yayi yawa.
Saboda bai ji ƙaran shigowar saƙon ba.
Bayi manta ranar da suna meeting a A&I. Ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kan mai yin presentation yana reading lips ɗinsa don ya gane abinda yake faɗa idan akwai abinda yake so a canza ayi nan take ba sai daga baya yayi zaman duba meeting Minutes ba su ma ya mayar da su baya.
Wayar shi dake kan table yana ta ringing kowa yana ji amma banda shi, har mai presentation ɗin ma saida ya tsaya saboda ƙaran yayi yawa.
Aunty Surayyah ta ɗauki wayan ta miƙa masa lokacin kiran ya dawo missed call tare da saƙon da aka ajiye masa. Saida aka tashi a meeting ɗin take ce masa ya bata wayan ta rufe masa muryan.
Ya girgiza kai. “Ina so in sani lokacin da ji na zai dawo koda ni kaɗai ne”
A yanzu ma bai ji ƙaran shigowan saƙon ba.
Sai ya cire Na’urar kawai ya mayar cikin gidan shi, ba yau ya fara gwadawa ba balle ya gagara jure zafin da yake ji a ƙirjinsa. Ya dai ɗauki tsawon lokaci bai gwada ba kafin yau, kuma dalilin yana da nasaba da maganar da Excellency yayi masa a kan Kiki da kuma… ya rintse idanu yana girgiza kai lokacin da ƙwaƙwalwar shi ta hasko masa fuskar Ilham a ganin da yayi mata da safiyar yau.
Ya buɗe su a kan wayan dake saman table a gefen case ɗin hearing aids ɗinsa, ya ɗauka ya kawo shi kusa da fuskarsa yana duba saƙon da ya shigo.
Saƙon guda biyu ne, na farko alert ne na shigowar kuɗin cikin asusun bankin shi, da ya fara ƙirga Zeros ɗin dake bayan lambar farko ya kai guda shida sai ya bar sauran kawai ya buɗe saƙo na biyu dake gwada sunan Excellency a kai, domin ya riga ya san kuɗin na menene.
‘Come in tomorrow and sign the contract. Da zaran ya cika mun samu abinda muke nima zan maido maka da patent ɗinka’
Ya miƙe tsaye yana zura wayan a aljihu ba tare da yayi reply ba tun da dole duk yanda Excellency yace haka zai yi.
parlour ya koma wurin Kiki, sai ya samu har tayi barci a kan kujera ga laidan sauran biscuit mai filling ɗin dabino da ta gama ci a matsayin abincin dare a gefen ƙafar ta, yau daga ita har shi sun gagara cin abincin da yayi musu order sai kame-kame.
Kewar abincin Ilham yake yi, wannan spaghetti da meatballs ɗin, jollof rice ɗin da ta fara girka musu, harma da tuwon da tayi ya ci ba don ran shi ya so ba, idan da zai samu yanzu zai sake ci.
Amma a yanayin da ta bar gidan zata kwana biyu kafin ta samu sauƙin dawowa bakin aikinta.
…..
ILHAM
Tare da Ihsan suka koma gidan zata tattara kayanta ta mayar gidan su Khausar, kaman yanda Yaya Aliyyu yace bai yarda wani abu nata ya sake kwana a gidan Ilham ba bare ita kanta.
Saida ta gyara ma Ilham gidan tass tana tilasta mata ta zauna ta huta kawai, sannan ta shiga haɗa kayanta a cikin akwati.
“Filiyan kiyi haƙuri dan Allah” Ilham dake zaune a gaban akwatin da Ihsan ta kwantar tana naɗe kayanta masu datti da bata samu daman wanke su ba tana zubawa a ciki ta ƙare tayi magana, bayan dogon shirun da ya ratsa a tsakanin su.
“Meyasa zaki bani haƙurin laifin da ba naki ba? Na san a sanadi na aka sauya miki kamanni, kuma Wallahi ko wuƙa za'a saka ma Ya Hashimu a wuya ba zai iya kawo dalilin da yasa yayi mana wannan wulaƙancin ba, amma ya jira, kwanan nan zan bashi dalili in sha Allah don wallahi sai kin bar gidan nan, ai mutum ce ke mai rai da hankali ba dabba ko itace ba”
Ilham ta girgiza kai “Ki bar maganan nan dan Allah, bayi da amfani. Duk abinda zan faɗa miki ba zaki gane ba Filiyan, don ni da wanda ke cikin hali irin nawa ne kawai muka san me muke ji”
“Sai kuma aka ce miki zama dashi dole? Tunda Allah ya haɗa ki da Azzalumin miji ba sai ki ƙara gaba ba? Ko mutuwa zaki yi idan kika rabu da shi?”
“Idan ni ban mutu ba Muftee fah?”
“Oh daman shi yake busa mishi numfashi? Ko akwai uban abinda yake tsinanawa Muftee ɗin a yanzu?” tana huci ta wurga pink ɗin Polo shirt ɗinta da ta gama linkewa a cikin akwatin har saida ya warware.
Ilham tayi shiru ganin ranta ya ɓaci sosai.
“Ki zauna ya kashe ki kinji” ta ja tsaki tana cigaba da abinda yake gabanta.
Murmushin da yafi kuka ciwo Ilham tayi tace “Na faɗa miki ba zaki gane bane Filiyan. Amma ba'a bazawari sai bazawara, ma'ana babu wanda yake kallon laifin namiji a mutuwar aure. Kece kawai mutuncin ki zai zube a idanun jama'a, haka za'a yi ta ganin ki da laifin kashe auren ki da kika yi duk inda kika ratsa ana yamaɗiɗi da ke, shiyasa aure rufin asiri ne”
“Wani auren ba? Banda irin naki wallahi. Auren da akwai mutunci da kwanciyar hankali a cikinsa ne ake kira da Auren rufin asiri, amma idan ta bakin mutane zaki bi ranan da aka kawo gawan ki sai sun yi ƙorafin ta hanyar da kika mutu bai yi musu ba.”
Ta sani daman duk bayanin da zatayi ma Ihsan ba zata fahimta ba, amma ita ta san abinda take hangowa.
Ta yi shiru tana sauraron Ihsan ɗin tana ta zazzageta kaman itace gaba da ita har ta gama haɗa komatsenta zata tafi ta fito rakata sai ga Hashim ya shigo gidan da laida a hannun shi.
Ilham kaman ba zata yi masa magana ba, don bayan sallama ko sannu da dawowa bakinta yayi mata nauyin furtawa, shi kuma ya musu tsaye bai kauce ya basu hanya ba kuma bai ce komai ba, yana riƙe da baƙin laida a hannu.
Ta ƙare tace “Ga Filiyan ɗin zata tafi”
“Ai mun gama magana na fahimta da Aliyyu kuma na yarda ta zauna” Da shirinsa na ya lallaɓata ta cigaba da zama ya zo a fasa zancen zuwanta gidan su Khausar.
“Eh shine yace ta tafi gidan Baffa Rabe, zata bar mana gidan ka sha iska daman mun takura ka”
Ya kalli Ilham da mamaki jin maganan da ta yaɓa mishi amma kwantacciyar wutar da ya gani a cikin idanunta ya saka yayi shiru, don sai yaga kamanta da Ihsan ma ya ƙara fitowa duk da gefen fuskarta na lulluɓe cikin farin bandeji.
Ya dubi Ihsan da ta saka ma bakinta sakata saboda kawai a zauna lafiya, ya ƙaƙalo murmushi yana miƙa mata laidan hannun shi.
“Har kuwa na yo miki tsaraba”
“Tsaraba ya wuce wanda nake samu a toilet da ƙamshin sa yake cika ko ina? Wancan ma ya ishe ni Nagode sai anjima” bata tsaya jiran rakiyan Ilham ba ta kinkimi akwatinta tayi gaba suka yi mata rakiyan idanu. Ƙafa ta saka ta hankaɗa ƙofar tana ficewa ta sake hankaɗo shi ji kake yi Bammm. Ilham ta lumshe idanunta da hawayen ciki zuwa yanzu sun fara kafewa, kamar zuciyarta Ihsan tayi wa wannan bugun haka ta ji, babu shakka Hashim yayi nasaran samar da giɓi a tsakaninta da ƴar uwarta mai sonta da fahimtarta tun da gashi sun gagara samun daidaito a kan shi.
“Kin gani ko? Kin ga dalilin da yasa nace Ƙanwar ki sai ta bar min gida? Wallahi baku da tarbiyya, ban san menene baffa Usman ya gani a jikin Jamila ba, gashi ta zo ta ɓata mishi gid…”
“Ya Isheka zagin Maama nah Hashimu! Ya isheka Wallahi. Ina so ka sani ba don Maama ba, ba don ta hore ni da yiwa mahaifina biyayya ba da ba zaka ganni ba balle kayi mun Abinda ka ga dama.”
Baki a buɗe ya saki laidan hannun shi a ƙasa tsaban kaɗuwa,sai ga yalon bello da ayan ruwa da ɗinya suna gudundule a tsakar gida.
Bai taɓa tunanin ko a zuciyarta Ilham zata iya faɗa mishi magana irin haka ba balle a gaban idanunshi.
“Me nayi maka? Me nayi maka ka tsane ni haka? Idan Muftee ne ba ni kaɗai na haife shi ba. Da ace jininka ba irin nawa bane da lafiya ƙalau zamu haife shi, bayan wannan da muka yi tarayya a ciki sai ka faɗa mun menene laifina na musamman?”
Yatsar shi yake kaɗawa yana gwada ta dashi cikin rasa ta cewa.
“Gajiyan da na tara miki bai ishe ki ba ko?” ya samu bakin shi ya buɗe yana muzurai.
murmushi mai sauti tayi. “Don Allah ka kashe ni ka huta ko Ahalin Baniza zasu baka kambun jinjina, daman sun baka wani a ranan addu'an ukun Taa(babana) sai su ƙara maka wani”
Ta ja tsaki ta juya ta bar shi a wurin da shi da su yalon bellon shi.
…..
Rabe ɗan sha'ani, baka faɗa da kowa sai ɗan sa Ido. Wannan shine taken mahaifin Khausar tun a zamanin samartakan shi.
A cikin yaran dijengala idan ka cire Ussy da sauƙin kai yake a halittar shi, shine kawai bai ɗauki ƴan ubanci ba don dukda baya jin magana a lokacin amma shi ya fara zaman gidan Baniza tare da yaran Amina.
Haka zai dinga tura yaransu su siyo masa sigari ko maganin mura, idan iyayen yaran suka tunkare shi da maganan sai ya sauƙe kai ya basu haƙuri amma gobe ma sai ya sake.
Shine yayi sanadin farkon haɗuwan Abdulhameed da Aliyyu.
A shekaran da Abdulhameed ya haɗu da Ilham Aliyyu yayi paper, shi kuma A Moher canje-canjen makaranta ne ya maida shi baya amma ya bashi kusan shekara biyu.
Ranan da Rabe ya fara aikan Aliyyu siyo masa sigari, Aliyyun ya je ba don ran shi ya so ba sai domin yanda Rabe ɗin ya dinga roƙon shi kaman ƙanin shi.
Yanda ya karɓi kwalin da malam Sama'ila ya lulluɓe masa a cikin baƙin laida tare da gargaɗi mai yawa na kada ya sake dawowa idan ba haka ba zai faɗa ma mahaifinsa, juyawar da zai yi, Abdulhameed dake tsaye a bayansa sanye da Uniform ɗin makaranta ya saka hannu ya karɓe laidan Sannan ya miƙa mishi Naira ɗari biyar sabuwa ya sayi wani.
Banzan kallon da Aliyyu ya bisa da shi ya tabbatar masa kaurewa ne abinda zasu yi na gaba.
“Na san gidan ku, na san babanka da inda yake aiki, and I can tell him if I want”
A cikin faɗan malam Sama'ila ya samu abinda yayi masa barazana da shi, amma ko wuƙa aka saka mishi aka ce a arean ya gwada ina ne gidan su Aliyyu saidai a cire mishi wuya.
Kuma tun daga ranan ne ya samu daman aikan Aliyyu in dai yana sanye da Uniform ɗin makaranta har zuwa ranar da ya gan shi tare da Ilham.
.
Da kan shi Baffa Rabe ya fita ya shigo ma Ihsan da akwatinta yana share mitan da Maman Khausar take yi a kan ya kawo mata ƴar Jamila, ya kai mata kayan har ɗakin da Khausar ke kwana tare da ƙanwar ta.
Duk butulcin sa ba zai manta da halaccin mahaifin su Usman a gare shi ba, shine ya tsaya masa ya samu aikin da ya rufa ma kan shi asiri har zuwa yanzu.
Ihsan ma tunda ta gaidata ta nemi wuri a ɗakin ta zauna, zata jure duka wannan a kan Ilham, saboda tana da tabbacin Ilham zata iya mata fiye da haka idan itace ta samu kanta a cikin halin da take ciki.
Saida aka kira isha ta fito zata yi alwala sai ga baffa Rabe ya shigo mata da laidan awara mai zafi da Cway peach mai sanyi sosai har ya fara ƙanƙara.
Daman cikinta yana kiran chiroma domin yau abincin ƙofar asibiti ta siya suka ci ita da Muftee ganin har rana tayi sosai Ilham bata zo ba.
Saida ta gabatar da sallanta sannan ta zauna a nutse ta cika cikinta, ta cigaba da amsa waya tana ganin kiran Sageer dake shigowa lokaci bayan lokaci yana jinta on another call, ba zata yi blocking ɗinsa ba idan ya gaji ne zai ƙara gaba.
Sai wuraren ƙarfe 10 Khausar ta dawo ɗakin, kuma har kowa tayi barci a cikinsu babu wanda tace ma ƴar uwarta ƙala.
….
7:18am.
A sannu yake takawa zuwa ɗakin Kiki, yana sanye da kayan barci shirt da dogon wando baƙi mai laushi da yayi complimenting fatar jikinsa, takalmin ƙafar shi ma na kayan ne.
Yana so ne ya fara shiryata kafin yayi wanka idan ba haka ba sai ta ɓata masa kaya.
Ya murɗa handle ɗin ƙofar ya tura a hankali, idanunshi suka fara sauƙa a kan Ilham dake zaune a bakin gado kafin Kiki dake tsaye a gabanta sanye cikin uniform, gashin kanta rike a hannun Ilham ɗin tana taje mata.
Sai ya tsaya kallon su da mamaki kaman yanda suma suke mishi.
“Meyasa kika zo?” fatar girarsa ta tattare lokacin da yayi mata wannan tambayar.
Har zata sauƙe kanta don ba zata iya cigaba da jure kallon cikin idanunsa ba sai kuma ta tuna da abinda ya faɗa mata.
“Ba zan sake latti ba ayi haƙuri dan Allah…”
“Nace ma Aunty Sharmama a bari ki samu sauƙi kafin ki dawo bakin aikin ki” ya katse ta.
ko bayi da imani ba zai koreta a kan abinda ya faru jiya ba, kuma a hakan ma saida tazo.
“Na samu sauƙi, Nagode”
Sai ya koma da baya kawai ya jawo ƙofar ya rufe musu ya koma yayi shirin office.
Indomie da dafaffen ƙwai tayi musu a matsayin abun karyawa kuma ya ji daɗin da bata ce zata wahalar da kanta ba.
Saida ya saka ma Kiki hearing aid dinta ya fita daga gidan ya bar Ilham tana saka mata takalmi, ganin ta fara yarda da ita sai ya ƙara samun nutsuwa, ya zauna a mota yana jiran su.
“Kiyi Addu'a” tace ma kiki lokacin da zasu fita daga cikin gidan.
Sai ta ɗago ta kalleta tana yamutsa fuska “wani addu'a?”
“Addu'an fita daga gida”
“Ni ki barni in tafi” ta fara ƙoƙarin kwace hannunta da take rike da shi
Da ta dage mata sai tace “bismillah” kawai.
“Tawakkaltu…” Ilham ta cigaba don ta bi bakinta ta ƙarasa.
Daga yanda Kiki ta maimaita kalmar Ilham ta fahimci bata saba da furtawa ba.
“Wa la haula…”
“Nikam ki kaini wurin Daddy na gaji” ta fara mata rashin kunyar da Ilham tayi tunanin mantawa tayi.
Sai ta ƙarasa addu'an kawai ta tofa mata, Abdulhameed yana kallon su ta cikin tinted glass ɗin motar har suka ƙarasa Kiki ta buɗe ƙofar ta ɗaya gefen da yake zaune ta shiga driver ya ja suka barta tsaye idanunta suna yiwa motar rakiya.
`````````````
Seemahwrites ✨
ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a turo shaidan biya ta 09039206763