← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 30

Chapter 8

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites*

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


08… KADUNA 2026.

Sallamar da ta shigo gidan da ita ne ya katse lokacin da ƙafarta ya shiga cikin plate ɗin da aka gama cin abinci aka ajiye daga bakin ƙofa. Ta ɗaga dubanta daga kai bayan ta tabbatar bata fasa ba sannan ta shiga kallon parlourn wanda kaman anyi wasan dambe a tsakiyar sa.

Yana da ɗan girma amma Babu komai na kayan ƙawa a ciki, Daga labulen dake maƙale a bango don suturta mata ɗakin sai carpet ɗin tsakiyar ɗaki da take da tabbacin ta ƙalƙale shi kafin ta fita asibiti jiya, amma yanzu wari yake yi.

Ba sai ta nemi dalili ba don ga kofin ruwa dake kife a wurin. Gefen shi kuma farin singlet ne, daga inda take tsaye kuma tana iya hango stain ɗin manja a jiki, sai rigan jamfa light brown da baƙin boxers yashe a hanyar da zai sada ta da bedroom.

Bata ji komai a ranta ba domin wannan yanayin ya riga ya zame mata jiki, rashin lafiyar muftee ne dai ta gagara sabawa dashi har yau. saidai shima ɗan kukan da ta samu tayi yau ya sanyaya mata rai kaɗan, kuma gobe sammako zata yi ma Hajiya Surayyah Kagarko tunda tayi mata alƙawari.

Tsugunawa tayi ta haɗa kwanukan a wuri guda sannan ta tattara kayan a hannunta ta nufi uwar ɗaka da su, tana daff da shiga ta fara jiyo murya na magana ƙasa-ƙasa.

“Uhmm baby nah?... Rowan ganinki kike mun ina?.... Toh yaushe zan zo?”

Ta sauƙe numfashi kana ta ɗaga labulen ɗakin ta kutsa kai.

Hango shi tayi kwance yayi ɗai-ɗai a tsakiyar gadon wanda shimfiɗin shi yake a yamutse kaman wanda take da wasu yaran masu hawa suyi birgima a kai, yana sanye da wandon jamfar da ta tsinci rigan shi a parlour.

Ta kalle shi sau ɗaya ta wuce jikin buhun da suke tara kayan wanki daga ƙofar banɗakin su ta zuba kayan hannunta a ciki, tare da zame hijabin wuyanta shima ta jefa don tun shekaran jiya take yawo dashi har tsami yake yi.

Tana jinsa yana cigaba da wayan shi hankali kwance ba don bai lura da ita ba sai domin sanin babu abinda zata iya aikatawa a kan hakan.

“Me yasa zaki dinga zama da yunwa?... Ba nace bani so ba?” ya ƙara kashe murya yana karkaɗa ƙafan da ya daura ɗaya bisa ɗaya.

Ita sai yanzu ta tuna da rabonta da abinci tun safiya, hala shiyasa ma take jin ta jigata sosai duk jikinta ciwo yake yi yanzu haka musamman ma mazaunanta.

Cikinta ne taji yayi wani irin ƙugi lokacin da ya ambaci

“toh yanzu me zaki ci? Shawarma?.... Da me kuma?”

Wanka taso shiga amma sai ta fasa, gwamma ta zauna ta jira shi har ya gama, sanin ƙaramin aikin shi ne cikin ƴan mintuna zata fito ta samu ya kwanta ya rufe idanunsa, kuma duk yanda zata yi ba zai kulata ba tunda ya san farkon wata ne zancen baya wuce na kuɗi, Idan ta matsa kuma yayi fushin gan-gan ya naɗa mata na jaki a cikin daren nan.

Haka suka gama tsinke furen su da koma wacece bata damu ba. Ita dai fatan ta ɗaya Allah yasa ta samu wani abu a wurin shi ko na abun hawan sintirin asibiti ne ta rage.

Ta fi minti 30 tana zaune a wurin tana tunanin sallolin dake kanta ga alƙawuran ƙarya da yake ta shirgiɗa ma ƴar mutane dake shiga cikin kunnenta. Mutumin da ya gagara riƙe mata ɗaya da ɗa ɗaya shine yake mata alƙawarin aure kwanan nan take yarda?.

Taɓe bakin da yaga tayi tare da sakin ƙaramin murmushi yasa yayi ma budurwar sallama ya katse kiran da suke yi ta WhatsApp cikin tsarguwa.

Tayi saurin gaida shi da “A fa fiyan Ya Hashim (ina wuni ya Hashim)”

Saida ya tsare gida sannan ya fara da faɗin “sai yanzu kika ga daman dawowa daga gantalin taki ina?”

Da ace baya cikin hankalinsa ne sai tayi tunanin bai san daga ina take ba, amma sanin niman wani abu take yi daga gare shi ya sanya ta karya murya kana ta amsa da “Jikin Muftee har yanzu babu daɗi, kuma babu kowa a jikin shi balle in samu in sato jiki in dawo, yanzu ma da na koma can ɗin Khausar ce tayi mun alfarmar kwana tare dashi in zo in huta.”

Shima ya san da hakan, shiyasa ya baje kolin shi a gidan da tunanin ba zata dawo ba saida safe “Daman ai ke kullum kina da tacewa, ba'a kada ke a baki. Amma wallahi ki bari na cigaba da tara ki Ilham hukunci zan ɗauka da hannuna ba tare da mun dangana da wurin Baba babba ba ma, ni Hashim na isa in yi maganin ƙaramar mara tarbiyya irin ki, tashi ki bani wuri.” Ya yunƙura ya kai mata dukan da ba don ta saba da saurin hannun shi ta ƙware a kaucewa dukan da yake kawo mata a kowani lokaci ba da tabbas ya same ta.

Ta miƙe a kan ƙafafunta tana ganin yanda yake watsa mata mugun kallo mai cike da tsana, wanda ita kanta ta shiga kokwanton ko akwai lokacin da Hashim ya taɓa kallonta da ƙauna a idanunsa, kaman ba'a yi lokacin da yake nuna mata soyayya gabanin rasuwar mahaifinta ba.

Ta haɗiyi miyau ko wani abu mai zafi da ɗaci da take ji a maƙogwaronta zai samu ya wuce amma abun bai matsa ko nan da can ba.
Ko kuɗin da zata hau napep ta tafi asibiti gobe babu, babu abinci a gidan bayan garin masara da bai wuce mudu biyar ba da shinkafar da bata saka ran zai kai mudu ɗaya, babu manja ba mangyaɗa balle a je zancen maggi da kayan miya, kuma ya sani tunda wata ya ƙare har an shiga sabuwa bai siyo ba bai bata kuɗin siya ba, kuma ya san tana tafiya da abinci asibiti tunda ɗan shi ne kwance a can yau fari gobe tsumma.

Ya ja dogon tsaki tare da juya mata baya yana mai cigaba da danna dalleliyar wayar shi wanda bata ma san wacce ƙira bace domin bai daɗe da siya ba kuma bata da ikon kai hannunta jiki.

Ta buɗe bakin da yayi mata nauyi saboda kukan da ya fara zuwa mata, daman ba wai ta ƙoshi da shi bane ɗazu, haske mata fuskar da aka yi da lantarkin mota ya sanya ta haƙura ta share hawayenta ta ɗauki hanyar komowa babban asibiti da sawayenta tunawa da cewa bata da ko sisi.

Murya na rawa tace “Baban Muftee babu abinci a gidan nan. Dan Allah ka taimaka kayi mana cefane ka ɗan bani wani abu ina yin na adaidaita dashi, sai in ji da na asibitin da sauran abinda ba’a rasawa”

Wani ƙundumemen ashar da ya juyo ya watsa mata ya sanya ta rugawa da gudu ta shiga banɗakin ta rufo ƙofar tare da saka sakata ta ciki domin tana da tabbacin da ta bari ya riƙeta toh fa saidai hala idan shine zai je zaman jinyar Muftee da kanshi gobe.

Hannu ta saka ta dafe kunnuwanta lokacin da ya tokari ƙofar da ƙafar shi kaman bai san tsakar dare bane. “Shegiya tsinanniya! Dan abu ta kazan uban ki babu abinda kika iya sai buɗe bakinki mai shegen wari kiyi ta ci gashi dai ko nunawa baya yi a jikin ki domin ni ba gane komai nake yi ba, da wani shegen baƙi kaman zunubi! Idan jinyar tsakani da Allah ne ba gashi masu maganin gargajiya suna bada maganin da yake warkar da sickler ɗin ba? Kawai Kina yawon banzanki kin fake da asibiti sai lale mun aljihu kuke yi Munafuka! Ko nine na ɗora mishi rashin lafiyar?”

Hawaye take zubarwa tana durƙushe a gaban shaddan da aka yi amfani dashi ba tare da an damu da a kora da ruwa ba.
Hawaye ba na zagi da kushewar halitta da yake yi mata ba, wannan ya zamo mata kaman ruwan sha. Hawayen zagin mahaifinta da yake cikin ƙasa da kuma na danasanin kasancewar ɗanta matsayin jinin Hashim a karo na barkatai take yi.

Ya dauki lokaci yana mita da zage-zage don saida ya tabbatar bai bar mata ƙofan da zata sake tambayar shi wani abu a kwanan nan ba sannan ya koma gado yayi kwanciyar shi, chatting ɗin ma ya haƙura dashi.

Saida taji shiru kaman na mintuna 20 zuwa 30, ta tabbatar cewa ya kwanta, sannan ta miƙe tsaye ta kwaɓe kayan jikinta.

A hankali yanda ba zata yi ɓuruntu da yawa ba ta kora shaddan kada ace ba barci yayi ba ya ƙara samun dalilin sababi, ga banɗakin yayi kaca-kaca, ta saka ma ranta dai saida safe kafin ta wanke shi, amma koda ta duba bata ga omo ko sabulu da zata wanke jikinta dashi ba ko ɗanɗani.
Ɗan kilin da ta siya na ɗari da hamsin jiya ta ajiye daga windown toilet ɗin ya ƙarar dashi tass sai laida ya bar mata.

Ruwa mai sanyi ta fara jiƙa jikinta dashi sannan ta jijjige laidan klin ɗin ta zuba ɗan ruwan kumfan a jikin sosonta ta cuɗe jikinta dashi kana tayi alwala ta fito cikin sanɗa, har ya fara sake minshari kuwa. Ta siɗaɗa zuwa ghana must go ɗin kayanta ta ciro wata shuɗiyar atamfa rubber ɗinkin doguwar riga da hijabi tiyebo ja, ta janyo darduma daga kan ƙofa ta fita parlour ta shimfida ta tada sallan Maghriba da Isha dake kanta.

A kowani sujjada idan ta saka goshinta a ƙasa sai ta rasa me ɗaya zata roƙi Allah ko kuma ta ina zata fara domin komai ma baya mata daɗi, amma sai ta samu kanta da yi mishi godiya tana zubda hawaye saboda akwai masu son irin rayuwanta da yawa kwance a gadon asibiti, indai zasu kasance cikin ƙoshin lafiya kamarta tabbas zasu so ace da sune a matsayinta.

A kan darduman da tayi sallah tayi kuka a wurin gajiya ya rako barci suka saceta dukda yunwa dake ƙwaƙular hanjinta.
….

Agogo ya kalla lokacin da ya fito daga bathroom ɗaure da farin towel a ƙugun shi, jikinsa yana fitar da tiririn zafin ruwan da yayi wanka dashi.
Ƙarfe sha ɗaya har ta gota, yayi saurin tsane jikin shi ya laluɓo baƙar jallabiya da gajeren wando ya saka. Ba zai taɓa iya zama babu turare ba balle ya fita a haka shiyasa har ya iya tsayawa ya shafa designer Oil perfume ɗinsa na Bakhoor by Seemah(08021689184) sannan ya ɗauki wayan shi da agogon hannun shi ya fita bayan ya kashe wutar ɗakin.

Driver dake zaune a cikin mota yana jiransa daga mashigar ɓangaren yana hamma tare da kare bakinsa da bayan hannun shi na hagu ya gyara zama yana wartsakewa da ganin fitowar Abdulhameed. Yayi ƙoƙarin yaƙi da duk wani barci da ya fara kawo masa ziyara saboda ba zai yi gangancin sake ɓata mishi rai ba, musamman a yanayin da yake ciki.

Tare suka fita da safe, ya kaishi wurin ganawar da suka yi da kamfanin da zasu basu wasu daga cikin kayayyakin amfanin marasa lafiya, kuma ganawar tasu a ɗauki tsawon lokaci shiyasa da lokacin Sallah yayi ya rufe highlander ɗin da suka fita a cikinta kasancewar ya kai ɗayan motar wurin wanki, yana idarwa kuma bai tsaya dogon addu'a ba ya fito sanin cewa shima ubangidan nashi zai iya fitowa a kowani lokaci, amma sai riskar shi yayi a jikin motar yana ƙwala masa kiran da ko shi ya amsa ba ji zai yi ba.

Da sassarfa ya ƙarasa wurin, Kuma Abdulhameed bai tsaya tambayan shi inda yaje ba ko yayi mishi bayanin abinda yake faruwa, ya wafce key ɗin motar daga hannunsa ya faɗa ciki, ya zugeta a ɗari ya bar shi a wurin.

Sai da ya koma gidan yake jin cewa ai Ikram ce ta faɗi a kan keke ta samu targaɗe a hannu, har an kwantar da ita a asibiti.

Abdulhameed ya fi zama a gaba ko ina ne zasu je amma a yau tunawa da hatsarin da suka yi da Nne da yayi, ya sake ganin komai a cikin idanun shi kaman jiya ne ya faru, ya sanya shi buɗe back seat ya shiga.

Saida drivern ya kunna fitilun motar da zasu fita a gidan ya tuna da ganin Ilham da yayi ɗazu da ya dalle mata idanu.

A lokacin da ta kare idanunta daga hasken, Reverse yayi, amma idanun shi a kanta har saida ya juyar da kan motar, hasken da suka bayyana mishi ita suka koma kan gate ɗin asibitin.
Ya sake juyowa yayi mata kallon ƙarshe a cikin duhun, yana daɗa samun tabbacin ita ɗin ce tabbas saboda Birthmark ɗin ƙasan bakinta.

Wannan birthmark ɗin da yake mata kyau a lokacin baya.

Amma yayi mamakin yanda ta canza tayi baƙi ta koma wata iri.

Bai tsaya mamakin abinda ya kawota asibiti ba sanin cewa ba zai wuce dalilin da ya kawo shi ba shima, ma'ana rashin lafiyar wani nata. Kuma kukan da yaga tana yi ya saka mishi yaƙinin mai jinyar na da kusanci da ita sosai, domin shima da ance mishi idan yayi kukan Kiki zata warke da tsaff zai yi.

Shiyasa a yanzu ma yayi ƙoƙarin cireta daga cikin tunanin shi har suka isa Medi-plus hospital yaje yaji da abinda ya dame shi.

Yana isa ya samu Aunty Surayyah zaune a gaban gadon Ikram tana cin tuwo a plate.

Ya manta da ana jin yunwa ma dukda kasancewar rabon shi da abinci tun breakfast da suka yi tare da Kiki.
Shima ƙarewa yayi a lallaɓata ta samu ta saka wani abu a nata cikin saboda kukan ciwon kai da take yi mishi, shiyasa ma bata je makaranta ba, ya fita ya barta da Nanny ɗinta.

Aunty Surayyah tayi mishi alama da har yanzu bata farka ba tun kafin ma ya tambaya, ya gyaɗa mata kai yana zama a bakin gadon tare da leƙa fuskar Kiki da yake ganin kaman har ta rame a wuni guda kawai.

Juyowa yayi ya fuskanci Aunty Surayyah yana mata alamun kai cokali baki sannan ya nuna Ikram da yatsa yabi ya ware hannun. A matsayin tambayar ita Kiki mai zata ci idan ta tashi.

Nuni tayi mishi da tuwon da take ci a plate sannan ta buɗe baki can ƙasa da murya tace. “Da ɗumi tuwon, ɗazun nan na saka aka tuƙo shi daga gida domin zai fi mata sauƙin ci. Kaima ka samu ka saka ko kaɗan ne a cikin ka”

Ya girgiza kai yana yamutsa fuska, samm baya son tuwo ko miyar menene, musamman tuwon shinkafa dama-dama semovita, rabon shi da na gari kuma ana niman shekaru uku da ƴan kai.

Saida ta haɗa mishi tea ya sha ya taɓa bread ɗin da ta tura aka siyo slice biyu, sannan ta yarda ta tafi gida ta huta kaman yanda yace. Haka ya koma gaban gadon yana kallon Kiki kawai don tsoron taɓata yake ji kada ya fama mata ciwo a rashin sani.

…..

ILHAM

Dake yunwa ba ƙanin ubanta bane ƙarfe uku da Arba'in na dare sai gata tana haɗa garin kwaki. A cikin drawern kayan Muftee kuma ta samu wani ɗan ƙullin sugar da ta ɓoye. Hashim ya buɗe baki yana ta sharar bacci har ta wanke garin a banɗaki ta wuce shi ta koma bai ko motsa ba, haka ta zauna ta saka sugarn da bai ishi garin ba amma daɗin shi take ji har maɗiga saboda yanda taji yunwa.

Da tayi sallar asuba ta so sake komawa ta kwanta ta daɗa huta gajiya amma bata son yin lattin zuwa wurin Hajiya Surayyah musamman yanzu da bata da kuɗin napep ɗin zuwa A&I, idan takawa zata yi a sayyada kuma dole sai tayi sammako ta samu isa a kan lokaci.

Wayanta ta fara jonawa a caji don har lokacin akwai wutan nepa, ta naɗe carpet ɗin parlorn ta fita ta shanya shi a garu iska ya ɗauke warin, da sanyin asubahi ta fara sharan tsakar gidan, ta dawo ta gyara parlon tass sannan ta ɗaura mishi ruwan wanka a kan murhun gawayi ko zata samu dalilin da zai tashi ya bata wuri ta gyara uwar ɗakin don idan ta tafi ta bar mishi ma ba gyarawa zai yi ba.

Sauran shinkafar da ta rage musu ta juye a farantin silver ta gyara, idan masu shagon unguwan sun fara fitowa sai ta karɓi bashin mangyaɗa, maggi da barkono ta haɗa dashi a lallaɓa.

Da ruwan ya tafasa ta fara shiga ta kora banɗakin da ruwa da tsintsiya tunda ba omo, kafin ta sirka mishi ruwan a bokitin plastic ta koma tashinsa a barci yana ƙunƙuni kaman wani ƙaramin yaro, haushi kaman ta kifa masa mari da zata iya.

Tana cikin kaɗe zanin gadon ya leƙo kanshi daga banɗaki.
“Ilham ina sabulun wanka?”

Sai ta kalle shi sheƙeƙe “ai ya ƙare ya Hashim, nima jiya a haka nayi wankan”

Tsaki yayi “Shiyasa ai ba zaki daina wari ba” ya sake jan wani tsakin.

Ya fito ƙofar banɗakin inda ya jefar da wandon da ya kwana dashi a jikinsa ya ɗauka ya mayar sannan ya duba rigarta da ta gama yamutsewa a cikin kayan wanki ya saka yana ƙwafa “ina ƙyashin wanda kike sakawa nake amfani dashi kike ji? Wallahi zaki ga baƙin hali, dani kike zancen” ya fice daga ɗakin ita kuwa ta cigaba da abinda ke gabanta gashi ƙarfe 7 ta gota.

Kafin ya dawo ta gama da abinda zata iya a ɗakin taje ta sauƙe shinkafar da ya gama nuna. Shikuwa ganin tukunya a kan murhu da zai wuce sai yayi zaman jiranta ta kawo masa abin karyawa bayan ya gama shirin fita.

Wanda zata kaiwa Muftee da Khausar da kuma wanda zata ci da rana ta fara zubawa a babban cooler ta yaryaɗa masa man da ta soya ko albasa babu, da yajin da ta daka a turmi tana zaune a wurin, ta samu laida ta ƙulle kwanon a ciki ta ɓoye, sauran kuma ta zuba a faranti ta barbaɗa mishi maggi rabi sannan ta saka cokali, ta shiga dashi ciki wurin Hashim dake zaune a saman darduma da ya shimfida a kan tiles ɗin ɗakin, cikin shigar shi ta kamala sanye da yadi mai kyau da ya sha ɗinki harda hula, sai zuba ƙamshi yake yi hankalin shi na kan wayan da yake dannawa.

Kallonta yayi bayan ya ɗago idanunshi daga kan shinkafar da bai san ko mai ma babu a cikinta ba, amma ya tabbata yaji lokacin da take daka yaji shiyasa ya tsaya yayi manejin koma menene take dafawa da saidai yayi karyawan shi a waje.


`````````

Seemahwrites ✨
Chapter 8 · 0% Book details