← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 25 OF 30

Chapter 25

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

Wattpad and Arewapen @Seemahwrites

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


25… Ba'a rufa kwana biyu ba sai ga wata daban ta zo. Ita dai ta Iya gaida Ilham kana ta gabatar mata da kanta da sunanta Ameerah, kuma ƙanwar Abdulhameed ce sannan ta faɗi abinda ya kawota.

Haka ta sake zuwa ta juye musu abin karyawanta, ta jira har saida ta gama abincin rana kafin ta samu abinda ta saka a cikinta mai nauyi.

Kaman da wasa sai suka maida hakan dabi'ar su, haka zasu zo su karɓi rabonta a barta da kame-kame, kuma tana tsoron taɓa sauran abubuwan da ba'a mata izini a kai ba ta koma ɓarauniya.

Ranan Alhamis da tayi chips and eggs na karyawa, bata jin motar su Abdulhameed ya bar unguwan Hudah ta zo ta karɓa, hakan bai yi musu ba, tana gama vegetable couscous da rana sai ga zakiyya da Ameerah sun zo a tare, ko su wanda ta dafa abincin domin su basu kai ga ci ba suka shigo har cikin kitchen ɗin kowa da plate ɗinta da suka ɗauka a cikin wanda ta wanke ta jera su a dish rack, suka ɗebi abinda yayi musu a cikin wanda tayi niyyar ɗiba ma Hajiya Surayyah da wanda zata kaima Ihsan da Muftee.

Bata jinjina ma lamarin su ba saida ta fito parlour ta same su sunyi ɗai-ɗai, sun kunna TV suna ci suna kallo, ga lokacin tashin su Kiki a makaranta yayi.

Ganin abin nasu na niman wuce gona da iri gashi duk gyaran da tayi ma wurin sun ɓata shi, couscous har kan carpet, sai ta kasa haƙuri ta je kansu ta tsaya “Bayin Allah zan rufe gidan mu je ɗauko Ikram daga school”

Wani wulaƙantaccen kallo kawai Ameerah ta watsa mata, sai Zakiyya ne tace “kiyi tafiyar ki mana ai muna nan, mun faɗa miki mu su wayene, me ma zamu ɗauka a gidan toh da sai kin rufe?”

“shikkenan bari na kira Hajiya Surayyah in sanar da ita tunda amanar gidan aka bani.” Ta juya zata koma kitchen ta ɗauko wayarta, da hanzari dukkan su suka miƙe.

“Laa daga ita har shi ba'a musu gwaninta kin ji, gwamma ma ki daina zaƙewa domin idan ya juyo ta kan ki kema ba daɗi zaki ji ba” cewar Zakiyya.

Ameerah ta fisgo hannunta “da’alla yi mata shiru kizo mu tafi” Suka tsallake plate ɗin sauran abincin da wurin da suka ɓata suka tafi suka bar mata.

Saida ta koma ta sake ɗauko tsintsiya ta shiga tattara wurin, tana durƙushe da kitchen towel a hannunta tana goge jikin kujerar da suka shafawa maiƙo, gani tayi kaman idan ta bari sai sun je ɗauko Kiki sun dawo ba zai fita ba.

A ɗan razane ta miƙe lokacin da aka turo ƙofar parlour, haka kawai jikinta ya bata Abdulhameed zata gani sanin cewa tayi ba daidai ba.

A maimakon shi ɗin sai ta ga yarinyar shi tana shigowa, biye da ita kuma Aunty Surayyah ce.

“Mimi oyoyooo” Kiki tazo da gudunta goye da jakan makaranta ta rungume kunkumin Ilham da ta bushe a tsaye.

Aunty Surayyah ta ƙaraso idanunta a kan tsintsiyan da aka ajiye a gefe da fakan da bata kai ga zubar da dattin da ta kwashe a ciki ba.

Cikin muryar da bai yi kama da na tuhuma ba take tambayarta “Sai yanzu kike sharan gidan Ilham?”

“Hajiya kiyi haƙuri, su Ameerah ne suka ci abinci shine nake share wurin, amma yanzu nake shirin zuwa in ɗaukota”

Fatan goshin Aunty Surayyah ya tattare lokacin da ta tsuke fuska tana yi ma Ilham kallon mamaki kaman bata yarda da abinda tace ba.

“Su Ameerah? A cikin gidan nan?” ta tambaya yatsarta na nuni da ƙasan parlourn.

Ilham ta sauƙe kanta don bata da amsar bayarwa.

“Toh ke kuma abincin wa kika dauka kika basu?”

Kanta a ƙasa tana kallon cikin idanun kiki dake rike da ita har lokacin tace “sauran wanda ya rage ne suka ci”

“Sauran wanda ya rage ko kuma abincin ki? Idan ba zasu ci abinda iyayen su suke dafwa ba basu da hannu ne zasu zo wurin ki su karbi abinci? Ko sune suka ajiye ki?”

Ilham bata taɓa jinta tana faɗa ba, ko yaushe suna haduwa ne da fara'a a fuskar Aunty Surayyah, tana faran-faran da Ita, matsalan da take gujewa gashi nan saida yayi mata dabaibayi, saboda da ta haƙura ta basu ma ba tsira tayi ba.

Ta rage tsayinta ta hanyan sauƙa a kan guiwowinta ta daidaita tsawonta da na kiki tana sauraronta.

Jin ta sake yin shiru Aunty Surayyah sai ta cigaba da faɗa.
“Banda iskanci wani kalan kayan abinci ne bayi siya ya jibge musu sai sun zo nan sun karɓa? Da abinda yake ci da wanda bayi ci duka yake cika musu store da shi ko wani wata. Kuma da kema baki basu fuska ba sun san basu isa su fara ba, amma sarai sun san gamuwan su dashi ba daɗi”


Saida ta tabbatar ta kai aya tace “Kiyi haƙuri Hajiya, ba za'a sake ba in sha Allah” amma ta sani idan aka faɗa ma Abdulhameed sabon faɗan da zata sha sai yafi wannan.

A hankali kuma ta zame ma yarinyan jakan bayanta tare da cire mata takalmin da ta shigo ciki da shi.

Ta shafa kitson Kiki da har yayi sako-sako saboda laushin gashinta, tana ɗorawa da “Kuma ban san an daɗe da tashin su ba ganin lokaci bai tafi ba, tattara wurin kawai naso yi mu tafi”

Numfashi Aunty Surayyah ta sauƙe kafin ta miƙo mata takardan hannunta.
Ilham ta saka hannu biyu ta karɓa.

“Kira na aka yi a makarantar tasu zasu yi talent show shiyasa na je da kaina suka yi mun bayani muka dawo tare. Na kira in sanar da ke ban same ki ba, amma na faɗa ma driver idan kin fito ya faɗa miki”

“Ayyah wayan na ajiye shi a saman fridge a kitchen ban gani ba, kiyi haƙuri dan Allah hajiya”

Aunty Surayyah ta amsa da “babu komai, ki duba Idan akwai abinda zaki iya taimaka mata da shi toh, ko kuma ni da mahaifinta muga yanda za'a yi a weekend tunda abun sai ranan talata”

Ta buɗe takardan dake ɗauke da tambari da kuma adireshin makarantar a sama tana duba abinda ke ciki.

Jeren gwanon abubuwan da yaran zasu zaɓa ne kusan guda goma, kama daga Creative art, story telling, cultural dance harda waƙoƙin yara Nursery Rhymes, da kuma kwanan wata da lokacin da za'a yi taron.

Wanka ta fara yiwa kiki ta bata abinci sannan suka zauna tana tambayarta ko tana son ta koya mata tatsuniyar da zata je ta bayar a makaranta, sai ta girgiza kai wai za'a mata dariya, kuma bata iya zane sosai ba tunda tana ganin yanda take yi idan zata taya ta homework, idan aka samu wa’inda suka fita iyawa zata faɗi tunda abun kaman gasa ne, sai gashi sun tsaya a kan cultural dance don shi Kiki ta fi so, amma bata sani ba ko babanta zai yarda.

Saida Abdulhameed ya dawo, Aunty Surayyah ta shigo ta ƙofar baya ɗauke da ƙaton cooler tace Ilham ta ɗauka ta tafi da shi abincin ranan ta ne, bayan kuma ta riga da ta ɗebi na dare.

Mamaki da damuwa yasa ta buɗe kwanon tana kallon taliya da miyan jajjage yana tururi, Aunty Surayyah girki kenan ta je tayi mata? ta ɗauka wancan maganan ya wuce ai, ta yi tunanin shikkenan ta fasa faɗawa Abdulhameed tunda ta mata faɗa kuma ta bata haƙuri.

Sannan a lokacin da tayi musu sallama zata wuce tana jin Aunty Surayyah tana mayar masa da abinda ya faru tiryan-tiryan, shi kuma ya bata hankalin shi ɗari bisa ɗari, idanun shi kafe a kan fuskarta yana karantar abinda take cewa a hankali kuma ɓacin rai yake bayyana a tashi fuskar, ko lura da Ilham bai yi ba har ta wuce.

Ƙarasa wuninta tayi a cikin zullumi bayan ta koma asibiti, aiki dai gashi kaman da sauƙi tunda ta fara gane kan komai amma matsaloli kala-kala sai tasowa suke yi duk ƙoƙarin da take yi na gujewa hakan.

Saidai washe gari tun tana saka ran Abdulhameed zai ce wani abu har ya fita da safe ko kallonta bai yi ba.

Bayan misunderstanding da suka samu a kan Ikram, ya ƙudurta a ran shi ba zai sake tuhumarta da laifin da bayi da tabbaci a kan itace mai laifin gaba ɗaya.

Shiyasa yayi ma tufkar hanci a inda yake ganin ya dace.

Saboda ya gwada rashin jin daɗinsa a kan abinda yake ganin anyi ba daidai ba, Mahaifinsa ya sake yin iyaka ma mutanen gidan da abinda ya shafe shi.

“Shikkenan yara ba zasu yi laifi a tsawatar musu ba Yaya?”

“Kiyi mun shiru Surayyah!” Ya daka mata tsawa wanda Abdulhameed ne kawai bai ji sautin shi ya shiga kunnuwan shi ya ratsa jijiyoyin jikinsa kaman sauran mutanen wurin ba amma ya gani a yanda jikin mahaifin nashi yake tsuma.

“idan abinci ne ya daina saya ya gani ko iyalaina ba zasu rayu ba. Uwar shi ma ni na ciyar da ita har ya samu yazo duniya balle yayi tunanin lalacewa na ya kai ya goranta mun”

Daman a haka aka fara, kuma a haka tafiyan yake cigaba har zuwa yau.

Ya fara ƙin mahaifin shi ne da danginsa saboda Nne bata son su, amma sai bayan ya dawo cikinsu a lokacin da ya rasa ta ya fahimci dalilin da yasa ta nesanta shi da su.

Ƙaddara da soyayya ne ta haɗa duniya biyu mabanbanta. Rayuwa, yau da gobe da kuma banbancin yanayi ya hana kowanne samun sukuni a cikin inuwar ɗaya.

Amma da yana da wurin zuwa, da dangin mahaifyar shi sun kalle shi a matsayin jinin su, a matsayin ɗa tilo a wajen ƴar uwar su ba ɗan bahaushe ba, da babu abinda zai kawo shi kusa da Kaduna ko arewacin Nigeria gaba ɗaya.

Ilham ta yi murmushi lokacin da Kiki ta ƙarasa addu'an da ta koya mata daidai babu kuskure ko ɗaya. Ta rataya mata jakanta da water bottle, suna ɗaga ma juna hannu ta shiga mota suka tafi.

Da taji knocking bayan tafiyar su har ta saka ma ranta yaran gidan ne suka sake dawowa, ta je ta buɗe tunda yanzu ta san nayi da su, sai ta ga Aunty Surayyah da shirinta na fita, ga jaka rataye a kafaɗanta key ɗin motar ta a hannu.

“Ilham zo muyi magana” tace tana shigewa ciki.

Ilham ta tura ƙofan ta mara mata baya, da Aunty Surayyan ta samu kujera ta zauna sai ita ta nemi matsuguni a ƙasa daga gefen kujeran tana sauraronta.

“Daga yanzu idan kina buƙatar wani abu kawai ki kira a waya ki sanar dani ba sai kin shiga ɓangaren mu ba, ko Kiki zaki iya faɗa mata ta sanar da mahaifinta idan na gaggawa ne ko baki same ni a waya ba. Idan kuma akwai wani abun daban ni zan zo da kaina, ko abinci ne zan zo in ɗauka amma bani son ki sake shiga wurin su tunda suma an yi musu iyaka da nan dan Allah”

Abdulhameed bai ce komai ba, ba don babu abinda ya faru ba, kawai bai ce mata komai bane wannan karon.

“In sha Allah Hajiya.” ta amsa kanta a ƙasa.

….

Tun ganin da yayi ma wata budurwa a wurin dinnern abokin aikin shi kwanaki uku da suka wuce bai yi tsammanin idan yayi mata magana zata kula shi ba saboda haɗuwarta, ya san tafi ƙarfin aljihun shi, amma yana daga cikin jerin mazajen da abu mai kyau ko kwalliya yake ɗaukan idanun su, shiyasa bai yi ƙasa a guiwa ba ya gwada sa'ar shi, sai gashi bayan lambar waya har adireshin gidan su dake unguwan Rimi ya samu.

Babu ƙarya ya ɗauki wanka a taron, har kaman zai fasa zuwa event ɗin saboda damuwan shi a yanzu shine ya ƙarasa haɗa lefen Khausar ne, kuma ya san ita da mahaifiyarta sun saka buri shiyasa yake son yayi mata mai kyau.
Sai gashi ya samu aron kuɗi a wurin ogan shi ya samu ya ɗinka babban rigan da abokai suka saka ya siya da sabon takalmi sai yayi aron hula.

Shiyasa da ya tashi zuwa gidan ma bai je mata a kan mashin ba, ya roƙi wani abokinsa mai hidiman ƙarya ma ƴammata irin shi amma shi yana da mota domin daga babban gida ya fito, wani ɓangare na halayen su da yazo ɗaya yasa abokantakan sun yayi ƙargo.

Suka shirya kaman mutanen arziƙi suka ɗauki hanyar Unguwar Rimi.

Kyau da sabuntakar motar da tazo wucewa a lokacin da suke ƙoƙarin gano gidan da zasu je yasa Hashim ya bi motar da kallo.

Gilasan motar a sauƙe suke don haka ya samu damar ganin wanda yake zaune a ɓangaren mai zaman banza, a lokacin da mutumin ya juyo alaman magana yayi da wanda ke zaune a gidan baya, sai ya ɗaura guiwar hannun shi dake maƙale da agogon fata a daidai inda sleeve ɗin baƙar rigar shi ta tsaya a jikin window ya ɗan dafe kan shi.

Kallon sakwan guda kawai ya samu yayi mishi, amma ya hango abubuwa da yawa da shi bayi da shi a wurinsa, abubuwan da kallo ɗaya zaka yiwa mutum fahimci suna tare da shi, cikin su harda kuɗi.

Bai fara lissafin abinda suka biyo baya ba, idanun shi suka sauƙa a kan wanda take gidan baya.

Daga kalan kayan jikinta, sarƙan dake manne a wuyanta, mayafin da ta lulluɓe kanta da shi, duk sun isa su tabbatar masa ba ita bace, amma raunin da ya ji mata a fuskarta shi yayi mishi rana.

Tabon wannan raunin na idonta da kuncinta shi ya haska masa Ilham ya ganta ya ganeta.

Sai kuma faffaɗan murmushin da ya wadaci fuskarta.


``````````````````
Seemahwrites ✨

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
Chapter 25 · 0% Book details