Chapter 12
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites*
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
12…. A wurin da suka yi parking Khausar ta tsaya tana saka hannu biyu ta riƙe basket ɗin da kyau kada kwanukan su tankware abun ciki ya zuba. Hashim ya zura key yana buɗe kan fara mayyan shi da ya rufe kada brothers ɗin da suka fishi so suyi mishi gaba da ita.
“Amma Ya Hashim ka sa naji kunya yau”
“Koh?” Ya ɗago ya kalleta da murmushi a saman fuskarsa sannan ya mayar da hankali akan abinda yake yi.
Cikin muryar da ta ƙara matseta saboda yanga ta cigaba da cewa “wallahi ƙirji na sai bugawa yake yi har muka fito, naji tsoro sosai”
Miƙewa yayi yana gyara zaman rigan jamfan shi da wadataccen murmushi a kan fuskarsa “tsoron me kuma? ba ita tace miki tana son ganin saurayin ki ba? Toh gani nazo mun gaisa” ya hau ya kunna mashin ɗin ta ɗauki diri sannan yayi mata alamu da kai tazo ta hau.
Ta taka a yangance ta miƙa masa basket ɗin, a wurin karɓa ya haɗa da hannunta da gangan.
Duk da tayi saurin janyewa amma ya riga ya ji abinda yake son ji.
Laushin hannunta.
Laushin da babu irin shi a hannun Ilham, don zai iya rantsuwa nashi hannun yafi tata taushi tsaban surfe da wankin jama'a da ta ɗaura ma kanta ana bata canjin da bai taka kara ya karya ba.
“Yaya Hashim mana!” ta turo baki cike da shagwaɓa tana mishi hararar wasa.
Ya lashe leɓen bakin shi yana dariya mai sauti “watanni nawa ne suka rage yarinya? Kinga hau mu tafi in mayar dake wurin mama lami lafiya.”
Dake makirci ne abun dama sai ta dafa kafaɗan shi da hannu ɗaya ta hau, suka juya suka hau titi suna hirarsu ta soyayya babu ma wanda ya sake tunawa da wata Halitta mai suna Ilham a cikin su.
Ita kuwa tana ciki tana tunanin yanda zata fidda wando ta ka, bata yi tsammanin Hashim zai shigo har asibitin ya fita ba tare da ya basu ko sisi ba. Ƴan canjin hannunta daga sayi Detergent sayi bleach ya dawo sauran Naira ɗari takwas, ta kasa haƙuri saida ta siya ma muftee ayaba da lemu na ɗari uku a bakin asibiti ya ci ya ɗan samu kuzari a jikinsa. Amma sai gashi zuwa dare zazzaɓi ya rufe shi, dole ta siya mishi paracetamol ta bashi, tana zaune tana kallon yanda ƙirjin shi yake ɗagawa yana sauƙa a hankali bayan ya samu barci hawaye suna bin kumatun ta.
Ji take yi kaman ƙaddara ta katangeta a wani ɗaki mai tsananin duhu da babu wani taga da haske zai shigo ko kuma ƙofar da zata buɗe ta kuɓuta.
Ji take yi kaman zata ƙare rayuwarta ne tana lalume a cikin wannan duhun har mutuwa tazo ta risketa.
Amma muftee take tausayi, shine a ranta shiyasa ta kasa hakura ta daina lalumen.
Ciwon shi ba na warkewa gaba ɗaya bane, dukda babu cutar da Allah ya sauƙar a duniya ba tare da ya fara sauƙar da maganinta ba. Amma ilimin na cutar sickler har yanzu bai gama bayyana ba, kuma ma bata da halin da zata fita tayi fafutukar niman shi.
Kuka tayi sosai ta bai wa uku lada, tana danne nadamar da yake tasowa daga ƙasan zuciyarta. Nadamar da shaiɗan yake saka mata na haihuwar Muftee. Amma nadamar komawa gidan Hashim bayan sakin da yayi mata a shekaran auren su na farko bata yi ƙokarin yaƙi dashi ba.
Wataƙila da yanzu akwai wani ɗan haske a rayuwarta ko yaya ne.
…..
*2:40am*
ABDULHAMEED
“Turn around dear”
A hankali ta juyo ta saka fararen idanunta da baƙin cikin su ke ƙyallin hawayen da suka gama zuba daga ciki a cikin nashi.
Ya sakar mata murmushi mai taushi, ya saka hand shower da yake riƙe dashi ya ɗauraye mata kumfan jikinta.
Saida ya tabbatar ta wanku tass sannan ya ciro pink towel ɗinta dake rataye a hangern banɗakin ya naɗeta a ciki kana ya raba ta da ƙasa suka koma cikin ɗakin tana kwance a kafaɗarsa, ya kwantar da ita a saman gadon da ya sauyawa bedsheet ya sake rufa mata ƙaramin blanket ɗinta saboda sanyin da daren ya saka.
Dake barci ba isarta yayi ba daman babu ɓata lokaci ta mayar da barcin, sai ya koma toilet ya ɗauraye kayanta da zanin gadon da kashin da tayi a jikinta ya ɓata su sannan ya jiƙa su a cikin ruwan comfort ya fito.
Lokacin har ƙarfe uku da rabi na dare ta gota amma haka ya fita sanar da nurses ɓacin cikin da Kiki ta samu saboda suyi mata abinda zai magance shi kafin ya galabaitar da ita.
Tare suka dawo ɗakin da Nurse dake ɗauke da tray ɗin da ta ɗora alluran da za'a yi ma Kikin da kuma ruwan da za'a ƙara mata.
Ba don ran Abdulhameed ya so ba ya sake tashinta daga barci a lokacin da zai saka mata riga kafin a ɗaura mata drip, kuma saida tayi kukan da yaji kaman ya taya ta a lokacin da ake saka mata Canular.
Ya san ba zai iya mayarda barcin ba sai ya ɗauro alwala yazo ya fara gabatar da nafila kaman yanda Mahaifiyar Kiki ta shawarce shi da yi a lokacin da damuwa yayi mishi yawa.
Yana kan darduma har gari yayi haske, sai a lokacin kuma ɗan nutsuwar zuciya da ya samu da kuma ganin Kiki bata sake farkawa ba ya baiwa barci daman zuwa ya sace shi.
Da tunaninta a ran shi ya rufe idanunsa, don haka yanzu ma ita yake gani, ita yake gani tana murmushi kaman bata da wani damuwa a duniya.
Sai tayi mishi nuni da takardar da ta ajiye masa tare da biro a saman desk ɗinsa, ta shiga yi mishi bayanin da bai fahimta ba da hannu.
Amma ganin sunaye da yawa rubuce a saman takardan yasa ya fahimci nashi sunan take son ya rubuta.
Sai ya juyar da kan shi ta daya gefen ya sake kwantar da kanshi a saman desk ya bata ƙeya.
zafin da yaji a bayan ƙeyar tashi yasa shi saurin dagowa tare da fitar da sautin “Ah” yana sosa wurin, sai a lokacin ya lura da plastic ruler dake hannunta.
Ta tamke fuska irin babu wasa ɗinnan tana sake nuna mishi takardan da rulern da take riƙe da shi.
Sai kawai ya miƙe tsaye a kan ƙafafun shi ta gane tsayin su ba ɗaya bane don ya lura ta zo da raini.
Daga nan kaman wanda yake kallon film a TV haka scene ɗin ya ɗauke zuwa wani wuri daban amma gata tsaye a gabansa.
Saidai a maimakon murmushi hawayene ke bin kumatunta tana kallon nashi ƙwayan idanun cikin wani yanayi.
“Please Abdulhameed, Please!!!” Ta riƙo hannunshi na dama cikin nata biyu tana magiya.
Ya ɗaga idanunshi daga kan fuskarta don ma kada ya fahimci abinda take nufi zuciyarsa ta cigaba da karyewa sannan ya kwace hannun shi daga ruƙonta.
“Please Go Ikram” ya faɗa ba tare da ya kalleta ba tunda yanzu ta warke ya san zata jishi.
Sai ta shiga dukan ƙirjin shi da hannayenta tana kuka mai gunji, dukan da yake jinsa kaman a kan zuciyarsa take yi kai tsaye.
Hannunta ɗaya ya riƙe ya juyo ya kalleta da idanunsa da suka fi gauta jaa sannan cikin kaushin murya yace “Nace ki tafi! Bana son ganin ki”
Bai rufe baki ba ta ɗauke shi da mari da ɗaya hannun.
“Allah ya Isa. Allah sai ya saka mun Abdulhameed. I hate you!”
Buɗe ƙofar da akayi yasa ya buɗe idanunsa, ya sauƙe su a kan Aunty Surayyah da ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, hannunta riƙe da basket ɗin abun karyawa da kuma jakan ƙarin kaya da yace a kawo musu tun jiya don ba zai na iya barin kiki ita kaɗai ya tafi gida wanka da shiryawa ba, kuma Aunty Surayyah da yake ganin zai iya aminta ya barta jikin Ikram aiki yayi mata yawa.
Ya amsa mata yana miƙewa tsaye ya duba Ikram ɗin.
Aunty surayyah da itama hankalinta ya koma kanta ganin ƙarin ruwa a hannunta yasa ta taɓa shi ya juyo sannan take tambayan shi abinda yake faruwa.
“She got sick last night, kinga da mun tafi gida da bansan halinda zata shiga ciki ba kafin mu dawo”
Ta jinjina kai cikin yarda da zancen shi sannan ta tofa ma Kikin addu'a don shine kawai abinda zata iya mata a halin da ake ciki.
“Yaya zancen Nanny? An samu?” shine tambayar da yayi mata na gaba damuwa bayyane a yanayin shi.
“Nayi magana ana kan dubawa, kafin satin ya ƙare in sha Allah za'a samu, kada ka damu”
Ya jinjina kai sannan suka mayar da akalar zancen su ya koma kan aiki, har zuwa lokacin da aunty Surayyah tayi masa sallama zata tafi office, sai a lokacin Ikram take farkawa, ya saka musu abincin suka ci tare bayan ta gama kukan ɓacinta.
…..
Saida ta duba ta tabbatar sauran Shinkafar bata ɓaci ba sannan ta bawa Muftee ya ci, tare da kunun da ake basu sadaka kullum da safe, don haka ta tafi da ɗan nutsuwa a ranta saboda yana ƙoshe, Inda ta hau mashin da sauran canjin ɗari biyun hannunta, suka yarda suka kaita gida da ƙyar da magiya a kan farashin.
Kamar kullum Hashim yayi ɗai-ɗai da gidan, ga kulolin da khausar ta kawo masa abinci wanda ya cinye sauran da ya rage kafin ya fita aiki ya bar mata kwanukan a wurin da ƙasusuwan da ya tattaune su har ɓargo ta tattara masa.
Ta gode ma Allah ma da bata same shi a gidan ba, don haka cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta shiga tattarawa ta share ko ina tayi wanke-wanke da sauran Omon da tazo dashi daga asibi ta ɗan rage wanda zata yi wanka don bata samu na wanke banɗaki ba ma ga wari da zarnin fitsari da yake yi, sai ruwa ta sake zubawa ta wanke da tsintsintsiya, ta ci Sa'a ma da yau bai yi mata ajiyan da ya saba a cikin seater ba.
Bayan tayi wanka ta ɗauro alwala tazo tana gabatar da sallan walha dukda lokacinta har ta kusa ƙurewa, ta cigaba da roƙon Allah ya kawo mata mafita a cikin kowani hali.
Ta miƙe tana naɗe darduma saboda ta san nayi, yanda za'ayi ta samu kuɗin da zata yi abincin da zata tafi musu dashi asibiti, don ta ƙudura a ranta ko tayi ba zata ajiyewa Hashim ba.
Wayarta ne ya shiga ruri. Ta duƙa da darduman a hannunta ta ɗauka a ƙasa tana duba sunan mai kiran.
‘Yaya Haidar’ ta gani kaman yanda tayi saving.
Sai ta latsa madannin amsa kira ta ƙara a kunnenta tare da sallama.
“A jifa’en Yaya Aliyyu (ina kwana yaya Aliyyu)” ta gaida shi.
“Fidela wai ke kika ce yaran nan su zo? Kina fama da majinyaci zasu ƙara miki wani nauyin iye?” Ya fara da tuhumar ta yana share gaisuwan da tayi mishi.
Tayi saurin Amsawa da “Eh Yaya, saboda hakane ma nace Filiyan tazo, yanzu ma da zan dawo gida yin wanka babu kowa a jikin shi”
Tana jin yanda ya sauƙe ajiyan zuciya, daman yaya Aliyyu ba dai zuciya da faɗa ba, halin mahaifinsu gare shi sakk, don har tayi aure tana matuƙar Shakkan Taa, shiyasa take mamakin yanda a lokacin baya A Moher ɗinnan yake iya aikan yaya Aliyyu siyo sigari kuma ya je.
“Toh Islam kam damuwa kawai zata zama miki, Ihsan ɗin tazo ita kaɗai”
Ta kwantar da murya “Allah sarki Yaya nayi kewar su ne wallahi.”
“Ai zaku zo taron shekara nan bada jimawa ba, zaki ganta a sannan, idan kika matsa kuma Ihsan ɗinma sai tayi zamanta”
Jan bakinta tayi ta saka mishi sakata, sai shine ya sake cewa “ki tura min account numbern ki in saka miki abinda ya samu, sai a cigaba da haƙuri har zuwa lokacin da Allah zai ƙara buɗa mana.”
Haka yake, yana da wannan ƙokarin na taimaka mata da abinda Allah ya hore mishi lokaci zuwa lokaci, ba kaman sauran yayyenta biyu ba da ko kiranta suka gani basu ɗauka, koda gaisuwa ne kawai tunda sun gaji da roƙonta, kuma Yaya Aliyyu ba aiki yake yi ba saidai buge buge, duk da ya samu ya kammala degree ɗinsa da kuɗin gadon da suka samu wanda ita nata ya ƙare a jikin jinyar Muftee don karatu ya daɗe da fita daga cikin lissafinta.
Kaman tace masa Opay ne saboda bata da ko katin tura masa saƙo amma gudun ɓacin ransa sai ta shiga godiya sosai cikin farin ciki da jin dadi.
Bai amsa ba ya katse wayar daga ɓangaren shi dan haka da sauri ta fita ta shiga makwabtan su ta karɓi aron waya ta tura masa.
Tayi tunanin dubu biyu dubu ukun da ya saba zata gani amma sai ga alert ɗin har naira dubu biyar.
Bata san tayi tsalle ta dire a wurin ba saida matar da ta bata wayan take tambayanta menene sannan ta shiga godiya ma Allah ta labarta mata itama ta taya ta murna sannan ta shiga ta siya katin ɗari uku daga cikin account ɗin wanda suka kwashe dari biyun da suke binta bashi a take ya koma sauran ɗari.
Ta danna kiran yaya Aliyyu dominn tayi mishi godiya amma har ya gama ringing bai ɗaga ba.
Sai tayi godiya wa matan ta tafi shagon dake kusa dasu tayi masa transfer ɗin sauran kuɗin, idan ya cire kuɗin da yake binta bashi sai ya bata sugar da maggi, omo, manja da mangyaɗa ya bata sauran canjin.
Sai gashi kuɗi ya koma dubu uku dukda ma bai karɓi charges ba. Ta bi ta sayi busashshen tattasai da tumatir domin fresh ones yafi karfin ɗan talaka a yanzu, ta haɗa da ɗan nama na ɗari biyar a wurin mai tukubar unguwan saboda muftee da ya daɗe bai ci naman ba har yana ce mata wai haƙorin shi na ƙaiƙayi.
Sai gashi dubu biyar ta koma dubu ɗaya da ɗari biyar. Amma nauyin laidan da ta shiga dashi gida da nutsuwar da zuciyarta ya samu ya biya. Don haka tayi musu tuwon gari miyan kuka mai lafiya da nama kuma gobe in sha Allah taliya da miya zata yiwa Muftee.
Da azahar ta koma asibitin ta bashi abincin yaci da yawa kuwa domin yayi mishi daɗi, sai taji ta ƙara samun ƙwarin guiwar cigaba da fafutuka saboda farin cikin yaronta.
…..
Bayan kwana biyu aka sallami Ikram daga asibiti har ma an cire mata cast ɗin hannunta don shima da sauƙi sosai.
Ya kasance ranar Alhamis ne, Abdulhameed ya fito ɗauke da ita a kafaɗa, ɗayan hannun shi riƙe da jakan kayan su, Aunty Surayyah na biye da sauran shirgin su har jikin mota inda ya saka Ikram a back seat ya saka mata seatbelt, suka zuba kayayyakin a booth sannan ya shiga gaba Aunty Surayyah ta shiga mazaunin driver suka dauki hanyar zuwa gida.
“Yauwa zancen Nanny ɗinnan…” ya fara magana sai ta bashi hankalinta da ta raba da tuƙin da take “... Wanda kika yi zancenta, mai yaro mara Lafiya, a ɗauke ta indai zata iya”
````````
Seemahwrites ✨
.