← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 19 OF 30

Chapter 19

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

Wattpad and Arewapen @Seemahwrites

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


19… Kallon shi take yi da idanunta da suka fara tara ƙwalla ba tare da ta sani ba saida yawan hawayen ya fara disashe kallon mamakin da take mishi.

Bata taɓa tunanin akwai wani hanyar samu da zai taɓa zuwa mata Hashim yayi yunƙurin datse mata shi ba, shi dai ba zai bata ba amma ba zai hanata nemowa ba koda naman jikinta ne zata ke gutsura tana siyarwa ko kuma ta tafi har bangon duniya ta dawo wannan ba damuwan shi bane, amma bata taɓa sanin muguntar shi ta kai haka ba.

Yawan dalilan da yasa take buƙatar aikin saboda gazawar shi da suka zo kanta idan tace zata fara zayyano masa su daga ita har shi a wurin zasu kwana.

“Meyasa?” shine kalmar da a hanyar shi na gangarowa ya biyo kan harshenta, sauran kuma zuciyarta suka wuce suka taru a kan sauran nauyin da ke kanshi suka ƙara matse shi a ƙirjinta.

“Saboda haka naga dama Ilham. Saboda na Isa!” Yayi maganar cikin isan da ya san yana da shi.

Ta rufe idanunta hawayen ciki suna samun daman gangarowa saman kuncinta, ji take yi kaman idan ta buɗe su ta ganta a wata duniyar daban da wannan, ko wannan ɗinma tana so idan babu Hashim a cikinta.

“Ko kuma ki zaɓa tsakanin tura ƙanwar ki gida da bautan da kike son zuwa, dole zaki haƙura da ɗaya” yayi magana yana ɗauraye hannun shi a cikin kwanon da ya gama cin abinci, hawayenta ba damun shi yake yi ba, shi dariyarta ma a yanzu ya fi bashi haushi.

Ta yaya zata iya zuwa aikin a yanzu ma bayan Muftee na kwance a asibiti idan babu Ihsan?.
Zuwanta ne yasa har ta ji ƙwarin guiwar amsawa Hajiya Surayyah cewa zata yi, har tunanin ƙarewar hutun makarantar Ihsan ɗin take yi ba tare da an sallame su ba, saidai idan zata dinga barin Muftee shi kaɗai kenan ta je nima masa kuɗin magani da abinci.

“Dan girman Allah ka yi haƙuri kayi ma ɗana rai ya Hashim. Duk abinda nake yi ka san saboda shi ne, idan ba haka ba kuma ka karɓi ragamar jinyar shi sai in saka Ihsan ta koma gida, nima na gaji!”

….

A Rana ta uku kawai, tun ba'a je ko ina ba Ilham ta fara makara, bayan duk gargaɗin da ya saka aka yi mata kafin a ɗauke ta, gashi ta jawo masa latti daga shi har Kiki, domin da ya san zata kai har wannan lokacin bata zo ba da ya shirya Kiki tun da wuri ya haɗa mata abinda zata ci.

Cire agogon hannun shi yayi ya naɗe hannun rigan jikinsa, ya riga da ya gama shiryawa cikin shirt kalar green mai duhu da wando ruwan madara, ya tuɓe Kiki yayi mata wanka ya saka mata uniform amma har suka fito parlor babu alamun Ilham.

Ɓacin rai ne ke niman kama shi, yana fatan tana da uzurin da zata tsayar a gaban shi mai girma, idan ba haka ba kuma zai haƙura da ita a sake niman wata.

Cereal ya haɗa ma Kiki ta sha, ya zuba mata cookies da chocolate a cikin jakarta sanin ba zai riƙe mata ciki na tsawon lokaci sosai ba.

Yana durƙushe a gabanta yana saka mata takalmi ita kuma ta dafa shi kada ta faɗi aka turo ƙofar tare da sallama.

Abinda yake yi ya cigaba tunda bai ji ba, har saida Kiki ta taɓa shi tayi masa nuni da inda Ilham ke tsaye sannan ya juyo ya dubeta, ya miƙe tsaye yana kallonta ba tare da ya gama saka ma Kiki takalmin ba.

Fuskarta da ta duƙar yake kallo, yana ƙoƙarin tabbatar da abinda yake gani idan ba idanun shi ne suke masa gizo ba.

Bruises.

Gefen bakinta kusa da birthmark ɗinnan a fashe yake, kumatun ta kaman wanda tayi hatsari ta faɗo a kan mashin, ga idanunta ɗaya da ya kumbura har bata iya buɗe shi da kyau.

Leɓen bakin shi ya ciza ƙwallan ɓacin rai na taruwa a cikin idanun shi.

“Who did this to you?”

Ya tambaya cikin wata iriyar murya bai ma lura da haƙurin da take bashi na makaran da tayi ba, da uzurorin da take ta haɗawa tun fitowarta daga gida ko zata samu ya aminta.

Yau ko abincin asibiti bata kai ba ta ƙaraso nan, bata ma jin zata iya dafa abincin don duk jikinta ciwo yake yi.

Ta ɗago idanunta ta ɗora a kan fuskarsa, ɓacin ran da ta gani a cikin idanunshi saida ya bata tsoro.

Shi kuma Ikram yake kallo.
Ikram Aminu Yashi.

Tsaye a gaban shi da kwatankwacin bruises ɗin dake kan fuskar Ilham a yanzu.

“Duka na yayi Abdulhameed. Duka na yayi”

Ya Lumshe idanun shi da nufi kawar da wannan hoton daga cikin kan shi, Ilham ce yanzu tsaye a gaban shi ba ita ba, Bruises ɗin fuskarta ne damuwan shi.

“Babu kowa” ta amsa kafin ya kai ga sake tambaya. Ta ɗora da “don Allah kayi haƙuri ba zan sake kaiwa iwar haka ba”

Babu kowa da tace ya bashi amsar da yake nima, ya kawar da kan shi gefe yana furzar da Numfashi, leɓen bakinsa dake rawa yake kan cizawa ya samu ya daidaita kansa.

Wannan ba huruminsa bane, shiga cikinta yana nufin ƙetare iyakar da ya saka tsakaninsa da Ilham kasancewarta matar aure.

Saida ya ɗau lokaci mai tsawo yana danne zuciyar shi, ƙwaƙwalwar shi na tuna ma zuciyar abinda ya faru shekarun baya da abinda zai cigaba da faruwa a dalilin hakan, kafin ya samu ta haƙura ta fara hucewa a sannu.

Ya katse shirun da faɗin “Okay”

Ya juya wurin Kiki da ta samu wuri ta zauna ta ciro laidan chocolate daya a cikin jakarta ta buɗe tana ci.

Ya ƙarasa saka mata takalminta ya ɗauke ta da schoolbag ɗinta, duk Ilham tana tsaye a wurin a tunaninta haushin rashin zuwanta a kan lokaci ne yasa tana wurin yake ƙarasa shirya ƴar shi da kan shi.

Saida yazo wuceta zai fita yace “don't do anything, ki huta kawai, zan saka a kawo abinci you don't need to cook”

Bai jira cewarta ba suka yi gaba suka bar mata gidan tare da jawo ƙofa a bayan shi ya rufe.

Sai ta zube a ƙasan parlon kawai ta shiga rera kukan da bata samu ta iya yi ba tun jiya, sai sauƙe ajiyan zuciya ta dinga yi bayan Hashim ya gama jibgan ta kaman ƙato ɗan uwan shi.

Babu wanda zata kai mishi kuka ya share mata hawaye, daga wa’inda ko sun sani babu abinda zasu iya a kai banda ta ƙara musu damuwa sai kuma wa’inda ko gawanta aka ɗauka aka kai musu aka ce gashi Hashim yayi ajalinta sai sun samu dalilin da hakan ya zamo laifinta.

Kuka take yi mai zafi da gunji, tana jin ba don yaron da zai shiga mawuyacin hali a bayan ranta ba da ta mutu ta huta.

….

Ran Abdulhameed a dagule suka sauƙe Kiki a makaranta ya wuce office. Ko da aiki sun ƙara mishi yawa saboda komawan da yayi gida jiya lokacin tashin sa bai yi ba amma yau ya kasa taɓuka komai sai tunanin halin da yaga Ilham a ciki ke masa yawo a kai.

Da ya kasa haƙuri ne ya ɗaga waya yayi text ma Aunty Surayyah.

Office ɗin shi babu nisa da nata amma yana jin nauyin zuwa ya sameta a kan wannan maganan, sai yake jin kaman hakan bai kamata ba, Saboda Ilham matar Aure ce, saidai tunda tana aiki a ƙarƙashinsa hakki ne a kan shi ya kula da ita.

Ita ma Aunty Surayyan da taga saƙon shi sai bata zo office ɗin shi ba ta wuce gida kai tsaye.

Bata samu Ilham a parlor ba da ta isa, ta duba ɗakin da aka bata nan ma bata ganta ba sai ta shiga kitchen.

Tana baje a kan tiles ɗin ƙasan kitchen ɗin idanunta a rufe Hajiya Surayyah ta shigo, tsoro ya kamata ganin kaman babu rai a tattare da Ilham, da azama tayi kanta tana jijjiga ta.

Ganin ta buɗe idon Aunty Surayyah ta sauƙe gauron ajiyan zuciya.
“Ƴar nan mai ya same ki haka? Tashi mu tafi asibiti.”

Ta tallafota suka fita har cikin jan motarta dake mashigar gidan daman ko kasheta bata yi ba saboda yanda Abdulhameed yayi mata bayanin halinda Ilham ɗin take ciki.

Private hospital mafi kusa ta kaita aka yiwa Ilham dressing ɗin ciwukan jikinta, aka haɗa mata da magani tare da allurai, Sannan suka koma gidan, Aunty Surayyah tace ta kwanta a kan gado tayi barci har sai ya isheta.

Wannan taimako da kulawan da ta samu ya saka ta ji sanyi sosai a ranta, ɗacin da take ji a zuciyar ta ma ya ragu, ga alluran da aka yi mata ya rage mata raɗaɗin ciwukan jikinta.

….

ABDULHAMEED

Ordern abinci yake yi a website ɗin wani restaurant bayan ya idar da sallan Azahar lokacin da saƙon Excellency ya shigo wayan shi cewa yana son ganin shi.

Ya so ace ya je ya ɗauko kiki daga makaranta ne ya kawota office ɗin ta ƙarasa wuninta a nan su bar Ilham ta huta sosai, amma akwai yarjejeniya mai ƙarfi tsakaninsa da Excellency wanda yafi duk wani schedule dinsa muhimmanci, don haka yayi text ma Hajiya Surayyah ya roƙeta ta taimaka mishi ta ɗauko Kiki daga school akwai inda zai je.

“No problem” shine reply ɗin da ta rubuto mishi. Sai ya koma cikin office ɗinshi ya ɗauki mouth spray ɗinsa da wallet ya rufe office ɗin ya bada makulli ma secretary ɗinsa ya tafi wurin Excellency.
.
.
.

Kallon Mutumin yake yi, kallo na tsanaki. Yana so ya bayar ma abinda yake faɗa muhimmanci amma ma'anar shi ta gaza haɗuwa a cikin kansa, bai fahimci dalilin ma da yasa ya same shi da zancen ba, amma ya zauna yana karantan abinda yake cewa daga farko har zuwa inda Excellency yake tunanin bayanin da ya kamata yayi ma Abdulhameed ta cika.

“.... Kai kuma nayi maka alƙawarin zaka ƙara samun damammaki, hanyoyin samun ka zasu ƙaru, idan mulki ya shiga hannun mu ma kaga sai yanda muka so, rayuwar ka da na wanda suke jikin ka zai ƙara kyau ko ba haka ba?”

Yayi ƴar ƙaramar dariya yana kallon Abdulhameed ɗin tare da shafa tumbinsa.

Saida ya nisa cikin yanayin rashin fahimta yace “Allah ya saka min albarka a abinda nake yi sir, har muna samu mu taimaka ma wasu, kuma mutane sun yarda damu da abinda muke yi muna samun tallafi a kai a kai.”

“Yauwaa kaga dalilin da yasa na zaɓi muyi amfani da hakan mu jawo mutane kenan, saboda sun yarda da kai. Idan ka cika min alƙawarin da ka ɗauka ni kuma ina tabbatar maka baka buƙatar tallafi daga wurin kowa”


“A&I ƙungiya ce mai zaman kanta Sir, ina ganin kaman idan aka yi yanda kace ta koma ta gwamnati”

Ganin Excellency yayi shiru yana kallon shi kawai da mamakin amsar da ya samu a wurin shi sai ya miƙe tsaye. “kaman yanda na ɗauki alƙawari duk wani abu da zaka saka ni a karan kaina zan yi maka shi duk wahala da hatsarinsa. Amma A&I Support organization bayi cikin yarjejeniyar mu. Zan je in duba yarinyata, na barka lafiya”

Ya juya ya ɗauki hanyar fita sai ga mutumin da a ko yaushe da riga ƴar shara yake ganinsa da hula dara ya sha gabansa, fuskar shi a tamke ya buɗe hannunshi wajen Kare Abdulhameed daga ƙofar fita parlon.

Fahimtar cewa Excellency ne bai gama magana da shi ba sai ya juya ya sake fuskantar shi ya ji abinda ya rage kuma.

“Yarinyar wajenka… zan taimaka maka ka bata kariya na dindindin idan ka amince. Idan ba haka ba kuma wata rana ina tabbatar maka zasu dawo, zasu dawo da nufin karɓanta kuma babu yanda ka iya, duk wani wahala da sadaukarwa da kayi zai tashi ne a banza.”

….

Da Aunty Surayyah ta ɗauko Kiki daga makaranta, ta shigo ma Ilham da abinci, kuma ta saka ta a gaba saida ta ci ta sha magani.

Duk wani motsi da Aunty Surayyah zata yi wajen taimaka mata da wani abun sai tace “Nagode Hajiya”

“Haba godiyan ya Isa haka na gaji da ji, ki bari bakin ya huta ko zai samu ya warke da wuri”

Ilham ta ja bakin ta ɗinke.

“Ki kalli yanda ya canza miki kamanni”

Sai tayi ƙasa da kanta a kunyace.

“Kuma zaki sanar da iyayen ki ne ko zaki yi shiru ya samu ƙwarin guiwar sakewa? Kafin yayi miki illa kinji..”

“Iyaye na sun rasu”

Ta samu kanta da bata amsa.

Sai faɗan da Aunty Surayyah ta faro ya tsaya.

“Magabata fah, waliyyi, wani babba wanda zai tsaya miki ya karɓa miki ƴanci baki da shi?”

Ta ja hanci saboda kukan dake zuwa mata. “Iyayen shi sune magabatan nawa Hajiya, baban shi shine babban yayan su baban mu. Kuma ma shi suke bayar da goyon baya a duk abinda zai faru tsakaninmu”

“Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Toh Allah ya Isa miki”

“Ameen” tace tana share hawayenta da bayan hannu a ƙoƙarinta na kada ta sake fama ciwon idonta, Amma ta san Allah baya zalunci kuma baya son Azzalumai, tabbas zai saka mata wata rana.


`````````
Seemahwrites ✨

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
Chapter 19 · 0% Book details