Chapter 27
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)
Wattpad and Arewapen @Seemahwrites
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
27… Ihsan ta sake kira bayan sun ɗauki hanya, ba zata iya jira sai ta isa ta ji ko ta ga me yake faruwa ba, gwamma ta fara faɗa mata sai ta san wani irin shiri zata yi ma zuciyarta kada ta kasa jurewa ta tarwatse.
“Filiyan mai ya faru?”
Cikin muryar kuka ta kira sunanta “Addah Fidela…. Mu.. Muftee.. ne”
Sheshsheƙar da take ya tabbatar ma Ilham Mutuwa yayi, amma sai bata sare ba ta tambayeta “mai ya same shi?” hawaye suka fara bin kuncinta tun kafin ta ji amsar tambayarta.
“Muftee ya…” ɗiff wayan ta katse, ta ciro daga kunnenta ko kuɗinta ne ya ƙare ta duba ta gani akwai saura, ta sake maida ma Ihsan kira zuciyarta na tsere fiye da na tayoyin napep ɗin da take ciki, bata ƙi ta rufe ido ta buɗe ta ganta a gaban gadon yaronta ba.
Ba'a amsa kiran ba har ya yanke, tana ƙoƙarin sake maida wani sai ga kiran Maama ya shigo. Da ta ɗaga bata san meyasa ta saka mata kuka ba, kukan da bata da tabbaci a kan dalilin yinsa, amma ta san tana bukatar tayi kukan kafin komai.
“Fidela ki riƙe addu'a, Innalillahi wa Inna ilaihiraji'un da hasbunallahu wa niimal wakeel su zaki riƙe kiyi ta maimaitawa ba kuka ba, dukkan tsanani maganin shi Allah, kuma shine kawai zai tsaya miki”
Tabbas Muftee ne ya rasu, bata hango wani dalilin da zai saka Maama take faɗa mata irin wa’innan kalaman ba bayan haka.
Sai kuma tayi sa’ar yin kaman yanda Maaman tace, bata samu bakinta ya ambaci sunan Ubangiji ba sai yanzu, tana farawa sai taji tunaninta na haɗuwa wuri guda, ba don ta samu mafita ba sai domin tana jin akwai wanda yake da ƙarfin iko da buwaya a tare da ita kuma yana sane da lamarinta.
“Zan turo yayanku ya dawo da ku idan kun shirya, amma kada kiji komai, Allah na nan, kaman yanda ma'anar inkiyar ki yake nufi ɗiyata, kuma yana tare da mai gaskiya.”
Lallashin da Maama take mata ƙara karya mata zuciya yake yi.
Ta riƙe wayan tana kuka har suka isa asibitin kafin ta sauƙa ta bada mai napep abinda yake hannunta tayi ciki da sassarfa.
A waje ta hango Ihsan tana ta matsar ƙolla, da alamu dai jiranta kawai ake yi a bata gawan yaronta, ta ji guiwowinta kaman an kwaɓe mata su, tun daga cikinta kuka yake taso mata amma ta danne ta isa ga ƴar uwarta ta.
“Filiyan ya rasu ko?”
Ta yi tunanin ta gama shirya ma abinda zata ji zuwa yanzu sai gashi tana niman zubewa a jikin Ihsan da tambayar ya fito daga bakinta.
Ihsan tayi saurin ruƙota tana girgiza kai kukanta yana ƙaruwa.
“Bai mutu ba Addah, Muftee bai mutu ba amma yana cikin mawuyacin hali, jijjiga yake yi yana suma, har yanzu likitoci suna kan shi”
A hakan ma ta ji sanyi, tun da ba rasa shi tayi baki ɗaya ba da sauƙi.
Ta saka hannu ta share hawayenta da yaƙinin Allah zai ɗaga mata kafaɗun shi kaman lokutan baya da yake shiga yanayin da sai ta gama yanke tsammani ya tashi ya samu sauƙi.
“Shine zaki tsinka mun zuciya Filiyan? Da kin faɗa mun tun a wayan ai, zan iya jurewa”
Ba shi kenan ba, ba iya abinda yake faruwa ba kenan, amma ba zata iya ƙara mata wani baƙin albishir ba, wannan ma daurewa take yi ta sani.
“Likitan ne ya ƙwace wayan, lokacin ina ciki tare da su”
“Babu komai in sha Allah, idan Allah ya yarda zai tashi, babu komai”
Duk wanda yayi tawakkali Allah zai kawo mishi mafita, ta tilasta ma kanta haƙuri cike da wannan yaƙinin.
Wayan hannunta ya sake ɗaukan ruri, Addah Iman ne take kiranta, saida taji wani daɗi da ta fahimci dalilin kiran a yanzu, tun ma kafin ita ta sani ta zo gashi har ƴan uwanta dake wani gari sun fita damuwa da damuwarta, don bata taɓa tunanin ko menene zai faru Aliyyu zai taɓa ajiye mata missed calls ɗin da suka wuce 3 ba balle guda 20.
Ta ɗaga kiran da nufin ta kwantar ma Addah Iman da hankali, Muftee ba mutuwa yayi ba.
Babu ko sallama Iman ta fara da faɗin “Ilham baki da hankali ashe? da auren ki ga ɗanki rai a hannun Allah amma hakan bai ishe ki ishara ba kike yawon barbaɗe mutuncin ki a gari kike ɓata mana suna saboda asara? Ke wace irin shashasha ce? Yanzu da kika kashe auren sai ki ji daɗin yin yanda kike so, jaka wawuya kawai”
Ta saba Idan ta kirata tana gama faɗin kalaman bakinta zata kashe wayanta, saidai ita ta kira idan tana da kalaman kare kanta. Yanzu kuwa bata jin koda Iman ta tsaya saurarenta tana da amsar da zata bata, saboda bata ma fahimci ina zancenta ya nufa ba.
Wani yawo take yi na zubda mutunci ita da take niman hanyar cire wando ta ka? Wani auren ta kashe? Nata da Hashim?.
Ita ko tunanin sanar da shi halinda ake ciki bata yi ba, babu amfanin da sanar da shi ɗin zai yi mata, kuma ba zata manta ranar da ya buɗi baki yace mata Mutuwar Muftee hutu ne a gareta ba, don kawai a lokacin ta yi ƙoƙarin raba damuwarta da wanda take ganin shima abun ya shafe shi kai tsaye kamarta.
Tayi ma Ihsan dake tsaye a gabanta kallon niman ƙarin bayani
“Filiyan…”
Ihsan ta sake fashewa da kuka ta juya ma Ilham baya ta haɗa hannunta a saman fuskarta ta kifa kanta a bango tana matsar ƙolla.
Ilham ta haɗiyi wani iska mai zafi a cikin maƙoshinta dake a bushe ƙamas, ta bi bayan kiran Yaya Aliyyu hannunta yana ɓari.
“Fidela.” Ya kirata muryar shi a dake.
Shiru tayi ta kasa cewa komai, tabbaci take nima amma bata da tambayar da zata iya mishi.
Jin tayi shiru sai ajiyan zuciyanta da yake ji daga wurin, yace “Ina hanya, amma kafin na iso ki tabbatar kin tanadi amsar da zaki bani domin na baro haƙuri na a gida. In Allah ya yarda Ibrahim zai tashi, muna ta mishi addu'a Allah zai bashi lafiya”
Ya ƙare da tausarta kafin ya katse kiran.
Ta ruƙo Ihsan ta zaunar da ita a dakalin barandar asibitin itama ta zauna a gefenta, tayi shiru tana kallon ƙasa ta rasa wani abu ɗaya zata riƙe tayi masa kuka.
Haka lokaci yayi ta tafiya suna zaune a wurin, likitoci sai zirya suke yi tare da nurses, amma babu wanda ya neme su, koda wani abu ne babu wanda yace su je su siyo su kawo.
An kusa fitowa daga sallan azahar kafin likitan da suka fara soyayya da Ihsan ya ƙaraso inda suke zaune yayi musu sallama.
Ihsan ta miƙe tsaye, Ilham kuwa ido kawai ta iya ɗagawa ta dube shi.
Fuska ba yabo ba fallasa yace “zaku iya shiga ku duba shi”
Shi da kan shi yaji akwai buƙatar ya musu ƙarin bayani, ma'ana ya faɗa musu laifin waye abinda ya faru, saidai ɓacin rai kawai zasu samu tun da ko mutuwa Muftee yayi babu abinda zasu iya saidai su ɗau dangana, amma tunda an samu ya tashi, manyan sa sunce shikkenan su zasu hukunta Nurse ɗin da tayi mishi alluran da ba nashi ba har double dose kuwa, ba sai iyayensa sun ji ba.
Ya ciro wayan Ihsan a cikin aljihun shi ya miƙa mata ya wuce ya barsu.
Ganin fuskar Muftee maƙale da oxygen mask da suka shiga ya sake sanyata a juyayi. Ta zauna ta zuba masa rinannun idanunta, so take ta samu ko a cikin zuciyarta ne ta tsayar da addu'a taji an kira sunanta.
“Ilham!”
Kaman muryar Hajiya Surayyah.
Da ta ɗago sai taga ita ɗin ce tsaye a kanta.
Aunty Surayyah bata ba ta sakwan biyu da zata ƙare mamakinta ba tace
“Ina Kiki?”
A tunaninta ma kowani uzuri ne ya taso ma Ilham ɗin ta tafi ba tare da ta sanar da kowa ba suna tare da yarinyar, tunda mai gadi da yaga sun daɗe basu dawo ba yayi azancin kiranta ya tabbatar mata a tare suka fita, shiyasa bata tsaya ɓata lokacin kiranta a waya ba ta biyo sawunta ta ɗauki ƴar Abdulhameed ta maida mishi ita gida kafin ya samu labari, kuma ta canka daidai da ta fara zuwa asibitin da ɗan Ilham yake kwance, amma bata ga Ikram ba.
“Ina Kiki?” ta sake tambaya tashin hankali na bayyana a fuskarta ganin Ilham tayi shiru.
“H.. Hajiya na tura ta wurin ki ai kafin na fito”
“Innalillahi wa Inna ilaihiraji'un!” Sai ga Aunty Surayyah ta ɗaura hannu a ka.
“Ilham tare aka ce kun fita, dan Allah tana ina in mayar da ita gida?kiyi tunani dan Allah, ko kin kaita wani wurin kafin ki zo”
Ilham ta mayar da dubanta kan yaron da bayi iya shakar numfashi da kan shi, bai ma san a ina yake ba amma kafin ta zo gare shi itama Kikin ce damuwarta, babu yanda za'ayi ta fito musu da yarinya haka kawai tazo asibiti da ita.
“Wallahi har ƙofan ɓangaren ku na rakata nace ta je wurin ki kafin na fito, babu wani wuri da nake da shi da zan kaita Hajiya”
“Shikkenan, bari na koma na sake duba cikin gidan sosai, Allah yasa tana can ɗin, yaron ki ma Allah ya bashi lafiya”
Ta amsa da “ameen” dake dukkan su babu nutsuwa a jikin su Aunty Surayyah ta juya da sauri ta fita ba tare da tayi mata sallama ba itama Ilham tana zaune bata miƙe da nufin rakata ba.
Parlour, kitchen, toilet, store, har filin ta bayan gidan saida Aunty Surayyah ta duba amma babu kiki babu labarinta, ɗakin Abdulhameed kuma a garƙame yake da makulli.
Da abun yafi karfinta ne ta kira Mukarram yazo suka fara knocking gida-gida suna tambayar ko sun ga ƙaramar yarinya fara mai shekaru huɗu tana sanye da simple gown yellow da kitso mai beads a kanta amma har ƙarfe huɗu shiru, kuma halin da ta baro Ilham a ciki yasa bata sake tuntuɓarta ba, amma yanzu ya zamo dole ta shigo ciki a bincika tare da ita tunda ita ce mutum na karshe da aka bari tare da Kiki.
Ilham jin shirun yayi yawa yasa tayi tunanin ko an ga Kiki ne, ganin kiran Aunty surayyah ƙarfe 4 da minti 12 ya ɗaga hankalinta matuƙa, gashi har lokacin Muftee bai motsa ba.
Haka ta tsallake ta bar shi da aka sanar da ita ba'a ga Kiki ba har yanzu, ta ɗale mashin zuwa gidan a fujajan.
Kuma da gaske babu Kiki, abun kamar Almara, sauran mutan gidan ma sun shigo parlourn yana cike kowa tana tofa albarkacin bakinta, Aunty Surayyah kuwa ta fice a hayyacinta zuwa lokacin, tunaninta ko menene ya faru ita ce mai babban laifi tunda ita ta kawo Ilham.
Ana cikin tuhumar Ilham ta faɗi inda yarinya take ya shigo gidan.
Ya ja tunga daga bakin ƙofa kawai yana kallon su, Ba’a taɓa masa irin wannan cikan a gida ba zai kuma so sanin dalilin na yau.
A hankali yake takowa ciki idanun shi na niman wanda zai samu amsan tambayar shi a wurinta.
“Aunty Sharmama” ya kira da ya hango ta zaune a farin one seater ta zamo gaba ta ɗora guiwar hannunta na dama a kan cinyarta sannan ta saka tagumi da shi.
Ta miƙe tana kallon shi, wannan nutsuwar da ta gani a fuskar shi ya kusan bacewa tana da tabbaci.
“Kiki ce Abdulhameed. Bamu ganta ba” ta sanar da shi kai tsaye sanin ɓoye-ɓoye ƙara tunzura shi zai yi.
“Tun yaushe?” Ya tambaya idanun shi a kan Ilham dake durƙushe a gefen kujeran Aunty Surayyah hawaye na bin fuskarta.
Ta ɗago ta kalle shi da rinannun idanuwanta “yaro na ne jikin shi ya tsananta da safe, shine aka kira aka..”
“Da safe? Amma sai yanzu ake sanar da ni?”
Ya ɗago hannun shi na hagu yana duba ogogon dake jiki.
“past 4:30pm, sai yanzu ya kamata na sani?!” sautin muryar shi ya fara tashi, sai gashi masu tofa albarkacin bakin su ma sun yi muƙus.
Ilham ta miƙe a kan kafafuwanta.
Murya na rawa ta fara mishi bayani da fatan zai fahimci ba laifinta bane “Kira na aka yi a asibiti, yarona ne…”
“SHUT UP!!” Ya daka mata tsawan da saida hanjin cikinta suka kaɗa.
“Idan wani abu ya samu ƴata I'll sue you! Wallahi tallahi I'll make sure you rot in prison if anything happens to her, ki fita ki nemo mun ita yanzun nan ko kuma Shari'a ce zata rabani da ke, Get Out of My House!”
ta rintse idanunta ta tsame a wurin bata ko motsa ba banda kakkarwa da jikinta yake na tsananin tashin hankali.
“Get Out I said!!!”
Ya sake daka mata wani tsawan yana mata nuni da hanyar fita kafin zuciyar shi ta saka shi ya angiza ta.
Kuma sai a lokacin ne Ilham ta san nauyin dake tafe da Haƙurin da Aunty Surayyah ta bata a ranar zata ɗauketa aiki.
Ɓatan yarinya sukutum. Ita ina zata saka kanta?!
Da ta ja ƙafarta ta bar gidan ta daɗe a bakin titi tana tunanin inda zata yi. A ina zata fara neman Kiki a yanzu? Ina yarinyar ta shiga ko kuma su waye suka saceta? Sai ta ji damuwar lafiyar Muftee da zuwan Yaya Aliyyu ya dawo ba komai ba a gaban wannan.
Idan ya tabbata ba'a ga kiki ba ta shiga uku ta lalace.
Saida wayanta yayi ƙara ta san ashe har lokacin tana riƙe da shi, ta ɗago ta kawo saitin idanunta da ƙwallan dake kwance a ciki yasa take gani dishi-dishi, ta saka hannu ta ɗauke su kafin ta iya ganin message din da aka turo daga lambar da tayi saving da ‘Baban Muftee’.
Wasu maganganu ne da Ƙwaƙwalwarta ta gaza fahimta a yanzu, saidai kalmomi huɗun karshe wanda shine yasa taga wuri yayi mata duhu lokaci ɗaya kafin ta daina ganin komai.
“Na sake ki, Fasiƙa”
`````````````
Seemahwrites ✨
ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a turo shaidan biya ta 09039206763