← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 30

Chapter 6

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites*

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


06…. Sosai take farin ciki har ta gama shirin makaranta, saboda a safiyar yau Juma’a awara Maama tayi musu. Tana son awara sosai, gashi yau idan aka je makarantan boko ba za’a daɗe sosai ba kuma babu islamiyya, sannan da yamma zasu yi kwalliya su sanya kaya masu kyau suje yawon juma’a a basu kuɗin siyan wainar fulawa kuma maama ba zata hana su siya ba saboda yau juma’a ce, jumu’atu babban rana.

“Maama zaki zuba mun wani in tafi da shi makaranta ina?” Ta tambaya daga bakin ƙofar kitchen lokacin da Maaman take miƙo mata kwanon na yayyenta maza ta kai musu ɗakinsu.

Daga bayanta aka ce “Ƴan JSS suna zuwa school da lunch box ne daman?”

Saida ta riƙe kwanon da kyau, saboda ta san idan tayi sake ta kifar da awaran nan a wurin ita da Maama ne, Sannan ta juyo tana hararar Ihsan.

“Ni nace miki a lunch box za'a saka mun?!. Ni ko a laida ma inaso yanda zan ji daɗin faffasa shi idan zan ci.”

Ihsan ta jinjina kai tare yin ƙwafa “Ni kike harara? In faɗa?”

Da sauri Ilham ta shiga girgiza kai “A'a kiyi haƙuri dan Allah, ba zan sake ba”

Maama sai ta tsaya kallon ikon Allah. “Menene zaki faɗa ɗin?” Tayi tambayar tana riƙe kwanon hannun Ilham kada ta samu ta gudu.

Ganin yanda Ilham ɗin ta diririce ga ƙwalla da ya fara taruwa a idanunta sai Ihsan tayi murmushi tare da faɗin “babu komai fah Maama, wani wasan mu ne” ko babu komai zata samu Ilham ta dinga mata abinda take so.

Ba don Maaman ta yarda dasu ba ta saketa ta tafi sai domin sun kusa yin lattin makaranta. Haka suka ƙarasa shiri suka fita bayan ta saka su sunyi addu'a.

….

Kallon Fire dake faman bincika jakar shi yake yi jikin shi na tsuma. Kwana biyu kenan bai cika huhun shi da hayaƙi ba saboda ya faranta wa Nne kaman yanda itama ta faranta mishi, ta hanyar ɗaukan Kuɗi Naira dubu goma ta bashi ba tare da wani dogon sharaɗi ba don kawai yayi abinda yake so. Amma akwai wani abu a cikin hayaƙin dake saka mishi wani yanayi na musamman wanda bai san ta yaya zai yi bayanin shi ba, ba wai fita hayyaci bane saidai yana daga cikin abubuwan da suke daidaita mishi lissafi.

Shiyasa zuwa yau yake jin kaman lissafin nashi yana niman ƙwacewa, gashi ba zai iya siyan sigari a unguwar su ba saboda kada wata rana labari ya koma wurin Nne. Sannan yanda yayi mata alƙawarin mayarda hankali a kan karatu musamman yanzu da yake ajin ƙarshe a secondary fashin makaranta ba nashi bane, daga ƙarshe kuma idan yaje siyan sigari shagon malam Sama'ila sanye da Uniform sai ranshi ya ɓaci kafin ya siyar mishi, idanma shiga ukun shi ya barshi kenan.

A yanzu fata guda ɗaya yake da shi, ya samu na rage hanya a wurin Fire koda kara ɗaya.

“Babu ko ɗaya?” ya tambaya hannun shi kaman zai shiga cikin jakan ya duba da kanshi, don gani yake Fire yana masa saiɓi.

“Wallahi Old man ɗina saida ya caje ni tass kafin ya barni na fito. Kaga har na cikin jakan ma ya ɗauke”

Abdulhameed yaja tsaki.

“Yanzu yaya za'a yi?” Fire ya tambaye shi.

Wani tsakin ya ƙara ja yana tunanin shagon da zasu samu a buɗe da sanyin safiyar nan a kusa. Son kuɗin malam Sama'ila yana iya barinshi fitowa shago da asubahi amma bai kai ya saka shi fita daga shirgin da ba nashi ba.

Irin numfashin da ta haɗiya lokacin da ta hange shi da kuma yanda taja tunga ta tsaya ya tuna mishi da wacece ita. A jiya ya samu amsar tambayar ƙwaƙwalwarshi shiyasa tun daga lokacin ya manta da ita da ma wannan birthmark ɗinta mai sakawa tayi kyau ɗinnan.

Tunawa da yayi yace mata ta kira masa Aliyyu jiya yasa ya ɗaga murya yanda zata jishi yace “Ilham… Zo.”

Ga mamakin shi sai yaga ta dafe ƙirjinta da hannu bibbiyu tare da ƙwalalo idanu, a hankali kuma take juya kanta daga dama zuwa hagu zuwa dama.

“Isn't your name Ilham?” ya tambaya ganin bata da niyyan ƙarasowa.

Juyawa tayi ta dubi Ihsan da ta cije baki kamar ƴar dambe tana kallon ta.
Sai tayi mata kallon ai ku kuka jawo, tunda jiya su suka sanar dashi sunan nata.

“Wallahi kika je sai na faɗa ma Maama da Taa” Ihsan ta gargaɗeta cikin ƙasa da murya amma dake hankalin Abdulhameed yana kansu duka ganin yanda Ilham ɗin ta kiɗime sai ya fahimci barazana Ihsan take mata.

“Kema zo. Ku zo dukkan ku biyu”

Dake Ihsan gani take yi daga farko kaman ta tsira shiyasa hankalinta a kwance ta saka Ilham ɗin a gaba, amma yanzu da layin markaɗe yazo kanta a take cikinta ya ɗuri ruwa. Itace ɗan shaye-shaye yake kiranta? Ta haɗiyi miyau muƙut, Allah Sarki marigagiya Ihsan.


“in ƙaraso in same ku?” yayi maganan idanun shi a kan Ihsan don haka ta riga Ilham ma ƙarasawa gaban shi.

Murya na rawa tace “gani”

Bai kulata ba saida Ilham ta ƙaraso, birthmark ɗinnan ya sake shiga idanun shi sosai kana itama ta amsa da “gani” cikin raunin murya.

Koda yau bata yi dariya ba amma a haka uniform ɗin yayi mata kyau. A ɗan haduwar su na kwanakin da ba zasu haura 5 ba ya lura ko yaushe kayanta a wanke a goge yake kafin taje makaranta kuma haka take dawowa babu abinda ya canza a jikinta.

“Ina yayanki?” Ya ƙare ya bayyana dalilin kiran.

Saboda tasan cikin yayyen nata Aliyyu yake nufi yasa ta amsa da “bai dawo ba sai gobe” a ranta tana tambayar dalilin tsurar mata da ciki kenan dama? Shine ba zai tambayeta tun daga can nesa ta bashi amsa tayi tafiyarta ba?.

“Amma kin sanar dashi ina niman shi?”

Saida ta ƙara ƙasa da murya ta amsa da “ai bani da waya, kuma ina tsoron kiran shi a na Maama, dukana za'a yi a gida”.

Ihsan dai tana ta tsilli-tsilli da ido.

Ya muskuta ya ciro wallet ɗin shi a alijun wandon shi sannan ya buɗe ya ciro naira ɗari biyu ya miƙa mata.

Saboda yanda ta tsorata da ganin kuɗin saida tayi taku biyu baya, da ace ta ƙara wani saidai ta jita fanjam a cikin kwatamin bayanta.

Bai damu ba ya ƙara miƙa hannunshi don kuɗin ya isa gareta.

“Me.. me zan yi da shi?” Ta tambaya ba tare da ta karɓa ba, ga jikinta da ya shiga rawa kaman mai jin sanyi.

A zahirin gaskiya tunanin da ya zo kanshi a lokacin, ya gwada sa'ar shi da ita ne. wataƙil ita su yarda su siyar mata sigarin idan tace aikota aka yi amma sai ya samu bakinsa da furta abinda ya saɓa da tunanin da ƙwaƙwalwar shi ta bashi.

“Tom-tom zaki siyo mun”

“Na nawa?”

“50 Naira”

Sai ta gyaɗa kai “toh” ta saka hannu biyu ta karɓi kuɗin. Idan ba wani abu marar kyau bane ba zata ƙi zuwa ba tunda babba ne ya aiketa kuma ya san yayanta.

Ta juya zata tafi ganin ƙaton jakar bayan da take goye dashi ya sanya shi sake kiranta da sunan da take ji kaman ba nata bane, domin cire H ɗin yake yi baki ɗaya yace “ILLAM”

Ta juyo ta kalli hannun da ya sake miƙo mata “give me the bag, zan ajiye miki so that kiyi sauri”

Babu musu ta zame jakan daga kafaɗunta ta miƙa mishi. Sai ya dubi Ihsan da take tsaye da nata jakan a baya, kusan girman shi daya da na Ilham, tayi tsuru-tsuru kaman kace Kyatt ta zura a guje.

yace “je ki raka ta”

Ta gyaɗa kai tare da amsawa da “toh” ta bi Ilham suka jera a tare kaman yanda suka fito tun daga gida.

“Ka fasa sha kenan?” Fire ya tambaye shi da mamaki.

Da “yeah” kawai ya amsa yana bude zip ɗin jakar Ilham yaga menene ya sanya shi nauyi haka.

Text books ya fara cirowa har guda shida. English, maths, basic science, basic technology, social studies da civic education. Ya ajiye su a gefe sannan ya ciro Exercise books ɗinta duka, kusan guda goma sha biyu ne, ya jinjina ma ƙoƙarinta don shi ba zai iya dakon wannan shirgin ba, ina laifin taba ɗauko wanda zata yi amfani dasu a ranar kawai.

Ya sake luma hannun shi a cikin jakar sai yaji ya taɓa wani abu mai laushi da ɗumi ga wani ƙamshi dake ziyartar hanci. Yayi saurin zaro shi don ganin menene sai ya yamutse fuska ganin awara ne ya mayar mata da kayanta yanda ya ɗauko shi yana jan ƙaramin tsaki.

Buɗe littafin farko yayi wanda ya kasance na maths amma kansile-kansilen da ya gani ga assignment da aka yi mata marking taci 4 over 10 yasa ya rufe ya buɗe na gaba. Saidai shi tunda Nne ta haife shi bai taɓa ganin rubutu mai munin wannan ba, kaman tafiyan tsutsa da ake faɗa ɗinnan yau ya ganshi a rubutun Ilham.

Ya rufe littafin yana karanta abinda ke jikin bangon littafin.

Name: Amina Usman Jen….

Sunan Nne ɗinshi. Sunanta ɗaya da Nne.

Wani abu yaji ya buɗe a ƙirjin shi kamar fure a lokacin da hasken rana ya bayyana, wani farincikin da bayi da dalili ya lulluɓe shi. Yana son duk abinda ya shafi Nnem ko menene.

Sai ya cigaba da karanta abinda ke kasan sunan.

Class: Jss 1
Subject: Islamic Studies
Date: 4, March, 2014.

Ya ɗaga littafin daga sama ya mayar dashi ƙasan sauran don ya samu daman ganin na biyun.

Shima sunan irin na farkon ne, Amina Usman Jen. Hakan na nufin wancan ma littafinta ne tabbas ba na wata ba, sunan nata ne.

Saidai bayanan da ya biyo baya yasha banban da na littafin farko.

A wurin da aka rubuta Class: sai ta Rubuta ‘High Class’ a gaban shi.
Subject: Ask the Teacher
Date: Check the calendar

Zai buɗe littafin yaga menene a ciki ya hango su suna dawowa, sai yayi saurin tusa shi ƙasan jakar shi dake ajiye a gefe kafin ta lura sannan ya fara ƙokarin maida mata sauran tarukucenta ciki.

“Gashi” tace tana miƙa mishi laidan tom-tom ɗin da canjin.

“open and take some” yayi magana yana zuge mata zip ɗin jakan.

“No thank you” ta mayar masa da turanci itama.

Sai ya tsaya da abinda yake yi. “ki ɗiɓa nace!”

Haka saida ta ɗauka musu ɗaɗɗaya kafin ya bata jakanta suka tafi bayan sun mishi godiya. Ita dai daɗinta ɗaya anyi mata maganin bakin Ihsan tunda dai gashi yau tare lamarin ya ritsa da su, da bata san inda zata saka kanta ba idan aka je gida, hala saidai wata Fidelan bayan ita.

…..

Haka ya gama gwaramniyan shi a ranan ya koma gida da littafin a cikin jakar shi. Saida yayi shirin kwanciya sannan ya fito dashi ya ɗale gadon shi ya buɗe shafin farko.

Bismillah ne da Harshen Larabci aka rubuta shi babba da ruwan biro baƙi, wasalin jiki aka yishi da jan biro. Sai zanen hearts da taurari da jinjirayen wata manya da ƙanana aka yi da blue ɗin biro, baƙi da kuma ja ta cike sauran space ɗin dashi.

Yayi mamaki da yaga rubutunta na larabci babu laifi.

Ya juya shafin zuwa na gaban shi, shafin dake hagu wasu kalamai ne na hausa na soyayya da yayi mishi kama da waƙa. Harda gyaran Muryar shi yana ƙoƙarin rerawa amma ya kasa fasalta waƙan sai yana yinshi da rapping, wasu kalaman hausan ma ya gagara karantawa.

_Madubi ke nai dubawa_
_Saurari bayani na_
_Soyayya linzami na_

Layi uku ya iya karantawa ya haƙura.
Sai a can ƙasa bayan ta gama rubuta waƙar daga farko har ƙarshe tayi Scribbling harufan M&I ta zagaye shi da heart shape.

Shafin dake bangaren dama kuwa waƙan Musulunci ne guda biyu, I pledge to Islam my religion da Rahman ya Rahman na Alafasy.

Ya tsallaka shafi na gaba yayinda ya kasance kaman profile domin bayanan rayuwanta ne, sai wasu zanen flower da yake gani a hannun mata lokutan Eidi an zana musu da wani baƙin abu a bayan hannu, amma zanen nata yayi kyau sosai.

I am Amina by name AKA Ilham AKA Fidela.
I am 12 years old
My tribe is Jenjo
My favourite food is awara with sauce or yajin tafarnuwa.
My hobbies are Sleeping, cooking, dancing and makeup.

Ya murmusa, daman tayi kama da malalaciya, amma zaiso ya ganta tana rawa da wa’innan siraran ƙafafuwanta kaman tsintsiyan kwakwa.

Haka yaci gaba da karanatawa.
Kalan da tafi so,
Kayan da tafi so,
Suran da tafi so a cikin Alkur'ani,
Ƙira’an Malamin da yafi burge ta,
Subject ɗin da tafi so a makaranta,
Jarumin da tafi so a film ɗin Hausa da na India,
Mawaƙin da tafi so,
Su nawa ne a gidan su,
Maza nawa mata nawa,
Yawan ƙawayenta dai yafi komai bashi mamaki.

Da ya kai karshen bayanan sai yake jin kaman ya gama saninta, kaman ba haɗuwar hanya kawai suka yi ba.

Kaman ya riga ya santa a zuciyar shi.

Shafukan da suka biyo baya bayanan ƙawayen nata ne da bai damu da saninsu ba don haka ya dinga wucewa harda shafukan da an rubuta sunayen wa’inda zasu cika a sama amma basu kai ga cikawan ba.

Saida ya isa shafin karshe ya tsaya domin abinda yake jiki ya banbanta da sauran.
Ƙaton Heart ta zana da jan biro sai kifiya da ya ratsa ya raba heart ɗin gida biyu.
A ta sama sai ta sake zana harufan M&I a ƙasan kuma sai ta saka cikakken Sunan MUHSIN and ILHAM. Sai wasu ƴan rubuce rubucen kalaman soyayya da tayi a gefe har ya tsinto kalmar “my handsome crush”
A ƙasan zanen kuma waƙan Turanci ne na P Square mai taken ‘No one like you” ta rubuce shi.

Takaici ya sanya shi wurgi da littafin ko kashe wuta bai yi ba ya ɗora kanshi a saman pillow ya rufe ido.

…..

Duk inda take tunanin ta ajiye littafinnan ta duba amma bata ganshi ba. A sanadinsa ko yawon juma'a bata je ba haka ta birkita ɗakin Maama kaff tabi ta gyara shi tass amma ba littafi babu labarin shi.

Dukda dai Allah ya taimaketa da bata je dashi makaranta ba da yau kashinta ya bushe.
Saboda suna zaune sai gashi an shigo Inspection. Aka ce dukka ƴan ajin kada su ɗauki komai su fita gaban aji su tsaya perfects kuma suka shiga caje jakakkunan su suna seizing ɗin abubuwan da aka haramta zuwa da su makaranta.

A cikin prefect masu inspection harda Health prefect Muhsin.

A cikin abubuwan da aka haramta kuma harda slum book.

Kuma slum book ɗin nata yana ɗauke da sunan shi.

Haka kaman zata fasa ihu tana kallo yake bubbuɗe litattafan cikin jakanta yana dubawa, amma sai wani lipgloss ɗinta mai shining ya cire a matsayin yayi siezing ya mayar mata sauran littafanta cikin jaka ya rufe.

Toh tun daga lokacin take niman slum book ɗinnan har dare bata samu ba, kuma duk wa’inda ta baiwa su cika a ajin ta tambaye su sun tabbatar mata baya wurin su.

Har suka zo tafiya Islamiyya washegari da safe tana dame, da taje shima ta tambayi ƙawayenta na can suka shaida mata baya wurinsu suma.
Sai a hanyar su na dawowa bayan la’asar ta tuna da cewa jiya da safe ya buɗe jakarta.

Wannan ɗan shaye-shayen.

Ta dubi wurinda ya saba zama. Babu shi a wurin sai abokinsa.

Kaman ta haƙura sanin babu abinda zasu mata da littafi saidai ance matambayi baya ɓata. Kuma littafin sabone da ta siya da kuɗin break dinta da ta tara har naira 35, tare da biron cika slum book ɗin kala biyu kuma ya tashi Naira 60 ne.

Kuɗin break ɗinta na wurin kwanaki uku kenan saboda a kullum Naira Hamsin Taa yake basu su raba ita da yayarta Iman wanda take hannun Shafa. Amma dake akwai rata sosai a tsakaninsu kuma Iman tana da ƙanne maza har guda biyu kafin azo kanta ya sanya babu wani shaƙuwa tsakanita da Iman sosai dukda uwa ɗaya ce ta haifesu, ba kamar ita da Ihsan ba.

Ƙwarin guiwa ta tattaro ta ƙarasa wurin Fire, sauran ƴan hanyar su kuma suna jiranta daga can nesa tare da Ihsan.

Sallama tayi mishi ya amsa Sannan ta nuna gefen shi da babu kowa tana faɗin “y..ya.. yana ina?”

“Wane?”

“Abokin ka”

“A moher?”

Sai ta gyaɗa kai dukda ba sanin sunan shi tayi ba daman.

“Gashi nan” yace yana nuna bayanta da kai.

Da sauri ta juya sai gashi tsaye ƙeƙam.
Kafin tace wani abu kuma ya raɓata ya wuce, ta juyo lokacin da har ya samu wuri a gefen Fire ya zauna amma kaman bai fahimci wurin shi tazo ba sai ya ciro waya yana dannawa.

“Nace ba…” bai ɗago ba.

“Ka ji…” shima bai ɗago ba.

“A Moher…”

Saida ya ɗago ya sanya idanun shi cikin nata ya san yayi hakan.

“Uhmm… dan Allah ka tsinci littafina jiya?” Tayi maganar tana cire idanunta daga cikin nashi ta mayar kan ƙasan hijabinta da ta riƙe da hannun dama tana nannaɗawa a jikin yatsar ta manuniya na hagu.

Bai san amsar da zai bata ba, gashi bai zo da littafin ba balle ya mayar mata da kayanta.
Lokacin da ya tashi da safe ya manta da ɓacin ran shi, da zai wuce banɗaki alwalan asuba sai kawai ya ɗaga littafin a ƙasa ya saka a drawern jikin madubin shi, bai kuma sake bi ta kai ba har ya fito daga gidan.

Jin yayi shiru yasa ta sake ɗagowa ta dube shi, ganin ya mayarda hankalin shi kan wayar kaman bata wurin sai ta ƙaddara a ranta bai gani bane.

Bata sake cewa komai ba ta juya ta koma wurin su Ihsan suka tafi gida.

“Me yasa baka amsata ba?” Fire ya gagara haƙuri ya tambaye shi tunda yaga lokacin da ya ɗauki littafinta guda ɗaya jiya.

“Kai meyasa bata tambaye ka ba?” Ya mayar mishi da tambayar don haka ya ja bakinsa yayi shiru.

Jin an fara kiraye-kirayen Maghriba ya miƙe tare da jefar da sauran sigarin da ya gama sha ya bi da takalmin ƙafar shi ya murje shi don kashe sauran wutan da yake jiki, kana ya rataya jakar shi bayan ya saka tom-tom guda ɗaya a baki cikin sauran wanda Ilham ta siyo mishi jiya.

“Lukman sai gobe” ya faɗa yana shirin daukar hanya.

Da sauri Fire ya miƙe yana cewa “Ah ah, ba zamu je ɗin bane?”

Ya ɗan yi zugum kana ya girgiza kai. “Nne Lukman, ina tsoron ɓacin ran Nnem”

“Amma ai kace ta yarda, me yasa kuma ranta zai ɓaci?”

Gyara tsayuwa yayi ya zuba hannayen shi cikin aljihu Sannan yace “Ta yarda in yi waƙa ba in yi tatoo a jikina ba. Su ɗin abubuwa guda biyu ne mabanbanta”

Fire ya girgiza kai cikin rashin amincewa “ka taɓa ganin shahararren mawaƙin da bayi da tatoo?”

A cikin mawaƙan da suke burge shi yake bin irin salon su kam bayi tunanin akwai wanda bayi dashi.

Jin yayi shiru bai amsa ba Fire yace “toh ka gani!. Ba za'a yi maka kallon mawaƙi mai muhimmanci ba kaima idan baka dashi, kayi ko ƙarami ne ɗan na burgan aiki ɗinnan idan munzo yin video ya ɗan fito.”


“Nnem nake ji Lukman” ya sake maimaitawa.


````````
Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi....


DAƊIN ZAMA by Seemahwrites
ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna


*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
Chapter 6 · 0% Book details