Chapter 7
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 21 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi *Seemahwrites*
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely to Aunty Hauwa Yarima 🤍
UMMEE'S BAKING EMPIRE
https://chat.whatsapp.com/L0WK91pLyVn8iQ6HjSwG8a?mode=gi_t
*My Sister matso kusa ki ji.. Wannan cake ɗin da kike gani a online yake burge ki kin san inda zaki samu irin shi? Koko sha'awar glazed ko filled donuts kike yi? Ga plain ones for your Husband, father or boyfriend if they don't have a sweet tooth.*
*Coming to you my brother.. kana iya bada kyautar nan mai sanya mace tsallen Murna? Ko Surprise ma abokai? For Eids, Anniversaries, birthdays, graduation or just to celebrate your girl or yourself? you can order a cake from us. Akwai crunchy cincin domin motsa baki ko a siya ma mama da baba su saka mana albarka.*
*And don't forget about friendship or sibling bonds, You can always order a cake to celebrate their success or even to mock them with class😎, requesting captions that are satire and funny.*
Muna siyar da:
• Cakes na for every occasions ( birthday, graduation, anniversary dai dai sauran su)
• Bento cakes
• Cupcakes
• Mouth watering brownies
• Samosas
• spring rolls
• Glazed puffs
• Filled, glazed and plain donuts. E.t.c
*Ummee's Baking Empire –*
*Making every Moment feels special. We always make sure that you recieved what you ordered 👌🏼💯*
📞 08173775170
📍 gwammaja, Kano
07…. Agogon dake manne jikin bango ya fara kallo lokacin da ya shigo gidan.
Ƙarfe 9 da minti 17.
Ya haɗiyi miyau yana damƙe hannun jakar shi, saidai zafin da yaji ya ratsa tsakanin yatsun shi ya tunasar dashi abinda ke wurin, don haka ya sake jakan yana yarfa hannu a hankali a yayinda yake baza idanu yaga ta ina mahaifiyar shi zata fito.
Kitchen ya fara leƙawa bai ganta ba, sai ya dawo ƙofar ɗakinta ya ƙwanƙwasa “Nne, Enwere m ike ịbata?(In shigo?)”
Ya ɗan jira yaji ko zata amsa shiru, ya sake ƙwanƙwasawa nan ma shiru, sai ya saka hannun shi na hagu ya murɗa handle ɗin ɗakin amma ya jishi a rufe.
Toh ina taje a wannan lokacin?
Wayar shi ya zaro a aljihu ya laluɓo lambarta ya danna kira, babu ɓata lokaci kuma aka sanar dashi ‘Line busy’ lokacin da ya ƙara wayar a kunne.
Hankalin shi bai kwanta ba saida ya fito ya zaga ta baya inda take shanya kayan wanki da wasu abubuwa nan ma babu alamunta.
Hankalin shi ne ya fara tashi sanin cewa Nne bata da wurin zuwa a garin Kano da ya wuce office sai gida, kuma ƙarfe biyar ɗin kowacce rana yana mata a cikin gidanta ne, bata taɓa bari tayi dare a waje saboda shi.
Toh yau me ya faru?
Ƙoƙarin sake kiran layinta yayi still yaji busy. Sai ya samu wuri ya zauna yana tunanin possibilities na wuraren da zata iya kasancewa a yanzu.
Lokaci ɗaya kuma aka turo ƙofar parlourn, dake a ankare yake yayi saurin miƙewa a kan kafafuwan shi yana kallon fuskar mai shigowa.
“Nwam” ta furta tana sauƙe ajiyan zuciya.
Sai ya koma ya zuba a kujeran yana sauƙe ajiyar zuciya “Ina kika je Nnem? I've been calling your phone!”
“Sorry ina waya da lawyer na ne….” bata rufe baki ba wayarta ya sake ɗaukan ruri kuma babu ɓata lokaci ta ɗaga, daman jiran kiran shi take yi ta ƙarasa zazzage shi.
“You're very very stupid Muhammad Kagarko…” shine sallamar da tayi wa mai kiran wanda Abdulhameed ya gane ko wanene.
Yana kallon yanda taja tunga daga bakin ƙofar saboda masifa ko rufewa bata yi ba gudun sauro.
“.. Ni yanzu court ne kawai zata raba mu because I don't have time for your nonsense. Idan da kai mai hankali da tunani ne after all these years da baka waiwaye muba ba zaka kira Abdulhameed da ɗanka ba ma balle har ka gwada kana da iko dashi, Bayan ka zaɓi ƴan uwanka a kanmu Muhammad!. bayan azaban da ni da shi muka sha a gidan ku a gaban idanun ka, Idan na kwanta barci Fuskar ƙanwarka Surayyah ke firgita ni cikin dare. kuma sai in ɗauki ɗana in baka?! Over my dead body! Wallahi Idan kaga Abdulhameed ya dawo hannunka saidai a bayan raina! Tupu m eliwe n'ala, Tufia kwa!” tayi tofi tuff kana ta datse kiran tana huci.
Abdulhameed kallonta kawai yake, saboda wannan ba shine karo na farko ba amma ya fara gajiya, girma ya fara kama shi meyasa wa'innan zuciyoyin biyu ba zasu yayyafa ma kansu ruwan sanyi ba su mayar da hankali wajen inganta goben shi?.
Tun yana jin fitar numfashinta daga inda yake zaune har ta fara ƙoƙarin daidaita kanta saboda kada ta cigaba da ɗaga mishi hankali.
Ta ƙaraso inda yake zaune ta samu matsuguni a gefen shi.
“I'll protect you with everything I have Nwam, so kada ka damu kaji?” tayi maganar tana ɗora murmushin dole a saman fuskarta tare da riƙo hannunshi duka biyu cikin nata.
Ƙaramin ƙaran da ya saki tare da saurin zame hannun shi na dama daga cikin nata ya sanya ta dubi hannun cike da damuwa.
“Ciwo ka ji?”
Girgiza kai yayi, yana ƙokarin mayar da hannun bayansa ta riƙe, ta sake janyowa gaban idonta don taga menene.
Daga gefen yatsar shi manuniya da ya kumbura yayi ja ta hango wani baƙin zane.
Ya sake ƙoƙarin zame hannun kafin ta fahimci menene amma ruƙon da tayi mishi ba na wasa bane.
Ta tsura ma abun ido a ƙoƙarinta na gano ko menene.
“Tatoo kayi Abdulhameed?” Ta ɗago tana kallon shi da matsananciyar mamaki.
Tun lokacin da aka fara yake nadama, tun kafin ya gama shanye raɗaɗin da yake da tabbacin Nne zata ji ninkinsa a cikin zuciyarta.
“Tatoo Abdulhameed!” Tayi maganar wannan karon da tabbatarwa. Sannan ta saka hannunta tana shafa sunan “A Moher” da take gani a rubuce taji ko ba tatoo ɗin bane, ko zane ne da tawadan da idan ta murza zai goge.
Ƙaran da ya saki wanda yafi na ɗazu ya tabbatar mata da ba kuskuren fahimta tayi ba.
“Sakayyar da zaka yi min kenan? After all I've been through to take care of you and protect you, is this how you'll repay me Abdulhameed?”
Kafin zancenta su kai ga taɓa zuciyar shi, hawayen da ya gani suna zuba daga idanunta ne suka yi matuƙar ɗaga masa hankali.
Ba zai iya tuna ranar da ya taɓa ganin Nne tayi kuka ba.
Macece ita mai ƙarfin guiwa da taurin zuciya, mace jajirtacciya, mace mai kamar maza wanda ta zamo masa uwa da uba ita kaɗai ba tare da taimakon kowa ba.
Sauƙe kai yayi cikin jin kunya da nadama, yana jin ko hakuri ne ya kamata ya bata amma bakinsa yayi mishi nauyi.
Ta miƙe tsaye ba tare da ta sake cewa komai ba saboda kuka dake niman kufce mata. Abubuwan da ta tara a ƙasan zuciyarta na tsawon shekara goma sha takwas ne yake niman tasowa shiyasa kawai ta shige ɗaki ta rufo ƙofa tunda a yau kam ba zata iya danne su ba.
Yana zaune a wurin ya fara jiyo gunjin kukanta, abinda ya ƙara ɗaga mishi hankali yayi saurin tashi ya ƙarasa ƙofar ɗakin yana jijjigawa ta buɗe mishi.
“Nne kiyi haƙuri ki buɗe please, ki daina kuka don Allah” muryar shi ta fito da kauri saboda yanda maƙoshin shi ya cunkushe.
“Nnem ba zan sake ba. I promise. Ki gafarceni ki buɗe dan Allah.”
Yana daga cikin dararen da suka yiwa Abdulhameed tsawo a rayuwar shi. Yayi magiyan, ya bada haƙurin, ya ɗauki alƙawari, ya zubda hawaye amma a ciki babu abinda ya sanyanta ran mahaifiyar shi, haka suka yi kwana zaune da ƙofar parlour a buɗe.
Da gari ya waye ganin zata yiwa kanta illa da yunwa don ta faɗa masa shi ɗinne bata son gani sai ya shirya ya fice ya bar mata gidan.
…..
ILHAM
“Har yanzu baki samu littafin ba?” Ihsan ta tambayeta bayan sun isa Islamiyya ta sake tambayan wasu ƙawayenta da basu zo jiya ba.
Girgiza kai tayi damuwa shimfiɗe a fuskarta.
“Sai kiyi haƙuri ki sake siyan wani toh, amma ni ina da yaƙinin shi ya ɗauka”
“A moher?” Ta tambaya tunda shine mutum na farko da yazo kanta itama.
“Eh mana, idan ba haka ba ai littafin yana nan kafin ya karɓi jakan ki”
Ta jinjina kai don ba karamin mamaki tayi ba lokacin da Muhsin ya duba jakan bai gani ba, sai tayi tsammanin yayi nufin rufa mata asiri ne, saboda saida ta tabbatar littafin yana jakarta kafin ta fito daga gida domin akwai ƙawayenta da suka dameta ta basu su cika.
“Amma kin gani ai na tambaye shi baice yana wurin shi ba”
“Daman ɓarawo yana faɗan abinda ya sata ne? Kuma ƴan shaye-shaye dukkan su ɓarayi ne musamman shi da yake bada manyan kuɗi a siyo mishi abu, kina gani kinsan kuɗin sata ne”
“Ko satan yake yi mai zai yi da littafi?”
Ihsan ta buɗe baki tana kallonta “Addah Fidela kare shi kike yi?”
Tayi saurin girgiza kai “kawai dai naga ko siyarwa yace zai yi tunda da rubutu a jiki babu mai siya, saidai idan wa mai ƙosai zai kai” tayi maganar karshen saboda ta ƙaryata tunanin Ihsan na kare shi.
Tana iya tuna komawar su gida jiya, da ta samu Yaya Aliyyu ta sanar dashi saƙon A Moher na niman shi da yake yi tasha faɗa kaman zai ari baki wai kula shi take yi shiyasa har yake bata saƙo ta faɗa. Kuma bai haƙura ba saida ya haɗata da Taa ya saka ta Kneel down, kaman zai saka bulala ya zaneta ma Maama ce ta bada haƙuri ta lallashe shi.
Tayi kuka kaman mene amma tayi mamakin yanda duk inda aka kaɗa aka rawa Ihsan taƙi cewa komai a matsayinta na wanda suke tafiya suke dawowa tare, haka aka saka su kneel down da ɗaga hannu tare a ƙasan hasken wata da sauro.
Shafa tayi ta habaicinta wai yaran Maama suna neman lalacewa, har bakinta yayi tsami babu wanda ya kulata a gidan. Sai bayan awa ɗaya Taa ya turo yaya Aliyyun yace musu su tashi suje su kwanta.
A nan ne yaya Aliyyu ya zaunar dasu a ɗakin Maama ya sake musu faɗa da gargaɗi sannan ya shiga musu nasiha sosai. Yana sanar dasu irin illar shaye-shaye da hulɗa da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, yanda suke ƙarewa a wulaƙance da yanda rayuwar su ke lalacewa. Ya basu labarai kala-kala a kan wa’inda suka yi shaye-shaye a baya yanzu sun ƙare a gidan mahaukata ko a bola ko a gidan gyaran hali kuma sun tsorata sosai.
Shi da idanun shi bai taɓa ganin A Moher yana maye ba amma ya gargaɗesu a kanshi sosai, daga ita har Ihsan yace duk wacce ta sake zuwa inda yake sai ya saka dorina ya zane su gaba da bai.
A lokacin kuma da Ilham ta ɗauko fuskar A moher a cikin kanta ta haɗa shi da wannan yanayin da yaya Aliyyu ya fasalta sai tsananin tausayinsa ya kama ta.
Yanayin bai dace da shi ba.
“Ai ko dan ya kaiwa mai ƙosan ma kinga zai iya sacewa”
“Haka ne” ta amsata kawai tana tusa lomar taliyan murji a bakinta.
Kafin a tashe su da yamma shaff ta manta da tunanin A Moher ko littafinta, dan haka ta cigaba da hidimarta da ƴan makarantar su, har suka ɗau hanyar komawa gida tana tsakiyar su kamar kullum tana bada labarikan dake sanya kowa dariya harda ita kanta.
Yana zaune yana kallon su amma yau ko da kuskure bata dubi inda yake ba. Yana kallon yanda take dariya cike da nishaɗi yayinda zuciyar shi take ƙara motsewa a ƙirjin sa.
Har sun wuce ya ɗaga murya ya kirata “Ilham!”
Suka waiwayo baki ɗayansu suna kallon shi. Sai ya ɗaga mata littafinta a hannu daya, ɗayan kuma da shi ya kai sigarin da yake sha bakin shi ya sake zuƙa tare da fesar da hayaƙin.
“Kada ki je” Ihsan ta riƙe hannunta tana girgiza mata kai.
“Littafina kawai zan karɓa Filiyan, dan Allah” ta zare hannunta sannan ta tunkari inda Abdulhameed yake zaune warin taban shi na ƙara ƙarfi a cikin hancinta har yana saka ta tari, amma a haka ta ƙarasa.
Tana zuwa kusa ya miƙa mata ba tare da yace komai ba. Ta saka hannu biyu ta karɓa tana duba sunan jiki ta tabbatar nata ɗinne.
“Na gode” ta faɗa murya a shaƙe tana saka hannunta a kan hancinta Saboda warin yana damunta.
Ya ɗaga kai ba tare da ya dubeta ba.
Ta juya da nufin tafiya, taku ɗaya… biyu… sai ta sake juyowa.
Saida ta haɗiyi miyau kana ta kira shi “A Moher”
Ya juyo ya saka idanun shi cikin nata da yake iya hango wani yanayi mai zurfi a cikinsu.
“Dan Allah ka bari” shine abinda tace na gaba dubanta yana komawa kan sigarin hannunshi wanda ko rabi bai zuƙe ba.
Amma wannan shine zai zamo karan ƙarshe da zai riƙe a hannun shi da wannan nufin.
Karo na ƙarshe kenan da zai sha sigari a rayuwar shi.
Kuma ba domin Ilham bane.
Ba don tace ya bari ba.
Saidai akwai wasu abubuwa a ƙaddara da sukan zamo mana sanadi na sauyawar rayuwar mu. Wannan sanadin ba Ilham bace gaba dayan shi, amma ta kasance wani ɓari na cikinsa wanda ba zai manta ba. Saboda ita kaɗaice ta taɓa duban shi a garin Kano ta bashi shawarar da zai amfane shi dukda tsoron da ya gani a yanayinta.
.
.
.
“Alhamdulillah” tace tana juya littafin a hannunta da faffaɗan murmushi a fuskarta ganin babu abinda ya same shi sannan ta sake buɗewa tana duba ciki.
Komai lafiya, domin bata lura da shafin farkon ba har saida ta tafi na ƙarshe inda tayi zanen M&I a cikin heart.
Ta daɗa matso da littafin kusa da idanunta dukda lafiyan su ƙalau kuma zanen ba ƙarami bane Amma tana son tabbatar da abinda take gani ne.
M&I ɗinta ne ya rikiɗe ya koma A&I.
Correcting fluid aka saka aka ɗauke M ɗin gaba ɗaya aka sauya shi da A.
Mamaki ya daskarar da ita a zaune. Saboda meyasa?. Waye yayi mata wannan aikin a cikin wa'inda ta basu littafin nan?. Da ta duba wurinda ta rubuta Muhsin Vs Ilham kanma babu sunan gaba ɗaya an rufe shi da farin fenti tass kuma ba'a musanya shi da komai ba.
Hankalinta samm bai bata zai iya kasancewa aikin A Moher bane. Saidai hala a cikin wa’inda littafin ya taɓa shiga hannun su akwai mai Crushing a kan Muhsin itama shine tayi mata wannan aikin.
Ta juya littafin ya koma shafin farko inda ta rubuta M&I ƙarami a Ƙasa shima ya koma A&I.
Waye yayi mata wannan aikin fisabilillahi?. Ko lokacin da ta baiwa class monitor ɗinsu namiji ya cika ne aka samu wani mai Crushing ɗinta ya karɓa daga hannun shi? Tunda shi sunansa Zulƙarnaini ba daga A ya fara ba.
*Monday 7th, March, 2014*
Bumm… aka banko ƙofar dakin sannan ta faɗo ciki.
“Abdulhameed! Abdulhameed tashi… tashi Abdulhameed!”
Zame bargon da ya rufe har kansa dashi yayi. A hankali ganin shi ya daidaita da hasken da ya gauraye ɗakin lokaci ɗaya, sannan ya tashi zaune yana hamma.
“Sauƙo Nwam, we have no time to waste, ka shirya mu tafi yanzu” tayi maganar tana birkito da kayan cikin wardrobe ɗinshi mai ƙofa huɗu, tana zaɓan wanda suka yi mata tana zuba su a cikin madaidaicin akwatin da ta buɗe.
Ya haɗiyi miyau, Lokaci ya sake zagowa kenan.
Lokacin tafiyar da babu waiwaye.
A yau ma bayi da zaɓin da ya wuce na barin kano, tafiya ta har abada.
Bayi da wani zaɓi bayan ya bar karatun shi, abokan shi, waƙar shi, rayuwar da ya saba da ita ya sake komawa inda zai shimfiɗa sabuwa.
Yanzu kuma Ina suka nufa? Bayi da ƙwarin guiwar yi mata wannan tambayar tunda ya sani ba zai canza komai ba.
Bayan komawan shi hannunta yana da shekaru shida, a Maiduguri suka fara zama na tsawon shekaru uku kafin rana ɗaya suka tashi irin wannan tafiya.
Faɗi ƙasa yayi yana bori yana kuka amma bata kula shi ba, haka da zata saka shi a mota kaman ɗan da ta sato aka fito ana kallonsu saboda a lokacin a compound suke zaune.
Daga nan suka wuce Bauchi, tsawon shekaru biyar har ya samu shiga Jss two, suka sake tashi rana ɗaya bayi mantawa shikam tafiyan dare suka yi tun yana kuka a mota har barci ya dauke shi, sai buɗe idanun shi yayi a garin Sokoto.
Yayi ƙoƙarin ganin bai bari ya saba da garin ba wannan karon, yaƙi yin abokai, ko yaran unguwan su yaƙi kulawa sanin cewa zaman su ba mai ɗorewa bane. Amma ganin har sun shekara huɗu sai ya fara samun fata, wataƙil shikkenan yazo ƙarshe, wataƙil zuciyar shi zata samu mahuta a nan.
A wannan karon dai ta sanar dashi kafin ranar da zasu sake nausawa gaba saboda ya shirya a tsanake. Ya sauƙa a saman guiwowin shi yana roƙonta ta haƙura su zauna saboda lokacin girma da hankali sun riske shi shekarun shi goma sha bakwai.
“Nwam I work with the NGOs, aiki na ba na zama a wuri ɗaya bane, kayi haƙuri inda zamu je ma zaka saba” shine amsar da ta bashi shekara ɗaya kacal daya wuce.
Amma bayan yazo kano ya haɗu da Lukman abokin da bai taɓa samun kamar shi ba, wanda suke da buri da mafarki iri ɗaya, sai lokacin nan ya sake zagowa a kurkusa ba tare da ya shirya ba.
.
Ta bar abinda take yi ganin har yanzu yana zaune, ta ƙaraso jikin gadon ta kamo hannun shi harda mai tatoo ɗin amma ba shi bane damuwar ta a yanzu.
Saida ta jawo shi ya miƙe tsaye sannan ta fara tura shi hanyar bathroom dake ɗakin “Kayi brush kawai mu tafi, bamu da lokacin wanka babanka ya riga da ya iso Kano tun jiya” ta tura shi banɗakin ta rufo ƙofa kana ta cigaba da haɗa abubuwan da take da tabbacin zai buƙata, in yaso sauran sai ta turo a kwashe daga baya.
Bai ko yi sallan asuba ba, don gari bai gama wayewa ba tukunna. Yana iya kallo daga ɗan windown dake banɗakin yanda waje yake da duhu har yanzu., amma ya san ba zata jira shi yayi raka'a biyun nan ba don haka yayi brush kawai kaman yanda tace ya wanke fuskar shi sannan ya cire rigan jikin shi ya jefa a laundry basket dake toilet ɗin ya fito daga shi sai sweatpants ɗin barcin sa.
Da sauri ta nufo shi da rigan dake hannunta ya ɗan ranƙwafa ta zura a wuyansa sannan ya miƙe tana taya shi zura hannuwan.
“Ka ɗauki wayanka da duk wani abinda zaka buƙata ka zuba a cikin wannan jakan” tace tana miƙa mishi wani backpack.
Bai ce komai ba ya karɓa ya ƙarasa gaban madubin shi yana tattara su mai da turarensa yana zubawa a ciki.
Ta ɗebo boxers ɗinsa da singlet ta zuba a ciki tana cewa “kayi sauri Abdulhameed kada yazo ya same mu a gidan nan, dan ba zan iya bashi kai ba koda na minti ɗaya, idan Muhammad yayi nasara a kaina zuciyata zata buga!”
Ta karɓi jakan ta zuge zip dinshi sannan ta koma ta bayan shi ta goya masa.
“Muje” tace tana riƙo hannunsa.
“Headphones ɗina” yace yana juyawa jikin drawern gefen gado ya ciro baƙin headphone din ya lanƙaya a wuyan shi bayan ya rufe yalwataccen gashin kansa da hulan baƙin hoodie ɗin da ta saka mishi.
Suka fito harabar gidan yana janye da akwatin shi itama tana gara nata a kan tayoyin su, ga iskar asuba mai sanyi dake kaɗawa.
Motarta ƙiran 406 ash colour ta fara kunnawa yayi warming a yayinda ta dawo ta taya shi jera kayan a booth suka rufe a tare.
Ita ta buɗe masa mazaunin mai zaman banza ya shiga ta saka masa seatbelt da kanta ba don bai iya ba. sannan ta dauko mishi biscuit da 7up a back seat sai yaci idan yana jin yunwa, taje ta buɗe gate kana ta koma mazaunin driver ta fice da motar daga gidan.
Gari na dusu-dusu suka harba titi, kuma yanda take jin daɗin zabga gudu yana da alaƙa da kasancewar babu yawan abubuwan hawa a kan hanya sai ɗai-ɗai.
.
.
.
“Maama wai Addah Fidela bata da lafiya”
Rufe tukunyar abincin karyawan yara da ya kusa nuna Maaman tayi, don dukda kasancewar Shafa ce da girki yau saidai yaran su tafi da yunwa ko suyi latti amma ba zata tashi tayi musu abun kari da wuri ba kuma har da nata yaran a masu zuwa makarantar.
“Salon Ƙin makarantarta kala-kala ai, kice ta tashi tayi wanka kafin na shigo ɗakin nan”
Daga inda take kwance a kujera a parlour tana iya jiyo kalaman Maaman yayinda take juyi riƙe da mararta.
Jin gyaran muryan Taa da ya shigo gidan a lokacin tun bayan fitan shi sallan asuba ya sanya ta daddafa ta miƙe ta shiga banɗakin Maama ta watsa ruwan da Ihsan ta rage mata.
Sai kuma taji daɗin jikinta.
Don haka da ta shirya cikin riga da wandon uniform ɗinta ta fito sai Maama ta tabbatar karyan ciwo ne kawai.
Tana jin ciwon maran sama-sama amma saboda Taa yana nan har yanzu ta daure suka karya, kuma shi da kanshi ya sauƙe su a ƙofar makaranta da motar shi ranan.
.
.
.
“Nwam.” ta kira ba tare da ta rage gudun da take fantsamawa a kan titi ba, don gashi har sun ɗau hanyar barin gari sun nisa ƙauyuka.
Bai juyo ba amma yana jinta. Ya toshe kunnen shi da headphones ɗinshi saidai bai kunna komai ba a ciki.
“Abdulhameed kayi haƙuri, Please”
Ya juyo da mamaki ya dubeta yayinda itama ta juyo tana sake mishi murmushi.
Wannan murmushin.
Wannan fuskar.
Wannan rayuwar.
A cikin sakwan ɗaya kacal duk suka haska a cikin idanun shi lokacin da ƙarar horn ɗin tankar mai ta shiga kunnuwansu, juyawan da zasu yi har ta haɗe da gaban motar su sun zama abu guda.
Fashewar gilashin gaban motar da ya watsu daga fuska zuwa jikin su, huruwar balon-balon Iska da ya bugo ƙirjin Nne wajen kareta daga buguwa da gaban motar saboda a lokacin da ta tuna da sakawa danta seatbelt ta manta da saka nata ita, da kuma zafi da raɗaɗi da ya ziyarce shi ta ko ina duk cikin sakwan guda ne kacal.
Daga nan babban motar taci gaba da tura motar tasu baya da ƙarfin tsiya kaman yanda suka zo da gudu haka yake mayar dasu tunda girma da nauyin ba ɗaya ba.
Zuciyar shi yake ji kaman zata fasa kirjin shi ta fito saboda yanda take luguden tashin hankalin da bai taba jin koda labarin kwatankwacinsa ba. cewa da ake yi mutum na ganin mutuwa ya haska a cikin idanun shi, toh da ya haska a cikin na Abdulhameed sai yaƙi dauke hasken da wuri.
A cikin wannan yanayin, a cikin wannan azaba da tashin hankali Nne ta sako hannunta ta danne ƙirjin shi da jikin kujeran a yunkurinta na kare shi daga cutarwa ko yayane.
Salati kawai take yi a bakinta a lokacin da suka tunkuɗa daji motar su ta shiga gudundule yana rotsewa ta ko ina, headphones ɗin kunnen shi ya daɗe da faɗi. Sai a lokacin suka samu rabuwa da babban tankar da tayi gefe itama ta cigaba da karo da bishiyoyi da duwatsu don control ya riga da ya kwacewa matuƙin ta.
Sai wani irin ƙaraa, ƙara mai disashe sauraro da yafi tashin hankalin shi tsanani ya biyo bayan hantsilawar da babban motar tayi, ya shiga cikin kunnen shi ya ratsa shi kaman mashi mai tsananin kaifi, wanda yasa yaji kaman wani abu ya tarwatse a cikin kanshi.
A hankali kuma jini ya fara gangarowa daga cikin kunnuwan shi.
Daga nan Abdulhameed bai sake sanin inda yake ba, azaba ya sanya ƙwaƙwalwar shi niman hutu na wucin gadi.
.
.
.
“A ɓalla kofar, kuyi sauri ku ɓalla”
Hayaniyan da ya kamata ya farkar dashi kenan. Amma ko lokacin da mutane suka zagaye motar ana ƙoƙarin ceton rayukan da basu da sani a kan masu ita, bugun zuciyar shi ne ya farkar dashi.
Saidai sauƙin da ya samu na ɗan lokaci ya mantar dashi azabar da yake ciki, don haka da ya buɗe idanunsa sai yaji kaman a wani wurin yake daban da gidan duniya.
Bai taɓa sanin ana jin raɗaɗi irin wanda yake ji ba, ga kunnuwan shi da yake jin kaman ana kaɗa mishi ƙararrawa a cikin su babu ƙaƙƙautawa bayan zogin azaba da suke masa, kaman ya mutu kawai ya huta.
amma idanun shi yana kan Nne wanda kanta yake kife a kan steering da airbag ya fasa shi ya fito, a yanzu ya gama aikin shi ya sace, saidai ko ina a jikinta jini ne.
Jini a goshinta, jini a fuskarta, jini a ƙirjin ta da gaba ɗaya kayan jikinta. Gabaƙi ɗaya motar ya ɓaci da jini.
Jini kawai.
“N..n..nem” ya san ya kirata amma bata ji kiran ba tunda bata amsa ko ta buɗe ido ba. Saidai shima bai ji sautin kiran ba, la’alla saboda ƙararrawar da ya cika mishi kunne ne.
Saboda haka ya tattaro duk wani juriya yanda yake jin kaman maƙogwaron shi zai tsinke banda nauyi da ya danne ƙirjin shi ga bakin shi a fashe ya sake kiranta da yunƙurin da yafi na da.
“Nne ki buɗe idanun ki, please”
Ya rintse idanun shi yana jin kaman zai sake ficewa cikin hayyacin shi. A hankali hawaye wanda yake gauraye da jini yake gangarawa saman kuncinsa.
Hamdala da mutane keyi na hango shi ya buɗe ido yana motsi, da shawarar da suka yanke na a fara taimakon shi kafin mahaifiyar shi duk bai ji ba.
Sai ji Yayi an sako abu ana yanka Seatbelt ɗin dake jikin shi Sannan aka fara ƙoƙarin janyo shi ta cikin window, ashe har sun ƙarasa cire gilashin duk bai ji ba.
.
.
.
“Maama, Maama jini. Jini Maama”
Zuciyar Maama da ya kusa faɗowa daga ƙirjinta ta dafe tare da miƙewa tsaye tana kallon Ilham wanda suka shigo tare da Ihsan, kana ganin idanunta zaka san taci kuka ta ƙoshi.
“Jini a ina?” Ta tambaya ƙirjinta na bugawa fatt-fatt.
Sai Ilham ta juya bayanta yanda ƙasan rigan uniform ɗinta mai haske ya rine da jan kala.
“Ina zaune ne a waje kafin a shiga aji, ina tashi kawai naga jini a jikina”
Ta sauƙe ajiyar zuciya na samun nutsuwa kaɗan, girma ne yazo ma Ilham da wuri.
“shiga banɗaki ki jira ni ina zuwa.” Ta juya kan Ihsan ”Ke kuma ki kwantar da hankalin ki ba wani abu bane, zata samu sauƙi”.
````````