← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 17 OF 30

Chapter 17

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

Wattpad and Arewapen @Seemahwrites

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


17… Babban kuskuren da ya taɓa yi a rayuwar shi shine kula matar Aure.

Ya bari matar aure ta raɓe shi, suka keɓe wuri guda tare da matar Aure.

A sanadin haka ne kuma Kiki take zaune a gaban shi yanzu haka, dalilin da yasa ya sadaukar da rayuwar shi wajen Kula da ita, amma a haka yake tsoron ta girma ta dube shi da kuskuren da ya aikata wanda bai taɓa tsammanin girman sakamakon shi zai kai haka ba.

Bayi jin zai taɓa danasanin haɗuwa da Ikram a rayuwar shi, amma a kowace safiya yana buɗe idanunsa ne cike da nadamar sake Kulata da yayi da Auren wani a kanta.

“Kina da Aure?” Ya maimaita tambayar shi cikin harshen da zai fi yiwa Ilham sauƙin fahimta.

Ba zata iya jure kallon cikin idanun shi ba, don haka ta sauƙe kanta ƙasa kafin ta amsa da “eh”.

“Look at me. I can't hear you if you don't look at me. Kunnuwana basu aiki”

Tabbacin da ta samu kenan a kan wannan ba A Moher bane. kama ce kawai da Ubangiji yake sanyawa a tsakanin wasu daga cikin halittun sa, amma a iya saninta babu wani dalili da zai saka kunnen A moher su daina aiki bayan garau yake ji da su a lokacin baya.

Ajiye tunanin A moher tayi a gefe ta buɗe baki tace ma Abdulhameed “Eh, ina da shi”

Ya furzar da Numfashi.

Shikkenan babu ruwan shi.

Duk abinda take ciki babu ruwan shi, ba zai yi gangancin sake maimaita kuskuren shi ba, ba zai ƙetare iyakar shi ba, zai tsaya ne a iya iyakar abinda ya sake haɗa su.

Haɗiye duk tarin tambayoyin dake kan harshen shi yace “We're done eating”

Ta miƙe da nufin tattara kwanukan abincin sai ya mayar da idanun shi kan program ɗin da Kiki take kallo kada ma ya sake kallonta.

Saida yaga ƙulewarta kitchen sannan ya tashi daga kan dining ya ɗauki kiki suka koma light brown couch dake fuskantar TVn suka zauna.

Ilham ta dauko Tupperware a cikin cabinet ɗin da aka gwada mata ta juye sauran abincin sai kawai ta yanke shawaran ɗaura abincin dare ɗiyanin.

Sanwan tuwon semovita ɗinta da miyan taushe suna zaɓalɓaka ta fita don ta gabatar da sallan La’asar, bata ga Abdulhameed ko Ikram a parlor ba da zata wuce, sai TV dake ta ɓaɓatun sa shi kaɗai da kayan wasan Ikram ɗin dake barbaje.

Ta ƙarasa ta kashe musu TVn ta kimtsa wurin Sannan ta wuce, amma har ta idar ta koma ta tuƙa tuwonta ta kwashe ta sake jere musu a kan dining bata ji ɗuriyar su ba.

Ganin biyar ɗin da suka yi yarjejeniya a kai da Aunty Surayyah yana niman wucewa yasa ta jawo musu ƙofar gidan ta koma wurin Aunty Surayyah don ta sanar da ita zata wuce asibiti.

Tayi sa'ar ganin an share tsakar gidan, amma maiƙon abincin na nan ƙudaje suna kan bi, ta ɗauke idanunta tana gaida manyan matan da taci karo da su a wurin har ta isa ɗakin Aunty Surayyah ta ƙwanƙwasa.

“Bismillah shigo” Muryar Aunty Surayyah ya fito daga ɗakin.

Ta tura ƙofar ta shiga da sallama a bakinta.

Ilham ta rage tsayinta a gaban kujeran da take zaune da takardu a kan ƙaramin teburin da ta ajiye a gabanta tana rubutu a kai.

“Hajiya na gama komai kaman yanda kika ce”

“Sannu da aiki Malama Ilham” Hajiya Surayyah ta ajiye biron hannunta ta miƙe tsaye ta shiga ciki sannan ta dawo da farin envelope a hannunta ta miƙa mata.

Gashi, dubu talatin ne a cikin kuɗin aikin ki zan fara baki tunda kince kina da mara lafiya a asibiti, sai ki fara rage wani abu kafin a cika miki sauran idan lokaci yayi.

Kyautatawa yana da daɗi koda a kan hakkinka ne, musamman idan aka maka shi a lokacin da ka fi buƙata. Ta saka hannu biyu ta karɓa idanunta na tara hawayen murna, sai taga kaman kyauta ne aka ɗauka aka bata.

“Hajiya Nagode, Nagode Hajiya Allah ya saka da mafificin alkhairi Allah ya jiƙan magabata”

Ta amsa da “Ameen, Babu komai, sun cinye abincin da kika zuba musu da rana ne?”

Ilham ta girgiza kai “A'a na juye sauran a roba mai murfi na saka a fridge.”

“Ki je ki ɗauka ki tafi da shi. Idan sun rage abinci kina tafiya da shi ko ki bayar ma masu buƙata”

Ta amsa da “toh” ta miƙe tana sake godiya.

Sai ta shiga bangaren ta ƙofar baya dake kitchen, ta juye shinkafar a laida ta wanke roban ma, ta fito zata fita ta ƙofar parlor saboda zai fi mata sauƙin fita gate, amma sai idanunta suka sauƙa a kan damatsen Abdulhameed dake waje saboda baƙin singlet ne kawai yanzu a jikin sa da gajeren wando, ya baiwa ƙofar kitchen ɗin baya.

Shima ganin lokacin tafiyar nata yayi sai yayi tunanin ta tafi, kuma idan yana son hutawa sosai, ko in aiki suka yi mishi yawa yana son yayi ya gama da wuri, ya fi jinsa a sake idan babu nauyin kaya a jikinsa.

Bata bari Kiki dake buga Ball a tsakar parlorn ta lura da ita ba ta lallaɓa ta koma ta inda ta fito.

Napep ta hau tunda akwai isasshen kuɗi a hannunta.

Bata taɓa ɗokin ganinta a asibiti ba kaman na yau. Tana isa ta fara gwada ma Ihsan kuɗin da aka bata, ta juye musu abincin da ta dawo da shi a plate tace su ci kafin ta je ta siyo magunguna da alluran Muftee ta dawo ta bata labarin duk abinda ya faru.

Suna cikin hiran wayan Ilham ya fara ruri, da ta duba sai taga babu suna, amma sai ta ɗaga kiran ta ƙara a kunne tare da yin sallama.

“Waalaikis salam, Fidela ina kwana”

Jin sunan da aka kira ta dashi ya saka ta ɗan yi shiru tana ƙokarin ɗago muryar waye.

Da hakan ya gagara sai ta amsa da “lafiya”

“Yaya gida, yaya jikin Baban mu”

Ta sake amsawa da “ da sauƙi alhamdulillah” sannan ta ɗora da “amma ka gafarce ni ban gane waye nawa ba”

“Sageer ne” ya amsa kai tsaye.

Saida ta ɗan ƙara wasa ƙwaƙwalwarta kafin ta tuna shi.
Ɗan yayan baban su ne, baffa Umar, wanda daga mahaifin Hashim sai shi.

“Ayya yi haƙuri yaya Sageer, ka san an dade ba'a gana ba shiyasa muryar ya kwanta mun”

Dogon tsakin da Ihsan ta ja jin ta ambaci sunan yasa Ilham ta kalleta. Nan ta ɗago dalilin kiran da sageer ɗin yayi mata don ta so tayi mamakin yanda ma aka yi ya samu numbernta.

Sageer yace “Gaskiya ne, kuma ban kyauta ba na sani amma in Allah ya yarda daga yanzu zan gyara, duk sati zan dinga kira ina jin lafiyar baban mu”

Ilham ta murmusa “Haba duk sati? Sau ɗaya ma a shekara ya isa.”

“haba auntyn mu kada kiyi Fushi mana.”

“Ni nace maka nayi fushi? Ba gashi yau ɗin ka kira ba”

Ya ɗan yi murmushi “Toh idan tana kusa dan Allah a ɗan bata”

“Wacece?” Ta tambaya kaman bata fahimta ba.

“Filiyan. Dan Allah”

Ganin yanda Ihsan take girgiza kai kaman ƙadangariya saida ta ba ma Ilham dariya.

Ta gimtse tace “toh gata nan” tana cire wayan daga kunnenta ta miƙawa Ihsan.

Saida ta harari Ilham kaman idanunta zasu faɗo ƙasa kafin ta karɓi wayan ta ƙara a kunne.

Kaman wanda aka cusawa tsumma a baki haka tayi sallama.
Kuma duk abinda Sageer ɗin zai ce mata daga ta amsa da Uhm, sai Uhm-uhm, tana yi tana murguɗe-murguɗen baki, har ta gaji da sauraren shi ta datse kiran ba tare da sun yi sallama ba.

“Baki da kirki yarinyar nan” cewar Ilham tana ɓare lemon ɓawo da yatsunta.

“Wallahi bana son haka Aunty Ilham bana so! Ai na san abinda nake yi na ƙi ɗaukan wayar tashi. Ko so kike yi nima in shiga wannan azababben familyn in ɗora daga inda kika tsaya?”

Saboda ta tsokane ta Ilham tace “kin san dai duk inda kika je kika dawo auren dangin nan dai shine, ko wa kike dashi kike ruɗin kanki dole haka zaki dawo gida ki samu mijin aure, gwamma ma ki samu mai son ki mai lallaɓa ki zai fi miki”

“Allah ya kiyaye! Ni da Ahalin Baniza saidai alaƙa ta jini da babu yanda ka iya da shi amma ba zan taɓa aure a cikinsu ba tunda mai tilastawan yanzu babu shi sai inga wanda zai min dole”

Ilham tayi murmushi, tunawa da yanda suka so Juna ita da Muhsin, kaman ba zasu rabu ba. Haka ta dinga koran maneman ta wa’inda suka zo da shirin su na Aure Saboda lokacin Muhsin yana karatun shi na likitanci, sai a shekaran da zai kammala ta tsinci kanta a ɗakin wani da ba shi ba.

“Ki ce In sha Allah”

Kaman ba zata faɗa ɗin ba sai kuma ta maimaita har sau biyu.

Ilham tayi murmushi ta mika mata rabin lemun da ta gama barewa, ta cire tsala daya a cikin ɗaya rabin ta saka a bakinta kafin ta saka sauran a hannun Muftee.

….

Saida ya je masallaci ya gabatar da sallan Isha kafin ya ɗauko Ikram a kafaɗan shi zasu ci abincin dare, ya ja kujeran dining ya zaunar da ita shima ya zauna sannan ya shiga buɗe kwanukan abincin da Ilham ta ajiye musu.

Ganin miyan taushe a flask ɗin farko yasa jikin shi yayi sanyi tun kafin ya buɗe tuwon semovita dake ƙyalli a cikin laidan da aka ɗaure su zam-zam.

A cikin sharuɗan da ya zayyana ma Aunty Surayyah ya manta bai lissafo abubuwan da baya ci ba.

Sai dai daman mai raino ya ɗauka ma Kiki ba wai mai aiki ma kan shi ba, tana girki ne a gidan saboda Ikram ta ci ba don shi ba, bai ma taɓa ɗaukan nannyn da ta taɓa girka abinci ya iya ci ba sai Ilham. Shi dai burin shi kawai a cika mishi cikin ɗiyar shi, in yaso shi yana fita yana niman abinda zai saka a nasa cikin ko kuma yayi ordering takeout ya ci a gidan. Amma da ya buɗe kwanon shinkafan rana da nufin zubawa Kiki, tururin ƙamshinsa ya bugi hancinsa, sai ya samu kansa yana ci shima har saida ya koshi, shiyasa yanzu ma yayi tsammanin ta dafa abinda zai ci ne.

Ganin bai fara zuba musu abincin ba Kiki ta taɓa shi “Daddy yunwa” ta ɗaura hannu a saman cikinta tana yamutsa fuska.

Tuwon ya saka guda ɗaya a plate da miyan kaɗan sai naman da yake saka ran shi zai iya taɓawa.

A lokacin da suka tashi daga table ɗin sauran kullin tuwo guda ɗaya a cikin huɗun da Ilham ta saka a cikin food flask ta rufe. Kuma ba zallan Kiki ba har Abdulhameed ya ji daɗin cikan da cikinsa yayi damm.

*Washegari*

Ƙarfe 7 na Safiya ya yiwa Ilham a gidan, ko karyawa bata yi ba don mai mashin ma yana jiranta a waje ta samu ta miƙa ɗanwaken da tayi ma su Ihsan a asibiti suka juyo. Amma saida ta shiga ta gaida Aunty Surayyah kafin ta shigo ɓangaren Abdulhameed dake a buɗe, ganin babu kowa a parlor sai ta wuce kitchen kanta tsaye ta.

Ta sha mamakin ganin har plates da cups ɗin da ta ajiye musu tare da abinci jiya a wanke an tanada su a inda ya dace, babu wani abu mai datti a cikin sink.
Ta buɗe fridge da tunanin abinda ya kamata ta dafa musu na karyawa sai taga sauran tuwon da ya rage da miya an tanada shi a cikin takeaway daban-daban.

Abun ya burgeta sosai, don ko lokacin da take da fridge duk yawan abinci idan ta zuba ma Hashim yaci ya bari haka zai barshi ya kwana a cikin kwano yayi yauƙi, sai dai da safe idan ta dawo daga asibiti ta zubar ba kuma wai don sun wadata da abincin ba.

Ta ciro ƙwai uku da kayan miya ta ajiye kana ta ɗauki doya ta fere ta zuba a tukunya non-stick da irin su kawai ta gani jere a kitchen ɗin, ta zuba ruwa da gishiri ta kunna mishi wuta, kayan miyan kuma ta markaɗa shi baya-baya a grinder.

Mantawa da zancen yarinyar bata cin yankakken albasa da Hajiya Surayyah tayi mata jiya, sai ta ɗauko karamin tukunya ta zuba mangayada a ciki ta yanka albasa mai yawa ta zuba ta dan fara juya shi kafin ta zuba sauran kayan miyan a kai. Cikin kanƙanin lokaci ta kammala sauce ɗinta ta kashe masa wuta, sannan ta koma kan doyan da yayi laushi ta kaɗa kwai ta soya shi.

Saida ta jera komai a kan dining sannan ta wuce ɗakin Kiki don tayi mata wanka da shirin makaranta.

Ihun da yarinyar ta dinga zundumawa kafin ta gama shiryata da kokuwa ba tare da Abdulhameed ya leƙo ba ko sau ɗaya ba, ya tabbatar ma Ilham kunnuwan shi basa aiki.

Faran fuskar nan tata tayi jaa lokacin da suka fito suka samu Abdulhameed cikin shirin fita aiki sanye da navy blue shirt da baƙin wando.

Ta zame daga jikin Ilham da gudu ta ƙarasa ta faɗa jikin shi tana sabunta kukanta.

A kiɗime ya ɗago fuskarta yana tambayan abinda ya sameta, fitowa da yayi yaga an shirya abinci a dining ya fahimtar dashi Ilham tana gidan, shiyasa ya zauna yana jiran ta fito da Kiki don bayi son ko karo suna yi da juna a cikin gidan.

Cikin sheshsheƙan kuka tace “Ha…ha.. hannuna Daddy” tana ɗaga mishi hannun da ta targaɗe a jiki.

Ya ɗago ya kalli Ilham dake tsaye daga gefe tana kallon taɓara, nata yaron bai isa yayi mata abinda Kiki take yi ba tare da ta gyara masa zama ba.

“Ba’a faɗa miki hannunta na ciwo bane?” ya tambaya.

Sauƙe idanunta tayi daga kan Kiki zuwa ƙasa, sannan ta gyaɗa kai a hankali jin yanda yayi maganan da faɗa.

“Look at me and talk to me Ilham!”

Ta ji yanda ya cire H ɗin cikin sunan nata, kaman yanda A Moher yake yi, amma dake ba abinda yake gabanta ba kenan sai hakan bai bada wata ma'ana ba a cikin kanta har ta ɗago ta kalle shi kaman yanda yace.

“An faɗa mun, amma ban taɓa mata ciwo ba”

Hasalima ko soso bata saka a hannun ba da zata yi mata wanka, daga kafaɗanta zuwa guiwan hannunta kawai ta wanke ta ɗaurayeta, kuma ko da take riƙeta tana tirjewa ta mayar da hankali wajen ganin bata taɓa hannun ba saidai ta riƙeta da ɗayan.

“Idan baki taɓa mata ciwo ba bazata ce kin taɓa mata ciwo ba”

Ƙarya kenan zata yi ma Kiki?, da girmanta zata yi ƙarya ma ƴar cikinta?.

Tunawa da Huɗubar Hajiya Surayyah yasa tace masa “Kayi Haƙuri” kawai.

Ya haɗiye rabin ɓacin ransa ganin wannan shine karo na farko, zai gwada yi mata uzuri.

“Be extra cautious next time, please” yace yana maida nasa idon kan Kiki da ya ɗaura ta saman cinyar shi yana share mata hawaye da handkerchief.

Ganin haka ta fahimci ya sallameta sai ta juya ta koma kitchen, sauran doyan da ya rage ta zauna ta ci.

Ta fara da wanke-wanke da sharan kitchen kafin ta fito ta samu babu su parlor, ta duba kwanon da ta saka musu abinci babu komai a ciki harda sauce ɗin albasan sun cinye tass.

Ita sai a lokacin ta tuna ance yarinyar bata cin yankakken albasa. Tayi murmushi kawai ta kwashe kwanukan ta kai sink.


```````````
Seemahwrites ✨

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
Chapter 17 · 0% Book details