Chapter 29
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)
Wattpad and Arewapen @Seemahwrites
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
29… Tafin hannun shi ya buɗe mata da nufin ta saka mishi zoben Nne a ciki. A tunaninta taimaka mata zai yi ta miƙe don haka ta goge ƙuran hannunta a jikin farin sweatpants ɗin jikinta sannan ta saka nata tafin hannun cikin nashi ta yunƙura zata miƙe tsaye.
Sake janyota yayi da ƙarfi ta dawo ta zauna daɓas, ta yamutsa fuska tana kallon shi saboda buga mazaunanta da tayi.
Yayi mata alamar yanda ake saka zobe da cirewa a jikin yatsar shi sannan ya sake buɗe mata tafin hannun shi ta saka mishi a ciki.
A razane ta ware ido tare da dafe ƙirji, ita ta manta dalilin da yasa yake bin ta a guje kenan, sai ya mata kaman tsere ne suke yi kuma ta haƙura ta sadaƙar masa ya ci.
“Chukwu m! (My God)” Abdulhameed ya furta a hankali ganin ta fara dube-dube.
Tun tana yi daga zaune har ta miƙe tsaye tana juye-juye ko zata hango ƙyallin zoben azurfan da ta jefar.
Shima ya miƙe tsaye ya ruƙo hannunta ta juyo ta fuskance shi kafin ya sake gwada ta da yatsa.
“Wallahi ki kuka da kan ki idan baki samo mun ring ɗina ba Ikram”
Bata ji me yace ba, amma ta gane gargaɗi yayi mata wannan karon.
Tashin hankalin da ya gani a cikin idanuwanta yasa da ta cigaba da bin hanyar da suka wuce tana dubawa shima ya fara taya ta.
Har tsakiyar filin da koren ciyawa yayiwa ƙawanya saida suka durƙusa suka duba babu zobe babu alaman shi, gashi almuru ta gabato wuri ya fara duhu sai ƙoyayen fitila da suka maye gurbin rana wurin haska makeken filin.
P.E teacher ɗin su ta haɗa kan sauran student ɗinta masu matsalar ji irin su sannan ta zo tayi musu alaman suma su zo su tafi saboda kowa ya watse, sai Ikram ta miƙe tsaye da sign language tayi mata bayanin da sha'awar fahimtar abinda take cewa ya kama Abdulhameed.
Malamar ta taɓa agogon hannunta sannan ta haɗa yatsar ta babba da manuniya sau biyu, ma'ana ta basu minti ashirin su shigo ciki sannan ta juya ta tafi da sauran students.
Zuwa lokacin hankalin Abdulhameed ya fara tashi, amma ganin yanda fuskar Ikram yayi kaman zata fasa Ihu yasa bai sake cemata komai ba suka cigaba da kewaye filin.
Can kaman wanda aka tsikara yaga ta miƙe tsaye. Ya tsaya da abinda yake ya ɗago yana kallonta, sai yaga ta luma hannunta a aljihu ta fito da shi a dunƙule.
Ya miƙe tsaye yana fatan abinda yake tunani ne.
Tana buɗe tafin hannun nata kuwa sai ga zobe a ciki.
Ashe yana cikin aljihunta duk tsawon lokacin nan.
Sai ta fashe da dariya kaman wanda taga wawan zama.
Saida ya saka hannu na ɗauki zoben daga cikin nata kafin ya dunƙule ɗaya hannun shi ya kifa mata ranƙwashi.
Mugun kallon da ya watsa mata yasa ta haɗiye kukanta tana ƙifi-ƙifi da idanu.
“Wuce muje” yayi magana yana tura ta gaba don ba wai ya huce bane, lokacin Sallah ne yayi idan basu je masallaci ba har aka idar kuma hukunci zai hau kansu.
Ta ɗaga idanunta sama tana kallon yanda sararin samaniya ya koma kalan orange saboda rana dake hanyarta na faɗuwa.
Abdulhameed ma ya ɗaga kan shi yana kallon yanda yayi kaman ranan ta bayan ginin makarantar su zai ɓuya, fiye da wata guda da gwamnatin tarayya na Nigeria ta ɗauki nauyin kawo shi makarantar ta hanyar scholarship ɗin STEM training amma sai yau ya taɓa lura da kyawun shi.
Ya sauƙe numfashi yana cigaba da angiza ƙeyar Ikram har masallaci, sai gashi tana wanke kwanuka yana ɗaurayewa a kitchen ɗin cafeteria bayan an gama cin abincin dare a matsayin punishment na makara Sallah da suka yi.
A wurin ma garin rikici saida suka fasa kofunan glass har guda biyu, saboda gani yake yi ƙiraren hannayenta basu da ƙwarin da zasu yi masa sauri yanda yake so, ita kuma tace ba zata yi ɗauraya ba domin idan ta gama sai ta saka kitchen towel ta goge su duka ta jera.
Sai goma na dare ya samu komawa ɗakin su a gajiye, daman baya kula kowa yana hawa gado sai barci.
Ya ɗauka daga nan shikkenan abinda ya haɗa shi da ita ya raba, sai gashi tare da ita a wajen class ɗinsu sun yi kneel down washegari, a dalilin lattin zuwa aji da suka yi, kuma gajiya da yaci jikin kowannen su jiya ya sanya barcin su yayi nauyi.
Kaman bata lura da shareta da yayi ba ta rarrafo kusa da shi ta jingina da jikin shi, barcin ba wai ya isheta bane ba har yanzu, idan ta samu dama zata ƙara ko kaɗan.
Shi tunda yazo bai ga wanda ke shiga mishi hanci da ƙudundune ba kamar wannan yarinyar.
Ya saka yatsar shi manuniya a goshinta, ya tura kanta baya dashi, sannan ya sake bada tazara a tsakanin su ta hanyar matasawa gefe yana kallonta a fuska a tamke.
Turo baki tayi ta jingina da bangon class ɗin ta cigaba da gyangyaɗinta.
Ya juya kan shi baki ɗaya daga kallonta yana sake tuna accident ɗin da suka yi da Nne kamar yanda yake yi a kullum.
Shekaru uku kenan amma har yanzu rayuwar shi bata dawo daidai ba. Shi da ya kamata ace yayi nisa a jami'a a shekarun shi 21 da haihuwa amma gashi nan a cikin shirmammun yara.
Ya juya ya dubi Ikram yana jan tsakin da babu wanda ya ji sautinsa harda shi kanshi balle Ikram da idanunta ke a rufe, dara-daran lashes ɗinta sun rungume juna.
Saida malamin dake cikin ajin ya gama zai ɗauki attendance ya fito yayi musu alamar su shigo da hannu.
Sai gashi ita ce mai zagawa da takardar da kowa yake rubuta sunan shi a kai, yayi mamakin yanda aka yi duk cikin masu dama-dama a ajin wannan ƴar yarinyar ce mataimakiyar shugaban aji.
Da yaga ta nufo desk ɗin shi sai ya harɗe hannun shi a ƙirji yana hararar ta.
Ganin ta yi kwana bata ƙaraso ba Ya jinjina kai tare da mayar da hankalin shi kan abinda malamin ya rubuta a kan allo kafin ya fita.
“100 days to exams”
Tun Kafin su zo an riga an sanar musu duk wanda bai ci jarabawa ba gwamnati zata dakatar da biya musu kuɗin makaranta saidai su dawo gida, saboda duk wani international student sai yaci jarabawar da ake kira da EJU kafin ya samu gurbin karatu a jami’o’in ƙasar.
Yana da tarin tambayoyi amma bayi tunanin akwai wanda zai iya tambaya balle ya samu amsa.
Ya ɗora hannun shi biyu a saman desk ya kwantar da kan shi yana kallon Ikram zaune tana rubutu a seat ɗin dake row ɗaya da nashi amma kujeru biyu sun shiga tsakanin su.
Ba zaice taƙamamme ina ne wurin zamanta ba a ajin, yau zai ganta a gaban aji gobe ya ganta a tsakiya jibi tana baya.
Sai gashi lura da ita da Abinda take yi ya zamo masa ɗabi'a, koda bai so ba sai ya kama idanun shi a kanta ko ita ta kama shi yana kallonta, sai ta saki lallausan murmushi a saman fuskarta tare da ɗaga masa hannu, borin kunya ya saka shi haɗe rai ya juya.
Idan ta tara mutane a kanta tana bayani da hannunta da sauri-sauri kuma, sai ta tuna mishi da surutun Ilham.
Zai iya cewa a lokacin da yake tunawa da ita kenan kawai, amma rayuwarta da alƙiblar da yake tafiya ba damuwar shi bane.
Kawai dai idan ya tunata sai ya tuna da birthmark ɗinnan na ƙasan bakinta.
Ba'a fi kwanaki da haka ba, a ranar lahadi, ya gama bin layin karɓan breakfast a dining hall kenan, yana shirin samawa kan shi wurin zama yaji mutum ya faɗo jikin shi, ba don ya riƙe tray ɗin da aka ɗora plate ɗin abincin nan da kyau ba a jikin shi zai kifar, a haka ma tea ɗin da ya haɗa a kofi ya zube duka a cikin abincin da zai ci.
Ta koma ta baya ta rungumo kunkumin shi a ƙoƙarinta na ya zamo mata kariya.
Fararen hannunta da suka zagaye cikin shi Abdulhameed ya kalla, ya ɗago yana kallon gayen dake ƙokarin zagawa ya cafkota daga bayan nashi.
Bai san mai yake faruwa ko kuma abinda tayi musu ba, amma ya san ita ce bata da gaskiya ba don haka ba ba zata gudu ba, saidai ta tsaya ta kama ɗan ƙugunta duk tsawon mutum tayi mishi rashin kunya.
Ya ajiye tray ɗin a kan table ya ɗauki chopsticks ɗin ƙarfe guda biyu da aka saka masa ya ci abincin da su, suna ɗigar da ruwan shayi ya saita su a fuskar saurayin kaman zai ɓula mishi idanu.
Da sauri yayi baya ya shiga yima Abdulhameed bayanin abinda Ikram ɗin tayi mishi da sign language.
Bai barshi ya gama ba dukda ba fahimta zai yi ba ya sake yunƙurowa kaman zai dake shi, hakan ya sa ya haƙura da kai mata hannu tunda Abdulhameed ɗin ya fishi a tsaye.
Da ya je ya kai ƙarar su, shi da ita basu karya ba aka saka su wankin banɗaki, kafin su gama su dawo an gama rabon abinci har sauran ɗalibai sun watse ana goge wurin.
Yana zaune a staircase tazo rungume da wasu manyan biscuit guda biyu da madaran kwali harda straw, ta miƙa mishi komai ɗaya.
Da bai karɓa ba, ta ɗora mishi a kan cinyar shi ta koma gefe ta ɓare laidan nata biscuit mai dabino a ciki ta fara ci.
Kafin ta gama shima yayi rabin nashi don har ƙullewa hanjin cikinsa suke yi saboda lokaci ya ja sosai.
Yunwar da yaji a yau, ya tuna masa da irin rayuwar da yayi a gidan mahaifinsa. Sai yaji yana son cigaba da zama a Japan, yana buƙatar yayi nesa da Nigeria na tsawon lokaci.
Madaran ya zuƙa ya ajiye kwalin a gefe sannan ya taɓata, ta juyo ta bashi hankalinta tana tauna a hankali.
Ya ɗaga hannun shi yana so yayi mata magana amma ya rasa yanda zai bayyana kalaman bakin shi da yatsunsa.
Sai ta ɗaga mishi yatsar ta ɗaya sannan ta tashi da sassarfa ta haura saman matakalan babu ɓata lokaci ta dawo riƙe da ƙaramin jotter da pountain pen ta bashi.
Idan ba ɓata gani yayi ba sai yaga kaman sunanta ne rubuce a jikin biron, rubutu tun daga kamfani.
A maimakon ya fara zancen abinda ya dame shi sai ya rubuta mata tambayar ma'anar ‘Yashi’ dake jikin sunanta.
Ya san family ɗin yashi, kaɗan daga ciki ƴan Nigeria sun san ƙauyen yashi dake ƙaramar hukumar alƙaleri a garin Bauchi, amma kowa ya san family ɗin yashi wanda suke da nasaba da garin, saboda dukiya da Allah ya wadata musu, suna da kamfanunuwa da gidajen mai a yawancin jihohin Nigeria, saidai Ikram bata yi masa kama da yaran masu kuɗi ba, shiriritan ta yayi yawa.
Kafin ya gama tunani ya ganta tana dawowa hannunta ɗaya a dunƙule, kafin ta nuna mishi ƙasan da ta ɗebo a ciki.
Ya kalleta ya sake kallon yashin da babu inda zata iya samun shi a cikin makarantar saidai filin sport dake ta baya, shi bai ma lura da tashin ta a gefen shi ba, lokacin tunanin shi yayi zurfi.
Ya gyaɗa kai cikin fahimtar abinda take nufi, bata da alaƙa da wancan yashin.
ya ɗauki jottern da ta ajiye ya rubuta mata. “Je ki zubar ki dawo”
Idan ba haka ba yanzu sai a saka su share matakalar baki ɗaya, domin ko ina an ɗauki tsafta da muhimmanci a ƙasar musamman a makarantu.
Ta je ta zubar ta dawo lokacin ya sake wani rubutu ya bata ta karanta.
“yaya zan yi in ci jarabawar da za'a yi?”
Ta ɗauki lokaci tana rubuta amsa, har saida yaji ƙirjin shi yayi nauyi da tunanin darussan da ake buƙata suna da yawa fiye da na Jamb da waec, kafin ta miƙo mishi tare da ƙura mishi idanu a lokacin da yake karantawa.
“dole kana buƙatar cin Maths, Japanese language da Sign language, Sai sauran subjects ɗin major ɗin da kake son zaɓa. Amma ni community Health nake son karantawa saboda ina son buɗe NGO a Nigeria ina taimaka ma masu disabilities da basu da halin zuwa makaranta da marasa lafiyan dake kwance a asibiti da ƙananan yara.”
Abinda bai tambayeta ba yafi yawan abinda yake son ji a cikin bayaninta.
Ya rubuta mata “who ask you?!”
Da ta karanta sai yaga tayi murmushi sannan tayi rubutu ta miƙo masa.
“Zan koya maka Sign language da japanese language, shekaru na 6 a nan duka na iya”
Kaman ta san abinda zai roƙa kenan a gaba amma yana gudun raini, kada ta samu fuskar sake mishi irin na ranan.
Sai ya rubuta mata “okay” kawai ko godiya babu.
“kai kuma zaka koya mun maths”
Harara ya watsa mata ya rubuta amsa “No” ya mayar mata.
Sai ta ruƙo hannun shi tana kwaɓe fuska alaman roƙo.
Saboda kada ta dame shi ya gyaɗa kai ya samu ta sake shi.
A sannu Abdulhameed ya fara koyan Sign language, ya fara amfani da shi, ya fara fahimtar mutanen da yake tare da su, sai yaji kaman yanzu duniyar ba shi kaɗai bane kaman yanda yake ji a baya tun bayan da ya rasa kunnunwansa.
Daga wannan rana kusancin su ya ƙaru da Ikram saboda lokacin da suke ɓatawa a tare da juna wurin karatu, da ma hira da take yi mishi koda baya so, sai ta gwada mishi shima darasi ne da zai saka ya ƙara gogewa a sign language, kuma hakan ya sanya ba tare da yayi aune ba ta shige jikin shi, ya saba da ita.
Kwanakin da aka fara ƙirga su tun daga ɗari a kwana a tashi suka ƙaraso, aka rubuta jarabawa saura sakamako, amma yana ji a jikin shi alaƙar shi da Ikram bata da ranar ƙarewa. Saboda ita ce mutum na biyu da ta taɓa shiga ran shi haka bayan mahaifiyar shi, ta zamo wani ɓari na rayuwar shi da baya jin zai iya haƙurin rashinta.
Result ya fito kuma shi da ita sun samu abinda ake buƙata, don haka course ɗin da ya cika ‘Biomedical Engineering Technology’ ma ya samu.
Bayan ya ji burin Ikram sai ya fahimci nashi bai wuce ya ƙirƙiri abinda zai dawo mishi da jin shi ba, saboda bai cire rai wata rana zai koma dai-dai ba.
Ranar Entrance ceremony ɗinsu sai ga Mardiyya, ƴar uwar Ikram uwa ɗaya uba ɗaya.
Sosai Ikram tayi murnan ganinta saboda bata yi tsammanin akwai wanda zai zo mata daga gida ba, amma duk yanda Mardiyya ta so Abdulhameed ya shiga hoton da za'a yi musu tare Ikram ta ƙi.
Bai ɗauki abun da zafi ba koda tayi mishi bayanin ƴan gidan su ne bata son su san shi tukunna, tunda ko ba daɗe ko ba jima matuƙar suna son juna da gaske dole watarana ya dangana ga wurin iyayenta.
Shikkenan kuma bayan Mardiyya babu wanda ya sake leƙo Ikram, shikam dama bai saka ran ganin kowa ba.
Akwai likitocin dake zuwa duk shekara su duba su, wanda suke da chance ɗin sake ji idan an taɓa kunnen su ko da taimakon hearing aid ne sai Organisation ta ɗauki nauyin surgery ɗin su.
Da shi aka fara, saboda nashi hatsari ne ya jawo mishi Lalacewar Inner Ear hair cells ɗin shi, shiyasa yake iya magana domin abun bai shafi ƙwaƙwalwar sa ba, ba kaman Ikram da aka haifeta da nakasar ba saboda gado tayi a wurin kakanta ta ɓangaren uwa.
Ita kaɗai ta raka shi har ƙofar ɗakin tiyata tana bashi ƙwarin guiwa, a shekaran da aka yi nata bayan nashi yayi failing, da hatsarin idan aka sake taɓa kunnen za'a sake jawo masa wani matsalan, shima ita ke bashi ƙwarin guiwa yayin da ake gungura ta a gadon marasa lafiya.
Shi kaɗai ya zauna jira har aka gama aka fito da ita, har ta farfaɗo, amma saida aka tabbatar cochlear implant da aka yi mata is successful sai ga Aminu Yashi tsaye a gaban Abdulhameed, yazo tare da mahaifiyarta da Mardiyya.
Idan kuma aka ce tsakanin rabuwar shi da Ikram zai ƙirga toh daga wannan ranan zai fara har zuwa ranar da suka zauna tare da Mardiyya tana faɗa mishi ko da iyayensu sun yarda zasu bashi Ikram ba zai iya bata rayuwar da ya dace da ita ba, shi ba kowa bane bayi da komai, ita kuma iyayenta suna da burika masu yawa a kanta.
Kuma duka abinda ta faɗa gaskiya ne. Bai ajiye ba bai bawa wani ajiya ba, ko a yanzu da suke shirin kammala karatun su idan aka ce ya fito ya auri Ikram ba zai iya ba, tun da ba zata iya rayuwa da shi a gidan su ba, Musamman a yanzu da yasan ita wacece, ya san wani Yashi ne maƙale da sunanta.
Shi ya fara jan baya da ita lokacin da take undergoing therapy, sai ta buƙaci ya rakata kaman yanda suka saba yaƙi zuwa, har ya ƙare ya fito ya nuna mata bayi ra'ayinta a yanzu, duk saboda ta samu kyakkyawar rayuwa.
Amma bayan tayi aure da wani ba shi ba, haɗuwar su a Nigeria ya zame masa darasin da har zuwa yau bai sake taɓa macen da ba muharraman sa ba da gangan.
.
.
.
Abdulhameed ya miƙa hannu ya karɓi Kiki a hannun Mardiyya ya raɓa ta a kafaɗar shi, ba tare da ya sake ce mata komai ba ya juya ya bar mata gida.
``````````
Seemahwrites ✨