← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 20 OF 30

Chapter 20

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

Wattpad and Arewapen @Seemahwrites

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


20… Ganinshi kawai suka yi a tsaye, bai shigo ba amma babu wani shamaki a tsakaninsu dake ƙofar ɗakin a wangale take, maganar da suke ya saka babu wanda ya ji sallamar da yayi daga farko, shi kuma bai sake yin wani ba.

“Daddy..” Kiki ta sauƙa daga kan cinyar Aunty Surayyah tayi kan Abdulhameed da gudunta.

Idanun shi a kan Ilham lokacin da ta rungume mishi ƙafafu, suma shi suke kallo ita da Aunty Surayyah, sun riga da sun san shine kawai mai shigowa gidan kai tsaye amma ganin lokacin da yake dawowa bai kusa yi ba yasa suke kallon shi kaman baƙo.

Nutsuwa kaɗan ya samu ganin idon Ilham ɗin ya saɓe gashi har ta buɗe tana kallonsa da shi, an rufe raunin kuncinta da bandeji, na gefen bakinta kuma an sakaye shi da wani magani mai kalan da ba na jini ba, ba kalan da a duk duniya ake amfani da shi matsayin alamar zafi, hatsari ko tashin hankali ba.

Don shima nashi tashin hankalin yana da wannan kalan.

Ga kuma wani ƙarin zafin kai dake tunkaro shi, wanda ya gama sakankancewa a kai har saida Excellency ya tunasar da shi.

Ganin Ilham ta cire idanunta daga cikin nashi shima sai ya sauƙe su a kan Kiki dake faman washe masa haƙora ya mayar mata da ɗan ƙaramin murmushi Sannan ya sunkuya ya ɗauke ta.

Saida Aunty Surayyah ta jira ya sake ɗagowa ya kalleta tace “Abdulhameed ka dawo?”

Ya jinjina kai fuskar shi babu annuri “Yes Aunty Sharmama, I have something to do outside of the office…”
Har ila yau Hausa ba ya gama zama a kan harshen shi bane, tunda bai gama ƙwarewa a kanta ba ya daina jin yanda ake furta sauran kalmominta balle ya riƙe su a cikin kansa yana amfani da su. Shiyasa bayi iya dogon magana ba tare da ya sirka da turanci ba, ya dai yi ƙoƙarin barin inyamuranci don ko yayi ma a cikin mutanen da yake rayuwa tare da su a yanzu babu mai ganewa sai ya fassara.

Ya ƙarasa da “Shiyasa na taso da wuri”

Iyaka ƙoƙarin shi yana yi wajen ganin bai sake ɗora idanun shi a kan Ilham ba duk da zuciyar shi dake ingiza shi, don gani yake yi kaman idan ya sake kallonta zai ga wani abu ya canza a fuskar tata, zai ga babu wannan raunin duk sun ɓace.

Amma Kiki saida ta kamo haɓar shi cikin ɗan hannunta, ta karkata fuskar shi ya tsaya a kanta kafin take nuna Ilham da yatsa tana cewa “Daddy wancan matar ta ji ciwo”

Ya ja dogon numfashi ya furzar a hankali yana kallon yarinyar, bai ga abinda a duniyar nan zai iya rabata da shi ba, shiyasa ya rufe ido ya amince da buƙatar Excellency.

“Kin ce mata sannu Allah ya sawaƙe?”

Gyaɗa kai tayi, kuma shi a karan kan shi ya san ƙarya Kiki take yi ba sai an faɗa ba amma tunda nashi gaisuwan ya shiga kunnen Ilham shikkenan.

Yace “welldone Aunty, bari na tafi da ita ku huta. Thank you”

Godiyan da yayi a kan taimakawa Ilham da tayi ne amma bayi son ita Ilham ɗin ta fahimci ya bayar ma lamarinta muhimmanci ko kaɗan, daga haka ya juya ya bar ƙofar ɗakin.

Yanda suke zaune a bakin gadon cinyar su na gogan na juna ita da Aunty Surayyah duk ya gama takurata, kuma ta ji rashin dacewar ganin su a haka da Abdulhameed yayi a matsayinta na wacce take aiki a ƙarƙashin su, amma ta kasa motsawa har saida Aunty Surayyan ta miƙe.

“Nima bari na baki wuri, ki kwanta kafin la’asar tayi, idan kin yi sallah sai ki je gida”

Ilham ta miƙe tsaye. “Hajiya idan babu wani abinda zan yi, tunda ya dawo nima zan tafi”

“Gaggawan me kike yi? Ko wani dukan za'a sake miki idan baki koma da wuri ba?”

Da sauri ta amsa da “A'a asibiti zan je wurin yarona, yau ban je na duba shi bane”

Ta ɗan tsura mata ido cike da tausayi.
“Kin tabbata baki buƙatar a haɗa shi da hukuma? Ni zan tsaya miki, kuma za'a hukunta shi daidai da laifinsa”

Ta shiga girgiza kai idanunta a rufe, a cikinsu ganin irin masifa da bala’in da zata ƙara gayyato ma kanta take yi, Idan labari ya isa familyn Baniza na ta haɗa Hashim da hukuma sai ta gwammace kiɗa da karatu. Ai idan dukanta ne ba yau ya fara ba, kuma bata jin yau ɗin zai kasance karo na ƙarshe koda kuwa zata cigaba da yin kaman yanda yake so a gaba, amma ba'a taɓa samun wanda yace mishi meyasa ba balle ace ya bari, saidai ita a hore ta da gujewa bacin ransa.

“A'a Hajiya dan Allah, ki rufa min asiri kawai in cigaba da lallaɓawa, wata rana zai wuce”

“Allah yasa” cewar Aunty Surayyah tana sauƙe numfashi. “Muje in ajiye ki a asibitin”

Har ciki suka shiga da ita ta duba jikin Muftee ta ajiye musu 5k sannan ta zaga ta gaida sauran majinyata kafin ta tafi.

“Addah Fidela na tambaye ki a ina kika ji ciwo haka kin yi mun banza?!” Ihsan ta tunkareta bayan ta dawo daga raka aunty Surayyah mota, tana taɓa mata wurin a hankali don gani take yi kaman ba da gaske ba, jiya-jiya suka rabu garas ɗinta.

Ta cire hannun Ihsan a fuskarta don tana jin zafin raunukan har yanzu. “Hatsari muka yi nida mai mashin da safe, amma da sauƙi sosai kada ki damu”

Ta wuceta ta ƙarasa ta ɗauki kofi mai murfin da suke ajiye ruwan sha a ciki ta buɗe murfin ta kafa a bakinta, tunanin yanda zata fara faɗawa Ihsan zancen zamanta da ta hakura da shi kawai ya saka ta ji maƙoshinta ya bushe matuƙa, kafin ma a zo kan yanda zata yi da Muftee idan ta tafi ɗin, gashi da suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wurin bashi kulawa har ya fara farfaɗowa yayi haiba.

Saida ta shanye ruwan tass, ta sauƙe kofin tana kallon cikinsa.

“Filiyan ki haɗa kayan ki kawai kiyi kuɗin mota da dubu biyar ɗinnan gobe ki koma wurin Maama ki ƙarasa hutun ki a can tunda kinga yanzu da sauƙi kwanan nan zasu sallame mu in sha Allah”

Ihsan ta yamutsa fuska tana kallonta a kaikaice. “Ban gane ba? Dududu yau kwana huɗu da zuwana idan ma zaki kore ni ai sai ki bari ko sati na cika.”

Ta ɗago idanunta da suka tara ƙwolla take ƙoƙarin mayar da su tace “Allah ya baki haƙuri ni ba koran ki nake yi ba, zaman asibiti ne babu daɗi na sani”

“Toh ace ma na yarda zan tafi yaya zaki yi da aikin ki? Kawai ki faɗa min ainihin abinda ke faruwa malama”

Ta saka hannu ta tallafe goshinta hawayen idanunta suna gangarowa kan fuskarta.

“Cewa yayi in haƙura da aikin ko in hakura da zaman ki a nan Ihsan. Ba zan iya haƙura da aikin ba domin abincin da kika kawo mana wata rana zai ƙare, haka jikin Muftee wata rana zai sake tashi a sake kwantar da mu a asibiti. Kuɗin Ya Hashim ma jikinsa da cikinsa yake kashewa da sauran bukatunsa amma hakkin mu dake wuyan shi bai ɗauke shi a bakin komai ba, kinga dole in dage in nemi kuɗi, shiyasa na zaɓi aiki na a kan taimaka mun da kike yi, Allah ba zai hana ni inda zan yi ba.” da ƙyar ta samu ta kai ƙarshen zancenta don jin maƙoshinta take ya sake bushewa ƙadagas kalaman suna fitowa da zafi.

“Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Amma wallahi Yaya Hashimu bayi da mutunci ko kaɗan, bayi da imani bayi da tausayi” ta ja tsaki tana karasawa ta karɓi wayanta a hannun Muftee da yace ta kunna masa game, amma shima tunda yaga fuskar Ilham jikin shi yayi sanyi.

Ilham ta riƙe wayan a tsorace “me zaki yi?”

“Maama zan kira, wallahi babu inda zan je”

“Dan Allah kada kiyi mata zancen hatsari na, hankalinta tashi zai yi”

Kallonta kawai Ihsan tayi tana kokwanton abinda Ilham din ta ɗauketa da ba zata fahimci ainihin abinda ya sameta ba daga bayanin da tayi yanzu.

“Naji, ba zan faɗa ba”

Ganin da gaske take yi Ilham ta maida mata wayan.

Har Ihsan ta laluɓo layin Maama sai kuma ta fasa ta danna kiran numbern da tayi saving da ‘Yaya Zaki’.

Bai ɗauka a kiran farko ba saida na uku ya kusan tsinkewa kafin ta ji sallamar shi yana ƙarawa da “ko bani da hankali idan nazo naga missed calls guda biyu kin san zan biyo. Sallah nake yi Filiyan!.”

“Kayi haƙuri yaya Aliyyu wallahi Addah Fidela ce dama” ta yi saurin katse shi don idan ya fara masifa bayi gamawa da wuri.

“Me ya sameta?” Tana jin yanda muryar shi ya canza yayi ƙasa in all seriousness.

“Wallahi mijinta ne yace wai saidai na bar masa gida, kuma jikin Ibrahim har yanzu, gashi tana zuwa gidan aiki kullum tun safiya har dare shine ta zauna take ta kuka”

“Me kika yi masa?”

Kaman yana gabanta ta zaro idanu tace “Ni kuma? Kwana na ɗaya a gidan kacal fah, kuma banda wanka babu abinda yake kai ni can, sannan bani zuwa ma lokacin da yake nan balle in yi karo da ajiyarsa”

Bai fahimci zancen ajiyar da tace ba kuma bai maida hankali a kai ba sai cewa yayi “shikkenan bari na kira shi mu ji, idan kuma kin je ne kika tada mata husuma a cikin gida ki kuka da kan ki”

“Ni wallahi babu abinda nayi, wa ma yake da lokacinsa banda ita Fidela ɗin?” ta turo baki tana ƙunƙuni lokacin da ya kashe wayan shi.

Ta riƙo hannun Ilham da ta ƙame kamar sabuwar soja duk tsoro ya gama kamata, tana jin gwara ta haƙura ita ta cutu a kan abinda zai biyo baya idan ta shigo da wasu cikin lamarin nan, wasun ma mutum mai zuciya da Fushi irin Aliyyu.

“Ki zauna ki kwantar da hankalin ki babu inda zan je kuma babu abinda zai faru, ai ko ce mishi aka yi an jefo ki duniya ne daga sama cin kashin ya isa haka.”

….

A parlorn mahaifin su khausar suka saba zama suyi hira, kuma Hashim bayi zuwa sai da daddare, saboda yanda yake son a rufe zancen auren har sai lokacin da yaga ya kamata ya fito ya bayyana da kansa.
Ya sani babu mai goya mishi baya idan aka ji ya rakito ƙarin aure bayan ga ɗan shi kwance a asibiti, kuma hakan zai bawa Ilham daman yin ƙorafi a saurareta, amma idan ya bari sai bayan an sallami Muftee daga asibiti ya ɗago zancen babu mai ganin laifinsa tunda ba a kan shi aka fara mata biyu ba a family.

shiyasa ba zai bari Ihsan ta ɓata masa shiri ba.

Ya dubi Khausar da ta rakuɓe daga cikin soron gidan su, rashin jin daɗin tsayuwar ya nuna a kan fuskarta amma baffa Umar yana cikin gidan kuma yana da baƙo wani abokin shi ya kawo masa ziyara.
Cikin taushin murya da ƴammata kawai yake lallaɓawa haka yace “na faɗa miki nayi wa tufkar hanci, idan Ihsan bata bar kaduna a yau ba gobe a kano zata kwana, yanzu menene damuwar?”

“Ai ni kawai cewa nayi kada ka bari Aunty Ilham ta faɗa mata zancen ta je ta sanar a family house, ba cewa nayi ka koreta ba, yanzu ka sani ma ko ɓacin rai yasa ta faɗa mata a je ayi ta yawo da ni a baki ban ji ba ban gani ba?.”

Ta kwaɓe fuska tana shirin masa kuka rurin da wayar shi ya ɗauka ne ya katseta.

Ganin sunan Aliyyu a matsayin mai kiran yasa cikin shi ya bada sauti Ƙulululu, ya tsani hidima da wannan ɗan balaja’un, don bayan mahaifin su mai rasuwa a saboda shi kawai yake ɗagawa Ilham ƙafa wani lokaci, domin ɗanyen kan Ihsan ba komai bane a gaban nashi.

Ba don ya so ba ya ɗaga kiran ya ƙara a kunne tare da yin sallama Muryar shi yana fitowa da rawan rashin gaskiya.

“Baban Muftahu an wuni lafiya, yaya mai jiki”

Bai taɓa kiran shi ya jajanta mishi rashin lafiyan Muftee ba sai yau, shiyasa ya amsa da tsoron abinda aka kira aka faɗa masa.

“Lafi… Au da Sauƙi alhamdulillah.”

“An sallamo su daga asibitin kenan?” Aliyyu ya tambaya.

“A'a ba'a sallame su ba tukunna, ka san samun lafiya sai a hankali dukda ma ita wannan cutar bamu san ƙarahenta ba, gashi nayi-nayi da ita a gwada na gida tunda ana dacewa taƙi ita sai na asibiti” ya ƙarasa da ɗan dariya kada Aliyyu ya fahimci maido da laifin kan Ilham yake son yi yanda za'a ce ita taƙi jin maganar shi.

“Hakane, ita Kuma Filiyan laifin me tayi aka ce ta dawo tunda naji na ita Fidelan, daman ba jin magana take yi ba na sani, in yaso ni sai in zo in taya ku ɗawainiyar asibitin tunda idan ba Ihsan ɗin ba sauran daga manya sai ƙanana sosai ba iyawa zasu yi ba saidai Ni”

“Hasbunallahu wa niimal wakeel!” Hasim Ya miƙe daga jinginen da yake yana dafa ƙirji. Ai gwamma ace Ihsan ta dawo da zama dindindin da ace Aliyyu ne zai zo yayi ma Ilham zaman jinya.

“Kada ka damu zata zauna kawai har ranar da taga daman dawowa don kanta”

Aliyyu yace “toh madallah, sai a ƙara haƙuri ka san mata ne rauni gare su kuma marayu ne, idan aka zalunce su sai Allah ya kama mutum yayi mishi ɗaurin da ba zai taɓa samun hanyar warwarewa ba. zan yi mata magana ta koma gidan baffa Rabe da kwana, Allah ya shige mana gaba”

Ƙittt, ya katse kiran ya bar Hashim da Khausar suna kallon-kallo.

An faɗo daga sama an faɗa rijiya.
….

Tunda ya samu aka fara program din da Kiki take so sai ya tashi ya barta a jikin TV ya shigo ɗan ɗakin da ya mayar da shi workshop ɗinsa na haɗe-haɗe da gyare-gyaren na’urar taimakawa ji.

Mafarkinsa kenan, ya zama babban Engineer ta wannan fannin, Amma abinda yake yi a yanzu, A&I mafarkin Ikram Aminu Yashi ne, saidai shine kawai zaɓin da ya rage masa a lokacin da ya siyar ma Excellency patent ɗin sabon samfurin hearing aid ɗin da ya ƙirƙiro don ya ba ma Kiki ingantacciyar rayuwa.

Saidai har yau Excellency bai yi amfani da patent ɗin ya bayar ana ƙirƙiran Hearing Aids ana siyarwa yana samun riba ba, ko ya siyar ma manyan kamfanunnuka, duk da sun tsaya ne a kan zai riƙe a wurin shi amma idan Abdulhameed ɗin ya biya shi ta wani hanya zai dawo mishi da patent ɗinsa.
Kuma tunda ya bashi ya daina amfani da samfurin kwata-kwata, har Kiki ba da irin shi take amfani ba, don yana so ne alaƙar shi da Excellency ya tsaya a iya patent kawai amma kaman hakan ba zai yiwu ba.

Drawer ya buɗe ya ɗauko wani case kaman na Airpods ya dawo ya zauna a gaban table ɗin da ya baza kayan aikin shi, ya ciro abun ƙananu guda biyu sannan yayi pieces-pieces da su kafin ya fara gyarawa.

Ya ɗauki lokaci yana tunanin abubuwan da zasu canza idan jin shi ya dawo, irin rayuwan da shi da yarinyar shi zasu yi a gaba, kuma babu buƙatar Excellency yayi amfani dashi wajen samun goyon bayan talakawan ƙasa a siyasa tunda shima yanzu yana ji kaman kowa.

Ya daɗe yana taɓe-taɓe kafin ya mayar da abubuwan ciki ya haɗa su kaman yanda suke daga farko, saidai akwai abubuwan da ya gyara daga ta cikin wanda shine yake fatan zai kawo sauyi a rayuwar shi.


Fata a karo na babu adadi.


``````````
Seemahwrites ✨

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
Chapter 20 · 0% Book details