← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 23 OF 30

Chapter 23

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

Wattpad and Arewapen @Seemahwrites

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


23… bata da amsar bayarwa idan aka tambayeta a kan tafiyar ƙaddararta.
Ya cigaba da gudu ne ko yana tsaye a wuri guda? wannan Allah ne ya bar ma kansa sani.

Amma idan aka barta sai tace kamar da baya yake komawa ba gaba yake yi ba, idan kuma ba tafiyan ƙaddararta bane yake hakan toh Hashim ne da ya ɗauketa matsayin bolar kasuwa yake sakawa take jin haka.

A daren jiya bayan ya ɗagata daga barci, daga alamun shi ta fahimci abinda ya kawo shi.
Ba'a kwana biyu ba da yayi mata lilis kaman zai aikata lahira, tun yana kutubol da ita tana ihu har ta fara neman hanyar guduwa daga gidan ganin bayi da asara idan ya rabata da ranta,. Sai gashi ko zafin raunukan da ya bar mata bata gama ji ba ya lallaɓo yana niman wani abu a wurinta saboda son zuciya.

“Haba kai kuwa!”

Saida ta buɗe baki tayi magana ta ji inda zuciyarta ke zafi har zuwa maƙoshinta.

“Ban gane ba! bani son rainin hankali fah Ilham. Don kin samu sake kina abinda kike so ba yana nufin zaman kanki kike yi ba Yauwa! Zaman aure kike yi kuma gidan nan ba da kuɗin ki nake biyan haya ina ajiye ƙatuwar banza da ba zata amfane ni da komai ba.”

Allah ya gwada mata lokacin da zai zo tayi wata guda babu sabon baƙin cikin Hashim dake ƙara taruwa a tsakanin ƙirjinta ya sakata taji kaman zai fasa haƙarƙarinta ya fito.

Bata sake cewa komai ba, ta tsaya jiran yayi yanda yaga dama da ita, amma bata cikin yanayin da zata iya masa wani abu.

Tsamin jikinsa na ranan da ya gama kwasowa ya sakata rintse idanunta, tana imagining yanda gobe zai yi wanka ya saka turare ya kaiwa mutanen waje da ƴammata ƙamshin, ita kuwa an barta da na boxers ɗinsa da idan tazo wankewa sai tayi masa saɓi biyu.

Bata san me ya faru ba, amma a hankali ta ji warin dake shiga hancinta na raguwa, da ta buɗe idonta sai taga baya tsaye a wurin, kafin ta ji motsin shi a bayanta, tana juyawa sai taga ya kwanta a ɗaya ɓangaren gadon ya juya mata baya.

Salum-alum ta ɗauki pillownta ta bar mishi gadon ya bararraje, daman wayan da yake yi a parlo lokacin da yake cin abinci da wani murya mai bata haushi yana tauna cafal-cafal baki a buɗe kaman rago yasa ta shiga ta kwanta a gadon har barci ya ɗauketa.

Ta koma parlo tayi kwanciyarta shine da ƙyar ma ta iya tashi tayi sallan asuba a kan lokaci, ta wuce shi yana ta minshari ta shiga banɗaki, har ta ɗauro alwala ta fito ta ɗauki zani da hijabi bai farka ba.

Ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita cikin nutsuwarta, ta mayar da mopper da take goge ƙasan kitchen dashi cikin bokitinsa sannan ta ɗauko wayan a saman fridge tana duba sunan mai kira.

Ƙaramin tsaki tayi ganin Sageer Baniza ne, itama ya fara addabanta zuwa yanzu tun da in dai ya kira Ihsan bata ɗauka ba sai ya kirata ta haɗa su.

Kaman ba zata ɗauka ɗin ba ta dai kai zuciya nesa.

“Assalamu alaikum”

“Addah Fidela ina kwana”

“Ba zaka bar addan nan ba ko Yaya Sageer?” Ta faɗa da ɗan murmushin da bai kai zuci ba.

Shima murmusawa yayi “Ai ni yanzu bani da wanda ta wuce ki”

Tace “Lallai kam” tana taɓe baki “gashi kuma bani tare da Filiyan ɗin, ka san na faɗa maka ina zuwa aiki”

“Ai nima ba saboda ita na kira ba yau, daman na faɗa miki duk sati zan dinga kira muna gaisawa. Yaya jikin Baban mu”

“Da sauƙi Alhamdulillah”

“Toh Allah ya ƙara sauƙi. Yauwa an dawo da taron shekara nan da sati uku, saboda akwai bikin ƴar wajen baffa Ussy da ɗan Inna Sahura, sannan ba'a so ya kai cikin damina saboda ruwan sama”

Bata samu labari ba ko a wurin Addah Iman tunda ta san yayyenta maza ba kiranta zasu yi su faɗa mata ba, Maama kuma ba lallai ta sani ba. Ko da yake idan ta ga Imam ta kirata toh wani magana taji yana yawo a family a kanta sai ta kira tayi mata faɗa koda kuwa jita-jita ne kawai. lokacin da suke zaune a kano ma har wanke ƙafanta take yi ta zo kuma duk yanda zata yi mata bayanin gaskiyan lamari ba zata saurara ba, idan kuma tayi Sa'a ta saurareta ɗin haka zata nemo duk inda rashin gaskiya yake ta ɗora mata.

Shiyasa rashin shaƙuwar su ya ƙara tsamari gashi ita ce kawai yayarta mace, ta gwammace idan abun kuka da jajantawa ya sameta ta kira ƙanwarta Ihsan su raba damuwar tare, ita da ba ciki ɗaya suka fito ba.

“Toh Allah ya nuna mana lokacin”

Sageer ya amsa da “ameen, ai zaku zo wannan karon ko?”

“In Allah ya yarda zamu zo”

Tana fatan ta je ta ga Maama da sauran ƙannenta harma da yaya Aliyyu, amma Allah yasa zuwa lokacin an sallame su daga asibiti kuma Allah yasa Hashim ya yarda su tafi tare, zata biya ma kanta kuɗin mota har da shi idan yana so, don abun ya zo mata a daidai, nan da sati ukun zata ɗauki albashinta na farko sai ta roƙi hutun sati ɗaya ta je ta dawo.

“Allah ya yarda, sai ki ɗan faɗa ma Filyan dan Allah tun da bani da ƙimar da zata dinga ɗaukan kira na, a ce ina gaisheta”

Toh Allah yasa dai Ihsan ba miji mai haɗa wuri zata aura ba.

A bayyane ta amsa addu'ar da tayi a zuciyarta da “Ameen” Sageer ya ɗauka tashi addu'ar ta amsa.

“Na gaishe ki Addah Fidela, a gaida yaya Hashim sai anjima” ita ta kashe wayan ta maida shi inda yake, ta cigaba da aikinta tana ƙira’ar suratul Kahfi daga kanta tunawa da yau juma'a ne, zata samu lokacin kula da Muftee gobe da jibi kasancewar su weekend sai Ihsan ta huta.

Ƙarfe sha biyu aka tashi Kiki daga makaranta suka je suka ɗaukota, kuma Abdulhameed ma daga masallacin juma'a gidan ya dawo. Ya samu tana kan aikin haɗa abincin dare, Kiki sai binta take yi ƙafa da ƙafa ta hana ta sukuni a kitchen ɗin.

A haka ta ƙarasa koya mata Addu'an shiga da na fita daga gida har suka fara na shiga banɗaki kafin ta kammala dakan sakwaran da kiki ta gama tsoma hannayenta a ciki sauran kaɗan ta daka mata ƴan yatsu, kafin ta gama yarinyar duk ta cika mata ciki.

Yau ma ta ɗebi sakwaran ta kai ma Aunty Surayyah da zata mayar da turmi, ganin mutan gidan a waje ta rage tsayi ta gaida iyayen su suka amsa da ƙyar amma yaran bata ishe su kallo ba, ta miƙe ta wuce ɗakin aunty Surayyah.

“Sannu da aiki fa Ilham, Allah ya bada lada”

Ta amsa da murmushi a saman fuskarta don Tana jin matar a ranta sosai.

“Yauwa Hajiya nace za'a ɗan masa magana ne ya siyo Shinkafan tuwo da waken suya da gyaɗa a ɗan samu sauyi a abincin? Wani lokaci ina rasa abinda zan girka saidai maimaici”

“Abdulhameed baya cin tuwo ai shiyasa kika ga babu ɗin, hakama awara nake gani”

Mamaki ya saka tayi shiru kana tace “sau biyu ina yin tuwo a gidan fa Hajiya, kuma bai yi mun magana a kai ba”

“Amma ya ci?” Itama Aunty Surayyah mamaki ne ya kama ta.

Ilham ta gyaɗa kai “yawan wanda na bari Kiki ba zata iya cinyewa ita kaɗai ba”

Aunty Surayyah tayi murmushi mai sauti tana tuna shi a wani lokaci da ya wuce kaman bai taɓa faruwa ba.

Wahala da daɗi suna canza mutum tabbas.

“Shikkenan, ki yi list ɗin duk abinda kike son a siyo ki ba ma driver ɗin shi, da abinda babu da wanda ya kusan ƙarewa ma duka ki rubuta zai siyo”

Ta amsa da toh tayi mata sallama ta fito, sai bata sake cewa mutanen wurin komai ba tayi wucewarta.

A cikin asabar da lahadi ɗin da suka wanzu a rayuwarta, wannan suna cikin masu daɗin da suka zo mata a garin Kaduna.

Ita kanta ta san jikin Muftee ya fara kyau don har a fuska yayi haiba gashi ɗan walwala ya dawo mishi, idan ta tuna ƙiriniyar Kiki dai sai ta ji tausayinsa ya kama ta, yanda yake abu da sanyi-sanyi kaman wani babba mai cikakken hankali.

Haka Ihsan zata zo su wuni suna hira sai dare ta tafi don zaman gidan Baffa Rabe ma da babu gwamma ba daɗi ne, har take ma Ilham taɗin kaman shirin auren Khausar suke yi don taga yanda mahaifiyarta take ta siye-siye.

Ta kwana biyu ma bata ga Khausar ɗin ba, ba kaman a baya da idan bata zo yau ba zata zo gobe, amma tun bayan zuwan Ihsan ta Janye jikinta.

Tana mata fatan alkhairi don idan haka ne ta ji shawaranta kenan ta rabu da Hashim ta kama dahir.


Da safiyar litinin tayi karo da abubuwan da ta lissafo an siyo an jibge su a store ɗin gidan, babu ɓata lokaci ta shiga haɗa awara, ta dafa shi mai laushi sosai bata zaƙe masa wurin saka tsami ba, ta saka a kwando ya tsantsame lokacin da take dafa zoɓonta mai kayan ƙamshi, ta soya shi tayi mishi lafiyayyen sauce sannan ta haɗe su wuri guda, lokacin da take tasting kaman zata sulale a ƙasan kitchen ɗin tsaban daɗi.

Da ta zuba ma Kiki ma saida ta ƙara mata a cikin na Abdulhameed bayan ta cinye. Sai ta zaunar da ita bayan sun gama ta kitse mata gashin kanta tass saboda ta gaji da ganin shi a haka, kuma dake hannunta babu zafi rikici kaɗan kiki tayi, tayi shiru tana sauraron tatsuniyar da Ilham take mata har ta gama mata cuku guda 16 ta tufke mata jelar su, sai gashi sun fito rass a farin kanta sun yi mata kyau.

Ta gama shirinta na tafiya bayan dawowan Abdulhameed sai ga Kiki ta shigo.

“Mimi wai ki zo in ji daddy” ta faɗa daga bakin ƙofa.

Kirjin Ilham ya buga dummm.

Ko magana bayi mata idan ba ya zamo dole ba, kiran menene yake mata yanzu?.

Tana taraddadi a cikin ranta taje, yana zaune a dining da food flask ɗin da ta zuba masa abinci a gaban shi, saida ta rage tsayinta a wurin kafin ya ɗago ya kalle ta.

“Do you have something else please? Bana cin wannan” ya nuna awaran da ya fara zubawa a plate don yayi zaton wani abu ne daban.

Ta ware ido tana masa kallon rashin yarda. Daman akwai wanda baya son awara a duniyar nan balle ace baya ci gaba ɗaya? Ai awara ne ya kamata ma ya zama abincin duk duniya kowa yana ci kaman shinkafa da kuma buredi.

Kaman ya karanci abinda ke zuciyarta yace “da gaske bana ci, ko Lukman ya sani, da ina ci da lokacin da na dauki littafin ki na ɗauki wanda ke cikin jakar ki saboda shima ƙamshin sa kaman wannan, amma ba zan iya ci ba”

Girman idanunta ne suka ƙaru fiye da na da, kaman zasu faɗo ƙasa.

Bata san bakinta ya furta “A Moher?” ba tare da sauti ya fito ba.

Saida ta ji muryar shi a cikin kunnenta “Abdulhameed Muhammad Kagarko. Not A Moher, he's gone”

Shine.

Ta tuna lokacin da yake miƙa mata laidan ice cream ɗinnan, ta ga wani baƙin abu a jikin ƙaramar yatsar shi ta ciki.

Da yake miƙa mata laidan fruit kuma sai ta saka ido ta fahimci tatoo ne amma ta kasa karanta abinda yake rubuce saboda mayar da hannun da yayi bayan ta karɓa.

Sai yanzu ta gane menene a rubuce.

A Moher. Ainihin sunan shi kuma Abdulhameed Muhammad.
Shine wannan.

“Ko oats ne a bani please, ba zan iya jiran isowan delivery ba and I'm starving” ya sake magana.

Ƙafafuwanta da take jin su kaman igiyar lilo ta samu ta miƙar dasu ta koma kitchen ɗin.

Saida ta ɗauko wata jibgegiyar tukunya ta kunna gas zata ɗaura sannan ta ankara ta mayar ta ɗauko karami ta zuba ruwa da oats ɗin a ciki.

Mamakin da take yi ba wai na kasancewar shi wanda take tsammani tun daga farko bane sai inda rayuwa ta kawo shi.

A tsawon shekarun da suka shuɗe bayan ganin da tayi masa na ƙarshe ta samu kanta da tunanin kalan rayuwar da yake ciki yafi sau nawa.

Amma bata taɓa hango shi da wani halitta a jikinsa da ya daina aiki ba, bata hango shi yana kula da ƙaramar yarinya shi kaɗai ba saboda bai yi mata kalan wanda zai yi aure ba ma, bai yi mata kalan mazan da har zasu ɗauki kafar su suje niman aure a ɗauka a basu ba, ya dai fi kalan mayaudara masu wasa da zuciyar ƴammata.

Amma yau A Moher ne ya koma haka?! Allah mai iko.

Oats ɗin ta juye a bowl bayan ya gama, ta fasa madaran gwangwani guda ɗaya ta juye a kai sannan ta kai mishi ya saka sugar da kan shi.

“gashi”

Ta dubi kuɗin da yake miƙa mata da ido.

“Kuɗin kitson Ikram ne, Nagode”

Girgiza kai tayi, “ka bar shi kawai” muryarta ya fito a hankali saboda har yanzu mamakin da ya kamata bai saketa ba.
Amma ba tayi ma kiki kitso don ya biyata bane.

Sai ya mayar da kuɗin wurin Kiki dake zaune a gefen shi tana kallo a wayar shi, ya karɓi wayan ya bata kuɗin yace “sauƙa ki miƙa mata”

Ta karɓi kuɗin ta sauƙo ta kawo ma Ilham inda take durƙushe. “Nima sai ki sake siya mun sweet ɗinnan”

Tayi mata murmushi tana saka hannu biyu ta karɓi kuɗin. Daga kaurin su ta san da yawa, a ina ake biyan kuɗin kitso kamar haka?”

“Sai kina mata Please, zan dinga biyan kuɗin shi separately”

Godiya kawai tayi, kuɗin da ya bata yanzu kawai zai kai na kitson Kiki duk sati na rabin shekara.

Kuma ranan da tunanin shi ta kwana, har tayi ma Ihsan taɗi itama ta dinga mamaki.

“Wa ya sani ma ko shine ya canza miki initials ɗin Slum book ɗinki ya koma A&I? da kin tambaye shi ai”

Ihsan ta ƙarasa da dariya tana tofe yatsuntsa suyi damshin da zata ji daɗin ƙirga kuɗin da ya ba ma Ilham.

“kuɗin kitso ya cika Naira dubu ashirin cuss, nima dai kitson nan zan fara a kan yaran masu kuɗi daga gobe, har da ƙunshi ma sai su cika mun ya kai hamsin abuna”

Ilham ta kai mata dukan wasa suka bushe da dariya dukkan su.

Daman Allah yayi alƙawari ma duk wanda yayi imani, dukkan tsanani yana tare da sauƙi.

Kuma itama ta fara ganin sauƙi a abubuwa masu yawa.

A faro daga kan Hashim.

Bai sauya sheƙa ba, yana nan da dunƙulallen hannu, amma cikin ikon Allah ya daina mata ajiya a cikin toilet tun bayan habaicin da Ihsan tayi mishi, wani lokaci ko ya manta ya fito sai ki ji ya koma yana korawa.

Babun da take fama da shi ma yayi sauƙi sosai, yanzu bata rasa taro da sisi a hannunta, ga kawo kaza siya kaza da ake mata a asibiti bata rasa yanda zata yi da su ba, kuma abubuwan da suke samu daga gidan aikinta suke ci har su rage yasa bata buƙatar yin cefane saidai ta je ta jalafta ma Hashim abinda ya samu idan yaga dama ya siyo abinda zata haɗa ta dafa masa yayi daɗi.


Seemahwrites ✨


ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
Chapter 23 · 0% Book details