← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 22 OF 30

Chapter 22

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

Wattpad and Arewapen @Seemahwrites

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


22… Saida ta ga fitan su ta juya ta koma cikin gidan ta fara aikin gyara ko ina.
Ita kaɗai take ta kaiwa da komowa, ko ina yayi shiru sai ƙamshin Diffuser da sanyin AC, ga wadataccen hasken hantsi dake ratsowa ta gilasan winduna bayan fararen ƙoyayen wuta da suke a kunne suna ƙara fito da kyawun gidan.

Wani nutsuwa da yake zuwa mata a irin wannan yanayin ya samu wuri a ƙasan ranta ya kwanta.

Ba gwamma da tazo ɗin ba?! idan ta zauna a wancan gidan ma zuciyarta ne zata cigaba da ƙonewa da baƙin cikin Hashim har sai ta murmushe ta dawo toka, amma a nan bayan ta samu nutsuwar jiki da na zuciya zata samu abu mai daɗi ta kai ma yaronta da Ihsan da ta baro su tare.

Da sassafe Ihsan ta zo ta karɓeta a asibitin da ta kwana tare da Muftee don haka rabonta da Hashim tun jiya da yamma.

Ta gama su shara da goge-goge ta gyara ɗakin Kiki ta wanke toilet ɗinta, sannan ta dawo kitchen tana tunanin abinda zata dafa.

Akwai abubuwa da yawa da suka zo mata a kai amma babu kayan haɗawa a cikin store ɗin gidan.

A cikin abubuwan harda awara da idan an soya shi ake haɗa sauce a zuba a ciki a gwamutsa.

Ga su masa, zoɓo, kunun aya da na gyaɗa, dambu, tuwon shikafa miyan kuka ko kuɓewa, biski da sauran abinci masu daɗi, duk babu kayan haɗa su sai abincin kwali da kayan flour.

Ta ci Sa'an samun wake amma ɗan turmin dake kitchen ɗin zata iya riƙe shi a cikin tafin hannunta, sai ta fita ta ƙofar kitchen ta shiga bangaren sauran mutan gidan da nufin aro turmin da zata surfe waken a ciki, ta san ba zasu rasa ba.

Tsakar gidan yana nan kaman yanda yake, ta ɗaga idanunta daga kan interlocks ɗin da suka yi duhu kaman sun shekara goma sha ana taka su tsaban dauɗa.

Ƙofar farko shine Aunty Surayyah tace mata na kakan yarinyar da take raino ne, wato mahaifin Abdulhameed, na gefen shi kuma yana rufe don haka ta wuce wanda ke kallon na farkon.

Sallama tayi ba'a amsa ba, kuma tana jin motsi da ƙaran TV don haka ta sake yin wani sallaman.

“Waye wai?” Wata siriryar murya ta fito daga cikin ɗakin.

“Nanny ɗin Ikram ne” Ilham ta bata amsar da zata iya ganewa.

Tana tsaye tana jiran a mata izini ta shigo ko ta faɗi abinda ya kawota sai ganin budurwar tayi ta fito kaman an wurgo ta, da Ilham bata yi saurin yin baya ba ma gware zasu yi.

Yanda take ƙare ma Ilham kallo daga bandejin fuskarta har ƙafa haka itama take ƙare mata.
Ba fara bace amma bata da duhu sosai, wankan tarwaɗa ce irin Abdulhameed, ya dai fita hanci, cikan gashin gira da na ido da tsawon fuska saboda dogo ne sosai, dogo irin wanda basu da yawa a cikin dogaye, amma sauran kamanninta duk irin nashi ne.

Sai da ta gama ƙare mata kallo itama kafin tace “yaya aka yi?”

A cikin ƙannenta Ilham ta fara tunanin wanda zai yi Sa'a da ƴammatan, idan kuma ta canka daidai toh Islam ne, ƙanwarta na uku.

Ilham tace “aron turmi nake son a bani dan Allah”

Ta harɗe hannunta a kirji “Turmi? Me zaki yi da shi”

Koda ace ma wani taji Islam tana yin magana da wannan tone ɗin tabbas sai ta gurje mata baki, amma wannan ba Islam bace, nima take yi a ƙarƙashin ɗan uwan su.

“Surfen wake zan yi”

“Ku baku da turmin ne a…”

“Zakiyya!!” Matar da ta fito daga cikin ɗakin tana ɗaura ɗankwali ta tsawatar mata.

Saida ta ƙulle ɗankwalin a kanta ya zauna sannan ta nuna Zakiyyan da yatsa. “Mun samu lafiya na kwana biyu kina niman sake rakito mana masifa ko?”

Ta juya ta dubi Ilham “malama ga kitchen ɗin can ki shiga ki ɗauki Abinda kike so. Daga yanzu kina wucewa kan ki tsaye ba sai kin zo mana nan ba” ta ja hannun ƴammatan suka koma ciki.

Taɓe baki Ilham tayi ta ɗauki hanyar kitchen ɗin, ko sati bata cika a gidan ba amma duk wanda ta taɓa haɗuwa da su sai sun nuna mata halinsu.

Saida ta ratsa tsakanin kwanukan wanke-wanke dake baje a tsakar wurin ga kwando a gefe ba'a tara a ciki ba, shima turmin saida ta duba ciki ta ga da sauran kayan miyan da aka daka ba'a kwashe ba, amma tsami yake yi. Ta samu plate ta juye musu a haka, ta ɗauki turmin da taɓaryar shi ta koma wurin aikinta.

Yau ma da ita aka je ɗauko kiki daga makaranta. Kuma a yau ne ta fara sanin yarinyar magananniya ce gashi bata damuwa ko babu mai kulata haka take biya karatun da aka musu a makaranta da waƙe-waƙe tiryan-tiryan, idan ta tsaya haɗiye yawun bakinta kafin ta ɗora sai ta tambaye su daddynta su kaita wurin shi.

Da suka yi parking Ilham tayi sannu ma driver, ta fita ta buɗe ma Kiki ƙofa ta cire mata seatbelt sannan tace ta fito su shiga ciki.

Maƙe kafaɗa tayi “Ni ki ɗauke ni”

Ita kuwa bata ga dalili ba da zata yi ta dakon jibgegiyar yarinya irin wannan da lafiyanta.

“Kin ga ina da ciwo Kiki, ba zan iya ɗaukan ki ba”

“Toh a ina kika ji ciwon?”

“A hanya”

“Da me kika ji?”

“Faɗuwa nayi”

“Toh yaushe zaki warke ki ɗauke ni?”

Saida ta rufe idonta ta ja dogon numfashi ta furzar sannan ta buɗe su ta sake kallon yarinyar.

Ɗan ƙaramin fuskarta abin sha'awa amma tana da yaƙinin da mahaifiyarta take kama ko da bata taɓa ganinta ba. Don bayan yalwar gashin ido da na gira sai dogon hanci babu wani abinda ta ɗauko a fuskar Abdulhameed ga farinta sosai har tana yellow-yellow.

“Nima ban sani ba kiki, mu je in baki juice mai daɗi a ciki”

Sai gashi ta sauƙo daga cikin motar ta kama hannun Ilham suna tafiya, bata bari sun shiga ba ta sake ce mata “kiyi addu'a”

Ta yamutsa fuska kaman yanda tayi da safe “Ke ni fah ban iya ba”

“Sunana ba ke ba! Mimi zaki ce”

Sai ta turo baki. “Ni toh ban iya ba”

Kice “bismillahi..”

Tayi mata shiru.

“Zan shanye juice ɗina ni kaɗai idan baki faɗa ba”

“Toh bismillahi” muryarta ta fito da alaman tana shirin kuka.

Ta so ta rabu da tarbiyyan Kiki tayi abinda aka sakata kawai amma ba zata iya ba saboda itama uwa ce, ta haifa, kuma ba zata so a bayanta a bar ɗanta da halinshi ba. Idan yayi laifi zata so a samu mai tsawatar mishi, idan bai san abu ba a koya mishi, idan yayi kuskure ayi mishi gyara. Amma tana tsoron faɗan Abdulhameed da fushin sa, bata son abubuwa marasa daɗi suyi ta haɗa su har ya ƙare ya sallameta.

“Walajna” ta ɗora tana kawar da tunanin a ranta tunda da kyakkyawar niyya zata yi.

Kiki ta maimaita.

Sai tace “kiyi ta maimaitawa zuwa gobe idan kin iya zan baki abun daɗi”

“Menene abun daɗin toh?”

“Sweet” ta bata amsa, tunda shine abinda zata iya siya.

Ta miƙo mata ƙaramar yatsanta “promise?”

Saida Ilham tayi murmushi sannan ta maƙala nata ƙaramin yatsan a jikin na yarinyar tana maimaita Kalmar “promise”

Alalen laida da tayi ta gutsutstsura mata ta saka mata sauce ɗin hanta da ta haɗa tare da shi sannan ta zuba mata juice ɗin Cucumber da tayi.

Har ɗan ƙaramin gyatsa kiki tayi lokacin da ta gama cinyewa, Ilham tayi murmushi “kice Alhamdulillah”

Shi kam bata yi musu ba ta faɗa.

Ilham ta sake maimaita mata addu'an shigowa gida har saida ta riƙe kusan rabi, ta taya ta tayi assignment ɗin da aka basu a makaranta kafin ta tashi ta ɗaura sanwan abincin dare tana haɗawa da alwalan la'asar.

“Kiki zo muyi Sallah” tace lokacin da ta dawo parlourn.

“Ina kallo ne” ta bata amsa idanunta kafe a kan cartoon ɗin da ake nunawa a TV.

Sai ta ƙarasa ta kashe TV ɗin, ai kuwa ta zube a wurin kaman gwate tana birgima, saida Ilham ta haƙura ta kunna mata TV ɗin kafin ta miƙe ta share hawayenta ta koma ta zauna ta cigaba da kallonta.

Lokacin da Abdulhameed ya dawo har ta kammala abincin dare, alalen da tayi kuma ta ɗibawa Aunty Surayyah a wani food flask.

Saida ta fara miƙa ma Aunty Surayyah abincin, ta mayar da turmin da ta wanke shi tass kitchen ɗin da yake cikin yanayin da ta barshi da safe, sannan ta ɗauki Abinda ya rage ta tafi da shi bayan tayi mishi sallama kuma ya bata ɗaya daga laidojin da ya shigo da su tayi godiya.

Saida ta isa asibiti ne suke duba abinda ke cikin laidan ita da Ihsan saboda a hanya kayan hannunta sun yi yawa.

Kayan marmari ne, kama daga Apples jajaye da koraye, transparent takeaway na inabi da na strawberry sai abarba da ayaba.

Ihsan harda takawa saboda murna, suka ci suka sha suka sammar wa maƙwafta, sun ma manta da shirgin Hashim har saida ya kira wayan Ilham bayan Isha yana tambayanta yaushe zata dawo yana jin yunwa.

…..
ABDULHAMEED

Ya daɗe yana tunanin abinda zai yi mata ba tare da ya ƙetare iyaka ba, yana da kuɗi mai yawa amma bayi da hujjan bawa Ilham kuɗi haka kawai tana matar wani, kada yaje garin taimako ya saka ta a masifa.

Suna hanyar dawowa daga Gidan Excellency ne bayan ya je ya saka hannu a kan takardar sabon yarjejeniyan su, idanun shi a kan hanya zuciyar shi kuwa ta nisa kan maganar da suka yi da lawyern Excellency a kan Kiki lokacin da ya hango masu fruits a gefen hanya.

Har sun wuce yace ma driver yayi reverse, ya fita da kan shi ya zaɓi abinda yake so a bashi, saida ya karɓi laidan farko yace a sake saka wani irin shi don kada Ilham tayi tunanin na musamman ya siya mata, kuma ya sanma Kiki zata ci wasu abun a ciki.

Card ɗin shi ya miƙa musu suka cire kuɗin su bai tsaya duba ko nawa bane ya karɓa ya tafi, kuma ya ji daɗin da ta karɓa tayi godiya duk da fuskarta bai gwada wani abu ba yana da tabbacin dai bata yi misunderstanding good intentions ɗinsa ba.

Wanka ya fara yi ganin yanda Kiki take walwala ya san babu yunwa a cikinta, ya fito sanye da gajeren wando brown da farin T shirt, ya ƙarasa jikin dining da yake hango kulolin abinci har guda huɗu a kai da jug ɗin da raɓa ya lulluɓe jikin shi saboda sanyin abinda yake ciki, dan saida ta saka juice ɗin yayi ƙanƙara sannan ta fito da shi kafin ya zo sha ya narke.

Ya buɗe food flask ɗin farko suka yi ido huɗu da alale. Shi kam ya saba ci a wurin Nne don yana daga cikin favourite foods ɗinta, amma shikafan da Ilham ta niƙa a Grinder ta turara shi kaman biski ba don rayuwar da yayi a gidan mahaifinsa kafin tafiyar shi Japan ba da bai san menene shi ba, amma ya sha cin na garin masara ko miya babu.

Haka ya raba plate ɗinsa gida biyu ya zuba kowanne a gefe ya fara ci, fuskar shi da murmushin jin daɗi don bai yi tsammanin zai samu damar cin wannan girkin a yau ba, amma gashi har kala biyu.

Kiki ma ta sake cin abincin kafin su kwanta, yace ta kawo assignment ɗinta suyi sai tace sun yi da Ilham, cikin jin daɗi ya miƙe ya juye abinda ya rage ya saka a fridge kamar kullum ya wanke komai tass saboda bai yi imani da kwanan kwanuka a cikin sink ɗinsa ba.

….

Jollof ɗin macaroni na manja tayi ma Hashim da kayan abincin da aka kawo mata daga gida, ya dai siyo kayan miya harda kifi. Bata kula abincin ba domin a ƙoshe take, ta shiga banɗaki ta watsa ruwan ɗumi a jikinta don ta gaji sosai sannan ta samu wuri ta kwanta.

Bata san ƙarfe nawa bane lokacin da taji ana taɓa ta, ta dai san barcinta yayi nauyi domin da ƙyar ta iya buɗe idanunta a kan Hashim dake tsaye a kanta daga shi sai boxers.

“Tashi mana” ya sake ranƙwafowa ya bubbuga kafaɗanta.

Sai ta zuba masa idanun da suka gagara buɗe girman su gaba ɗaya amma mamakin dake cikin su ya fito.

Ta buɗe baki da ƙyar tace “Haba kai kuwa!”

Shima saida ya ji ɗacin dake cikin muryarta amma bai san yaya aka yi ba yau yake jin yana buƙatar ta bayan tsawon lokacin da ya ɗauka bai nimeta ba, fiye da watanni huɗu.

Kaman dai akwai wani abinda ya canza a jikinta, kaman ita ɗince ta canza masa yake mata kallon sabuwar Ilham ba wanda ya gama kashe kishirwar shi ya watsar da shirginta ba.

Idan ba ta ɓata lissafi ba ma ovulation take yi, kuma rabonta da pills ɗin planning ya jima tunda babu abinda yake haɗa su, amma yanzu idan ta zaɓi ta sauƙe hakkin da Allah ya ɗora a wuyanta ta sake samun ciki suka haifi wani SS ɗin fa yaya zata yi?.

Ta yiwa kanta adalci bayan shi ko ita abinda zata haifa da zai ƙare a wahale kaman Muftee?
.
.
.
6:30am.

Yau jikinta a mace take jinsa gaba ɗaya, bata ƙi ta kwanta ta sake hutawa ba, da ace babu wani abu mai muhimmanci dake jiranta, da barci zata ƙara har sai ta ji ya isheta kuzarinta ya dawo.

Amma haka tayi abinda zata iya a gidan, ta haɗa abun karyawa ta ajiyewa Hashim dake barci har yanzu, sauran macaronin jiya kuwa ya rufe shi a kwano zafi ya saka ya buga sai zubarwa tayi ta wanke coolern ta saka abincin asibiti a ciki ta tafi da shi.

Yau bata ga Abdulhameed ba har saida ta gama shirya Ikram ta kawota dining sai gashi a zaune cikin irin shigan da ya saba fita da su, amma yau rigan shi kalan Olive green ne da grey ɗin wando.

Ta gaida shi ya amsa sannan ta tafi ta basu wuri su yi breakfast.

“Kiki baki biya mun karatun da nayi miki ba jiya” cewar Ilham lokacin da suka zo fita daga gidan.

Ta kwaɓe fuska “Toh ai baki bani sweet ɗin bane uhmm…”

“Mimi” Ilham ta ƙarasa mata.

“Ai baki bani sweet ɗin bane Mimi”

“sai kin fara biya mun kafin in baki” ta nuna mata laidan minti mai tsinke da ta siyo mata a shagon asibiti kafin ta zo.
“Idan kuma baki yi ba shikkenan sai in shanye kaya na”

Sai gashi ta karanto addu'an tiryan-tiryan sai gyaran da ba za'a rasa ba, Ilham ta rage tsayinta a gabanta tana murmushi ta miƙa mata sweet ɗin. “Masha Allah kan ki yana ja my dear”

Kiki ta karɓi laidan mintin tana washe baki.

“Mai kika ce?” ta tambaya jin ta karɓa tayi shiru.

Kiki ta kalleta da iya gaskiyarta tace. “Babu”

Ilham ta girgiza kai “Thank you zaki ce”

Gilashin motan a rufe suke duka, amma kaman a cikin kan shi yake jin maganar da Ilham take yi da Kiki saboda yana iya kallon motsin leɓenta daga inda yake zaune.

Lokaci yana tafiya, wataƙil Ilham ta manta da haka ne. Amma bai yi interrupting ɗinsu ba har saida Ilham ta gyara ma Kiki kusren da take yi sannan ta ƙarasa mata addu'an shiga gida da alƙawarin zata ƙara mata wani sweet ɗin idan ta iya duka.

Abinda yake so kenan, wannan part ɗin da ba zai iya cikewa Kiki ba ya samu wanda zata kamanta hakan.

Ta shafa kan yarinyar tana saka mata albarka, sai a sannan ya bada driver daman yayi musu horn Kiki ta zo su tafi.


`````````````
Seemahwrites ✨

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
Chapter 22 · 0% Book details