← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 28 OF 30

Chapter 28

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

Wattpad and Arewapen @Seemahwrites

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


28…. Saitin kayan shafa shine kusan abinda ya ragewa Hashim kawai a haɗa lefen Khausar saboda ya daɗe da fara shiri, a ranar da suka dawo kaduna da zama suka sauƙa a gidan baffa Rabe ya ɗora idanun shi a kanta ya ji a ran shi ya samu mata, ganin yanda ta girma ta cicciko.

Da inner wears da night gowns ya fara haɗa kayan, a wurin wata abokiyar aikin shi da suka yi saving numbern juna tana saka irin kayayyakin a status ɗinta, ya fara siya da ɗaɗɗaya yana ajiyewa ganin yanda Ilham ta lalace a yanzu albarkatunta duk sun lamushe, ko ta saka ba zata mishi kyau ba balle ta dauki hankalin shi, gwamma ya samu sabon jini yanda zai more kuɗinsa.

Mahaifinsa Ibrahim Baniza da ƙanin shi Umar Baniza sune suka shige masa gaba a kan zancen auren Khausar kuma Rabe ya basu domin idan ya hana zasu iya cewa don shi da su ba ƴan ɗaki ɗaya bane ba.

Aka saka aure watanni huɗu, kuma hakan yayi ma Hashim, yanda zai samu isasshen lokaci ya ƙarasa shiri a tsanake.

A lokacin da yake shirin sanarwa sauran dangi kwatsam cutar sickler ɗin Muftee ya motsa, yanzu kusan watanni biyu kenan suna kwance da Ilham a asibiti, Shiyasa zancen auren ya koma sai wanda suka ji kawai, gashi sun haɗa kai wurin ɓoyewa yaran marigayi Usman Jen kada suce ba'a kyauta ma ƴar uwar su ba.

Shi a karan kan shi ma zai fi so ya ba ma Ilham mamaki da auren, ya ƙara gwada mata iyakar ta.

Sai gashi kafin ya kai ga ida nufinsa ita ta shayar da shi mamakin da saida ya bugar da shi, domin haka ya bi motar nan da kallo bakinsa a buɗe cikin tsananin kaɗuwa.

Ilham dai da yakewa kallon banza ashe ta fi shi sanin gari, nata iskancin ba da irin shi take yi ba sai masu manyan motoci.

Sun yi ƙoƙarin bin bayan su shi da abokinsa amma inaa, sun daɗe da yi musu nisa.

Haka ya haƙura suka ƙarasa inda suka nufa, bai shirya asarar kuɗin man da suka ƙona ba.

Yana ganin gate ɗin gidan su yarinyar da ya je wurinta ya fara hamdala a cikin zuciyar shi, kakan shi ta yanke saƙa.

Hudah ta fito cikin ƙwalliya ta burgewa, Hashim yana ayyana kuɗin leshin jikinta don ya kasa sakawa Khausar irin su saboda tsadan shi.

Ɓangaren Abdulhameed ma ta shigar da su, sanin ya fita kuma ba dawowar yanzu ba.

Ta shimfiɗa musu carpet a inuwa da ƙaryar daddyn su yana da baƙi a parlour ne, tayi nuni da part ɗin Abdulhameed dake a rufe.

Saida suka fara gaisawa ta shiga jere musu kalolin abincin da ita da mahaifiyarta suke ta kiciniyar haɗawa tun farar safiya.
Hudah ta faɗa mata akwai maiƙo a jikin Hashim daga gani, shiyasa zasu yi masa tarban bajinta.

Ta basu wuri suka ci suka gyatse sannan ta dawo suka taɓa hira sai burga yake mata ita kuwa tana ta murmushin jin daɗin ta samu miji. Saida taga an yi azahar har biyu tayi basu tashi tafiya ba tace masa zata koma ciki kanta yana ciwo, kafin Abdulhameed, Aunty Surayyah da ma sauran wa'inda suka tafi talent show ɗin Kiki su dawo su riske su.

Haka Hashim ya miƙe ya kaɗe rigarsa, ba don kada ajinsa ya zube ba da yace ta saka mishi sauran abincin a takeaway ya tafi da shi, amma ko sile biyar bai ajiye mata ba suka juya suka tafi.

Ayyanawa yake a ran shi Idan ya samu ya auri Khausar ya riƙe wannan ƴar masu kuɗin a hannunsa shikkenan ya huta da takaicin duniya.

Ilham ce kawai zata zamo masa cikas, kuma a yanzu ya san ta yanda zai yi ainihin koya mata hankali.

Daman tunanin inda zai ajiye Khausar yake ta yi, gidajen haya sun yi mahaukacin tsada yanzu, idan ya buga mata red card shikkenan babban matsalar shi ta kau.

A yammacin ranan ya haɗa kayan shi cikin jaka, Ya kira office ɗinsu ya ɗauki excuse da ƙaryan Mahaifiyarsa ce babu lafiya zai je dubota a garinsu.

Tattaki zai yi har Gidan Baniza ya samu magabatan su tunda yanzu yana da hujja ƙwaƙƙwara na rabuwa da Ilham ba tare da wani ya ga baƙinsa ba.

…..

Kai tsaye asibiti Aliyyu ya nufa da isowar shi Kaduna, ɓacin ran da yazo da shi kuma ba kaɗan bane, har ƙananan ƙannen shi da mahaifinsu ya mutu ya bari bayi tausayin su kaman yanda yake tausayin Ilham, saboda yanayinta ga kuma irin abokin rayuwar da Allah ya haɗa ta dashi.

Ashe ba mutunci gareta ba.

Idan ya tabbata tana abubuwan da Hashim ya lissafo yau sai yayi mata dukan mutuwa saidai su koma da gawarta kano.

Ran shi ya ƙara ɓaci da ya samu babu ita a jikin yaron da aka sakawa bututun numfashi, ya tasa Ihsan a gaba ta kawo shi gidan da aka ce tana aiki, tun da koda bata taɓa zuwa ba ya san Ilham zata kwatanta mata unguwan, idan ma suka je basu gane gidan ba tambaya zasu yi ta yi har sai sun samu, ya shiga yaci ubanta a can.

Hangota da suka yi tsaye a gaban gate ɗin wani gida yasa Aliyyu ya dakatar da mai napep ɗin da ya kawo su a gefen wata bishiyar neem, suka fito ya biya shi kuɗin shi ya tsaya ya karyi reshen bishiyar ya figeta, Ihsan tana ta kuka tana bashi haƙuri ya shareta ya nufi Ilham gadan-gadan.

Ba zai yi mata magana ba saidai ta ji tsumagiya a gadon bayanta, amma kafin ya ƙarasa gareta yaga tayi luuu zata fadi, ya jefar da reshen bishiyan da ɗan iskan gudu yayi kanta.


Sai dai ya makara, ta rigada ta kai ƙasa.

….

Har bayan Isha Abdulhameed da Aunty Surayyah suna yawon neman Kiki, sun je har school ɗin su da A&I koda ace wasu sun tsinceta tayi musu kwatancen can sun kaita, haka suka gama zagawa a banza duk ya rasa mafita, gaba ɗaya idanun shi sun gama kaɗawa sai zafin rai yake tayi, nutsuwar da ya samu na yin Sallah ma ba mai yawa bane.

Aunty Surayyah da Mukarram sun tafi kai cigiya masallatai da gidan Radio kuma har an fara watsa hotunan Kiki a social media, shi kuma yana police station zaune a kujeran gaban DPO dake ɗaukan bayanan da zasu yi amfani dashi wurin nemota da kan shi.

Ya tambayi Abdulhameed ko akwai mutanen da yake tunanin zasu iya ɗaukar ta ba tare da sanin shi ba, sai ya fara tunanin shima wa yake dashi a yanzu balle Ikram? Tun da Nne ta rasu ƴan uwanta suka juya mishi baya, tun da ya zama nakasasshe mutane da yawa suka cire shi a cikin lissafin su, amma ita Ikram tun farkon rayuwarta bata da kowa, da tana da shi da ba'a damƙa mishi ita tana cikin tsumma ba tare da damuwa da rayuwa ko mutuwarta ba, to waye zai ɗauke mishi ita yanzu idan ba mai fatan raba shi da sauran farin cikin shi ba?.

Ya tsayar da ƙafar shi na dama da yake girgizawa yayinda ya zurfafa tunani, yace “Babu, amma akwai wanda I'm sure tana da masaniyar inda take, saboda ita ce last person da na bari a tare da ita, maybe idan ku ne kuka tambaye ta zata faɗa muku inda yarinyata take.”

Iya lokacin da zai iya ɗiba ma Ilham ya cika, idan kuwa yau ba zai koma gida tare da Kiki ba toh kwanciyar hankalin da ba zai samu ba itama sai ya haramceta.

Cikin zaƙuwa DPO yace “Toh me muke jira? Faɗa mana wacece a je a kawota sai ta bamu amsar tambayoyin mu”
Aka kawota suka lagabtar da ita tuni zata warware musu komai, Idan hakane solving case ɗin zai zo musu da sauƙi, kuma zai samu alkhairi sosai a wurin Excellency tunda shine ya ɗaura shi a kai ya jaddada masa muhimmancin Abdulhameed a gare shi kada ayi wasa da lamarinsa.

Abdulhameed ya sauƙe gajeriyar numfashi tunawa da kallon da yayi ma Ilham ɗazu. Ya ga damuwa matuƙa a cikin idanunta, ga yanda ta dinga zubda ƙolla.

Ya ciro wayan shi ya kunna, ya dubo text message ɗin su da Aunty Surayyah na wata ɗaya da ya wuce, kana ya miƙa ma DPO wayan ya saka hannu ya karɓa.

“Nanny ɗinta ce, ga Address ɗinta”

DPO ya jinjina kai yana mayar masa da wayan kafin ya bada umarnin a je a taho da Ilham yanzu-yanzu.

Abdulhameed ya cigaba da zama a ofishin na kusan mintuna talatin, babu inda yayi saura da zai je neman Kiki shiyasa kawai ya zauna ɗin, kaman yace a fasa ɗauko Ilham a motar ƴan sanda ya tura a ɗaukota a mutunce idan ba zata yi gardama ba, amma idan ya bita a lalama ba zata faɗi inda Kiki take ba.

Bayi so ya fara saka tunanin haɗa baki aka yi da ita aka yi garkuwa da Kiki a cikin kan shi, sai dai ya karanta labarin faruwar irin haka sau da dama, ya gagara yaƙi da shaiɗanin da yake kissima masa yiwuwar hakan.

Ƙarfe 9 dai-dai wayar shi tayi vibration ɗin shigowar saƙo.

Ganin numbern ta ya saka gaban shi faɗuwa matuƙa, shin cireta a cikin lissafin shi da yayi har yayi tsananin da bai yi tunanin zata iya ɗauke Kiki ba duk tsawon lokacin nan?.

Ta faɗa masa tana cikin Kaduna.
Ta faɗa masa zata zo ta ganta.
Amma bai zarge ta ba sai Ilham.

Cikin sanyin jiki ya buɗe saƙonta, ya ci karo da abinda bai bashi mamaki ba, amma ya kai maƙura wurin ɓata mishi rai.

‘ta ƙi yin barci tana ta kuka, Muna gida na dake Millenium City.’

Sai a lokacin ya ga saƙon da ta turo mishi tun ƙarfe uku na rana.

‘Na tafi da baby zata kwana mun, gobe da sassafe kafin lokacin school zan dawo da ita.’

Ya rufe idanun shi ya buɗe a kan message ɗin.

Ilham tayi ƙoƙarin yi masa bayani bai saurareta ba. Kaman yanda shima ba'a saurare shi ba lokacin da yaje da Kiki gidan su tana da kwana uku kacal a duniya.
Bai duba rashin lafiyar ɗanta yayi mata uzuri an bi komai a hankali ba, kaman yanda shima ba'a duba nakasar shi an sassauta masa ba.

Bai duba yanda take kaffa-kaffa da kanta da ma hidimar su ba ya tura mata ƴan sanda su je su zubar mata da mutunci.

Lallai ya kwafsa. He messed up big time!.

Ran Abdulhameed ya gama ɓaci yayi baƙi.

Ya miƙe tsaye yana huci, jijiyoyin jikinsa sun tashi, a daƙile yacewa DPO da ya ɗago yana kallon shi.
“An sameta. Ilham bata da laifi, a rabu da ita”

Ya juya ya fita, kiran da DPO yake masa da tambayar inda take a banza tun da bai ji ba.

Minti 18 tsakani driver ɗin shi yayi horn a gaban gidan da suka iso bisa kwatancen Abdulhameed.

Bai tsaya an buɗe musu ƙaton gate ɗin ba ya ɓalle marfin motan ya fita, ya shige ciki ta ƙofar dake gefe kai tsaye.

Sai yaga gidan ya ƙara masa girma da isa inda take tsaye tana jiran shi, sanye da hijabi light brown iya guiwarta, daga ƙasa kuma wandon kayan barci ne mai faɗi ya sauƙa har ƙasa, kafafunta a cikin farin crocs. Ita shirin barci take da shi kenan bayan ta gama ɗaga masa hankali?.

Fuska a tamke yake takawa inda take idanun shi a kanta.

“Tana ina?!” Ya tambaya cikin hargagi.

Da ace ya iya ɗaga hannu ma mutane zai iya kifa mata mari saboda yanda ran shi yake tafasa.

Ta dubi security guards dake kai kawo a harabar gidan, Ameer ne ya ajiye su don kare lafiyanta amma ta san akwai masu leƙen asiri ma babanta a cikin su.

“Mu shiga ciki” tace tare da juyawa sanin zai biyo bayanta tunda linzamin shi yana hannunta a yanzu.

Saida suka shiga cikin makeken parlorn da ya jinjina ma girma da tsaruwan shi a baya kafin ya ja ya tsaya.

“Mardiyya! Ina yarinyata?”

Ta dakata da tafiya, ta juyo ta dube shi.

“Tea tace zata sha, shine na haɗa mata a upstairs, tana gama sha barci ya ɗauketa, da ban ɗago ka da tsohon dare ba”

Murmushi yayi da bayi da haɗi da nishaɗi, “Are You kidding me? Ki ɗauke mun yarinya kizo kina faɗa mun maganar banza? I was searching all over Kaduna for her!..”

Ganin zai tara mutane ta katse shi da faɗin “I Texted you Abdulhameed! Na faɗa maka na ɗauke ta, banda ma ni ɗin ce da cigiyar gaskiya zaka yi saboda a waje na sameta tana kuka. And na dawo kaduna ne musamman saboda ku, saboda na sanar da kai a kan shirin su na karɓanta.”

“What?” Ya tambaya muryar shi yana sauƙowa.

Gyaɗa mishi kai tayi “Yes Abdulhameed, sun damƙa maka ita ne saboda gudun ɓacin sunan su a siyasa, yanzu kuma lokacin zaɓe ya sake ƙaratowa sun fahimci zata musu amfani tunda kaima ka fara yi ma wanda zai fito takaran gwamnan Kd, zasu karɓeta Abdulhameed very soon”

Kaman wanda aka watsa masa ruwan ƙanƙara haka jikinsa yayi sanyi.

“Bata cika shekara huɗu a duniya ba Mardiyya”

Lokaci ɗaya Idanunta suka tara ƙwalla
“Ba a kanta suka fara sadaukarwa ba ka sani. Da ni suka fara.”

Ya shafa kanshi da yanzu bayi tara masa gashi yana furzar da numfashi.

“I'll not allow it. Never. Ki je ki ɗauko mun ita mu tafi”

Bata musa ba ta juya zuwa matakalan da zai kaita sama, ya bi bayanta da kallo yana tunasar da zuciyar shi wacece Mardiyya.

Amma ko sunanta ba zai taɓa zuwa kan shi ba tare da ya fara Tuna Ikram ba.

Ikram Aminu Yashi.


JAPAN 2017


Ganin yana niman cim mata yasa ta tsaya da gudun da take falfalawa tayi surrender. Saidai duk yanda yayi ƙoƙarin cin burki lokaci guda abu yaci tura saida yayi ciki da ita dukkan su biyu suka zube a ƙasa warwas gefen jikin shi a kan nata.

Ƴar ƙara ta saki na bugewar da tayi, ga nauyin shi ya danneta, amma Abdulhameed bai ji ba saida ta taƙarƙare ta ture shi daga jikinta tana kwaɓe fuska. Ya ɗago guiwar hannun shi da ya kuje a Yashin dake gefen Filin yana nuna mata ganin ita ta takalo shi kuma wai ranta ya ɓaci.

Ta turo baki tana watsa mishi harara ta saka hannu ta gyara zaman farin hulan kanta, ta rufe gashin dake kwance luff a goshinta sannan ta yunƙura zata tashi ta bar shi a wurin, yayi saurin jawo hannunta ta dawo ta zauna daɓas.

“What's your name?” Ya tambaya.

Tafin hannunta ta juya mishi alaman mai yake faɗa? Ita ba iya reading lips take ba kuma bata ji kwata-kwata.

Ya nuna ƙirjinta shima yana juya mata nashi tafin hannun da ƙura ya gama buɗe shi.

Idanu ta waro ta saka hannayenta ta kare ƙirjinta tana masa wani irin kallo.
Shi hankalin shi ma bayi kan abubuwanta da basu kai sun kawo ba banda yanzu da ta saka ya ankara.

Tsaki ya ja ya saka yatsar shi manuniya ya rubuta mata tambayar a ƙasa.

Saida ta karanta ta saki ƙirjinta sannan ta saka hannu ta share tambayar itama ta saka yatsarta ta Rubuta mishi.

Ikram Aminu Yashi.

Ya ɗago ya dubeta lokacin itama shi take kallo.

Ya gwada ta da yatsa yana faɗin “Ki kiyaye ni.”

Sai ta sake masa murmushi.


`````````````
Seemahwrites ✨

ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites

*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*

*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*

Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Sai a turo shaidan biya ta 09039206763
Chapter 28 · 0% Book details