Chapter 18
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)
Wattpad and Arewapen @Seemahwrites
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
18… Idanun shi ita suke kallo, tana zaune daga gefen shi a gidan baya, a cikin seat ɗin da ya katange ta da seatbelt, Amma zuciyar shi ta koma nazarin abinda ya faru ɗazu a tsakaninta da Ilham.
Kaman yanda yace, har cikin zuciyar shi ya yarda Kiki ba zata yi ma Ilham ƙarya ba tunda ya fi kowa saninta a duniyar nan, tun tana cikin tsumma yake kula da ita har zuwa yanzu.
Amma sai yake jin kaman wani dunƙulen abu ya tsaya a ƙirjin shi tunda Ilham ta buɗe baki ta bashi haƙurin nan, kuma duk yanda ya kai hannun shi ƙirjin ya shafa inda yake jin abun ya gagara bajewa.
“Kiki”
Ta buɗe idanunta da suka fara lumshewa a kan shi, kukan banzan da ta gama sha ne yasa taji jikinta yayi laƙwas.
Sake tambayarta a kan taɓa mata ciwon da tace Ilham tayi yaso yayi, amma da wa’innan manyan fararen idanuwan suka shiga cikin nashi, sai yaji wannan shine mafi girman rashin adalcin da zai yi ma kanshi, idan har zai yarda da baƙuwa a cikin rayuwar su fiye da yarinyar da yasha kwana da yunwa saboda ita ta ƙoshi.
“Kada kiyi barci school zaki je”
Muryar shi tana sauƙa ne ko ta tashi da control ɗin emotions ɗinsa. Kaman yanda ji yake taimakawa yanayin fitar sauti daga bakin mutum mai cikakkiyar halitta shi zuciyar shi ne take wannan aikin a maimakon kunnuwan da suka mutu suka barshi a tsaye. Shiyasa idan ranshi ya ɓaci sai muryar ta fito da ƙarfin da ya wuce ƙima, haka ma idan yana cikin nutsuwarsa sai muryar ta fito da taushi kaman yanda yayi magana da Kiki a yanzu.
Sai ta kwaɓe fuska ta cigaba da ƙananan kuka. Da ya barta ta fara baccin ta san saidai ta buɗe ido ta ganta a kujeran office ɗin shi ya saka an fasa zuwa makarantar sun tafi tare.
Fitowa yayi riƙe da pink schoolbag ɗinta bayan sun yi parking a gate ɗin makarantar, ya zago ta bangaren ta ya buɗe mata ƙofa, ya ranƙwafa ya cire mata seatbelt ɗin kana ya miƙa mata hannu, ta maƙe kafaɗa tana narai-narai da idanu.
“Zan dawo miki da ice cream. I promise” yace yana ƙara miƙa mata hannun shi.
Sai yaga ta kama shi da hannunta na dama ta fito a cikin motar.
Kanshi ya sake kullewa. Hannu mai ciwon da ta kawo ƙaran Ilham ta fama mata kenan, wanda ta samu targaɗe a jiki.
Ya rage tsayinsa ta hanyar durƙusawa a gabanta yana kallonta, amma ya kasa cewa komai, saboda fuskar mahaifiyarta yake gani a duk lokacin da ya kalleta, macen da a duk lokacin da ta aikata ba daidai ba a wurin shi take samun mafaka koda ya san da abinda ta aikata.
Jakan ya rataya mata a bayanta ya gyara mata zaman hearing aid ɗinta sannan ya shafa gashin kanta da Ilham ta tufke mata shi.
Yana kallo har ta wuce cikin gate ɗin tare da sauran ƴan makaranta sannan ya koma cikin motar drivern shi ya ja suka ɗauki hanyar A&I.
9 ta gota da ƴan mintuna lokacin da ya shiga cikin office ɗinsa. Ga mutanen da suke zaune a waje suna jiran shi, ga tarin takardu a kan teburin shi harda na aikin da suka fara last week da kuma wanda ke zuwa a gaba.
Nutsuwan da ya samu ɗaya, bayi bukatar nan da wasu awanni ya sake fita dauko Kiki daga makaranta tunda tana da Nanny yanzu, sannan makarantar tasu da nisa sosai saboda saida ya nemi inda ake bawa yara abinci mai kyau da inganci ya sakata tunda ba iya haɗa mata lunch box kullum zai yi ba.
…..
ILHAM
Jiya ta daɗe a asibiti suna hira da Ihsan, tana bata labarin irin abubuwan da ta gani a gidan da take aiki har suka gangaro kan abinci, tana mafarkin itama ace wata rana gidanta ne ya wadata da kayan abinci da abubuwan sarrafa shi irin haka, a ce komai tana da shi a cikin store ko a kitchen cabinet ko a fridge, ita da yaronta su ci abinda suka so a lokacin da suka so kuma mai daɗi mai ƙara Lafiya.
“Idan kuma rabona na gidan duniya bai kai haka ba ina miki fatan Allah yasa ki samu filiyan. Ko ba miji mai tarin dukiya ba Allah ya baki miji mai zuciya wanda ya fi ƙarfin Abinda za'a ci a gidansa”
Abinda tace ma Ihsan kenan jiya.
“Shine kuma kike mun fatan Auren Sageer Umar Baniza a hakan?” Ihsan ta kalleta a kaikaice.
Ilham tayi murmushi “Ai ƴan familyn Banizan ba taruwa suka yi suka zama ɗaya ba, tunda mahaifin mu ma mutum ne mai ƙoƙari, sai kiga shima ya riƙe mana ke da amana”
“Allah ya kiyaye wallahi” ta ja tsaki tana juyo ma Ilham fuskar wayanta dake kan wani shafin girki ta gwada mata wani fried spaghetti da meatballs.
“Gobe kiyi musu irin wannan abincin ki kawo mana sauran”
“AL Mayya’u” Ilham ta kai mata dukan wasa kafin ta karɓi wayan tana kallon yanda aka haɗa. Saida ta kalli video ɗin sau uku ta tabbatar ta haddace yanda aka haɗa da abubuwan da aka zuba sannan ta wuce na gaba, haka tayi ta kallon girke-girke, Idan lokacin Sallah yayi ta tashi tayi ta dawo ta cigaba da kallo har saida datan Ihsan ya ƙare ta haƙura.
Ta bata dubu biyu a cikin kuɗin da ya rage ta sayi Datan a ciki, tunda ga zaman wuri ɗaya sai ta ɗan samu na kashewa a hannunta sauran kuma zasu dinga amfani da shi wajen zirga-zirga.
Yau bayan su Abdulhameed sun fita sun bar mata gidan sai ta shiga gyara shi tana yin faɗa ma kanta a kan Kiki tunda gashi har an fara samun matsala a rana ta biyu, zata yi ƙoƙarin binta a yanda take a zauna lafiya, ba zata yi saken da zata rasa aikin da har ya fara rufa mata asiri ba.
Da ta gama ta dawo kitchen haɗa abincin rana kafin lokacin da aka faɗa mata zasu je ɗauko ta a makaranta yayi sai tayi karambanin haɗa spaghetti da meatballs ɗinnan, bayan ta gama ta yi juice ɗin kankana ta saka a fridge yayi sanyi sannan ta shirya ta samu driver a waje yana jiranta.
Gaban motan ta shiga, bayan ta gaida shi ta ja bakinta tayi shiru tana kallon hanya.
Yau a mahanga daban take kallon mutane, saboda bata cikin wa'inda ke tafe a kan sawayen su cikin zafin rana ga tarin damuwa, sai taga garin yayi mata daban, gashi tafiya kawai suke yi sumul ko ƙaran tafiyan motan bata ji sai sanyi da ƙamshi mai daɗi dake ratsa ta.
Ta ɓalle marfin motan ta fita ta ƙarasa wurin masu tsaron makarantar bayan sun isa,
“Sannun ku da aiki nazo ɗaukan Ikram Abdulhameed a Nursery One”
Saida ta jira a ƙofar wurin aka kawo mata Kiki wanda ta fito da murnanta a tunaninta daddynta ne yazo daukanta, amma ganin Ilham sai ta ɓata fuska kuma taƙi zuwa.
Da ƙyar drivern ya lallaɓata ya dauketa ya saka a bayan mota, bai manta kashedin Abdulhameed a kan saka mata seatbelt a koda yaushe ba kafin Ilham ta koma gaban motan suka dawo gida.
Ilham tana cire mata seatbelt ta bangaje ta tayi cikin gidan da gudu tana niman babanta, saida ta gama dubawa bata gan shi ba ta dawo wurin Ilham.
“Fitsari” tace tana rawan mazari.
Ilham ta riƙe hannunta zata kaita toilet ta tirje a wurin.
“Ni ki ɗauke ni”
Haka ta sunkuya ta ɗauketa har kofar banɗakin sannan ta ajiyeta a kan tayi addu'a ta shiga da kafar hagu sai kawai ta shige da gudunta bata yi addu'an ba ta ɗaga skirt ɗin uniform ɗinta ta zame farin leggings da pant dake ƙarƙashin sa tayi abinda yake gabanta tukunna tace Ilham tayi mata tsarki.
Haka da ta canza mata kaya ta zuba mata abinci zata bata a baki kaman yanda taga ake mata sai taƙi amsa, ta karɓi fork ɗin a hannunta na hagu tana ci tana zubarwa.
Ganin ba zata iya cigaba da shiru ba tace “Kiki ba kiyi bismillah ba”
Bakinta a cike da dunƙulen naman da ta tusa tace. “Bismillah. Ina daddy na?”
“anjima kaɗan zai dawo”
“Ni ki kaini wurin shi”
“Sai idan kin gama cin abinci” ta amsa ta tana tsince taliyan da take zubarwa kan table ɗin tana mayar mata cikin plate ɗinta.
Saida ta cinye abinda ke kan Plate ɗin tass tace a ƙara mata, kwatsam sai ga Abdulhameed ya faɗo cikin gidan babu notice, ko sallama bai yi musu ba, don yana so ne yaga yanda Ilham zata ke kula da kiki a bayan idon shi.
Ilham dake zaune a kan kujeran dining da yake gefen na Kiki sai ganin shi kawai tayi a kansu, bata ma ji lokacin da ya buɗe ƙofar shigowa ba. Tayi saurin miƙewa tsaye tana kallon shi, ta ma rasa me zata yi, Allah dai ya taimaketa da hijabi a jikinta sanin ba gidanta bane bata da hurumin cirewa.
Kalmar “sannu da dawowa” ta laluɓo a kan harshenta, sai ya gyaɗa mata kai fuskar shi a sake, babu wannan ɓacin ran da ya fita da shi da safe.
Kiki ta sauƙa daga kujeran murna duk ya cikata, zata yi kan shi da gudu Ilham tayi saurin ruƙota ta dawo da ita sannan ta zari tissue ta goge mata maiƙon bakinta kafin ta saketa ta ƙarasa gudun da ta fara ta rungume ƙafafun Abdulhameed.
Ajiye laidan hannun shi yayi a ƙasa ya ɗauketa. Ganin haka Ilham ta ɗauki hanyar komawa kitchen ta basu wuri, sai ya kirata.
“Ilham”
Ta tsaya cakk amma bata juyo ba. Muryar ta canza amma yanda yake kira iri ɗaya ne. Iri ɗaya da A Moher, anya ba shi bane wannan?.
Ya ƙara cewa “ki ɗauki ɗaya”
Da ta juyo sai taga laidan da ya shigo da shi yake gwada mata.
Ganin ba zata ƙarasa ta ɗauka din ba sai ya sunkuya riƙe da kiki ya ciro roban Ice cream guda ɗaya daga cikin laidan, ya bayar ma Kiki ta riƙe tana ta murna sannan ya miƙa ma Ilham laidan da sauran abinda ke ciki.
Ta tako kusa da su kaɗan ta rage tsayinta Sannan ta tallafe ƙasan laidan da hannayenta biyu.
“Na gode Allah ya saka da alkhairi”
Ya sake mata laidan yana juyawa riƙe da yarinyar shi a cikin ran shi yana fatan idan ta sha Ice cream ɗin ya sanyanta mata zuciya a kan faɗan da yayi mata ba tare da laifinta ba.
Ko yanzu saida ya sake taɓa hannun Kiki da tace yana ciwo amma ko lura bata yi ba, kuma da shi ta karɓi roban ice cream ɗin da ya bata.
Sauran abincin da Ihsan take zaman jiran a kai mata bai samu ba, haka Ilham ta sake ɗaukan kwanon dake kan dining bayan sun gama babu komai a ciki, sai sauran ice cream zata kai musu ta rarrasheta da shi.
Isanta ke da wuya ta samu Khausar tana zaune da basket ɗin abinci a gabanta, Ihsan tana daga gefe tana danna wayanta ta bar Khausar ɗin tana tsuru-tsuru kamar marainiya.
“Aunty Ilham” ta kirata da wannan muryar da a da yake mata kama da na marasa wayo ashe na Munafurci ne.
“Sannu khausar” tace da ita tana ƙarasawa ta kusa da gadon.
“Spaghetti da meatballs ɗin kenan?” Ihsan ta wafce laidan hannunta fara'arta yana dawowa saman fuskarta, daman ba shiri suke yi da khausar ba tun da kuma bata jin zasu fara a yanzu shiyasa da suka gaisa sama-sama sai ta kama kanta.
Ilham ta barta saida ta buɗe taga abinda yake ciki sannan tace “Ai daman ban ce miki zaki samu ba”
Ƙwafa tayi kawai saboda Khausar dake zaune a wurin ta ciro Ice cream ɗin ta fara sha.
“Ki rage ma Muftee amma sai ya narke sanyin ya fita kafin a bashi”
Ta juya wurin khausar dake dogon wuya tana leƙa abinda ke cikin robar “ko zaki sha ne Aunty Khausar?”
Dariyan yaƙe tayi, “A'a wallahi nagode, ai ina ta jiran ki ne nima na cika alƙawarin da na ɗauka, na musamman nayi miki girki yau”
“Ayyah Nagode, gashi ina ƙoshe ni, saidai Filiyan su ɗiba in kai sauran ma Ya Hashim, mun gode sosai”
Ta saki wani murmushi kaman na dole, gabaki ɗaya a tsarge take tunda Ilham ta iso amma ta gagara tashi ta tafi, ganin ta kasa kunnuwa tana son ta ji gulma yasa ko Ihsan ta ɗauko hiran gidan aikinta sai ta kawar da zancen kafin Khausar ta rigata kai ma Hashim labarin ta fara aikatau.
Ana kiran sallan Isha ta ɗauki kwandon abincin tace Khausar ta taso su tafi, ko babu komai ta hutaceta komawa ta daura tukunya.
Suka shiga napep ɗaya aka fara sauƙe khausar a gidan su kafin aka wuce da ita.
Har saida ta gyara ɗakin da Hashim ya gama wargazawa tayi wanka ta fara hutawa kafin ya dawo. Ganin yau ya shigo yanayin shi babu laifi yasa tana gabatar mishi da abincin Khausar ta zauna a gaban shi ta tanƙwashe ƙafafu.
“Baban Muftee daman aiki ne na samu”
“Aiki? Yaushe aka fara daukan jahilai aiki? Ko kina da kwali ne da ban san da shi ba?”
Bata san a wani bangare na jikin shi furta kalma mai daɗi yake gutsuran shi ba.
“A wani gida ne na samu”
“Bauta dai zaki ce ba aiki ba”
A cikin ranta tace ai gwamma shi akwai sakamako mai kyau duk wata.
A fili kuma cewa tayi “Eh shi”
“Toh yanzu izini kike nema ko sanar da ni kike yi?” Ya maimaita mata irin tambayar da yayi mata lokacin da ta sanar da shi zuwan Ihsan.
Saboda a zauna lafiya tace “Izini nake nima”
“Toh ban yarda ba”
`````````
Seemahwrites ✨
ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a turo shaidan biya ta 09039206763