Chapter 24
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)
Wattpad and Arewapen @Seemahwrites
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
UMMEE'S BAKING EMPIRE
https://chat.whatsapp.com/L0WK91pLyVn8iQ6HjSwG8a?mode=gi_t
*My Sister matso kusa ki ji.. Wannan cake ɗin da kike gani a online yake burge ki kin san inda zaki samu irin shi? Koko sha'awar glazed ko filled donuts kike yi? Ga plain ones for your Husband, father or boyfriend if they don't have a sweet tooth.*
*Coming to you my brother.. kana iya bada kyautar nan mai sanya mace tsallen Murna? Ko Surprise ma abokai? For Eids, Anniversaries, birthdays, graduation or just to celebrate your girl or yourself? you can order a cake from us. Akwai crunchy cincin domin motsa baki ko a siya ma mama da baba su saka mana albarka.*
*And don't forget about friendship or sibling bonds, You can always order a cake to celebrate their success or even to mock them with class😎, requesting captions that are satire and funny.*
Muna siyar da:
• Cakes na for every occasions ( birthday, graduation, anniversary dai dai sauran su)
• Bento cakes
• Cupcakes
• Mouth watering brownies
• Samosas
• spring rolls
• Glazed puffs
• Filled, glazed and plain donuts. E.t.c
*Ummee's Baking Empire –*
*Making every Moment feels special. We always make sure that you recieved what you ordered 👌🏼💯*
📞 08173775170
📍 gwammaja, Kano
24… Daga inda Abdulhameed ya saka kujera ya zauna da coffee table a gaban shi, ya daura laptop da takardu a kai, yana iya hango Kiki dake karaɗe harabar gidan a kan kekenta.
Tun kafin a sallame su daga asibiti ya ɗaga keken a inda zata iya ɗaukowa, kuma bayan abinda ya faru bai yarda yana barinta ta fito waje wasa ita kaɗai ba, sai yau da ta saka mishi bori shine ya ɗauko aikin da yake ƙarasawa suka fito tare.
Rabin hankalin shi na kan abinda yake typing a cikin laptop ɗin rabi yana kanta lokacin da saƙo ya shigo wayar shi.
Kafin hankalin shi ya kai kanshi wani saƙon ya sake shigowa, kuma sai a lokacin ya lura.
Ya bar abinda yake yi, ta cikin akwatin bayan wayan yaga an rubuta ‘2 Unread messages’.
Ya ɗauki wayan a cikin hannun shi na dama, da yatsar shi babba ya buɗe shi, haske ya cika screen ɗin yana bayyana masa hoton wacce ya fi ji a kusa da zuciyar shi a yanzu.
Tun tana shekara biyu yayi mata hoton a gidan zoo da ya kaita taga namun daji.
Yana iya tuna yanda take dirin murna tana nuna mishi biri da ƴar yatsarta tana cewa “daddy monkey” sai kuma ta shafa overall ɗin jikinta tana washe haƙora don overall ɗin monkey ɗin ya saka mata mai kunnuwan biri a jikin hulan rigan harda bindi ta baya, farin cikin da ya lulluɓeta yasa ya saita cameran wayan shi ya ɗauketa a hoto, kuma ko da ya tashi canza waya hoton ya mayar a kan lock screen ɗinsa, kuma shine har zuwa yau.
Ya jawo notification bar don ya duba wanda ya turo saƙon, idan ba mai muhimmanci bane ya bari sai Kiki ta sauƙa daga kan keken nan da yake ganin kaman zata sake faɗi ta sake jin wani ciwon.
Number ya gani babu suna, saboda bai yi saving ba, ko kuma yace ya dawo ya goge bayan yayi daga farko, saboda bayi buƙar kusancin mai lambar da su a yanzu.
Shigowar saƙo a karo na uku yasa ya danna abinda aka rubuto ya bayyana.
‘Na sani I'm asking for too much, amma ka taimaka min na ganta ko sau ɗaya ne’
‘please Abdulhameed’
‘Dan Allah’
Yana gama karantawa kuma saƙo na hudu na shigowa.
‘rabona da saka ta idanu na fi shekara, kamanninta zai ɓace a cikin kaina’
Sai saƙo na biyar
‘sau ɗaya kawai Abdulhameed. Dan Allah!!!'
Fita yayi daga kan saƙon baki ɗaya ya rufe wayan ya mayar da shi ya ajiye.
Bayi da lokacin ta.
Ya mayar da hankalin shi kan yarinyar dake zagayawa a kan kekenta pink colour mai tayoyi uku daga baya ɗaya a gaba.
Daga shi har ita sun samu nutsuwar da basu da shi kafin shigowar Ilham Rayuwar su.
A kallo ɗaya zaka gane haka a jikin Ikram,
Da walwalan ta, da ma ɗabi’unta.
Shi kuma a zuciyar shi yake jin akwai wani kaso mai girma na nauyin da ya ragu masa.
Kaman yanzu yana da wani assurance ne na komai zai tafi lafiya a tare da yarinyar shi, tunda Ilham tana nan.
Basu koma cikin gida ba saida Maghriba ta gabato, ya shiga da ita bathroom ɗin shi zai yi mata alwala ganin ta fara son sallah amma sai tace zata yi da kanta.
Famfon cikin tub ya kunna mata saboda na sink yayi mata tsayi. Kuma ta kamanta yin alwalan dukda ba a jere ta yi komai ba don da fuskarta ta fara, ta wanke ƙafa sannan ta dawo ta kuskure baki ta wanke hannu. Ya dai samu tayi ɗin kuma haka yayi masa daɗi, dama ganin ta yi ƙarama ma fara Sallah yasa ya sakankance bai fara koya mata komai ba.
Gyalen wani abayanta yayi ƙoƙarin tukuikuya mata saboda bata da hijabi, da tace da ƙafarta zata tafi sai ya saka mata takalmi, suka shiga part ɗin mahaifinsa yana riƙe da hannunta har ɗakin Aunty Surayyah saboda idan ya je masallaci sai yayi Isha yake dawowa.
Ya haɗu da mahaifiyar Hudah tana alwala a ƙofar ɗakinta da zasu wuce, amma yanda bata ɗaga ido ta dube shi ba haka shima ko sannu bai ce mata ba, bai kuma umarci Kiki ta gaida ta ba suka wuce abinsu.
Kiki tayi ta dungurawa a darduman Aunty Surayyah bayan ya tafi ya barta, sai ɗauko wani darduman Aunty Surayyah tayi ta bar mata wancan.
…..
“Ba zaki ci abincin ba?”
Tambayar da Hashim ya tsareta da shi kenan bayan ta tashi zata bashi wuri.
Juyowa tayi ta sake kallon abincin kaman ba ita ce ta dafa ba. Shinkafa ce ƴar gida da miyan busasshen tumatir, ita kuwa basmati ta ci da nama zuƙu-zuƙu a cikin miyan da haɗaɗɗen coleslaw ya ji ƙwai da mayonnaise harda wake da masaran gwangwani.
Ta taɓe baki ba don ta raina abincin ba, sai don Hashim ɗin ya fi ƙarfin wannan cimar a gidan shi, shinkafar ma wanda aka kawo mata daga wurin Maama ne kayan miya kawai ya kawo. Mutumin da albashinsa babu laifi kuma ba nauyin kowa yake da shi a wuyansa ba bayan nasu da ya gagara sauƙewa, ita bata san ma me yake yi da kuɗin ba bayan siyan tsadaddun sutura ma kan shi da kashewa ƴammata.
Ta girgiza kai “Alhamdulillah. Na ci abinci a gidan aiki na”
“Muftee fa? Banga kin ɗiba zaki kai mishi ba”
“Shima yaci”
“Na gidan aikin?”
Ta gyaɗa kai.
“Gaskiya ne, zo ki rage tsayin ki a nan” ya cire cokalin da yake motsa abincin da shi ya nuna mata inda yake son ta zauna da shi.
Da tayi kaman yanda yace sai ta ɗago tana kallon shi.
Ya kalli cikin idanunta da kyau, sosai yaga ta canza masa, ba kamanninta ba, amma akwai wani abu da ya canza a game da ita a kwanan nan. Har yanda take kallon shi, akwai wani abu da ya ɓace a cikin idanunta. Wannan raunin nata yau bai gan shi ba, kuma hakan bai yi masa daɗi ba.
“A gidan aikin naki ne suke baki abinci har ki kai ma ɗan ki?”
Da “Eh” ta amsa cikin tabbatarwa.
“Aikin me kike yi?”
Sai yau yaga daman tambaya?
Ta bashi amsa da “Gyare-gyaren gida ne da girki sai rainon yarinya.”
“Kuma kina da majinyaci a kwance kike zuwa kiyi duk wa’innan abubuwan?”
Shiru tayi ta sauƙe kanta ƙasa, don wannan ba tambaya mai niman amsa bane, accusation ne, so yake yi tace wani abu ya samu dalilin mata wani wulaƙancin amma ba zata ce komai ba, ta riga da ta san halin shi maganin zama da shi zata cigaba da haɗiya.
“Nawa ne suke biyan ki da kika zaɓi ki kai ƙara na don nace ki bar aikin, kika zaɓi ki kori ƴar uwar ki a kan ki ji magana ta?”
Da sauri ta sake ɗagowa tana kallon shi da mamaki kaman ba shine ya bata zaɓin hakan ba amma ya dawo da komai kanta.
Yanzu idan ta faɗa masa gaskiyar nawa ake biyanta abubuwan da take samu tayi da kuɗin ba zai yiwu ba. Don ko lokacin da take ɗaukan dubu goma sai yace tayi cefane ko wani buƙata idan ya taso mata a cikin kuɗin zai bata daga baya, shikkenan kuma ya wuce ba zai bayar ɗin ba, idan tayi magana kuma cibi ya zamo ƙari.
Don haka da ta buɗe baki sai harshenta ya furta “Dubu Talatin da biyar”
Ta ƙara biyar ɗin a kai ne saboda lissafin zai fi zama masa.
Kuma ya yarda daga ganin yanda ya waro ido “Kaii. Da gaske?”
Ta jinjina kai “Masu rufin asiri ne sosai kuma suna ci daga dukiyar da Allah ya hore musu”
Maimakon ya gane magana ta faɗa masa sai ya girgiza kai “Dole ki daina cin abincin gidan nan kam. Kin samu Capacity Hajiya Ilham, Allah dai yasa ba da kuɗin haram ake biyan ki ba, ko wata rana a haɗa dake a siyar a ƙara yawan dukiya”
Bata san meyasa maganar tashi ta bata dariya ba, amma ta ga mamakin murmushin da tayi a kan fuskar shi.
Ya ɗaura da “Toh daga yanzu dai sai a sakar mun wuya in sha ruwan sanyi tunda na barki ki nemi na kan ki, idan ma wani abu daban kike yi ake baki wannan kuɗin ke kaɗai zaki san nayi randa ta kwaɓe miki”
Bayan yawan kuɗin da ta ɓoye mishi, akwai abinda bata fito ta sanar da shi ba.
Kasancewar ma single father take aikin, saboda ta san ba zai fahimta ba, koda tayi masa bayanin yanda abin yake ba zai fahimta ba.
“In sha Allah sai alkhairi, Nagode sosai” daga haka ta miƙe ta fita ta kimtsa inda ta gama dafa abincin don barci take ji tun goma bata cika ba.
……
7:20am
Kayan da zai saka yake dubawa, kullum sai ya zo irin haka yake lura da yawancin wandunan shi farare ne ko kuma kala masu haske. Amma idan ya je siyan kaya kaman ya manta sai ya sake debo irin su, kuma bai iya saka manyan kaya ba, bai saba da sakawa ba tun tasowarsa, takura sosai yake yi idan ya saka har sai ya dawo ya cire ya ji sakat, shiyasa wata rana idan yazo niman abinda zai suturta jikin shi sai ya daɗe yana lalumen wanda zai banbanta da sauran wanda ya sanya a cikin satin, don sai ayi tunanin kaman kaya ɗaya yake maimaitawa.
Farin wandon ya haƙura ya ɗauka ya haɗa shi da farin riga mai laushi, sai ya ɗora baƙin open suit a kai kada yayi kaman gawa a cikin likkafani.
Yana maƙala agogo a tsintsiyar hannun shi saƙonta ya sake shigowa.
Bai ji tsaƙin da ya ja a cikin kunnen shi ba amma ya san yayi. Tun jiya ta dame shi, messages kusan 20 a tsakanin yammaci zuwa safiya duk ya share amma bata haƙura ba.
Ya saka wayan a aljihu ya feshe jikinsa ta turaren Amouage king Blue, sannan ya kashe wutan ɗakin ya fito.
Kiki na zaune a kujeran dining, Ilham na ɗaukan wani round abu da fork tana saka mata a plate amma daga wurin ƙamshin abun yana shiga masa hanci duk da suma na turaren shi ne yasa duk suka juyo suka dube shi, Kiki ta sauƙo da gudu ta zo ta rungume ƙafafuwan shi kaman yanda ta saba.
“Daddy kazo Mimi ta saka mana abinci” ta ja hannun shi zuwa teburin, kuma Saida ya ƙarasa kusa ya gane menene, masa ne, abinda bayan a dalilin yunwa da ta kusa masa illa bai sake ci ba.
Ai kuwa jiya yaga shinkafan yin masan da ta jiƙa, sauran kaɗan ya zubar da yazo wanke kwanukan da suka ci abincin dare don ya ɗauka ruwan datti ne, har ya fara juye farin ruwan a cikin sink yaga shinkafa a ƙasa sai ya sake zuba wani ruwan a kai ya bar mata kayanta, ashe ma sune zata markaɗa ta soya ta basu su ci.
Saida ta ƙarasa zuba yanda plate ɗin zai ɗauka ta lulluɓe sauran da baking sheet da ta saka saboda tururi kada ya jiƙa shi, ta mayar da murfin ta rufe kana ta buɗe kwanon miyan shima ta zuba yanda zai ishe su su biyu.
Kuma bai samu ƙwarin guiwar cemata baya cin abinda ta dafa yau ba ma don yaga alamun abun bai yi mata daɗi ba last week da tayi awara bai ci ba.
Bayan ta wuce da ya ɗauki fork ya gutsiri ɗaya ya dandala masa miya ya kai baki sai ya gyara zama ya zaƙe yana ci sosai.
Vibration ɗin da wayan shi ya cigaba da yi yasa ya dakata ya ciro wayan ya duba.
‘Abdulhameed’
Ita ɗin ce dai.
‘Na dawo Kd. Zan zo in ganta please, sau ɗaya kawai”
“Pleeeesee”
Kaman zai share saƙon sai dai kuma bai san me zata aikata ba don ya lura halin su kusan ɗaya da ƴar uwarta, duk abinda suka ga dama suke yi a lokacin da suka yi niyya.
Ya saita cameran wayan a fuskar Kiki dake fama da wani ƙashi tana ta gwaigwaya, bakinta duk miya, ya ɗauketa a hoto ba tare da ta sani ba, ya tura ma wannan numbern. Sannan ya shiga cikin gallery ɗin shi, ya ɗauko wanda yayi mata ranar da zata fara zuwa makaranta, da uniform a jikinta, jaka goye a bayanta, tana ta murna kafin ta je ta dawo da kuka, shima ya tura mata kana ya shiga rubuta reply.
‘She’s Healthy and Happy’
‘Kada ki zo mun gida.’
‘Don't you dare come to my house’
Daga nan kuma sai ba'a sake turo komai ba har ya ƙammala shirin barin gidan.
Da ɗan dama Ilham ta haɗa ƙullin masan don tana son zuba ma aunty Surayyah ga kuma wanda zata ci, dukda ta so tafiya da shi ma Ihsan amma sauran babu yawa sosai, saboda wanda ta cika food flask ɗin da shi a kan idan suka rage zata ci Kiki tace ta saka mata a kwano ta tafi da shi makaranta.
Tana cikin soya wanda ya rage ɗin bayan sun tafi, sauran ita kaɗai a part ɗin ta fara jin knocking a ƙofar parlour.
Ta juya masan ta rage wutan ƙasan kaskon kafin ta fita ta duba wanene.
Ɗaya daga cikin yaran gidan ne, amma bata san sunanta ba, ita ce dai ranan tace mata babu Hajiya Surayyah a gidan.
Suka tsaya suna kallon kallo an rasa waye zai fara gaida wani a cikin su.
“Yaya Abdulhameed yana nan?” Huda ta tambaya bayan saida ta tabbatar da baya nan ɗin tazo.
Ilham kaman zata bata amsa daidai da tambayarta tunda sun fita sanin yana zuwa aiki amma sai tace “baya nan”
“Okay daman yunwa nake ji, shine na zo ki saka mun abinci.”
Daga yanda Hudan tayi magana har yanda ta coge da hannunta goye a kirji, ko ita ce take biyan Ilham kuɗin dafa abincin albarka.
Amma a wannan gidan bata da ta cewa ne, sai ta ce mata “toh ina zuwa” ta koma ciki.
Ba zata so su kai ƙarar ta wurin Abdulhameed ta hana su abinci ba, bayan ita ƴar aiki ma yana gani take tafiya dashi bai hana ta ba.
Sauran duka ta kwashe daga cikin kasko don ya soyu, ta zuba mata a plate da sauran miyan sannan ta rufe da wani plate ɗin ta fito da shi, a parlour ta samu Hudah zaune a kujera ta ɗora daya kan ɗaya tana jiranta.
Ta ƙarasa ta miƙa mata, kuma babu sannu balle na gode ta karɓa tayi tafiyarta.
Ƙofar da ta buɗe ta wuce ta ciki ma ta bar ma Ilham ɗin ne tazo ta rufe.
````````````
Seemahwrites ✨
ƘARFE ƊAYA BAYA AMO by Gureenjoh
JODA by Sadi-sakhna
DAƊIN ZAMA by Seemahwrites
*A whatsapp
One 1k
Two 1800
Three 2400*
*Telegram
One 700
Two 1200
Three 1500*
Account details
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin
Sai a turo shaidan biya ta 09039206763