← Book details Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 30 OF 30

Chapter 30

Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

*DAƊIN ZAMA🍁*


Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)

Wattpad and Arewapen @Seemahwrites

*Women of Words Writers*

#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)


Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍


30… Aliyyu yana zaune yana jira saida Ihsan ta taimaka mata ta zauna da kyau tare da saka mata pillow a bayanta sannan yace ma Ihsan ɗin ta fita ta basu wuri suyi magana.

Sun yi Sa'ar samun ɗakin da babu kowa, kafin Ya cicciɓo Ilham ya kawota aka sallami wanda ke ɗaya gadon.

Saida ya ji ƙaran jan ƙofa da rufeta da Ihsan tayi kafin ya tattara hankalin shi gaba ɗaya a kan Ilham da bai san zabgewar wuni ɗaya bane tayi ko na tsawon lokacin da ya ɗauka bai saka ta a idanun shi ba.

Bayan gungun tashin hankali da suka yi mata rubdugu harda rashin cin abinci a cikin sanadin rashin samun kuzari a jikinta, kuma bayan ta farfaɗo zuciyarta bata huta ba, musamman da taga Yaya Aliyyu a gabanta.

“Fidela” ya kira sunanta yana tsareta da idanuwa.

Kai a ƙasa ta amsa da “Na'am” kan kace mene hawaye sun sake samun hanyar gangarawa fuskarta.

Ba zallan Rashin lafiyan Muftee ko ɓatan Kiki ba, ƙazafin zina da aurenta da hashim ya jefe ta dashi shine ya fi bata tsoro, amma zata yi ƙarya idan tace sakin da yayi mata bai girgizata ba.

“Ki buɗe baki kiyi mun bayanin abinda yake faruwa idan kina son in saurare ki da kunnen fahimta, da zaran mun koma kano ba lallai ki samu wannan damar ba”

Da wani abinda yake faruwa ɗaya zata fara?

“wallahi Allah shine shaida na, bayan fafutukar da nake yi da izinin shi da amincewar shi, ban taɓa tsallake iyakata a wurin nema wa kaina mafita ba”

Ta fahimci da abinda yake so ta fara kuwa, hujjan da Hashim ya riƙe yake so ayi mata hukunci da shi ba tare da an ji ta bakinta ba.

“Shi kuma wanda yace ya gan ki a mota ke da shi da idon shi shekaran jiya da misalin ƙarfe 11 na safe fa? Da suturar da ba taki ba a jikin ki Ilham?”

Ƴan gidan su basu kiran sunanta sai sun saka ta ji bugun zuciyarta ya tsananta, saboda babu wasa ko wargi a tare da hakan koda daga bakin Ihsan dake matsayin ƙanwarta ce kuwa.

Hawayen dake ɗiga daga idanunta yasa take jin hancinta ma kaman zai taya shi ɗiga, saida ta ja hanci kafin tace “taron makaranta zamu je suka bani kyautar sutura shine na saka a jiki na, kuma wallahi ba mu kaɗai bane a cikin motar, akwai ƴan uwan shi guda biyu mace da namiji da suka mallaki hankalin su a tare da mu…”

“Tambayar ki nayi wanene shi?” Aliyyu ya katseta idanun shi a lumshe, yankan jiki da tayi ta faɗi ya ɗarsa masa tausayinta a zuciya, amma bayi so ta ƙure ɗan sauran haƙurin da ya samu a sanadin haka.

“Mahaifin yarinyar da nake raino ne.”

“Yarinyar da aka sace?”

Ihsan ta faɗa mishi komai kenan, babu amfanin ɓoyewa.

Ta gyaɗa kai.

“Duk ke kaɗai Ilham?! Yayi kyau. Ina fatan kin tanadi kuɗin da zaki yi belin kanki tun da gashi can ya tura ƴan sanda gidan ki a kama ki”

A zahiri shi take yiwa kallon mamaki baki a buɗe hawaye na wanke mata fuska amma Abdulhameed take gani a baɗini. Shi take kalla da mamakin da ya hana ta ko motsin kirki, shi da ta karɓi lamarin shi da zuciya ɗaya ta hidimta ma yarinyar shi fiye da yanda take yiwa nata yaron bayan yana cikin halin buƙatar kulawa na musamman.

Ya san bai yarda da ita ba yake barinta da yarinyar su biyu a gida babu idanun kowa a kansu? Da tana da niyyar cutar da ita da tuntuni bata yi amfani da wannan damar ba? Abdulhameed bai duba wannan ba, cin mutuncin da yayi mata a gaban ƴan uwansa bai ishe shi ba sai ya tozarta ta a idon duniya.

Ta haɗiyi wani abu mai ɗaci a maƙogwaronta sannan ta tsinkayo muryar Yaya Aliyyu yana cigaba da magana cikin faɗa.

“Me yasa baki sanar ma Maama cewa wanda zai ɗauke ki aiki bayi da mata ba? Ƙofar zargi komin kashin sa kin san hatsarinsa Ilham? Neman kuɗi hauka ne? Ko akwai wanda yace miki lallai sai kin ɗorawa kan ki abinda yafi ƙarfin ki? Da kika ga ba zaki iya ba meyasa baki bar masa ɗansa kin dawo gida ba?”

Tun da tayi shiru har ya bar ɗakin bata sake cewa komai ba, bayan fitan shi Ihsan ta dawo, ta saka mata ruwa a buta tayi alwala da Sallah, ta koma gadon ta zauna tana jin yanda ƙirjinta ya riƙe.

Ta kasa cin komai a daren ta kasa barci tana tunanin abinda wayewar gari yake tafe da shi.

Hala yanda ta kwana a gadon asibiti yau gobe saidai kwanan police station.

Sai taji duniyar duk tayi mata zafi.

.
Duk yanda taso ta cigaba da kwanciya da safe saida ta tashi ta je duba Muftee saboda Ihsan tace ya farka wajajen ƙarfe huɗu na asuba kuma idan jikin shi ya ƙara kyau zasu cire mishi oxygen ɗin.

Yaya Aliyyu ta hango tsaye tare da likitoci uku, hankalinta ya sake tashi kada wani abune ya sake faruwa.
Kaman cece-kuce suke yi.
Majinyata da yawa sun bar gadajen yaran su sun zo jin kanun labarai.

“Zo nan Fidela” ya yafato ta da hannu lokacin da ya hangota.

Likitocin sai tausan sa suke yi amma fafur ya ƙi sauraren su.

Cike da sanyin guiwa ta taka ganin manyan likitoci ne a wurin, ƙaraminsu a matsayi shine wanda suke soyayya da Ihsan, Dr Bello. Aliyyu ya fara mata bayanin abinda yake faruwa dalla-dalla.

Dawowar shi jikin Muftee bayan yayi sallan asuba ne ƙus-ƙus ɗin da nurses suke yi a kan Crises ɗin da Muftee ya samu, dalilin alluran mara lafiyan gefen gadon shi ne aka yi mishi.
Shine ya tada rikicin ba zasu yarda ba, duk da sun tabbatar mishi zasu sallami nurse ɗin a asibitin ko a bata suspension mai tsayi.

“Ai zai tashi ko?” Ta tambayi wanda take tsammanin zai faɗa mata gaskiya cikin sanyin murya.

Dr Bello ya gyaɗa kai tare da cewa “in sha Allah, ya riga ya fita daga cikin danger”

“Shikkenan, babu komai ku barta a bakin aikinta, ta taimaka ma mutanen da suka fi yawan wanda aka samu kuskure a kansu, Allah ya kiyaye na gaba”

Idan bata yi mata uzuri ba, bai dace tayi tsammanin ya kamata Abdulhameed yayi mata uzuri ba itama.

Babu ɗan adam ɗin da ya wuce kuskure.

…..

A gadon shi ya kwantar da Kiki ya rufa mata bargo iya cikinta, sannan ya jawo kujera ya ajiye a gaban gadon ya zauna.

Saƙo ya rubuta ya turawa Excellency, yau ya kasance rana ta farko da ya fara yi masa tuni a kan alƙawarin su shi da kan shi.

Saboda Excellency ya san zai neme shi ɗin yasa tun bayan da aka sanar da shi Abdulhameed yace an samu yarinyar bai sake tuntuɓar shi ba.

Saboda ya san bai wuce dangin mahaifyar ta bane suka ɗauke ta.

Indai haka ne kuma zai neme shi.

“Da safe ƙarfe 10” shine reply ɗin da ya samu daga Excellency na dogon saƙon da ya tura mishi.

Ya ajiye wayan yana kallon rigar jikinta kalan pink da Mardiyya ta saka mata, har kitson kanta sun sake mata, yanzu rabin kitson an tufke mata ne a tsakiyar kanta sauran an sauƙo dashi gefen fuskarta, har beads ɗin da aka saka mata a jiki ba wanda ta fita dashi daga gidan bane.

A wuni guda kawai ya ji kaman har an fara nesanta shi da yarinyar.

A wannan karon ba zai bari lokacin da zai fara ƙirga tsakanin rabuwar shi da Kiki ya zo ya riske shi yana zaune ba, tun da wuri zai dauki mataki.

7:03am

Yana kitchen yana soya ƙoyin da zasu haɗa da dankali ta shigo tana murtsuka idanu.

Ta ƙarasa wurin shi ta taba shi ya juyo sannan tace “Daddy ina Mimi?” Ta zuba mishi idanu tana jiran amsa saboda yanzu ta saba kusan kullum Ilham take samu a kitchen ɗin.

Sai ya rasa me zai ce mata, ita kanta Ilham ɗin idan ya ganta yanzu bayi da abinda zai ce mata.
Tayi haƙuri? Abinda yayi mata ya fi ƙarfin kalmar haƙuri.

Ƙaurin kwan da ya shiga hancinsa yasa shi saurin kashe gas ɗin kafin ya saka majuyin hannun shi ya juya ɓangaren ƙwan da ya fara baƙi ya dawo sama.

Mai kyau ɗin da ya fara soyawa ya saka mata ya saka ma kan shi ƙonannen sannan ya ɗauki plate ɗin, ya riƙe hannunta zuwa dining.

Abincin bai yi mata daɗi ba kaman yanda na Ilham yake, idan tayi musu dankali irin haka sai ta haɗa musu da sauce ɗin albasa ko na hanta a maimakon Ketchup da suka saba dashi a da.

Ya shiga damuwa ganin bata ci dankalin da yawa ba. “Kiki Aunty da ta ɗauke ki jiya tayi miki wani abu ne?”

Gyaɗa kai tayi, tace “Ta cire mun kaya da pant ɗina tayi mun wanka. Kuma Mimi tace duk wanda ya cire mun kaya ko pant in faɗa maka”

“Kin yi daidai. Mimi ta faɗi daidai” yayi murmushi yana shafa kanta.

Alkhairin Ilham a gare shi mai yawa ne, abinda tayi masa a wata ɗayan nan bayi da abinda zai iya saka mata da shi, sai gashi yayi mata halin ɗan Adam, kuma tun ba'a je ko ina ba ya fara ganin gurbinta.

Saida ya sauƙe Kiki a school kafin driver ya wuce da shi gidan Excellency.

A wani wuri da aka yi kejin adana tsuntsaye kala daban-daban ta bayan gidan ya same shi yana zuba ma wasu fararen baru tass abinci, irin foreign breed manya masu yawan gashi ɗinnan.

Ya tsaya a lokacin da wanda yayi masa Iso ya sanar da Excellency zuwansa kafin aka bashi damar ƙarasawa.

Saida ya gama abinda yake yi kafin ya juyo ga Abdulhameed.

“Karfe 10 nace” yayi magana yana kallon Abdulhameed bayan ya duba lokaci a jikin agogon shi.

“Kayi haƙuri, ba zan iya jira ba”

Ya ɗauka parlourn shi zasu shiga suyi maganar saboda muhimmacinta, ko wanda bai kai shi ba ma basu yin shi a waje, ko baƙi yazo gidan ya tarar sai Excellency yasa an shiga da shi private parlour ɗin shi ya jira shi.

Amma yau a tsakar fili suka zauna suna fuskantar juna.

Waya Excellency ya ciro ya kira lawyer ɗinsa da ya ɗora a kan case ɗin Abdulhameed.
“Yaya ake ciki?”

Abdulhameed ya karanta kalmar da lips ɗinsa suka furta.

Sai yaga Excellency ɗin yayi shiru yana sauraro kawai.

Bai shiga waswasin dalilin da yasa Excellency ya ƙi haɗa shi da lawyern kai tsaye ba saidai komai za'a yi ya zamo shine a tsakani.

Saboda ya san waye Excellency.
Ɗan siyasan da ya fara gwagwarmaya tun a jami'a, ya riƙe muƙamai tun daga ƙananu har zuwa SUG president, a lokacin ne ya samu sunan Excellency a bakin ɗalibai ƴan uwansa. Daga nan kuma har matakin sanata ya riƙe, yanzu yana shirin fara niman kujeran gwamna, kuma ranan da ya kira Abdulhameed suka zauna cikin sirri yana bashi labarin yana da burin yayi har shugabancin Nigeria gaba ɗaya bai san amfanin mene sanin hakan tun da wuri zai yi masa ba.
Amma ya fahimci dalilin da yasa Excellency yake son juya mutane suyi yanda yake so, saboda cikar burin shi dole sai da taimakon mutane.

Saida ya katse kiran ya dube shi.
“duk yanda zamu yi ba zamu samu takardun nan cikin sauƙi ba. Idan muka ce da kuɗi zamu yi amfani sun fimu kuɗi ka sani, kuma muka ce zamu saka gaggawa a ciki muka yi saken da zasu gane shirin mu komai zai lalace, suna da tarin hujjoji bamu da komai, zan sama maka duk irin flight ɗin da za'a samu nan da kwana biyu ku bar Nigeria”

Abdulhameed ya ja numfashi a sannu ya furzar kana yace “Sabon contract ɗinmu fah?”

Bayi taɓa saka hannu a jikin ko wani irin takarda ba tare da ya duba dokokinsa ba. Kuma sharuɗan da Excellency ya gindaya ma wanda aka samu tangarɗa daga ɓangaren shi kuɗaɗe ne da yawansu ya kai ya tattara dukka abinda ya mallaka kafin ya iya biya. Idan ya amince da hakan kuma yaya za'ayi ya iya cigaba da kula da Kiki banda ɗaruruwan mutanen da lafiya da ilimin su ya dangana da A&I support Organisation?.

Idan kuma Excellency bai ce sai ya biya ba, toh zai kawo masa wani sabon sharaɗin da zai saka ya ji kaman yana ɗaya daga cikin tsuntsayen dake kulle a cikin kejin nan.

“Idan na koma da ita Japan, zasu binciko mu duk inda muka shiga muka fita, akwai ƙasashen da alaƙa na da ita ya saɓa ma dokokin su musamman ace babu mahaifiyarta a tare da mu. Sannan bani so in yi breaching contract ɗinmu, so zan cika maka alƙawari kafin in tafi, ina fatan bayan nan I'll gain my freedom, ina buƙatar in yi protecting abubuwan da suke da muhimmanci a wurina da kaina. Ba tare da kutsen kowa ba.”

Excellency yayi murmushi.
Daman ya san daga lokacin da wani abu ya samu Kiki, toh ko Abdulhameed ya daɗa depending da shi ne ko kuma yayi mishi tawaye.

Amma lokaci ne zai bayyana komai.

“We shall see”

…..

Ganin zuwa dare Muftee har yana karɓan abinci yasa suka fara shirin barin Kaduna, saboda yanda Ilham take jin bata iya numfashi da kyau a garin, yanda take ganin yayi baƙi a idanunta, dalilin da ya kawota kuma Allah ya kawo ƙarshen shi.

Duk da Yaya Aliyyu ya tabbatar mata Hashim ya kwana a kano kafin shi ya taso amma Bata iya sake taka ƙafarta a gidan Hashim ba sai Ihsan ne ta je ta haɗo mata kayan sawanta.

Ta so tayi mamaki da bai tafi da key ba ma ya mayar gidan da suke bada ajiya, a jikinta take jin akwai Abinda Hashim yake shiryawa da bata san menene ba.

Ranar juma'a da hantsi suka dangana tasha.
Aliyyu yana rungume da Muftee a haka yake ta musu cuku-cukun samun mota da biyan kuɗi daga aljihun shi.
Wani yanayi da a cikin shekaru biyar da ta ɓata da Hashim bata taba samun kanta a makamancin shi ba.

Har Ranar da zasu dawo Kaduna da zama daga aljihunta ta biya kuɗin motar da ya tattaro kayan ɗakinta, shiyasa ma bata zo da kujeru ba ta zaɓi ta siyar ta sayi wani a nan, amma a haka kuɗin ya lalace.

Da akwatin su da Muftee kuma haka ta dinga tiƙi-taƙa da su, damuwan shi kan shi kawai.

Kuɗin seat ɗinta ma da ƙyar ya biya domin daga farko dagewa yayi ya kashe kuɗi da yawa saidai ya biya mata rabi ko ta jira sai ya samu tazo. Kunyar idon Maama da ta rakota har tasha daga fitan ta daga takaba yasa suka wuce salum alum.

“Yaya akwai kuɗi a wurina” tace ma Aliyyu tana bashi katinta na opay. Jiya ma ta ga dubu ɗarin da Hajiya Surayyah ta turo mata tare da dogon saƙon ban haƙuri bayan ta kira ta bata haƙurin har tana cewa zata zo Ilham tace ba sai tazo ba, tunda an samu Kikin falillahil hamd.

Ko kallon katin bai yi ba yace “ki bari zaki buƙaci kayan ki daga baya” yayi gaba ya samu drivern motan da zasu shiga yayi mishi magana a basu seat ɗin da Muftee ba zai wahala ba.

Isar su cikin garin Kano bayan sallar Juma'a yayi daidai da ɗaurin Auren Hashim Ibrahim Baniza tare da Amaryar shi Khausar Rabi’u Baniza.
….

*Hmm Wasa farin girki.*

*Hashim da Khausar Alƙawari ya cika.*

*Ilham ta bar Kaduna ma Abdulhameed*

*Zawarcin da take tsoro, gudun abinda mutane zasu ce, akwai wanda zata iya tare ma kanta a halin yanzu?*


*Mu haɗu da ku a littafi na biyu domin cakwakiyar yanzu aka fara. It will be available on arewapen by 17/09 Telegram and WhatsApp by 20/09.*


*Sneak peak*

“Na dawo Ilham, I am back once again”

Kallon shi tayi daga ƙasa har a kaikaice. Ya sake canzawa.

Saida ta kalle shi a cikin ido kafin cikin gatse tace
“ka dawo daga ina?.”

Zuciya ɗaya ya amsa da “Na kai Kiki an yi mata a aiki a kunne. Ta samu Lafiya yanzu, she doesn't need hearing aids anymore”

Har cikin zuciyarta zancen yayi mata daɗi amma sai ta taɓe baki tace “yayi kyau, matsa mun a hanya Abdulhameed, ana jira na”


UMMEE'S BAKING EMPIRE
https://chat.whatsapp.com/L0WK91pLyVn8iQ6HjSwG8a?mode=gi_t

*My Sister matso kusa ki ji.. Wannan cake ɗin da kike gani a online yake burge ki kin san inda zaki samu irin shi? Koko sha'awar glazed ko filled donuts kike yi? Ga plain ones for your Husband, father or boyfriend if they don't have a sweet tooth.*
*Coming to you my brother.. kana iya bada kyautar nan mai sanya mace tsallen Murna? Ko Surprise ma abokai? For Eids, Anniversaries, birthdays, graduation or just to celebrate your girl or yourself? you can order a cake from us. Akwai crunchy cincin domin motsa baki ko a siya ma mama da baba su saka mana albarka.*
*And don't forget about friendship or sibling bonds, You can always order a cake to celebrate their success or even to mock them with class😎, requesting captions that are satire and funny.*

Muna siyar da:

• Cakes na for every occasions ( birthday, graduation, anniversary dai dai sauran su)
• Bento cakes
• Cupcakes
• Mouth watering brownies
• Samosas
• spring rolls
• Glazed puffs
• Filled, glazed and plain donuts. E.t.c

*Ummee's Baking Empire –*
*Making every Moment feels special. We always make sure that you recieved what you ordered 👌🏼💯*

📞 08173775170
📍 gwammaja, Kano
Chapter 30 · 0% Book details