Chapter 14
Dadin Zama Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read
*DAƊIN ZAMA🍁*
Saliha Ahmad Na'ibi (Seemahwrites)
Wattpad and Arewapen @Seemahwrites
*Women of Words Writers*
#THE TRIO OF TALES
(Three minds, Three stories, One journey)
Sincerely, to Aunty Hauwa Yarima 🤍
UMMEE'S BAKING EMPIRE
https://chat.whatsapp.com/L0WK91pLyVn8iQ6HjSwG8a?mode=gi_t
*My Sister matso kusa ki ji.. Wannan cake ɗin da kike gani a online yake burge ki kin san inda zaki samu irin shi? Koko sha'awar glazed ko filled donuts kike yi? Ga plain ones for your Husband, father or boyfriend if they don't have a sweet tooth.*
*Coming to you my brother.. kana iya bada kyautar nan mai sanya mace tsallen Murna? Ko Surprise ma abokai? For Eids, Anniversaries, birthdays, graduation or just to celebrate your girl or yourself? you can order a cake from us. Akwai crunchy cincin domin motsa baki ko a siya ma mama da baba su saka mana albarka.*
*And don't forget about friendship or sibling bonds, You can always order a cake to celebrate their success or even to mock them with class😎, requesting captions that are satire and funny.*
Muna siyar da:
• Cakes na for every occasions ( birthday, graduation, anniversary dai dai sauran su)
• Bento cakes
• Cupcakes
• Mouth watering brownies
• Samosas
• spring rolls
• Glazed puffs
• Filled, glazed and plain donuts. E.t.c
*Ummee's Baking Empire –*
*Making every Moment feels special. We always make sure that you recieved what you ordered 👌🏼💯*
📞 08173775170
📍 gwammaja, Kano
14…. Wallahi nayi kewar ki sosai ƴar ƙanwata” Cewar Ilham idanunta suna tara ƙwallan farinciki, suka sake rungume juna suna murna a tsakar gidan zuciyoyinsu na shawagi, kusan shekaru biyu kenan rabon su da saka juna a idanu.
Last Year da aka yi taron family Muftee ya ɗan taɓa pnuemonia, amma ta jinkirta kaishi asibiti ganin idan suka je gida zasu ɗan kwana biyu in yaso sai ta kaishi asibitin Malam Aminu Kano, don likitan da ya fara ganin shi ma lokacin da aka gano shi sickler ne Kafin su koma kaduna da zama yana can.
Amma Hashim bai tashi faɗa mata ba zai tafi da su ba, saida ya bari ta gama shirya musu kayan su tsaff ta haɗa ɗan tsarabar da zata kai gida don shi ba baƙon zuwa wa mutane hannu na dukan cinya bane ko lokacin da yake niman aurenta.
Duk da ya san ba son shi take yi ba a lokacin, kuma ta gwada mishi hakan a aikace, amma ko ma wa’inda suka yarda aka haɗa auren bai taɓa ruƙo komai ba, haka zai zo hannu rabbana ya cikata da surutu a Falon Taa ɗinsu tana kuɗundune cikin hijabi tana gumm da baki har ya gama ya tafi babu wani ɗan ihsani.
Ihsan ta ɓamɓare jikinta daga na Ilham tana yamutsa fuska “Yunwa nake ji Addah Fidela! Kin san idan zan yi tafiya bani iya karyawa in ba haka ba sai nayi amai a mota”
“Yi haƙuri acici mala’ikun tauna” Ta kama hannun akwatin Ihsan ta raba shi da ƙasa don babu taya guda ɗaya a jiki balle ta ce zata ja shi.
“Kai-Kai Filiyan?! garin Kano kika ɗauko kika zo dashi ne?” tace jin nauyin akwatin yayinda Ihsan ta ɗauki buhun da take da tabbacin yafi akwatin nauyi suka shiga parlorn Ilham ɗin da ta ƙalƙale shi harda maƙala turaren tsinke sai ƙamshinsa ke tashi.
“Fidela ina kayan ɗakin ki?”
Shine sallamar da Ihsan ta shiga dashi.
Ilham tayi murmushin yaƙe “wani kayan ɗaki kuma? Kin san daman ai tunda na siyar da kujeru na da zamu bar kano ban sake siyan wasu ba”
“Toh ina TV da fridge ɗinki? Babu komai a parlorn ki sai carpet da wani yamutsolon labule?”
“Suma ba don kada sanyi ya kama Muftee na ba da ba zaki zo ki same su ba. Ni zauna in baki abincin kafin kice wa Maama nah na barki da yunwa.”
Ta ja hannun Ihsan din suka zauna a gaban tray ɗin da ta shirya mata abincin cikin wani koɗaɗɗen food flask da kwanon samiran da yasha lamba har ya godewa Allah.
Ƙamshin taliyan ya tuna ma Ihsan yunwar da take ji don haka ta mayarda hankali a kan abincin da ta tursasa Ilham saka hannu suci tare har saida suka ga bayan shi tass, daman babu yawa sosai ne Ilham ɗin taƙi ci don gani take yi Ihsan ba zata ƙoshi ba. Sai gashi Allah ya saka masa albarka dukkan su sunyi tamm suna hamdala.
Ihsan ta tashi ta nufi inda suka jingine buhun sannan ta fara firfito da kayan ciki.
Ƙullin shinkafa da flour kusan mudu biyar biyar a cikin laida mai yellow da baki ta fara direwa a gaban Ilham, sannan laidojin taliya guda huɗu, macaroni huɗu, goran faro mai cike da mangyaɗa guda biyu na manja guda ɗaya. Laidan maggi guda biyu, omon wanki babban jaka da sinkin sabulun wanka ga na wanki ma harda man shafawa babban roba, da doya guda biyu a ƙasan buhun.
Saida ta gama fitowa dasu ta dubi Ilham da hawaye ke gangarawa saman Fuskarta, tace “toh gashi in ji Maama. Ita ta saka yaya Ahmad ya baki shinkafa babban yaya kuma ya kawo doya.”
“Allah sarki Maama, Allah sarki Maama nah”
Ihsan taƙi kallonta kada itama zuciyarta ta karye, ta sake miƙewa ta kwantar da akwatin kayanta, ta ciro wani laida da aka samu da ƙyar ya shiga cikin akwatin ta miƙawa Ilham.
Share hawayenta tayi da bayan hannu ba don sun daina zuba ba ta warware ƙullin laidan don ganin abinda ke ciki.
Kaya ne, riguna da wanduna na yara gumama da yasha wanki da guga suka fito tass fiye da wasu na kantin ma don masu kyau ne sosai. Har set guda uku haka ta ciro su tana da tabbacin kuma na Muftee ne. Bayan haka ga safan ƙafa har guda uku da na hannu guda ɗaya, da hulunan sanyi guda biyu. sai kuma rigan sanyi mai kauri guda ɗaya da mara kauri mai hula da dogon hannu duk na Muftee.
Itama Maaman bata barta haka ba, an saka mata dogayen riguna irin marasa nauyin nan guda biyu, sai riga da skirt kalan purple mai matuƙar kyau.
“Allah ya saka da alkhairi Maama nah, Allah ya biya ki da gidan aljannah, Allah ya bani abinda zan biya ki dashi”
Ihsan ta amsa da “Ameen ya rabbi, sai ki tashi ki gwada mu gani”
Ganin sabon kaya a jikinta kawai ya sanya ta farincikin da bayi misaltuwa, sai juyi take a gaban fasashshen madubin da ta jingina a jikin windown parlourn tana karewa kanta kallo.
Ihsan dai kallonta kawai take kaman ba ita bace ta zuba uban ƙiba lokacin da ta haihu ba, har Taa ɗinsu yana tsokanarta da wai ta dawo cin-cin saidai tayi ta murmushi don basu saba yana zolayar su ba.
Amma yanzu ta zabge tass ta ƙare, har haiban da take dashi a da yanzu babu, kamar ba ita ake kira da ‘Ƴar ƙwalisa’ lokacin ƴammatancinta ba, har sunan gidan su a unguwan ya koma gidan su ƴar ƙwalisa dake tayi sana'ar kitso da zana baƙin lalle dayis, kana zuwa niman kwatance ka faɗi wannan sunan za'a kaika har ƙofar gidan su.
Ga farin jini da Allah ya bata ba ga zallan maza ba har mata kowa yana yin Ilham saboda Ado, kwalliya da kuma fara’arta.
Amma duk da yanzu sanye take da rigan da Ihsan har tana harsaso irin kyan da zai yi ma Ilham ɗin lokacin da aka siya sai taga bai yi mata kyan ba.
Kaman ba Fidelan da suka tashi tare bane wannan, kaman an canza ta da wata matar da ta girmeta nesa ba kusa ba.
Rayuwa kenan.
Ta ɗauke ƙwallan dake kwarmin idanunta a fakaice tare da ɗora murmushi a saman fuskarta “Yayi miki kyau”
Ilham ta juyo da murmushin da duk yanda kamanninta ya kaiga canzawa, da yin duhu, bai hana shi mata kyau ba, ga birth mark ɗinta dake ƙara bajewa a sanadiyar hakan.
Tayi ma Ihsan fari da ido tana rangwaɗa tace “wani abu sai nayi kwalliya ma.” Sai kuma ta tuna ko powder bata dashi amma ta san ba zata rasa samu a wurin Ihsan ba.
Ta ɗora da cewa “Allah sarki Islam, Yaya Aliyyu ya hanata zuwa”
“Kuma ta saka rai ba. Ta yi kuka sosai da aka ce ba da ita za'a taho ba, saida ya ɗauke ta suka je Cravings ya siya mata ice cream kafin ta haƙura. Kuma da gaskiyan shi idan muka zo har mu biyu zamu cika muku gida ne mu takurawa ya Hashimu”
“Toh tabbata zaku yi a nan ɗin? Abu na ɗan lokaci?” Ilham ta harareta.
“Zaki sani ne” Ihsan ta mayar mata da hararar sai kuma aka jawo wani hirar aka ɗora.
Hankalinta a kwance tunda Khausar da bakinta ta amince zata zauna a jikin Muftee har sai ta dawo bayan tazo tana kukan da yayi ma Ilham kama da abinda ake kira Munafurci, musamman da take mayar mata yanda ta kasance tsakaninta da Hashim a daren jiya, tana ƙara ƙarfafa zargin da Ilham ɗin take yi a kansu.
Amma Ba ita ta kira ta ba don haka bata ji nauyi ba ta tattaro ta dawo, bayan ta bata shawaran da take ganin zai fishsheta albarkacin zaman tare da kuma ƙaunar da ta nunawa Muftee koda kuwa na riya ne.
“Idan soyayya kika tsaya yi da Ya Hashim zan baki shawara khausar, idan kina da tsayayyen manemi ki bashi dama ya fito kiyi auren ki don ya Hashim bai shirya yin aure yanzu ba”
Warewa idanunta suka yi cikin tashin hankali tace “soyayya kuma Aunty Ilham? Na shiga uku!” ta ɗora hannu a ƙirji. “In rasa da waye zan yi soyayya sai mijinki? Ai sai na zama butulu. Wallahi saboda ke nake girmama shi amma babu wata soyayya a tsakanin mu.”
Ilham dai ta jita ne, amma ai ita ba yarinya bace. Ko dan bata nunawa Khausar din ita take kula da kanta da ɗanta bane take tunanin wani abu Hashim ɗin yake dashi saboda yana saka kaya masu tsada yayi ado ya fita?.
Sai dai bata sake cemata komai ba ta barta da halinta ta dawo gida tana zaman jiran isowar Ihsan.
….
ABDULHAMEED
“Daddy…”
Ta dago Jin bai amsa ta ba.
Idanun shi na kafe a kan wayan shi da yake karanta saƙon da ya shigo masa yanzun nan.
Sai ta saka hannunta biyu, harda mara lafiyan da tace ba zata iya riƙe cokali da shi ba ta tallafo fuskar shi.
Ajiye wayar yayi yana maido da duban shi kanta.
“Daddy.” Ta sake kira.
“Yes my Kiki” ya amsa yana bata sauran hankalin shi.
Sai ta saki fuskar tashi ta mishi nuni da plate ɗin plantain and chips dake tsakanin su.
“Oh sorry” ya ɗauki fork ɗin da ya ajiye ya soka plaintan ɗaya da dankali ɗaya sannan ya haɗa da scrambled egg dake gefe ya kawo bakinta, ta wangale mishi ya saka a ciki.
Ganin saƙon Excellency ne ya mantar dashi cewa abinci yake bata. Girman abinda saƙon ya kunsa kuma ya sanya shi karantawa yana sakewa don ya samu ya fahimtar da ƙwaƙwalwar shi abinda sakon ke nufi.
Kuma tsawon layi guda gare shi amma yana niman hargitsa masa lissafi.
“I'm going to run for governorship”
Shine abinda saƙon yace.
Toh shi meye nashi a ciki?.
Da sign language Ikram ta tambaye shi wani abu, sai ya girgiza kai cikin rashin amincewa “No, sai kin warke tukunna”
Ta sake daga hannu zata roƙe shi da sign language ya riƙe hannun don bayi so.
Bayi son ta tashi a matsayin nakasashshiya bayan kunnuwanta suna iya ji da taimakon na'ura, kuma akwai yaƙinin aikin da za'ayi mata a kunnen idan ta fi haka zai iya dawo mata da jinta kaman yanda ya dawo da na mahaifiyarta.
Amma bayi son sign Language ne Saboda yana tuna masa da Mahaifiyarta Ikram, His ‘I’.
Itace sanadin da ya yarda ya fara koyon sign language.
Ita ta saka yaji yana nan a matsayin ɗan Adam kamar kowa bayan ya riga da ya rasa komai.
Ita ta bashi kwarin guiwa ya dage yayi karatu har ya samu yanda zai yi ya kula da Kiki a yanzu.
“It's dangerous, so we're not going to the park until you've fully recovered”
Ta riga da ta saba da komai take so sai yayi mata koda kuwa yaƙi amincewa daga farko.
Sai ta zame daga kan kujurar dining ɗin da take zaune ta kwanta da bayanta tayi flat a ƙasa sannan ta shiga ihu tana birgima.
Ba jin ihun nata yake yi ba, amma ya san yana kama ne da ƙaran da yake ji a kunnen sa a duk lokacin da ya gwada amfani da Hearing Aid ɗin shi.
Bayi kawo masa komai sai ƙara, ko sau nawa zai shiga workshop ɗinsa ya gyara, ko sau nawa zai canza samfurin shi bayi iya jin komai bayan wannan ƙaran.
Sauƙowa yayi, ya durƙusa a kan guiwar shi ɗaya ya rike kafaɗunta da hannu biyu kada a garin haka ta fama ciwon nata da yake tsoro.
“Okay okay, we're going shikkenan?!”
Ta bar birgiman tana gyaɗa kai.
Zaunar da ita yayi ya ɗauko serviette a saman table ɗin yana share mata hawaye.
“Ohh Kiki you're a handful!”
Sai tayi masa murmushi, murmushin da ya ɗauke shi ya kaishi wasu shekaru can baya.
JAPAN 2017.
.
Babu kowa a ajin sai shi kaɗai kaman ko da yaushe, domin tun da aka kawo shi makarantar bayi zuwa ko ina daga Hostel sai class da ake masa dole, sai dining hall tunda ya daɗe da fahimtar yunwa ba ƙanin uban kowa bane. Amma duk wani extracurricular activities da za'a yi bayi shiga.
Daga inda ya kwantar da kan shi a kan desk ɗinshi dake jikin windown bayan ajin kuma yana iya kallon abinda ke faruwa a filin.
Babban filin wasa da ya haɗa kalolin mutane a cikinta, baƙaƙe, farare, Larabawa, chinese, turawa, indiyawa da sauran yaruka daban-daban har da hausawa irin shi, duka a cikin filin wasan The PEN international Academy Dake ƙasar Japan.
Saidai dalili ɗaya ne duka ya tara su a wurin.
Kasancewar su nakasassu a cikin Al’umma.
Ya cigaba da kallon yanda suka rarrabu. Masu lalurar gani sun taru a wuri guda da malaman PE ɗinsu, masu lalurar tafiya kowa a kan keken shi, haka masu lalurar ji da magana suma a wuri guda…
Kuma a cikin su ne ya hango ta, cikin uniform dinta na sport fari mai ratsin ja da kuma farin hula a kanta. Gudu take yi tana bin wani ƙwallon kafa har sai da ta samu isa gareshi ta buga, sai dai a maimakon ya shiga cikin raga sai ya bi ta bayan ragan.
Ya ɗauka zaiga damuwa a yanayinta amma dariya take yi sosai harda riƙe ciki. Sai ya fara tunanin menene abun daɗi da har zai saka mutumin da bayi ji bayi magana kaman sauran mutane dariya haka?.
zuciyar shi ta shiga angiza shi da yaje filin shima.
Ya tashi riƙe da zoben Nne wanda yazo dashi tun daga Nigeria, ya sauƙa ƙasa har filin wasan. Amma a maimakon ya shiga cikin su sai ya samu wuri a kujerun ƴan kallo kusa da inda zai ga abinda suke yin da kyau don ba ma sport wears bane a jikinsa.
Ko minti biyar bai yi a wurin ba sai ga wani ya bugo ƙwallo daga ta bayanta, ita kuma ta saka kai gaba dan haka bata gani ba.
Yayi saurin miƙewa yana ƙwala kiran “Hey!” da nufin ta kaucewa ƙwallon.
A karo na farko da ya buɗe baki yayi magana tun bayan zuwan shi.
Mantawa da itama bata ji kamar shi.
Har saida ƙwallon yayi nasaran samunta a kai sannan ta juyo tana matse fuska tare da sosa ƙeyarta.
Sai ya samu kanshi da murmusawa ko babu komai an rama mishi dukan shi da tayi a ƙeya da ruler last week.
Saka idanunta da tayi cikin nashi yasa dariyar tashi ta ɗauke, ganin ta ƙura masa idanu sai ya tsuke fuska ya kawar da duban shi daga gareta.
Yana tunanin tashi ya bar wurin sai gata tsaye a gaban shi riƙe da ƙugu tana huci.
Magana tayi mishi da sign Language.
Bai gane ba saboda bai iya ba, bai taɓa koyan koda abu masu sauƙi ne da sauƙin ganewa ba, don haka ya shareta ya cigaba da murza zoben a hannunshi.
Sai kawai ganin wasu ƴan fararen yatsu yayi sirara sun gifta a gaban idon shi, ya duba sai yaga zoben Nne dake hannun shi babu.
Ɗaga idanun da zai yi kuwa Ikram ta arci na kare tayi cikin filin, ai babu ɓata lokaci yabi bayanta da ɗan iskan gudu.
.
ƙoƙarin kawar da tunanin yayi daga cikin kan shi don yana kara masa damuwa. Ya dauki Kiki ya mayar da ita saman kujera ya cigaba da bata abinci har saida ta ƙoshi don kanta kafin ya shiryata suka fita amusement Park kaman yanda ta buƙata.
…..
ILHAM
Labulen da aka ɗaga lokaci ɗaya kaman ana yaƙi ya katse hirar da suke yi a tsakanin su. Idanun Ihsan dake zaune a kan carpet kanta a buɗe da kuma Ilham da ta saka karamin kujera a bayan Ihsan ɗin ta zauna tana kitsa mata gashin kanta suka sauƙa a kan Hashim da ko shigowar shi gidan basu ji ba tsaban hira tayi daɗi.
Aka tsaya kallon-kallo na minti guda curr.
Ita Ilham jikinta ne yayi sanyi saboda kashedin da yayi mata jiya.
Ihsan kuma kallon cikin idanun shi take yi kai tsaye babu wani girmamawa ko tsoro, shi kuma idanun Ihsan din ne suka sanya guiwowin shi suka yi sanyi a kan rashin mutuncin da yazo yiwa Ilham.
Don khausar ta tabbatar masa da Ihsan tana hanyar zuwa masa gida yau, kuma ta labarta masa abinda Ilham ɗin ta faɗa mata a kan shi.
“Sannu da dawowa baban Muftee” Ilham tace daga zaune gudun kada ta ƙarasa ya ci mutuncinta a gaban ƴar uwarta.
Sake labulen yayi ba tare da yace komai ba yana shigowa ciki.
“Filiyan ba zaki gaida shi bane?” Ilham ta buga mata ƙasan kifiya a tsakar ka ganin har zai wuce ciki tana gumm, kuma shima ya gagara cewa komai.
“wash!! Shine sai kin dake ni? Ai jira nake yi yayi mana sallama ki gani ko ba zan gaida shi ba”
Hashim bai ce komai ba, Siɗif-siɗif ya ƙara sauri ya shige ciki yana jin dama tun farko juyawa yayi ya fice a gidan.
````````
Seemahwrites ✨