Part 9
Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Written By Zulaihat Aliyu Misau
Wattpad@zulaihatualiyumisau
No comment, no vote, no update on time, eheee...
A hankali ta ke bude idonta, da takejin sun mata nauyi, p.o.p, da fankar da ke faman juyawa idonta suka fara sauka a kai, kafin ganinta ya kai kan dogon karfen da ke sagale da ledar karin ruwa. Gefen damanta ta kalla mata ce zaune a kan kujerar roba ta kifa kanta kan gadon da hubby ke kwance,. Dakin tabi da kallon, tabbas a asibiti take. Sai lokacin abubuwan da suka faru suka fara dawo mata tiryan tiryan, kamar ansa majigi.
Hawaye suka fara ambaliya, daya hannunta mai lafiyar ta daura a kan kirjinta dake zafi tare da karanto. "INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN,ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI WA AKHLIFNI KHAIRAN MINHA. "Allah ya jiqanka ya mukhtar ya gafarta maka,ya Allah ka tsareshi daga azabar qabari da fitinarsa,ya Allah gashinan yana mai buqatuwa izuwa rahamarka,kai mawadaci ne daga barin azabtar da shi,idan ya kasance mai kyautatawa ya Allah ka qara masa kan kyawawan ayyukansa,idan ya kasance mai sabo ya Allah kayi masa afuwa,ya ubangiji ga mukhtar nan,bawanka ne Allah ka gafarta masa kayi masa rahama,ka yalwata masa makwancinsa,ka wankeshi daga laifuffukansa da ruwa da qanqara kamar yadda ake tsaftace farin tufafi daga dauda,ka sauya masa gida wanda yafi gidansa,da iyali wadanda suka fi nasa,da mata wadda tafi tasa......."
Jin muryarta yasa gwaggo dagowa, daga gyangyadin daya tafi da ita.
Ganin kukan da hubby keyi, cike da ban tausayi, gwaggo ta rungumota jikinta, tana lallashinta, da kokarin kwantar mata da hankali, tare da nuna mata, yanzu fa Yusuf ba abunda yake bukata daga gareta, sama da adduarta.
Haka suka kwana, daga ita har gwaggon ba wanda ya samu damar runtsawa.
Cikin kwana daya tal amma ji take duniyar ta mata daurin huhun goro,babu abinda qwaqwalwarta keyi sai bitar rayuwarta da yusuf, idanunta sunqi dakatawa da zubda hawaye dai dai da second d'aya,cikin kwana gudan tal ta rame ta fige ta fita hayyacinta,ba ta cewa uffan sai ido kawai, da yawa yan uwa suka zo dubata a asibitin, amma ko gaisuwa aka yi mata saidai ta amsa da ka,daga jiyan zuwa yau babu abinda ta kai bakinta illa ruwa da take kurba, shi din ma gwaggo ke matsa mata shansa, sai tea lokaci zuwa lokaci idan an matsa mata,sam abincin bai iya wucewa ta maqogaronta balle ya kai ga uwar hanjinta,a washegarin ranar aka sallamota. Direct part din Mmn Yusuf aka wuce da ita, wanda tun rasuwar basu haduba., don ita tana jin maganar rasuwar ta sume. Baa samu kanta ba, sai dare can. Ita kam bata samu damar ganin gawar dan nata ba. Tana ganin Mmn Yusuf sai sabon kuka ya balle tsakaninsu,ba qaramin tausayawa hubby tayi ba,yarinya qarama amma taga jarabtar rayuwa iri iri,da qyar aka sha kansu.
Bayan sallar la'asar tana saman abun sallah tana lazumi cikin dakin gadon Mmn Yusuf,Aisha, ummu khulsum da ta iso tun daren jiya, ummu ruman, ummu sulai, samira ummul khair, sai kawayenta na family. Kowa ka kalla cike da tashin hankali da damuwa, ga carbi wasu na ja, wasu na karatun Qur'an.
Gwaggo ce ta shigo, hannunta dauke da karamin trey. Ummul khair ce ta matsa, don ta samu damar zama kusa da hubby.
Cike da tausayawa ta kalli hubby " takwara tashi, ga dan kunu na samo miki ki dan sha ko kyaji karfin jikinki, baya yuwuwa dan adam ya zauna bai ciba, a ce tun jiya banda ruwa ba abin da kika sa a bakinki." Hawayen idonta ta share " banjin yunwa, bakina daci yake, ko ruwanma dakyar yake wucewa." Ta fada cikin dasashshiyar muryarta.
" haka zaki daure ki ci abinci ko mai kan kantarsa, kar wata cuta ta shigeki, kiyi hakuri, ki dau dangana. Wanda ya mutu baya bukatar komai sama da addua, ita kuma adduar sai da natsuwa, wanda bai ciba kuwa ina yaga natsuwa, da karfin jikin da zai samu damar yin adduar? Ki daure takwara kici ko kadan ne."
Da kyar suka samu tasha kunu kadan da farfesun kifin. Tasha magungunanta da tunda aka sallamota ko kallonsu batayi ba. Sai da gwaggo ta tabbatar tasha sannan ta fita.
Muryar da taji a falo ne ya sata saurin dagowa daga kwancen da take, jikinta na faman rawa, zuciyarta na bugawa. In ba kunnenta da jiya zuwa yau yake yaudararta da kamar jin muryar Yusuf, tabbas ma yanzu kamar muryar tasa taji yana magana da yan falon.
Ko kafin takai ga mikewa tsaye da nufin fita falon. Junaid yayi sallama bayan su sulaim sun amsa ya shigo, hayder, na biye dashi a baya. Saboda tsayawar da yayi, yana kara ma yan uwan Mmn Yusuf gaisuwa.
A hankali ta gyara zamanta, tana sauke ajiyar zuciya. Hawaye na bin kuncinta. A gabanta junaid ya tsugunna ya kamo hannayenta duka biyu yana kallonta, shima idonsa na zubar hawaye. Yayin da hayder ke gaisawa da yayyennasa, tare da musu gaisuwa. Kallo daya zaka masa kaga tsantsar rama da tashin hankali a tare dashi, idon nan sun Kada jajur, sun kara shigewa ciki. Kamar yadda fuskarsa tayi ja, a lamar kuka. Abinka da farin mutun.
Aisha ke tambayarsu saukar yaushe.
" 30min ego " cikin murya mai cike da alamar rauni.
" Allah ya ji kansa, yasa aljanna ta zama makomarsa, Allah ya bamu hakurin rashinsa. What a great lost Anty!!!" Cikin muryarta da bata fita, saboda dashewar da tayi, ta amsa masa da "amin" tana kallonsa hawaye nabin kuncinta.
" take heart Anty,." Ya fada a hankali yana share mata hawayen, wanda shima hawayen ke bin kuncinsa.
Kallon yadda hubby ta koma lokaci daya ya karawa karyawa hayder jiki, tausayinta, da tausayin Mmn Yusuf yafi komai daga masa hankali,. Don yasan ba wanda zai kaisu jin mituwar, sai daddy da shi kansa. Bai San lokacin da nashi hawayen da yake kokarin boyewa suka fara saukowa ba.
A hankali ya karasa kusa da hubby " ya hakurinmu " a hankali ta dago ta kalleshi " alhamdulillah " lebbanta kawai zaka iya kalla ka gane me take fadi.
" Allah yaji kansa, ya gafarta masa."
" Amin "
Juyawa yayi ya koma wurinsu Ahmad. Junaid ya dade da ita yana kwantar mata da hankali kafin ya bi bayan hayder.
*******************
Haka aka ci gaba da karbar gaisuwa. Jamaa nata tururuwa, ta fannin ko wanne member of there family.
Su mommy Hauwa sun so Kwarai hubby ta koma gida, bayan 40days. Amma Alhaji Jamal da Alhaji babba (Yusuf zubair Oregon) suka ki.