Part 3
Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 23 min read
Written By Zulaihat Aliyu Misau
Wattpad@zulaihatualiyumisau
Not Edited.......
Baka jin komai sai karar cukula da plate.
Mommy Hauwa ta kalli Alhaji Munir. " sai ga yaronka da zukekiyar mota."
Murmushi Alhaji Munir yayi " na ganta Allah ya sa albarka."
Ajiye spoon dinta tayi " haka ma zaka ce? nifa abun ya fara bani tsoro, har yaushe suka fara business din, da zasu samu manyan kudi haka?"
Murmushi still Alhaji Munir yayi " ki kwantar da hankalinki. Shi kasuwanci sirrine, kashi casa'in na arziki yana kasuwanci. In Allah ya sa maka albarka sai kiga cikin lokaci kadan ka zama wani Abu. Kamar yadda suka fara nasu cikin nasara. Shekara uku da wani abu, ai ba yanzu bane."
" ehhhmm!! Haka dai kace."
Junaid Alhaji Munir ya kalla " kai baka mata bayanin kasuwanci naku bane?"
" na gaya mata, kawai bata yadda bane."
Alhaji Munir ya kalli mommy Hauwa "duk abun da suke yi is under our watch."
" shi kenan ai!!! Allah yasa albarka."
"Amen " suka fada baki daya. A nan Alhaji Munir ke shaida musu za a je tambayar auren jafar, yana son nan da 5month a hada dana hubby gaba daya.
Kallon jabir mommy Hauwa tayi " kayi kokari nan da lokacin ka fito da taka a hada in huta. Don na kosa in dinga ganin yan dagwai dagwai a gidan nan."
Dariya suka yi gaba daya, banda jabir dake faman Sosa keya, yana murmushi kasa kasa. " tu kunna dai mommy. "
" ba wani tukunna, ni da zaka bani zabi dana hada ka da kawar amir, Zainab. Yarinyar akwai hankali da natsuwa. Ina son yarinyar. Don haka nake fatan ko kai ko junaid ya auro min ita."
" lala!!! Ban dani." Junaid ya fada yana dariya
" nima aa!" Jabir ya fada
Alhaji Munir ya kalli mommy Hauwa " wai ke me yasa bakya son zaman lafiya ne? Ki barmin yara su zabi abinda suke so."
" ai shi kenan, Allah baku hakuri." Ta fada tana yamutsa fuska
Dariya hubby keyi kasa kasa. Ita ta rasa wannan son hada zumunci na mommy. Gashi duka are in vain.
Harara mommy Hauwa ta maka mata. Ba shiri ta Mike ta nufi dakinta, kafin mommy ta kai mata mangara, bayan ba ita takar zomon ba.
***********"*******
"Lafiya meya samu kafar?" Ummu khulsum ta fada tana zama kusa da hubby.
Hubby da ta cika tayi tam. Don bata kaunar ko kwarzane a jikinta. Ta nunama ummu khulsum in data kuje har yayi jini kadan. " subhanallahi garin Yaya?" Tsaki hubby ta yi " wannan dan banzan yaron ne, ya so yabi ta kaina da gwangwanin banza mashin dinsa."
Baki ummu khulsum ta rike. " kar ki gayamin har yanzu kina nan kuna shirmenku."
" bar miskilin banza, sai na masa dukan kawo wuka, tukun na zai shiga hankalinsa dani, in farfasa gwangwanin banza kowa ya huta."
Ummul khair dake shigowa ta fashe da dariya, jin hubby na maganar yima hayder duka. Itama ummu khulsum dariyar tayi.
" gaskiya kam, don ya gama raina ki, wata kila in kin nuna masa tsohon kashi ya shiga hankalinsa." Ummu khulsum ta fada tana dariya
" kai uhtee!! Wannan ai zuga ne! Ina hubby ina hayder? Loma biyu kawai zai yi da ke, ko in ce hadiya daya. Ki daina shiga harkarsa kawai. Don yanzu kosu Yaya Ahmad ai basa ce zasu bugeshi ba, balle ke mace." Ummul khair ta fada
" laifinta ne ai, yayi ta hon taki matsawa, da ba dan na janyeta ba da ya karairayata, yadda ya taho da gudun nan." Ummu sulaim ta fada tana shigowa da fist aid a hannunta.
Harararta hubby ta yi cikin fushi, da jin haushin maganarta " duk filin compound din nan ya rasa inda zai bi sai ta inda nake tsaye?"
" Allah ya shiryeku, ke son girma shi son girma da raini. Sai kuyi tayi, wanda ya gaji ya sake." Ummu khulsum ta fada
Zama ummu sulaim ta yi ta na ma hubby dressing din inda ta kuje.
" daga yau da dorinata zan dinga zuwa gidan nan. Don ni bazan dauki rainin hankali ba. Dukan tsiya zan masa ko ya shiga hankalinsa. Don yaga yayi tsawon kafa, bashi zai bashi lasisin raina na gaba dashi ba. Don duk ta gina ne bata shigaba. Agric chicken kawai."
Dariya sukayi gaba daya, banda hubby dake cika tana batsewa.
Ummu sulaim ta ce " ke yanzu ko cewa akayi ki bugeshi sai ki buga?"
Harararta hubby tayi " mai zai hana. Ki zuba ido ki gani, ya sake shiga gonata kiga yadda zamu kwashe."
Hayder ne ya shigo da sallamarsa, wucewa dakinsa yayi ba tare daya ko kallesu ba.
" tabdijamm!!! Anty khulsum bai fa gaishe kiba, ya wuce."
Murmushi tayi tana kallon hubby " ina zai gaisheni, bayan yanzu gani yake shine gaba damu, ya kwace girman Hajiya kuma ta goya masa baya."
" tabdijamm!!! Allah ya ragewa aya zaki, da anyi karamin yakin badar a gidan nan." Hubby ta fada
Ummul khair dariya tayi " ba abunda zakiyi ko ke din ce,. Don Hajiya ta daure masa kafa, harda wani shine uba, kuma yaya a garemu. Can u imagine, ke hatta su Yaya Ahmad shakkarsa suke. Don wani abun in yanayi har mamaki yake bani. Karfi da yaji ya kwace girman ya dora ma kansa."
Tabe baki hubby tayi " Ku kuka so, wallahi."
Hayder ne ya fito da niyyar fita. Hubby ta mike ta tareshi " dutse halan ka taka dasu ko? Kasan Allah duk randa ka kuskura ka kara aunani da gwangwanin mashin dinka, sai jikinka ya gaya maka, sannan in fasa gwangwanin banza kowa ya huta." Kallon up and dawn ya mata tare da tabe baki ya bi ta gefenta ya wuce abinsa.
" miskilin banza, dani kake zan cen." Ta fada tana zama. Su ummu sulaim kam dariya hubby ta ba su yadda ta dage adole tana masifa.
Hirar zumunci, da na shirye shiryen biki suka kafa. Duk da already an gama duk kan wani shiri daya da ce. Lokacin bikin duka duka saura 10days.
*********************
" kayi hakuri, kafi kowa sanin halin mahaifinka, wajen kafiya, munyi iya kar kokarinmu amma abun ya ci tura. Don haka ka daure ka amince da zabin sa shine zaman lafiyarka. Don ban taba ganin bacin ran Yaya ba irin wannan karon, har cewa yayi nida hajiyanka mune masu daure maka kafa, shiyasa kake son bujirewa zabinsa."
Cikin tashin hankali, suraj ya zo ya tsugunna a gabanta. " nasan kinyi kokari, amma sanin kanki ne ke kadai zaki iya sakko da daddy kan raayinsa. Na amince muddin ya yarda na auri zabin raina, zan auri doctor ita ma. Ko don in faranta masa rai."
Kada kai Anty tayi " ka kasa ganewa ne kawai. Amma wannan karon is different da sauran time din. Kafi kowa sanin mahaifinka ba zai aminta da auren bazawara ba, after all ba wani ilmi tayi mai zurfi ba. Sannan babban matsalan status din is far different."
Suraj da yake cike da tashin hankali da damuwa. Idon nan ya kada yayi jawur, shi kansa ya manta rabon da yasamu natsatsuwa da isashshen bacci. tun kan yakai maganar hubby gaban mahaifin nasa.
" wannan ba hujja bace Anty. Musulunci ya ce mu auri mata don kyanta, ko don kudinta, ko nasabarta, amma sai aka horemu da auren maabociyar addini. Me yasa Ba a ce mu zabi maabociya dukiya da nasaba ba? Saboda wannan iyakarsa gidan duniya. Bazawara kuma, kun manta manzo SAW ma da bazawara ya fara. Kinga kenan nima nayi koyi dashi, meye aibu a nan?"
" ba aibu, suraj. Amma kasan halin mahaifinka fiye da kowa. Gobe in sha Allah zan je in sameshi, ka cigaba da addua, don ita ce kawai mafitarmu a yanzu."
Duk da tashin hankalin da yake ciki, bai hana bayyanuwar murmushi a fuskarsa ba, don duk cikin dangin mahaifin nasa ba wadda yake saurarawa sama da kanwartashi. In ya tuke ita kadai ke iya lallabashi.
" na gode Anty Allah ya biyaki da gidan aljannah. "
Murmushi tayi, tana mai fatan nasara. Zuciyarta cike da tausayin suraj, don ta tabbatar yayi nisa a son hubby.
*****************
shakuwa ce ta shiga tsakanin hubby da suraj, don yanzu takan sake dashi a waya, susha hirarsu. Suraj mutun ne mai saurin sabo, ga ban dariya some times,. Satin daya yi alkawarin zuwan family nashi, basu samu zuwa ba, saboda uncle dinsa da ragamar tafiyar ke hannunsa baya kasar. So sai aka daga zuwa next week. Yanzu haka kwana uku kacal ya rage.
********************
Zaune yake a gaban mahaifin nasa. Kansa a kasa, zuciyarsa na faman bugu, don ya tabbatar yau zai samu duk kan amsarsa, in ma nasara da akasinta. Jikinsa yayi sanyi sosai ganin fuskar mahaifinsa daba wani annuri a tattare da ita. Sai dai duk da haka bazai yi saurin karaya ba.
Kallon da mahaifin nasa ya masa, yasa hantar cikinsa kadawa.
Gyara zama Alhaji saad kangiwa yayi. Cikin dakakkiyar murya wadda ba wasa ko wargi a cikinta ya ce " na samu sakonka, sai dai ka sani ban lamuta ba, bazan taba yadda ka auro min yar talakawa ba," da sauri suraj ya dago yana kallon mahaifin nashi baki na rawa " Allah daddy babanta nada arziki dai dai gwargwado." Bai karasaba Alhaji saad kangiwa ya tareshi " rufa min baki, mutumin banza. Waye Alhaji omer Oregon, ballantana shi? Ina yaron sane? Me na sama ya ci balle na kasan?. Na gama magana, yanzu haka yan aike sun dade da isar da sakona ga iyayenta. Don haka kar koda wasa inji ance an sake ganinka tare da yarinyarsu. Bakai ba ita. Sannan maganar aurenka da doctor nan da sati mai zuwa, ya rage naka kaje Ku tsara yadda abubuwan zasu kasance ko kar kaje, ba fashi. Don na lura da take yakenka in na ci gaba da zuba maka ido, mutuncina zaka zubar."
Fadin tashin hankalin da suraj ya shiga a lokacin bazai faduba. Gaba daya jinsa yake kamar a sama yana plotting. Ga kirjinsa da ya masa nauyi kamar an daura dutse. Kallon mahaifin nasa yake. Gani yake kamar an canza masa shi. Mahaifinsa mai matukar son sa, da son farin cikinsa, yau shine da kansa yake son fatali da duk wani farin ciki na rayuwarsa. Don rabuwa da hubby tamkar rabuwa da wani bari na jikinsa ne.
" tashi ka ban wuri, kar ka manta nasa matakan tsaro a kanka, koda wasa ka kuskura kayi gigin tsallake umurnina, tamuce ni dakai."
Da kyar ya kawo kansa part din hajiyansa. Rungumeta yayi, ya saki kuka kamar wani karamin yaro.
Tasan dama zaayi haka, don daga kanta aka fara, Tausayin tilon yaron nata ne cike da ranta. Taso Kwarai mahaifin ya masa adalci ya auresu gaba daya, amma yaki. saboda wani ra'ayi Mara tushe balle makama.
Lallashin suraj ta yi, tare da nuna masa muhimmancin biyayya ga iyaye, sannan ta kwantar masa da hankalin in har hubby rabonsa ce, to ba makawa sai ya aureta, in kuwa ba rabonsa bace to no matter how baza ka sameta ba. " I promise u, in har ka kwantar da hankalinka, bayan aurenka da doctor, zanyi iya yina in ga ya barka ka auri zabin ranka kaima. Amma hakan bazai samu ba, sai ka natsu ka nuna masa kayi naam da zabin sa."
Kallon hajiyansa yayi, da jajayen idonsa da suka kara kan kan cewa. " kina ganin baza suyi kokarin aurad da ita ba, kafin lokacin?"
Ajiyar zuciya tayi " shiyasa na ce ka dage da adduar ai. Sai kaga komai yazo da sauki."
" shikenan. Amma tayaya zan tari Habiba da wannan maganar? Dama da yaya na samu ta saurareni."
" yanzu kam na tabbata bayani ya isa ga iyayenta. Nasan zata nemi Karin bayani daga bakinka, then sai kayi anfani da hikimarku ta maza, ka bata baki, tare da shaida mata matsayarka."
" na tabbata gani zatayi kamar yaudararta zan kuma yi. I can tell her. "
" u have to tell her, this is the right thing."
" I will try." Ya fada in low voice.
***********
Zaune suke a falon Alhaji babba, bayan sun sallami bakinsu. Alhaji kawu ne ya kalli Alhaji babba, fuskarsa cike da bacin rai da damuwa
Zai yi magana, Alhaji babba ya katseshi.
" kar kace komai. Nasan abun da ciwo. Amma karka manta kullun cikin yima yaranmu addua ta gari mukeyi, mu dauka hakan wani alkhairi ne a garesu baki daya. Sannan ina neman alfarma kamar yadda na nema a baya, in har Habiba bata da wani tsayayye to ina son a hada da Abdul majid ko abdul Karim, kamar yadda na bukata a baya."
Ajiyar zuciya Alhaji kawu yayi, tare da kai kallonsa kan Alhaji Jamil, da abokan Alhaji Munir su biyu, sai Alhaji Jamal, da abokan shi kansa Alhaji kawu su biyu dake falon. Ya maida kansa kan Alhaji babba.
" bamu bukatar sake mai maita wannan kuskuren. Don haka koma da wanne ne a ciki na amince. Zuriata da zuriarku tamkar Abu daya ne, ko da dana bukaci a bata dama, ganin ita a yanzu bazawarace musulunci ya bata damar zabar abokin rayuwarta. Sai dai yanzu iya sanina duk masu son nata matasa ne, marasa aure, bana son a maimaita yar gidan jiya. daya ne mai iyali, shi kuma akwai dalili daya dazai hana in bashi auren Habiba. Dama mun so a hada dana dan uwanta,."
Murmushi Alhaji babba yayi irin na jin dadi. " alhamdulillah wannan Abu ya min dadi. Ban son ko kadan Habiba ta fita daga zuria ta. Shiyasa tun farko na bukaci ka yarje min in hada ta da daya daga cikin jikokina. Don haka ba fashi, nan da lokacin da akasa auren, muna fatan su samu fahimtar juna."
Duka yan falon addua sukayi da fatan alkhairi.
Taro ya watse kowa na cikin farin ciki da annashuwa, kamar ba wani abun bacin rai daya faru.
Abokan Alhaji Munir suka fara masa bayanin abunda ya faru, kafin ya koma gida, Alhaji kawu ma ya mayar masa da yadda abubuwan suka kasance. Ran Alhaji Munir ya baci sosai. Addua yayi Allah yasa haka ya zama mafi alkhairi garesu baki daya.
So koda ya koma gida mommy Hauwa kawai yama bayani, sannan ya bukaci datayi shiru tukun na, har suji daga bakin Alhaji Jamal kan wanda zaa hada dashi. Mommy Hauwa bata ji dadin wannan lamari ba, duk da dama ta dade da hasaso hakan. Don wata aminiyarta ta shaida mata akwai yar abokin kangiwa da akeson a hadasu tun shekaru biyu da suka wuce, ya ki. So ta dauka maganar ta wuce ne,ko kuma sun hakura tunda shi ya nuna baya so. Fatan alkhairi tama yarta da kudurce kara dukufa da yi mata adduar zabin nagari........
Yau ne Alhaji Jamal ya Tara iyalansa, da yaransa maza. Ahmad, Abdul Karim da hayder. Abdul fatta bai samu zuwa ba, saboda yanayin aikinsa.
Alhaji Jamal ya kalli iyalan nasa bayan ya tabbatar da duk hankalinsu na tare dashi, don jin abun da yasa ya tarasu.
" ina son tsakanin Abdul Karim da Abdul fatta daya daga cikin su, ya auri Habiba don maye gurbin dan uwansa, bai kamata ina da samari a gida ba ace nabar irin wannan natsatstsiyar yarinyar ta fita daga zuriata. Don haka na tara mu a nan don muyi shawarar wanda ya dace ya maye makwafin marigayi a cikin su biyun nan."
Kallon kallo aka fara tsakanin matan, su Ahmad dai Kansu na kasa. Mmn Yusuf ce tayi karaf ta cafke da " Abdul Karim din dai, don wannan karon bazan taba yadda amin abinda aka min wancan karon ba."
Da ido Alhaji Jamal ya tsareta " ko zaki gayamin abinda kike ikirarin an mikin?"
Cikin jin haushi ta ce " in maye ya manta, ai uwar diya bazata manta ba. Wan can karon naji Yusuf da kansa yaki nafisa, ka daure masa kafa, to a wannan karon an samu akasi, don Abdul fatta da kansa ya bani damar zaba masa mata, kuma na zabo masa, har sun aminta da juna. Don haka abi wani sarkin ba dai yayana ba."
Still idon Alhaji Jamal a kam Mmn Yusuf. " Allah ko? Duk da yaushe akayi hakan bani da labari?" Ya tambaya
Shiru tayi tana dan ture turen baki.
Numfashi ya ja " gidana ne, yaya nane, nike da ikon kafa doka a gidan nan kuma dole abi. Don haka ki bini a hankali"
Hajiya ce ta amshe da " aa gaskiya ta fada, kamar yadda kake da iko da Abdul itama tana dashi, a matsayinta na uwa. Ya kamata a mata uzuri, tunda ya samu mata, ba matsala Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu."
Harara Mmn Yusuf ta dallawa Hajiya, murmushi Hajiya tayi. Don bata manta gashin kuman da sukawa hubby a wan can karon ba, bata fatan ta kuma kasan cewa a kalkashinsu kuma. Ita hakan ma dadi ya mata.
Alhaji Jamal ya maida kallonsa ga Abdul Karim da ke zaune gefensa, kansa a kasa. " to Abdul Karim magana ta dawo gareka, ya kake gani? Zaka iya cika min wannan burin nawa ko kai ma ka samu wadda kake so?.'"
Shirune ya biyo baya, kowa idonsa na kan Abdul Karim, yana jiran yaji mai zai fada.
Mmn Yusuf ce ta katse shirun da " a bashi lokaci yayi tunani ai ko?"
Harararta Alhaji Jamal yayi, dauke idonta tayi tana fadin " Allah baku hakuri da ga fadar gaskiya."
Mmn samira da tun da suka zauna sai yanzu ta yi magana. " ka bashi lokaci yayi nazari tukunna."
Da tsananin mamaki Hajiya tabi Mmn samira da kallo. Bata taba tunanin ko a mafarki Mmn samira zata samu second true akan hada Habiba da daya daga cikin yaranta ba. Ganin yadda suke zaune kai a hade, sama da shekara talatin. Kin yadda su hada ido Mmn samira ta yi, duk yadda Hajiya taso su hada idon.
" zan cen banza, ba maganar shawara a ko aa, kawai nake son ji." Alhaji Jamal ya fada, don shma jikinsa ya fara sanyi da lamarin iyalan nasa.
" ka bashi lokacin kamar yadda suka bukata, sai dai ina son Ku Sani Habiba, bawai ta rasa manema bane, so karkuyi tunanin wai kunyi favoring dinta ne." Hajiya ta fada
Dariya Mmn Yusuf tayi " munga alama ai.?" Ta fada cikin gatse.
" ya isa haka!! Ban kiraku don Ku daga min hankali ba, don Ku baa taba abun arziki daku. Kaje na baka nan da rana ita yau, ina jiran amsa daga gareka, sai dai karku manta baku kadai bane yayana, in Ku kunki min wannan alfarma akwai masu bukata ido rufe, sai dai an ce so so ne amma son kai yafi. Ku tashi Ku tafi."
So ko a cikin gida, gaba daya Mmn samira daukewa Hajiya wuta tayi, ganin haka Hajiya ta fita a hanyarta. Sai dai mamakin Mmn samira har yanzu bai barta ba. Ita kam ko a jikinta, don ta tabbata koda Abdul Karim ko bashi hubby bazata rasa mijin aure ba. Da badon yadda take kin sauraran masu sonta ba da tun tuni ta dade a gidan mijinta. Addua da fatan alkhairi ta bi lamarin dashi, sannan ta sata cikin adduainta na musamman.
*******************
Koda suraj ya kira hubby ya mata bayani, don ya tabbatar bata da labarin abinda ke faruwa. Bata wani nuna masa damuwarta ba, duk da deep down she is broken. Ba wai tana son shi bane, aa, amma shine mutun na biyu data bashi damar shiga cikin rayuwarta.
Tattara komai tayi ta ajiye a gefe, don dama bawai auren bane a gabanta. Ta wani fanninma dadi taji, don ta dan Shana kafin su kara bijiro mata da wani zan cen aure."
Su ummu sulaim da sauran friends dinta suma abin bai musu dadi ba, amma suka bita da fatan alkhairi.
*****************
Abdul Karim Jamal Yusuf zubair Oregon. Kani ga Ahamad, Shi ke binshi a dakinsu. Ya yi degree dinsa na farko Dana biyu a Malaysia, in da ya karanta architecture yanzu haka yana aiki da ministry of works abuja. Yana da rufin asiri dai dai kwargwado Kyakyawa ne, duk gidan in ka dauke Yusuf da hayder to ba ya shi. Dan gayune na karshen zamani, cikakken womanizer, amma a boye yake alamuransa. Sai sigari da yake busawa time to time, wannan kam kowa ya San dashi. Yana son wayayyar mace mai ilmi, don duk yan matan da yake muamala dasu wayayyune, wanda ilmi da kudi suka zaunama. Burinshi duk in da matarsa ta fita a San yes ya iya zabe, ya kere sauran maza.
Hubby no way!!! She is alliterate, sannan bata waye ba ko kadan, ba irin Matar da yake muradin ajiyewa a gidanshi bace. Yasan she is beautiful and wealthy, amma shi is not his type.
*******************
Hidima ake ba kama hannun yaro. Yau gidan kamar an yashe, duk suna wurin lunching. daga iyayen amare sai tsoffi da suke ganin wurin ba wurin zuwansu bane.
Hajiya ce sai manyan aminanta biyu, Hajiya Balkisu da Hajiya Fatima. Suna zaune a falon hajiyar ana hirar duniya. Daga can suka fara jiyo magan ganu na tashi daga tsakar gidan da ya hada part dinsu.
" lafiya kuwa?" Hajiya Fatima ta fada tana kallon kafar falon.
" muryar Hajiya kaka ne, Allah yasa lafiya." Hajiya ta fada tana mikewa don ta gano abinda ke faruwa. Kafin ma ta isaga fita Hajiya kaka da kanwar Mmn samira, Hafsat suka iso bakin kofar Hajiya.
" ina kike, yar ayi ba yar a rababa. Dama tun da naga kina shishshigewa yarinya nasan kin kulla tuggun cuta. Ita kuma da yake sakarya ce, Mara tunani take biye miki, kina cutarta. To wallahi bazata sabuba. Bazan taba yadda da wannan hadin cutar ba eheee!!!." Gaba daya su Hajiya suka fito don jin ba'asin zance.
" lafiya dai ko Hajiya? " Hajiya Balkisu ta tambaya, don bata gane kan maganganun da Hajiya kaka ke fada ba.
" ina fa lafiya, ana son cutata, a cuci zuriata. Ta ya zaa dauki second hand a ba jikana, babban abun ma Mara haihuwa? Yarinyar da shekara kusan hudu ko batan wata bata taba ba, har mijin ya koma ga Allah baiga kwansa ba, saboda an asirce shi, an hanashi auro wadda zata Haifa masa yaya. Shine ni ake son a lallaba a cuci jikana ko? To wallahi bazai taba yiyuwa ba, matukar ina raye. Ni da nake fatan ganin yayan jika zaa min sagegeduwa don rashin imani."
" Haba hajiya!! Ba girmanki bane, koma menene, ki bari a warwareshi a tsanake, be kamata kina daga murya haka ba, kefa babbace." Hajiya Fatima ta fada cikin murya mai taushi, ganin yadda Hajiya kaka ta hakikance tana zuba ruwan balai, ga bakinta sai kunfa yake fitarwa.
Hafsa ce ta amshe da "haka dama ake fakewa da cin girma a cuci mutun. Ai gaskiyar Hajiya kaka ne, tana son yadda ta mallake yaya Amina, sai abunda ta ce, ta mallake mata dan da take ji dashi. Gara tun wuri ki sake lale, a nemi wani sarkin."
" ni kike gayawa wannan maganar? Ki Sani in Hajiya kaka ta fada na kyale, ke kam gidanku zanci, har kina da bakin da zaki gayamin zan cen banza? Ina abun yake?" Hajiya ta fada cikin fushi da bacin rai
Yan uwan Mmn Yusuf dake tsaye suna kallon ikon Allah.
Innani ta ce " meye laifin Hajiya a wannan magana? Sai ki jira Alhaji Jamal shida yake son hadawar kuyi dashi. Amma gaskiya wannan ba dai dai bane.
Agi ta harari innani " zancen banza kenan!!! Ai maganar Hajiya kaka a kan hanya take. Karki yarda haka ina ji ina gani, jikana har ya koma ga Allah banga kwansa ba, baya ga mallakeminshi da akayi, baya ganin kowa da gashi in ba su ba. Me ake da wannan hadi? Ko cuta? "
" ta ina zan yadda da wannan danyan hukunci? Shima Abdul Karim din ya ce bai so, don haka babu dole. A kara gaba, a sakarma jikana mara yayi fitsari, kar inji kar in gani, in fa ana son zama lafiya."
" wai gaya muku a kayi neman kai ake da ita ne da kuka, ishi jamaa da tashin hankali? Yau ya ce baya so, dubunsa nanan na jira. Meyayi zafi? Ko an ce dama dole sai jikanki ya aureta, sannan zata ci gaba da rayuwa.? Hajiya Balkisu ta fada rai a bace.
" ya dai rage naku, in gaskiya ake son kullawa, ba cuta ba, ai itama ta haifi namijin, shi ya aureta mana. Amma da yake ba Allah a ciki, zaa cuci dan kishiya." Hafsat ta fada tana barin wurin.
" aiko fadi ki kara, na haifi da daya tamkar da dubu, ke kanki kinsan hakan." Hajiya ta fada
Ido Hajiya kaka ta zaro " to in kin cika yar halas, cikin Uwale da ubale, shi ya aureta. Amma ba jikana ba."
Murmushi agi tayi " gaskiyarki Hajiya kaka tunda Allah ya raba yaba kowa, kinga tuwona maina kenan. Kai wannan abu yayi kyau." Ta fada cikin izgili
Iska Hajiya ta busar daga bakinta, ta sauke ajiyar zuciya, ta dade rabon ranta ya baci irin na yau. Murmushi tayi.
" na gode da shawararki, in sha Allah gobe iwar haka Habiba ta zama mallakin Aliyu hayder, zan nuna miki tabbas nidin yar halasce,. In kin cika ki nemowa jikan naki wadda tafi Habiba a gobe."
" gasu nan kamar jamfa a Jos, takin ce dai baa so. Tunda kun janye falillahil hamdu, aniya bi aniya. " ta fada ta juya ta nufi part din yar tata tana faman surutai.
****************
Sanye take da ankon cotton material milk sai design dark blue, dinkin riga da skert 8picess yasha adon dark blue less da yazo da material din. Dinkin ya zauna das a jikinta, tasha make-up yau kan make-up sosai ta tsaya aka mata, ga daurin head irin wanda ake yayi, gashinta da yasha gyara ya fito sosai yayi tim a bayanta. Karamin gyale ne, Mara nauyi dark blue da takalmi da jaka to match. Tayi mugun kyau, kai kace ita ce amaryar. Kana ganinta kasan tana cikin farin ciki, ga abokansu da sukayi secondary tare sunzo, sai kashe selfie suke ana shafta baka jin komai sai karar sautin DJ da dariyarsu
Kasan cewar wurin duka mata ne, yasa hubby sake jikinta.
Daga inda suke tsaye da Anty samira yana iya hango hall din, da jamaar dake ciki. Tun yana fahimtar abinda Anty samira ke fada har ya daina jinta. Gaba daya hankalinsa ya koma kan wata hadaddiyar yarinya da yake hangowa daga inda yake tsaye. Ba abunda ya kara tafiya dashi irin dirin jikinta unique, kamar murmushinta da dariyarta. Gaba daya wani irin yanayi ya tshinci kansa a ciki, mai wuyar fassarawa. Ya hadu da mata iri iri, yayi muamala dasu, amma bai taba cin karo da irin abunda idonsa ke hango masa ba. Ba abunda ya kara tayar masa da hankali, irin lokacin data tashi ta nufi wani table din dake kusa da inda take zaune. Takunta da yadda jikinta ke juyawa. Ajiyar zuciya tare da wani nishi gaba daya ya sauke lokaci guda. Da sauri samira ta kalleshi. Rufin asirinsa yana sanye da dark glass a idonsa. Da ta gama dagoshi.
" lafiya ahehh!!! Ina magana kayi min Shiru?"
Kanshi ya shafa, yana kokarin saita natsuwarsa. " ba damuwa in kin dawo ma karasa maganar, I have to go. " ya fada cikin rawar murya
" are u OK?" Ta tambaya tana tsareshi da ido, ganin yadda ya koma lokaci daya.
"I'm OK."
" shi kenan sai mun hadu a house, ka kwantar da hankalinka, komai na hannun Hajiya kaka, nasan she will handle it."
" thanks sis, shi yasa nake sonki da yawa."
Dariya tayi cike da jin dadi. " in dai ina raye ba mai makala maka abinda baka so."
" thanks " ya fada yana murmushi. Cikin dabara ya daddauki picture din yarinyar da gaba daya ta tafi da imaninsa.
Har Anty samira ta juya zata tafi, ya kirata, yarinyar ya nuna mata " waccan fah, gani nake kamar na santa, a wani wuri.?" Kallonta takai kan yarinyar, sannan ta kalleshi. Ganin ba wani alama a tattare dashi, he ask normal yasa ta tabe baki tare da Jan tsaki. " habiban da ake son manna maka ce, kasan bawai kwalliya take yi ba, kullun tana lullube kamar Matar liman, shi yasa ba lallai ka ganeta ba."
" what." Ya fada da karfi. Ganin hankalin Anty samira ya dawo kansa tana masa kallon tuhuma, ya dan wayance. " good for her. Ni na wuce." Ya fada cikin basarwa.
Da ido ta bishi har ya fice a wurin. Allah yasa ba sonta ya fara ba, don ta lura da canjin yanayinsa. Musamman yazo don su tattauna hanyar da ya dace yabi ya kubucewa auren hubby, amma gashi ko gama maganar basuyi ba ya kawo excuse, ya tafi. Bari zasu hadu a gida koma menene taji. Allah ma yasa Hajiya kaka ta aiwatar da abunda ta ce zata aiwatar, A wuce wurin.
Tafiya yake, amma gaba daya hankalinsa da tunaninsa yana kan hubby. Tabbas yaso ya cuci kanshi, bai taba tunanin haka yarinyar take ba. Wannan ai irinsu ne ake kira matan Niima. Murmushi yayi yana shafa tattausar sumar kansa. Tabbas yayi mata, ta nunawa saa, irin Matar da ko a mafarki bai yi zaton zai ci karo da ita ba. A tunaninshi is just fairy Tell ne kawai. But its real.
Yanzu kam baiga wanda zai hanashi auren hubby ba. Sauri yake ya isa gida, don ya samu su tattauna da Mmn samira da Hajiya kaka, don yasan dukansu are against the marriage.
" Habiba Abdul Karim Jamal Yusuf zubair Oregon " ya fada yana murmushi. ga picture dinta daya bude yana kallo, yaci saa kuwa lokacin tana murmushi, kyawawan hakoranta farare masu dauke da siririyar wushirya sun fito tar, saboda zooming din da yayi lokacin da zai dauka, abinka da babbar waya, kamar yana gabanta ya dauka...........
[04/03, 18:17] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA