← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 11 OF 28

                            Part 10

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 35 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau

Wani haushine ya kume hubby. Ta Dade bata ga mutun mara zuciya irin wannan bawan Allah dake gabanta ba.

Kallonta yake cike da so da Kauna, sai wani killer smile yake sake mata.

Har bata San lokacin da ta dalla masa harara ba, Tare da Jan tsaki.

Murmushi ya kara sake mata " mai nema baya fushi, mai son dan tsuntsu shi ke binshi da jifa. Na gani ina so, don haka no matter how u try bazan taba barin abinda rai ke so ba. Nasan zaki ce wannan mutun ya cika naci? But I don't care, haka nake da naci kan abinda nake so." Ya fada yana tsareta da kyawawan idanuwansa.

Ganin tana kokarin komawa cikin motar yasa ya iso da sauri ya rufe kofar da already ta bude, ya jingina jikin kofar dare da mikar da kafafunsa. Yanda bata da choice dole ta tsaya.

Saitin zuciyarsa ya kai hannunsa ya dafe yana kallonta still da murmushi akan fuskarsa. " please ki taimaki zuciyata ki tsaya ki saurareni koda sau daya ne."

Agogon hannunta ta kalla, tare da scanning din wurin, taga ba wata hanya da zata iya escaping. Kallonsa tayi tare da hada hannayenta alamar roko " na rokeka don Allah ka fita a rayuwata, ka daina bibiyata haka, ka takuramin, bana bukatar jin komai daga gareka, Please live me along."

Murmushi yayi Wanda ya bayyanar da kyawawan jerarrun fararen hakoransa.

" Habiba ke nan!! Ke kina ganin akwai abinda zai sani daina bibiyarki? Zuciyata bazata dauka ba, don bataji bata gani, in dai a kanki ne. Tunda idona sukayi arba dake a saudiyya har yau zuciyata bata samu sukuni ba. Kin San daga inda nake bugo mota duk 4 to 5 days in zo kankiya don in ganki? U don't have idea? Nazo gidanku yafi a kirga kin ki fitowa, na biki wurare da dama, kin ki saurarena. Kina tsammanin duk hakan zai sa zuciyata tayi fushi ta rabu dake?" Murmushi yayi mai sauti. Never bibiyarki kuma yanzu na fara matukar baki saurareni kin ji bayanan bakina ba."

Wani Abu ne ya tsayawa hubby a zuciyata, ga haushinsa ta taji ya kara mamayeta, ji take kamar ta man mangara mai mari ko taji saukin haushinsa da takeji.

" malan don Allah kaban hanya in tafi, kaga nayi latti. "

Tsayuwarsa ya gyara. " in kinga mun bar nan, kin saurareni ne, ko kin bani appointment din inda zamu hadu, da alkawarin zaki tsaya ki saurareni. In ba haka ba, zamu shekare a nan ni dake."

Harara ta watsa masa. Murmushi yayi tare da daga mata gira daya,.

Ganin da gaske yake, ya tasata gaba sai kallonta yake, yana murmushi. Alamar yanayin na nasa dadi, don har wani lumshe ido yake. Wanda yasa hubby kara fusata.

" ka matsa na wuce, ko nayi maka ihun barawo."

Dariya yayi, yana kallon area din. " da kin kyauta, don nasan bazan rasa masu tayani rokonki da ki tsaya ki saurareni ba. Dama ihun kwarto kikayi da, da dan sauki,. " ya fada yana kashe mata ido.

Tsaki tayi ta kauda kai.

" i like everything about u, komai naki me kyau. Hararaki, tsakinki, fushinki duk suna miki matukar kyau. Keep it up."

Ganin in har ta biyeshi tabbas zata bushe a wurin yasa ta kalleshi cikin fushi da gundura.

"Bari in baka phone number dina."

Murmushi yayi tare da ciro phone din a aljihunsa na Jeans ya mika mata.

Number tasa ta mika mai. " ban hanya na wuce."

Murmushi yayi " not so fast, let me try the number first. "

Gabantane ya fadi, tana ta shiga uku da wannan mayen, tare da rokon Allah ya rabata dashi. Don ya addabi rayuwarta.

" number baya shiga" ya fada yana kafeta da ido.

Kauda kanta tayi " phone din na gida na barshi ba charge, sai na koma zan sa a chargi sai ka kirani."

Dariya yayi " bana bukatar number, appointment nake bukata."

Kallonsa tayi, tana harararsa,don haushi bata san lokacin data furta " wai kai wane irin maye ne."

" in a kanki ne, ki kirani da fin haka ma in kinso, don bakiga komai ba, sai mun shekare a nan  tukun."

Tayi minti 2 tana tunanin yadda zata rabu da wannan mayen ta huta. " OK ka dawo nan da 1month."

Dariya yayi sosai " lallai ma, so kike zuciyata ta buga kenan."

" don Allah ka tafi, ai dai nace ka dawo ko?"

" zan zo gabe da yamma gida, in kin min alkawarin zaki saurareni fine."

hararasa tayi tana tura baki.

" kinyi alkawarin zaki fito in nazo?" Ya fada yana murmushi

Kauda kanta tayi " yes " ta fada tana daukar Jakarta data ajiye a kasa.

Murmushi yayi " thanks " ya fada yana murmushin jin dadi. Jakar ya karbe a hannunta " muje in kai miki, bana son kina wahala." Gaba yayi ba tare daya ko saurareta ba.

Jiki a sanyaye tabi bayansa, tana tunanin yadda zata bullowa lamarinsa.

Har kofar hole din yakai mata jakar, ya ba security ya karasa mata dashi cikin hole din, Sannan ya juya.

Already ta samu har an dade da fara program din. Hakuri ta basu kafin ta nemi wurin zaman da aka tanadawa members.

                 ******************
Suraj M. Sa'ad Kangiwa, da na miji tilo ga Alhaji Muhammad Sa'ad  kangiwa. Haifaffen garin kangiwa dake jahar kebbi. Mamallakin kangiwa groups of company. Wanda suke harkar sufuri, na motoci gari zuwa gari, na shiga, dana daukar kaya, har da na jirage masu taken kangiwa air lines.

Suraj yarone matashi dan shekara 30, yayi karatunsa a aviation dake Zaria, in da ya wuce   Cairo don Karin gwanan cewa a harkar tukin jirgin sama.
Yanzu haka yana  daya daga cikin matukan jiragen  company din mahaifin nasa, na kangiwa airlines limited.

Kyakyawa ne,  dogo mai dan jiki, sai dai shi baki ne, irin mai daukar idon nan, ga kuma Hutu. Yana da kanne mata uku. Biyu sunyi aure, sai autarsu.

Suraj a kwai kirki, ga kyauta, ga son jama'a,. A kwai naci a kan duk abinda yake so. Ya fara ganin hubby a garin madina a farfajiyar masallaci. Suna zaune ita da gwaggo da Alhaji Kawu. Sai abokin Alhaji Kawu, malan saminu. Su kuma suna zaune daga gefen su shida abokinsa, BK. Tun da ya daura ido a kanta, ya nemi natsuwa ya rasa. Lokaci daya yaji soyayyyarta ya ratsa zuciyarsa. Fargabansa daya Allah yasa bata da aure, don yadda ya ganta cikin shiga na doguwar riga, brawn da hijab dogo mai hannu brawn da milk. Dissent dress hatta kafarta tana sanye da sock's, daga fuskarta sai tafukan hannunta kawai kake iya gani. Wanda yasan matan aure ne suka fi yin hakan. She look classy Lady, in good dissent way. Ba abunda ya kara tafiya da shi, irin yanda take magana cikin sanyi, sanyi- shagwaba - shagwaba. Murmushinta. Su suka shagalar dashi da kallonta. Har KB ya farga da abokin nasa. Bai boye masa ba ya gaya mishi halin da yake ciki."

" baka gudun ko Matar aure ce? Daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki? Ko dai halin ne ya motsa?" KB ya jero masa tambayoyi yana tsareshi da ido

Harararsa yayi " haba duk iskancina ai banayi a kasa mai tsarki ba. In har bata da aure to nikam nayi mata, zai yi wuya in tana da aure, da gani yarinya ce karama."

" taya zaka yi ka banbance? Kar ka manta a nigeria ba wani abu bane aure da wuri, so ba abun mamaki bane in tanada shi. Kaga yanayin shigarta ma?ko ina a rufe, bayan nasan full option kake nema."

Murmushi yayi " koma ya cikin yake ina so haka, don tamin, da gani cikin ma zai yi kyau."

Dariya KB yayi " na manta dan hannu ne ashe. "

" tuba yazo tunda naga matar aure."

" Allah yasa."

" yanzu ya zaayi in samu information a kanta?"  Ya tambaya still idonsa na kan hubby

" karka damu, na san dayan hotel dinmu daya dashi, tare sukazo da his Excellency, ban san ya akayi na ganshi kuma a nan ba."

" maybe sun san juna,."

" its quite obvious, zuwa gobe in sha Allah zan samo maka duk wani information a kanta."

" na ko gode"

Har washe garin ranar suraj na cikin zullumin abunda zaiji a kan hubby. Don zuciyarsa ta gama matowa a kan sonta. Har mamakin yadda yake jinta a zuciyarsa yake.

After 2 days sannan KB ya zo masa da albishir cewar bata da aure, tana zama da kakan ninta a kankiya, amma iyayenta na Kaduna. Iya abinda ya samo kenan. Hankalin suraj ya kwanta, sai tunanin yadda zai tunkareta. Don duk ganin da zai mata suna tare da gwaggo.

A Makka ne yayi nasarar yi mata magana da suka hadu a Hilton, ya taki saa lokacin ita kadai ce. Ta fito siyan chocolate. Duk yadda yaso ta saurareshi ki tayi, don ko kallon arziki bai samu ba. Tun daga nan ya shiga bibiyarta, har ta gane, don baya samun damar yi mata magana sai tana ita kadai. Don haka ta dena fitowa ita daya.

Har suka dawo bai samu damar Isar mata da sakon zuciyarsa ba.

So koda ya dawo yana yawan zuwa kankiya musamman don ita, amma bai taba samun damar ta saurareshi ba, in yaje gidan bata fitowa, har ya gaji da tsayuwarsa ya tafi. Kusan duk inda take zuwa ba inda bai Sani ba, saboda bibiyarta, ko zai samu ta saurareshi amma ina. Sai yau Allah ya bashi Saar ritsata. After good 5month of supering. Har mamakin kansa yake yadda yan mata masu kyau da aji ke bibiyarsa yana musu yanga, yau sai gashi ta juyo kansa, shi mace da da bai dauketa komai ba, face abar holewa da jin dadi, ke ta garashi, kamar gare."

               *******************

Yau gidan gwaggo yayi albarka. Zuwan su Ahmad da kakarsu Hajiya Aisha. Bayan sun tafi sai gasu yusra da humaira kawayen hubby na secondary. Zo kaga murna wurin hubby. Tama rasa ina zata sa su don dadi. Wannan shine karo na farko da yusra ta kawo mata ziyara kankiya. Ita kanta gwaggo taji dadin wannan ziyara.

" gaskiya naji dadin ganinki, haka ake son musulmi ya zama mai tawakkali, da rungumar kaddara in tazo masa, mai kyau da mara kyau. Shi yasa kwanakin baya baki ganni ba, don yadda naji su Aisha na bani labari, sai naga bazan iya jurar ganinki a hakan ba." Murmushi hubby tayi " ya zanyi? In ma na ci gaba da daga hankalina, ba abunda zai canza. Sai dai har yanzu nakan ji wani lokacin abun ya zamemin sabo, duk yadda naso ban iya jurewa."

Dafata yusra tayi " hakane dama, baki isa ki cire shi kwata kwata a ranki ba, addua ita ce garkuwa ga mumini, in har kin ci gaba, sai Allah ya kawo miki sauki, sannan ya musanya miki da abinda yafi Wanda kika rasa alkhairi."

" Alhamdulillah addua kam inayi. Zuciyata ta danyi sanyi, bana jin kuna kamar da."

Humaira tace " Allah ya baki Wanda ya fishi, shi kuma Allah yaji kansa yasa ya huta."

" Amin" sukace gaba daya.

" ni kam na gama aure ai. Fatana in zama uwargida a wurin king dina, anan duniya da kuma can Aljannatul firdaus in sha Allah. "

Murmushi sukayi, humaira ta ce " kina wasa ne, ta Yaya kike tsammanin zasu zuba miki ido kiyi ta zama ba aure? Wannan ai tatsuniyace, mutuncin ya mace dakinta, da kuruciyarki, ko haihuwar farko bakiyi ba. Amma ki ce kin gama aure? Haba hubby ki canza tunani, nayi imanin ko shi Yusuf din bazai so haka ba."

" gaya mata dai! Wata kila Ku taji naku." Gwaggo ta fada tana shigowa falon.

Harararta hubby tayi. Daga ita har humaira

" ban san mutun na hararata ba sai naga idonsa a kasa. Ke yanzu baki gode Allah ba? Yanmata da zawarawa nawa suketa gararamba suna neman ko mai shinshinawa ne, basu samu ba. Amma ke kin samu kina wulakantawa. Jibi gidan Alhaji jibo, yan mata sun kai biyar, haka gidan Alhaji mamman ga gidan Alhaji Ibrahim duk ko wanne cike da yan mata,kuma duk a layin nan, amma ba mazan aure, ke kuwa fa? Nawa zuwa yanzu suka fito? Banda Wanda kike kora ban Sani ba."

Baki su yusra suka rike " gaskiya baki kyautawa, ni kaina da na samu mijin ai da tuni nayi aurena na huta. Amma ina kullun wannan yazo ya zuba min karyarsa, da anyi maganar ya fito baki kara ganinsa. Don Allah hubby kiwa kanki fada."

Harara hubby ta zubawa humaira " Allah ya baki na gari, keda kike nema, ni kam akai kasuwa."

Kwafa gwaggo tayi " yi iya yinki yarinya. Don muddin kika kaimu makura sai dai kiji an daura. Gara ma ki natsu ki fitar da Wanda kika ga ya dace da tsarinki."

" tabdijam!!! Asheko zaku kwance shi ba shiri. Na kusa tattara inawa I nawa in bar miki gidanki, don na lura so kike ki takurawa rayuwata." Hubby ta fada tana tura baki cike da fushi

"Allah raka taki gona, can din ma ba bakona bane ai, na dade da jin wannan zan cen."

Bayan fitar gwaggo yusra ta kalli hubby " gaskiya gwaggo ke gaya miki, yanzu shekara daya kenan da rasuwar Yusuf, ba laifi bane don kin sake aure. Aure shine gata da rufin asirin duk wata ya mace, duk abunda zaki samu, ko zaki zama a duniya, matukar baki da aure kinyi aikin banza. Kar kiyi wasa da damarki, Allah ya dube ki ya baki masoya ki natsu ki fitar da miji, kiyi aurenki."

Cikin fushi da daga murya hubby tace " Ku wai me yasa kun kasa ganewa ne? Kowa aure aure. Kina ganin zan iya wata rayuwa da wani namijin in ba Yusuf ba? Bazan iya ba, Yusuf kadai zuciyata taso shi kadai zata ci gaba da so har karshen rayuwata." Hawayen da suka ga yana bin kuncinta yasa duk jikinsu yayi sanyi, cike da tausayawa suka fara lallashinta.

" yusra ba sai na gayamiki komai ba! Ke kanki ganauce ba jiyau ba, ke zaki ba wani labarima, kinsan yadda rayuwata, da zamana da Yaya Yusuf yake. Wane namiji kike ganin zai soni, ya kula dani, koda kwatan kwacin na Yaya Yusuf ne.??? Babu, wane ne zan zamu mai nagartar Yaya Yusuf? so please live me along, Ku barni inyi rayuwata the way I want"

" I known hubby, Allah ya zaba miki mafi alkhairi, amma karki debe tsammani ga rahamar Allah. Sai kiga ya baki Wanda ma yafishi komai da komai, ke dai ki ci gaba da adduar neman zabin Allah, aduk kan rayuwarki." Yusra ta fada in carm voice.

Tsaye yake a tsakar gidan, duk abunda suke fada yana jiyosu daga inda yake. Duk da hirar da gwaggo ke masa bai hanashi maida hankalinsa don jiyo abinda ke kara karyar masa da gwuiwa ba.

Saboda ita yake yawan ziyartar kankiya a watanni biyu da haduwarsu, yazo kankiya a kalla sau biyar kenan, abunda bai taba yi ba a tarihin rayuwarsa, tun da aikinsa ya koma abuja. Sai haduwarsa da hubby da ta sace dukkan natsuwarsa. Soyayyarta ta gama ratsa duk kan zuciyarsa burinsa ta aminta dashi. Sai dai kash wadda yakeyi don ita bata ma san yanayi ba. Don duk wata hanya da zai cimmata ta toshe masa shi. Shi kuma kunya da nauyi ya hanashi ya magantu ga iyayensu. Duk da ya lura sun gama da goshi, sun dai zuba masa ido ne suga gudun ruwansa. Wannan zuwan yayi alwashin bai komawa abuja sai da gamsashshiyar magana tsakaninsa da hubby. But wannan kalaman nata da yaji yasa gwuiwarsa ta fara sanyi. Amma duk da haka yaci alwashin ganawa da ita.

" takwara kizo Ku gaisa da hashimu.? Gwaggo ta fada cikin daga murya, yadda hubby zata jiyota.

Yi tayi kamar bataji ba, sai da gwaggo ta kara maimaitawa, sannan ta amsa. Tsaki taja don ta dade da harbo jirginsa.

" ke ko lafiya kike yiwa mutane tsaki?"

Tsskin ta kuma tana kallon yusra " I hate him, naga alamar yana son takurawa rayuwata, ita kuwa gwaggo ta kasa ganewa, sai wani yashe masa hakora take kamar kantin cukula."

Humaira ce tayi dariya " lallai kin rika, gwaggo kike fadawa haka?"

Harararta hubby tayi. Yusra ce ta tambayi hubby dake kokarin zunbula hijabinta, kafin gwaggo ta fara sababi. " waye ne shi?"

" no body. Just a nevour." Murmushi dukayi a tare, don sun dago zancen.
Humaira ce ta mike, " nima bari in zo mu gaisa" mikewa yusra tayi ta gyara gyalenta. " muje nima in kwashi gaisuwa."

Da kallo hubby ta bisu ta gyabe baki tare da kada kai, a tare suka fito.

Cike da girmamawa suka gaisheshi. " aa sister baki kika yi ne?"

" eh!!" Ta fada a takaice tana kara tamke fuska.

" sannunku da zuwa" ya fada yana kallon su yusra

Gwaggo ce ta amshe da " kawayenta ne suka kawo mana ziyara tun daga Kaduna."

Murmushi yayi " masha Allah, kun kyauta, kuma kunyi zumunci. Ya karatu ko kuma yan uwan dayan ne?"

Murmushi sukayi, hubby kam tuni ta koma inda ta fito.

" karatu alhamdulillah, ni na gama, service nakeyi, wannan kuma tana final level. " yusra ta fada tana nuna humaira.

" waw wonderful." Nan yayi ta jansu da hira. Aikuwa tuni suka saki jikinsu dashi suka fara hira, Wanda yawancin labarin secondary school life dinsu ne.

Hashim kam na cikin walwala musamman jin wasu labarai na ban dariya na mutuniyarsa, Wanda suka sashi nishadi Kwarai da gaske. Hubby na daga falo ta cika   tayi tam, don haushin yadda su yusra suka saki baki sunata bashi labari suna kwasar dariya.

Hashim mutun ne mai faraa da saurin sabo, akwa hira. Shi yasa suke shiri da gwaggo.

Ya dade dasu kafin ya musu sallama ya tafi, Tare da musu kyautar 10k.

Ganin suna ta mata magana tai banza da su. Yasa yusra darawa. " Haba gimbiya a gidan doctor Hashim, Allah ya baki hakuri, don nasan haushin munsha hira da doctor ne yasa ake mana shan kamshi."

Tsaki hubby tayi " aikin banza, daga ganin mutun Ku zauna Ku saki baki, fadi baa tambaye kuba."

Dariya su kayi " because he is a nice man. He Love's u so much. Kin ga kallon da ya dinga miki kuwa?" Yusra ta fada tana dafe zuciyarta tana wani kashe ido " wow, kin tafi dashi."

Duka hubby ta Dada mata a cinya. Don't u Dare say it again."

" wai wai wai" yusra ta fada tana Sosa inda hubby ta duketa.

" meye aibunsa? To me, kun dace sosai kin san ance in kanason more rayuwar aure to ka auri Wanda ya baka shekaru da yawa. Ya fika ilmi da sanin rayuwa, so zai iya jure duk yarintar da kaje masa da ita."

Banza hubby tayi da su, sunata tattaunawarsu a tsakanin yusra da humaira, sai gwaggo data shigo daga baya. Itama ta shiga anayi da ita.

" hashimu yaron kirki ne, mata ce kawai baiyi saa ba. Bata da mutunci ko kadan, a cewarsu ashahadu a wuyansu, don ban ganiba, kar a tsaidani ranar shaida. Ance har shige shige takeyi,."  Dariya sosai su yusra keyi ganin yadda gwaggo keyi ta baki da hannu.

" Allah ya zaba mata mafi alkhairi. " humaira ta fada still tana dariyar gwaggo

" amin dai, amma ni kaina ban son auren hashimu nan da takwara. Saboda wannan shuumar Matar tasa, zai yi wuya ta bari a zauna lafiya. Shi yasa nake fatan kar ma ya samu damar furta abinda ke ransa."

Murmushi yusra tayi " nima dai ban mata fatan auren mai mata wallahi."

Sallamar da akayi ya katse masu hirarsu. Driver dinsu yusra ne ya dawo, don dama shima ya shiga gari duba wani baffansa, bayan sun bashi time din da zai dawo daukarsu. Sallama sukawa su gwaggo.

Sha tara ta arziki hubby da gwaggo suka musu, hubby ta rakosu har mota, sai da taga bacewarsu kafin ta juya ta nufi cikin gida.

Ta dafa get din gidan kenan da nufin turawa ta shiga, taji sallama daga bayanta. Tare da wani daddadan kamshi daya doki kofofin hancinta. A hankali ta juyo don ganin mai mata sallamar tare da amsawa, don sanin muhimmancin amsa sallama a musukunci. Ido hudu su kayi da.........
,
  ...Wani bakin ciki da takaicine ya cikata a lokaci daya. Nan take ta kara tamke fuska, tare da shigewa farfajiyar gidan.

Bayanta ya bi fuskarsa cike da murmushi Wanda hubby ta dauke shi a rainin hankali.

Sanye yake da black Jens, da shirt mai gajeran hannu, maron colour  mai cubes din adon baki. Kafarsa sanye da covershoe baki, sai agogo silver mai matukar daukar ido, kamar yadda gashin kansa yasha gyara tare da siririn sajen daya hade da gemun da aka sai sayeshi sosai, Wanda ya karama fuskar kyau da kwarjini. Kana ganinshi kaga big guy mai ji da ilmi da hutu, musamman yadda fatarsa ke glowing duk da yake baki.

Ganin tana kokarin shigewa ciki ta barshi yasa shi shan gabanta cikin sauri. Yana mata wani hadadden smiling mai fallasa sakon zuciya ga maabociyar zuciyar.

" me yasa kike hakane? Kin ce nazo yau. nazo tun 4:30pm ina kofar gidan nan, ina faman tunanin ta yadda zan samu mai kiramin ke, tun da kin hanani phone number, Ban samu ba. Allah yaji kaina ya turo min ke. Ta ina kike ganin zan bari ki subuce min?"

Kallon gefenta tayi, " zan fito ai, daga rakiya bai kamata aga na dade ba."

Murmushi yayi yana cikin jin dadi " OK. Ai da sai kiyi bayani." Ya fada yana bata hanya.

Da sauri ta shige cikin gidan. Da kallo ya bita yana murmushi, wani farin ciki ne ya lullube zuciyarsa. Runtse idonsa yayi yana furzar da iskar bakinsa. "Ya Allah" ya fada a hankali tuno kyawawan hannayenta masu dauke da dogayen yatsu, kumbunan dogaye sun sha adon bakin lalle, lukui lukui dasu, haka kafarta gwanin shaawa, kamar ka taba jini ya fito, duk da ba fara bace, amma tanada haske mai daukar ido, don bazaa kirata chocolate ba. Yadda ya lura da juyawar jikinta, ya sa shi shiga wani yanayi,  duk da tana sanye da dogon hijab har kasa, ash mai hannu. don ko kayanta na ciki baka iya hangoshi ta kasa. Sai plat shoe yellow mai adon White stones manya. Wanda ya kara fito da kyan kafafunta.

" ya Allah, suraj aure kazo nema fah!" Ya tunawa kansa tare da shafar sajen kansa. Yana sauke ajiyar zuciya.

"I wander abun da yarunyar nan ke boyewa cikin wannan zunbulelen hijaban, ko zafi bata ji." Wata zuciyarsa ta fada

Kujerun roba ya hango kusa da wani daki, da gani dakin megadi ne, amma bai ga alamar akwai megadin ba. Biyu ya jawo tare da zaro handkerchief a aljihunsa ya goge sannan ya gyara zamansa, kafa daya akan daya yana bin gidan da kallo. "Not too bad"  wata zuciyar ta fada

Gidane dan dai dai, ginin zamani, mai wadataccen fili, da shuke shuke.

Gwaggo ta samu a tsakar gida " har sun tafi." Ta tambayeta " eh!!!"

" To Allah ya saukesu lafiya."

" amen" hubby ta fada tana kallon gwaggo ta rasa yadda zata gaya mata.

Ganin yanayinta yasa gwaggo ta kalleta da kyau " lafiya dai ko?"

Tsaki hubby ta ja dan shiru tayi kafin ta iya lalubo abin cewa. " wannan da nake gaya miki ya takuramin tun a saudiyya, shine mukaci karo dashi, yanzu haka yana get."

Baki gwaggo ta washe " masha Allah. Maza jeki  kin barshi a tsaye, ai haka ba kyau."

Harararta hubby ta yi ganin yadda gwaggo take faraa kamar wadda akawa albishir da gidan aljanna. ". Ke maza wuce mana, kika tsayamin akai."

Har hubby ta juya zata fita gwaggo ta kirata. " a haka zaki fita? Ba dan ko gyara fuska, balle aje da bashi ruwan sha? Ke kuma kalan naki kenan?"

Juyawa hubby tayi ta fice tana mai jin haushin gwaggo dashi kansa suraj din
Bai kai matsayin da zata tsaya tana wani kwalliya saboda shi ba. Mutun daya ne, kuma yanzu babu shi. Ita yanzu neman hanyar da zata rabu da wannan karfen kafar takeyi.

Murmushi ya sakar mata, tare da nuna mata kujerar dake kusa dashi. " bismillah gimbiyata"

Harararsa tayi tare da janye kujerar can gefe ta zauna tana kallon gefenshi. Shi abun ma dariya ya bashi, ganin tazarar data bayar a tsakaninsu.

Matsowa yayi kadan, still akwai space a tsakinsau. Shirune ya biyo baya, na wasu minute.

Kallonta yake yana godiya ga Allah, tare da fatan ta zamo rabonsa. Don shi kansa baisan iya adadin son da yake mata ba.

" kiyi hakuri, nasan na matukar takura miki, I'm sorry."

Shiru tayi masa, ganin bata da niyyar tanka masa yasa ya gyara zamansa. Cikin muryarsa mai dadin sauraro ya fara da " labarin zuciya, masu iya magana suka ce a tambayi fuska. Nasan kin dade da gane manufata a kanki, but yana da kyau kiji daga bakina. Da farko sunana......" Nan ya bata takaitaccen tarihinsa da matakin da yake a yanzu na aiki, ya kara da tun ranar da idona ya sauka a kanki, zuciyata ta kamu da so da kaunarki, Wanda ni kaina ban san adadin son da nake miki ba. Tun daga lokacin na rasa walwala, da natsuwa, har sai idona yayi tozali da naki, koda bazan ji ko kalma daya daga bakin kiba. Ina fatan ki bani dama na shigo cikin rayuwarki, na tabbata ba zakiyi dana saniba, aure nake fatan ya kasance a tsakaninmu nan da dan lokaci kadan, in sha Allah. "

Shiru yayi yana kallonta da kokarin gano yqnayin da take ciki.

Wasa take da yatsunta, a hankali ta dago ta kalli gefensa, tare da sauke ajiyar zuciya. Wani murmushi ne ya subuce mata, saboda idea daya fado mata a rai. Ta dan kalleshi kadan yanda ya kafeta da tsayayyun idonsa yasa tai saurin dauke nata idon.

Dadine ya cika suraj ganin Murmushinta Wanda ya bayyanar da jerarrun kyawawan hakoranta, masu dauke da wushirya. Yana ganin Wanda murmushi ke musu kyau, amma bai taba ganin wadda mirmushi ya mata kyau irin hubby ba.

Cikin muryarta mai dadin sauraro, kamar ana busa sarewa ta ce. " na gode da kaunarka gareni. But ina baka hakuri, don abinda kake so bazaka samu ba."

Kallonta yake cike da so da kauna. Ko kadan kalmarta nata girgizashi ba, don ya dade da sanin hakan, ko yadda ta ki saurarensa yasan zai sha fama da ita. " ko zaki iya gayamin dalili?"

Sai da taja numfashi sannan ta amsa shi " ba wannan a tsarin rayuwata. Sannan kai kanka kasan abinda kazo dashi ba mai yiwuwa bane, so kayi hakuri."

Shafa kansa yayi yana Kallonta. Murmushi yayi " ko zan san dalili.?

Kallon gefen ido ta masa, cike da jin haushi don duk ta kosa ta shiga gida, jinta take kamar akan kaya. Amma ta lura wannan mutumin ya wuce inda ta ke zato a naci. So bari ta masa gwari gwari. " na taba aure, Allah yama mijina rasuwa."

Wani kishi ne ya mamaye zuciyarsa, amma yanzu ba lokacin nuna kishi bane, duk da ya dade da sanin hakan.

" I known. "Ya fada a hankali tare da karawa da " Allah yaji kansa yasa aljanna ta zama makomarsa."

" amen ya Allah. Na gode."

Ta fada, tare da jin zuciyarta na karyewa. " shine mutun na farko da zuciyata ta aminta dashi, ina fatan ya zama na karshe, so na yanke maganar sake aure a rayuwata, har zuwa nawa lokacin. Ina fatan yadda muka rayu a nan duniya, mu rayu a aljannatul firdaus in sha Allah. "

Kallonta yake yi, ya tabbatar iya gaskiyarta ta fada, don idanunta har sun kada sun canza launi. Ajiyar zuciya ya yi.

" ita rayuwa da kika ganta ba mu muke tsarawa kanmu yadda muke son ta tafi ba, huwacewa ce ta ubangiji. Ni nayi imani Allah ya kawoni rayuwarki ne don in maye miki gurbin abinda kika rasa. Don in nayi laakari da tawa rayuwar, wata uku baya duk Wanda zai gayamin zan tsinci kaina a matsananciyar soyaytar wata, tabbas zan ce karyane. Amma ta shi daya Allah ya sanya sonki da kaunarki a raina. Wanda har nake ganin in baki  rayuwata bazata yiyuba. Ina rokonki da ki bani dama, ko ban zama 100% at least  kya samu 80%. "

Shirune ya biyo baya, kowa da abinda yake sakawa.

" 1 baka taba aure ba, ni nayi for 4 good year's. 2 your billionaire only son, I'm no bodys daughter. You're educated, I'm just ordinary secondary school woman. I'm barrier women also."

Ta fada tana kallonsa " so please live me along. Kaje ka nemi dai dai kai."

Murmushi yayi " duk abubuwan da kika lissafo ba Wanda ban Sani ba. I known everything daya kamata na Sani a kanki, so please give me a chance, that all I asks for. "

" sorry. Kamar yadda na gaya maka ne, ba aure a rayuwata. So please ka gyaleni kawai."

Shiru yayi for sometime yana nazarinta da kalamanta.  " OK zan baki lokaci kiyi shawara, sannan kiyi tunani."

Kallon sa tayi kafin ta galla masa harara. " ni kam me yasa baka da ganewa ne? Bana bukatar wani lokaci, ko tunani. This is my decision."

Murmushi yayi " Allah ya huci zuciyarki, I understand  know. Ki bani phone number dinki to, ko gaisawa mu dinga yi."

Karamin tsaki taja ciki ciki. " bani da phone. "

Dariya ce ta kufce masa, yadda take wani shan magani.

Phones din dake hannunsa I phone 10, ya zare sim din ya mika mata. Kallonsa tayi, ta kalli phone din, ba tare da ta nuna ko alamar karba ba. Ta dan tabe baki " bana bukatar ta ne, Shiyasa ban rike ba, bawai don bazan iya mallakanta bane."

Murmushi yayi " na sani, nima ai bance bazaki iya mallanta bane. Amma bazan iya barin nan ba, ba tare da na Samar da wata hanyar da zan dinga jin ko muryarki ba ne. So please ki karba, yanzu zan dauko miki sim card a mota."

" kabar kayanka, don bani da ingress akan rike waya."

" kin yadda in dawo next week?" Kallon data masa ne ya sa shi sakin dariya. " I'm sorry na cika naci ko?"

Ta shi tayi ta nufi cikin gida " don't come hare again. " ta shige ciki

Murya yadan daga yadda zata jiyosa " sai nazo next week. Thanks for the time u give me. " ya juya yana murmushi ya fice.

" yarinya naki wasane yanzu muka fara." Ya fada yana tada motar.

               ********************

Tun isowar suraj a idon Hashim, har tafiyarsa. Yana daga benen gidansu yana hango wurin da suraj yayi parking, yaga lokacin da yabi hubby ciki. Zuciyarsa ta fara zafi, ya rasa sukuni, don haka ya fito ya nufo gidan. Amma abinda ya kara rikitashi ganin shi zaune da hubby a farfajiyar gidan. Da sauri ya juya.Wani nauyi ya ji kirjinsa ya masa. Sam idonsa ya rufe har baya iya ganin gabansa. Karo sukaci da abokinsa muh'd shima mazaunin unguwarne.

"Aa doctor daga ina haka? I hope lafiya, na ganka a hargitse.

Ajiyar zuciya yayi, yana Jan numfashi. "I'm in trouble friend"

Kallonsa muh'd ya yi na dan lokaci, yana nazarinsa fuskarsa dauke da murmushi. " ko dai zargin da nake ya tabbata. "

" na me fah" Hashim ya tambaya

" you're in love with habiba, right?. "

Kallon muh'd Hashim yayi, kafin yayi murmushin " yes friend. How do u known? "

" tun da naga kana sintiri a garin nan, nasan akwai bayani ai." Ya fada yana dariya.

Fitowar siraj, yasa duk hankalinsu ya koma kansa. Kasan cewar suna kusa da inda yayi parking ya sa shi yi musu sallama tare da mika musu hannu. Cikin mutunci muh'd ya mika masa, kafin ya juya ga hashim da ke dan basarwa, haka dai ya daure ya mika masa hannu. Zuciyarsa na zafi, kamar ya mangareshi.

" suraj  kangiwa right.?" Muh'd ya fada still da murmushi akan fuskarsa. shima murmushin ya masa " right " kara mika masa hannu Muhd yayi. " nice to meet u, I'm Muhammad mustafa, that my friend doctor Hashim Adam. " 

" nice to meet u too." Ya fada yana murmushi tare da musu sallama, don ya kagu ya bar wurin, ganin irin kallon da Wanda aka kira da doctor Hashim yake binsa dashi.

Bayan bacewarsa ne, muh'd ya kalli Hashim " lallai kam kana cikin matsala abokina. Suraj kangiwa da kansa?."

Cike da jin haushi, Hashim ya ce " saboda iskanci kuma ka zauna kana washe masa baki. Naso in mangare ka, daga kai har shi din."

Dariya muh'd yayi. " I'm sorry, so nake na tabbatar da cewa shidin ne."

"To yanzu da ka tabbatar sai me?"

" let go and find the place to discuss the issue."

              *******************

Gwaggo sai faman washe baki take " har ya tafi?"

Haushine ya cika hubby, so ko kulata bata yi ba ta fara cire hijab dinta.

" ke kam anyi sokuwa, kayi bako ko ruwa baki bashiba har ya tafi? Wannan ai ba hali mai kyau bane, rowa."

" ke meya hana ki dauki ruwan ki kai masa tunda kin damu da yasha?." Ta fada cikin jin haushi

" ai sai in kai masa, ina laifin mai son naka?" Gwaggo ta fada cikin son tura haushi

" sai ki sa himma ai."

" a cikinta nake kin sani, bako bai taba sa kafarsa a gidan nan ba, sai ya sha yaci na tabbatar bashi da damuwa in dai ta cikin sane."

Shiru hubby ta mata, don tasan in har ta tanka to sun dinga kenan, ita kuwa bata da lokacin wannab. She have so many things in her plates.

" ki kira mommynki, ta kira tana maganar zuwa co gurandin din su junaid ko me? Ban gane zancen ba."

" graduation, aka ce." Hubby ta fada tana murmushi.

" koma dai menene. Nayi kokari ai, tunda ba yaren qurani bane."

" kin yi kam Hajiya gwaggo. "

Murmushi su kayi gaba daya.

" bikin gama karatunsu junaid ne, za ayi next week. Tun jiya jafar ya fara min maganar. Mommy ta ce zanbi daddy da jabir muje,."

Washe baki gwaggo tayi " masha Allah, yanzu har su junaid an kammala karatu? Rayuwa kenan."

" abin ba wuya ai." Hubby ta fada

" haka ne kam, kamar yau sukazo min sallama shida balarabena. Kinga har an gama?"

Kiran sallar magriba ne, ya katse musu zancen. Kowacce ta yi alwala suka nufi daki don gabatar da sallah.

              ********************
Zaune suke gaba daya a farfajiyar gidan, dadduma ce mai kyau da laushi shimfide. Sai kayan abinci, gaba dayansu a trey daya suke cin abincin gwanin shaawa. Wannan yana daya daga cikin abinda ke sa hubby son kasan cewa da kakan nin nata. Don in kaga yadda suke gudanar da rayuwarsu abin shaawa, baka taba cewa sun kwashe irin Wannan shekaru a tare, kullun a cikin tarai rayar juna da nuna kulawa suke ga junansu.

Bayan sun kammala, hubby ta tattara wurin, kafin ta dawo kusa da Alhaji Kawu ta zauna. Cike da shagwabar data saba masa " jibi zan tafi Kaduna, zamuje graduation din junaid." Murmushi Alhaji Kawu yayi. " babanki ya min bayani dazu. Allah ya kaimu, ya dawo daku lafiya.

" amen" suka fada a tare.

Alhaji Kawu ne ya gyara zamansa. " dama ina son muyi magana, dazu su Hashim sun sameni da magana a kanki. Sai dai na shaida musu Wannan tsakanin ke da shine, don haka an jima zai zo. In kin aminta dashi mu namu addua ne kawai. Don yanzu ke kike da yancin zabawa kanki miji ba muba."

Baki hubby ta tura " gaskiya ni ban sonshi, da kawai ka bashi hakuri, ban son damuwa, yazo ya ishi mutun da surutan banza."

" aa Habiba ai baa haka. In ma bakya son sa ki bishi a hankali, a rabu lafiya, kin dai san tsakaninmu?"

Haba gwaggo ta rike" oh ni haihuwar Fulani. Hashimun ne mai surutan banza? Ko dai da na dazu zaa yi ne?"

Da sauri hubby ta kalleta " Allah ya kiyaye. Ya takurawa rayuwata ne, shi yasa kawai na saurareshi don ya fita hanyata."

Nan ta kwashe labari Kaf ta basu. " kangiwa, kangiwan da na sani?" Alhaji Kawu ya tambaya cikin mamaki

" shi " ta bashi amsa a takaice

Kada kai yayi. Gwaggo ta amshe da " mai jirgin saman da muka tafi hajji shekarar data wuce?"

Kai Alhaji Kawu ya kada mata " shifa "
Haba gwaggo ta rike, tana kallon hubby " iko sai Allah. Banda abinshi ai kwarya tabi kwarya KO, ina mai sunana ina dan kangiwa?

Murmushi Alhaji Kawu yayi " shi aure ai nufin Allah ne, in Allah yayi matarsa ce ba abun da yake gagararre a wurin Allah. Fatana Allah ya zaba mata miji na gari. "

"Amin dai" gwaggo ta fada

Sallamar da akayi ne, ya sa su maida hankali ga mai shigowar.

Saif ne, kanin Hashim. Bayan ya gaishesu ya shaida musu Hashim ne ke son ganin Habiba.

" kamar wani bako, kace ya shigo." Gwaggo ta fada fita saif yayi don ya Isar da sakon da aka aike shi.

" tashi ki sa muku kujera daga can." Gwaggo ta fada tana nuna mata gaban part din Alhaji Kawu, Wanda daga inda suke suna iya hango su, sai dai bazakaji mai ake fada ba, in ba daga murya nutun yayi ba, saboda yar tazarar dake tsakani.

Ruwa da juice gwaggo ta daura a wani karamin trey da cups. " oya dauka ki kai masa." Bata rai hubby tayi, dama a cike take tam.

Tabe baki gwaggo tayi " in mun ajiyeki gidan me zaki mana? Jikaki ki ke son muyi, musha? Ki shiga hankalinki dani wallahi." Gwaggo ta fada tana aikawa da hubby harara

Zun bura baki tayi, tare da figar trey din tayi gaba.

" kyaji dashi kuma" Alhaji Kawu murmushi kawai yake yana kallonsu.

Sai da ya karasa ya gaishe dasu gwaggo, sannan ya dawo ya zauna, kujerarshi nesa kadan data hubby. Murmushi ya sake mata. Dauke kanta tayi tana kallon gefe.

Gyara zama yayi, tare da gyaran murya. " ba sai na gabatar da kai na ba, already kin san ko ni wanene, daga ina na fito. Abu daya ne baki sani ba, ko in ce kin runtse idonki, shine irin sonki, da kaunarki da nake yi. Hakika zuciyata ta kamu da kaunarki. Fatana ki bani dama, don wallahi ba wasa ya dawo ni ba, in kin amince wata daya yayi yawa, don ni a shirye nake."

Shiru sukayi na wani lokaci, ganin bata da alamar tanka masa yasa ya kara karkace murya. " shirunki na min nuni da amin cewarki." Ai bai karasa ba hubby ta tareshi " aa. Maganar gaskiya, kayi hakuri, ba aure a rayuwata."

Murmushi yayi " ta ya zaki fadi haka? Bayan dukan mu nan aure ya samar damu?"

Numfashi taja tare da dan Kallonsa, yanda ya kafeta da ido, yasa ta daukar da nata kasa. " na san da haka. Ni dai rokonka nake da kayi hakuri, in Karin auren kakeso ga yanmata nan birgik a gari. Na tabbata ko nan cikin unguwar bazaka rasa wadda zaku dai daita ba."

Dariya yayi mai sauti " Habiba kenan,!! Na san dasu din, amma na tsallake zuwa gareki. Don ke kadai zuciyata ta zaba cikin dunbin matan nan, da ke kuma take son kulla alaka ta har abadan. In kuma nine ban miki ba ki fito kai tsaye ki gaya min. Maganar aure ta wuce wasa, duk kanmu nan ba yara bane, mun mallaki hankalin kanmu."

Duk yadda take jin haushinsa, bazata iya bude baki ta ce bata son shi ba. Duk da ko kadan har yau din nan bata kallon ko wanne da namiji da wani kallo na daban. Ta riga ta sawa zuciyarta bata ba wata alaka ta soyayya ko makamancinta tsakaninta da ko wanne da namiji, no matter how Hansom's there are.

Ganin tayi shiru, ya tabbata bazai samu wani gamsashshen amsa daga gareta ba. Duk da yana matukar son jin raayinta a kansa. " shi kenan, tunda kin ki cewa komai, zan baki time kiyi shawara,. "

Ledar dake gefenshi ya mika mata. Kallonsa tayi, ta kalli ledar. Ganin bata da alamar karba " kyauta ce, tsakanin Yaya da kanwansa. So please don't say no." Ya fada cikin muryar lallashi.

Karba tayi, tare da masa godiya. Mikewa yayi ya mata sallama. Ya tafi cike da Karin sonta da kaunarta.

Ta hada kujerun ta maida su mazauninsu, ta juya da nufin komawa wurin su Alhaji Kawu da har lokacin suna wurin suna hira.

Sunanta da taji an kirane yasa ta juyo. Ganin mai kiran yasa ta fadada faraarta. " babana daga ina haka?"

Murmushi ya sake mata, tare da jin Gina da katangar dake kusa dashi, yana kada car keys din dake hannunsa. " tunda baa nemana ai dole ki ce daga ina." Dariya tayi " ni na isa, jiya muke maganarka da dija, Ashe kana tafe."

Dadine ya kamashi, ya kara fadada murmushinsa. " really?"

" of course. Ta ina zamu manta da hero."

Dariya yayi " kun kyauta ai."

Lú" yaushe a gari?"

" jiya na iso, after ishaa. Mun sameku lafiya?.

" lafiya kalau, ya aiki? "
"Alhamdulillah." Ya fada yana gyara tsayuwarsa.

" mu karasa man, ka tsaya daga nan."

" ba matsala zan karasa ai mu gaisa dasu gwaggo. But kafin nan akwai maganar data kawoni."

Kallonshi tayi tana murmushi ba tare data kawo komai a ranta ba. " I'm all Eyer's "

" me ya kawo doctor wurinki?"

" wane irin tambaya ke nan?"

" just want to known. "

" ba abunda ya shafeka bane." Ta fada tana tsareshi da ido

" ni ko ya shafa."

" as in how?"

" because he want to take what is actually my."

Kallonsa tayi cikin son Karin bayani.
Murmushi yayi " nasan bai wuce zuwa yayi ya shaida miki yana sonki ba. Sai dai baku da ce ba. Daya ma bai iya controlling dinta ba balle ya kara. Koda yake is not my place to say so. But shine your eyes. Ni nafi da cewa dake, ni nasan zafinki, nasan kuma na fishi sonki da bukatarki. So please give me a chance, to show u how much I love u."

"Dakata babana, me kake nufi ne. I don't understand u?"

" please Habiba married me, I'm so much in love with u."

Kallonsa ta tsaya yi, kafin ta kwashe da dariya. " u are joking right? "

Serious face yayi. " I'm serious, Habiba, ba wasa cikin abinda nake fada. Tun ba yau ba nake son gaya miki. Ban samu chance ba.but amma believe me."

Rike baki tayi, tana kallonsa. " lallai ma, to kai koda auren zanyi ai baka ciki. In aureka in ce na auri wah?" Karka manta tare mukayi wasan kuruciya, Duka duka 3 months ka bani a haife. Ta ya ma zuciyarka zata baka irin Wannan lamari?"

Marai raice fuska yayi, yana hada hannunsa guri guda. " Wannan duk ba hujja ba CE, koda kin girmeni ai ba aibu bane don na aureki, kin ga nayi koyi da manzo S.A.W, balle ma na baki har wata uku. Don't say no please. "

" dallal manta da wannan maganar, in aure kake so ni da kaina zan zabo maka, in kai ka kasa. Ni yanzu ba aure bane a gabana. So muje Ku gaisa dasu gwaggo. Tayi gaba tana masa dariya

Binta yayi cikin sanyin jiki, dama abinda yake gudu kenan. Don ya dade da sanin hubby da son girma. Da wuya ta amsheshi cikin sauki, but zai ci gaba da trying don gaskiya yana sonta sosai, ba zai iya hakura ba, sai inda karfinsa ya kare.

Sun dan taba hira dasu Alhaji Kawu, kafin ya masu sallama, har get hubby ta rakosa. Sannan ta juya cikin gida.

              ********************

Munir mustafa da ga Alhaji mustafa, kani ne ga muh'd, Makota ga Alhaji Kawu.

  Munir yaro ne dan shekara 25, ya kammala karatunsa na degree a alkalam, yanzu haka a can yake koyarwa, sannan yana karatun degree dinsa na biyu. Yarone mai kokari sosai, ajinsu daya da hubby a primary shi ke zuwa musu na daya a class.

Da farko basa shiri da hubby, kullun suka hadu sai tasan abin da tayi ta sashi kuka. Saboda Alhaji Kawu na yawan mata fada, da misali da Munir Ta wurin kokari da maida hankali a karatu.

Shirunsu ya faro ne, lokacin still tana aji biyu, shi kuma aji biyar, saboda repeating da ake mata. Su kayi wani danbe ta kusa cire masa yatsa da cizo.
Alhaji Kawu ya musu sulhu ya nuna mata ko don sunan mahaifinta da munir keda shi, ya kamata ta raga masa.  Fada sosai ya mata. Wannan shine musabbabin da take kiransa babana. Daga nan kuma suka fara shiri sosai, koda ya tafi secondary school dake bording ne, in yayi hutu bini bini yana gidansu. Har barinta kankiya.

Ta fannin halitta kam Sam bashi da makusa, yana da dan kyansa dai dai kwargwado, da cikar halitta, bashi da tsawo sosai, average person.

                ****************

Alwala tayi kamar yadda ta saba kafin ta kwanta. Tayi azkar din kwanciya bacci kafin ta janyo ledar da Hashim ya bata.

Waya ce, kirar Samsung galaxy x 10 silver da mtn sim card. Tsaki tayi ta maida wayar cikin gwalinta ta ajiye a gefe. " ko an ce masa ina fatarar waya ne oho? Na rasa me yasa mutane basu da ganewa." Ta kara Jan tsaki. Tunani ne ya rufeta mu samma yadda zata rabu da wa'annan sarakan nacin. Don ta lura baza su barta ta dadin rai ba.  Tunanin King dinta ne ya dawo mata, da moment dinsu a tare, hawaye ne ya fara zarya a kumatunta. Tunawa tayi da alkawarin data dauka. Suratul ikhlas ta karanta 7× ta roka masa gafara da rahamar Allah. A haka barci yayi gaba da ita.

                 ***************

Thursday jirginsu ya daga, Daga Abuja zuwa Cyprus............

Tofa!!!!Suraj, Hashim ko babanmu Munir?
[03/03, 12:03] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 11 · 0% Book details