← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 23 OF 28

                            Part 21

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 24 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau
   
Not Edited.......

Wata uku kenan cif da bikin hubby da hayder,  suna zaune lafiya, kowanne na kokarin sauke hakkin dan uwansa dake kansa, dai dai iyawarsa.

Har zuwa lokacin ba wani maganar soyayya a tsakaninsu, sai dai akwai shakuwa mai ban mamaki.

Hubby ta kwantar da hankalinta, duk da dayawan lokaci, tana shiga damuwa. Tunowa da zamanta da Yusuf wanda gaba daya sunyi hannun riga da zamanta da hayder. Sai dai dama bata da higher expectation a kansa.

Yau su hayder suka tafi kasar India, shida Hafiz omer. Kayanta take hadawa, zuwa gidan Hajiya kafin ya dawo. Taso zuwa gidansu, amma yaki yadda. Har yanzu a tsorace take da gidan, gani take magen gidan barrister zata kara kawo mata ziyara.

Mariya ce ta dauka mata akwatin, ita kuma ta dauki Jakarta, Suka fita. A gida ta sauke Mariya ta wuce gidan Hajiya.

Cike da farin ciki Hajiya ta tarbeta. " yanzu nake kokarin kiran wayarki,"
Hajiya ta fada tana kallon hubby da faraa a fuskarta.

Cikin shagwabe fuska hubby ta zauna a kusa da Hajiya, tare da daura kanta a cinyar Hajiya. " tun dazu na keson in fito, na jira sai da Mariya tazo, yau ta makara bata zo da wuri ba."

" ya gidan? Ba dai matsala ko?" Hajiya ta tambaya.

Kai hubby ta daga mata.

Sun dade suna hira hubby na kwance a cinyar Hajiya. Shiru Hajiya taji, tana magana hubby bata amsa taba. Kanta ta sunkiyo tana kallon fuskar hubby da tayi wani gaske, sai glowing take, kamar ka taba jini ya fito. Murmushi tayi ganin hubby tayi bacci. Tashi Hajiya tayi ta gyara mata kwanciyarta, da yake 3 sitter ce, kujerar.

Ko ba komai yanzu, hankalinta ya fara kwanciya da zamansu hubby. Kara kallon hubby tayi, tayi kiba kadan, ta murje, kirarta ya kara fitowa sosai, kamar yadda kirjinta, yadan kara habaka. Tayi haske gwanin sha'awa. Masha Allah ta fada cikin jin dadi.

                 ******************

Zaune suke a reception na hotel din da suka sauka.  Ya kara cika, yayi kyau na ban mamaki. Yana sanye da black Jens da light green shirt mai dogon hannu. Kafarsa sanye cikin cover shoe black sai daukan ido yake. Jingina yayi jikin kujerar tare da runtse idonsa. Gaba daya kewar hubby ta lullube shi, bai taba tunanin zaiji kewarta haka ba. Moment dinsu yake tunowa. Bai san lokacin da murmushi ya subuce a kan fuskarsa ba.

Kallonsa Hafiz omer yake, yana kallon yadda hayder ke faman shafa sage, ido a rufe yana murmushi. Duka ya dada masa a cinya. Da sauri ya bude idonsa, da suka fara canza color. Gira ya dagama Hafiz omer " lafiya. "

Kallonsa Hafiz omer keyi, " kai zan tambaya? Nasrin ko antynmu ake tunani haka? Irin wannan smiling "

Harararsa hayder yayi " ban son sa ido."

Ido Hafiz omer ya fito dashi tare da nuna kanshi " nine dan sa idon."

Da ido hayder ya amsa shi, tare da mikewa, let live that place. "

Gyara zama Hafiz omer yayi " u can go, I'm enjoying my self hare."

"Allah ya shiryeka Hafiz, a dai dinga tsoron Allah." Hayder ya fada yana hararar Hafiz

" amen, jeka." Hafiz omer Ya fada yana murmushi

Kada kai hayder yayi, ya nufi lifter da zata kaishi room dinsa.

Gaba daya Allah Allah yake yabar wurin. yan mata ne gasunan sun sha matsatstsun kaya, wasun ma bai sake da tsirara ba, sai kai kowo suke a kansu.

Wayarsa ya dauko, zai kira hubby sai kuma ya fasa, to in ya kira ya ce mata mene? Tun da yazo da su kayi waya da Hajiya taba hubby suka gaisa, ya shaida musu ya isa lafiya, bai sake kiranta ba, haka itama batayi tunani kiranshi  ko sau daya ba. Iyaka ya kira Hajiya. Hajiya kuma, a tunaninta suna waya da juna.

Nasrin ya dannawa kira, ringing biyu ta daga, cike da jindadi.

              ********************
Yau gaba daya main house a cike yake, da yayan gidan mata. Saboda sa ranar bikin Abdul Karim da Abdul fatta da akayi, nan da 3month.

Hubby dasu Aisha, ummu sulaim, Ummul khair. Sun lume a dakin Hajiya. Don tun bikinsu, wannan ne zuwansu gida na farko.

Baka jin komai sai dararrakunsu da shewa. Ummu aiman ta shigo cike da faraa " wai yaran nan me kuke ci a dakin ne, kowa na waje, Ku kun kunshe kanku a daki, kun ishi mutane da ife -ife.'"

Dariya suka sa " an dade baa haduba, so hirar zumunci muke yi." Aisha ta fada

Zama ummu aiman tayi " in zumuncin ne, Ku fito ayi shi gaba daya mana? Ba Ku ware kanku ba."

" wannan hirar tamuce, bama son saura suji." Ummul khair ta fada. Harararta ummu aiman tayi " ai dama nasan ke kam sai addua. A dai dinga son jamaa, don jamaa rahama ne."

Kallon ummu sulaim, aiman tayi, "ke kuma Anty samira na nemanki."

Baki ummu sulaim ta tabe " banni ina nan ina kallon Matar hayder. Don Allah ko ni kadai nake ganin abinda nake gani?" Ta tambaya tana kallon su

" me kike kallo." Ummul khair ta fada tana kwantowa kusa da ummu sulaim

Hubby ta nuna da yatsanta. Dariya Ummul khair ta bushe dashi. " tun tuni nake son inji wani ya fara maganar, kar inyi nawa yayi zafi, kunsan nafi kowa daukar laifi a gidan nan." Ta fada tana dariya.

Harara hubby ta aika mata, ganin duk sun zuba mata ido, sai taji tadan muzanta. " kallon na lafiya ne?" Ta fada

Gaba daya suka sa dariya " Kinga yadda ki kai wani kyau, ki kayi jiki. Gaskiya gaba daya auren yafi karbarki." Aisha ta fada

Tsaki hubby tayi " saboda ni ce marainiyar wayonku ko? Kowacce bata kalli kanta ba sai ni?" Hubby ta fada tana huhhura hanci

Ummu aiman ta dawo kusa da hubby " Anty hubby dan gaya min anya, ba ajiyarmu a nan?" Ta fada tana daura hannunta a kan plat Tommy din hubby. Hannunta hubby ta buge.
" Allah ya kiyaye!!! Ki dai tambayesu, banda ni.?" Ta fada tana harararta

Dariya sukayi " Allah ban yadda da ke ba. Tun da na kawo miki favorite chocolate dinki naga kin ajiye baki shaba, na sa miki ayar tambaya?" Ummul khair ta fada tana kallon hubby

" don ban sha chocolate ba, bashi zai nuna komai ba, just bana jin sha a lokacin ne kawai." Ta fada tana harararsu

P - test, Ummul khair ta fito dashi a Jakarta, "gashi a gwada, in har Anty hubby bata da komai, in zama agwagwa."

Dariya suka yi, hubby da haushinsu ya isheta, ga faduwa da gabanta keyi. " zako ki zama abun da yafi  agwagwa kuwa. "

Ummu sulaim dake kallon hubby tana dariya. " ke Ummul khair meye naki na sauri? In ma shine, ai baya boyuwa."

" kunfa samin besty a gaba!!!" Aisha ta fada

" Ummul khair naga alama sai na miki wankin babban bargo kafin kibar gidan nan. In har baki fita daga idona ba." Hubby ta fada ganin yadda Ummul khair ke binta da kallo tana dariya

" Allah ya huci zuciyar Amarya a gidan Aliyu hayder. "  mikewa hubby tayi ta nufeta gadan gadan. Waje Ummul khair tayi da gudu tana dariya. Binta hubby tayi sai da ta tabbatar ta fita a dakin ta dawo, tana huci.

" karku ja mana asara, da kananan cik' kunanku kuke wannan guje -gujen." Ummu aiman ta fada tana kallon hubby

Harara hubby ta aika mata, ta zauna a bakin gadon kusa da Aisha
" da yake a ruwa ake sha ba." Hubby ta fada tana duba wayarta

Da kallo dukan su suka bita, baki sake. Ummu aiman ta zaro ido " kar dai duk kayan aikin nan, komai masha Allah, rowarsu akewa kanina."  Banza hubby ta mata, don duk haushinsu take ji.

Tabe baki ummu sulaim tayi, tana mikewa, " meye naki na damuwa Anty sulaim? Komai wayon Amarya sai ansha romonta, balle na yadda da kanina." Ta fada tana barin dakin

Ummu aiman ma baya ta rufa mata, tana hararar hubby, Don har ga Allah ta yadda da abinda hubby ta fada.

Aisha data tsare hubby da kallo, kallonta hubby tayi, ta harareta tare da Jan tsaki. " kallonfa? Me kike jira baki bisu ba?"

Murmushi Aisha tayi, hannun hubby ta kamo ta kurawa hannun ido, idon hubby ta gwale tana kallo, buge hannunta hubby tayi, " ban son iskanci, likitancin naki a kaina zai fara?" Murmushi Aisha ta sake yi. " alhamdulillah ki yadda ko karki yadda tabbas kina da ciki." Ido hubby ta zaro tana kallon Aisha, kirjinta na bugawa da sauri da sauri. A take wani tashin hankali ya shigeta. Amma tai saurin saita kanta.

Dariya tayi. " wasa kikeyi." Daure fuska Aisha tayi " bamu taba wannan dake ba, abin farin ciki ne, amma naga kina kokarin denied, bayan abunda kike nema ne, shekara da shekaru. I'm very happy for u." Ta rungumeta cike da farin ciki.

Tureta hubby tayi " u are joking right? "

" I'm not joking, in baki yadda ba, kije any   hospital a gwada." Aisha ta fada tana mikewa.

Har takai kofa hubby ta kira sunanta, juyowa tayi, tana kallonta. " please don't tell anybody." Murmushi Aisha tayi ta fice a dakin.

" innalillahi wa inna ilaihir rajiun. I'm finish." Hubby ta fada tana shafa flat Tommy dinta. Gaba daya jikinta da zuciyarta sun dau rawa. Tunani ta fara don ta gano amsar ta da kanta.

Zata iya tuna tun bayan haduwarta da hayder batayi mensuration ba. A tunaninta juyin da yake mata ne, don wani lokacin sai tayi 2 months bata yiba. A yan kwanakin kam tafi son Abu mai ruwa -ruwa, yawanci yanzu bata cika cin Abu mai nauyi ba, amma ta danganta hakan da son kartayi gaining weight. Chocolate da sauran kayan zaki ma a kwanakin bata ko sha'awasu. In banda wannan bata jin wani canji a tare da ita.

It can be possible, 4 good years tayi da Yusuf, ko batan wata bata taba yi ba, duk irin magun gunan da tasha don tayi  conceiving, amma shiru. Amma a ce yanzu wai she is pregnant, "pregnant with hayder." Ta fada kasan ranta, tana dafe kanta " no it can be." Ta fada hawaye na bin kuncinta. " ina zan kai wannan abin kunyar ni Habiba." Kwanciya tayi ta ci gaba da kukanta. Jin kamar an tunkaro dakin, tai saurin share hawayenta tare da rufe idonta kamar mai bacci.

Murmushi Hajiya tayi, ganin hubby na bacci. Ta dauki abinda zata dauka ta fita.

               ********************

" don Allah Anty hubby da gaske, maganar da kika fada dazu?" Ummu aiman ta tambaya bayan ta rutsa hubby a daki ita kadai, don abun na cin zuciyarta.

Kallonta hubby tayi cikin rashin fahimtar kan zancen " wace magana kenan?"

" ina nufin da gaske ba abunda ya shiga tsakaninki da hayder har yanzu?" Ta fada tana tsare hubby da ido.

" ba kyau bin kwakwafi Anty aiman.? Hubby ta fada tana murmushi

Harararta ummu aiman tayi " kiji tsoron Allah, kar ki cutar min da kani, kin san girman hakkin miji a kan matansa? Me yasa kike son halakar da kanki, kan wani dalili naki mara tushe? Ko kina tunanin kinfi iyayenmu sanin abinda ya dace ne? Da suka hada ki da hayder?"

Baki sake hubby take kallon ummu aiman, kai ta kada tana jin jina, son kai irin na Anty aiman. " sannu mai dan' uwa." Hubby ta fada tana tashi don tabar dakin.

Da sauri ummu aiman ta rikota " ba haka nake nufiba, kinfi kowa sanin, akwai mutane da yawa da suke zuba muku ido, suga yanayin zaman naku, ba nason a samu kofar da wani zai samu abin fade, amma kiyi hakuri, tabbas bai dace in muku shishshigi cikin lamarin aurenku ba, I'm sorry. " ta fada cikin sanyin murya.

" its OK." Hubby ta fada tare da fita ta nufi falon yara inda su Aisha suke.

Da kallo ummu aiman tabi hubby.  Hajiya ce ta shigo dakin, ganin ummu aiman a zaune ta kalleta" ke kuma lafiya kike zaune ke kadai a nan? Ina sauran yan' uwan naki?"

Ajiyar zuciya Ummu aiman tayi " nida Anty hubby ne, yanzu ta fita."  Kai Hajiya ta kada tare da bude woodruff dinta, don ta dauki kayan da zata sa, fito warta kenan daga wanka.

" amma Hajiya kina ganin zaman Anty hubby da hayder ba wani matsala?" Ummu aiman ta fada cikin sanyin jiki

Barin abinda take yi tayi tana kallon ummu aiman " me yasa kike wannan tambayar?"

" dazu muke tsokanarta a kan tana da ciki, shine take cewa wai  in ba a ruwa zata shaba ba."

Shiru Hajiya tayi, tana nazarin maganar. Juyawa tayi ta ci gaba da shirinta, ba tare da tace komai ba.

Ganin haka, yasa Ummu aiman barin dakin.

Shiryawa take amma tana nazarin maganar ummu aiman. Ita tana nan tana murna, ganin kamar hubby nada ciki, a she shirmen banza take? Kada kai tayi, yaran yanzu sai Allah ya shirya. Hubby son girma, hayder son girma, watan an rasa mai sauke nashi? In sun san wata ai basu san wata ba.
Ta wani gefen kuma tana kwakwkwanton maganar ganin, daga hayder din har hubby, sunyi kyau, sun murje abinsu, alamar kwanciyar hankali, Koma menene she will find it out.

Washe gari su Ummul khair, kowacce ta koma dakinta.

Gaba daya hubby ta shiga damuwa, gashi ta rasa hanyar da zata bi ta fita, at lest ta je ko hospital ne, amma ta rasa dabarar da zatawa Hajiya. Gashi nauyi da kunya, ya hanata ta amshi P -Test din Ummul khair.

                 ****************
Kwanan su hayder goma, a kasar India, kafin suka nufo gida Nigeria.

Hajiya tasa hubby da mai aikinta, suka gyara dakin hayder, don tun da yabar gidan ba kowa a ciki. Tare da turara, turaren wuta,  Hajiya na sane da dawowar hayder a ranar. Abunda ya kara sa jikinta sanyi, bata ga hubby na wani shirin tarbar mijin nata ba. Ya kamata tayi mata maganar zuwa share gidansu, da goge- goge, tunda sun dade basa gidan, gashi an fara sanyi. Amma hubby bata yi mata maganarba, itama share wa tayi.

Hubby kam bata da masaniyar dawowar hayder. Mantawa ma wani lokaci take dashi, sai in ta tuna da damuwarta tukun take tuno da musabbabin.

Girki na musamman Hajiya tasa hubby ta mata, aka zuba a wormars masu kyau da daukar ido.

Suna zaune a falon Hajiya, wurin 8:9 na dare. Hubby na sanye da cotton material, dinkin bubu, mai shape. Yayi mata kyau sosai ya zauna a jikinta, material din irin mai sharking din nan ne, saboda full stones. Shima Kamar yadda jikinta ke rawa, in ta motsa, haka yake sharking, tare da daukar ido. Sai gyalensa da ta rufe  kanta dashi. Simple makeup ne a fuskarta.

Tana kwance a cinyar Hajiya kamar yadda ta mayarma Hajiya cinya filo. Suna kallon news. Tare da hira jefi jefi.

" ni kam Ummi, kin shanye abinda na baki, ko yauma ajiye min shi ki kayi?"

Baki hubby ta turo, cike da shagwaba, don ji take in tana tare da Hajiya, kamar tana tare da gwaggonta ne. " zan sha anjima."

Bata rai Hajiya tayi " tashi ki dauko min, haka jiya kikayi, karshenta sai zubarwa akayi." Tashi hubby tayi taje ta dauko kofin mai cike tugudi, wanda yaji kayan kamshi. Zama tayi tana sha tana bata rai. Don harga Allah yanzu bata son Abu mai zaki, ji take har tsakiyar kanta.

Mikawa Hajiya tayi " na koshi." Karba Hajiya tayi ta duba cup din, ganin tasha ba laifi ta ajiye shi a kan side table.

Sallamar da suka ji, yasa su maida kallon su bakin kofar, Hajiya dauke da fara'a, yayin da hubby zuciyarta ke faman dukan uku- uku...........
Rungume juna sukayi da Hajiya, tana "oyo-oyo auta, bakin India."

Hubby kam daskarewa tayi a wurin tana kallonsu, tasan girman soyayyar dake tsakanin Hajiya da autan nata, bata hada son sa da kowa, cikin yayanta.

Har lokacin zuciyarta rawa take, ganin yadda hayder ya kara haske, da ciki. Sanye yake da kananan kaya. Trouser army green da White shirt, mai layi- layin army grean color. Hannunsa daure da black  I phone watch. Ga wani kamshi, mai dadi da sanyi daya cika dakin.

Zama yayi kusa da Hajiya, suka fara gaisawa, da tambayarsa hanya. " "alhamdulillah tafiya tayi riba." Ya fada yana kallon Hajiya yana murmushi.

Lallausan gashin Kansas, da yasha gyara, sai daukar ido yake, ta shafa " Masha Allah, Allah yasa albarka a abunda ake nema."

" amen." Ya fada yana kai kallonsa kan hubby, da gaba daya take kokarin jawo jaruntarta. Ido hudu sukayi. Cikin rawar murya " ka dawo lafiya."

Smacking yayi, " na sameku lafiya." Ya fada still idonsa na kanta. Don wani kyau yaga ta kara masa, daga zaunen da take, yana iya hango komai mu samman kirjinta daya kara cikowa. Shigar tata ta burgeshi sosai. Maganar Hajiya ya dawo dashi hankalinsa.

Murmushi yayi, yana shafa sajensa. Harararshi hubby tayi, kasa- kasa. Don ta lura bashi da kunyar kallo, gashi ta kasa tambayarsa abun da yake kallon, kullun ya tsareta da mayun idonsa.

Hajiya ta kalli hubby " ki shiryawa auta table. "

Tashi tayi, don ta nufi dinning. " no barshi tukun, kisa a warmer in munje gida naci, yanzu ban jin yunwa." Ya fada yana kwanciya tare da daura kansa a cinyar Hajiya. " I miss this very much. " ya fada yana lumshe ido.

" daga kai har matarka in kun karsa min cinya kun huta, kun mayarmin da cinya kamar filo."  Kara gyara kwanciya yayi, cikin shagwabar da yasa hubby sake baki tana kallon ikon Allah, duk da ba yau ta fara ganiba, amma a tunaninta ya girma yanxu. " ki daina barinta tana kwanciyamin a cinya. It's ally for me. "

Dariya Hajiya tayi. " kai ma yaranka na xuwa, ban sake yadda ka kwanta min a cinya."

" kai Hajiya, autanki ne fah? Su ma  suna da cinyar mama ai."

" tawan dai zaku bar musu, suma su Mora." Ta fada tana murmushi

Hubby kam kunya ne ya kamata, musamman irin kallon da Hayder ke mata a kai- kaice, yasa ta kasa sakewa. Mikewa tayi, zata koma dakin Hajiya.

" ki dauko akwatinki, mu tafi." Ya fada

" aa hayder! Ku kwana a nan, gobe in sha Allah ido na ganin ido, sai Ku tafi, tunda baa gyara gidan ba, gashi yanzu an fara sanyi, akwai kura. Nasa an gyara maka dakinka."

Ba haka yaso ba, " OK, bari in je inyi wanka, sai in ci abincin."

" Ummi debo masa ruwan zafi, a toilet dina. Na manta baa gyara water hitter din dakin ba."

Tashi hubby tayi, ta nufi dakin Hajiya.
Shi kuma, ya dau wayarsa ya shaidawa driver ya shigo masa da kayansa."

                ********************
Ta gama hada ruwan tana kokarin fitowa falon, shi kuma yana sawo kai dakin.

Matsawa tayi, ta bashi hanya. Kallon kallo, a ka tsaya yi, tsakanin hubby da hayder. Ganin bashi da niyyar bata hanya " Hajiya na falo, bari in wuce."

" and so." Ya fada yana daga mata gira

Kokarin bi ta gefenshi tayi ta wuce. Jefa jakar hannunsa yayi kan bed din, ya jawota zuwa jikinsa. A tare suka sauke ajiyar zuciya. Kara rungumeta yayi a jikinsa. Yayi missing everything about her,. Ga wani filling dake fusgarsa, Allah -Allah yake ya dawo gida, gashi Hajiya ta rusa masa plans, sai yanzu yayi regretting turota, da tana gidansu, ba abinda zai hanashi nemar ma kanshi natsuwa a yanzu.

Da kyar hubby ta kwace jikinta, tayi falo da saurinta.  Dafe kirjinta tayi " thanks to Allah. " Hajiya bata falon.

Jingina yayi da bangon dakin, yana maida numfashi. Ya dade a haka, kafin ya lallaba ya shige toilet. Yana jin jina, yadda yau zai iya bacci ba tare da ya sauke damuwarsa ba. Don ganinta gaba daya ya kara rikitashi.

Hajiya tasha mamakin ganin hubby kwance a falo. Kai ta kada ta nemi wuri ta zauna.

Sanye ya fito da kayan bacci farare. Yayi kyau, sai kamshi ke tashi. Direct dinning table ya wuce.

Kallo daya hubby ta masa, ta dauke kanta. Ido suka hada da Hajiya, kunya ce ta kamata. Da sauri ta mike ta nufi dinning table din, don tayi serving dinsa. Ko don ta cire zargi a zuciyar Hajiya

Hannayenta yake bi da kallo, yadda sukayi kyau, sukayi wani haske, kamar ka taba jini ya fito. Kallonsa ya kai kan fiskarta, ta kara haske sai glowing take. Bakin nan yasha pink wet lips.

Harararsa tayi kasa- kasa. Jin ya kamo hannunta, yana murzawa a nashi. Wani shock ne gaba daya ya xiyarcesu, Hajiya ta kalla, ganin hankalinta gaba daya yana kan nta news. Yasa tasa daya hannun da nufin banbare hannunta.

Duka hannun biyu, ya rike yana murzawa a hankali. Kiss ya mata a hannun, sannan ya saketa, ganin yadda take a tsorace.

Abincin ya masa dadi, amma darene, don haka kadan yaci, ya hada green tea. Ya koma kusa da Hajiya yana sha suna hira sama - sama.

Mikewa hubby tayi ta shige dakin Hajiya, wanka tayi, ta sa kayan baccinta, tare da feshe jikinta da turare masu sanyin kamshi. Tayi kwanciyarta.

Tsayawa Hajiya tayi, tana bin hubby dake sharar baccinta hankali kwance da kallo.

" Ummi, Ummi." Hajiya ta fada tana dukan kafar hubby kadan.

Bude ido hubby tayi mai cike da bacci, tana kallon Hajiya.

Daure fuska Hajiya tayi. " oya tashi ki wuce wurin mijinki, bazaki kwana min a nan ba."

Ido hubby ta zaro, tare da shagwabe fuska tana turo baki. Zatayi magana Hajiya ta katseta. " tashi kafin ranki ya baci, bada ni zaayi wannan rashin hankalin ba." Mikewa hubby tayi, tana tura baki. Zani ta daura akan kayan baccin, tare da zunbula hijab dinta. Hajiya na kallonta, bata ce komai ba. Sai da tazo zata fita, ta kirata. Dawowa tayi, Flack's Hajiya ta mika mata, irin 5 liter electric Flack's, wanda zaka jona shi da wuta, kamar kettle.

Kallon Flack's din tayi, ta kalli Hajiya cikin rashin fahimta. " kije dashi, ko zakusha tea."  Dauka hubby tayi ta wuce, cikin sanyin jiki. Ajiyar zuciya Hajiya taja tare da shirin baccinta ta kwanta.

A hankali ta tura kofar ta shiga. Kwance yake yana juyi, gaba daya hankalinsa a tashe yake, tunanin yadda zai fito da hubby daga dakin Hajiya yake yi, don gaskiya bazai iya hakuri ba. Yaji an bude Kofa an shigo. Ajiyar zuciya yayi, tare da fesar da iskar bakinsa. Wani dadi ne ya ziyarci zuciyarsa tare da furta " alhamdulillah" a saman labbansa.

A kan table ta ajiye Flack's din. Dakin tabi da kallo, a tunaninta yayi bacci, ganin wuta a kashe, sai hasken fitilar waje dake hasko dakin. " wannan Flack's din kuma fah?" Ya tambaya yana tashi zaune.

Gabanta ya fadi, jin maganar kamar daga sama. " Hajiya ta ce in taho dashi, ko zaka sha tea." Murmushi yayi yana shafa kansa. Tare da godewa Hajiya a ransa.
" ta kyauta kam, kamar tasan ina da bukatarsa sosai."

Kofar fita hubby tayi, da sauri ya tsayar da ita. " ina kuma zaki?" Ya tambaya yana kallonta

" wai zan kawo maka kayan tea din ne." Ta fada

Smacking yayi, Tare da mika mata hannunsa. " I have them already, let me show u." Dawowa tayi ta tsaya, ba tare data mika masa hannunba.

" ban son Jan aji, I know you Miss me." Ya fada yana jawota ta fada saman jikinsa, in da ya mata kyakyakyawar runguma. " please hayder, Hajiya nanan, she can hear us."  Hayder kam bama ya jinta, hijab din da zanin ya zame ya watsasu gefe.

Gaba daya jikinsu, rawa yake, hubby kam harda na tsoron kar Hajiya ta jiyosu. Don dakunan a Jere suke da juna. Hayder kam tsabar bukatuwa, yasa yama manta da Hajiya can hear them.

Hajiya kam ranar kwanan dakinta, bai samu ba, sai dakinsu ummu sulaim ta kwana. Hankalinta kam yanzu ya kwanta, dama abinda take da bukatar tabbatarwa kenan.

Tunaninta da wane idon zata kalli Hajiya, don ta tabbatar ba abinda zai hanata jiyosu, kasan cewarta mutun mara nauyin bacci. A gogon gefen gadon ta kalla 4am dai dai lokacin da hayder ya fito daga toilet din. Jallabiyya ya zura, tare da shinfida dadduma ya kabbara sallah.

Tashi tayi, duk jikinta yayi tsami.  Tsaki tayi a hankali, taga alama ciwon bacci sai ya kamata in batayi da gaske ba, a ce mutun baya gajiya, a dare sai tayi wanka ya kai  hudu- biyar. Duk don karta kwanta da najasa, amma sai ya San yadda yayi, ya bata mata wankanta.

A hankali ta bude dakin ta fita, dakinsu Ummul khair ta wuce, ga mamakinta, mutun ta gani kwance a kan gadon ummu sulaim. Da sanda ta nufi dakin Hajiya. Ganin bata dakin ta sauke ajiyar zuciya. Toilet ta wuce, ta tsarkake jikinta, tare da dauro alwala.

Hand rayed tasa ta busar da kanta. Ta maida kayan baccinta. Sai da tayi sallar asuba, sannan ta dale gadon Hajiya, taja bargo nan da nan bacci yayi gaba da ita.

Hajiya na kallon hubby, murmushi tayi tana binta da kallo, yadda take sanda abin ma har yaso yaba Hajiya dariya. Wai nan ita a dole mai wayau. In dauka kamar a dakinsu ummu sulaim ta kwana. Hubby na fita, ta tashi ta dauro alwala ta kabbara nafila.

Sai to 9, ya shigo gidan tun daga fita sallar asubah. Ba kowa a falon, kai tsaye yayi dakin Hajiya. A gadonta ya hango hubby lullube da bargo, tanata bacci, hankalinta kwance.

Karasawa yayi dai -dai fuskarta, lallausan hannunsa yasa yana shafa fuskarta a hankali, gyara kwanciyarta tayi " lazy bone." Ya fada yana sumbatar goshinta.

She look beautiful, sai yanzu ya kara karewa fuskarta kallo,ta kara kyau, tayi haske kamar ka taba jini ya fito, bakinta ya kai idonsa da zagayen bakin ya kara bifowa sosai,. Bakinsa ya kai ya sumbaci labbanta, sannan ya fita. A falo suka ci karo da Hajiya tana shigowa.

Rungumeta yayi, tare da gaisheta. Cike da faraa Hajiya ke amsawa, tare da tambayar gajiyar hanya.

" alhamdulillah. " ya fada yana nufan dinning table.

Yana fita, ta mike, tare da kai kallonta kan agogon dake makale a bangon dakin yana kallonta, After 9. Da sauri ta sakko daga gadon, cikin sauri sauri ta gyara gadon, tare da gyara dakin. Wanka ta shiga, bayan ta fito ta shirya cikin wani red Chinese dress, mai matukar kyau da santsi.  Riga da wando. Simple makeup tayi, cikin sauri take shiryawa don ko Hajiya bata gaisar ba.  Red Vail ta yafa, Wanda ya dace da kayan, ta feshe jikinta da turaruka bayan deodorant da humra, ta tasa a jikinta.

Cike da jin nauyi ta gaishe da Hajiya. Cike da faraa take bin hubby da kallo. " masha Allah, wannan kwalliya tayi kyau. Kamar mai zuwa gasar sarauniyar kyau?" Hajiya ta fada dariya hubby tayi " tsarabar China da junaid ya kawo min."

" ya kauta, sunyi kyau, suka kuma tarar da kyan."  Hajiya ta fada tana mikewa " maza kije kici abinci, gashi can har ya huce." Ta fita a falon

Gaba daya idonsa na kanta, tunda ta fito, kamshin turarenta ya fara masa sallama, gaba daya shigar tata ta matukar burgeshi, kayan sun mata matukar kyau, kamar don ita aka halittasu. Kasa dauke idonsa yayi a kanta.

Takunta da yadda jikinta ke juyawa, gwanin sha'awa ya zuba ma ido, yana tasbihi a ransa.

" ban son kallo." Ta fada a hankali tana Jan kujerar dinning din daya, ta zauna.

Smacking yayi " its my property. " ya fada in his husky voice

Gug din kunu ta jawo ta zuba a cup. Ta kai bakinta, Still idonsa a kanta. Harararsa tayi, ji take kamar ta makeshi, wannan murmushin rainin hankalin da yake binta dashi.

" kayan sunyi kyau, ina imagining dinsu a jikin My Nasrin." Ya fada

Sai da ta hadiye kunun bakinta cikin tabe baki. " in kana so, sai in cire ka kai mata."

Jingina yayi da kujerar sosai, yana shafa sagensa. " ya zama second use."

Tabe baki tayi " good for u."

Waina da soup din kayan cikin, data zuba zata ci, ya janye gabansa.

Kada kai tayi, ta zuba wani.

" ki shirya da wuri." 

Kai kawai ta daga mishi.

Mariya ce ta shigo, ita da mai aikin Hajiya. A nan take shaidawa hubby tun safe Hajiya ta sasu suka je gyaran gidan, dawowarsu ke nan.

Hubby taji dadin hakan.
              *******************
Hajiya da Hajiya Balkisu, suna zaune a falon Hajiya suna hira irin ta aminan juna. Don zuwan Hajiya Balkisu kenan bata dade ba. Hubby ta fito rataye da Jakarta. Ganin Hajiya Balkisu yasa ta rusuna tana gaisheta. Cike da faraa take amsa mata, tare da tambayarta mai gidan.

" yayi, tafiya ne, shine aka zomin kwana biyu, Jiya ya dawo. So zasu tattara suyi gidansu." Hajiya ta fada cike da jin dadi.

" Masha Allah, mun gaisa da hayder din ai yanzu da zan shigo."

Sallama hubby ta musu, cike da kewa Hajiya ta sallameta, part din Mmn samira da Mmn Yusuf taje ta musu sallama, ta fito already hayder na cikin motarta driver sit yana jiranta.

              *******************
" kinga ikon Allah ko? Wannan shine rabo ajali." Kallon  rashin fahimta Hajiya kebin Hajiya Balkisu dashi. " ban gane maganarki ba." Hajiya ta fada

Baki Hajiya Balkisu ta rike " kar dai ace, baki hango abinda na hango ba, duk kwana kin nan da kukayi tare?"

Zama Hajiya ta gyara, tana fuskantar Hajiya Balkisu da kyau. " kin kara Sani a duhu."

Cike da mamaki Hajiya Balkisu ke bin Hajiya da kallo " zaki ce min baki ga alamun ciki a tattare da Habiba ba?"

Kara gyara zama Hajiya tayi " ciki fa kika ce?" Ta tambaya

" sosai ma kuwa ciki." Hajiya Balkisu ta fada With Confidence

" kinsan ni in ba laulayi naga mace nayi ba, bana ganewa, sai kuma in ya fito."  Hajiya ta fada

" lallai kuwa, amma tabbas ciki ne jikin Habiba. "

Da sauri Hajiya ta tashi ta rungumeta Hajiya Balkisu cike da farin ciki. Dariya Hajiya Balkisu tayi. " auta ya girma, mun kusa zama kakan nin asali."

" kai!!! Na so in zargi hakan, amma ganin ba wani laulayi take ba, na dauka kawai cikar daki ne, da kwanciyar hankali. Ashe abin farin ciki ne? Wai!! Allah na gode maka, daka nunamin wannan rana ta farin ciki. Yau ina masu kiran Ummi juya? Yanzu kuma mai zasu fada kenan?"

" barsu tukun, Lokacin maida martani na nan zuwa, very soon." Hajiya Balkisu ta fada tana murmu
.........

 
[09/03, 10:43] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 23 · 0% Book details