← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 28

Part din Alhaji Jamal ta ja hayder don gidan ba masaka tsinke da jamaa.

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Duk da faduwar gaban da yake, bai yadda ta gane tashin hankalin da yake ciki ba. Bata kawo komai ba, ganin ya dan fada mata, ta daukeshi matsayin stress.

Kallonsa tayi cikin natsuwa. " meye matsayina a wurinka? Da sauri ya dago yana kallonta cike da far gaba.

Sunkuyar da kansa kasa yayi, yana jin zuciyarsa na karyewa. Saboda tuno girman matsayinta a wurin shi.

" matsayinki gareni ya wuce yadda labba da harshena zasu bayyana, kamar yadda girman hakkinki a kaina ya girmama, har musulunci ya mana umurnin kyautatawa gareku,  saboda girman matsayinku, ya sanya aljannarmu a kalkashin kafafunku, wanda sai kun daga kafin mu samu damar shiga aljannah, wadda take burin duk mai imani."

Murmushi Hajiya tayi, tana kokarin maida hawayenta. " ina neman alfarma a gareka, zaka iya mun?"

" umurni kawai zakiyi, bakya bukatar alfarma a gareni. Ni da duk abunda na mallaka muna kalkashin ikonki ne, duk abinda kika ce, matukar bai kauce wa shariar Islam ba, an gama."

Hawaye mommy dake kokarin mayarwa suka fara bin kuncinta. Hakika hayder ya cika dan halas da daya tamkar da dubu, abin alfaharinta. Hakika tana daya daga cikin iyaye masu saar yaya a duniya. ba abunda zata ce sai Alhamdulillah.

" an taba mutuncina, an yi challenging dina in har na cika yar halas in aura ma ummi." Tayi shiru tana goge hawaye

Da sauri ya taso zuwa inda take zaune, rigarsa yasa yana share mata hawayenta, bai damu da kwalin da ya samu wurin zama a fararen kayan jikinsa ba. Ya fara lallashin Hajiya.

" in wannan ne ki kwantar da hankalinki, na miki alkawarin zan auri Habiba, kamar yadda kika bukata."

" na gode hayder Allah ya maka albarka, ya baka yaya na gari, ya baka abinda bazai kareba, ya karemin kai daga dukkan sharri."

"Amen "ya fada

" ka je ka fara shiri, don in an sakko masallaci zaa daura auren. Sunday zata tare, already an samu gidan da zaku zauna, yanzu zan je mu gani, bayan daurin aure sai kuje kuma, in akwai gyare gyare ko wani abu da ake bukata. Sauran kayan lefe duk zanyi in sha Allah sai kayi alfahari da wannan auren."

" na gode sosai, amma ki bar min kayan lefen zanyi da kaina, in kunyi estimate din amount din kwa gayamin in bayar."

" shi kenan." Hajiya ta fada a part din ta barshi, don ya kulle tunda ba kowa. Tana fita ya hada kanshi da gwuiwa ya saki wani marayan kuka. Rabonsa da ya samu kanshi cikin irin wannan tashin hankali da bakin ciki, har ya manta.

Sai daya sha kukanshi, ya shiga toilet din daddy ya wanke fuskarsa, ya nufi masaukinsu.

Zuciyarsa cike da tsana da jin haushin hubby. Adduar yaye bakin ciki yayi ta maimaitawa saman labbansa har ya isa. Sultan guise inn dake kusa dasu. Don tunda aka fara biki, shida su Hafiz omer sukayi kaura zuwa can.

               ******************

Gida yayi kyau, well polished. daga Hajiya har su, Hajiya Balkisu gidan ya burgesu.  Duplex ne, falo biyu a kasa, kowanne da toilet dinsa. Sai kitchen, store, sai dan karamin daki a karamin falon. Sama kuma dakunan bacci ne guda uku da falo daya. Kowanne  bedroom da toilet dinsa. Gidan akwai fili sosai, da motoci kusan goma zasu iya parking, yasha interlock. Ga shuke shuke na fruit da flawers, sai dakin maigadi da toilet. Gidan na Unguwar malali ( sami close) sabon ginine baa dade da gama shi ba. Yaji finishing na zamani, komai high quality standard na gidan.

Nan take Hajiya ta biya kudin 2 years bayan sun koma office din kanin mijin Hajiya Balkisu.

Kiran mommy Hauwa Hajiya tayi ta shaida mata an samu gida, ta turo masu furnitures din su auna.

                *****************
Kuka take harda birgima, su Hajiya salwa sun sha lallashi har sun gaji.  Da bulala mommy Hauwa ta shigo dakin, kan hubby tayi gadan gadan cikin fushi. " dan gidanku, me yasa shi da ya gaya miki, baki masa wannan haukar ba? Sai mu da kika raina? Ana lallashi kina kara botsarewa." Da sauri Hajiya tunba ta tare mommy Hauwa " haba ki bar yarinya ta yi kukanta! Taya zaa bugeka a hanaka kuka? Don haka karki fara dukanta.

Hubby da tun shigowar mommy Hauwa da sharbebiyar bulala, ta boye bayan salamatu. " don Allah karki bugeni, na daina, amma ki cewa daddy ya aura min koma, wane ne, ko kuturune, ko makaho, duka na yadda amma banda hayder don Allah..,........


   
Not Edited.......[05/03, 14:03] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 16 · 0% Book details