← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 27 OF 28

                            Part 27

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 17 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau
   
Not Edited.......

Da sauri ta kammala wankan ta fito, saboda amatullah data tashi taketa tsandara kuka. Da sauri ta dauketa tana jijjigata, kafin ta zauna a bakin gadon, ta fara shayar da ita, saboda kin shirun da tayi.

Dakyar ta samu ta kama, tana Jan ajiyar zuciya. Hubby ma ajiyar zuciya taja, Tana shafa kanta. " sorry habty." Ta fada tana mata kiss a goshi

Tsaye yake a bakin kofar, kwata kwata hubby bata san da shigowarsa ba, saboda yadda amatullah ta rikitata. A hankali ya tako zuwa inda suke cike da tsantsar son iyalan nasa. Zama yayi kusa da ita. " sabahul khair. " da sauri ta dago. Tattausan Murmushi  ta sake masa, cike dajin kunya da nauyinsa.

" sorry banji shigowarka ba, Barka da safiya?" Ta fada cike da shagwaba

Yana rike da kafar yana dan wasa da ita. amatullah da taketa wuntsilata a hankali. " princess dina ta iya rigima ashe?" 

" lokacin tashinta yayi, ni kuma na shiga wanka."

" shine baki jirani, muyi tare ba." Ya fada yana daga mata gira.

" I think zaka wuce karatu, daga sallar asubah." Ta fada

" waya gaya miki karatu nake zuwa?" Ya tambaya yana mikewa

" a bakin Hajiya naji." Ta fada tana tsare shi da ido

Smirk yayi, " bari inyi taking shower tunda anki jirana!! Ko in bari a sallami princess tukun aji dani." Ya fada yana kashe mata ido

" in hakan ya maka!" Ta fada a takaice

Har ya isa kofar toilet din, ya juyo " next month zamu tafi!! So ki fara shiri ."

Shagwabe fuska tayi " ya maganar ziyarar kankiya, kano, abuja da na maka?"

" zamuje amma tare!!" Ya fada yana shigewa cikin toilet din

Ba haka taso ba, amma ba yadda ta iya, karta matsa ya hanata gaba daya, don yanzun ma saida Hajiya tasa baki tukun.

Cikin wata dayan da sukayi, sun yishine cikin ziyarar yan' wa da abokan arziki. Ta gefe daya kuma suna cin amarcinsu.

                   *******************

Kallon hubby Aisha tayi, ta kalli beby Amatullah. Ta kwashe da dariya, harda rike ciki. Kwafa hubby tayi, tana Jan dogon tsaki " ba laifinki bane, laifinane dana zo gidanki, kika samu damar min iskanci. "

" sorry. " Aisha ta fada tana toshe baki
Rungume Amatullah tayi a jikinta, tana jin son yarinyar a ranta, tare da tunowa da yaya Yusuf, da yanzu wannan kyakyawar yarinyar tashi ce? Rayuwa kenan? Wani baya haihuwar wani. " yanzu wannan kyakyawar bebyn taki da hayder ko." Harararta hubby tayi " bari in zo in bar miki gidanki, ina gadai kora da hali kike so kiyi min."

" Allah ba haka bane Anty hubby!!! Kawai ina jin jina abun ne, in na tuna rayuwar secondary sch. Da yadda muamalarki da hayder take, cika bakin ki lokacin aurenku. Sai inga abin kamar almara, Jiya muka gama hirarku da humaira."

" kice jiya muka gama gulmarku da humaira. " hubby ta ce

" ba gulma bace wallahi. " ta fada

" kun kyauta. Allah ya shiryeku." Hubby ta fada tana murmushi

" muna labarin aurenta ne, shine zancen naki ya shigo, kin san itama iyayenta sun nace sai ta auri cousin dinta! Ita kuma akwai wanda takeso. Shine nake bata shawarar tayi hakuri ta bi maganar iyayenta, ta musu biyayya, kamar yadda kikayi, ke dama a lokacin kinada damar zabawa kanki abinda kike so, amma kika daure kikayi biyayya.  gashi tun baaje ko ina ba kin fara ganin alkhairi a rayuwarki."

" nima dazu abinda na gaya mata kenan da mukayi waya." Hubby ta fada

" dama tace zata kiraki, bata samu ta miki tsiya ranar suna ba, saboda jamaa, gashi tun daga lokacin baku haduba."

" bar yar banzar yarinya. Naso ganinta kafin mu wuce, but wuraren ziyarar suna da yawa, ba isashshen time. "

" haka ne, Allah yasa kin yiwa kanki dabara." Aisha ta fada tana murmushi

Cikin rashin fahimta hubby ke kallonta. " dabara wace iri?"

" kefa matsalata dake bakya saurin kawo wuta. Planning nake magana! Don't tell me bakije kinyi ba, kafin ki koma.?"

Mararraice fuska hubby tayi " wallahi na manta, kwata kwata munyi maganar dake, yanzu meye abinyi?"

"Yanzu kam sai dai in kun isa, sai kuje kiyi, in baki kunshi wani ba. Don naga alama hayder ba wasa." Aisha ta fada tana dariya

Harara hubby ta jefa mata " bakinki ya sari guntun kashinki. Amma fah ina tsoron masa maganar, don ban san yadda zai dauketa ba."

" haba!!! Kamar ba mace ba? Kalallameshi zakiyi, tuni zai amince, tunda duka saukin kune, kodon Ku samu natsuwar karatu nasan bazai kiba. Namayi mamamkin da bai miki maganar ba shi da kansa."

Numfashi hubby taja " bazaki gane son yara irin na Hayder ba? Shi yasa nake tsoron masa maganar, a gefe daya kuma, ina tsoron daukar wani cikin."

Dariya Aisha tayi sosai tana nuna hubby da yatsa " ke kike tsoron hayder!!! Wayyo!!! Duniya juyi juyi "

Tabe baki hubby tayi " ya zanyi? Tunda Allah ne ya bashi girman dole na hakura na sadakar."

" good for u!!! Kina burgeni!! Har ga Allah ina son halayyarki. So da yawa na kanji inama nice ke! Tabbas gwaggo ta ciri tuta. Dauraki a kan tafarki na gaskiya, Da jajir cewa wurin biyayyar aure. Shi yasa har gobe Mmn Yusuf na bakin cikin saken da tayi, na rashin yadda ki auri Abdul fatta. Gashi wadda ta zaba Masan baaje ko ina ba, kullun matsalar yau daban ta gobe daban. Yanzu haka tana Niger wai tayi yaji! Shi kuma yace wallahi bazai bar aikinsa yaje bikonta ba, sanda taga dama ta dawo dan kanta. Mmn Yusuf data kira yayantan a waya don ta basu hakuri, in kinji masifa da bakaken magan ganu, karema bazai Ciba. Harda gorin shi yarikesu tsawon shekaru, amma yarsa daya sun gagara rike masa. Alhalin sun san itace Mara gaskiyan. Har yaushe miji baya gari zaki dinga tara masa kartin banza, dasunan makotaka? Mu kanmu ranar da mukaje ganin daki, baya kasar matasa da yan mata sun kai shida muka samu a falonta sun baje bamai suturar arziki a cikinsu, har gara ita da Arabian dress a jikinta. Sun baje kayan abinci dana sha, ga kida kamar a club.

Muda mukaje da niyyar kwana uku, kwana daya mukayi, sai gidan uncle omer muka karasa sauran kwanakin. Hakan ma wai yar uwarmu, da muka hada jini. Abin Sam ba dadi, ni kaina banso hadin ba, amma ba yadda ka iya."

Kasa cewa komai hubby tayi, sai kada kai, tana godewa Allah da bata sake fadawa cikinsu ba. Don bazata taba manta izaya, da cin mutunci da tozarcin da suka mata ba. Da sunan bata haihuba. Gashi cikin ikon Allah ko bantaren magani bata sha ba, Allah ya bata nata rabon. Haka Allah ya kaddara bazata haihu da Yusuf ba, haka zai koma ga Allah ba tare daya ajiye kwansa a duniya ba, hakan na cikin kaddararsa da suka kasa ganewa, suka dauki karan tsana suka daura mata a lokacin.

" Allah ya kyauta. " ta fada tana mikewa don gabatar da sallar la'asar la'asar, kafin hayder ya karaso.

                ******************

Yau su hubby suka iso kasar Cyprus, lefkosia town. A kusa da school din apartment din da zasu zauna yake, mallakin don Harris. 3bedrooms with toilets 1 falo with toilet, sai kitchen.

Allah ya taimaki hubby mahaifiyar Mariya ta amince ta taho da ita, da sharadin sata a school. Hakan yama hubby dadi, don ta saba da ita, yarinyar ta iya aiki, ga son yara, bata da matsala ko kadan, sai dan rawar kai, wanda hubby bata daukeshi komai ba.

Cikin sati daya suka kammala, duk wani shirye shiryen fara karatu. Haka ta bangaren bukatu na gida. A kusa dasu suka sama ma Mariya day school. Amatullah sun mata register da day care,dake cikin school din. inda hubby zata dinga ajiyeta kafin ta fito lectures, Mariya kuma tunda tana rigasu dawowa, zata kula da tsaftar gida da sauran aikace- aikace.

Alhamdulillah hubby kam at first tasha matukar wahala, kafin komai ya dai daita. Hayder na matukar kokarin ware lokaci na musamman don kara fahimtar da ita abunda bata gane ba, duk da dunbin nashi karatun da business dake kansa.

Yau watansu hubby uku a Cyprus. Tana kwance a falo, tana nazarin wani assignment da aka basu. Mariya da amatullah suna garden ta korasu don ta samu cikakken natsuwa.

Kamshin turarensa ya tabbatar mata da dawowarsa, kafin sallamarsa ya shigo. Ya kara kyau da budewa, sanye yake da Jens blue da Shir gashin kansa da kyakyawan sajensa sai daukar ido suke. Da sauri ta tashi tare da taryansa. Dagata yayi yana juyi da ita, kafin ya sauketa suna dariya. " Allah matarnan kin kara nauyi sosai, meye sirrin ne? Don na lura nan da dan lokaci kadan dau kanki zai gagareni." Ya fada yana dukawa alamar gajiya.

Bayansa take kokarin danewa tana dariya " kato dakai ka kasa dagani? Ai da kaji kunya wallahi." Ganin da gaske bayan zata hau yasa yayi ciki da gudu. "Allah bazan yadda ki karyamin baya a banza ba." Da gudu ta bishi, suka fara zagaye falon. Da ta kasa kamashi ta tsaya tana maida numfashi. Dariya ya fada mata shagwabe fuska tayi. " zamu hadu, Allah bazan yadda ba, sai ka goyani."

" Rikicinki yafi na princess kwanan nan, ban kara goyaki." Ya fada yana smirk

"Kwantar da hankalinka, lokacin da zaka goyani ma, ba wanda ya sani. Ta fada tana mayar masa da smirk dinsa

Shafa kai yayi. Tare da karasowa inda take, dukawa yayi " oya!! hau." Murmushin mugunta ta masa " aa na fasa." Ta fada tana makale kafada.

" Allah sai kin hau! Don bazan yadda kimin mugunta ba." Ya fada in husky voice dinsa

Dariya tayi " ba yanzu ba, in my right time. " ta nufi kitchen don hada masa lunch.

Yana kallonta harta shige, ya shafa sajensa yana smirk

Books dinta ya dauka yana dubawa. Yaji dadin yadda take forming yanzu. Har ta gama hada dinning din, yana nazarin takardun.

" wanka zaka fara, ko abinci?" Ta tambaya cike da kulawa

Dagata yayi bridal style zuwa bedroom dinsa. Toilet ya wuce dasu, a tare sukayi wanka, bayan sun sha romance dinsu, suka fito, a shiririce suka shirya, suka fito dining.

" ware is my princess, tunda na dawo banji motsinta ba.?"

Dagowa tayi daga zuba masa abincin. " suna garden." Ta fada a takaice

" jeki dauko min ita, I want to see her." Ya fada in husky voice

Tura baki tayi, " ka gama cin abinci tukun."

" no!" Ya fada in serious tone

Tabe baki tayi tare da nufar kofar da zata sadata da garden din.

Masha Allah, Amatullah ta yi wayau abinta. A zaune na ganta kan wani tattausan carpet ga kayan wasa baja- baja a gabanta, sai zillo da tsalle take daga zaune, tana dauko wancan tayar ta dauko wancan. Tasha riga da wando na blouse pink masu matukar kyau. Kanta an mata kakaba kanana dayasha molti color ribbons gashin har kafadunta baki wulik dashi.

Mariya ce ta dauketa, ta kaiwa hubby dake tsaye dan nesa dasu, kafin ta dawo tana tattara kayan.

Amatullah tana arba da hayder ta fara tsalle tana mika hannu ya dauketa, sai wangale masa baki take. Da sauri ya mike ya amsheta tare da cillata sama, yana dariya, itama dariyar take harda kyakyatawa. Ya Rungumeta yana " miss u my princess. " ya manna mata kiss a kumatunta. Hubby na tsaye tana kallonsu cike dajin dadi, inda sabo ta saba da hidimar hayder da amatullah.

Bayan ya gama lunch, shiya taimaka mata tayi assignment dinta. Yana zaune kanta akan cinyarsa, yana shafa sumar kanta, kamar mai massage. Ta kalleshi cike da shagwaba " ya maganar da mukayi dakai jiya?"

Kallonta yayi, ya tabe baki, sai da yaja fasali tare da sauke ajiyar zuciya " tun yaushe muka gama wannan maganar? Bana son kina taso da ita kuma."

" please hayder!! Its just a matter of 2years." Ta fada cikin muryar ban tausayi

" tun ba yauba na gaya miki, bana sha'awar family planing a rayuwata, koda duk shekara zaki haifamin, ina son kayana. So stop bringing the subject again and again." Ya fada

Tashi hubby tayi ta zauna, ta kamo hannunsa, tana murzawa cikin nata a hankali. " kai kanka kaga irin wuyar da akesha!! Amma shine kake min fatan duk shekara? Saboda badaga jikinka zasu tsago su gito ba shiyasa zaka fadi haka. " ta fada cike da damuwa

Harara ya zuba mata " duk abinda zaki ce, ni dai ina nan kan bakana. Ki gode Allah wani da kudi yake so bai samu ba, so in Allah ya baki ki amsa da hannu biyu ki gode masa. Har nawa kika haifa da kike maganar planning? In ke bazaki iya rainonsu ba, ina da inda ake maraba dasu. Wannan ya zama na karshe da zaki sake zuwa min da maganar family planing a gidan nan." Ya mike cike da bacin rai ya fita.

Kanta ta daura akan hannun kujera, sai kuka. Ta rasa dalilin da yasa ya kasa fahimtarta. Yanzu haka a tsarge take da kanta, saboda wasu alamu data kasa tantan cewa,. Yanzu ta sake daukar ciki, yazatayi da amatullah? Ta gefe daya kuma karatunta.

Ta bashi tausayi, amma baya jin xai yadda da kudirinta, Yana son yara.
Zama yayi kusa da ita, tare da rungumota jikinsa. Cikin lokaci kadan ya lallashi abunsa.

" shirya min Amatullah zamu FIta." Ya fada in husky voice

" kai da ita kawai." Ta tambaya cike da rauni.

Kai ya daga mata. A sanyaye ta nufi dakinta, ta hada dan bag dinta, da duk abinda zai bukata. Kafin ta kira Mariya ta kawo mata ita, ta shiryata cikin pink din roll-on.




Har mota ta rakasu ta dawo. Gidan suka sake gyarawa, tare da baza turaren wuta bayan sun kammala dinner.

Ta idar da sallar magrib tana azhkar ta tuna da sauran p- test dinta da tazo dashi. Da sauri ta mike, ta fara duba inda take tunanin ta ajiye.

Hamdala tayi data ganshi. Ta nufi toilet gabanta na dukan tara - tara.

Safa da marwa take tayi, tana fanan kallon agogo jefi -jefi, tare da Jan tsaki. Falo ta dawo  kamar ance ta  daga labulen da zata iya hango compound din gidan.

Gabanta ne yayi mugun faduwa...........Hayder ne a saman mota, kafafunsa na dan sarke da juna, sai waya a hannunsa. A gefensa Nasrin ce dauke da Amatullah tana jingine jikin motar, da alama hirar ta musu dadi, don daga inda take tana iya hango hakoran Nasrin dake waje, alamar dariya take. Shi kuma fuskarsa na dauke da lallausan murmushi daya fito da kyawawan dimples dinsa. Kasa jure kallonsu tayi, daboda zuciyarta da takejin yana bugawa kamar zai faso kirjinta.

Duk iya yadda taso daurewa kasawa tayi, ta saki wani kuka, mai cike da kunar zuciya. Dakinta ta wuce har bata ganin gabanta sosai, saboda damuwa da bacin rai, Wannan shi ake kira abu goma da ashirin. Tana kukan targade ga karaya tazo.

Sai da taci kukanta ta koshi, sannan ta nufi toilet ta wanke idonta. Agogo ta kalla to 11, amma har lokacin bai shigo gidan ba. Kwanciya tayi. Tunanin Yusuf ne, ya dawo sabo dal a zuciyarta duk yadda taso kauda tunanin ta gagara.

Zuciyarta ta fara ba hakuri, tunda abunda ta dade da sanine, ko ba dade ko ba jima, dole sai hakan ta faru. The early the better. Allah ya bata ikon danne kishinta, yasa tafi karfin zuciyarta.

Motsinsa da kamshin turarensa shiya shaida mata isowarsa. Da sauri ta rufe idonta, tare da gyara kwanciyarta kamar mai baccin gaske.

Kusa da ita ya kwantar da Amatullah, ya manna mata kiss a goshi,. Shafa fuskar hubby yayi a hankali, tare da kai bakinsa kan nata, ya nata kiss. Sannan ya fita a dakin.

Jin fitarsa ta bude idonta. Tana kallon Amatullah daketa baccinta hankali kwance. Kofarta ta murzawa key, ta dawo tai kwanciyarta. Don gaba daya ta tsinci kanta dajin haushinsa., ta wani gefe kuma tana ganin bata yi masa adalci ba.

Hayder yasha mamakin jin kofarta a rufe, abinda bai taba faruwa ba, tun bayan shiryawarsu. Juyawa yayi ya koma dakinsa, kasan cewar yasan basu kadai bane a gidan balle ya tsaya yana buga mata Kofa.

Iya tunanin abinda zai sa ta masa hakan, yayi amma ya kasa, maganar family planing ce ta dawo masa, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah yasa ba har yanzu tana kan bakanta ba, shiyasa ta zabi wannan hanyar don ta tursasashi ya mata abinda takeso. In ba wannan ba baiga dalilin da zai sa ta masa hakan ba. Gashi a bukace yake da ita, sosai. Wayarsa ya dauko ya fara  trying number dinta, swhech up!! Tsaki yaja yafi kwando dubu. Dakyar ya samu bacci ya daukeshi. Don ta riga ta gama saba masa da bacci a jikinsa. Ga bukatuwa dake tare dashi.

Ta bangaren hubby kam, baccin ma kin zuwa yayi. Yanzu ne lokacin da zata kara kaimi wurin mallake zuciyar mijinta, ta hanyar data dace. don samowa kanta mafita, da saukin zama a cikinsu, in ba hakaba tana ji tana gani zata zama yar kallo, ko machine for producing children. Lokaci yayi da zata kara maida hankalinta kan karatunta, don tallafawa rayuwarta dana yaranta. Ko batayi don kanta ba, yanzu dole tayi don yaranta, kafin a dauko mata kishiyar da ta fita ilmi da wayewa. Yanzu ne ta fara ganin wautarta da tun tuni bata farga da hakan ba. Allah ma ya taimaketa kafin Nasrin ta shigo ta yi nisa, a nata karatun. Cikinta ta fara shafawa a hankali, tana hawaye, ikon Allah yanzu wata halittarce kwance a ciki, ba tare da ta farga ba. Ya makomar Amatullah yanzu? Ci gaba da shayar da ita zatayi, ko yayeta zatayi? Dole ta nemi shawarar doctor but how? Bata son kowa yasan da cikin, har sai ta tabbatar dashi, da kuma watanninsa. Kallon Amatullah dake ta baccinta hankali kwance tayi cike da tausayin yarinyar, tare da tausayin kanta. Tama gode Allah da ba wani laulayi na tada hankali take yiba, da ya zatayi da karatunta?.
A gogo ta kalla 2:14am  sai lokacin Amatullah ta farka ta fara kukan neman abincinta.

Daukarta tayi, ta shayar da ita, tare da sata a kafadarta tana jijjigata har bacci ya sake gaba da ita.

Alwala ta dauro, ta kabbara nafila.

3 am dai dai hayder ya farka, alwala shima ya dauro, ya fara jera nashi nafilfilin, kamar yadda suka saba, duk dare. Yaso zuwa ya tasheta, amma baya son Mariya ta jishi yana buga kofa, ba mutuncin su bane, don haka ya share ta.

                ********************
Sai 7:23 ta fito daga dakinta, sanye cikin wata maron Arabian gown, mai adon gold stones and bits. Rigar ta bude sosai da wadataccen mayafinta. Amatullah ma tana sanye da riga da wando masu matukar kyau yellow and White, ta mata fakin din gashinta, ta daura mata hular kayan tafito a balarabiyanta sak, Sai kamshin sukeyi daga ita har hubby.

Already Mariya ta tafi school, don 7 school bus dinsu ke zuwa daukanta, so in ta tashi sallar asuhah bata komawa, zata rage ayyukan gidan, kafin ta nemawa kanta abinda zataci, sannan ta shirya ta tafi. A school ake basu lunch.

Kitchen ta nufa, don hadawa amatullah priso cream, a kujerarta ta sakata don ta samu damar yin komai a natse. Kamshin turarensa da dariyar amatullah taji, yasa ta juyowa. Ido hudu sukayi, da yasa gabanta faduwa. Yana sanye da black jeans da white shirt, sai hannunsa dake daure da silver watch. He look hansom.
Dauke idonsa yayi a kanta, ya durgusa ya dauki Amatullah daketa mika masa hannu tana zillo tare da dariya irin ta yara. Dagata yayi, ya cillata sama kamar yadda ya saba, yana juyawa da ita, suna dariya.
Kafin ya mata kiss a chic dinta.

" an tashi lafiya?" Hubby ta fada cikin karfin hali da basarwa, don ganinshi ya kara sa taji kishin ya kara taso mata

Takowa yayi zuwa inda take tsaye, tana juya priso din don ya huce, yadda zata iya bata, Rungumeta yayi da hannunsa daya, ya manna mata kiss a goshi.

" what I have don to u? To deserve this kind of punishment? " ya fada yana daga mata gira

" notting!" Ta fada in very low voice

Kallon idonta yayi, for some time, yana karantar yanayinta. Ya kada kai " ban yadda ba komai ba, amma koma menene daga yau komai nayi, amin wani punishment din banda wannan."

Harararsa tayi kasa- kasa. Smirk yayi don ya ga me ta masa " u see!!! Allah yasa ba maganar planning bace tasa ake min wannan horon? "

Tabe baki ta yi, tana kokarin amsar amatullah a hannunsa. Kin yadda yarinyar tayi, ta kara makalewa a jikin hayder. " kinga princess ma tasan na fiki gaskiya." Ya fada in husky voice dinsa yana amsar abincin a hannun hubby. "

Batayi niyyar musu break fast ba, amma wata zuciyar ta gargadeta, da kar ta biye kishin banza, yanzu ne lokacin da zata kara zage damtse ta kama mijinta a hannunta. Agogo ta kalla at lest tana da  sauran time, hakan ya bata damar daura musu break fast mai sauki.

Cikin minti 30 ta kammala, ta jera komai a dinning.

 
[12/03, 12:44] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 27 · 0% Book details