Part 7
Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 26 min read
Written By Zulaihat Aliyu Misau
Wattpad@zulaihatualiyumisau
Not Edited.......
" wai yarinyar nan kwana biyu kin kara nauyi " Ya fada yana direta a tsakiyar dakin. Gimtse dariyar tayi tana masa harara mai hade da kallon love, " yar ni dinnan har zakace nayi nauyi? Randa na zama katuwa kuma fa? Kasan dai baka isa kace bazaka iya daganiba!! Don ba yadda zan ba, tunda ka saba min"
" so dai kike ki buda min kirji, naga alama amma yar lukuta na nawa kuma, bayan yadda kike a yanzu?"
Kafa ta fara bubbugaga cike da shagwaba,Wanda yasa duk kan jikinta juyawa, dama sanye take da kayan bacci. Rigace aimless da gajeran wandonta ko ciya bai rufe ba, Wanda ya fita da kyan sigarta. Tsayawa yayi yana kallon yadda komai ke juyawa gwanin shaawa, da burgewa. wani Abu yaji yana kara taso masa tun daga babban yatsansa har ysakarka.
Jinshi shiru yasa ta tsaya da juye juyen da take. Kallo daya ta masa ta karanto tsantsar fitinan dake dankare a kwayar idonsa. Ido daya ta kashe masa, tare da daga kanta kadan alamar tambaya. Ajiyar zuciya yayi tare da murmushi, smacking ya mata tare da sanya hannu ya jawota. Kwasa tayi da gudu, still fuskarsa na dauke da murmushi ya bita, suka fara zagaye bed din dakin. Cafkarta yayi bai direta ba sai tsakiyar bed din dake cike da kayanta data barbaza tana zabar na tafiya.
Dariya take tana maida numfashi, magana take son yi amma ko kalma daya ta kasa furtawa.
Sun Dade suna kallon juna, cike da so da kauna, kafin yakai bakinsa kan nata ya fara kissing dinta. Ganin yana son wuce gona da iri, da kyar ta kwaci bakinta a nashi cikin maida numfashi tace " abincinka fa na jira a falo " kara jawota yayi jikinsa, ganin abun ba sauki yasa ta tallafi mijinta ta fara aika mai da nata salon cike da kwarewa da sanin ta kan mijin nata.
Kukan shagwaba ta fara " Allah bazan yadda ba, ji yadda kamin da kayana" dakin yabi da kallo. A kwatin can gefe ya kusa bakin kofa, sai kayan da suke da a goge kowanne ya kama gabansa baa maganar guga. Shi kansa gadon da suke kwance kan wasu daga kayan ne, wanda fadin yamutsewarsu bata baki ne.
" it's your folt princess, you look hot, "
Kara shigewa jikinsa tayi
Allah ya miki albarka, you make me a happeyers man on earth. Na gode Allah daya sakoki cikin rayuwata, Allah ya bamu zuria tsarka kakkiya. I'm very sorry da abinda ke faruwa tsakaninki da yan uwana, I known everything, I try my best to make things right. I known your worries, mu ci gaba da addua, wataran sai labari, ki dauka taki jarabawar kenan, don ko wanne Dan Adam da kika Ganshi yanada irin tashi jarabawar. Ki kula min da kanki sosai, na jama su abida da aira kunne sosai, in sha Allah ba wani matsala. Zanyi iyaka kokarina in ga na yi scuising time in zo da wuri, don nima hankalina ba zai taba kwanciya ba."
Kwantar da kanta tayi a kirjinsa tana shafawa a hankali, ajiyar zuciya tayi " baka ci abinci ba fah?"
Hancinta ya danja, yana murmushi, " me kike dafamin ne?"
" you're favorite "
Goshinta ya sumbata " thank u, I'm going to miss u"
Hawayen da taji na Neman fitowa yasa tayi saurin mai dasu. " me too. "
Bayan sun tsarkake jikinsu, suka nufi falo. Da kanta ta dinga ciyar dashi har ya koshi. Ga labarai na ban dariya da ta tanada, musamman don ta sashi nishadi. Cikin nishadi take ciyar dashi tare da bashi labarin dan fillo da babarbare, dariya sosai suke kwasa. Duk rashin son surutu irin na yusuf, in yana tare da hubby zaka sha mamakin yadda shima yake iya kokarinsa, wurin biye mata, hira sosai yake zagewa ya mata,don ya lura shiru baya cikin kundinta. Duk yanda ta motsa idonsa na kanta. He never except irin wannan kulawar daga gareta, duk da auren soyayya sukayi,. Tsawon shekara dayan nan ba zai ce ga wani aibunta da ya ganiba. Kullun tana cikin tarairayarsa, da bashi kulawa, hatta abinci ya rasa when last da yaci abinci da kansa. Ta riga ta shagwabashi karshe, duk inda yaje Allah Allah yake yadawo gida.
Idonsa ta hure cikin salon daukan hankali, ganin yadda ya zuba mata mayatattun idonsa baya ko kiftawa. Murmushi yayi tare da sauke ajiyar zuciya. Sai daya hadiye ruwan tie din daya kurba. Ya kalleta da dara daran idonsa, yana shigar dasu a hankali " I love u" murmushi tayi don inda sabo ta saba, akalla a rana takanji Kalmar a bakinsa ba adadi. Kiss tama bakinsa, da ta Dora goshinta kan nasa hancinsu na gogar juna " I love u more "
Sun Dade a na nuna ma juna kauna, kafin suka koma dakin ya tayata hada kayan da zata tafi dasu. Ranar kwana sukayi basuyi bacci ba.
****************
Karfe 2:43 dai dai jirginsu ya sauka a Miami na kasar Niger. Mota biyu suka zo daukarsu,.
Alhaji mamuda Hammani, ya ya ga Mmn Yusuf, kuma marikinta. Hamshakin Dan kasuwane, Wanda yayi fice a kasar Niger, wurin shigowa da Samar da kayan masarufi. Sannan dan siyasa, mai rike da mukamin dan majalisar tarayya.
Alhamdulillah sun samu karba sosai, cikin mutunci da karramawa. Gidan cike yake da baki na nesa, yan kusan ma sun samu halatta saboda shirye shirye.
Abida kam tuni ta shige cikin kawayen Amarya. Dayawansu dama duk yan uwan junane.
Hubby na zaune ita da Aira, sai kannen Hajiya Ai dake ta aikin ware kayan Amarya. A hankali Aira ke janta da hira, tana gaya mata matsayin kowa a wurinsu. Ajiyar zuciya hubby tayi don bata taba zaton family din suna da yawa haka ba. Kwanciyar hankalinta, da tun da tazo bata samu matsala da kowa ba. Hatta abida silent treat ta mata. Kamar yadda Aira ke mata a da. Ita dai bata nuna bata son taba, amma ba ruwanta da duk wani harkarta. Daga gaisuwa shi kenan bata kara bi ta kanta. Amma ikon Allah yau ita Aira kewa hira?
Muryar Aira ce ta dawo da ita daga dogon tunaninta. " nifa gidan Innani zan gudu, don gaskiya gidan nan ba dadi zai yiba, duba tun yanzu har gida ya cika."
Murmushi tayi don tana yawan jin labarin innani a bakin Yusuf. So she known who she is. " kiyi hakuri mu zauna a nan, ban son zama ni kadai"
Tabe baki Aira tayi " ba nisa fa, 3 houses ne kawai a tsakaninsu, in zaki je muje, amma ni bazan iya zama a nan ba gaskiya, ko dama can nafi sauka a gidanta, in munzo"
" OK zan tambayi mommy in ta yadda sai muje"
Saurayine da ba zai wuce 25 years ba,dogo wankan tarwada, yana da kyau sosai, ga alamar Hutu, da kwalisa bayyane a tare dashi, kallo daya zaka masa kasan irin mazan nan ne masu aji. Kyau, kudi, ilmi.
Shigowarsa na uku kenan falon in ba batan lissafi nayi ba. Daya daga cikin matan dake jera decorations a cikin kwali ta dago ta kalleshi tana murmushi " lafiyarka kake ta mana sintiri a kai?"
Keya ya dan shafa, yana murmushi idonsa na kan su Aira dake can gefe, suna hira sama sama da hubby. " kaji cikin ummana? Naga duk dakin nan iyayenane? Meye a ciki don na shigo?"
Dariya sukayi gaba dayansu. Dayar ta ce " kaji da gulmarka, nasan sintirin da kakeyi ai, Mara kunyar banza, ina tun safe muke nan muna aiki? Ko keyar ka bamu gani ba sai yanzu, zaka ishi mutane da sintiri, bako kunya "
" wayyo!!! Ai sai yanzu na harbo jirgin" wadda ta fara magana ta fada
Ganin duk sun hayayyako masa yasa cikin borin kunya ya ce " nifa ba wannan ya kawo niba, kuke Neman fassarani, snacks nake so, Hajiya tace in zo wurin cikin umanta in karba"
" kadai ji dashi, yaro" suka fada suna masa dariya.
Kallon Aira yayi " please sister ki karba ki kawo min ina waje, kafin wa annan matan su tsitstsigeni" " OK" ta fada tana mikewa daga inda take zaune.
Wani mayataccen kallo ya bi hubby dashi, kafin ya fice a falon. Hubby kam bata ma San wainar da suke soyawa ba, don idonta na kan waya, suna charting da junaid, sai Aira da ke mata hira jefi jefi.
A waje ta sameshi da friends dinsa, sun shinfida katuwar dadduma, ga kayan shayi nan birjik ko wanne da kofinsa a hannu.
"Mai hali bai fasa halinsa, iya saninta da Yaya Khalil duk yamma yake hada wannan majalisar ta abokansa, asha shayi, ayi musu, ayi hira da dariya. Da alama shi zai gaji Alhajin su ta fannin siyasa, don yanzu haka ya kammala degree dinsa na biyu akan political science. Duka duka satinsa daya da dawowa gida Niger. Sabanin sauran yayyensa dake harkar kasuwanci.
Sallama tayi cikin muryarta mai sanyi. " Yaya Khalil gashi! " ta mika masa trey din.
Murmushi yayi, Wanda ya bayyana kyawawan hakoransa farare masu dauke da wushirya. " thanks siste",
Gaishe da friends dinsa tayi, sannan ta juya zata koma ciki.
Biyota yayi da sauri " 2 min sister" tsayawa tayi, tana kallonsa tare da jiran mai zai ce.
Murmushi yayi, yana shafa dan kyakykyawan gajeren gemun da ya bari. " na ganki da wata? I don't know her, please wa ce ce ita?"
Gaban Aira ne ya mugun faduwa, mu samman ganin yadda yake ta sake mata murmushi.
" she is our Anty, Matar Yaya Yusuf ce"
Nan take annurin fuskarsa ya kau, hannu yasa yana shafa lallausar sumar kansa. Ji yake kamar ya kwala ihu, saboda abinda ya tsaya masa a kirji. Tunawa yayi Aira fa kallon sa take, zata iya harbo jirginsa, Wanda hakan bazai musu dadi ba. Murmushi ya yi, cikin basarwa " amma baki da kirki, shine baki min bayani ba in kwashi gaisuwa"
Murmushi tayi " sorry na shaafa ne"
" shike nan, bari in je na bar friends dina, zan shigo anjima in kwashi gaisuwa "
" OK no prb"
Jiki a salube ya koma wurin friends dinsa, nan suka dinga tsokalarsa wai yayi new catch.
Ajiyar zuciya tayi " iko sai Allah, bisa duk kan alamu ya kamu da son hubby, shin bai San da alkawarin hadin aure tsakaninta dashi bane? Bisa dukkan alamu bashi da masaniya a kai. Bayan hadin auren Yusuf da Hafsat ya wargaje, shine suka maida abin kan abida da Khalil, nan take abida ta nuna ita bata yadda ba don akwai Wanda ta ke so, juyin duniya taki, ganin haka yasa aka yanke shawarar a hada Aira da Khalil. Baa samu matsala a wurin Aira ba, don lokacin ko secondary school bata gama ba, bata fara kula samariba. Wannan kenan.
Jikinta a San yaye, ta koma ciki, don gaskiya tana matukar son Khalil, tun ba yau ba, yana burgeta sosai,.
******************
Sosai innani ta karbesu, mu samman hubby. Abin ya matukar burge hubby, yanda innani ta dinga nan nan da ita.
Innani kanwa ce gasu Mmn Yusuf, su uku Allah yaba iyayensu. Itace karama. Yaranta uku. Khadija ( kadi) wadda saa ce gasu abida, sai Fatima ( ya fati) Saar su aira, sai auta umar, Wanda duka duka shekarunsa biyar kenan, don har ta cire ran sake haihuwa, sai ga ciki, on expected. Mijinta Dan kwangilane, yana da rufin asiri sosai.
Dakin kadi aka sauke hubby, kasan cewar kadi na cikin kawayen Amarya, yasa ya xama hubby ce kawai a Dakin. Sai Aira da ta sauka a dakin Best friend dinta yah fati.
***************
Lallausan cotton less ne a jikinta kalan lilac da milk, dinkin straight skirt, dinkin rigar ambreller ne, zuwa gwuiwa. Dinkin yasha aiki ga stone sai daukar ido suke, set din White gold tasa mai hade da siraran bresslet guda biyu. Dan kwalin less din tayi hadadden dauri dashi Wanda ya kara fito da kyan fuskarta sosai, simple makeup tayi, ta feshe gikinta da turaruka masu matukar kamshi da tsada. Don hubby akwai son kamshi, ta hadu da oga Yusuf da baya jin tsadar siyan turare komai tsadarsa. Gyale milk color ta yafa, sai takalmi da Jakarta milk and lilac. Juyawa tayi tana kallon kyan da tayi ta jikin dogon mirrow da ke manne a side din dakin, Wanda zai baki damar ganin Head to toe dinki.
Gadiya tayi ma Allah daya kagi halittarta. Take Yusuf ya fado mata. Murmushi tayi. Shigowar yah fati ne ya dawo da hankalinta.
" woww!!! Masha Allah, Matar Yaya kin hadu ba karya wallahi" yah fati ta fada tana bin hubby da kallo, fuskarta fal murmushi.
" yayanmu ya iya zabe, irin wannan full option haka"
Murmushi hubby tayi tare da hararar yah fati, don dan zaman da tayi da ita daga jiya zuwa yau ta lura yarinyar akwai barkwanci, ga saukin kai,.jininsu ya hadu, kamar yadda ya hadu dana innani. Kadi ce dai har lokacin basu haduba.
Ganin hararar da hubby ke aika mata, yasa tayi dariya, "Matar Yaya kefa muke jira, don in mun rakaki can gidan, mu kam gari zamu shiga"
Nan danan fuskar hubby ta canza. su tafi su barta da wa? Bayan dasu kadai take iya sakewa, su ke debe mata kewa, tunda ba sanin kowa tayiba.
" ban gane zaku shiga gari ba?"
" zamu je gidan wata friend din mu ne, daga nan Yaya Abba zai kaimu yawo, kin San kanwar taki, kamar shan shani take,."
Marai raice fiska tayi " please karku tafi Ku barni ni kadai, kunga Ku kadai na saba da, kuyi hakuri mu zauna"
" wai zaman me kuke a daki? Daga bari in je in kirata kin zauna kamar an aiki bawa garinsu!"
Da kallo tabi hubby " kinyi kyau " ta fada tana murmushi
" thanks, don bakuga kanku bane, na tabbatar kunfini yin kyau" hubby ta fada tana mayar mata da murmushin
Kallon Kansu sukayi, tabbas ba karya sunyi kyau sosai, sanye suke da atamfa super exclusive Riga da skirt Wanda kowacce yabi jikinta das gwanin shaawa. Komai nasu iri daya. Don dama haka sukeyi in sun hadu, komai iri daya suke sawa like twin's. A fisge kuma akai saa suna kama da juna ta wurin hasken fata, da yanayin bakinsu. Don itama yah fati badai kyau ba, babanta buzune, mahaifiyarsa kuma babarbariya.
" kin dai zagemu kawai, " yah fati ta fada tana dariya.
" zagi ko gaskiya. Look at you" hubby ta fada tana nuna su jikin mirror din.
" kina wuri ai bamu isa yin magana ba. I had a lot about you. Ashe ma kinfi yadda ake kwatan tawa " ya fati ta fada tana murmushi
" haka dai kika ce, but ban yadda ba "
Haka sukayi ta musu, cikin anna shuwa. Kafin daga karshe zuna nufi gidan bikin.
Mmn Yusuf ce ta bukaci su aira dasu zagaya da hubby ta gaishe da sauran muta nen gidan. Sai a lokacin hubby ta tabbatar da girman gidan, don hatta yaran gidan manya su uku a nan cikin gidan suke zaune da matansu, kowa part dinshi daban.
A part din babban Yaya badamasi suka samu sauran matan. Matar badamasi hilwa, ta karbesu cike da faraa. Tana Jan yah fati da wasa, da a lama mutuniyarta ce. Ya fati ce ta gabatar musu da hubby. Sannan ta fara introducing dinsu ga hubby, hilwa Matar yaya badamasi, sai yasin Matar yayaKabir, sai humaira Amarya a wurin Yaya Abba. Ya fati ta karashe tana dariya.
Dariya humaira tayi " fadi ki kara, uwargida, kuma amarya. In zaki zage ki nemo naki, ki zage don na tare gaba na tare baya. Don haka a kara gaba a daina shin shina min miji."
Duka dariya suka sa, ganin yadda humaira keyi. Banda yasin data hade fuska sai wani harare harare take.
" oh !!! Ji yadda kike wani tada jijiyar wuya. Kisa ranki a inuwa da ina da bukatarsa da baki samu shigowa ba, don kiji. Ni nan da kika gani sai na zaba na darje. Mijinki ya zama second hand yanzu. Ki rike kayanki."
" kin dai ji tsoro kawai" humaira ta fada tana dariya
" Allah ya kiyaye in ji tsoronki. In ina da bukata, kwace shi ba zai min wuya ba, ke kinsan haka."
" oho dai abi wani sarkin ''
Hilwa ce ta katsesu da cewa " kun bani kullun kuka hadu sai an zubar da hali. Wannan ma ya hadaku ai karasashi zakuyi"
" barta kawai, yanzu haka ma dashi zamu fita, please Anty hilwa ga amanar Anty hubby a hannunki yanzu zamuje mu dawo."
" lallai ne, ke yanzu kina kallo yarinya karama tana kokarin juya miki miji.? Kar kiji tana wani dadin bakin ba son shi take ba. ki sake jiki a miki sakiyar da ba ruwa.yan matan yanzu da suke neman miji ido a rufe, balle an samu ready made. Kina nan sai dai kiji labari yasha ban ban." Yasin ta fada cikin yatsina tana kallonsu a Dage.
" iko sai Allah, cin dankon har da su kaza.? Ina ruwan agwagwa mai bakin baki. Allah mun gode maka da kasa sauran garin ba baki bane kamar dayan, da kunun ba zai shawuba." Ya fati ta fada tana kafeta da ido cike da rashin kunya.
" karki fara!!! Ko yanzu in tattaka yarinya a wurin nan"
" tafdijan!!!! Da kin tarowa kanki mach wallahi. Kuma kashedi ban saka mutun ba ban son ya tsoma kansa. Ehe!!!!!!! Shish shigi ba aji"
Tashi yasin tayi zata fallawa yah fati mari, da sauri humaira ta tare, tare da janye yah fati da sauri.
" haba ke kuwa? Wannan ai ba girmanki bane." Humaira ta fada tana janye yah fati.
" abinda kike bakya kyautawa, na ga dai ba da ke take ba? Bana son irin haka. Ke ce babba ya kamata ki kama kanki. Da baki tanka taba ai bazata gaya miki magana ba."
Harara yasin ta makawa hilwa " dama ai ke kike daure mata gindin yiwa mutane rashin kunya."
Kallon su yah fati hilwa tayi " ki wuce ku tafi kayanku."
Harara ya fati ta jefawa yasin tare da Jan tsaki, ta ja hannun Aira da tun dazu ta daskare a wurin tana kallon ikon Allah. Sukayi waje.
Hubby ji tayi kamar ta bisu. Don gaba daya jinta take kamar akan kaya. Ga wani kallon banza da yasin ke aiko mata, kamar ita takar zomon.
" gaskiya ce bakwaso, ni kuma sai na fada, kina wani yashe mata baki, ke a dole wasa, baki San a wasa ake cutar ka wani lokacin ba! Ga example nan a gabanki ai." Ta nuna bubby da yatsa
Cikin bacin rai hilwa ta ce " kinga ban son dibar albarka, zo ki wuce gidanki tunda ke har abada baa iya zama lafiya dake."
" ko baki ce in fita ba, tafiya zanyi. Don bana zama inuwa daya da snatchers. Gashi nan Allah ya kama su ai, dan farin cikin nan da kowa ke samu, da karuwa sun rasa, har yanzu shiru. Waya Sani ma ko juya ce, an gama gantali a titi, an ga sankacecen yaro an manne masa. "
Duk inda bacin rai yakai hilwa da humaira ransu ya baci. Hubby kam baa magana zuciyarta ce taji tana mata wani zafi, ina ma ace ba bakunta taxo ba, da yau yasin sai ta raina kanta, sai tasan ta taba hubby. Duba da duka duka bazata wuce Saar taba.
Kallon yasin take, mai cike da maanoni da dama.
Har zata fita ta juyo, tayi saa kuwa duk suna binta da ido.
Murmushi tayi " da kika tsareni da ido, in fitsarin kaza kunfa ne, wata tayi mana. Nan da wata Tara muzo suna. In har ba juya aka kwaso mana ba. Snatcher kawai" tayi tsaki ta fice.........
" kiyi hakuri don Allah, wallahi halinta ne, duk nan hakuri muke da ita." Humaira ta fada cike da damuwa
Hilwa ta kara da cewa " karki sa abinda ta fada a ranki don Allah. Nasan da zafi, kwata kwata bata iya magana ba, bata iya ban bance kalaman da ya kamata ta gayawa mutun, komai yazo bakinta fada take."
Murmushi hubby tayi mai ciwo. " ba komai ya wuce"
Hira sosai sukayi ta Jan hubby dashi, cikin kan kanin lokaci ta sake jikinta, don hubby akwai saurin sabo.
*******************
Yau kwanan su hubby biyar a garin Miami. Zuwa lokacin ta saba dasu hilwa da humaira sosai, in ka gansu kamar dama can sun San juna. Hubby mai farin jini ce, da shiga rai muddin zaka zauna da ita na dan lokaci, tuni zata shige ziciyarka. Kamar yadda ta samu masoya haka ta samu makiya da yan hassada (Allah ka mana tsari da hasiduna)
Yasin da mukarrabanta dama kadan suke jira, su dinga yada mata da habaici da mafanganu,dasu gori. Bata daga kanta ma balle ta nuna musu ta damu da abinda suke yi, sau da yawa su humaira ne masu shiga mata suyi uwa suyi makar biya.
Hakika sun nuna mata kauna wadda bazata misaltu ba.
Sai ana gobe daurin aure su Yusuf suka sauka a Miami. Shida Alhaji jamal, Ahmad, Sai Mmn samira da ummu sulaim.
Wai zo kaga murna wurin hubby, ganin ummu sulaim. Don tun bikinsu da suka raka ummu khulsum gidanta a Lebanon suka riketa a can.
******************
Alhamsulillah yau su hubby suka dira gida Nigeria.
Da kyar ta lallaba ummu sulaim ta bita su kwana biyu. Don ba karamin kewar juna sukayi ba. Koda ummu khulsum tazo haihuwa gida, lokacin ummu sulaim na shirye shiryen exams a can aka barta.
****"""*""**********
A kwana a tashi asarar mai rai, inji masu iya magana ( but nah true oo) yau auren hubby da Yusuf 4years kenan. Abu buwa masu dadi, da akasasinsu sun faru. Har lokacin ko batan wata bubby bata taba yiba. Su Kansu abin ya damesu, Sai dai duk asibitin da sukaje a ka gama gwaje gwaje zaa ce musu komai normal. Ba wata matsala a tare dasu.
Yanzu haka satinsu daya da dawowa daga Egypt, ganin doctor, suka wuce saudi don yin umra.
A hankali ya tako in da take tsaye a gaban mirror tana shirin tafiya suna gidan Ahmad. Matarsa munaya ta haifi second yaronta namiji.
Rungumota yayi jikinsa yana shakan kanshinta, yana faman limshe ido. Murmushin karfin hali tayi, duk a kokarinta na boye damuwarta. Don tun da akayi haihuwarnan take fuskantar wulakanci da gori iri iri. Hatta Wanda bata taba tsammanin haka daga garesu ba. Balle yau da gidan zai cika.
Shafa lallausar sumarsa tayi tana kallonsa ta mirror din. " nayi latti fah!!!" Ta fada cikin shagwaba
"I know " ya fada yana juyo da ita, suna fuskantar juna.
Kallonta yake cike da tausayinta, yayi mata kiss a goshi, hannunta duka biyu cikin nashi " take good Care of your self. Karki bari maganar wawayen cikinmu ta dameki, Allah shike ba da haihuwa ga Wanda yaso, ya hana, Wanda yaso, A lokacin da yaso.Keep that in mind."
Murmushi tayi " in sha Allah "
Yana rike da Jakarta suka fito, tana bashi labarin yah fati da yasin suna dariya. Don lokacin yah fati na matsayin Matar Yaya Kabir, kishiya ga yasin. Zo kaga drama.
Sai da ya tabbatar ta zauna dakyau ya mika mata jakar, ya rufe mata kofar, ya koma driver sit, yaja suka nufi gidan Ahmad, dake kusa dasu.
Sai da ya tabbatar ta shiga tukunna yaja ya tafi.
Da Anty samira suka fara cin karo,. " manyan mata, sai yanzu ake ganin Ku?" Ta fada tana karewa hubby kallo.
Murmushi hubby tayi " kai bisa wuya, ina kwana"
" lafiya kalau, gimbiya a gidan Yaya Yusuf. Zan zo dai abani sirrin nan"
" Anty samira kenan, sirri kam ai yana wurinku "
Ido samira ta dan fito dashi " suwa ? Ke dai kice bazaki bani ba kawai."
Ganin Jan maganar zaiyi yawa yasa hubby saurin katseta, " su Aisha fah?"
Tabe baki tayi " suna ciki "
Da sauri tabi hanyar da zai sadata da falon gidan.
Da kallo samira ta bita tana tabe baki.
**************
" kai amma less dinkin nan yayi matukar kyau, baki ga yadda ya fito da keba wallahi" hubby ta fada tana kallon munaya
Murmushi munaya tayi don irin matan nan ne masu son ace sunyi kyau, ko kuma abunsu ya burge. Don yar karyace ta karshe. A kwai daukar wanka kam.
" thanks Matar Yaya. Kin ganshi musamman nayi oder dinsa daga England. Da aka kawo sai naji bai yi min ba. Amma sweetheart ya ce ya masa kyau, shi yasa na dinka, da kyauta zanyi dashi."
" yayi kyau sosai, ba karya kin fito "
Murmushi munaya tayi cike dajin dadi " thanks "
Anties dinsu Ahmad ne suka shigo. Dayar ta kalli munaya tana murmushi " mejego ta fito ras, wannan kwalliya haka kamar zaki gasar sarauniyar kyau."
Dayar ta amshe da " masha Allah kyau ya tarda kyau "
Hubby ce ta fara gaishesu, ba yabo ba fallasa suka amsa.
Dayar ce ta dawo kusa da hubby " yauwa dama ina son magana dake, "
Gyara zama hubby tayi tana kallon ta cike da ladabi, don ta girmeta nesa ba kusa ba.
" yanzu don Allah Habiba me yafi wannan dadi?" Tana nuna munaya mace duk kyanta duk kudinta, duk nasabarta in bata haihuwa meye anfaninta? Ina baki shawara tun wuri in har kin San da gaskene kwayoyin hana daukar ciki kike sha, ki shafama kanki lafiya ki bari. In kuma matsala ce Ku nemi magani tun kan lokaci ya kure miki. Don mace lokacinta takai tacce ne, ba kamar namiji ba. Kar kiga kin mallake miji, sai yadda kikayi dashi, akwai ranar kin dillanci. ban da haka ma ai haihuwa rahama ce. Shawara ce, don ni bazan fada a bayan idonki ba, kuma ba zan iya shiru ba."
Tunda ta fara maganar kan hubby na kasa, duk kokarinta na danne kukanta ya gagara. Hawaye ne suka fara bin kuncinta.
Jin Matar tayi shiru dayar ta amsa " gaskiya kam, surutu yayi yawa a kanki. Naji ma kamar aure uwarsa take nema masa "
Da sauri hubby ta dago tana kallon matar.
Itan ma kallonta take yi " da gaske gara kinsan abinda kike ciki.
" haba Ku kuwa, Ku kyaleta taji da abunda ke damunta. Ni nasan hubby bazata taba yin abin da ake fada a kanta ba, suma sun San haka, son zuciya ne, kawai da kin gaskiya. Haihuwa kuma ta Allah ce, ni nasan da ana siyarwa da kun samu sun kai goma a wurinta, yanda take son yara." Munaya ta fada tana zama kusa da hubby
Maganganu masu sanyaya rai ta dinga gaya mata, har ta samu natsuwa, suma hakuri suka bata . tace ba komai ta gode.
A ranar hubby tasha bakaken magan ganu da habaici iri iri. Su Aisha ne su ka dinga shiga mata, su dinma daga baya hanasu tayi.
A daddafe takai 5, ta zame jikinta tayi gida. Kuka ta sha kamar ba gobe, sai da tayi mai isarta sannan ta nufi toilet ta wanka ta dauro alwala.
Ko da yaje daukarta su Aisha suka shaida masa ta Riga ta tafi.
Kamar yadda ta saba masa komai yauma haka, ko afuska bazaka taba ganin damuwa ba. Shima bai tada maganarba duk da Aisha ta gaya masa komai. A kullun addua da godiya yake ma Allah daya azurtashi da mata ta gari. Duk abunda yan uwansa zasu mata bata taba kawo masa kararsu, saanninta in sun mata ta rama, in ka girmeta ta kauda kanta. Ko a fuska bata taba nuna masa an bata mata, ko an mata ba dai dai ba.
*******************
Zaune suke a babban falon yaran gidan, bakajin komai sai karar cokula da tashin muryoyi maban banta, da dariya.
Ummu sulaim, Ummul khair, Aisha, sai yaran uncle omer asima da asiya. Ko wacce na cikin farin ciki sai zolayar juna suke. Gwanin shaawa.
Da sallama ta shigo falon. Wani ihu Aisha tasa ta rungumota tana murnar ganinta.
Ita din ma dariya tayi tana kara rungumeta. " ke karfa ki karya mana Matar Yaya" asima ta fada tana dariya.
" congratulation my betsy " hubby ta fada tana mikama Aisha hannu bayan sun saki juna.
" thanks, na dauka ai bazaki zo ba "
" ni a wa? "
Hubby ta fada tana dariya. Sadi driver yayi sallama sai da suka bashi izni bayan sun amsa ya shigo da wasu manyan kwalaye guda biyu ya gaishesu, ya ajiye ya fita.
Gaisuwa suka fara cike da kaunar juna. Suna tsokanan hubby.
" congratulation to you too " hubby ta fada tana rungume ummu sulaim.
" thanks sister "
Zama hubby tayi kusa da Aisha. " to su alhuda huda, an kammala degree an dire, what is next? "
Duka Aisha ta kai mata. " tun da kin ji tsoro kinki direwa. Mun dire kuma sai A B U, kin ga mun zama daya kenan."
Dariya hubby tayi " wane ke yarinya, kya hada Wanda ya ke da 4 years experience da Wanda ya shiga new? Na gaba yayi gaba,."
Dariya sukayi " gaskiya ne kam, za muzo daukar lectures, don gaskiya kina bala'in burgeni, yan da ake kula da yayanmu, ina son nima in sace zuciyar sweety na, da irin waannan salona. Ya zama ba kowa a gabansa sai ni."
Asiya ce ta tashi tsam daga inda take zaune ta koma kusada hubby dake zaune kusa da Aisha, ta zauna.
" gaskiyarki sister Aisha, nima please zan zo a bani horo na musamman."
Dariya sukayi gaba daya. Ummul khair ta rike haba tana dariya " amma dai rashin kunyarki yayi yawa, ki bar manya suyi maganarsu, ba ke ba dako secondary yanzu kika kammala. Amma kike maganar koyon zaman aure, anyah???"
Harararta Asiya tayi " wa yasa dake? "
" gaskiya ta gaya miki, muna maganar manya Ku daina sa mana baki." Ummu sulaim ta fada
" kefa surukata ce be kamata kina min haka ba. Kamata yayi ki roki antinmu ta bani hints na yadda zan sace zuciyar !! Eh !!!! Kin gane ba sai na fada ba"
Dariya ummu sulaim tayi tana nuna Asiya da yatsa " ina warning Dinki bakyaji, I don't want u to get hot at end"
Bata rai Asiya tayi cikin tura baki " just pray for me "
Asima ta tabe baki cike da jin haushin kanwar tata " ki kyaleta Wanda yayi nisa baya jin kira, jiki magayi ai, in ji masu iya magana "
Hubby dake zaune tana jinsu. Aisha ta kalli Asiya " rabu dasu sister, ba dai kina son shi ba? I will teach u, how to woo him, he felt for u, like crazy."
Dariya ummu sulaim tayi har da rike ciki. Da ido suka bita, sai da tayi mai isarta sannan.
" lafiyarki kuwa? Mu gudu ko mu tsaya ?" Hubby ta ce yana tsareta da ido. Don sun San muddin kaga ummu sulaim tana irin wannan dariyar to ko dai ta mugunta ce, ko kuma ta gama raina maka hankali.
" waannan har yau baku gama sanin waye haidar ba!!! Ya wuce da sanin da kikai masa can baya. Ina gudun miki wulakancinsa, in kinga yadda yake gara yaran jamaa a IUC zakisha mamaki. Bashi da mutunci ko kadan. Kin San Afrin ai? Yarinyar uncle Harris. Kwanciyarta a hospital 2, akan haydar dan banzan daga karshe dukan kawo wuka ya mata, wai ta addabi rayuwarsa. Dole uncle Harris ya dauketa ya mai da family house a Oregon, Saboda abun yaki ci yaki cinyewa. Kadan ke nan wasu ma ban iya fada, shiyasa na baki shawara matsayina na yayarki, but tunda kinji kin gani, shi kenan. Allah ya baku saa keda teacher din taki"
" zai aika abin da yafi haka ma, in dai wannan mai idon a tsaitsaye ne " hubby ta fada
Jikin Asiya yayi sanyi, don tasan afrin farin Sani, duk wani Abu da take takama dashi, bata kama kafarta ba. Don uncle Harris babban mai kudine da duniya gaba daya an San da zamansa. Yana cikin top 20. Haka ta fannin kyau, da wayewa. Mamakin haydar ya cika zuciyarta lallai halinsa sai shi, yanzu haka a gidan uncle Harris din suke zaune, shida yayanta Hafiz omer da friends dinsu. Amma ya iya karfin halin dukan yarinyar da ko kaffara baza ta yiba in ta ce baa taba dukanta ba, tunda tazo duniya. Don yar gata ce ta bugawa a jarida, ya daya mace tilo a wurin iyayenta. Amma ina so ya gama rufe mata ido. Take wata zuciya ta fara ayyana mata ita zata iya samun matsayin da sauran suka kasa samu. Don abun daga jini ne. Mu samman in tayi laakari da yadda suke shiri dashi.
" Wanda yai nisa baijin kira." Asima ta fada in I don't care tone
Ummul khair ta ce " Ku kyaleta ta gwada saarta. I'm so happy in har hakan ta kasance. Nasan kanina is in good hand. Dama ni bana wani son afrin din nan. Jin kanta yayi yawa, ga izgilabci. Gara ma daya mata haka, ko tayi hankali."
" me kika kawo mana gift ne,?" Aisha ta tambaya tana kokarin janyo kwalayen da driver ya shigo dashi.
Murmushi hubby tayi. " open it and see!"
Wanda sunan ummu sulaim ke jiki, ta mikawa Asiya " mika mata nata" ta fara kokarin bude nata kwalin don ganin abinda ke ciki. Su Ummul khair suka matso su tayata ganin abin da ke kunshe a kwalin da yasha rapping sheet mai kyau da daukar ido.....
[01/03, 10:41] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA