← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 20 OF 28

                            Part 18

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 26 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau
   
Not Edited.......
" just sign, let me cheek the door. " ta fada tana nufar kofar.

Ahmad ne da iyalansa. Yaran na ganin hubby ta bude kofar suka dale jikinta, suna dariyar murna. Itama dariyar ta fara tana kara rungumosu jikinta. Murmushi munaya tayi. " ni dai aban hanya na wuce, na gaji da tsayuwa." Dariya hubby tayi ta daga jenior, tare da rike hannun ashraf suka shiga ciki, tana musu bisimillah.

Da sauri hayder ya taso rungume dan uwansa yayi, tare da goga kumatun juna, kamar yadda suka saba. Sannan ya fara daga yaran sama suna dariya.
Tasnim ya amsa a hannun munaya, sannan ya gaisheta.

Jan dan uwansa yayi, suka nufi main falo. A kabar hubby da munaya da yara.

Kitchen ta nufa, yaran na biye da ita, sai zuba mata surutu sukeyi. Kayan sha ta hada a trey taba Mariya takai main falo. Sannan ta dauki na munaya suka fito. Zama tayi bayan ta ajiye trey din. Sannan suka gaisa, cikin mutunci kamar ba abunda ya hadasu.

" a mana afuwa, bamu samu zuwa ganin daki da wuri ba.?" Munaya ta fada tana murmushi

Murmushi hubby ta mayar mata " ba komai, ai gashi kunzo yanzu."

Gaba daya hubby ta kasa sakewa da ita, hakan yasa da yawan hiran ita da yaran suke kayansu, sai jefi jefi, munaya ke saka musu baki. Ita kanta kunyar hubby take ji, abinda ya Jamata rashin zuwa tun tuni kenan, sai yau da Ahmad ya matsa mata tukunna.

Mariya ce ta shigo, tama hubby sallama, lokacin tafiyarta yayi. Kallon ta hubby tayi. " Mariya yau kam, zaki min hakuri, zuwa dare sai in sa a mayar dake gida."  Kada kai Mariya tayi " to Anty, amma zaki kira mama ko? Don kartaga shiru."  Phone hubby ta dauka zata kira mmn Mariya. " ki barta kawai ta tafi, I will help u" munaya ta fada

Ba yadda hubby ta iya, ta sallami Mariya ta tafi.

Kitchen suka nufa, nan idon munaya ya raina fata. Da kallo takebin ko ina na kitchen din. " woww!!! Gaskiya Anty hubby gidanki ya burgeni ba kadan ba." Munaya ta fada tana kara kallon kitchen din.

Murmushi hubby tayi " na gode."

" me zamu dafa?" Hubby ta tambayeta.

" abun dadi, kin san nayi missing din girkinki sosai." Munaya ta fada tana murmushi

Murmushi hubby tayi, tunowa da old-time.

Book ta mikewa munaya "  duba mu gani, ko akwai abunda zamu iya yi a ciki."

Wani hadadden drawer hubby ta bude, ba komai a ciki sai chocolate kala kala, da kwalayen Lipton, green tea, black tea, English break fast, flavour tea gasunan kala kala. Chocolate ta zuba a plate, ta nufi falo inda su jenior ke kallon cartoon. Ta basu, ta koma wurin munaya, da ruwan ido ya hanata tsayawa a kan girki daya.

Suna aiki, suna hira jefi jefi. Munaya ta kalli hubby dake soya rice. " Anty hubby don Allah kiyi hakuri ki yafe min abinda ya faru, wallahi sharrin shaidan ne, da zugar su Anty samira. Sai rikicin aurenki da Abdul Karim nake jin komai, na makircin da take kullawa a kanki. Kunyarki ta hanani zuwa gidan nan. Don Allah kiyi hakuri. "

Murmushi hubby tayi, tare da sauke ajiyar zuciya. " na dauka kinfi kowa sanin halina, a lokacin sama da ita? Saboda nafi kusa da ke a kanta. Na dauka ko wani ya fada wannan maganar a kaina, ke me bada shaida ce gareni. Bazan boye miki ba naji zafin abinda kika mun a cikin jamaa, wanda da ni dake ne, bazan damu sosai ba. Amma ba komai na yafe miki, komai ya Riga ya wuce. Sai dai ina son kisa a ranki. Hubby bata taba son wani ba, bayan Yusuf. Tsakanina da Ahmad mutunci ne, da ganin girman juna, Nothing more."

" kishine ya rufe min ido, a lokacin. An sha kawo min gulmar, ban taba daga kai ba, sai lokacin. I'm sorry "

" ba komai ya wuce. I understand." Hubby ta fada

Hira suke yi, suna dariya kamar ba abinda ya taba faruwa. Dama can akwai shakuwa tsakanin hubby da munaya. Munaya bata da matsala, barta dai da son class, komai nata irin na big class take yi.

Hayder ne ya leko, ya shaida musu sun wuce masallaci, har da yaran.

Suma lokacin sun kammala komai, hubby na wanke kayan da suka bata, munaya na goge -goge. Sai da hubby ta shirya musu abinci a dinning din main falo, nasu kuma, suka haura dashi falon sama.

Wanka sukayi bayan sun idar da sallah. Wani hadadden arebian dress hubby taba munaya tasa. Sannan suka nufi falo don ba ciki hakkinsa.

Santi kawai munaya ke zubawa. " Allah kinji da dinki, ina ma ni na iya girki haka. Munyi missing abincinki sosai wallahi. " murmushi hubby tayi. Don a zamanin baya sau da yawa gidanta munaya take zuwa suyi girki ta dauka zuwa gidanta. Expectially weekend's. Wani lokaci kuma, hubby ke girkawa ta aika musu.

Bayan sun tattara wurin. Munaya ta dauko Jakarta. Mikawa hubby wata Leda tayi. " gashi kowanne da yadda zakiyi anfani dashi, suna da kyau sosai. Tun daga Niger aka kawomin su." Amsa hubby tayi, tare da godiya. Don bazata iya ce mata tabar kayan ta ba. Ko ba komai ta ajiyewa  Aisha ko su ummu sulaim. Duk wandda Allah ya kawo ta.

Wani tablets ta fito dashi, guda biyu tasha daya ta mikawa hubby daya. " ki sha wannan ki gani, a kwai aiki. In ya miki next time in zaa kawo min, zan ce a kawo kwali biyu."

Kai hubby ta kada " ki barshi kawai Maman junior in zaa kawo miki, a kawo mana tare." Ta fada don karta dagota.

" no. Kin san kalan kyansa.? U have to try it." Munaya ta fada tana ballo tables din daga gidansa.

Ganin hubby tana mata wasa da hankali, yasa ta bata rai. " Allah sai kin sha, ke matsalata dama dake kenan. Dole mutun ko yana da kyau ya kara da wanka." Ruwa ta zuba a cup ta mikawa hubby.

Dole yasa hubby amsa. Ruwa ta kurba, tare da jefa tablet din a baki, da niyyar ta ma munaya wayau ta ajiyeshi a bakinta for some second taje ta zubar. Tana jefawa a bakinta ya wuce. Ido ta zaro. Tare da  fadin " innalillahi wa inna ilaihir rajiun." A kasan ranta.

Dariya munaya tayi, ganin yadda hubby keyi da fuska. " bafa shi da wani taste," ta fada don a tunaninta, ko taste din ne baima hubby ba.

Hira suke yi sama, sama, munaya ta kalli hubby. " wai Anty hubby bakya gajiya da wannan zunbulelen hijab din ne? Tun da muka zo kike ta fama, har girki duk dashi, ko zafi bakyaji? Kamar wata matar malan."

Murmushi hubby tayi, ba tare data tankawa munaya ba.

" au!!!! Sorry, ashefa matar aramma ce. Amma don Allah adinga cirewa ana shan iska. Ni ina zan iya?, sallama Allah- Allah nake in idar in cire."

Murmushi hubby tayi kawai.

Sai after 8 su hayder suka shigo. Yau ne rana ta farko da hayder ya saka abincin hubby a bakinsa. Shi din ma don gudun kar Ahmad ya gano, irin zaman da sukeyi ne. Yasa shi zuba soup din kaza.

Ahmad kam santi yayi ta zubawa. Tare da gayawa hayder yadda sukayi missing girkin hubby. Shi kansa bai san ta iya girki haka ba. Yasan dai duk lokacin da ta kawo, kamshin girkin na kayatar dashi, amma bai taba marmarin dan danawa ba, duk da santin da yake jin su Hafiz nayi.

Sai after 9 su Ahmad suka musu sallama. Set din sarkar gold mai kyau da girma yaba hubby. A matsayin gudunmawarsa. Godiya sosai ta masa. Tare da cika yaransa da kayan zaki, Leda guda. Suka rakosu har mota.

Cike da kewar juna suka rabu, suna daga musu hannu.

Suna shigowa hayder ya wuce sama, ba tare da sun cewa juna komai ba. Duk da taso ta tambayeshi maganar takardar yarjejeniyarsu. Amma ganin yadda ya hade fuska, yasa itama ta shareshi.

Kayan da suka ci abinci dasu ta tattara, tare da gyara wurin.  Sai da ta wanke su tsaf, sannan sauran abincin ta sasu a containers ta sa a fridge. One this about her. Bata son barin ko cokali, ya kwana ba tare data wanke ba, Matukar anyi anfani dashi.

Direct toilet ta nufa, ruwan sanyi ta sakarwa kanta, Saboda yadda take jin jikinta.

Hadadden man culachum, ta shafa sama- sama, tare da sanya kayan baccinta, Aimless da boom shot. Fink colour. Gashinta ta kama ta nade shi, kafin ta saka hula pink.

Shigewa cikin duvet dinta tayi tare da karanto adduoin kwanciya bacci.

Juye- juye ta fara, tana jero tsaki. " haka kurun ina managing kaina, tazo ta tsokalomin fitina." Wata zuciyar Hubby ta fada. Tana kara Jan tsakin.

Zuciyarta ce ta fara mata wasi- wasin anya kuwa tasa key a kofarta? Don shigowarta Allah -Allah take ta shiga toilet ta watsawa kanta ruwa. Ganin ta kasa samun natsuwa yasa ta sakko ta nufi kofar, cike da kasala, da nauyin jiki. Tana kokarin kai hannunta kan kofar, yana turo kofar tare da shigowa cikin bedroom din.

Sanye yake da kayan bacci, marasa nauyi, Riga da dogon wando. Light blue.

Ido hubby ta zaro tana binsa da kallo, don bata taba tsammanin yanada karfin zuciyar da zai sake shigo mata bedroom ba. Matsawa tayi, ganin jikinsu na neman gogar na juna. Hakan ya bashi damar murza key din, tare da zareshi daga jikin kofar.

Zuciyarta ta fara dukan tara- tara, " what bring u hare at this time? " ta fada tana mai hadiye yawu dakyar. Don a tsorace take, smacking yayi, yana kara jingina da kofar, hannunsa duka biyu nade a kirjinsa, kamar yadda ya harde kafafunsa biyu. Daga inda take tsaye tana iya hango faffadan kirjinsa dake bude, ga six pack dinnan sun fito sosai masha Allah. Kana ganinsa kasan akwai karfi, yadda damtsen hannunsa suke a murde, ga jijiyoyi sun fito  sai daukar ido suke,  jikinta ne ya dau rawa ganin kallon da yake binta dashi, yasata tunowa da kayan dake jikinta. Da sauri ta juya don ta sa hijab dinta.

Bataji takowarsa ba, sai ji tayi an kwace hijab din. Da sauri ta waigo sukayi ido hudu. Jikinta na rawa kamar yadda muryarta ta dau rawa.

Wurga hijab din yayi can gefe. " what come over u." Ta fada cikin rawar murya.

Murmushi yayi, tare da daga mata gira. " laifine don miji ya shigo dakin matarsa?" Ya fada in husky tone. Zuciyarta ne ya kara tsananta bugawa.

Kallonta sosai hayder keyi tare da furta " fatabarakal lahu ahsanul khalikin." A kasan zuciyarsa. Wani irin filling ya ke fisgarsa zuwa gareta. Duk da ba abin daya shigo dashi ba kenan.

Hannunta ta hada duka biyu, jiki na bari. " don Allah ka fita, koma meye zamuyi magana da safe."

Bakinta yake kallo zuciyarsa na saka masa abubuwa da yawa kanta. A hankali ya fara takowa zuwa gareta. Ganin haka yasa ta fara ja baya, still hannunta a hade, tana mai maita " please please. " gaba daya ta gama rudewa da yanayinsa.

Ritsata yayi, lokacin da takai bangon dakin. Hannayensa duka biyu yasa ya dafe bangon dashi, ya sata a tsakiya. Zuwa lokacin hubby sumane kawai batayi ba don tsananin fargaba, don gaba daya ya canza mata, kamar ba hayder data sani ba.

Fuskarta ya dago da daya hannunsa. Da sauri ta runtse idonta, don bazata iya kallon cikin idonsa ba. Cikin karfin hali " please hayder don't do this to me, I'm your sister, Please."

Murmushi yayi, har tanajin sautinsa a kunnenta. A hankali yakai bakinsa kan nata. Gaba dayansu wani shock ne ya ziyar cesu a tare, ga hubby kan tsananin tsoro, ne ya kara cika mata zuciya. Datse hakoranta tayi, taki bashi damar samun abinda yake so. Tana jin sautin murmushinsa a kan fuskarta. Gaba daya ya rungumota jikinsa, yayin da daya hannunsa ya fara yawo a jikinta. Still bakinsa na kan nata, yana lasan labbanta a hankali kamar yaro ya samu alawa.

Kokari ta fara don ta kwace jikinta, amma ko gezau, hannunsa da taji a kirjinta, yasa ta bude baki, don tayi ihu. Hakan yabashi damar zura harshensa sosai cikin bakinta.

Duk yadda hubby taso kwatar kanta ta kasa, tun tana dan turjewa, har itama sakon ya fara kaiwa ga kwakwalwarta. Abinka da an dade baa haduba, ga aikin munaya.

Gaba daya tsayuwar ta gagaresu, dagata yayi cak, zuwa saman bed dinta.

Sunkai tsawon lokaci, suna sarrafa juna. Hayder yakai kololuwar bukatuwa da ita, yana gaf da cimma burinsa. Tunanin basuyi nafila daya dace suyi ba, ya masa birki, duk yadda yaso yayi ignoring din abun ya kasa. Dole yadan janye daga hubby yana sauke ajiyar zuciya, Tare da gangameta a jikinshi sosai. Kara narkewa tayi a jikin nasa. Don gaba daya tunaninta ya dade dayin kaura daga jikinta. Gaba daya hayder ya gama rikitata da salonsa. Daga ita har shi ajiyar zuciya suke sakewa a hankali.

Iskar bakinsa, ya hura mata a fuska. Far tayi da idonta, wanda ya kara mata kyau. Kar idonta ya sauka a kan hayder. Kamar ringing din bell haka taji a tsakiyar kanta. Ido ta zaro, tare da mikewa da sauri. Kokarin sauka daga bed din tayi, zuciyarta na zafi, da kuna, takaici, da haushin kanta duk sun cika zuciyarta a lokaci daya.

Kara tayi, tare da janye duvet din dake tattare a gefe, ta rufe jikinta, tare da yin toilet da gudunta.

Yana daga kwance yana kallonta, gaba daya jikinsa ba kuzari. Murmushi yayi ganin tayi toilet da gudu.

Tana sa key din kofar, ta jingina tare da fashewa da wani irin kuka, mai cin rai. A zaune take dirshan tana kuka iya iyawarta.

A hankali ya tako zuwa jikin kofar, kwankwasawa yayi, yana kiran sunanta. Daga inda yake yana jiyo sautin kukanta.

Yakai 15 min a tsaye, yana faman kwankwasawa, taki budewa.

" ka fitar min a daki, ban son ganinka, mugu sai Allah ya sakamin." Ta fada cikin muryarta data fara dashewa don kuka.

" just open the dam dor." Ya fada in high tone

" anki din. Da in kwana da kai gara na kwana a toilet." Ta fada

Ranshi ya fara baci, yanzu kam. " in kin so ki shekara a ciki." Ya fada cikin bacin rai

" yafi min ganinka ai, mara kunyan banza. Tun mutun bai tafasa ba yana son ya kone."

Murmushi mai ciwa yayi " ni kike gayawa wannan maganar, don na nemi hakkina a wurinki? In kin isa ki fito ki gaya min face to face mana." Ya fada cikin bacin rai

Tsaki hubby tayi. " duk maitarka wallahi bazan fito ba. Kuma An fada din kayi abunda zakayi. Mara kunyan yaro. Kwalelen kare da hantar kura, nan gani nan bari, kar kuma in kara ganin kafafuwanka a dakin nan, in ba haka ba duk abinda na maka, kai ka siya da kudinka."

Shi abinma dariya ya fara bashi. Wannan shine, ga tsoro ga ban tsoro. " ki jika kisha in kin isa!! Keep that in mind da kanki zaki kawomin kanki, ina shararren wurina. Bana bukatar sake zuwa dakinki. Wannan shine alkhawarin hayder to u."

" Allah ya kiyaye,." Ta fada tana Jan tsaki.

Murmushi yayi, " zamu hadu ne, very soon, zakiyi bayani." Ya fada yana maida kayansa. Sannan ya fita zuwa dakinsa.

Wanka ya sake, sannan yayi shirin bacci. Daya rufe idonsa moment dinsu yake gani a idonsa. Murmushi yake ta sakewa cike da nishadi, don shi kadai yasan garar daya kwasa, duk da bai kai inda yaso ba, amma he's happy. A haka har bacci ya sace shi.

Hubby kam, jin fitarsa, yasa tai saurin fitowa ta sawa kofarta key. Toilet ta koma, tayi wanka, tare da Dirje jikinta sosai, tanayi tana hawaye, tuno da yanayin da suka kasance ita da hayder. Ihu ta sake tare da durkushewa a wurin. Abune da ko a mafarki bata taba kawawa ba, ta dauka ko giyar wake hayder yasha bazai tunkareta da bukatar shiba, but she is mistaken. Tabbas ta yadda namiji ba kunya, tunda har ya iya shafawa idonsa toka.

Allah ya isa tafi kwando dubu, ta jawa munaya da hayder. A ganinta da badan tablet din munaya ba, ba abunda zai sa tayi losing control dinta irin haka.

Yau gaba daya bacci kaura yayiwa hubby. Tunanin rayuwa, da tunanin Yusuf su suka tsaya mata a rai. After all mamakin hayder da karfin halinsa. Tabbas sai ta dau babban mataki a kansa, in har tana son ta zauna lafiya......
Yau da farin ciki hayder ya tashi, rabon da ya tsinci kansa cikin farin ciki haka, tun kan aurensa da hubby.

Har ya gama break fast, ba hubby ba alamarta. Dama ya kwana da sanin ganinta zai masa wuya kam. Murmushi yayi daga gani na mugunta ne, ya kara kai kallonsa steps din. Key din bike dinsa ya dauka yayi gaba.

Sai da ya dan tsaya typing a wayarsa, yayi sending tukunna, ya tada bike dinsa, malan idi ya wangale masa get, tare da kwasar gaisuwa. Ya fice abinsa.

Tana tsaye daga window taga fitarsa. Tsaki taja. " jishi sumi sumi, kamar in an sa masa hannu a baka bazai ciza ba." Ta fada tana sake labulen. Sannan ta dau hijab dinta ta zunbula, ta sakko donta nemama kanta abin da zataci.

Sun gama gyara gidan, tare da sa turaren wuta, mai matukar kamshi. Ta haura sama donta dauko wayarta data manta a bedroom dinta. Miss calls ne, sai sms. A hankali ta fara bin sms din. Har tazo kan wani un save number, kamar bazata budeba wata zuciyar ta ce ta bude tagani. " ki shirya kije ki gaida su mommy, Hajiya da Hajiya babba, Hayder "  tsaki taja duk da taji dadi, don ta dade tana son zuwa, amma saboda sai ta tambayeshi, yasa ta gwammace taita zama a gida.

Cike da murna da doki ta fara shiryawa, cikin wani rantsatstsen less light yellow, dinkin doguwar Riga, taji aikin da stones. Light blue na hijab mai hannu, da shoe and bag light blue. Tayi kyau sosai.  gida ta kai Mariya, sannan ta wuce gidan Alhaji babba.

Tarba Sosai ta samu, tayi saa Alhaji babba na gida. Turaruka masu tsada da kamshi, ta kawo musu. Ta dade tare dasu, sannan ta musu sallama, nasiha sosai suka kara mata.

Gidansu ta wuce, a harabar gidan taci ta tarad da su junaid. Ranta bai so ba don yanzu dukansu haushinsu take ji.
Da faraa suka gaisheta. Dole haka ta saki fuskarta ta amsa musu, tare da shigewa ciki. A kofar shiga falon mommy Hauwa sukayi karo da hayder dake fitowa, Da sauri taja baya. Tsayawa yayi, yana kallonta. Kin dago kanta tayi, don haushinsa dosai ta keji, da kunyar ya gama ganeta. Murmushi yayi tare da furta " sorry " a kasan makoshinsa. Ya bi gefe ya wuce.

Da harara ta raka shi, har ya bacewa ganinta, sannan ta shige ciki da sallamarta.

Mommy Hauwa na zaune a falo da jafar hubby ta shigo. Tana arba da mommy Hauwa a zaune da gudu ta je ta rungumeta.

Dariya mommy Hauwa da jafar suka sa. Jafar ya ce " yar halas taki anbato, yanzu dama mijinki yake cewa kina nan zuwa, Ashe ma har kin iso." Harararsa tayi, jin ya kira hayder mijinta.

Dariya yayi, don bai gane dalilin harararba. " harara daga zuwa? Allah ya baki hakuri."

" nayi fushi da kai da jabir. Don haka karma ka kulani." Ta fada tana turo baki cikin shagwaba.

Kunne ya kama " tuba mukeyi sis, jiya muke maganar zuwa wurinki da jabir.'"

Harararsa tayi " ba wani nan!! Don ka ganni ne, shiyasa. Amma na tabbatar kun manta dani kwata kwata, ba zuwa ba waya. "

Mommy Hauwa ya kalla, yana mata alamar tasa baki.

Dariya mommy Hauwa tayi. " karka sani a ciki, ba ruwana."

" kai mommy!! Kina wurinfa muke maganar zuwa gidanta." Ya fada cikin shagwaba, kamar wani karamin yaro.

" zan rama, very soon. "  ta fada

" very sorry, muna nan zuwa, da zaran jabir ya dawo zamu zo." Ya fada cikin miryar lallashi.

" ina nan ina jira." Ta fada

Mommy Hauwa taji dadin ganin yadda hubby ta kwantar da hankalinta, tayi kyau ta murje. Duk inda hubby ta gilma idon mommy na kanta, cike da jin dadi.

Hubby taji dadin yadda mommy Hauwa ta sake da ita, suka sha hirarsu, cikin hikima ta dinga tambayar hubby game da zamanta da hayder. Hubby nuna mata tayi komai normal ba wani problem. Sai after 2 sannan tai sallama da mommy ta nufi main house. Duk da bataji  dadin rashin ganin daddy dinta ba, saboda tafiya da yayi.

Part din Mmn samira ta fara zuwa, kamar yadda ta saba. Sun gaisa, cikin mutunci, hubby bata nuna mata komai ba. Sai dai ta lura jikin mmn samira yayi sanyi, kusan kamar ma kunyarta take ji. Bata dade ba, ta nufi part din Mmn Yusuf.

Itama kadaran- kadahan, ba yabo ba fallasa. Kamar all times, har yau ta rasa abinda ta tsarewa matar. Shin kaso dan mutun Ashe yakan zama laifi? Meye laifinta don ta nuna tsantsar soyayyar danta? Da wannan tunanin ta nufi part din Hajiya.

Zo kaga murna, kamar waanda suka shekara basuga juna ba.  Hajiya ma taji dadin ganin hubby. Sai washe baki take, cike da farin ciki. Da kanta tama hubby jagora zuwa part din Alhaji Jamal. Shima yayi farin ciki da ganin hubby.

Sai 5pm Hajiya ta ce, ta tashi ta tafi yamma tayi, badon taso ba, haka ta ja motarta zuwa gida. Cike da kewar yanuwanta.

               ******************
" Salamu alaikum, malan idi yau ba redio ne.? Wani dattijo dake cikin keken guragu ya fada, bayan ya iso wurin da malan idi ya kafa kujerarsa a wajen get din gidan.

" yau kunne nake son ji, bana son hawan jini ya kamani tun yanzu. Don na lura jin abinda ke faruwa a kasar nan ba abunda zai kara ma mutun sai hawan jini." Malan idi ya fada cikin dan bacin rai.

" shi yasa in ba a wurinka ba, ba ruwana da redio." Gurgun mutumin ya fada

Kallonsa sosai malan idi yayi. " me ya kawoka kuma yanzu? Nafa kusa fara maka rashin mutunci, baka tashi zuwa wurina sai kaji kamshin girkin hajiya na tashi, ka dai daici an kusa gamawa, ka wani lallabo, kai baka koshi ba, ni ban koshiba."

Marairaice fuska gurgun mutumin yayi. " bama haka da kai. Kasan ance duk Wanda yaci shi kadai, zai mutu shi kadai. Ci bibbiyu yafi albarka."

"Ai sai kayi, gaba don yau Hajiya bata nan." Malan idi ya fada yana harararsa

Dariya gurgun mutumin yayi " ina fa jiyo kamshi, tun daga dakina. Nakuma san daga gidan nan yake fitowa. Don ni yanzu saboda lakantar kamshin girkin Hajiya, nakan iya ban banta kamshin Jan zakara, da farin zakara, yau kam kamshin kifi na jiyo."

Dariya sosai malan idi yakeyi " lallai abin naka, babbane. To da gaske bata nan. Wannan gurkin oga ne, don shi kadai ne a ciki."

" haba ai nasan daga gidan nan kamshin ke fitowa, don duk Unguwar nan ba inda zaka jiyo kamshin girki, mai sa miyau tsinkewa sai gidan nan. Allah ka mana arziki, mutun ya dace da matar data iya girki, ai ka more zaman duniya. irin matan nan ko ruwa suka dafa maka dadinsa da ban ne. Ashe shima alhajin gwanine a girki. Yau zamuci ma ban bance Wanda yafi wani."

"Kaga tashi kayi gaba abinka, ban san sa ido. In kuma ka yadda oga yajika kana yaba girkin matarsa ba ruwana"

" gaskiya na fada ai!! Inda ni  na samu ina kwasar girki haka ai  bazan koma  kauye ba.  ko bazasu biyani ko sisi ba, in dai zan kwashi girki bani da matsala."

Dariya malan idi yayi, don yasan mutumin nasa, kan girki.

" Allah ya shiryeka. Yau dai bamu da kwano a gidan nan. Don haka kai zaka kawo mana naka abincin muyi maneji."

" sai fa manejin kam." Gurgun mutumin ya fada yana tabe baki
 
Hango motar hubby yayi, malan idi ya tashi da sauri ya wangale mata get, gurgun mutumin kam sai wangale baki yake yana daga mata hannu. Sallama ta musu, bayan ta dan sauke glass, ta wuce ciki.

             ********************

Tun 4 hayder ya dawo, kitchen ya nufa, bayan ya rage kayan jikinsa. Daga shi sai  short nicka da singlet.

Irish ya soya, da onion source, dayaji attaarugu da kayan kamshi. Sai catfish daya gasa.




Hubby na shigowa, sama tayi. Don ta tabbatar yana gida ganin bike dinsa a compound, sannan gidan a bude, ga kamshin girki dake tashi.

Key tasawa ta kulle kofarta. Wanka tayi tare da dauro alwala, don magrib ya gabato. Ta dau takardun islamiyyarta ta fara mura jaa.

Yana jin shigowar motarta. Dai dai lokacin da ya fito ta kofar kitchen din, ita kuma tana shiga ta falo. Malan idi ya kira ya mika masa plate cike da chips, roasted fish and Onion source. Washe baki malan idi yayi, yana godiya. Don yau ya fitar da rai da abincin gidan, ganin uwar  dakin nasa bata nan.

A wani square plate ya hada nasa kwanin shaawa. Ya sa rapper din Leda  ya rufe, ya daura a kan deepfreeze. Daki ya koma ya watsa ruwa da sauri sauri, ya daura alwala.  ash color din jallabiyya yasa ya nufi bike dinsa, cikin sauri yabar gidan don karatowar lokacin sallah.

Sai da ta idar da sallah tare da azhkhar, ta fito don daukan cake. Don bata jin yau zatayi wani girki. Kamshi ne ya doki hancinta, duk da na'urar fitar da kamshi amma kitchen din a kwai kamshin girki. Idonta ne ya sauka a kan plate din hayder. Murmushi tayi tare da ajiyar xuciya. " tsuntsu daga sama gasashshe." Ta fada tare da daukan plate din tayi dakinta. Key tasa ma kofarta, don ta gama fita kuma, sai in Allah ya kaimu gobe.

Abincinta taci hankalinta kwance. Gashi yayi mugun dadi, rabon dataci gashin kifi irin haka, tun zamanin school, Da take cinye masa abinci.

              ******************
Koda hayder ya dawo, yaga babu plate babu dalilinsa. Murmushi kawai yayi, ya bude oven ya dauki wani fish din. Irish ya fito dashi a freezer yayi fraying. Tsaf ya hada plate dinsa ya nufi falo.

Yana kallon  huda tv, yana cin abincinsa cike da natsuwa. Nasrin ce ta kirashi, wani kayataccen murmushi yayi, tare da daga wayar.

Sun fi 30min suna waya, kafin sukayi sallama.

               *****************

Kamar a mafarki, hubby ta fara jin kukan mage ta window dinta. A tsora ce ta tashi zaune, tana raba ido a duhu, jikinta sai bari yake, in akwai abinda take balain tsoro to mage na ciki.

Inuwar abu taga ya gilma ta windonta. Da yake ciki akwai duhu, waje akwai hasken fitila. Ta jikin labulenta tana iya ganin inuwar abu na kaiwa da komowa. Still kukan mage ne, ba imagining take ba. Ai da gudu ta duro daga gadon, har tana buge kafa.

Daga jikinta, har zuciyarta bugawa suka fara yi. Musamman jin magen ta tsananta kuka, na yanzu ma yafi mata kama dana jariri.

Da gudu ta fito a dakin, daya dakinta da tunda tazo, ko sau daya bata taba kwana a ciki ba ta shiga, tare da danna key.

Ajiyar zuciya ta fara saukewa tana dafe da kirjinta, dake bugawa kamar zai fito.

Adduoin ta fara jerowa, daga ta kai wannan ta cafko wannan,.  Kwanciya tayi, still a tsorace take, tana son tashi ta kunna ac amma tsoro ya hanata kwakwaran motsi.

Windows din da yake a Jere suke dana bedroom dinta. Magen ta dawo ta nan, kamar tasan hubby ta gudu a can. Kuka ta fara tare da yakushin window din. Kamar tana son budewa. Ai a 360 hubby ta fito a dakin. She have no idea kawai tsintar kanta tayi a dakin hayder.

Da sauri ya dago kai yana kallonta, da gudu ta karaso kan kujerar da yake zaune, ga system a gabansa,. Zama tayi a kusa dashi, tare da sakalo hannunta a nashi. Jikinta sai bari yake.

" ikon Allah, lafiya?" ya fada  Kofa take nuna masa, still tana makale da hannunsa.

Ganin ta kasa magana, yayi yunkurin tashi, yaje ya ga meye. Da sauri ta janyoshi tare da kara kan kameshi.

Bakinta na rawa " mag, mage ce."

" mage?" Ya fada yana kallonta.

Kai ta kada masa. Alamar eh!

" OK. Sakeni in je in ganta. But how come mage a gidan nan?" Ya fada yana kokarin raba hubby da jikinsa.

" please don live me along. I'm scared" ta fada baki na rawa

" what I don't understand shine, a cikin dakinki kika ga magen, ko ya akayi?" Ya fada yana tsareta da mayun idonsa.

" a window na, tana son ta shigo."

Tsaki yayi, tare da harararta. " na dauka ma dakin naki ta shigo ai! Kike rawar jiki haka."

Sun kai 10min ba Wanda ya kara tankawa dayansa. Zuwa yanzu hubby ta fara samun natsuwa, koba komai tasan she is safe known.

Kallonta yayi, ya kalli hannayenta dake sakale da hannunsa daya. " sakar min hannu malama." Ya fada in his husky voice.

Da sauri ta saki hannun tana dan tura baki.  Haushinsa, da haushin kanta, ya kamata lokaci daya. Matsawa tayi, ta takure wuri daya, tare da daura kanta a kan hannun kujerar. Da yake kujerar mutun uku ma zasu iya zama a kai.

Kallonta yayi, yana tabe baki. Sanye take da night dress riga ce dukanta bata kai gwuiwarta ba. Mai dan karamin hannu. Pusher pink da drawing din apple a gaban rigar. Kanta ko dankwali babu, Ta kamashi da ribbon.  Kansa ya dauke, ya ci gaba da aikinsa.

Hannunsa yayi tapping a dai dai, kan hubby da ke bacci, hankali kwance. Ido ta bude a hankali ta sauke su a kanshi. Gaba dayansu sai da gabansu ya fadi.  " go to your room, zan kwanta." Ya fada yana mai goge gashin kansa, alamar daga wanka ya fito. Sai lokacin ta lura daure yake da White trowel, sai karamin da yake goge kai dashi. Da sauri ta kauda kanta.

" don Allah ka barni in kwana a nan, tsoro nake ji." Ta fada cikin siririyar muryarta.

" no!!!! U can sleep here.?" Ya fada yana tsareta da idonsa.

" I sleep right hare, I won't disturb u." Ta fada, cikin yanayin ban tausayi.

" what u say yestaday?" Ya fada still idonsa a kanta.

Gabanta ne ya fadi, tunowa da karansu na yestaday night. Kanta ta sunkuyar tana wasa da yatsunta.

Sai da yayi shirin baccinsa tsaf, sannan yakai kallonsa kan hubby data dungule wuri daya.

" Habiba. "  ya kirata in high tone. Dagowa tayi ta kalleshi, tare da kauda idonta.

" bafa zaki kwanamin a daki ba. Ki tafi toilet dinki ki kwanta. Amma ba nan ba."

Kwal kwal tayi da ido,  cikin rage murya da lallashi. " Allah tsoro nake ji. Kayi hakuri ka barni in kwana a nan please. "

Daure fuska yayi, kamar bai taba dariya ba, kallo daya hubby ta masa jikinta ya kara daukar mazari. Tafi kowa sanin halinsa, in yaso rashin mutunci. Tunowa da school tayi, Ita kuwa a yanda take jin tsoron fita, ko yankata zai yi, ba inda zata.

" I say get out!!! Tun kan in dagaki in watsaki waje." Ya fada ransa a bace

Takowa tayi a hankali zuwa inda yake hannu ta hada " don Allah hayder kayi hakuri, ka barni a nan, kaifa dan uwana ne, bazaka so abinda zai cutar dani ba."

Shiru yayi yana kallon yadda jikinta ke rawa, hatta muryarta rawa take. Murmushi ne yakusa kwace masa. The mighty hubby ke bashi hakurin ya barta ta kwana a dakinsa. Wonder shall never end. Rai ya kara hadewa " on one condition. " kai ta daga masa baki na rawa " meye condition din?"

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali. " u do what I ask u to do, without a guying. In ba haka ba I will trow u out. "

Kauda kanta tayi, saboda kallon da yake mata, she can handle it. Hawayene suka fara bin kumatunta. She never been so helpless like this. " please hayder don't do this to me, I'm your brother wife, please. " ta fada tana durkushewa a wurin, tare da sakin kuka mai tsuma rai.

Idonsa ya runtse, yanajin tausayinta, tare da jin kukan har tsakiyar kansa. Bai taba tausayinta kamar lokacin rasuwar Yusuf da kuma yanzu da take gabansa,  so Helpless.  Dan uwansa ne ya fado masa a rai, gaba daya yaji hankalinsa ya tashi. Jingina yayi da bangon dake kusa dashi, still idonsa a rufe, ga jijiyoyin kansa sun fito sosai.

Sun kwashe 12min a haka, kafin ya bude jajayen idonsa. Still tananan a durkushe a wurin.

Sai ajiyar zuciya ta ke saukewa da Jan hanci.

Dagata yayi cak, ya nufi Kofa da ita. Hubby kam ganin zaiyi waje da ita yasa ta fara kokarin saukowa, amma ta kasa. A wajen kofarsa ya sauke ta. Tare da zuba mata jajayen idonsa. " go." Ya fada a takaice.

" juyawa tayi, da nufin tafiya dakinta, cikin Jan kafa.

Daga idon da zatayi, sukayi ido hudu da magen tsugun ne a kofar dakinta ta zubo mata manyan  Golding eyes dinta. Ai a 360 ta kwasa ta koma dakin hayder tana ihu, magen ta rufa mata baya.........
[08/03, 20:31] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 20 · 0% Book details