← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 19 OF 28

                            Part 17

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 24 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau
   
Not Edited.......


NOT EDITED

Allah Allah Mariya ta ke hubby ta dawo, ta gaya mata wani balarabe yazo. Bata ji dadi ba data dawo dauke da ruwa ta samu baya nan.

Hubby koda ta dawo ta samu malan idi na goge bike din hayder bata kawo komai ba, ta nufi cikin gida.

Ko Jakarta bata ajiye ba, Mariya ta fara bata labarin zuwan balarabe. " Anty baki ganshi ba, mai kyau sosai. Na ce yanzu zaki dawo, kafin in shiga in dauko masa ruwa, ya tafi."

Gaban hubby ne ya fadi, hayder ya dawo. Jakarta ta dauka tayi sama.

Wunin ranar basu hadu ba. Da yamma su junaid suka zo, sun shiga sun gaisheta kamar yadda suka saba. Abubuwan sha ta tura Mariya ta kai musu, kafin ta tafi gida. Don in tazo da safe sai 5 take komawa gida.

Yauma a wurin basketball ta jisu, har kusan magrib, sannan suka nufi masallaci.

Yau hubby tun magrib ta rufe dakinta, don har lokacin tana cikin jimamin yadda hayder zai yi reacting kan maganar zuwa islamiyyarta.

Ana sallar ishai, ya nufo gida, yau ko tsayawa karatun da yake dauka bayan sallar ishai bai samu ba. Dakin hubby ya nufa, amma ina yajita a kulle. Kwafa yayi, sannan ya nufi nashi dakin.

                  ****************
Da sauri -sauri, gudu -gudu, kamar yadda ya saba saukowa daga steps ko hawa.

Dinning table din da hubby ke zaune tana break fast ya nufa, kujerar da take facing dinta yaja ya zauna.

Kirjinta sai faman bugun tara-tara yake yi, mu samman kallon da yake binta dashi, yasa jikinta yin sanyi, ga wani faduwar gaba da take ji. Daurewa tayi, ta ci gaba da cin abincinta.

Tambayar daya watso mata ne, ya sata saurin dago ido tana kallonsa. Shima idonsa a kanta. " ina kika je? Jiya na dawo, bakya gida?"

Tabe baki tayi, tana juya dankalin da fork din hannunta. " meye damuwarka, don na fita?"

Shiru yayi, yana karantar yanayinta. " da izinin wa? Kika fita?" Kallonsa tayi tare da waro ido waje, cikin mamakinsa. Musamman yadda yayi tambayar, Tamkar uba a gaban dansa.

" don zan fita sai na tambayi wani?" Ta fada, tana kai dankali bakinta.

" yes, tunda ba zaman kanki ki keyi ba ba?!"

" Allah hayder ka fita a idona! Kai har ka isa, inki fita, sai na tambayi izininka? Ka sani duk lokacin da naji fita, fita zanyi." Ta fada cikin daga murya kadan.

Jingina yayi, sosai a jikin kujerar. " ki sake fita bada izinina ba kiga, yadda zamu kwashe, karki rainamin hankali, nasan aure nasan kuma yadda yake. So be careful."

" baka isa ba hayder kayi kadan! Ka kafamin doka da oder."

Tashi yayi, ya nufi kitchen " let see." Ya fada yana shigewa ciki.

Yana falonsa yaji tashin motarta. Lekawa yayi, ai kuwa fitan ta sake yi.

Murmushi yayi, " yaro bai san wuta ba, sai ya taka." Ya fada yana gyara zamansa, ya ci gaba da aikin da yake yi a system.

              *********************
Yau makarantar batawa hubby dadi ba. Don yau basuyi darasiba ko daya. Ilah waazi da aka musu. Daya shafi mata yan wuta, da dalilan shigarsu wuta, kamar hadith's din da yazo na cewa mafi yawan yan wuta mata ne, kuma sun shiga wuta ne, saboda yawan butulcewa mazajensu, da mazansu zasuyi shekara da shekaru, suna kyautata musu, duk ranar da aka samu sabani, sai ta ce meka taba min. Sannan malan ya gangaro kan sauran dalilan dake sa mata shiga wuta. Sannan ya kara musu da muhimmancin, sallah ga mace, sannan biyayya ga mijinta.  Da yawaita sadaka. Da yawansu sai da suka zubar da hawaye.

Hubby samun kanta tayi, da tambaya. "Shin koda auren dole akawa mace, in batayi biyayya wa mijin ba, zata shiga wuta."

" so sai ma, muddin an daura mata aure da mutun, dole ne, ta masa biyayya koda bata sonsa. In ba haka ba tabbas azabar Allah zata tabbata a gareta." Takai tacciyar amsar da malan ya bata kenan.

Jikin hubby yayi sanyi, tsoro da fargaba duk sun cika zuciyarta. " mafita kawai take tunanowa kanta. Don bazata yadda haka kurun ta jawa kanta shiga wuta ba, gara in ma rabuwa ce, to su rabu. Don bazata iya masa biyayya ba."

Wata daliba ce ta shigo da sallama, bayan an amsa mata, ta shaidawa muallim ana neman Habiba Munir a office din principal. Nan take muallim yaba hubby izinin zuwa amsa kira.

Gabanta na faduwa, haka ta nufi office din principal. Tana tunanin dalilin kiran.

Gabanta ne yayi mugun faduwa, ganin hayder zaune, a daya daga kujerun gaban table din principal din. izinin shigowa principal din ya bata, tare da nuna mata kujerar dake facing din hayder, alamar ta zauna.

Kanta a sunkuye, ta zauna, ba tare data yadda ta kalli hayder ba.

" gaishe da principal din tayi, cikin rawar murya."

Fuskarsa dauke da murmushi " malama Habiba, haka ake, Ashe kinyi aure shine baki gaya mana ba? Da badan mai gidan yazo da kansa ba, da bamu sani ba, Baki kyauta ba gaskiya."

Kanta a sunkuye, still muryarta na rawa " ayi hakuri. "

" ba komai malama Habiba, gashi mai gidan ya ce daga yau bazaki sake zuwa ba, da sai in ce muna binki, shinkafa kaza. Na biki da bamu ci ba."

Da sauri ta dago ta kalli hayder, ido hudu su kayi da juna, da sauri ta dauke idonta.

" naji dadin ganin maigidan naki, hakika ki gode Allah, nasan hayder tun kuruciyarsa, ni na fara koyar dashi ilmin addini, shida sauran yan uwansa. Allah yasa albarka a aurenku, ya baku zama lafiya da zuria tsarkakakkiya." Nasiha sosai ya musu, kafin ya shige gaba hubby na bayansa, har Hall din da ake waazi. Nan yasa hubby ta musu bankwana. Basu ji dadin barin hubby islamiyya ba. Don sun saba da ita, saboda son jamaarta.

Hubby naji tana gani haka, hayder ya tasota a gaba har wurin da tayi parking din motarta. Hannu ya mika mata alamar ta bashi key. Harara ta watsa masa kafin ta wurga masa. Da mamakinta ya cabe key din.

A hankali yake murza sitiyarin, cikin kwarewa, har suka iso gida, ba wanda ya tankawa dan uwansa.

Hubby takaici ne, ya cikata, data san abinda zai aikata mata kenan da ta hakura da zuwa makarantar har sai tasa Hajiya ta roka mata shi, tana matukar son makarantar, akwai koyarwa sosai, don ita dai, bazata taba iya tambayarsa ba.

Yana tsaida motar tayi cikin gida. Juya kan motar yayi ya fita.

A falonta ta tarad da Mariya da yusra, ai da sauri ta ajiye jakar suka rungume juna, suna murnar ganin juna. Tare da ihun murna. " baki da kirki ko kadan!!! Sai yanzu kika tuna dani?" Hubby ta fada suna zama a 2 sitter din falon.

Kunne yusra ta kama, tana murmushi " tuba nake, tun da muka dawo daga abuja banda lafiya, shiyasa ban zo ba. Sai satin nan na fara fita."

" ayya shine ko a waya baki fada min ba? Ai da nazo dubiya." Hubby ta fada tana murmushi

Ido yusra tadan zaro. " ina ni ina fito da Amarya a dakinta. Ko Aisha sai jiya nake gaya mata."

" to ya jikin? Duk da banji dadi ba da baki fada min ba, ko ba komai ai sannu tana da dadi."

" sorry. Ya amarci?" Yusra ta fada tana murmushi

Harara hubby ta mata, " yana wurin amaren asali."

Mariya ce tama hubby sannu da zuwa, sannan ta bar falon.

" su waye kuma amaren asali, ban da Ku?" Yusra ta fada tana dariya

" su Aisha zaki tambaya." Ta fada

Murmushi yusra tayi " har dake, kinga yadda kikayi kyau, kikayi fresh? Gaskiya amarci ya karbeki, kodai mun samu ne?"

Duka ta dada mata a cinya. Da sauri yusra tasa hannu tana sosawa, saboda yanda dukan ya shigeta. Hararar hubby ta yi " daga fadar gaskiya, sai ki tafasamin cinya?"

" wai ki dawo hankalinki ne, don na lura kamar kin kume, a ciwon nan." Hubby ta fada tana harararta

" bakya kallon madubine halan? Amma duk wanda ya ganki ai yasan kin canza. In kuma mune baa son musan sirrin ai shikenan. Shi din ai dan duma ne baya boyuwa, da kansa ma zai bayyana kansa."

Tsaki hubby ta yi, " zako Ku Dade kuna jira."

" don Allah kar ki mana bakin ciki. Ki bada hadin kai sosai nan da 8 to 9month muzo suna." Yusra ta fada tana fuskar tausayi

" Allah ya tsare ni, in ce na haihu da wa? " da kallo yusra ta tsare hubby

Har hubby ta tsargu da irin kallon da take mata. " kallon na lafiya.?" A jiyar zuciya yusra tayi, tare da kyara zamanta.

" family planning kike yi hubby? "  ido hubby ta zaro. " wane irin family planning kuma?" Ta tambayeta

" gani nayi, in ba family planning kike yi ba. Mu muna da kyautata tsammanin in sha Allah kema ki samu rabonki, ki huta gorin rashin haihuwar da ake jifanki dashi. Tunda ko dama can ance miki komai naki is normal."

Murmushi hubby ta yi " zan so hakan, amma situation din, da nake a yanzu, ba maganar haihuwa a gabana."

Kallonta yake cike da tambayoyi. Ganin kallon da take mata, yasa hubby mikewa, "muje ki canza kaya, ki tayani mu daura girki." A tare suka nufi sama, ta bata wasu kayan ta canza, sannan suka nufo kitchen.

Fried rice, pepper chicken da coslow. Suka hada. Yusra na kallon ikon Allah, yadda hubby ta zubawa kowa, har mai gadi, bataga  ta ware na maigidanba. Kasa shiru tayi, " banga kin zuba na hayder ba?" Murmushi hubby ta yi " in ya dawo zai nemi abinda zai ci." Da mamaki yusra ke kallonta.

" ta yaya zaki dafa abinci, amma ace ba kwanon mijinki? Anya hubby? "

" karki damu, kema kinsan halin hayder, shi yafi son hakan." Hubby ta fada tana daukan trey din data zuba musu nasu a ciki.

" Allah ban yadda da ke ba." Yusra ta fada tana tsareta da ido.

" shi kenan naji, mu ci abinci tukunna, sai muyi magana." Kada kai yusra tayi, ta dau trey din ruwa da drinks tabi bayan hubby.

" hubby kiji tsoron Allah, ki rike aurenki da muhimmancin. Kar kibi, soye soyen zuciya, hakika zata kaiki ta baro. Menene laifin hayder? Kamar yadda kikayi biyayya, shimafa biyayyar yayi. Amma ace yayi cefane ya ajiye miki, amma ki dafa ki kasa bashi? Har sai lokacin da ya dawo sannan zai samawa kansa abin da zai ci? Bisa dukkan alamu hakkinsa ma na aure  ba bashi kike yi ba. A haka kike tunanin Allah zai barki? Hakkinsa ma kawai ya isheki."

Ajiyar zuciya hubby tayi " bazaki gane ba wallahi, its very difficult for me."

" ehmm!!! Kin zabi kiji kunyar lahira data duniya ko? Fine." Yusra ta fada

Shiru hubby tayi tana jin jina lamarin. Gaskiya yusra ke fada, amma gaskiya abin da kamar wuya, ita da hayder? Kai ina, bazata sabuba, wai bindiga a ruwa.

" ko zaki cemin ke baki da sauran filling ne?" Yusra ta jeho mata tambayar tana tsareta da ido.

Ido hubby ta zaro, tare da yamutsa fuska. " a yanzu dai kam babu."

Murmushi yusra tayi. Cikin ido sosai ta kalli hubby. " wallahi karya kike, ba yadda za'a yi ki ce baki filling, muma da bamu taba auren ba, ya muka kare, balle Ku da kuka san dadin abun. Ko matan da kike ganin suke kin kara aure, don mazansu sun rasu, ko sun rabu, zaki samu 80%  sun manyanta. Amma mace da kuruciyarta da komai, ta ce bata filling? Wannan tatsuniya ce kawai.  Ki daina cutar dan uwanmu ki barshi ya mori kuruciyarsa. Haka kurun, ga mata komai yaji, amma zaki hana ruwa gudu."

" sai kiyi kuma ai." Hubby ta fada

" Allah ya shiryeki, tunda na lura kin zama mai kunnen kashi, baa isa a gaya miki gaskiya ba." Yusra ta fada cikin bacin rai, tashi tayi ta yafa mayafinta, tare da daukar hand bag, " ni na wuce, sai wani jikon."

Agogo hubby ta kalla, 5:23pm " tun yanzu? Ki bari dan can anjima sai ki yafi, please. "

" nop!!!! Akwai inda zan biya, kafin in koma gida. Nama manta ban gaya miki ba, an sa bikina, in 1 month time. "

Tsalle hubby ta fara, tana murna, tare da rungume yusra. " congratulation, I'm so happy for u. Woww!!! What a greet news."

" thanks. " yusra ta fada tana murmushi.

" aminu ko halil?" Hubby ta tambayeta cike da murna.

" halil."

" what a nice choice, kun dace, sosai wallahi. Allah ya kaimu lokacin." Hubby ta fada.

Har mota ta rakota, sujayi sallama cike da kewar juna, Ta tafi.

           **********************

Tana kwance a 3sitter dake falonta na sama. Jira take 9 ya cika taje ta kwanta, kafin hayder ya shigo. Don yanzu ta riga ta karanci lokacin dawowarsa. Rabin hankalinta na kan series din da ake nunawa, a tashar starlife, Rabi ya tafi ga tunanin waazin da aka musu dazu a islamiyya da kuma magan ganunta da yusra.

Kamshin turaren da taji ya bugi hancinta, yasata dago da idonta, da sauri, ta kalli kofar falon..........
Gabanta ne ya fadi, kokarin tashi zaune ta fara, tunowa da kayan dake jikinta, yasa ta koma ta kwanta. Sanye take da aimless gown red. Roba ce, tabi jikinta sosai, kanta ko dan kwali babu, illah kama gashin da tayi donut dashi.

A hankali ya karaso cikin falon, hannunsa daya dauke da mog, dayan kuma wani kwali ne, karami. Sanye yake da jallabiyya fara Sol, mai gajeren hannu. Zama yayi a kujerar da take facing nata, Ya daura kwalin kan center table.

She is uncomfortable, mu samman da taji, an dau lokaci bai ce mata komai ba. Kasa hakuri tayi, duk da yadda zuciyarta ke faman biting. " what bring u hare?" Ta fada idonta na kan TV.

Kafarsa daya kan daya, yana sipping Green tea, da yasha kayan kamshi, hankali kwance. Ganin bashi da niyyar tanka mata, yasa ta daga kai ta kalleshi, ido hudu sukayi. " am talking to u, wai me yasa ka gama raina nine." Ta fada a lamar ranta ya fara baci.

Murmushin gefen baki yayi, sai da ya kara sipping Green tea dinsa, sannan ya kalleta, idonta a kan TV. " tunda kika tako gidan nan, a matsayin matar Aliyu hayder ai raini ya kare."

Ido ta zuba masa, cike da mamakin maganarsa, shi din ma ita yake kallo.

Murmushi tayi. " kai a tunaninka hubby ta shigo gidan nan don zaman aure? Uhimmm!!! Lallai kam, bude kunnenka da kyau kaji.  u are a big dreamer. I came to your house as your big sister, babu dadi babu kari. Har zuwa time din da zaka samu abokiyar zama, u are free to married your choice."

Murmushi yayi har tana jin sautin mirmushin nasa. " I don't understand u"

Harara ta watsa masa " bafa da Hausa, ko wani yare nake maganar ba,? Ina nufin dani dakai kowa yayi harkarsa, don't inter fare in my matters, nima I'm not inter fare in yours. That all."

" yanzu na gane. Lokacin da zan wani auren, ke kuma inyi ya dake?" Ya fada still idonsa a kanta.

" ina nan a matsayin sister dinka, mana." Ta fada

Gira ya daga yana tabe fuska, " what about our parents?"

" ba zasu sani ba, we just pretend."

Tabe baki yayi, yana jijjiga kai, a hankali. " hakkokin igiya ukun dake kanmu fa? In mun boyewa iyayenmu, zamu iya boyewa Allah ne?"

Ganin alamar nasara yasa hubby mikewa ta zauna da kyau. Gaba daya tama manta da kayan dake jikinta. Burinta kawai ya amince da bukatarta.

" innalillahi wa inna ilaihir rajiun." Hayder ke maimai tawa a zuciyarsa. Wani shock yaji, lokaci daya, da wani abu dake bin duk wani bargo da gaba na jikinsa. Lokaci daya hankalinsa ya tashi. Ba wani lafiyayyen namijin da zaiga hubby a lokacin hankalinsa bai kai kololiwar tashi ba. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da dauke idonsa a kanta.

Hubby Sam bata lura da kallon da yake binta da shiba. " wannan ai abu mai sauki ne,! Na yafe duk wani hakkina dake kanka, kaima sai ka yafe hakkinka dake kaina, kaga shi kenan an zauna lafiya.?"

Kallonta ya kara yi, murya a shake, da kyar ya iya fisgo haruffan bakinsa. " kinyi tunani me kyau. Ashe zero Head din, wani lokaci yana ja."

Da mamaki take kallonsa, gani tayi ya canza mata lokaci daya, amma bata kawo komai ba. Illa haushin zero head din daya fada. " amma kasan ban son rashin kunya ko?" Idon da suka canza kala ya zuba mata. For some time, ya kauda kansa. " lokacin baccinki yayi." Harara ta watsa masa " na fika sani ai. Ba mu gama magana ba. Ka yafe din ko yaya.?

" in ban yafe ba, yazakiyi da ni.?" Ya fada idonsa can tv, kamar mai kallo, nan ko shi kadai yasan halin da ya ke ciki.

" you have your girlfriend right? U love her. Me and u a not in the same page,  We never love each other. So what is the big deal? " ta fada cikin kosawa

" let me think about it. Zamuyi magana gobe, zan gaya miki abinda na yanke."

Ba haka taso ba, amma ba yadda ta iya, dole ta bashi lokaci, she hope he accept her idea.

Mika mata kwalin da ya zo dashi yayi, " from Ummul khair. Nasan zata miki anfani sosai." Ya fada tare da gyara zamansa.

Amsa tayi tana jujjuya kwalin. Gaba daya ta manta da Ummul khair ta ce mata, taba junaid sako ya bata, tun ranar da aka kai Kowacce gidan mijinta. Ta manta shaf da maganar sakon, bata tambayi junaid ba, da taga shiru bai kawo mata ba. Sai yanzu ta tuna.

Mikewa tayi zata tashi, da sauri ta koma ta zauna, tare da rungume hannayenta duka biyu a kirjinta. Zuciyarta na faman dakan tara tara. " innalillahi. " ta fada a ranta. Kunya da jin takaicin kanta ya kamata. Idonta takai kan hayder TV yake kallo kamar bai san abinda takewa ba. Ganin hankalinsa na kan TV, yasa ta kwasa da gudu zuwa bedroom dinta.

Da jikin kofar ta jingina, tana sauke ajiyar zuciya. A hankali ta isa gaban madubi. " la haula wala kuwwata illa billah." Ta fada ganin yadda kirjinta ya fito sosai a cikin rigar, hatta nippule dinta kana iya hango shatinsu. A tsaye suke char, kamar sa tsole maka ido. Su ba manya ba ba kuma kanana ba, Masha Allah.  Kunya da takaici ne suka cikata. Tabbas hayder ya gama ganeta tsaf, tana can tana shirmenta. No wonder taji muryarsa ta canza, lokaci  daya.
" Allah ya isana." Ta fada tana shigewa toilet.

Wani wawan ajiyar zuciya hayder ya sauke. Da ido ya bita, har ta shige bedroom dinta. Sannan ya dauke idonsa, tare da kara kashingida a jikin kujerar, don baya jin yana da sauran kuzarin da kafafuwansa zasu dauki gangar jikinsa zuwa bedroom dinsa.

Kanshi ya dafe da hannu daya. Yasha ganinta ba hijab, amma bai taba tsayawa ya kare mata kalloba. No wonder, shi abun na daure masa kai yadda samarinta ke nunawa a kanta. Abin har haushi yake bashi, yaga me tafi sauran mata da suke nuna hauka a kanta haka? Tunawa yayi, da week din aurensu yadda suraj kangiwa ya zo ya sameshi, lokacin yana masallaci yana daukar karatu. Rokonsa ya fara, harda ko nawa yake so, zai bashi ya saki hubby. Murmushi yayi a lokacin " bazan iya abinda kake son inyi ba.?"

Tsugunnawa yayi, yana rokonsa " nasan baka son Habiba, kamar yadda na kwana da sanin bata sonka. Don haka ina rokonka ka saketa. Daga million daya, zuwa billion zan baka in har zaka mun wannan alfarmar."

Tsugunnawa hayder yayi shima. " kayi hakuri, tabbas bana sonta, iyaye suka hada mu, bani kuma  da ikon rabuwa da ita. Baka da kudin da zaka bani don in saketa, I have my on business, my on earning. Kudinka bazai sani in sabi mahaliccina ba. In saketa don ka aura, haramun ne, don haka bazan yi don in faranta maka ba. Shawarata a gareka shine ka rungumi kaddara, kamar yadda muka runguma da hannu biyu."

Tashi yayi, ya barshi a wurin, yana mai jin tsananin tausayinsa.

Tunowa yayi da Abdul Karim, yaya Ahmad, duk da shi bai bayyana nashi soyayyarba, amma ya kwana da sanin dan uwansa na son hubby. Salis da Engr Sahabi. Tabbas yaso hubby ta auri salis, don duk inda kamilin mutun yakai salis ya kai. Yana mutuntashi, da ganin girmansa matuka. Kamar yadda ya kwana da sanin matsayinsa a wurin Yusuf.

Ajiyar zuciya ya sauke, tunowa da irin son da Yusuf yake mata. Magan ganunsa suka fara dawo masa one after the oder. Musamman haduwarsu ta karshe, bazai taba manta wannan lokacin ba. Kamar yadda abubuwan da suka faru a lokacin ba zasu taba gogewa a ransa ba. Mutun baya taba gujewa kaddararsa tabbas haka abin yake.

Tunanin maganganunta na yanzu suka fara dawo masa, Murmushi yayi yana shafa sajensa a hankali. Duk da baya sonta, shi ba jahili bane, yasan tanada hakki a kansa, daga lokacin da aka daura aurensu, kamar yadda yake da hakki a kanta. Dama ya daga mata kafa ne yaga iya gudun ruwanta. Yanzu ne zaa fara wasan. Don ba zai taba yafe hakkinsa ba. Ama tsayinsa na lafiyayyen namiji, wanda yake ganiyarsa. Ba zai iya hakuri ya zuba mata ido ba. Ganinta a yanzu ya kara masa son kasan cewa da ita.

Mikewa yayi, ya kashe komai, ya nufi bedroom dinsa, wanka yayi, tare da shirin bacci. Gaba daya daren baccin hayder kadan ne. Daya rufe idonsa surar hubby ke yawo a danuwansa. Dole ya tashi ya fara nafila.

               ******************
Sai da tayi shirin kwanciya, sannan ta dauko kwalin ta bude. Dariya tayi ta daga bulalar tana kallo. " ya Allah ka shiryi Ummul khair. " ta fada tana Ciro karamar takardar dake ciki.

" special gift to my beloved sister. Karki raga masa ko kadan, naji su Anty ummu khulsum na cewa ki bishi a hankali.  In ya miki ba dai dai ba, Zaneshi zakiyi sosai, jikinsa ya gaya masa, ba daga kafa, in ba haka ba rainaki zai yi."

Dariya hubby tayi tunowa da ranar da hayder ya aunata da bike dinsa. Watan Ummul khair bata manta maganar bulala ba. " yar banzan yarinya, zamu hadu ne." Maida bulalar tayi ta ajiye. Maganar hayder ce ta fado mata. " nasan zata miki anfani sosai. " me yake nifi? Haka taita kokarin hasaso abinda maganar ke nufi ta kasa, don haka, ta tattara ta watsa tunanin a kwandon shara.

              *******************

Da safe basu hadu ba, kamar yadda suka saba tashi, kusan a tare. Don hayder baccin da bai samu da daddare ba, yake ramawa. Hubby kam abun ya mata dadi, don bata shirya fuskantarsa ba. Har yanzu yana jin kunyar yanda ya ganta.

Sai bayan sallar la'asar ya sameta a falon ta na kasa, ita da Mariya. Shigowarsa Mariya ta fita, bayan ta gaishe shi. Yanzu kam ta San shine mai gidan, saboda yawan ganinsa da takeyi. Sannan tasan duk baki mazan da sukeyi iyakarsu falon gasa, amma shi sau da yawa tana ganinshi ya sauko, ko zai hau.

Zama yayi, tare da mikar da kafarsa daya kan center table din gabansa.

Sun kai 15min ba wanda ya tankawa dayansa. Kunya da haushinsa ne suka hana hubby magana.

Cikin muryarsa mai kama da anmasa dole, don sanyi, da yadda yake fitar da haruffan bakinsa. " I accept, amma ina son muyi a rubuce, kar daga baya ki canza magana."

Murmushi tayi, nan da nan farin ciki ya cika ranta. Mikewa tayi da sauri ta nufi of stairs, minti kadan sai gata da pepper da pen, Mika masa tayi. Kallon pepper din yayi, ya kalleta. " ke kika bukata, don haka ke zaki rubuta."

" OK. Me kake son in rubuta?" Ta tambaya tana kallonsa

Tabe baki yayi, yana shafa sagensa, alamar ya zama masa jiki, yin hakan.

" fist ki fara jero hakkin mata a kan mijinta, then hakkin miji kan matarsa. U write kin yafe duk kan hakkokinki dake kaina. Then sai kiyi sign. I will write my on, sai kowa yayi sign. Sai muyi photocopy kowa da nashi. Then shi kenan."

Zama tayi, ta fara jero su, kamar yadda ya bukata. Duk da wasun ta kanji nauyi da kunyar rubutawar.

Hakkin mata a kan mijimatarsa::;-

1. Ya biya ta Sadakinta na Aure.
2. Ya kula da Addininta.
3. Ya daukin nauyin cinta, shanta, suturarta, har da kayan kwalliya nata.
4. Ya ba ta hakkinta na aure.
5. Ya dauki nauyin kulawa da lafiyarta.
6. Ya daukin nauyin karatunta musamman ma na Addini.
7. Ya nuna mata soyayya a fili.
8. Ya rika mu’amala da ita a cikin sauki kamar karamar yarinya.
9. Idan ya shigo gida ya rika sakar mata fuska da fara’a.
10. Ya rika yaba mata idan ta yi abin kirki tare da yi mata Addu’a ta fatan Alkhairi.
11. Ya rika sauraron korafe-korafenta da shawarawarinta.
12. Ya rika yafe mata idan ta yi masa ba dai-dai ba, kuma yana gyara mata cikin hikima.
13. Ya rika yin kwalliya da ado domin ta gani ta ji dadi.
14. Ya ba ta lokaci na musamman a lokutansa domin yin hira da ita kawai.
15. Ya rika cin abinci tare da ita.
16. Ya ringa taimaka mata wajen aiyukan gida musamman idan ta samu rauni na laulayin ciki ko na rashin lafiya tare da tausaya mata.
17. Ya rika nuna damuwa cikin abin da ta damu da shi, da farin a cikin abin da take farin ciki da shi matukar bai saka wa Allah ba.
18. Ya girmama iyayenta da ‘yan uwanta.
19. Ya ringa yi mata kyuata ta musamman domin faranta mata rai.
20. Ya rika fita da ita wurare na musamman kamar ziyara ko wurin karatu ko wurin shakatawa.
21. Ya rika b oye aibinta.

Hakkin miji a kan matarsa::;-

1 – Soyayya ta gaskiya.
2 – Tsare Amana Miji.
3 – Tausasawa miji da wasa da dariya da shi.
4 – Tsare sirrin miji.
5 – Ba za ta fita daga gidansa sai da izininsa.
6- Ba za ta yi azumin nafila ba sai da izininsa.
7 – Ta yarda ya sadu da ita duk lokacin da yake bukata, dan Annabi Mai tsira aminci yace duk matar da taki mijinta ya sadu da ita a duk lokacin da yake so, toh Mala’iku zasu ta la’antar taba zasu su daina ba har sai lokacinda ta yarda da shi. (BUKHARI/MUSLIM).
8 – Ta saurari mijinta kuma tayimasa biyayya matukar ba aikin laifiya umurceta dayi ba.
9 – Mace ta nisanci raina abin da mijinta ya bata, domin Annabi Muhammad mai tsira aminci ya ce “Mata zasu shiga wuta ne saboda kafurce wa mazajensu, wato raina alherin miji” (BUKHARI/MUSLIM)
10 – Ka da mace ta cutar da mijinta da magana ko da aiki.
11 – Mace tayi ado da kwalliya wa mijinta, saboda Annabi mai tsira da aminci yace “Allah kyakkyawa ne, kuma yana son kyakkyawan abubuwa, (IMAM MUSLIM YA RUWAITO).
12 – Mace ta tsare dukiyar mijinta da na ‘ya’yansa harma da na gidansa, dan Annabi mai tsira da aminci ya ce “Mace mai kiwo ce a gidanta, za’a tambayeta abin da ta kiwata.
13 – Mace tayi gaggawan baiwa mijinta hakuri a duk lokacin data ga yayi fushi, Tace masa, dan Allah kayi hakuri, ban san abin da na yi zai ba ta ma ka rai ba, ka yafe mi ni dan girman Allah.
14 -Mace ta yiwa mijinta dukkan irin aikin da ake bukata ayishi a gida.
15 – Mace ta kyautata halayenta ga iyalan mijinta.
16 – Mace ka da ta yi abokantaka da mugayen kawaye, sai su hallakar da ke baki sani ba.
17 – Mace ta zama mai tausayawa mijinta, kamar yadda uwa take tausayin ‘Danta.
18 – Mace ta zama mai Biyayya ga mijinta.
19 – Mace ta zama Abokiyar rayuwa ga mijinta.
20 – Mace ta kusanci dukkan abinda mijinta ya ke so.
21- Mace ta nisanci dukkan abin da mijinta ya ke ki.
22 – Ki yi murmushi a duk san da mijinki ya kalle ki.
23 – Ki yi masa addu’a a duk lokacin da zai fita, ki ce a dawo lafiya Allah ya bada sa’a.
24 – Ki yi masa addu’a kuma a duk lokacin da bakya ganinsa bayan bayanan.
25 – Idan mijinki ya dawo ki karbi abin hannunsa, tare da yi masa sannu da zuwa, dan girmama shi.
26 – A duk samda zakiyi magana da mijinki ki gaya masa magana mai dadi, mai tabshi, kada ki daga muryanki a kan nasa, kuma kada ki masa tsawa har ki harare shi.
27- Ki zama cikin tsabta da kamshi mai dadi duk lokacin da kuke tare.
28 – Ki sanya hijabi a duk lokacin da kuke tare da wadanda ba muharramanki ba.
29 – Ki sa lokaci idon ki, ki kuma shafa jan baki, kuma ki shafa turare, amma sai kuna tare dashi a gida dan mace bata shafa turare ko jan-baki ta fita anguwa dashi.
30 – Ki kaskantar da kai dan biyayyaa gare shi.
31- Ki san lokacin da yake dawowa dan kada ya sameki a cikin kazanta, ki kuma san lokacin cin abincin sa dan ki tanada ba sai ya zo yana nema ba.
32 – Bayan kin gama masa komi ki tambaye shi ko yana da wata bukata a gareki, dan mi biya masa ita.
33 – Kar ki nuna murnan ki idan wata hasara ta same shi, ki nuna masa kamar kece kika yi hasarsar.
34 – hakanan kiyi murna da duk wani alherin daya samu.
35 – Ki zama kamar matan sahabbai, yadda sukewamazajensu. Idan miji zai fita sai su ce a dawo lafiya, kar ka kawo ma na haram zamu iya hakuri dayunwar duniya, amma baza mu iyahakuri da azaba ba gobe lahira.

Kallonta yake yadda ta Dage sai zuba rubutu take. Murmushin gefen baki yayi yana kada kai.  Mika masa tayi.
" I'm don."  Ta fada tana murmushi

Amsa yayi, yana bin abunda ta rubuta daki daki. Murmushi yayi. " Ashe ba zaman cika benci kike a makarantar ba?" Ya fada still idonsa a kan pepper din.

Harararsa tayi, " just sign, ban tanbayeka dogon turanci ba. Koma mai zaka ce, ka dade baka fada ba."

Kansa ya dago yana kallonta, mika mata hannu yayi, pen din ta sa masa a hannun. Tana watsa masa harara. Don taji haushin maganar daya fada. Badon tana son su rabu lafiya ba, da sun kwashi yan kallo.

Ya daura pen din kenan zaiyi sign sukaji nocking, gaba daya suka kai kallonsu ga kofar shigowa.......

 
[07/03, 17:27] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 19 · 0% Book details