← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 21 OF 28

                            Part 19

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 19 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau
   
Not Edited.......
Da gudu ta banko kofar, har tana bangajeshi. Baki bude yake kallonta, gaba daya ta fada jikinsa, ta gankameshi, jikinta na matsanancin kyarma. Kyakyawar runguma ya mata, yana buga bayanta a hankali. Kanta ta gara cusawa a kirjinsa. Tana Jan numfashi da kyar.  kaman zata shide haka numfashinta ke fisga da kyar.

Sun dade rungume da juna. Jin yadda take sauke numfashi, tare da ajiyar zuciya, jikinta ya rage rawa sosai. Yasa ya dago fuskarta idonta kam a rufe, gani take in ta bude magen zata kara gani. Iskar bakinsa yadan hura mata a fuska " its OK. Open your eyes. " ya fada in husky voice yana ci gaba da hura mata iskar bakinsa.

Kara runtse idonta tayi, tanajin iskar bakinsa mai kamshin strawberry na sauka a kan fuskarta. Gaba daya tsigar jikinta ya fara tashi. A hankali ya zareta daga jikinsa, resting chair din ta kara komawa, ta dungule wuri daya.

Jin alamar taba kofar yasata saurin dago kanta. Hayder ne yasa key, fridge ya nufa, ya zuba ruwa mai sanyi a glass cup ya tako inda hubby ke dungule ya mika mata. Jin mutun a kanta yasata dagowa, ganin yana mika mata cup din. Ta mike ta zauna da kyau tare da amsar cup din, don tanada bukatar ruwan ko don kuka, da tayi. Tsaf ta shanye sannan ta mika masa cup din.

Kwanciya ta kara yi, tare da runtse idonta. Daga nan tana jiyo yanda magen ke yakushin Kofa, kush- khush- kush, tare da kukanta. Ajiyar zuciya ta sauke. Hankalinta ya fara dawowa jikinta, don tasan koma menene ba ita kadai ba ce a dakin. Yana tsaye daga jikin window idonsa na hango malan idi dake baje a kofar dakinsa, yayi shinfida yana kwasar bacci. Tsaki yayi a zuciyarsa yana furta " ji wai nan a dole me gadi? Mai gadi da aka Sani da sintiri cikin dare don ya tabbatar da tsaro, amma shi ke kwasar bacci hankalinsa kwance."

Kallonsa yakai kan hubby, yasan harda  sanyin ac yasata dungulewa haka. Takowa yayi, zuwa inda take kwance " Habiba!! " ya kira in sweet low voice. Kanta ta dago ta kalleshi, hannunsa ya mika mata. Kallon hannun tayi, mai matukar haske da laushi, dogayen yatsunsa kwanin shaawa. Kallonsa tayi, alama ya mata da ido. Kanta ta dauke tare da mikewa ta zauna.

Ganin bata da alamar kama hannun nasa, da kansa ya kamo nata hannun, tsigar jikintane ya yi wani yar!!! Tare da shock daya ratsa jikinta lokaci daya.

Lumshe idonsa yayi, saboda shock din daya ratsa jikinsa. Bata da zabin da yafi ta mike, kamar rakumi da akala haka ya ke rike janye da ita. A tunaninta wajen zai kara turata, amma sai taga sabanin haka.

Toilet ya nufa da ita, suna shiga wani kamshi mai sanyaya rai ya daki hancin hubby. ya kalleta yana shigar da idonsa in sexy way. " kiyi alwala, I'm waiting for u outside. "

Kallonsa take ido waje, don yanzu ta fara tsinkewa da lamarin Hayder, gaba daya gani take kamar ba shi ba. Ba karamin aikinsa bane ya kulleta a toilet din. Yana juyawa, da sauri ta riko hannunsa. " wait please. " baki ya Dan tabe, ya jingina da kofar.

Cikin Sauri- sauri tayi alwalar. Kallonsa tayi, matsawa yayi daga jikin kofar, da sauri ta wuce zuwa cikin dakin. Hakan ya bashi damar yin nashi alwalar.

Woodruff dinsa ya bude, wani alkabbarsa  mai hade da hula, ya dauko. Carpet din sallah mai matukar kyau da laushi, ya shimfida. Sannan ya mika mata rigar, Kallonsa tayi, cike da fargaba da tsoro. " nayi sallah." Ta fada muryarta na rawa.  Murmushi yayi, yana ajiye mata rigar a saman cinyarta. " I known. This one is special." Ya fada in sexy voice dinsa, yana murmushin gefen baki.

Gabanta ne ya fadi, da sauri ta dago tana kallonsa. " don't forget our agreement? " ta fada, muryarta na cracking

Murmushi yayi, har tana jin sautin numfashinsa. " kin San na ce miki no a guying, ko I will trow u out, just do as I say." Ya fada yana tsareta da idonsa.

Idonta ne suka ciko da kwalla, mikewa tayi a hankali ta saka rigar, kamar mai sharan kasa, yadda ta mata tsawo, da fadi baki daya. Su Kansu hannayen sun mata yawa sosai. Kallonta yayi, tare da Jan hannunta, har kan daddumar, She have no choice.

2 rakaat sukayi, ya musu addua sosai, tare da dafa kanta ya karanto adduar da manzo  S.A.W ya umurci ko wanne ango, da gabatarwa kafin yaje ga iyalinsa.

Allhumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha ala'ih, wa'auzu bika min sharraha wa sharra ma jabaltaha ala'ih.

Kwanciya tayi kan carpet din, zuciyarta da jikinta rawa kawai suke, don ta tabbatar yau Allah ne kawai zai kwaceta a hannun hayder. Tun jiya take tsoron randa zai rutsata don ta lura abun nasa ba sauki.

Dagata yayi, tare da rungumota jikinsa, yana Ajiyar zuciya. Dagata yayi cak zuwa saman bed dinsa. Kokarin cire alkabbarsa yakeyi, ta cukui kuyeta, tare da nade kanta a ciki.

" Habiba don't make it had for us." Ya fada yana rage kayan jikinsa. 

Hawayene wani na bin wani, maganar ummu sulaim ne suketa kara kaina a ranta " kamar yadda Allah ya kaddara Yaya Yusuf ya sanki matsayin matarsa, haka ya kaddara hayder shima ya sanki a matsayin matarsa, so take heart and deal with it. Duk yadda kika kai ga gujewa hakan it won't work."

Ko kafin ta tuno amsar data bata a lokacin,. Sai jin  hayder tayi, yana kokarin zare rigar a jikinta. Karfinta tasa tana kokarin hanashi, amma ina hakan bai samu ba. Karfi ba daya ba. Yana zare alkabbar tana dira kasa daga gadon.

Kofa ta nufa, burki taja, ta tsaya. Zuciyarta na bugawa. Tare da wasi wasin, ta fita su kara da mage?ko ta tsaya hayder yayi yadda zai yi da ita. Don tasan bazai taba barinta ba. Kanta ta kifa a jikin kofar ta fashe da kuka mai cin rai. " how can she help her self know? "

Bataji takowarsa ba, sai jinsa tayi ya rungumota ta baya, yana sauke Ajiyar zuciya. Ta bashi tausayi sosai, amma gaskiya baya jin zai iya hakura da ita, don wani filling yake ji, Wanda bai taba experiencing ba, a rayuwarsa. Ji yake in har bai rabeta ba, tabbas zai shiga matsala. Ta wani fannin kuma, zai sauke hakkinta dake kansa, duk da bata da bukatar hakan.

Wuyanta ya fara kissing, a hankali, shivering ta fara, tare da kokarin zame kanta. Juyo da ita yayi ya hadata da kofar. Yana ci gaba da kissing wuyanta, zuwa ear loop dinta
Gaba dayansu jikinsu yadau kerma lokaci daya. Kanta ya dago, yana kallon kyakyawar fuskarta, data jike da hawaye. Idonta a rufe, don batajin zata iya kallonsa. Bakinsa yakai kan nata, like last time she denied him access to har mouth. Labbanta ya ke tsotsa a hankali, hannun daya na tallabe da fuskarta, dayan na zaga duk kan sassan jikinta. Jikinsa ya mata katanga a jikin door din.

Tun tana kokarin avoiding, har gaba daya jikinta, ya fara amsar sakon ninsa. Dagata yayi bridal style zuwa bed din, tare da sweching  light. Wasanni masu zafi ya fara aika mata, Wanda ta kasa control din kanta, ta fara maida masa.

Gaba daya daren hayder ya hana hubby sakat, Tun tana dauriya, har ta gaza, ta fara masa kuka.

Yana kwance hubby na rungume a jikinsa, Yana jin saukar hawayenta. Shi kanshi hawayen yake zubarwa for 2 think. Fist tunowa da Dan uwansa, second godiya ga Allah bisa niimar bashi hubby a matsayin mata. Yau ya kara tabbatar da maganar Yaya Yusuf, Yau ya kara tabbatar da dalilin da yasa Yusuf ke matukar kaunarta, Yanzu ya gane abunda sauran masoyanta ke hangowa a tare da ita. Bai taba tarayya da ko wacce irin mace ba, a rayuwarsa. Amma yasan she is special, unique and different from others.

Hubby tunanin Yusuf ne, dankare a ranta, gani take tamkar taci amanarsa ne, tare da takaicin kanta, yadda ta kasa control din kanta, da har hayder ya samu dama a kanta, So ita yanzu da wane ido zata kalli hayder? Hayder kanin bayanta? He is know controlling her. She is know his real wife. Ya zatayi da wannan katuwar kaddarar? 

Alarm dinsa ne ya kada 4am, Yana son tashi, amma baya son disturbing nata,. Kanta ya ke shafawa a hankali. Tare da tuno maganar Yaya Yusuf mai kama da wasiyyah, last ziyara daya kai masa Cyprus.

              ********************

Zaune yake a harabar apartment dinsu. Wurine mai yalwar hasken fitilu, da furanni masu kamshi, Wanda su suka zuba kujeru don hutawa da daddare, in sun dawo. Idonsa a sama yana kallon taurari, tare da girmama, girman halittar Allah, da tasbihi a kasan zuciyarsa.

Baiji takowarsa ba, sai dafashi da yaji anyi, da sauri ya juya, don a tunaninsa junaid ne, ko ashir, amma ga mamakinsa yaga Yusuf. Murmushi sukawa juna, Yusuf ya zagayo, ya zauna a kujerar dake fuskantar hayder.

" na dauka ka dade da bacci, saboda gajiya." Hayder ya fada yana murmushi

Shima murmushi yayi " baccin yaki zuwa. Me kakeyi kai daya a nan" Yusuf ya tambaya.

" muraja'a and looking at star's. " ya fada a takaice.

Murmushi Yusuf yayi, yakai lallonsa sama, yadda stars din suka fito sosai, ga wata da alamar ya kusa 10 to 11 days. " tabbas kallonsu kansa mutun ya kara tsoron Allah da sanin girmansa."

Hayder ne ya amsa da " sosai brother" ya fada a takaice

" you no what, duniya bata da tabbas,  dole mutun sai yanayi yana garanbawul din imaninsa." Yusuf ya fada still idonsa na kallon sama

" ga mai imani ya dauketa, bata da tabbas, ga Wanda ta aura gani yake matabbatace da zai aikata abinda yaso,"

Murmushi Yusuf " shin duka duka, farin cikin guda nawa ne? Me ye kesa bawa farin ciki a duniya, da har zai salwantar da lahirarsa a kanta?.......

Murmushi hayder yayi. "  dukiya!!!Mufi yawan mutane suna halaka ne don son duniya da kuma son hutu da jin dadi a duniya.
Shuwagabannin masu rayuwa cikin hutu da jin dadi suke jawa alummarsu halaka don irin fasadin da suke aikatawa a bayan kasa.da yawan mutane na ganin jin dadin duniya shine ka samu kudi. Sun manta da ko kanada kudin, sai Allah yaso kaji dadi dasu. Sannan dukiya kan zama fitina ga maabocinta, don dayawan mutane ita ke halakar dasu, kota wurin nemanta, ko kuma ta wurin gudanar da ita. Dukiya kan kawo shagala da lamuran duniya, ga Wanda ba Allah a zuciyarsa. Mutun zai iya yin komai, don kawai ya tara abin duniya, I mean everything kisan kai, cinamana, zalunci, yaudara duk don yaji dadi a duniya. Kasan abinda yafi daure min kai?" Kallonsa Yusuf yayi, tare da kada kansa.

Ajiyar zuciya harder yayi, " ka gama tara dukiyar, amma baka tanadi lokaci, da kwanakin da zaka zauna ka moreta ba."

Murmushi Yusuf yayi. " rigima ke nan.  Duniya ke nan, yanzu kananan lokaci kadan ka gushe. Shin wane ayyukane na lada da bayan mutun ya gushe zai kawo masa lada?"

Still idon hayder a sama, murmushi yayi. " bayan mutun ya mutu, ayyukansa sun yanke, abunda zai ci gaba da wanzuwa na lada kona kankare zunubi ga bawa, shine da na gari, dazai ci gaba da yi masa addua. Sai sadakatul jariyyah. Kamar gina masallatai, Gina rijiyoyi, tallafawa marayu. Da sauran ayyuka masu gudana."

Ajiyar zuciya Yusuf yayi, tare da gyara zamansa. " ga mutumin da kejin kamar rayuwarsa baza tayi tsayi ba, kuma bai mallaki Dan da zai masa addua ba? Mai zai yi, bayan sadakatul jariyyah.?"

Kallonsa hayder yayi, cike da alamomin tambaya, saboda yanayin da Yusuf yayi tambayar.

Hannun Yusuf ya kamo cikin nashi "1. Ayyukan mutum anan duniya suna tare da shi a duniya da lahira. Makomarsa na tattare da ayyukans a nan duniya.
2. Duk abin da mutum ya fada ko ya aikata anan rayuwa za'a rubuta shi a nuna masashi ranar kiyama kamar yadda ya fada ko ya aikata su.
3. Kotun ranar kiyama kotu ne wanda ayyukan mutum basa boyewa. Hatta da kansa zai iya yiwa kansa hisabi don kasancewar ayyukansa a fili suke. Baya bukatar wani shaida wanda zai tabbatar da ayyukan da ya yi.
4. Bautar Allah shi ne abinda ake gabatarwa kafin a sami kaiwa ga kusanci ga Allah da kuma sanin girmansa. 5. Dare shi lokaci mafi muhimmanci wajen samun kusanci ga Allah. 3. Massalaci shi mahallin da aka fi samun kusanci da Allah. Kuma sallah ce mafi girma daga cikin abidu. Don haka ne ma ake kiranta mirajin mumini. Rashin da baya rage komai ga bawa, sau da yawa ma yakan zama alkhairi ga bawa."

Hannunsa Yusuf ya kara kankamewa tare da dan bubbuga hannun da daya hannunsa, Kallonsa hayder keyi, yana nazarinsa. " tun da kazo na lura da canji sosai a tattare da kai, don Allah ahee!! Meke faruwa.?"

Murmushi Yusuf yayi, tare da Jan numfashi. " yanayin rayuwane kawai. I wish ni kaina nasan abunda ke damuna, I want to ask u a fervour. "

" ask everything u want, in sha Allah zan maka." Hayder ya fada still idonsa a kan Yusuf

Murmushi Yusuf yayi " na gode sosai da soyayyarka gareni, duk a yan'uwana kai ka zama mafi soyuwa a gareni. Ina sonka saboda Allah, fiye da yadda nake son kaina. Ina rokonka ko bayan bana raye ka kasance mai yawan yi min addua, Don kai kadai nake ganin kani kuma da a gareni."

Idon hayder ne suka cicciko da kwalla, saboda yanayin da Yusuf yayi maganar, cike da rauni. Rungumeshi hayder yayi gaba dayansu hawaye suke fitarwa a idonsu. Sun kai lokaci mai tsawo rungume da juna, kafin suka saki juna. " na maka alkawari, matukar ina numfashi, in sha Allah zan kasance mai yawan maka addua. Kamar yadda ban taba ma kaina addua ba tare da na sakaka da sauran yan uwanmu ba."

Murmushi Yusuf yayi still yana rike da hannun hayder. " na gode, hakika kai dan uwane na gari, ina alfahari da kai. A another fervour!!! Ina son ka kulamin da Habiba. Don bayan son Allah da manzonsa, da baa hadashi da komai. Iyayena da kai, sai kuwa Habiba. Habiba tamkar wani bangarene na jikina, bana son rashina yasata shiga wani hali, zan so ka maye mata gurbina, don nayi imanin zaka kulamin da ita, fiye da yadda zan kula da ita."

Kallonsa hayder keyi idonsa na zubar da hawaye, wnnan wasu irin kalamai ne ahehh dinsa keyi, tamkar mai barin wasiyya. Mu samman yanayinsa dake sanya tsoro a zuciyarsa. " aheeh!! Wannan wane irin magana ce mai kama da wasiyya?" Hayder ya fada cikin raunin murya.

Murmushi Yusuf yayi tare da jingina sosai a jikin kujerar. " ka dauketa a matsayin wasiyya hayder.  Ina son bayan bana raye ka auri Habiba,  Habiba mace ce ta gari, abin alfaharin kowanne miji daya dace da samunta, duk yadda zan maka bayani bazaka gane me nake nufi ba, sai zuwa gaba. "

Mikewa hayder yayi zuwa kusa da Yusuf, tsugun nawa yayi, hannunsa duka biyu yasa ya dafa gwuiwowinsa dasu. " don Allah karka karya min zuciya, zan iya daukar komai, amma banda irin wannan kalaman naka. In sha Allah zaka ci gaba da rayuwa damu har tsufanmu, kaga aurena kaga yayana, kamar yadda in sha Allah kaima very soon Habiba zata Haifa maka naka. In wani ciwo ke damunka please don't hide it. Ba cutar da bata da magani."

Kanshi Yusuf ya safa, yana kokarin maida hawayensa. " bawa baya wuce kaddararsa hayder. Allah yasa ina da rabon ganin aurenka in ga yaranka. In har hakan alkhairine gareni. Ina maka fatan samun maratus saliha, kamar yadda na dace. Shi yasa nake tsoron haduwata da Allah, don duk wani jin dadi, da kwanciyar hankali na duniya alhamdulillah na samu,. Kudi, mata ta gari, lafiya, kwanciyar hankali. Lahira kuwa, kaga baka da tabbas din karbar ayyukanka na alkhairi."

" ka Sani mutane kashi uku ne, a duniya: 1. Daga ni'ima zuwa ni'ima, 2 daga ni'ima zuwa azaba,( Allah ya tsaremu) 3 daga wahalar duniya, zuwa azabar lahira, (Allah ya tsaremu). Ina maka fatan jin dadi, duniya da kiyama." Hada hannunsa hayder yayi " don Allah kabar wannan maganar haka, ka fara tsoratani da gaske."

Karamar dariya Yusuf yayi. " shi kenan, Allah yasa mu cika da kyau da imani. Gobe ni zan wuce, Oregon. "

" amen, na dauka zamu kwana biyu a nan." Hayder ya fada yana mikewa tsaye.

Tashi Yusuf yayi, yana murmushi. " no!!! Zan je ziyara Oregon one day, in koma gida,."

" please ahehh! Ka kara ko kwana daya ne." Hayder ya fada cikin fuskar shagwaba.

" no way, I miss my wife already, I have to go." Yusuf ya fada yana tafiya zuwa apartment din

" u love her too much ahehh!!" Hayder ya fada cike da kishin hubby, gani yake Yusuf yafi sonta a kanshi.

" I love u more." Yusuf ya fada yana dariya

" if u say so." Hayder ya fada cikin muryar tausayi.

Juyowa Yusuf yayi, ya kalleshi yana dariya. " ina adduar Allah ya kawo karshen yar tsamarka da my wife. "

" ta cika son girma da yawa." Hayder ya fada yana kwallo da wani karamin dutse.

Kallonsa Yusuf yayi yana murmushi " kai kuma ka cika raini ba? Bansan me yasa ka rainata haka da yawa ba."

" bata jin magana, ba kokari a school, ga dan banzan shagwabar tsiya. Ni Tun dawowarta daga kauye, yadda take behaving take ban haushi, shiyasa bana shiga harkarta, amma duk ban tsira ba, ta tasani a gaba da mugunta. Tayaya zan wani girmamata."

" kafa rama koma me ta maka, kaga kunyi 50-50 don haka sai kayi hakuri. In don kifinka da ta cinye ne, zan biya, a zauna lafiya. Ko ba komai ai ta girmeka, gashi kuma tana matsaya yin matata, bana jin dadin yadda kake treating dinta." Yusuf ya fada

Kunne hayder ya kama " sorry, yanzu kam ai ina gaisheta in mun hadu." Dariya Yusuf yayi " good for u." Ya fada yana shigewa ciki, a baya hayder ya biyoshi, a kofar dakin hayder sukayiwa juna sai da safe, hayder ya shige dakinsa, shi kuma ya wuce nashi masaukin dake gaba da dakin Hafiz...

             *********************
Ajiyar zuciya harder ya sauke. Jin numfashin hubby na sauka a hankali, tare da ajiyar zuciya ya bashi tabbacin tayi bacci. A hankali ya gyara mata kwanciyarta, ya mike ya nufi toilet.

Addu'o'i sosai ya jerowa dan uwan nasa, kamar yadda ya saba, tare da masa fatan samun rahamar Allah, ya roka masu zama lafiya shifa hubby da zuria masu albarka.

Yana wurin har aka kira sallah. Sai da ya tashi hubby sannan ya wuce masallaci.

Rashinsa a dakin ya bata damar tashi a natse, duk jikinta yayi tsami, a hankali ta taka zuwa cikin toilet dinsa. Ruwa mai zafi ta sa, ta gasa jikinta tare da yin wankan tsarki, Dana sabulu.  Kokari take ta maida hawayen dake kokarin fitowa.

Duk yadda taso manta abinda ya faru dakika kadan da suka wuce, abun yaki fita a ranta.

Gani take kamar a mafarki, lokaci kadan zata farka. Amma wasa wasa mafarkin yaki karewa.

Taso tafiya dakinta, amma still tana tsoron fita. Rigar daya bata jiya, ita ta dauka tasa tayi sallah.

A wurin ta kwanta, minti kadan bacci ya yi gaba da ita..

Sai to 7 hayder ya shigo gidan. Dagata yayi ya mayar kan gadon, bayan ya gyarashi tsaf. Bai saba baccin safe ba, don haka computer dinsa ya dauko ya fara aikinsa kamar yadda ya saba. Har 9:39 kafin ya kashe, ya nufi kitchen don sama musu abinda zasuci.

Karar rufe kofar ne, ya farkar da hubby. Dakin tabi da kallo, kafin ta mike. Sakkowa tayi, ta nufi dakinta, zuciyarta cike da tsoron kar su hadu da mage.

A bakin Kofa ta tsaya, tana lellekawa, sai da ta tabbatar ba komai, tukun ta shiga dakin. Key take kokarin sawa amma sai taga wurin wayam, ba key a jikin door din.

Wanka tayi, ta shirya cikin atamfa Holland mai kyau, dinkin Riga da skirt sunyi mata cip, komai masha Allah. Kwalli kawai ta shafa, ta gyara packing din gashinta. Feshe jikinta tayi, da turarenta mai kamshi, dan da nan dakin ya dauka, dama ga kamshin humra data sa a jikinta. Higab dinta ta zunbula ta nufi kasa, don yunwa takeji, har tana ganin jiri- jiri.

Mamaki sosai tayi, ganin Mariya harta gama gyara komai, ta sa mata turaren wuta, gidan gaba daya ya dauki kamshi. A kitchen suka hadu da Mariya. Da faraa ta ce " Anty ina kwana?" Murmushi ta mata "lafiya kalau, ya mamanki?"

" ta ce in gaisheki." Mariya ta fada

" ina amsawa, sannu da kokari'" hubby ta fada tana kokarin jona kettle.

Murmushi Mariya tayi. " Anty akwai abinda zan kama mikine? Ko inje in gyara falon sama?"

Kallonta hubby tayi, tana murmushi. " ki bari muci abinci, sai in tayaki"

" na gama cin abinci kenan, na wanke plate din kika shigo." Mariya ta fada

Kallonta hubby tayi, ganin iya gaskiyarta ta fada, yasa ta ce taje ta share falon.

Cup ta dauko, ta zuba madara, sugar  da Millo. Tana jiran ruwan ya tafasa.

Kamshin turarensa ne, ya fara mata sallama. Bata juyoba don bata da courage din fuskantarsa after what happen.

Rungumota yayi ta baya, tare da daura kansa a kafadarta. " good morning. " ya fada in husky voice dinsa. Jikinta ne, ya dau rawa. She can believed what hayder do to her, Ta kara yadda mazan yanzu kunyarsu rageggene.

Hijab din ya cire, a kan dogon kujerar da aka tanada a kitchen din ya wurga. Tare da juyo da ita, Kanta a kasa. Hannunsa yasa ya cire ribbon din kanta, gashin ya baje a bayanta. Ya zubo da kadan ta gaba gefe daya, Wanda ya sauka har kirjinta. " u look good, karki kara samin wannan abun, in har ba baki bane a gidan.

Hubby kam tsabar takaici ne, ya hanata koda kwakwaran motsi. Mamakin karfin halin hayder take yi.
Batayi aune ba, sai bakinsa taji a cikin nata. Kokarin tureshi ta fara, amma ina ya mata kyakyakyawan rukon da bazata iya kubu cewa ba.

Sai da ya gaji, don kansa ganin tsayuwar na Neman gagararsu, yasa ya saurara mata. Hannunta ya kamo, suka jero zuwa main falo, A kasa ya shirya musu kayan break fast. Sai da ya tabbatar ta zauna, sannan yaje ya sallami mariya, don yau bayi da bukatarta a gidan.

Cike da karfin, hali, da tusawa zuciya dangana hubby ta ke cin abinci a hankali. Gaba daya idon hayder na kanta, tausayinta yake ji, ganin yadda gaba daya tayi sanyi, kamar ba hubby ba. Shi kansa yasan bai kyauta mata ba. Amma ba yadda ya iya, dole su rungumi kaddararsu.

Gefensa ta dan kallah. " kai ka kawo mage gidan nan?" Ta fada da muryarta cike da rauni.

" nop." Ya fada yana Kallonta

Shiru tayi, ba tare data yadda da abinda ya fada ba. Don ta tuno da kalaminsa na cewa ita da kanta zata kawo masa kanta, yana shararren wurinsa. In ba shi ya shigo da magen ba ta ina ta samu ta shigo?

Ganin alamar bata yadda ba yasa ya gyara zamansa. " look habibi, da gaske bani na shigo da ita ba, magen gidan barrister ce, dawowana masallaci naji suna tambayar malan idi koya ganta.  jiya  aka kawota, sun tashi da safe, basu ganta ba. Shi kanshi malan idi bai San ta shigo ba.  Ina shigowa mukayi karo da ita a kofar falo, shine na dauketa na mika musu ita."

Ajiyar zuciya hubby tayi, tare da Jan Allah ya isanta ga mamallaka magen.

" magen is so cute!! Kinga picture din da na mana tare." Ya fada yana murmushi tare da bude wayarsa don ya nuna mata picture din.



Haushine ya kama hubby, bata San lokacin data balla mai harara ba. Murmushi yayi yana nuna mata picture din.

Tashi tayi ta nufi, sama da gudunta. Da ido ya bita yana murmushi, tare da shafa sajensa. Kiss yama magen tare da furta " your the best. ".........
[08/03, 20:33] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 21 · 0% Book details