Part 15
Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 23 min read
Written By Zulaihat Aliyu Misau
Wattpad@zulaihatualiyumisau
Not Edited.......
Murmushi mommy Hauwa tayi, duk da dunbin tausayin yar tata. " hayder din dai da baki so, shine. Gara ma ki kwantar da hankalinki, don ba abunda zaa fasa."
" kiyi hakuri, kiwa iyayenki biyayya, matukar sunyi don Allah ba don wani abu na duniya ba. To in sha Allah zakiyi alfahari da hakan. Ballantana Sani kanki ne, duk abunda su kayi, sunyi ne don maslahar, da kuma kyakyawan manufa."
" Allah rainani zai kara yi." Hubby ta fada tana kara sake kuka.
Duk yadda su Hajiya suka so daure dariyar data taso musu kasawa sukayi. Cikin dariya Hajiya salwa ta ce " banda abinki Ummi, yanzu kuma ai ke ce a kasa. Maganar raini duk bata taso ba, dole ki masa biyayya don aljannarki na kalkashin kafarsa. In kina neman aljannah to dole ki ajiye komai ki rungumi aurenki."
Ta bude baki zatayi magana mommy Hauwa ta buge bakin. " rufawa mutane baki, ana magana kina mayarwa, kamar saoinki. Allah ki shiga hankalinki dani. Shi bai yi kukan bai son kiba, sai ke? Yana yaro dashi son kowa kin Wanda ya rasa, an hadashi da uwar mata."
" aa Hajiya Hauwa!!!! Yarinyar tawa kike kira uwar mata, duka duka nawa ummin take? In kyau ne, nima ai baa nunama diyata ba."
Dirin shigowar motoci gidan ya sa hankalinsu ya koma can. Hubby zamewa tayi daga jikin salamatu ta shige dakinta, kuka ta saka iya karfinta ta fada saman gadonta, ta ci gaba daga inda ta tsaya.
Su gwaggo ne, da tawagarta. Lallai kam gwaggo tayi gayya kamar yadda ta fada. Kun San mutanen karkara da son zuwa bikin nesa! Balle sun samu motoci available. Direct part din da aka gyara musu aka wuce dasu. Tare da cikasu da kayayyakin abinci, da na sha, da duk wani Abu da zasu bukata.
******************
Hafiz omer ya samu a reception. Da sauri ya nufo hayder ganinsa a hargitse. Rungumeshi hayder yayi yana sauke ajiyar zuciya. Cike da tashin hankali don bai taba ganin hayder a yanayin da yake ganinsa jiya zuwa yau ba. Na yanzu is worse.
" what is happened? Don't Tell me is notting, tun jiya na lura some think its not right? Hafiz omer ya fada yana dan bubbuga bayansa.
Sakinsa yayi, tare da Jan numfashi. Hafiz omer ido ya zuba masa cike da damuwa. " ka gaya musu, a kwai daurin aure a sultan bello masjid, after sallar jumaa."
" daurin auren wah?" Hafiz omer ya tambaya. Ko kafin ya karasa tambayar hayder ya wuce sama, zuwa dakinsa. Da kallo Hafiz omer ya bishi, yadda yake hada steps 2 to 3, ya haye.
Kai Hafiz omer ya kada tare da cewa " Allah ya kyauta" wayarsa ya Ciro ya shaidawa su junaid. Don duk a tunaninsa daurin auren daya daga cikin yaran abokan daya daga cikin daddies dinsune.
Yana shiga direct toilet ya wuce, wanka yayi tare da dauro alwala, duk da lokacin, ba lokacin nafila bane. Bayan ya shirya cikin daya daga cikin kayan da suka dinka don fitar bikin su Ummul khair.
Shadda ce, mai matukar kyau da tsada milk color. Duk da dan fadawar da fuskarsa tayi, yayi kyau sosai. Time ya duba to 1pm daga hannu yayi, ya karanto suratul fatiha x7, sai karshen suratul bakhara. Sannan ya fara jero adduar jagorancin ubangiji, game da lamarinsa da hubby, ya bashi ikon yima iyayensa biyayya.
********************
Zamewa tayi daga kan gadon, ta kifa kanta cikin pillows ta saki kuka mai tsuma rai, har numfashinta na shishshidewa.
Gwaggo ta matso kusa da ita, cikin tausayawa, da sanyin jiki. " haba takwara, aure an riga da an daura. Balarabe dan uwanki ne, kin san shi, kin San daga inda ya fito. Yanzu ba abinda ya rage face kiyi biyayyaya ga Allah da manzonsa. Kiyiwa iyayenki, da mijinki biyayya."
Maganar gwaggo ta kara sa hubby kara fashewa da kuka, ji take kamar gwaggo ta watsa mata ruwan zafi, jin tace wai hayder mijinta. Dago fuskarta data jeme, tayi ja, ido sun kunbura, don kuka, cikin dasashshiyar murya da bata fita sosai ta bude baki zatayi magana, ko harafi daya ta kasa furtawa. Sai hadiyar zuciya take.
"Ayya har yanzu kukan ne, bai kare ba? Ki bar kukan nan haka zai cutar dake. Aure ne an rigada an daura, ba mu da abin yi, a yanzu. Na fahimce ki, kiyi hakuri da abinda iyayenki suke so, in sha Allah zakiyi alfahari da hakan." Inna shatu ta fada tana shigowa dakin.
" Allah na tsaneshi?" Hubby ta fada cikin dashewar murya.
" to sai me in kin tsaneshi? Mu muna son sa, kafaffiya. Mommy Hauwa ta fada
Harara gwaggo ta watsawa mommy Hauwa. " ana lallaba yarinya kina neman ballo wani ruwan?"
Daukar abunda ya kawota tayi ta ficewarta.
*******************
Gaba daya mamaki ya cika su Ahmad da daukacin jamaar da suka San gidan Alhaji Jamal.
Daurin aure kam yayi jamaa sosai. Abdul Karim gaba daya hankalinsa ya tashi, ganin abun yake kamar almara.
Haka ta kasance gasu junaid da sauran abokan hayder. Da kallo suka dinga binsa.
He act normal, amma deep down his heart, shi kadai yasan yadda zuciyarsa ke suya. Duk yadda suka so jin Karin bayani daga bakinsa, basu samu ba.
Haka sukaita gaisawa da abokan su Alhaji Jamal da sauran family and friends. Kowa na masa Allah ya sanya alkhairi.
Rungumeshi Ahmad yayi, yana masa congrat. Abdul Karim dai ya kasa ko kwakwkwaran motsi, sai bin hayder da kallo yake, da sauran iyayensu da kakanni kowa ka kalla yana cikin matukar farin ciki, da anna shuwa.
A haka suka dungumo zuwa main house.
*******************
A tsakiyar bedroom din Mmn samira, Hajiya Fatima, da wasu mutun biyu da suka mata rakiya, suka ajiye kwalayen sweet, dabino, da biscuit.
Buda daya daga cikinsu ta rangada har sau uku. "Cika alwashi sai dan halas, taka haye baya i'yawa. Allah yayi, alkawarin Allah ya cika, mai kyashi, da hassada sai kallo. Da daya tamkar da dubu, farin wata sha kallo, yaro mai halin dattako, kyau baa fika ba, haka ma arzikin baza a gwada dakai ba, balle ilmi da aiki dashi. Na Habiba Allah ya yarda." Guda ta kara sawa.
Hajiya Fatima ta kalli Mmn samira, da yan uwanta da suka zuba musu ido suna kallon ikon Allah. " ki kwantar da hankalinki, Habiba yanzu haka ta zamo mata ga Aliyu hayder. Wannan goron albishir ne, da kuma godiya."
Kallonta Mmn samira tayi, ta kalli kayan sweet din dake tsakiyar dakinta. Cikin sanyin jiki ta kauda kanta. " Allah sanya albarka."
" amin in da gaske kike." Daya daga cikin matan da suka zo da Hajiya Fatima ta fada
" alhamdulillah tun da an barmin jikana. Meye kuma na bita da kulli?" Hajiya kaka da ta shigo ganin abinda ke faruwa ta fada.
" babu kam!" Hajiya Fatima ta fada tana juyawa don barin dakin. A bakin kofa suka ci karo da Abdul Karim na shigowa, a hargitse. Kallo daya ta masa ta dauke idonta suka wuce, zuwa part din Hajiya.
Jikin Mmn samira yayi sanyi, tabbas bata kyauta ba, bata taba tunanin Hajiya zata zartar da wannan hukuncin ba, nadama da dana sani su suka lullube zuciyarta. Da bata bi zugar su samira da hajiyanta ba, da duk haka bata faruba. Koda Abdul Karim bai auri hubby ba, da ta kwantar da hankalinta an rabu cikin mutunci da ganin kimar juna. Amma yanzu wa gari ya waya. Ta bata da matar da take iyaka kokarinta na kwato mata hakkinta, ba tare da laa kari da zamowarta kishiyarta ba, kasan cewarta mara baki.
Shihowar Abdul Karim ya dawo da ita daga dogon tunanin data tafi. " me yake faruwane mama?" Ya fada bayan ya zauna kusa da ita.
Hajiya kaka ta amshe " meko ke faruwa, banda Allah ya kubutar mana dakai daga auren juya, second hand. Ai sai Ka godewa Allah. "
Wani kallo ya zubama Hajiya kaka kafin yakai kallonsa kan Mmn samira, da jikinta ya kara sanyi. Daya daga cikin kannen Mmn samira ta fara koro masa bayanin duk yadda abun ya kasance.
Kai ya rike, hawaye na bin kuncinsa. " kun cutar dani wallahi, koda na ce ita ba irin matar da nake so ba ce, ai ban ce bazan aureta ba ko? Haka kurun Ku yanke min wannan danyen hukuncin. Ai da sai Ku bari satin da daddy ya diba min su cika kuji matsayata ko? Kun San yadda nake sonta? U have no idea?"
" innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yanzu Abdul mu kake cewa mun cutar dakai? Me yasa tun farko ka ce baka sonta, ina kai da bakinka ka gayawa yar uwarka hakan. Shine don ka raina mana hankali zaka zo ka canza managana, salon kasa a mana dariya. To tun wuri ka cireta a rayuwarka, don ta zama mallakin kaninka." Hajiya kaka ta fada
Idonsa da suka kada su kayi jajur ya daga ya sauke su kan Hajiya kaka. " ina samiran tazo ta gayamin gidan uwar da na ce mata ban son hubby? Ya fada yana waige waige
" ya rage naku kuma, aikin gama ya gama. Ni kaina sai da na bada shawara aka ki saurarata. Yanzu wa gari ya waya? Hakuri kawai zaka dauka, aikin gama ya gama, ka dauka Dama can ba matar ka ba ce." Cikin yan uwan Mmn samira ta fada.
Mmn samira kam ta kasa cewa komai. Sai Karin nadama, da dana Sani dake nukur kusarta.
" idona idon samira, sai naci mutuncinta, munafuka kawai." Abdul Karim ya fada yana barin dakin cikin fushi da bakin ciki.
" a kan wata banza can kake kiran, yar uwarka da munafuka? Ko Anty babu?." Hajiya kaka ta fada tana bin batansa da kallo.
******************
Ko kafin su iso main house, su Hafiz sun kira daukacin friends dinsu dake garin Kaduna, sun shaida musu daurin auren hayder da walimar da zasuyi a gobe Saturday after magrib.
Suna isowa sun samu wasu daga friends din har sun iso. Kowa cike da mamaki, misamman wa 'anda su kayi secondary school tare.
Direct part din Hajiya suka nufa, bayan gaisuwa, hayder yasha albarka, sannan suka shiga part din Mmn samira, sai part din Mmn Yusuf. Wadda itama daga baya taga rashin dacewar abunda sukayi. Ko ba komai tana jin hayder a zuciyarta kamar yadda take jin yayanta. Da tasan abun a kansa zai kare, da ta amince Abdul fatta ya auri hubby, in yaso a hada da nata zabin.
Gidansu bubby suka dun guma, don gaisawa da su mommy da sauran yan uwan hubby kamar yadda al'ada ta gada.
Sun samu tarba mai kyau, kamar a hadesu, musamman gwaggo data zage su kayi ta kashe hotuna da su hayder. Bakinta har kunne, don ji take tafi kowa murna da wannan Abu.
" yanzu da wannan Ummi ke kira da yaro? Wannan ai sai ya sabata a wuya ya kaita, Zaria ya dawo, baiji komai ba." Inna Maryam ta fada
Hajiya salwa ta yi dariya " kin San yaran yanzu akwai saurin girma, kamar ana basu takin zamani. Kalli su junaid? Wa zai ce Ummi ce yayarsu?"
" babu kam!!" Inna maryam ta fada
Yau kam hayder yaga kara da karamcin katsinawa. Duk da dayawansu ya sansu. Amma yaji dadin karamcinsu gareshi. Sun sha pictures kam, kamar ba gobe.
*****************
" don Allah sake trying number din hubby, shirun yayi yawa." Humaira ta fada tana kallon Aisha
" ina ga kuje gidan Ku gani, don nasan lafiya lafiya hubby bazata kai yanzu, bata xoba, kuma bata kira ba. Ga number dinta baya shiga." Aisha ta fada
Ummul khair ta mike," muje " harararta Aisha ta yi " kin manta dokar rashin fita, a kanki ko?"
" share don Allah, sharf sharf zamu je mu dawo, ba tare da kowa ya farga da bana nan ba, in har ba Ku kuka fada ba."Ummul khair ta fada tana daukar mayafi.
" ba ruwana wallahi." Aisha ta fada
Ummu aiman ce ta shigo. "Ke kuma sai ina?" Ta fada tana kallon Ummul khair dasu yusra
" Hubby's house. " ta fada a takaice.
" zauna kusha labari. U can believed what is happened in this house. " Ummi aiman ta fada tana zama kusa da Ummi sulaim.
" me ke faruwa?" Suka tambaya a tare.
Bowl din hannunta ta mika musu cike da sweets masu dadi, da tsada. Kowa ya zabi Wanda ransa ya masa.
" an daura auren hayder da hubby, dazu bayan sallar jumaa. This is the sweets for their wedding. "
Ummu sulaim ne ta mike da sauri, baki na rawa, ta kalli yayar tata " ba kyau irin wannan wasan."
Murmush tayi " ina wasa da ke ne, da zan maki karya? Go and ask."
Kuka Asiya ta fashe dashi. Cike da tashin kankali suka juya kan Asiya.
Mayafi Aisha ta jawo, suka fice ita da Ummu sulaim dasu yusra. Suka nufi gidan su hubby.
A compound din suka hadu dasu junaid. " ta tabbata.? Ummu sulaim ta fada hango su hayder cikin kaya na alfarma, sai kashe pictures a keyi.
" lallai abun da kamar yuwa." Aisha ta fada
Duk yadda suka so jin yadda abun ya faru ya ci tura, don su kansu su Hafiz ba su san takamai mai meya faru ba. Ummu sulaim duk da ita ce gaba da hayder to tana matukar shakkarsa. Don haka kasa tambayarsa tayi. Allah ya sanya alkhairi suka musu, tare da shigewa ciki.
Hubby na zaune da daurin kirji a baikin gadonta, bayan hajja kolo ta gama turareta da wasu itatuwa masu matukar kamshi, fatarta sai glowing take. sai da Hajiya salwa ta tsaya a kanta sannan ta yadda a mata gyaran jikin. Don tana jin nauyin matar sosai.
Da gudu gudu suka shigo, ana rige rige. Hubby na ganin su Aisha ta taso da gudu ta fada jikin ummu sulaim, tare da sake sabon kuka.
" oh!!! Ni yau Allah na gode maka, wai ke bazaki gaji da kukan nan haka ba? Tun safe kina abu daya." Hajja kolo ta fada tana har hada kayan kyaran jikin dake baje a tsakar dakin hubby.
Sai da ta dau some second kafin ta rabu da jikin ummu sulaim, kama hannunta tayi suka zauna. Suma su Aisha sukama kansu mazauni, bayan sun gaishe da hajja kolo. Kallon hubby sukeyi cike da tausayawa ganin yadda ta koma lokaci daya.
" kun ga yadda rayuwata ta kare ko? A rasa wanda zaa hadani dashi sai kanin kanin bayana, wanda a haihuwar kaji, nayi jika, da tattaba kunne dashi. Yaron da na tabbata na taba goyashi a bayana, wace irin rayuwa ce wannan?" Ta fada tana hawaye.
Aisha ta dafa ta " kiyi hakuri, koma me nene, na tabbata akwai babban dalilin da yasa sukayi haka."
" ki rungumi kaddararki, Allah yayi hayder shine mijinki, duk da dunbin masu sonki, Allah yasa akayi dashi, alhalin ba Ku kuka sasanta kanku ba, hakan na nuni akwai hikima mai girma a tare da wannan lamari. Duk mu nan waya taba kawo hakan a ransa? Ko da wasa, amma Allah cikin hikimarsa gashi ya tabbata. Just accept the true, and deal with it." Yusra ta fara
Harararta hubby ta yi da kunburarrun idonta. " don bake aka aurawa wannan karamin yaron ba, kya ce inyi hakuri mana!!!"
Rungume hubby Ummul khair ta yi tana murmushin maganar hubby " na dade ina fatan haka ya kasance tsakaninki da hayder. Duk lokacin da kuke drama dinku, kuna burgeni, ina ma ina nan in muku zaman daki. Ko ba komai zan sha kallo."
Da sauri hubby ta banbareta a jikinta, tana kai mata duka " ban yafe miki ba kuwa, Muguwa."
Gaba dayansu dariya suka sa. Ummul khair ta tabe fuska " nama dauka zaki ce, zakimin tukuicin takwara."
" in baki rufe min rubabben bakin kiba, zan fasa miki shi wallahi. Allah ya tsare ni, Bakinki ya sari guntun kashinki da haihuwa da wannan dan yaron." Hubby ta fada tana huci
Hajja kolo dake faman dariyar su hubby, ta kalli hubby still tana dariya " yaro man kaza, waya gaya miki namiji na kadan? Zako kisha mamaki."
" barta kawai, ran da muka ganta da turtsi billi, tayi mana bayani ai.?" Ummul khair ta fada tana dariya
Ai da gudu tabar dakin tana dariya, saboda hubby da tayo kanta........
Dariya su ummu sulaim suke wa hubby da Ummul khair. " na rasa yadda akayi, yarinyar nan ta rainani da yawa." Hubby ta fada tana kwafa.
" gaskiya Ummul khair ta fada. Kun matukar dace wa. Nima nayi missing din drama dinku wallahi. A ture batun wasa. He is the perfect match for u. Sai dai wannan karon sai kinyi a sannu, don nasan ba canzawa zakiyi ba, in ba haka ba kyaci na jaki, don karayrawyaki zai yi, daga ke se shi, ba mai karbarki." Yusra ta fada tana dariya
Tsaki hubby ta ja. " Allah ya kyauta me jiya tayi, ballan tana yau."
" wan can karon an turguda kafa, wannan karon kam tabbas, in baki bi a hankali ba, karyaki za'a yi. Bana kusa balle in zo zaman jinya." Aisha ta fada
" kun zo kumun jaje ne? Ko kunzo Ku kara bata min rai ne? Ku nuna min kuna bayan dan uwanku?" Hubby ta fada cikin bacin rai.
" sorry sister, ba nufin mu haka ba. Amma To tell u the true, we a happy for u." Ummu sulaim ta fada
Hajja kolo dake kwasar dariyar drama dinsu, ganin abun nasu bana kare bane, ga lokaci na ta tafiya. ta kalli hubby tare da mika mata hadin da tayi a wani bowl "gashi, ki shiga ki shafe jikinki da wannan."
Hararar bowl din tayi, "banda na dazu kuma har da wani, nafa gaji gaskiya, dazu haka kikai ta dirzar min jiki, kamar kin samu kayan wanki, ni kam bazan sake ba,."
" Aisha kira min Hajiya salwa a falon Hajiya Hauwa. " ya kolo ta fada tana kallon Aisha
Karba tayi ta wuce toilet tana kun kuni. " kunyi a banza, asarar kudi, da wani abun kukayi da yafi muku." Ta shige toilet din.
" Zuma sai da wuta." Humaira ta fada
Hajja kolo ta ce " ai abubuwan hubby sai a hankali, Allah ya bashi ikon hakuri da ita."
" miskili kafi mahaukaci ban haushi, shine dai dai da ita, dama kuma ai sun saba, wanda yaji wuya ya sake." Aisha ta fada
" ya maganar walima, zaki samu zuwa ko ya zaa yi?" Yusra ta tambayi hubby bayan ta fito.
" I don't no." Ta fada
" yanzu kam ai sai da izinin mijinta, in ya yarda mai zai hanata zuwa, tunda duk na gida ne." Hajja kolo ta fada
Yamutsa kumburarriyar fuskarta tayi " lallai kam zaa rube a gida, in har sai na tambayi wannan yaron zan fita."
Dariya sukayi Aisha ta ce " da ko baki kyauta mana ba. Kin manta ke kikayi paganizing komai? Sannan ki ce bazaki ba? Meye a ciki don kin tambayeshi? Naga durkusawa wada ai ba gajiyawa bane."
" kin san in ba kya wurin ba zaiyi armashi ba." Ummu sulaim ta fada
Banza hubby ta musu, don duk haushi suke bata. Don ta lura dadi ma sukaji an aura mata kanin bayanta.
" ki shirya don Allah, zan ma Hajiya magana, sai ta turo a daukeki." Aisha ta fada tana fita daga dakin. Baya su yusra suka rufa mata, bayan sun ma su hubby sallama.
" ko Janeway zaa kawo, ban zuwa ko ina." Ta fada tare da bin bayansu da harara.
Dariya humaira, da zata zauna da hubby tayi. " aikin banza harara a duhu."
Harara hubby ta aika mata. " kema tashi ki bisu."
Harararta ta rama. " nima sai ki kawo Janeway ai, ki fita dani. Zama daram, har sai randa muka mikawa hayder matarsa.
Robar humra ta jefeta dashi.
Gwalo ta mata " oho!!! Dai."
******************
Su hayder daga gidan su hubby, mai furniture da mommy Hauwa ta hadasu dashi suka dauka, zuwa gidan da zasu zauna.
Duk kansu gidan ya musu kyau. Komai a tsare. Mai furniture ya gama aune aunensa yayi gaba.
" don Allah hayder ka bani wuridin da kake yi, nima in fara." Hafiz ya fada
Dariya sukayi, banda hayder da ya harari Hafiz. Dafa Hafiz amir yayi. " nafi kowa bukatar wuridin nan."
" gaskiya you're very lucky, you bit the whole kangiwa, in just few day's. " Hafiz omer ya fada
" gaskiya na maka murna, kun balain da cewa." Daya friend dinsu ya fada
" ka bude mana hanya, nima kaga yanzu ba wanda zai ce min nayi yarinta, in na daddago aurena." Hafiz omer ya fada tana murmushi.
" dama kai akawa auren ai da an huta, da tsince yaran jamaa da kake yi." Alim ya fada yana dariya
Duka Hafiz omer ya kaima alim.
" ko ina sai kun nuna hali ne?" Junaid ya fada yana musu inkiya da ido, saboda basu kadai bane, akwai some friends da bazasu so susan sirrin su ba.
" bar dan banza, in masge shi." Hafiz omer ya fada cikin wasa
Sai kusan magrib suka bar gidan. Sun tsaya tsara yadda komai zai kasan ce, ya bada tsari da ma'ana.
********************
Zaune suke a babban falon gidan Alhaji babba. Dau kacin iyayensu maza, suna wurin, sai Alhaji kawu da aminansa biyu.
Kowacce sanye cikin kaya na alfarma, tasha lullubi da manyan mayafi, sai kamshi daya cika falon tamkar shagon perfume.
Nasiha mai ratsa jiki, Alhaji babba ya musu, bayan ya gama Alhaji kawu ya amsa:---
Ku qudurce a ranku zaman ibada zakuje. Kuma ku sama ranku sabida Allah zaku zauna da mazajenku, ku yadda da qaddara kowane iri a cikin rayuwarku. In har kuka riqe haka to bazaku shiga shahun masu cewa " duk wacce tace namiji ubane xata mutu marayainiya ba.
komai talaucin mijinki, ko kaushin halinsa, ko kananun shekarunsa, ku rungumi abinku, ku yi ta mai addu'a, domin wata kamarshi ma take nema bata samu ba.
Ina dada Jan kunnenku, da kusani, mijinki abin tausayi ne, abin lallashi ne, abin tarairaya ne, gareki domin shine mahadin rayuwar ki, kuma aljannarki.
Kuji tsoran Allah, kar Ku zama masu
yawan buri da son duniya, kwata kwata duniyar kwana nawa ne, kina tabbacin xaki maimaita shekarun ki na baya? Sannan in kin sameta, kina da tabbacin lokacin da zaki moreta?
Duk halin da kike ciki a gidan mijinki ki godema Allah, domin akwai wacce ta fiki matsala, amma tana godiya ga Allah. Ki tuna Allah da kansa yace " bayan tsanani sauqi na zuwa"
kuyi haquri da mazajenku, babu abunda haquri baya haifarwa. Musanman a wannan lokaci. in kin tuna Allah da kansa yayi magana akan haquri. To ashe ko ba qaramin abu bane. In kikayi riqo dashi zaki samu riba mai tarin yawa. Domin Allah yana tare da mai haquri, Kuma haquri haskene. kuji tsoran Allah kar wayewa da ilimin boko, ko yawan shekarunki, yasa ki dinga ganinki dai dai da mijinki. Hakika shine gaba dake, Allah ne ya bashi wannan matsayin, don haka Ku kiyaye.
Allah ya muku albarka, ya Baku yaya na gari, ya sanya yalwa da tsoron Allah cikin rayuwarku."
Gaba daya suka amsa da "amin" banda amare da jikinsu ya kara yin sanyi. Kowacce kukanta ne ya karu.
Sauran iyayen ma albarka suka sa musu. Sannan aka fito dasu, Kowacce aka nufi, motar da zaa kaita gidanta da ita. Ummul khair da Aisha, abuja aka nufa don kaisu dakunansu. Sai ummu sulaim kano, sai hubby malali.
Hubby tayi kuka kamar ranta zai fita, ga kewar su Aisha, sannan abun da take ganin kamar wasa, yana neman zama gaske, koma ya zama gaske.
Gida yayi kyau, ba karya, su mommy Hauwa sunyi matukar kokari, fiye ma da last time. Don komai sabo suka zuba mata, High quality dakunan bacci biyu da falo biyu. Sai hayder da ya gyara nashi bedroom din da babban falon gasa, sai small bedroom dake kasa. Fadin haduwar gidan hubby kauyan cine, ko a turai sai haka. Bikin yar gata da autan Hajiya, ai kuma kunsan baa magana.
Nasiha sosai su Hajiya salwa suka karawa hubby. Sannan suka tafi, a kabar hubby da kawayenta biyu. Humaira da Khadija.
Hira humaira da Khadija ke yi, hubby kam tana kashin gide, a hadadden Italian bed dinta. Tayi nisa cikin duniyar tunani.
" don Allah Ku tashi muje, mu dan zaga gidan, na dade banga gidan daya burgeni irin wannan ba." Khadija ta fada, tana mikewa.
Tashi humaira tayi, dama zaman ya isheta, hannun hubby ta kamo. " please tashi muje." Mikewa tayi suka fito ko ina sun shiga a sama dakin hayder ne kawai suka samu a rufe. Suka sakko kasa, nan ma sun shiga ko ina, kafin suka yi branch a kitchen.
Katon kitchen ne, yaji cabinet, ka naurorin girki na zamani kala kala, wasu ma su humaira basu san anfaninsa ba. Fridge humaira ta bude, mai 2 door, " na dade ina ganin irinsa a TV, yau gashi ina ganinsa a fili. Gaskiya kitchen din nan yafi ko ina kyau."
Murmushi Khadija tayi. " ai nima abun ya burgeni. Na dade banga kitchen daya burgeni irin wannan ba. Ai in a gidan nan nake, kullun ina nan."
Kallon TV dake manne a bangon kitchen din tayi. " Irina kam, ai kullun sai na babbaka girki." Humaira ta fada.
" mayyar series ba!!! Balle ga TV a kitchen ai kam sai abunda Allah yayi."
Dariya humaira tayi. " masha Allah, komai yayi kyau. Allah ya bada zama lafiya, nan da 9month muzo suna."
Tsaki hubby ta yi, tana maka mata harara, ta fita.
" komai barazanar Amarya, sai ansha manta." Khadija ta fada tana dariya
Sallamar da sukaji yasa su fitowa. Mata biyu ne, yan uwan mommy Hauwa suka shigo da jerin akwatuna, na auren hubby.

Sai da suka jera mata su tsaf a dakinta. Sannan sukai mata sallama. Ganin mota free, ga dare ya fara yi yasa su humaira binsu. Tare da ma hubby fatan alkhairi.
*******************
Mota kusan hudu suka shigo, harabar gidan. Su hayder ne da 6 best friends dinsa.
Sanye yake da kananan kaya. Blue Jens, sai White shirt mai gajeran hannu. Kafarsa sanye da sandal farare,. He look handsome.
Tsayawa sukayi suna kallon gidan, kowa da abunda yake sakawa. Hannu junaid ya mikawa hayder.
" dud Allah ya sanya, alkhairi ya baku zama lafiya, Ni kam ina daga nan." Ya kalli su Hafiz " I'm wetting for u hare." Ya fada yana shigewa motarsa.
Dariyar Hafiz omer yayi " kai kam Allah yayi matsoraci."
" naji sai kun fito." Junaid ya fada
A hankali suka taka zuwa kofar da zata sadasu da cikin gidan. A bakin kofar harder yayi burki, juyiwa yayi yana kallonsu. Hannu ya mika ma ashir dake rike da ledojin kaza, fresh fruit, yeghout, sai chocolate. Mika masa yayi, yana masa kallon tambaya.
Murmushin gefen baki hayder yayi " na gode, Allah tashemu lafiya."
Baki bude suka tsaya suna kallonsa.
Gira ya daga musu " what?"
" kana nufin baza mu shiga ciki ba? Ko ya?" Amir ya fada cike da mamakin hayder.
" na hutar daku, sai da safe." Hayder ya fada yana shigewa ciki, tare da murzawa kofarsa key.
" kam biji, biji iskar sanyi. Amma yaron nan yama raina mana hankali."
Hafiz ya fada yana rike baki.
Dariya Hafiz omer ya saka, har yana rike ciki. Suma dole suka tayashi, don abun da haushi, da mamaki.
" in kun gama tsayuwar sai kuja, akwalar kafafunku, mu tafi." Amir ya fada yana yin gaba.
" garama da bamu shiga ba, da da wane ido zamu kalli Anty hubby, a ce mune yan siyan baki? I wander how she feel, about all this thing. " Hafiz ya fada
" its true, nima na dade ina wannan tunanin." Alim ya fada
" abun da kamar wuya, ina imagining yadda wannan zaman zai kasan ce." Ashir dake kokarin shiga motar da suka zo da ita ya fada.
Dariya Hafiz omer yayi " ehhhimmm hayder ne fah!!! Muna nan daku, tsaf ze bi da ita."
Junaid ne ya leko da kansa, " zaku zo mu tafi? Ko zaku tsaya, shiga abinda bai shafe kuba."
" I Wonder. " ashir ya fada
Haka suka ja motocinsu kowa ya nufi makwancinsa.
Malan idi, ya maida get ya rufe.
A kan kunnen hubby suka shigo, tashi tayi, ta murza key a kofarta, tabar key din a jiki. Wanka tayi, tare da shirin bacci. Maganin da Khadija ta bata na ciwon kai, ta dauko ta bude fridge dake bedroom din, ta dauko faro. Tasha, adduoin kwanciya barci tayi, taja lallausan bargonta ta lullube, saboda sanyin ac. In no time bacci yayi gaba da ita. Saboda gajiya, ga rashin isashshen bacci.
Hayder kitchen ya wuce, ajiye komai a muhallinsa. Sannan ya wuce bedroom din sa. Wanka yayi, tare da shiryawa cikin kayan bacci Mara sa nauyi. Baya tare da yunwa, don haka shima yabi lafiyar gado. Abubuwan da suka faru ne, suka fara dawo masa kamar majigi. Nasihar su Alhaji babba ta tsaya masa a rai. Sai tunowa da dan uwansa, da yayi. Ajiyar zuciya ya sauke, yana tuno ziyara ta karshe da dan uwan nasa ya kai masa, lokacin bai wuce saura sati uku kacal yabar duniya ba. Magan ganun da sukayi a lokacin suka fara dawo masa, kalma by kalma. Hawaye suka fara zarya a kuncinsa. Adduar da ya saba ma dan uwan a duk lokacin da ya tunasa, yayi. Tare da kara gyara kwanciyarsa. Ya fada tunanin yadda zata kaya shida hubby.......
[05/03, 14:06] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA