← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 28

                            Part 2

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau
   
Not Edited.......

Falon da yake mallakin yaran gidan ya nufa. Su Anty khulsum ya samu a folon suna kallon series a Tashar zee would. Sallama yayi, ya wuce dinning ba tare da yace musu komai ba. Suma bayan amsa sallamar da kallo suka bishi, har ya zauna a kan kujerar dinning din,  ya fara cin abincinsa.

"Muskili kafi mahaukaci ban haushi, wannan dashi aka fara haifa a gidan nan da mun bani" cewar Anty Aiman.

"da gani yauma wani ya taboshi" sulaim ta fada idonta a kansa.  " brother ba gaisuwa?

Kamar bazai amsa ba,  da dago ya kalleta " nayi sallama " yace a takaice yaci gaba da cin abincinsa.

" munsan da kayi sallama, amma ka gaishe mu ko? Anty khulsum ta ce tana harararsa.

Abincinsa ya ci gaba daci, ko dago Kai bai yi ba,  balle tasa ran zai amsata.

Khair ce tace " haba haydar ba dakai ake magana ba,  kayi mata banza.

Harararta yayi, don duk cikin yayyen nasa yafi rainata, saboda shi yake binta.  " sallama itace wajibi kuma nayi.  Ya fada

Tsaki tayi Allah ya yaye maka mugun hali,  wata rana ayi abun arziki dakai wata rana iskancinka yafi na tsohuwar mota.  Khair ta fada tana harararsa, wanda bai ma San tanayi ba.

" naga dai mmn yusuf aiki take a kitchen, ne makon kuje ku tayata, kunzo kuna kallon abinda bazai anfane kuba "  ya fada yana kallon su

" Zanci gidanku kam yanzu,  mu Kake gayawa muje muyi aiki a kitchen?  Anty khulsum ta fada cikin fada da jin haushinsa.

" zo ka kwashemu ka kaimu,  Dan ban zan yaro, Mara kishin uwarsa. Sulaim ta fada

Bakin shi ya tabe, tare da daukan plet dinsa yayi waje.

"Allah yaron nan sai hajiya ta tashi tsaye a kansa, in ba hakaba wata rana cewa zai Ba ita ta haifeshi ba.  Khairi ta ce

Anty Aiman tayi murmushi "lamarin haydar sai a hankali, tunda kunsan halinsa, meye na tada jijiyar wuya, wani irin fada ne hajiya batayi ba,? amma me ya canza?  So ku Dena bata bakinku a banza.

Sallamar su Abida, ya katse maganar da sukeyi.

           ********************

Hajiya hadiza (hajiya) uwar gida a gidan Alhaji Jamal. Auren hadi aka musu da ita. Mahaifiyarsa ta zabo masa ita, kasan cewarsa mai biyayya ya amsa da hannu biyu.

Matace mai kirki dason jamaa,  but akwai son iko, da nuna isa.  Bayan aurensu da she kara biyar,  ya auro Hajiya Amina itanma kusan zamu iya cewa hadine yar aminin babansa ce.  Mata mai hakuri,  da biyayya. Duk iya abunka baka taba ganin bacin ranta.  Haihuwarta daya ya auro Hajiya saadatu itan ma hadi ne, kanwar abokinsa ce dake Niger.  Akwai kirki, sai dai bata daukar raini.

Hajiya hadiza da Hajiya Amina kansu a hade yake, koda Hajiya saa tazo, sai ta zama wararriya a cikinsu.  Ba shiri ko kadan tsakaninta da uwargidan. In kaji fada ya tashi, ko ana sulhu to tsakanin hadiza da saa ne. Don ita Amina bata da abokin fada a tsakanin su.

Tun tasowar haydar Allah ya hada jininsa Dana Hajia saa, yana sonta. Haka favorite brother dinsa yusuf, yaronta na farko,  suna matukar shiri.

Wannan Abu na matukar bata ma hajiya rai,  tayi fada har duka amma ba abunda ya canza.  Musamman ganin duk yadda take da Hajiya Amina amma haydar gaisuwa ne kawai ke hadashi da ita. Duk da kirkinta mu samman akan shi.

                ******************
Still hajiya da mmn samira ya samu, a falon hajiyar.  Dakin sa ya wuce ba tare da ya ce musu komai ba,  bayan sallamar da yayi.

Suma gaba daya hankaalinsu nakan kayan da suka zaba, don bikinsu anty khulsum ya matso.

" to yanzu zamu kirata ta duba ne ko ya zaayi?  Mmn samira ta tambaya.  Hararar mmn yusuf tayi " kin jiki da maganar banza, kedai ba kin zabi naki ba?  Sauran da suka rage,  zan aika mata, ya rage nata kuma.

" bakya gudun tace bata so,  har maganar taje kunnen Alhaji?  Kin san abun bazai yi kyau ba.

" ke dai wallahi anyi matsoraciya, mai jiya tayi balle yau?  Naga mune gaba da ita a gidan nan.

" haka ne, amma kin san bata raina abin fada. Kuma ya kamata in ma zamu Fara zaba, mu zaba a gabanta. "

Tsaki hajiya tayi, tare da harararta" an dai ji haushi,  kwashe sauran kayan in kin kai ta zaba sai ki dauki sauran."  Aliyu ta kwalawa Kira.

Fitowa yayi bayan ya amsa, fuskarsa Ba faraa, don yana jin duk abinda suke cewa, ya rasa wannan kishi dake damun hajiya. Abu yaki karewa tun kuruciya,  gashi har an Fara manyanta. Amma kullun sabon rigima suke bullowa dashi.

Ganin yanayin fuskarsa yasa ta harareshi,  " kwashe kayan nan ka kaimin daki ". Ta nuna masa kayan da ta zaba. Kallonta yayi yana son yayi magana,  amma baiga fuska ba.

" zaka dauka ka wuce, ko sai naci gidanku,  a wurin nan " ta fada tana ci gaba da harararsa.

Dauka yayi ya wuce dakinta dake kallon nasa.

" kinga kwashe kayan nan, kiyi gaba" ta fada tana gyara zamanta

Murmushi mmn samira tayi " me yayi zafi, shi ba wuta ba "

" ai kece kina bani haushi wani lokaci"

" Aliyu dauki kayan nan ka kaiwa mmn yusuf" mmn samira ta fada tana nuna masa kayan da suka rage a gefe.

Ranshi bai so ba, ya dauka ya fita.

Can Sai gashi da kayan,  " tace bata so, ku hada duka" ya fada yana ajiye kayan inda ya dauka.

Mmn samira ce ta Kalli hajiya " kinga dama abinda nake fada ko?

Murmushi hajiya tayi " wannan kuma ya rage nata, kaya dai dole ta amsa,  in bataso Sai ta bari, in wanda ya ajiyeta ya dawo, ta mayar masa, don ni kam na riga na zabi nawa"

Kayan ta zuba a Leda, ta fita zuwa kitchen.

Har lokacin mmn yusuf na ta kokarin hada abinci, don hajiya ta aiki Mai tayata aikin, duk don ta kun tata mata,. Su abida da ke taimakonta yau basu dawo school da wuri ba,  gashi kuma kowacce ta dawo da home work. So dole ita kadai take aikin, don tasan ko zata mutu su khulsum bazasu tayata ba, saboda suna taya uwarsu kishi,. Sannan don kuturun wulakanci Alhaji ya aiko da kaya amma bazasu kira ta ba, sai sun gama zaba sannan don sun rainata su aiko mata da abinda sukaga dama.

" to sababbiya, gashi nan in Wanda ya aiko da kayan ya dawo ki mayar masa, don nikam bazan ajiyesu wurina ba. " hajiya ta fada tana jefa mata ledar can gefe.

zuciyar mmn yusuf ne ya fara tafasa, ba don komai ba sai jifo kayan da hajiya tayi. Cikin bacin rai ta juyo tana kallonta. " Allah sarki duk inda akayi da jaki, sai yaci Kara, kin dai san gidan da na fito?  Ke kaya ya dama, da har kike wani takama akai,  ki hada da naki ki rike, banso, kin San zan iya siyan dubunsu in har naso, ke kike fatarar kaya. " tayi tsaki ta juya don ci gaba da aikinta.

" kam bala'i, ni kike gayawa wannan maganar, dadin abun mun san komai, balle a mana fiffika, gidanku yafi gidan mune?  Da har kike wani ikirarin ansan gidan da kika fito?  Muko muka san gidan da kika fito. Dadin abun da gidan uba ake tinkaho,  Ba gidan yaya ba. Kaya kuwa in kinga dama ki zubar a bola, bai daman ba. Dole inyi tinkaho da kayan mijina, ba Wanda zan siya da kudin da nayiwa yayana yar murya ba.  Banza karya tseeeee!!!!!!!

" ni kike kira karyar?!!!!!!  Mmn yusuf ta fada tana nuna kirjinta, cike da bacin rai

Dariya hajiya tayi, "au!!!! Da kin dauka da WA nake??

" kun kyauta, nawa tukuicin kenan, ina can ina Nemo muku abinda zakuci kuna nan kuna tona min asiri" Alhaji Jamal da ya shigo tun fara hayaniyar tasu,  ya tsaya yana jin duk abinda suke yi ya fada cikin tsananin bacin rai.

Juyowa sukayi a tare jin muryar mijin nasu.............
"sannu da zuwa" hajiya ta fada cikin rawar murya, ganin yadda ransa ke bace.

Harararta yayi,  yayi tsaki ya wuce part dinsa. Itama tsakin tayi ta koma falonta.

Mmn yusuf ta ci gaba da aikinta, cikin bakin ciki, da bacin rai. Don bata so abin ya tsaya a haka ba 😎 duk da tasan magana bata mutu ba.

                *****************
Zaune suke a falon Mai gidan, bayan sun kammala cin abinci. Yau gaba daya cin abincin ba armashi, don ran Mai gidan a bace yake dasu.

" dauko min fruit salad din da nace ki hada min" ya fada yana kallon mmn yusuf.

Shiru tayi kamar baza tayi magana ba " bari in je in hada. Yau aiki yamin yawa shiyasa ban samu yi ba.

" ban gane aiki ya miki yawa ba?  Duk yaran dake gidan nan? " ya fada yana kallon ta

" hajiya ta aiki ladi, su abida yau basu dawo da wuri ba, already kowacce ta dawo da home work, so I have to do it by myself "

Kai ya kada cike da bacin rai. Su kam hajiya da mmn samira ba wadda ta tofa nata suka ci gaba da kallon news.

Har ta kusa fita dakin, yace ta dawo ta zauna.  TV ya kashe tare da gyara zamansa, ganin haka, yasa kowacce shiga cikin natsuwarta.

Hajiya ya kalla " meye maanar abinda nazo na samu kunayi dazu?

Kallonta takai kan mmn yusuf dake zaune can gefen Alhaji. Itama kallonta take yi, harara suka aikawa juna.

"dake nake " ya fada cikin daga murya

" kayan da ka aiko mana ne, na aika mata da nata,  ta dawo min dashi wai bata so. Shine na dauka na bita dashi kitchen."

Tayi shiru " sannan sai akayi me? " ya tambaya.

" magan ganu ta fara gaya min ni kuma naga bazan iya yin shiruba na Meyer mata.

Juyawa yayi wurin mmn yusuf " me yasa kika maida kayan bayan an kawo miki "

" da aka kawo kayan, in da sun shirya gaskiya ai nima sai su kirani mu zaba a tare, in ma su zasu fara zaba, bazan damu ba. Amma basu kirani ba saida Suka gama abinda zasuyi suka aiko min da saura, bayan sun zabe, shiyasa nace ya mayar musu banso, su hada duka. "

" ke Amina ya akayi? Ya juya yana kallonta. Shiru tayi ta rasa abun cewa, don ta tsani tashin hankali a rayuwarta. Da hajiya taji shawararta da duk haka bata faru ba.

" kun kyauta. Amma ku sani bazan dauki wannan halin banzan ba,  na gaji da matsalarku, kun girma amma kullun abinku karuwa yake.  Yaran ku ake kokarin aurar wa, wannan shine tarbiyyar da zaku basu su dinga yi a gidan mazajensu?

Ku dubeni da kyau son kowa kin wadda ta rasa, kyau, kudi, Hali mai kyau. San kacecen mutun Irina 😂 na kwasoku don in rufa muku asiri, ni kuke kokarin tona min nawa ko?  To kuji da kyau duk randa irin haka ta Kara faruwa, gaba dayanku Sai kun bar min gidana. Don duk cikinku ba wadda naje na makale a soron gidansu don neman soyayyarta. Balle ta zame min matsala a gida.

Hajiya ce cikin bacin rai tace "kai kullun Abu ya faru Sai ka mana gori?  Naga ba masoya muka rasa ba, muma ai mun rufa maka asiri"

" ja can ki rufe min baki. Duk samarin naku sun Kama kafata ne?  Shi yasa kuna ganina duk kuka rude, kunga hadadden yaro. Da nasan in na taimake ku abin da zakumin a gida ke nan da ban kwaso ku ba.  Mu samman ke da wannan yana nuna saa kunfi kowa matsala.

Kuje ku kwaso kayan ku kawo min. Ina duk akan rabo ne fadan?  To zan raba da kaina. Tunda ni zaawa kwalliyar ko wacce nasan Wanda zai dace da ita."

Dole kowacce taje ta dauko ta kawo masa.  Rabawa yayi da kansa ya dauka ya mikawa kowacce.

" ku Ba kyau ba, Sai Dan banzan fitina, 😂 dole ne yanzu nima in kwas kware in Nemo sweet sixteen zabin zuciyata, ko na more, sauran kuruciyata.

Duk kansu hararar sa sukayi, in da sabo sun Saba da halin mijin nasu. Duk ranar da suka bata masa rai, sun shiga uku da gori.

" Ai wallahi kai kanka kasan duk cikin mu ba mummuna, Kai din ma banda fari mai zaka nuna mana" mmn yusuf ta fada tana tura baki kamar wata karamar yarinya.

Dariya yayi ganin yadda suka Shaka, ko wacce ta cika tayi fam, banda mmn samira dake murmushi kasa kasa.

" ke kam in ana magana, be kamata kisa baki ba, ki bar Amina tayi magana, duk da ita din ma in muna wuri, bata isa zuwa ba. Ku Bari ku ga zankada ziyyar da zan kawo muku. Tattaro min kan yarana "

Ya fada yana kallonsu.

" Allah ya kawo ta lafiya,  ta makara tunda ka zama saura, sai dai ta samu sidi. " hajiya ta fada cikin jin haushi

Murmushi yayi ya tashi yana Dan jujjuyawa a gabansu " waya gaya miki na miji na tsufa?  Don baki san yanda yan mata keta kawo min Hari bane, Yanda kuka San zasu lashe muku ni. 😝 ba komai, zan nuna muku har yanzu irin mu ake yayi.

Sallamar yaran nasu sukayi, suka basu izinin shigowa.

Sun gaishe da iyayen nasu, suka nemi wuri suka zauna. Kallon yaran yayi cike da jin dadi, da alfahari " Masha Allah LA kuwwata Illa billah" ya ambata Kamar yadda ya Saba in ya gansu haka a hade.

Kallonsu yayi ya nuna khulsum " meye cikakken sunan ki?  Kallonsa tayi cikin rashin fahimta.

" ina nufin da wane suna kike bearing "
"ummu khulsum jamal yusuf "

Kai ya kada, haka ya dinga tambayar sauran ma kowa na fada masa. Bayan sun Gama ya ce " waye Jamal yusuf zubair Oregon? "

Aaira ce tayi saurin cewa " kai ne mana daddy "

Murmushi yayi, ya daurata kan cinyarsa " yau wa autan kaji"

Kallon sauran yaran da suke sauraron abinda zai ce, don duk sun shiga rudani.

"kun yarda nine dai daya ubanku ko?  Amsawa sukayi da "eh !! "

" fine!!!  Na lura da wasu abubuwa dake faruwa a gidan nan, da zuciyata bazata laminta ba. Ni ne dai daya mahaifinku duka, kuk kanku daga tsatsona kuka fito,  kunga kenan Baku da ban banci, Ba nason halin yan ubanci da kuke son tsiro dashi, so nake naga kun hada kanku, ku so junanku don Allah, ku zama tsinstiya madaurinki daya, ku zama sirrin juna. Masu taimakon juna, da jin kan juna,  wannan shi nake bukata a cikin gidan nan.

Ya juya wurin su hajiya " a matsayinku na iyayensu mata, zan so ku hada kawu nan ku, ku so juna don Allah, ku zama masu taimakon juna, da son ci gaban juna, babu bakin ciki, ba kyashi.  hadi kan ku shi zai tai maka wurin hadin kan yara na. Amma ku sani, muddin na ci gaba da ganin baraka a kan yarana.  Wallahi duk sai kun tafi gidajenku.

Magana ta gaskiya kenan, bazan lamunce, ku raba min kan yara ba, zan gwammace in rabu daku, in Nemo waanda zasu kulamin dasu.

Ban yadda yarana su raina daya daga cikin ku ba, wai don ba ita ta haifeshi ba, dole su girmamaku kamar yadda zasu girmama mahaifiyarsu. In har kuna son zama lafiya a gidan nan.

Yan mata na, dole ne ku Saba musu da shiga kitchen, in dai suna da free time. Ba ban banci da wadda take girki a lokacin.
Sannan daga yanzu har sati biyu Kafin bikin su khulsum, su zasu dinga girki a gidan nan. Kafin lokacin ko wacce ta samo Mai tayata aiki, ranar girkinta. Case close "

In akwai Mai magana yana iya yi?

Ya tambaya yana binsu da kallo.
Duk jikinsu a sanyaye,  kowa yayi shiru.

" OK kuna iya tafiya, ku kuma mazan ina da word daku "

Fita su khulsum sukayi, bayan sunma iyayen sai da safe.

Kallon shi yakai kan yusuf  " yah!!!  Ka gama shawarar? "

Kai yusuf ya sun kuyar cikin jin kunya. A hankali ya kada kai tare da cewa " eh!!! Daddy "

" good kana nan akan bakan ka ko ka canza shawara?

" aa "

"ka tabbata kana sonta, itama tana sonka? Kun dai dai ta? "

"eh!! Daddy " ya fada cikin jin kunya.
Su hajiya da basu San kan zancen Ba, shiru sukayi suna sauraro.

" Masha Allah.  Wannan Abu yayi min dadi, Allah ya sa albarka a ciki. "

Amin sukace gaba daya.

" wai zancen me Kake yi ne?  Kun samu a duhu? " hajiya ta tambaya

Murmushi daddy yayi " maganar yusuf da yar wurin Hauwa, habiba."

" wace habiban?  Mmn yusuf ta fada tana zaro ido.

" habiba dai daya da kika sani, yara sun hada kansu, tunda Ahmad ma ya fito da tashi, gara a hada gaba daya da nasu khulsum.

"Tabdijam !!!!! Wallahi bazata sabu ba......... 😮😬


 
[29/02, 19:22] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 2 · 0% Book details