Part 11
Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 32 min read
Written By Zulaihat Aliyu Misau
Wattpad@zulaihatualiyumisau
Not Edited.......
Junaid da ashir ne suka je tarbarsu a airport.
Direct masaukin baki suka wuce, na Don Harris, Wanda ke kusa da apartment din su hayder.
Hubby, umma sulaim, Asiya, dakinsu daya. Sai Hajiya da Hajiya zuwaira, mahaifiyar Hafiz omer. Suma daki daya. Alhaji Munir nashi special suite. Abdul fattah da jabir kam apartment dinsu hayder suka sauka.
Wanka kowacce ta fara gabatarwa, kafin suka fito tafkeken falon da ke tsakiyar dakunan don ba ciki hakkinsa.
Nan suka samu duk kan samarin sun hadu. Nan fa aka fara gaisawa, da tambayar su hubby gajiyar hanya.
Congratulation suka musu na kammala karatu.
Ummu sulaim ta nufi dinning table din da aka Jere shi da dishes na abinci masu matukar kyau, da daukar ido. Bubbudewa ta fara, tana kallon abinda ke ciki. " wowhh!!!! Gaakiya kun burge, irin wannan delicious haka?" Ta fada tana Jan pleat signal tama hubby dake zaune a kusa da junaid suna hirar zuminci.
Tashi tayi ta nufi in da sulaim ta ke.
" na dauka zamu jira su Hajiya su fito, tukunna. Kin San cin abinci a tare nada dadi." Hubby ta fada tana kallon pleat din
Harararta ummu sulaim tayi " tab har yaushe ina ganin abinci a gabana, zan wani tsaya jira? Kin ko San kalan yunwar da nakeji?"
" maida wukar na manta, bakya juriyar yunwa."
Ummu sulaim ta kalli Asiya dake zaune. " Uhtee ."
Ajiyar zuciya Asiya taja tare da mikewa. Cikin sanyin jiki ta nufi wurin su hubby.
Murmushi hubby ta mata, tare da dafa kafadarta " take it easy sis," ita ma murmushin tayi cikin jin kunya. Ummu sulaim ta tabe baki " aiki ya ganki,"
Fitowar su Hajiya ya sa falon kara armashi, kowa ya dibi abinda zaici, suna ci, suna hira sama sama. Cike da farin ciki. Kowa ka kalla fuskar nan a sake.
Hayder na zaune kusa da Hajiya, kamar zai koma ciki, sai shagwaba yake kamar wani karamin yaro. Abincin ma pleat daya suke ci.
Bayan sun ci, sun sha, ko wanne ya koma dakinsu don su kwanta huta gajiya. Suka bar samarin a falon, suna shan hirar yaushe gamo.
" take this one." Ummu sulaim ta fada, tana mikawa hubby wani hadadden Dinki, atamfa mai combination din boil. Atamfar baki da touch din lemon green, voil din lemon green dinkin free half bubu da stret skirt. " wow amma kayan nan sunyi kyau sosai. Thanks " murmushi ummu sulaim tayi. " meye na wani godiya, yiwa kai Ne. Kin manta har yau bikici alayina na nysc ba." " gashi naci ai yanzu."
Shiryawa sukayi don tafiya wurin convocations. Ummu sulaim ma da asiya same kaya sukasa sai dai colours din is different. Lemon green Vail mai touch din white da stone masu haske hubby ta sa. Sai black shoe and bag. Na kamfanin cucchi new design.
" kuda ya kamata kuyi shigar larabawa, kuka je kuka zunbulo kaya haka kamar masu zuwa didan biki." Hajiya zuwaira ta fada tana murmushi tare da gyara zaman after dress dinta mai matukar kyau da tsada.
" mommy kowa yabar gida, gida ya barshi, na tabbata yawanci arebian dress zasu sa. Kinga mu munyi namu different don bama son mu saje dasu. We want something different than others, shiyasa." Rike baki Hajiya tayi da itama take sanye da nata alkabbar mai matukar kyau. " lallai fa!! Kishin kasa Abu ne mai kyau, ana ganinka aga alamar in da ka fito. Nigerian lady's kunyi kyau kam ba karya. Kowa ya ganku yaga cikakkun yan arewacin Nigeria. Masha Allah."
" a takaice dai Hajiya yaran nan na nufin mu bamu da kishin kasa fa kenan?"
Dariya sukayi gaba daya, ganin yadda take bin dressing dinta da kallo.
" Allah ba abunda muke nufi ba kenan. " Asiya ta fada tana rungume mahaifiyar tata tana dariya. Ta kara da cewa " don baki ga yadda kukayi kyau bane, wannan su daddy's suka ganku, kasa ganeku, zasuyi." Ummu sulaim tayi dariya " kina ga su Hajiya harda alkyabba kamar mai kai ziyara emir's place. "
Duka hubby ta kaiwa ummu sulaim. " Ku barsu su wala, don shigarsu tafi tamu daukar ido, anya baza mu canza ba?"
" yauwa yata, gaya musu dai. Ba maganar canzawa Nigerian lady's kumu tafi kawai kar kusa mu makara." Hajiya ta fada tana daukar hand bag dinta.
******************************************
A farfajiyan school din sukayi parking din land cruiser da suka zo da ita. Already wurin ya fara cika, a wurin da aka kayata shi da decoration. Suka nufa,. Gefen perent. sun samu har Alhaji Munir da Alhaji Jamil sun iso, sai mahaifin Hafiz Alhaji ayuba da yayansa Ahmad da suma suka samu isowa. Sai yayan alim da suke tare da jabir. Amir ma yasamu zuwa taya abokan nasa murnan gamawa.
Zamansu ba dadewa, bayan sun gama gaishe gaishe. Aka fara gudanar da programs din.
Bayan jawabin director na school din, da masu fada aji na kasar da suka samu halatta, aka Dan gudanar da entertainment, sannan aka fara rabon aword da gifts. Cikin su shidan nan ba Wanda bai karbi aword ba. Don hayder aword uku ya samu, da gifts 2. Sai Hafiz omer daya samu aword 2, sauran 1. Abun yama iyayensu dadi, musamman kyakyawan yabon da yaran suka samu, daga bakin malaman har da students.
Bayan an gama raba aword da gifts, sai entertainment, sannan aka nufi hall din da aka kawatashi don cin abinci. Tablets Ne da kowanne aka zagayeshi da kujeru sunsha decoration na cotton White da satin Amy green sai flowers da vases masu matukar kyau da daukar ido. Su Kansu plets da spoons din abin kallo Ne. Nan take aka fara serving din jamaa, bayan kowa ya samu wuri ya zauna, ga kida mai taushi da sanyaya rai na tashi, cikin low voice. already drinks kam waiters nata zagayawa dashi, ga maiso ya karba duk irin Wanda kake so. Ban dawanda ke kan tables din. Ga fresh fruit kala kala.
Anyi hotuna videos kowa, da iyayensa da friends dinsa. Sai teacher's da baa barsu a baya ba suma.
Asiya ta kalli ummu sulaim dake gefenta ta rada mata a kunne " waccan da take faman shishshigewa Yaya hayder wacece?" Kallonsu ummu sulaim tayi don itama tun dazu take son tambaya, bata samu damar da zata tambaya ba.
Rada mata tayi " I don't known, ina ga school mate din su ce."
" ki kalli fa irin kallon da take masa? Allah ba wani class mate. There is something "
" jealousy beby. I don't thing so. Amma koma menene we go figure it out, ammafa ta hadu."
Harara Asiya ta zuba mata. "Ina haduwa a nan? Abu a bushe." Dariya ummu sulaim tayi. Dan da nan Asiya ta toshe mata baki, tana kallon table din. Ganin duk hankalinsu baya Kansu, ta saki ajiyar zuciya.
Hubby kam gaba daya hankalinta baya Kansu. Tunanin yusuf da kewarsa ne taji nan take ya rufeta. Musamman yadda yaci burin akan graduation din nan. Amma Allah ya kaddara badashi zaa yi ba.
A hankali take diban chocolate cake din zuwa bakinta. Dariyar da taji ummu sulaim tayi yasa ta dago ta kallesu tare da kada kanta ta ci gaba da cin cake dinta. Don tasan maganar bata wuce ta hayder har tausayin asiya ta ke, ganin yadda ta kwallafa rai ga yaron da bai ma San tanayiba.
" da alama sis kinyi babban catch, " ummu sulaim ta fada tana kallon hubby tana dariya.
Tsaki hubby tayi, ta ci gaba da cin cake dinta.
Asiya ta kalli hubby tana murmushi " gaskiya kam, tunda muka zauna a wurin nan idon bawan Allah nan a kanki."
Hubby dai tana jinsu tayi musu banza. Don gaba daya haushi ma suka bata. Tun da suka shigo school din ta ankare da yadda ya sa mata ido,.
Daya daga cikin yanmatan da suke zaune table daya dasu hubby ce, ta kalli yar uwarta. " I can believed what my aye's so." Kallonta yar uwar tayi. Tare da bin inda yar uwar ke kallo tana nuna mata.
" suraj kangiwa." Dayar ta fada under her breath
Gaban hubby ne ya buga dam. Su ummu sulaim kam jin sunan suma suka bi wurin da kallo. Yana zaune a daya daga cikin kujerun table dinsu Alhaji Munir, suna magana.
Ummu sulaim ce ta tambaya " dama shine, kangiwan da naji ana magana?"
Dayar cikin farin ciki, da tun zamansu wurin, ba Wanda zai dauka tana faraa haka. " Ally son of M. Saad kangiwa, CEO of kangiwa group of companies. " ta fada tana kada ido.
" what bring him here." Dayar ta tambaya still idonta a kansa.
" me be yazo wurin daddy ne."
" I don't thing so, Sis."
Hamida da Sadiya (sady) yayan abokin Alhaji Jamil ne, Alhaji salis,. Shima yazo graduation din yaron sa , Imran tare dasu sady Wanda suke yayye ga Imran, da mahaifiyarsu Hajiya fatee.
Hamida da sady yan Hutu ne na karshe, don a England ma sukayi nasu degree din. Akwai jin kai da yanga ga son nuna su yayan wani ne. Shi yasa Sam tasu bata zo daya da hubby ba, don ta dade da saninsu, age mates ne, kuma duk shaanin da ake na family din Oregon suna zuwa, in dai suna kasar.
" is he your boyfriend? " Asiya ta tambayi sady
Rike baki sady tayi tana yamutsa baki. " no."
" fadi gaskiya sady? Don naga tun tuni kin kasa dauke idonki a kansa."
Kallon ummu sulaim sady tayi. Tare da yin murmushi. " he is my crush, amma yafi karfina."
" haba babbar yarinya irinki har akwai wani da namiji da zaifi karfinki? Kin ganki kuwa?" Dadine ya kama sady don tana son a yabata ko a kodata. Ta kalli ummu sulaim " thanks for compliment. Amma da gaske yafi karfina. In kinga manyan bebs dake dying a kan guy din nan zakiyi mamaki."
" ya hadu kam ba karya." Asiya ta fada tana kara kallonsa.
Hamida ta ce " ko kema kin kyasa ne?"
Ido Asiya ta zaro " ni ? Aa ko daya, nima ina da nawa crush din."
Duka dariya suka sa. Banda hubby dake zaune kamar bata wurin.
Hafiz omer da amir ne suka iso wurin. " hello sisters? How fah?" Hafiz ya fada yana murmushi, tare da Jan empty sit din daya rage ya zauna. " Anty hubby ba matsala ko?" Murmushi ta masa tare da kada kai.
Amir ya ce " muje mu dan kashe pictures da zaman da kuke a nan."
Asiya ce tai saurin mikewa " gaskiya kam, na gaji da zama wuri daya. Ina son in ga yanayin school din, don gaskiya ta burgeni ba kadan ba. Dana Sani nima nan nayi applying."
Tashi sukayi, hubby ce ta gayawa su Hajiya zasu Dan zaga cikin school din. Sannan suka fito.
A garden dake cike da dalibai da yanuwa anata kashe hoto, da videos. Masu hira nayi. A nan suka samu su hayder.
Kallon ummu sulaim Asiya tayi, tana nuna mata hayder da wannan yarinyar zaune suna magana kasa kasa. Sai annuri ke fita daga fuskar yarinyar da gani tana jin dadin yanayin.
" wa cece waccan yarinyar? Tun dazu nake ganinsu a tare." Ummu sulaim ta tambayi Hafiz omer
Murmushi yayi " Nasrin Nada Khan ke nan, da alama da ita zaayi." Kirjin Asiya ne yayi wani irin dokawa, cikin tashin hankali take kallon su amir " kamar Yaya?" Da kallo suka bita. Murmushi ta kakalo tana kokarin saita natsuwarta. Hannunta ummu sulaim ta kamo cikin nata.
" ita ce fist yarinyar da hayder ya saurara, har ya bata lokacinsa a kanta. Kinga ko ai ta ciri tuta. Na tabbata tana da matsayi ko Yaya ne a ransa. Yarinyar bata da laifi, tana kuma balain son shi." Amir ya fada yana murmushi
" he is lucky guy." Hafiz omer ya fada
Da ido ummu sulaim ta ma Asiya alamar tayi cooling down.
Hubby kam ta dade da isa wurinsu junaid. Cikin girma mawa suka kara gaisheta. Nan alim ya fara daukarsu pictures.
A hankali hayder da nasrin suka karaso in da su hubby suke. Sallama ya musu.
Cikin murmushinsa na miskilanci ya kalli ummu sulaim., sannan ya kalli nasrin dake binsu hubby da kallo. Jikinta yayi sanyi, ganin irin kallon fire da Asiya ke aiko mata, tun da suka nufo wurin.
" meet my sisters. Ummu sulaim, hamida, Sadiya sady and Asiya. " hannu ta mika musu suka gaisa tare da rungume juna. Duk da zuciyar Asiya na zafi haka ta daure.
Kallonsa ya kai kan hubby yana murmushin gefen baki " meet our Anty hubby. " hannu ta mika mata tare da rungume ta. Gaisuwa ta mata cike da nuna tausayawa.
" thanks. " hubby ta fada don ji tayi kamar mutuwar ta dawo mata sabo a lokacin.
" she is nasrin Nada khan. My friend " hayder ya fada yana kallonsu. Still da murmushi a fuskarsa.
Murmushi sukayi. " friend manya, kuji wani sabon salo." Hafiz ya fada yana murmushi
Harararsa hayder yayi. Nan suka ci gaba da daukar pictures dinsu.
" can I joined u." Gaba daya suka juyo ganin mai maganar
Sanye yake da blue Jean's, sai T-shirt White da lines din blue mai dogon hannu. Kafar sa sanye da White canvas mai kyau, sai agogon silver mai matukar daukar ido. Kanshi yasha gyara, ga farin glass a idonsa, Wanda ya karawa fuskarsa kyau da kwarjini. Ga wani kamshi mai dadi dake tashi a jikinsa.
Suraj m saad kangiwa.
Murmushi su Hafiz omer suka mayar masa " why not." Alim ya fada yana mika masa hannu.
Kirjin hubby banda bugawa ba abun da yake yi. Ita kam taga ta kanta.
Kin yadda su hada ido tayi, tana ji sunata gaishe shi. Shima cike da sakin fuska yake amsa musu, tare da musu congratulations.
" very sorry, I came un invited. It's you're sister fault she didn't Tell me. But I can Miss our brothers gradations." Suraj ya fada yana murmushi idonsa kafe a kan hubby da ta sunkuyar da kanta, ta gagara dagowa. Don haushi da nauyin kannen nata.
Gaba daya kallonsu ya koma kan hubby cike da mamaki.............
Jin yadda gaba daya ido a kanta, ba tare da ta kalli kowa ba ta juya ta nufi hall din dasu Hajiya suke.
Murmushi suraj yayi " 2min" ya fada tare da bin bayanta.
Hafiz ne ya kalli alim, da jikinsa ya gama sanyi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da zama a kujerar dake kusa dashi. Ummu sulaim da su hamida sai kallon kallo ake tsakaninsu.
"Habiba" jin ya kira sunanta, ta tabbatar biyota yayi kenan. Cikin fushi ta juyo tana jifanshi da wani riki taccen kallo. " don Allah wai maina tsare maka ne a rayuwa, kake son takuramin? Na Riga na gayama iya gaskiyata why can't u understand?"
Murmushi ya sake mata, tare da kashe mata ido daya. " I never understand you're language Habiba. The ally think I known is that I'm crazy about u. So duk yadda kike tunanin I will live u. Is not gonna happen. Ta Yaya zaki tafi da zuciyata sannan kiyi tsammanin zan iya barmiki ita?"
Kallon sa tayi for the fist time ta tsaya ta kalleshi da kyau, for some second. Ta kauda kanta gefe tana jin jina naci irin na wannan bawan Allah.
Maganar shi ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi.
" nasan kin San so? kin kuma San yadda bawa yakeji a duk lokacin da ya tsinci kansa a cikinsa. Ina rokonki don Allah ki bani dama mu fahimci juna. Wallahi ba yaudara tsakanina dake, face alkhairi. Har ga Allah ina sonki tsakani da Allah. Son da nake jin tamkar in baki ba zan iya ci gaba da rayuwa mai dadi ba, ke ce farin cikina. "
For the fist time taji ya Dan bata tausayi. Tabbas da baya sonta bazai ajiye dunbin ayyukansa ya tako tun daga Nigeria zuwa Cyprus kawai don ya ganta ba. Duk da bata da tabbas din ita ya biyo ko tashi ce ta kawoshi. Ajiyar zuciya ta yi kafin ta dago ta kalleshi, still idonsa na kanta yana sake mata murmushi mai kayatarwa.
Ganin Dan sassauci a kan fuskarta yasa shi jin wani kwarin gwuiwa da farin ciki, ya lullube zuciyarsa.
" baki tambayeni ya akayi nazo nan ba."
Tabe baki tayi, tana kallon gefe. Murmushi yayi, don hakan ba karamin burgeshi yayi ba." naje kankiya on Thursday, kamar yadda na miki alkawarin dawowa a satin. a ka cemin ranar kika tafi Kaduna, sorry nayi magana da Alhaji kawu ba tare da izininki ba. I'm happy yadda suka karbeni shida takwararki."
Da sauri ta dago tana kallon sa. Murmushi yayi tare da daga mata gira daya.
Ajiyar zuciya ta yi, don ta yadda da gaske yake nashi abun.
" tun jiya naso in taho, ayyuka sun sha karfina, amma fa still kina raina. Yau gari na wayewa ko mai ban jiraba. Burina in ga rabin raina, duk da nasan bazaayi farin ciki da ganin nawa ba."
Ganin bata da niyyar tankashi, shikuma zuwa lokacin muryarta kawai yake son ji, mai dadin sauraro da tsumashi. Kallonta yayi yaga yadda take wasa da yatsunta da sukasha bakin lalle. Tabbas akwai sassauci a tare da ita, alamar ta fara sakkowa, hakan yafi komai yi masa dadi.
Hubby kam yaki take da zuciyarta data kasu kashi uku. Daya na bata shawarar ta bashi dama ta gani, daya na mata shawarar ta tatamai rashin mutunci kawai yadda gobe ko mai sunanta ya gani bazai tsaya a kusa ba. Dayar na gargadinta data watsar da komai ta koma makaranta. Kamar zabin da Mommy hauwa ta bata, zuwantan nan.
Muryarsa taji ta daki dodon kunnenta
" yawan tunani bashi da kyau ga lafiya, ya kamata ki rage."
Ajiyar zuciya ta yi ta kalleshi " naji zan baka chance, amma banyi maka alkawarin komai ba."
Kallonta yayi for some time yana nazarinta. Murmushi yayi.
" ban gane baki min alkawarin komai ba?"
" just friends. " ta fada tana kallonsa.
Dariya yayi wadda ta kara masa kyau
" na yadda friends, but ki Sani zata iya riki dewa."
Kallon sa tayi " kamar Yaya riki dewa?
Shafa kansa yayi yana murmushin gefen baki " forget it. Yanzu dai ni dake are friends right? "
Kai ta daga masa.
" good." ya fada yana murmushi
"Muje nima a kashe pictures din dani ko?"
Harararsa ta yi.
Marai raice fiska yayi " don't forget I'm you're friend, Kinga ba laifi ki dauki photo da friend dinki."
" karka manta akwai ban banci da friend mace, da friend namiji. So stay in your limit. "
" ban Sani ba, amma ya kamata mu zauna ki jeromin differences din don in kiyaye."
Ganin tayi gaba, yasa shi binta. A tare suka jero zuwa wurinsu ummu sulaim da lokacin sun babbaje a kan grass carpet dake malale a garden din suna kwasar hira.
Gefen ummu sulaim ta nema ta zauna. Shikuma jabir ne ya tashi ya mishi alamar ya zauna. Sannan suka gaisa, don dazu basa wurin shida Abdul Karim, Ahmad.
Gaba daya hubby a tsarge take ganin irin kallon da kowa ke binta tashi. Ummu sulaim ce ta rada mata " kin kyauta" dagowa tayi ta kalleta da ido ta mata alamar " sorry I have no idea. " su sady kam haushin hubby ne ya kara cikata. Sai Kallonta take tana son ganin abinda tafi sauran mata da tayi mata zarra a rayuwa. Duk iya Kallonta ta kasa gano makusarta. Illa kawai ta ce, bata da wayewa a nata fassarar. Don da wuya kaga hubby cikin kaya masu nuna siffar mutun. Dressing dinta is decent.
Shikam ya saki jikinsa da samarin sai hirarsu suke kwasa. Duk wani movement na hubby a kan idonsa.
Sai 2oclock sannan taro ya watse kowa ya fara kama hanyar masaukinsa, masu tafiya a ranar sun kama hanyarsu. Su hubby sun so dawowa ranar but ba dama saboda walima da sheikh dawood al- maisani ya shiryawa su hayder na haddar alqurani da yayi a wurin sa, shida wasu matasa su biyar sai mata 2.
Suraj ne ya kalli samarin da suka rakoshi har mota, bayan su hubby sun wuce masauki. " Ku mai ya hanaku joining din hayder?"
Murmushi sukayi junaid na shafa kai. " nida shine dama mukayi joining banfi sati ba na gudu."
Dariya su Hafiz suka sa tunowa da drama din.
" as how" suraj ya tambaya still da murmushi a kan fuskarsa. Don yaran sun matukar burgeshi.
" kana ji ko? Fist day da mukaje tun a fatiha an min gyaran tajweed yafi goma, a fatiha kawai, duk iya dagewata ranar ban samu wuce fatiha ba. Shima hayder yasha gyara. Duk kanmu a fatiha ranar muka kare. The next 3day hayder ya wuce ikhlas da kyar ni kuma ina nan a fatiha. In takaita maka 5 days nayi a fatiha, sannan na tafi ikhlas, lokacin hayder yana suratul nas. 1days ina ikhlas ranar na dauka zan shiga sabuwar sura amma Dan malaminka haka yayita dawo dani. In takaita ma gani nayi bazan iya ba kwana 7 a fatiha da ikhlas ina kuma mun fara shiga manyan sura. Malamin Dan gani kashenin tajweed ne, ko ja daya ka manta sai ka faro daga farko. Ai tun daga nan ban sake komawa ba." Dariya sosai suke masa. Hayder na daga gefe yana danna waya.
" daka daure ai, da komai ya wuce." Suraj ya fada yana dariya
" ina wane mutun. Sauka biyu fa mukayi kafin mu taho nan. Waye besan karatu irin na ibn kayyim memorial college ba.? Munje gasa yafi a kirga, muna winning.Amma dan malaminka kamar ya samu fresh meat."
" don't insults my sheikh. " hayder ya fada yana hararar junaid.
Murmushi junaid yayi, " sorry na manta kana wurin ai.?"
Card hayder ya mikawa suraj 5oclck tare da masa sallama ya shige mota, don a gajiye yake, Allah Allah yake su je ya huta kafin su wuce gidan sheikh.
Sallama sukawa suraj tare da godiya. Don wasu manyan gifts ne da akayi rapping dinsu, guda six ya basu, kowa da sunanshi a jiki.
*******************
"Yanzu kiyi irin wannan catch din amma ki kasa sanarmin gaskiya banji dadi ba ko kadan" ummu sulaim ta fada tana shafa lotion,.
Tsaki hubby tayi " me kike son in gaya miki."
" sorry na manta, na Yaya Yusuf ma saida magana tayi karfi mukaji. Amma dai kin San mu ba haka muke miki ba. Its un fair. Yanzu da wani mugun halinshi su sady suke fada da ya zakiji."
Kafada ta makale tare da tabe baki " so what. Ke baki San kalan nacin mutumin nan bane, ba wai son shi nake ba, balle in damu don an fadi mugun halinsa." Nan ta kwashe labari Kaf ta fada musu. Baki suka rike suna mamaki.
" kun masifar dacewa, sai kin ganku lokacin da kuka jero tare, don har picture na kashe muku baku Sani ba." Asiya ta fada yana murmushi tare da nunawa ummu sulaim pic din.
" its true. Gaskiya yana sonki sosai, kar ki bari ya kufce miki hubby, zamanin yanzu ka samu Wanda zai soka haka yana da wuya. You're very luky, ji yadda Yaya Yusuf ya soki, yanzu kuma ga suraj. Ki gode Allah don ba kowa ke sanun hakan ba."
Asiya ce ta kara da " gaskiya kam."
Banza dasu hubby tayi ta ci gaba da shiryawarta. Don har lokacin bata jin natsuwa da lamarin ta da suraj.
Hajiya ce ta shigo. Wuri ta samu ta zauna tana kallon hubby. " Ummi wane labari nake ji ne?" Kallon Hajiya hubby tayi cikin rashin fahimta. ummu sulaim tayi murmushi tana kallon hubby " na biki da muka kusa sha mana"
Tsaki hubby tayi ta harareta. Asiya ce ta korowa Hajiya bayani dalla dalla kamar yadda hubby ta gaya musu.
Ajiyar zuciya Hajiya tayi " ai ni hankalina bai kwanta bane, amma ba komai zamu ci gaba da addua. Allah ya zaba miki mafi alkhairi. Ki ci gaba da addua."
" in sha Allah." Ta fada kanta a kasa.
Ajiyar zuciya tayi bayan Hajiya ta fita.
Dariya su Asiya suka sa baki daya suna tsokanarta.
****"**************

Hayder
"
Agric chiken" hubby ta fada tana murmushi.
Kallon ta ummu sulaim dake kusa da ita tayi, ta kalli su junaid da suka sha jallabiyyoyi da nadi irin na larabawa.
Murmushi tayi " Allah girma ba wuya, ni kaina bana gajiya da kallon yaran nan ina mamakin girmansu. Musamman hayder da junaid. Har gara junaid shi bashi da jiki, amma dubi hayder wa ze ce 19 going to 20 years.
********************
Walima ta kayatar sosai. Hajiya tasha kukan farin ciki, hatta su Alhaji Jamil dasu hubby sai da sukai hawayen dadi. Jin yadda haidar ke kwararo karatun alkurani cikin kiraar kalun. Haka su Hafiz
Bakajin komai sai kabbara, duk inda aka ja masa in ya amshe, sai yakai inda zaa ja wata, haka tambayoyi kan tajweed da tafsir, Abin masha Allah. Ya samu kyaututtuka da dama, bayan an kammala akaci aka sha sannan kowa ya kama gabansa.
Rungume shi Hajiya tayi tana kuka, shima hawayen yake fitarwa na dadi.
Burin hajiyarsa ke nan, ya samu yalwataccen ilmin addini. Kullun taga yara a wurin gasar alkurani takance ina ma wata ran inga hayder dina haka. Yana secondary school ansha zabansa ya wakilci school dinsu, hakan ya kara sashi son zurfafa ilmin addini, alkawari ne ya daukarwa kansa duk wuya duk runtsi, yadda ya dage neman ilmin zamani, haka zai dage a kan ilmin addini koma, fiye. Shiyasa duk tsaurin sheikh ya daure ya cige batare da kosawaba don ya cimma burinsa. Kuma alhamdulillah ya samu ya taka mataki na farko da yake fata a rayuwarsa.
Albarka kam yau hayder ya sha a wurin su Alhaji Jamil. Nan take ya tura ma yan uwansa da mahaifinsu.
Alhaji Jamal na masallaci sallar magrib yaji shigowar sako wayarsa. Bayan ya kammala tasbihi da azkhar ya fito da wayar don ya duba.
Gaba daya kiraar hayder ta fara tashi a cikin wayar, Wanda ya jawo hankalin liman, da sauran mamu da suka rage a masallacin. Hawayen dadi Alhaji Jamal ya fara ya dago yana kallon liman da ya masa zuru da ido. Wayar ya fara nuna masa, cikin rawar murya " Aliyu, Aliyu hayder. " liman da mamu suka zagaye Alhaji Jamal suna kallon hayder dake zubo kiraa cikin kwarewa da dadin murya. " Allahu Akbar suka fara fada. Har bidion ya kare. Alhaji Jamal na ta sharar kwalla. Murna suka dinga tayashi tare da fatan Allah yasa albarka a karatun, yasa ya zama mai anfani ga alummar musulmi. Nan liman ya fara kwararo falalar mahaddacin qurani da darajarsa a wurin Allah. Gaba daya imani ya kara cika zukatansu.
Hakika a cikin zuriarka a samu mahaddacin qurani ko da guda daya ne, ba karamin falala bace ga wannan zuri'a.
Haka ta faru da Alhaji babba da Hajiya Aisha. Suna tare a babban falo dasu Ahmad da iyalansa sun kawo musu ziyara. Kamar Alhaji babba bazai daga wayarba ganin sunan Jamil yasa ya duba.
Duk Kansu sunyi farin ciki matuka. Hajiya Aisha kam har da kukanta ita ma.
****************
Zaune suke a babban falon masaukinsu. Gifts din su hayder ne baje a falon, sai manyan jakun kuna da su hubby ke arranging din gift's din a ciki, bayan sun ciresu a kwalayensu. Saboda in sunce zasu tafi dasu haka zasuyi accupying space da yawa.
Wani hadadden box hubby ta daga, ya matukar burgeta yadda akayi rapping dinsa. Da ita kanta rapping sheet din. " wow!!!" Asiya ta fada tana karba daga hannun hubby.
Sunan da Asiya ta gani an rubuta yasa jikinta daukar rawa, cike da son ganin abinda ke cikin rapper ta fara yagawa cikin sauri, da kaguwa ido ta zaro... Gaba daya su hubby dake Kallonta cike da mamakin abunda ya fusata ta lokaci daya su kabi box din da kallo.
Zaro wani hadadden box din turare da aka rubuta SHUMUKH ( The sprite of Dubai )da manyan baki sa a Kansan an rubuta ( Deserving The Highest)

Budewa tayi ta zaro kwalbar yar madai dai ciya mai kyau. Ga wani kamshin dadi dake tashi tun bata fesa ba

Tsaki hubby tayi, tana juya turaren a hannunta. " yanzu duk girman abun nan, abunda ke ciki kenan?"
" wannan mayyar yarinyar ce ta bashi, nasrin take ko wace?" Asiya ta fada cikin jin haushi, tana tabe baki.
Dariya suka mata " nama dauka wani Abu ne, yadda naga kin haukace lokaci daya, kina son ganin abunda ke ciki." Ummu sulaim ta fada still tana dariya.
Hafiz ne ya ankare da abunda suke yi.
Kwalbar ya amsa daga hannun ummu sulaim yana kallo. Kallon su junaid yayi " guys look hare." Gaba daya suka juyo suna kallonsa
" oh my world. " junaid ya taso da sauri ya amshi turaren yana juyashi a hannunsa cike da mamaki. Rapper din da box suka dauka suka nufi wurin sauran guys din.
" amma gaskiya yarinyar nan tana ji dakai. Kasan nawa kudin turaren nan?"
Hafiz omer ya fada yana kallon hayder da duk abinda suke ko a jikinsa. Laptop dinsa ma yake daddannawa. Tabe baki yayi ya kalli amir da turaren ke hannunsa yana fesawa ya ci gaba da aikinsa.
" nawa? Don gaskiya akwai kamshi ba karya ko nawa ne yaci kudinsa. Jabir ya karba yana kallo
" 3,571 USD."
" What?" Suka fada a tare.
Dariya Hafiz omer yayi " da gaske nake yi. Ranar ba na baku labarin turaren da huzaifa ya siyo a Dubai ba? Har nake cewa zan yi oder don yamin dadi sosai. To shine wannan. Last month akayi launch dinsa. It's take them 3 years to create it. That why there called it deserving the highest. "
" gaskiya yaci sunansa. Amma ban iya cire makudan kudi haka in sai just one perfume!!" Amir ya fada yana karewa turaren kallo
Junaid yayi murmushi " tasan mutumin nata kan son kamshi, turaren komai tsadarsa zai saya in har ya masa. Hakan na nuna ta gama karantar mutumin nata. Don in kanason burge haider bashi turare ammafa designer mai dan banzan kamshi."
Harararsa hayder yayi " what do you mean?"
" nasan kaji dadin wannan kyautar. Kuma dama burinta kenan kaji dadi. Right? "
" of course. " hayder ya fada yana kallon junaid dake masa murmushi
Hafiz ne ya dan Sosa kai " da har ina cewa na samu turare?"
" in kana ciki, mu buga oder kawai. Tunda bamu da wadda zata bamu." Hafiz omer ya fada
Asiya dake gefe ta cika tayi fam, ganin yadda suketa koda turaren. Ta kallesu tana tabe baki " banda abinku meye abun burgewa a wannan turaren da har za a shekara uku wurin kirkirarsa? Ni wannan ko kyauta ban so balle insa kudina in siya."
Gaba daya kallonta suke cike da mamakin maganarta. Alim ne yayi dariya don sun dade da harbo jirginta. " haba kanwarmu kema kinsan kin fada ne kawai, amma ba Wanda zai ji kamshin turaren nan ko ya ganshi, ya ce bai burge shiba."
Junaid shima murmushi yayi " anya kanwarmu? Kodai kishi kike?"
Baki ta tura " Allah ya kiyaye in tsaya kishi da wannan slender din." Gaba daya dariya suka kwashe dashi
Hafiz omer ne ya harareta, kauda kanta tayi. Ido hudu sukayi da hayder dake aika mata da wani irin kallo mai kamada gargadi gargadi, harara harara. Zuciyarta ne ta fara rawa, don tunda suka zo banda gaisuwa ba abun da ya hadasu, ko kallon arziki bata samu ba. Da sauri ta dauke idonta don bazata jure kallon fire da yake aiko mata ba. Kwafa yayi kadan ya ci gaba da abinda yake yi.
Jabir ne ya canza akalar hirar. Nanfa aka koma musun kwallo, su hubby suka ci gaba da parking din gift din. Asiya kam jikinta yayi sanyi, don haka tashi tayi ta nufi room din su Hajiya.
Abdul fatta ne ya shigo, kusa da hayder yama kansa mazauni. " wash!!!! " sannu suka fara masa, tare da gaisuwa. Hubby ya kalla " suraj na jiranki a waje, nayi nayi ya shigo yaki,." " OK" ta fada tana ci gaba da abin da takeyi.
" na manta munada uwa a bakin murhu, kuka Samu wahala. Allah yasa muna shiga airport muka hadu da suraj. Yanzu haka tare da maaikatan company dinsu muke, zasuyi packaging din sauran kayan."
Hafiz omer ne ya cabe da " haka nefa!!."
Junaid ne ya fita ya shigo dasu. " amma dai kin San kin ajiye mutun a waje ko?"
Harararta hubby tayi " na ajiyeshi ko ya ajiye kansa? Ko gayyatoshi nayi?"
" ba kyau wulakanci, ki tashi kije, kar ya gaji da jira."
" so what? " hubby ta fada
Tashi ummu sulaim tayi, " muje in rakaki to."
Ganin hankulan samarin ya fara kaiwa Kansu, duk da a hankali suke maganar yadda baza suji ba, yasa hubby mikewa.
" bari in tambayi Hajiya tukunna.?"
Baki ummu sulaim ta rike " to fah!!!"
Ido hubby ta zaro mata tare da daga gira daya. " what? Ko kina tunanin zan iya fita ne ba tare da sanin taba."
" no wai gani nayi nan ne, ba wani dadewa zakiyi ba. Its almost late." Ummu sulaim ta fada tana duba agogo.
" dozen matter."
Bayan ta gayawa Hajiya ta basu izni tare da jaddada mata karta Dade.
Zaman gyalenta ta gyara, Suka fito. Suna zuwa dai dai corridor din wurin ummu sulaim ta juya abinta. Ko kafin hubby ta bude baki, har ta shige ciki da dan gudunta. Baki hubby ta sake tana kallonta, kafin tayi kwafa. " zamu hadu ne."
Juyawa tayi tana scanning din wurin. Motar Kangiwa air ways. Ta fara hangowa, daga gefe ta hangoshi tsaye jikin wata farar mota kirar Mitsubishi
A hankali cikin takunta mai daukar ido, da natsuwa ta nufi inda yake. Tun fitowarta idonsa a kanta, ya kasa dauke idonsa.
Sai yau ya kara kare mata kallo sosai. A cikin hasken fitulun da suka kawata wurin, ga kamshin furanni.
Sanye take da material purple, yellow, blue, brawn. Sai mayafi purple Wanda har kana iya hango kitsonta back and front, daya kara fito da kyan fuskarta sosai. This is the first time da ya ganta ba zunbulelen hijab. Duk da yanzu dinma rigar bubu ce, wadatacciya har kasa, don ko takalminta bai iya gani, Sai dan tsininsa da yake hangowa.
Dressing din ya matukar burgeshi, don ya bashi damar ganin daya daga cikin abunda yake fatan matarsa ta sunna ta kasance tana dashi. Gashinta da yake iya hango tudunsa ta bayan gyalen yayi kamar a cuci.
Kanta a kasa, amma tana jin yadda idonsa yake a kanta. Gyara gyaleta tayi, ta kara jawoshi da kyau, yadda zai rufe gashinta.

Sallama ta masa, cike da nutsuwa.
Murmushi ya sake mata " waalaikumus salam, barka da fitowa gimbiyar mata."
" ya gajiyarka." Ta fada a hankali, kamar bata so.
" alhamdulillah, mu kam ai mun saba, so ba wata gajiya, wannan Sai Ku mata."
Shiru tayi tana wasa da yatsunta. She is uncomfortable, don ko yan matancinta bata yi wani tsayawa da samari ba. Zata iya cewa Yusuf ne kawai. Shidin ma ba ko yaushe ba. Don zata iya kirga zancen da suka yi alone, after all she known him. Wannan kuwa is total stranger.
Tsayuwarsa ya gyara fuskarsa cike da annuri " nazo miki sallama ne, zan wuce tomorrow morning. Yaushe zaki wuce kankiya in kin koma?"
Shiru tayi tana dan nazari " one week my be."
" OK. In that case ina ga zanzo kafin ki koma, don nima yanzu haka Italy zan wuce. Ina sa ran dawowa nan da 3days."
Kallonshi tayi kafin ta kauda idonta gefe.
" OK. Allah ya kiyaye hanya."
Yaji dadi sosai, daya kasa boyuwa a kan fuskarsa. "Amen na gode,."
Shiru sukayi na dan lokaci. Ita ta kauda shirun. " zan shiga ciki."
" OK. Sai nazo din."
Harta juya tadan dawo " mun gode sosai da hidima." Ta juya ba tare da taji mai zai ce ba.
Yana tsaye har ta shige ciki,. Murmushi yayi yana shafa sumar kansa. Allah yayi halitta a nan. Komai nata mai kyau. Ya fada a ransa.
Lokacin ne maaikatan nasu ke kokarin saka manyan jakun kunan a bayan van din. Su hayder ne suka karasa wurinshi don su kara masa godiya.
********************
Hajiya da ummu sulaim jirgin Lebanon suka hau zuwa Oregon. Don dubo ummu kulsum dake fama da laulayin ciki, shiya hanata zuwa graduation duk da suna kusa. So time din flight din su da safe 7:30. Su Hajiya Balkisu, Asiya, Hafiz omer, kuma jirgin Lego's. 1:15. Alhaji munir, jabir, junaid, haider, alim, da amir. Direct jirgin Kaduna 4:00. Alhaji Jamil da ashir sunbi jirgin abuja tun last night.
Wuraren tarihi su junaid suka kai hubby don tunda su ummu sulaim suka tafi, taji garin ya fita a ranta gaba daya.
Golden lake sukayi branching. In da kowa yasai abinda yake so na ciye ciye suka nemi wuri suka zauna suna ci suna hira, duk labarin school ne, da friends dinsu.
Hayder kam gefe daya ya samu ya zauna yana kallon jamaar dake shige da fice. Yau shigar ash and black yayi yayi kyau sosai.

Hubby ta kalleshi tana tabe baki. " a karatun harda miskilanci ake kara koyar daku ko?"
Kallon hayder suke yi da ke waya hankali kwance.
Junaid yayi murmushi " ina kika taba jin an koyawa mutun miskilanci? Dama dai miskilin ne."
" naga abin ya kara shaharane, na Sani ko harda shi ya koya."
Dariya sukayi
Amir yace "gaskiyarki Anty miskilanci ya karu, ni kaina shaida ne."
Murya hubby ta dan daga yadda zai jiyota " agric chicken. " ya jita sarai ya mata banza, bai ma nuna ko alamar yasan dashi take ba. " agric chicken " ta kara daga murya.
Haushine ya kama hayder musamman jin dariyarsu amir. Don ya tsani sunan.
" arage dai a sami ta gobe, kowa na hira da dan uwansa, don mugun hali ka koma gefe."
Ko kallon ta bai yi ba. Ya ci gaba da danna wayarsa.
" Allah ya shiryi mai bakin hali."
" amin" su junaid suka fada suna dariya.
" Matar hayder ta banu, wallahi har tausayinta nake." Alim ya fada
Tabe baki hubby ta yi " ita taga zata iya ai."
" haka ne kam, tunda yanzu ma yan matan duk da sanin halin nasa suke kara manne masa." Alim ya fada
Dariya junaid yayi " kasan mata da yawa na son muskilayen maza."
" in ji wah?" Hubby ta fada tana tsareshi da ido.
" kema fa kina ciki, naga Yaya Yusuf ma ai miskilin ne,." Junaid ya fada
Harararsa tayi " in kana maganarka karka kuskira ka tsomani ciki."
" afuwan."
" in kun gama shirmen Ku tashi mu tafi." Hayder ya fada yana yin gaba
Agogo junaid ya duba past 3. Da sauri suka mike suka nufi mota. Don isa airport don sunyi dama da Alhaji Munir da jabir zasu hadu a can.
" waye yake shirmen? Allah ka shiga hankalinka, don kaga kayi tsawon kafa, bashi zai baka lasisin yimin rashin kunya ba."
Juyowa yayi ya kalleta, ya juya ya ci gaba da tafiyarsa. " mai hali bai fasa halinsa." Ya fada a ransa
Haushine ya kara kama hubby. Ta yi tsaki
*******************
Kallon sit din tayi, ta kalleshi. " dawo nan! Ban son sit din kusa da window" kallonta yayi ya kalli sit din, Ya kauda kanshi.
" agric chicken!! Da kaifa nake magana, ka koma can sit din."
Air piece ya sa a kinnensa tare da kunna kiraa ya kyara belt dinsa da zamansa da kyau.
Haushi ya kuma hubby, ji take kamar ta kifa masa mari, ta rasa yadda akayi number din sit din su yazo a hargitse. su junaid ma kowa sit dinsa da ban dana juna, ita da hayder ne kawai sit dinsu ya zo daya.
Tsaki tayi, ta gyara yadda zata wuce ciki, bata son window sit. Koda za su mata burking ta gayawa jabir amma see how she end of. Kafarsa ta take da karfinta kafin ta wuce.
Ya jita sarai, don yaji zafi sosai, amma ko motsi be yi ba, balle tasa ran zai tankata.
Wayarsa ce tayi kara, a yan gace ya duba, tare da answering din call din. Hatta hubby dake kusa bata iya jin me yake fada, saboda yadda yake maganar, cikin Jan aji da natsuwa. Sake baki hubby tayi tana kallon ikon Allah.
Kallon ta yayi, tare da mika mata wayar. Wayar tabi da kallo, kafin ta amsa. Nasrin ce ke son mata sallama, don basu hadu ba a wurin walima, saboda tana jin kunyar Hajiya so bata xoba.
Jininsu ya hadu, da hubby duk da ba wani dadewa sukayi suna magana ba. She respect her, don tasan matsayin Yusuf a wurin hayder. Haka tana jin labarin hubby sosai a bakin su Hafiz. Gani daya ta mata taji ta kwanta mata a rai.
Hira sosai suka yi, har sai da akayi annausing cewa jirgi zai tashi, kowa ya kashe wayarsa. Sannan sukayi sallama ta mika masa phone din.
" she is nice girl. In baka shawara?" Ta fada tana kafeshi da ido.
Kallonta yayi cikin muryarsa mai kama da anmasa dole " ina jinki?"
Tabe baki ta yi tana dan rainin sense a gasan ranta.
" mai zai hana ka nemi Asiya. She is the perfect choice for u. Kun matukar dacewa."
Kallonta yake, girarshi ya dan Sosa ganin takai karshe.
" thanks for the advice, keep it to your self, I don't need it."
Harararsa tayi " wai kai me yasa baa abin arziki da kai ne?" Tsaki ta yi ta gyara zamanta. Tunawa tayi da assignment dinta na islamiyy da ta taho dashi don tayi, amma bata samu time ba. So yanzu da zaman banza bari ta dauko tayi, ko ta rage takaicin hayder. Tausayin Asiya take. Yarinyar na matukar sonshi..........
[03/03, 12:07] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA