Part 16
Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 21 min read
Written By Zulaihat Aliyu Misau
Wattpad@zulaihatualiyumisau
Not Edited.......
A hankali ta fara bude idonta, da sauri ta mike, tana dauke da adduar tashi bacci a harshenta, da labbanta. Ganin gari har ya fara haske, toilet ta nufa da saurinta.
Bayan ta idar da sallah, ta zauna tana azhkar, tare da adduoin da bata samu ta tashi cikin dare kamar yadda ta saba ba.
Kanta ta daura a jikin gadon ta fada duniyar tunanin. Bata san ta ina zata fara wannan zamanba. Abu daya ta Sani, bazata taba yadda wani abu ya shiga tsakaninta da wannan yaron ba. yan zuma ya ta kare da rainin hankalinsa, balle yaga gadon baccinta. After all he is her younger brother kuma brother din Yusuf. Ko da yake tasan ko giyar wake yasha shima ba zai tunkareta da wannan ba.
Murmushi tayi, tama tsaya tana bata hawayenta a banza. Zaman gidan nan bai sake da tana zama da brother dinta bane, sannan ta huta da damuwar masu cewa suna sonta, da kuma su gwaggo dake son tayi aure. Yanzu kunnenta shiru. Shi kuma zuwa gaba yana da right da zai yi aurensa kamar kowa, don ita dama ba auren bane a gabanta. Zama dashi tamkar Katanga ce da zata bata kariya ta fanni biyu. Masu sonta da iyayenta. Murmushi ta kara yi, " I have my freedom, I will do what I want. "
Hayder kam yana dawowa masallaci, muraja'a ya zauna yi, bayan ya kammala azkhar. Sai to 8 tukun ya nufi toilet yayi wanka, ya shirya cikin wasu kananan kaya shirt da trouser masu kyau da asalin tsada. Ya gyara sumar kansa, mai matukar laushi da daukar ido. Kamshi kam baa magana, kamar wanda ya fito daga kamfanin turare.
Hajiya ya kira, suka gaisa, tana tambayarsa hubby, ya amsa da lafiyarta kalau, nasiha ta kara masa sosai, sannan sukayi sallama. Alhaji Jamal ya kira suka gaisa. Sannan ya nufi kitchen don samawa cikinsa abun da zai ci.
Gidan shiru bakajin karar komai, sai na naurar sanyaya daki, dake tashi. kamshin turaren wuta, da sanyin ac dake bada wani kamshi, mai sanyaya rai. Ya shaka yana lumshe ido. Don kamshin ya masa dadi.
Jin gidan shiru, ya tabbatar bata tashi ba, ruwa ya sa a kettle. Ledojin daya shigo dasu jiya ya dauko, kidney kebab ya juye a plate ya sa a microwave. Jin gina yayi da cabinet din kitchen din yana bin kitchen din da kallo, ya masa kyau matuka. Ina ma a ce shida nasrin ne da wannan hadadden gidan, sannan suna a matsayin maaurata. Gabansa ne ya fadi, tunowa da nasrin. Ya zataji in ta samu labarin aurensa? Yasan ba karamin tashin hankali zaayi da ita ba. Don yarinyar tana sonsa matuka, shima zuwa yanzu, ya tabbatar yana jin wani abu dangane da yarinyar.
Ajiyar zuciya ya sauke, abinda ke kara daga masa hankali, wane irin zama zasuyi shida hubby. Baya sonta, ya tabbatar itama haka, kawai biyayya ce, da rashin madafa. Zai bata lokaci yaga iya gudun ruwanta. Ta hakane, zai gane matsayin aurensu a gareta.
Karan kettle ne ya dawo dashi daga dogon tunanin daya tafi. Cup ya dauko ya hada black tea. French bread ya dakko yayi slicing dinsa, ya shafa butter, jerasu yayi a bread toster. Ya dauko trey kenan da zai jera break fast dinsa, yaji wani kamshi ya doki hancinsa. Duk da turarensa daya gauraye kitchen din bai hanashi jin kamshin daddadan turarenta ba.
A bakin kofa tayi burki. Tana sanye da doguwar riga, ta material da mayafinsa. Ba ko pawder a fuskarta, amma tayi kyau sosai, sai glowing fatarnan keyi. " nan dama akafi auki." Ta fada under her breath
Ya jita, sarai ya share. Sai da ya jera komai kan trey din, kafin ya dauka zai fito.
Ganin zai wuceta ba alamar zai kulata. Tayi murmushi cikin tsokana " agric chicken ba gaisuwa." Kallon sama da kasa ya mata ya wuce abinsa.
Murmushi tayi " dani kake magana, a sannu zan gyarama zama yaro." Ta wuce cikin kitchen din, don wata mahaukaciyar yunwa take ji. Tea ta hada mai kauri, ta zuba cake a plate ta haura falonta dake sama.
" good for u, Ashe ka gane, zamane na kowa yayi ta kansa." Ta fada tana murmushi
"*******************
Ranar gaba daya cikin baki, yan ganin daki, hubby tayi shi. Sai yamma lis ta samu kanta. Hayder kam tun haduwarsu a kitchen da safe basu sake haduwa ba. Hakan ba karamin dadi ya karawa hubby ba.
Next day yan secondary school dinsu suka kawo musu ziyara, Nan ma tasha hidima. Sai dai taji dadin still yadda suka nuna mata respect. Ta dauka aurenta da hayder zai sa su kara rainata, sai taga sabanin haka. Mazan na tare da hayder a main falo. Matan suna falonta na kasa. Taji dadin wannan ziyara, don da yawansu tunda aka gama basu sake haduwa ba.
Sai to 6pm sannan suka tafi. Sai da ta kyara ko ina tsaf tukunna, ta nufi bedroom din ta, wanka tayi, ta shirya cikin English Ware's Riga da skirt masu matukar kyau. Sun zauna a jikinta tsaf. Wayarta ta dauko tana son kiran gwaggo. Kusan 20miss calls ta gani, abin haushin tana kokarin kira, ta tuna, dazu suna waya da yusra kudinta ya kare. Datanta ta kunna don siyan kati true bank, but network is bad.
Hijabinta ta zunbula ta Zari 2k a bag dinta ta nufi falo. Direct falon hayder ta nufa, yana kashin gide a 3 sitter ya rufe idonsa kamar mai bacci.
Kamshin turarenta ya masa sallama. Bai ko motsa ba balle, ya nuna yaji shigowarta. Tunda ba sallama tayi masa ba.
" agric chicken. " ta fada tana kallonsa, ko motsi be yi ba.
Bubbuga kujerar tayi kadan, ta kara daga murya "agric chicken." Tsaki tayi ganin ya mata banza buga kujerar tayi da karfi, tare da ware murya " agric chicken, kana jina fah!!!."
Idonsa ya bude a hankali, ya sauke su a kanta. " kanaji ina maka magana kamin banza, don wulakanci." Ta fada tana harararsa.
Agogonsa ya kalla 6:35. Lokacin sallar magrib ya gabato. Mikewa yayi ya zauna da kyau. Ganin bashi da niyyar mata magana, haushi ya kara kamata. Sai aika masa da uwar harara take. Ta mika masa kudin " recharge card nake son ka siyo min, mtn na 1500, airtel na 500." Kallonta yayi ya kalli kudin da take mika masa.
" karba mana." Ta fada cikin kaguwa, da jin haushi.
Mikewa yayi, har zai fita, ya dawo, ya karbi kudin, a aljihun gaban shirt dinsa ya saka ya fita.
Da harara ta rakashi. Ganin ya nufi sama yasa ta fito da sauri, " agric chicken ina kuma zaka? Yanzufa zanyi anfani dashi, kake shigewa ciki."
Ko waigota be yiba, ya haye abinsa. " oh!!! Allah," ta fada tana dafe goshi.
Sai da ya dauro alwala, ta gabanta ya wuce, tana kara jaddada masa, yanzufa take son anfani dashi. Kwafa yayi, bayan ya fita, tare da busar da iskar bakinsa, don ransa a bace yake, da yabi ta zuciya ba abinda zai hanasa mangareta, watan ita a matsayin Senior tazo ke nan, She want to boss him rawn. "A sannu zanyi maganinki" wata zuciyarsa ta fada.
Har akayi sallar ishai, ba hayder ba alamarsa. Hubby takaici kamar tayi yaya. Don ta samu ma wasu daga cikin wanda suka mata miss calls, sun sake kiranta.
Tana son magana da gwaggo. Still rashin kyan network ya hanata, samun damar siyan kati ta waya.
Hayder bai shigo gidan ba sai 9:24 lokacin har ta gaji da jira, ta kulle kofarta. Zagi kam yashashi. Don ranta ya baci sosai.
Kota kanta hayder be biba, shima shirin bacci yayi, yayi kwanciyarsa.
*****************
Hannu ta mika masa " ina kudina?" Black tea dinsa ya ci gaba da sipping
" agric chicken, da gaske kazo da rainin hankali, taya zan aike ka, baka siyo, abinda na aike kan ba, sannan baka dawomin da kudina ba?"
Kallonta yayi. " dan aikenki ne ni?" Ya fada yana kafeta da ido.
Gefe ta kauda kanta. " wa zan aika, banda kai? Ko bayan kai akwai wani yarone a gidan?"
Smacking yayi, still yana kallonta. " ba recharge card ba money, karfi yaci, in kina dashi kuma bisimilla ki kwata."
Ido ta zaro. " tabdijan!!! Kana neman fitina wallahi, kasan kudina ba zai yi ciwon kai ba, don seka biyasu."
Wuceta yayi, ya fita a gidan.
Kwafa tayi, bedroom ta koma, ta sake dauko wasu kudin, taba malan idi ya siyo mata.
********************
Ta windon bedroom dinta ta leka don ganin abinda ke faruwa.
Tsaki taja. " kuruci dangin hauka, wa annan ne zaa kira da masu hankali, har a dauki aure a basu." Ta fada tana kwabe baki. Tun da dama naga ana kafe- kafe da aune -aune, nasan za'a rina. Tsayawa tayi tana kallon yadda suke buga basketball din, sai ife, ifensu daya karade gidan.
Kitchen ta nufa, ta daura abincin dare. Wanda tun zuwanta, daga ita sai malan idi maigadi take dafa abincinta, sai ko in sunyi baki. Hayder da kansa yake dafa abinda zai ci, baya damuwa da rashin sa masa abinci da takeyi. In takai abinci falonsa to su junaid ne sukazo, ko bakinsa maza, a nan kam tana kokari, don duk abunka in kazo baxaka gane irin zaman da sukeyi ba. Abinci kuwa, zata dafa taba bako, batajin kyiwar girki, in ba lokacin cin abinci kazo ba, zata kawo maka juice, ruwa, da snacks. Wannan koyarwar gwaggo ne. Bata yadda bako yazo ya tafi baisha ko ruwa ba. In ma yaki sha. Ta dinga mita, har sai mutun ya kurba. A cewarta mugun bako ne, zai zo ka kawo masa abu yaki ci, ko sha.
Sai kusan magrib suka bar gidan. Yauma 9 ta wuce taji dirin bike din hayder alamar ya dawo kenan. Kwanciyarta ta gyara tare da lumshe idonta. Tana jin kewar Yusuf. Tabbas mutuwa mai tonon asiri, da yanzu tana tare da masoyinta, mutuwa ta mata yankan kauna, a dai dai lokacin da tafi kowa bukatarsa. Ya tafi ya barta, cikin gwagwarmayar rayuwa.
*****************
Yau kwana biyar ke nan, da tarewar hubby. Tana zaune a falonta na kasa. Indian series take kallo a tashar zee world.
Nocking din da taji, yasa ta mikewa, ta zura hijab dinta dake kusa da ita.
Hajiya kaka, da samira ta gani. Cikin faraa ta tarbesu, tare da masu iznin shigowa.
Kitchen ta nufa don kawo musu abin motsa baki,. Da kallo Anty samira kebin falon. Iyakar haduwa ya hadu. Gaba daya tunda ta shigo daga get, jikinta yayi sanyi, ga wani kishin hubby data ji ya kara darsuwa a zuciyarta. Ta rasa me yasa yarinyar ke darata a komai. Yadda take jin labarin haduwar gidan, har yafi yanda ake labarinsa.
Hajiya kaka ta rike baki, tana kallon Anty samira. " aljannar duniya, ki ce Hajiya ta tatse Jamal tas. Don wannan dukiya da aka zuba a nan, yafi karfin arzikin Munir."
" ehemmm!!!! Kema kya fada, duk anyi ne don muji haushi." Anty samira ta fada cike da kyashi
" sunyi ta banza kuwa, don baa taba canzawa tuwo suna, har gobe a tuwonsa zai zauna." Hajiya kaka ta fada
Hubby ce ta shigo da babban trey dauke da cups juice, water, cin cin da cake. Ajiyewa tayi a center table din dake gabansu. Sannan ta zauna. Hajiya kaka ta fara gaisarwa cikin ladabi, sannan ta gaishe da Anty samira.
Hajiya kaka ce ta kalli hubby, duk da katon hijab din da take sanye dashi, bazai hanaka ganin kyanta ba. Fuskar nan sai walkiya da daukar ido take, ta kara haske tayi kyau. " masha Allah, yarinya, ke kam kakarki ta yanke saka, na dauka zanzo in ganki, cikin damuwa, an hadaki da kanin bayanki, sai naga sabanin haka. Bako jin nauyi kinyi tarayya da yaya, kuma kina yi da kani, kanin ma na bayanki. Kinyi kokari matuka."
" me ko zai dameta, ta samu santalelen yaro, ana tsotseshi." Samira ta amshe
Gwaggo ta kara da " koda yake haka ne, kin san in mutun yayi kwantai, koma wa yazo ba damuwarsa bane, shidai ya jishi dakin aure kawai. Ni kam Allah ya tarfa min alam nasharaha."
Hubby kam kanta ta sunkuyar, zuciyarta na tafasa. Bawai dama ta manta abinda Anty samira ta mata bane, kawai dai ganin ita ta tako har inda take, bai kamata ta wulakanta taba. Sannan tasan tsaf sune, Ummul aba' is na aurenta da hayder. Darajar sun tako har gidanta, da darajar furfura, shi yasa ta daga musu kafa. Koba komai suna sama da ita.
" ai kam na tausayawa yaron nan, da yarintarka, a dauki uwar mata a hadaka da ita. Ban taba ganin irin wannan lamari ba. Koda yake sunfi kusa."
Bataji karar shigowar power bike din saba. Sallamarsa kawai sukaji. A hankali ya tako zuwa cikin falon. Sanye yake da lallausan yadi fari, half jamfa mai gajeren hannu, yayi kyau sosai, ga kamshi na musamman dake tashi a jikinsa.
Kujerar kusa da hubby ya zauna tare da daura kafa daya kan daya, ya jingina hannunsa mai dauke da phone dinsa a hannun kugerar, daya hannun yana shafa sagensa, zuwa gemunsa. Idonsa kar akan su Anty samira.
" babiba." Ya fada da wata irin murya daya sa hubby saurin dagowa ta kalleshi, cike da mamaki. Lokaci daya ya canza mata kamar ba hayder din data Sani ba. " go inside. " ya fada yana mata wani irin kallo. Bata san lokacin da ta mike ta nufi stairs ba.
" hayder wane irin abu ne haka? Bako gaisuwa, ka zauna zaka nuna mana kai ka zama mai gida, mai bada umurni? Ko ni baka gaishe ni ba, ai ka gaida Hajiya kaka ko?" Anty samira ta fada cike da jin haushi.
Kallonta yayi,tare da murmushin gefen baki. "A addinance sallama ya kamata nayi, kuma nayi dazan shigo. Duk da ba dole bace, amma amsata dole ne, cikinku waya amsa min sallamar? Babu?, kuna nan kuna cin zarafin yar mutane."
Cikin fusata Anty samira ta mike " in kana rashin mutuncinka karka yadda ka gangaro kaina! Don naga alamar kanka na rawa.?
Murmushi yayi mai sauti " duk wanda ya siya, dole a siyar masa, bazan dau rashin hankali a gidana ba. Ba yadda zaa yi, Ku tako har gidanta,. sannan kuci zarafinta. In a da kunyi, to ni bazan dauka ba, matukar ba zumunci zai kawo mutun ba, to bana nemansa a gidana, in ba haka ba tamuce ni dashi."
Hajiya kaka ce ta fara sallalami " ta tabbata! Ta tabbata! Wallahi ta tabbata. Kaima har an wanke an baka? Yo in ba an wanke an baka ba, a gabana bako kunya da ganin darajar furfura, kake kunfar baki don an taba tsohuwar matarka. Ina abun yake? Kake wani kafafa..."
" naji kina baki taba ganin aure, irin namu ba? Kin manta da auren manzo Allah, Annabi Muhammad SAW da Nana Khadija? Yana dan shekara 25 ita tana 40years. aurenta biyu, da yara biyar. Kafin ta auri Annabi Muhammad SAW. Kin ga ashe ba sabon abu bane, koyine da manzon Allah SAW. After all ke ce silar hakan, banga kuma dalilin zuwa ki tozartata ba, bayan ke kika ja, abinda yasa aka aura mata yaron."
Hajiya kaka da ranta ke bace, ya zaayi kamar hayder ya zauna yana gaya mata magana, hankalinsa kwance, kamar mai magana da saansa. " baka cewa ni na daura auren, mara kunyan banza."
" ko baki daura ba, ai kinyi sila. Ke daba dan darajar zamowarki kaka ba ta wani bangaren kuma furfurar da kike ikirari, da koda kudi aka ce ki tako kafarki gidannan bazaki fara ba. So leave us in peace. "
" ka rika wallahi, hayder Hajiya kaka kake ciwa fuska? Yanzu zaka iya yiwa Hajiya babba haka? Saboda mun tako gidanka, maganar nan bazata tsaya a nan ba, sai na kai kararka, ai gaba ma da gabanta. " samira ta fada cikin bacin rai.
" nan kika fi auki dama, an girma baa san an girma ba. Karki fasa kai karar tawa. Amma ki sani bama keba, duk wanda ya kara yunkurin cin fuskar matata, ko da dai dai da bakar magana ne, he will answer to me."
Takaici ne, ya kume Anty samira, tana jin labarin rashin mutuncinsa, amma bata taba tsammanin yakai haka ba. Don ko da tana gida, ba wani shiri sukeyi ba. Kamar yadda bayayi da mahaifiyarsu, haka ita ma, Karin jin haushin yadda yake treating din mamanta, yasa bata shiga harkarsa.
Hajiya kaka ta kalla. " tashi muje, kafin ya rufemu da duka kuma, don naga abun nasa ya yi yawa.'
Mikewa Hajiya kaka ta yi, Cike da sanyin jiki, ga takaicin hayder, a cikin jikokin nata ma, shi bai kai saan dan autan subama. Still yana zaune kafa daya kan daya, sai faman shafa sajensa, yake da kyawawan zara zaran yatsunsa, farare Sol dasu. Kai ka rantse maganar arziki yake furtawa, yadda yake maganar cikin yanga da Jan aji. Idonsa kar a kansu.
A fusace suka bar gidan. Tsaki yaja,. Tunowa da drama daya tarar anayi a main house. Abdul Karim da Anty samira, da kyar aka janyeshi yana sai ya mata dukan tsiya, sanadinta tasa ya rasa muradin zuciyarsa. Sai a nan ma suka ji, wasu kulle kullen data hada duk don taga auren hubby da Abdul Karim bai tabbata ba. Da badan shi, da ya janye Abdul Karim ba, da abun ba karamin kazanta zai yiba. Don su Hajiya sun kasa, gashi ba maza a gidan. Cikin ikon Allah sai gashi ya shigo.
Ya tausayawa Abdul Karim, duk da shima tawani fannin yana da nashi laifin. Mikewa yayi ya nufi upstairs, don dama wani documents yazo dauka.
A last step suka hadu da hubby dake rungume da hannu, cikin damuwa da bacin rai. Duk abinda suka fada kan kunnenta, shine dai bata ji mai yake fada musu ba, saboda a cikin natsuwa yake maganarsa, amma daga amsar da suke bashi, tasan ba maganar arziki ba ce. Babban abinda ya kara kona ranta, da yace ta tafi, ita kuma sokuwa, har dabin maganarsa, sai bayan ta tashin ta dinga jin haushin kanta.
Wuceta ya so yayi, tai saurin tare hanyar, kallonta yayi, ya koma ya jingina da jikin karfen benen, ya nade hannayensa duka biyu a kirjinsa. Ya zuba mata fararen idanuwansa.
" meye sunan abunda kayi? " ta tambaya tana kallon hannayensa dake sarke a juna. Ganin bashi da alamar amsa mata yasa ta kara jin haushi, don ta tsani tayi magana ya mata banza, gashi ta lura halayyarsa ke nan.
" abunda kayi, baka kyauta ba, koba komai sune gaba damu, dole muyi hakuri da duk abunda zasu fada mara dadi. Karka manta Hajiya kaka tamkar uwa take gasu Hajiya. Please don't do such thing again. "
Wani kallo ya mata data kasa tantance na menene. Ganin zai bangajeta, yasa tai saurin bashi hanya, da ido ta bishi har ya shige bedroom dinsa. Ajiyar zuciya ta sauke. " oh!!! Allah wannan wane irin yaro ne. Ke nan rashin mutuncin nasa kowa ma bai bari ba kenan.? Maganar ummu khulsum ce ta dawo mata. " rashin mutuncin hayder sai dai in baka shiga gonarsa ba, amma komai girmanka, bazai daga maka kafa ba. Don haka kibi a hankali, kika fusata shi, wallahi zaki gane baki da wayau, abin da ya miki da, nafila ne dana yanzu, don yanzu yana ganin kina kasanshi, matsayin matarsa, bazaku kwashe da dadi ba. Don haka ki kiyaye, Ku zauna lafiya, banda raini." Tana kokarin tuno da ansar data ba ummu khulsum a lokacin. ya fito, ganinta yayi still a wurin. Wuceta yayi ya sauka daga steps din, cikin gudu- gudu, sauri - sauri. Hubby ji tayi kamar ta tade kafar tasa ya fadi.
Ganin tsayuwar bazai mata ba, ta nufi falo, ta dauki trey din data kawowa su Anty samira ta nufi kitchen dashi.
******************
Tana kitchen taji shigowar mota, a tunaninta baki su kayi. Hayder ne ya shigo kallo daya ya mata ya nufi kofar da zata sada ka da waje, ya bude tare dama malan idi bismillah. Malan idi ne ya shigo da wasu manyan ledoji a hannunsa. Gaisheta yayi cike da ladabi, sannan ya ajiye. Haka ya dinga shigo da ledoji da kwalaye har ya gama, sannan ya kalli hayder dake rike da cup din juice " oga an gama." Hannu ya daga masa, cikin sauri yabar kitchen din.
Kallonsa tayi, takai kallonta ga shirgin kayan da malan idi ya shigo dashi. Juyawa tayi ta ci gaba da aikinta. Bebi ta kanta ba, ya fara ciccire ko wanne, yana sa su a muhallinsu. Nama ma mahaka ya jera su tsaf a deep freezer. Anyi shilling dinsu a kananan mazubi da white rapper. Juice, drinks, da bottle water duk ya jerasu a store.
Duk abinda yake yi tana jinsa, bata ko kalli inda yake ba. " in kin duba, akwai abunda babu let me know. " ya fada yana kokarin barin kitchen din.
" wai kai baka iya gaisuwa bane?" Dawowa yayi da baya, yana kare mata kallo. Harararsa tayi " wannan kallonfa?" Hada rai yayi cikin miryarsa mai kama da an masa dole ya ce " ni dake waya kamata ya gaishe da wani.?
Baki ta bude cike da mamakisa, ta amsa masa da " kai ya kamata ka gaisheni, after all kai kazo ka sameni, kaga kenan kai zaka gaisheni."
" sau nawa kika shigo kitchen din nan, da safe kika ganni, kika gaisheni?"
" taya zanyi dama in gaisheka? Karami ai shike gaida babba."
Smacking yayi, tare da shafa sajensa. Idonsa kar cikin nata. " shi yasa ai ban gaisheki ba, kin san yanzu abin ya juye. Ko da ban gaishe kiba, balle yanzu, da nake samanki." Ya fada yana gwada mata da hannunsa, daya daga a saman kanta.
" Allah ya kiyaye, in zamo a kasan ka, in mafarki kake, gara ka farka, har gobe ina nan a matsayin yayarka. Dole kuma ka bani wannan girman." Ta fada cikin bacin rai
" keep dreaming. " ya fada yana barin kitchen din.
" kam bala'i, me wannan yaron yake nufi? Kar dai auren da yake ganin an daura musu, yasa kansa ke rawa. Lallai kam zai sha mamamki."
Haka har ta gama aikinta tana tunanin maganarsa.
Ta idar da sallar ishai ke nan tana ninke hijab din da tayi salla dashi. Ya shigo dakin tare da sallama.
Gabanta ne yayi mugun faduwa, don tsawon sati dayan nan da kawota gidan, ko sau daya bai taba gigin shigowa dakinta ba. Hasalima da daddare kafin ya dawo ta rufe dakinta. Da kyar ta hadiye yawun bakinta tana binsa da kallo. " lafiya malan? Meya shigo dakai nan.?
Dakin yabi da kallo, komai tsaf, gwanin shaawa, ga kamshi mai dadi na tashi. Lallai su mommy Hauwa sun kashe money, ya fada a ransa. Don shi kansa dakin ya burgeshi sosai.
" me kike tunanin zai kawoni dakinki?" Ya fada yana isa wurin dressing mirror dinta.
" koma menene, ka gaggauta ficewa a dakin nan. Kuma ya zama fist and last da zaka shigomin daki."
" really.? " ya fada yana daddaga turarukan dake wurin, yana gani, tare da kaiwa hancinsa ya shinshina ya ajiye, ya dauki wani.
Tsayawa kawai tayi, tana kallon ikon Allah Don abun nasa ya fara daure mata kai. Kirjinta sai dukan tara tara yake, don bata san da wadda yazo ba.
" gobe Hajiya zata aiko miki da yar aiki, in kuma bakya bukata ki kira, ki shaida mata." Ya fada
Ajiyar zuciya ta yi, tare da ajiye hijab din a mazauninsa.
" OK, naji sai da safe." Ta fada tana nuna masa kofa.
Juyowa yayi ya jingina da jikin dresser din hannunsa duka biyu dafe da gefe- da gefen dressen. " I will travel tomorrow. " ya fada idonsa a kanta.
" Allah kiyaye hanya." Ta fada, still tana nuna masa kofa.
Kudi ya Ciro a aljihun rigarsa. Bunch din 1k ya ajiye mata. Ya juya zai fita. Sunansa data kira yasa ya juyo, yana kallonta.
Kudin ta dauka, ta nufi inda yake tsaye. Mika masa tayi " I don't need you're money. " kudin ya kalla, sannan ya kalleta, juyawa yayi yatafi ya barta da kudin a hannu. Kiransa ta fara, amma ko waigowa beyi ba. Tsaki ta ja, tare da komawa ciki ta murzawa kofarta key.
****************
Washe gari, jirginsu hayder ya tashi zuwa Paris, shida Hafiz, da amir.
Hajiya ta kawowa hubby yar aiki, mai suna Mariya, ta ji dadi sosai, don dama zaman gidan ya fara isarta. Musamman yanzu da yan ganin daki suka fara sauki.
Kwanan hayder biyar da tafiya, hubby ta koma islamiyarta. Ko da ta gayawa hajiya maganar islamiyya, tambayarta tayi hayder ya sani? Ta ce mata eh!! Kawai. Ce werta no need da zata tsaya har sai ta tambayi hayder, No way.
Islamiyyar daga 10 to 12pm, kafin ta tafi, sun gama komai na gyaran gida, tayi saa Mariya bata da kyuiwa, akwai aiki. Tana dawowa zata daura musu lunch. Dadinta ba nisa tsakaninta da school din.
*****************
Zaman gidan Alhaji Jamal yanzu ya sauya salo, duk yadda yaso yaga ya sasanta iyalan nasa, abun ya faskara. Don haka ya kai kararsu wurin Alhaji babba.
Alhaji babba da kansa ya tako har gidan dan nasa. Nasiha sosai ya musu, tare da rokonsu dasu manta duk wani abu daya faru, su yafewa juna.
Sannan ya shaida musu ya ba Abdul Karim da Abdul fatta nan da 2month kowannensu ya fitar da Matar aure.
Hakan ne ya kawo dan sassauci. Musamman tsakanin Hajiya da Mmn samira. Sai dai Hajiya ta Riga tayiwa kanta alkawarin bazata taba sake mata kamar da ba. don an shata ta warke. Kuma maciji baya sarin mumini sau biyu a rami daya. Yanzu tasan yadda zata zauna da kowaccensu. Dama Mmn Yusuf kowa yasan inda ya ajiye dan uwansa.
******************
Satinsu hayder biyu, suka dawo cike da nasarorin abinda ya kaisu. Sunyi saukar safe. Main house ya fara isa yaga Hajiyansa kafin ya nufi gida.
Ko da ya shigo gidan, bai ga motar hubby ba, bai kawo komai a ransa ba. Malan idi ne ya shigar masa da kayansa, Tare da masa sannu da zuwa.
Karar TV da yaji a falon hubby na kasa yasa shi nufar can. Cikin sallama ya shiga. Mariya dake zaune a kan carpet tana kallon Hausa film. Ta amsa tare da gaisheshi cikin Ladabi. Ta dauka bako hubby tayi, don bata san shiba. Ta ce " Anty bata nan." Kallonta yayi yana juya maganar a ransa.
Cikin muryarsa mai dadi, cike da muskilanci ga hausar sai a slow ya ce " ina taje."
" ta tafi makaranta, amma ta kusa dawowa."
" makaranta, makaranta, ya fara juya Kalmar a bakinsa, kamar mai son gano maanarta."
Jin yana ambatar makaranta, Mariya ta dauka bai gane bane, don taji hausar tasa wani iri, da ganinsa kuma ba bahaushe bane. Ta ce " makarantar islamiyya, nan kusa ne, ba nisa, yanzu zata dawo." Wucewa tayi da sauri, ita a dole zata kawowa bako ruwa, kamar yadda hubby ta umurceta in anyi baki.
Ranshi a bace ya haura sama. lokaci yayi da zai takawa yarinyar nan burki. Yan zune ya kamata tasan waye Aliyu hayder..............
Kuyi hakuri, weekend bazaku jini ba, saboda hidimomi da nake dasu. Sai mun hadu Monday in sha Allah.
[07/03, 17:22] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA