← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 28

Part din Hajiya ta koma, inda Hajiyan ke ci gaba da kula da ita. Tunda gwaggo ta koma, after 40 days.

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 19 min read

Rayuwa tama hubby zafi, a wannan lokacin, gaba daya ta canza kamar ba hubby ba.  Har lokacin kullun dare haka take raba dare da ibada, tana nema ma Yusuf gafara da rahamar Allah.

Kuka kam har lokacin a cikinsa take, mu samman in ta kadaita.

Takanyi Allah ya isa ga wanda suka zama sanadin rabata da masoyinta.

Sanadi

Bayan sun kama hanyar abuja, kamar yadda suka fita salis ke driving sai Yusuf a gefensa. Sai motar su Engr Sahabi da Imran da ke gabansu, don sun rigasu yin gaba, saboda Yusuf ya sasu biyawa main house.  Sun kusa isa zuba. Yan fashi ko in ce kidnappers suka tare motar su, da wasu motoci biyu. Gaba daya suka sasu fita daga motocinsu sukayi daji dasu. Basu dade suna tafiya ba Yusuf ya yiwa  salis signal a Lamar su kokarta ko zasu iya escape. Kafar dayan ya tadiyo, ya zube a kasa, wanda ya jawo hankalin sauran. Signal yama salis yana nuna masa na kusa dashi, cike da tsoro shima ya masa kafa, nan fa mutanen suka farga da abin da ke shirin faruwa. Fada ne ya kaure a tsakaninsu duk da hannayensu Yusuf a daure suke bai sa sun kasa kokarin kare Kansu ba.  Suma sauran mazan da aka kamo tare dasu Yusuf basuyi kasa a gwuiwaba. " try as much as u can. Daku mutu a hannun karnuka gara ku mutu kuna masu kokarin kare rayukanku," Yusuf ne ya fada masu salis da karfi don ya kara musu karfin gwuiwa. Kasan cewar basu da bindigogi, sai su takubba, da gariyo, ga kuma su Yusuf na neman yin galaba a kansu. Yasa dayan janyo addar dake kusa dashi ya dabawa salis a kafa, ya kara daba masa a baya. Jin ihun da salis ya saka, tare da zubewa a kasa jini na zuba, yasa Yusuf dakatawa daga dukan dayan da yake yi, cikin tashin hankali da kidima ya nufi salis. Tun kafin yakai biyu suka rike shi. Da sauri babban ya janyo hankici da wata kwalba a aljihunsa ya zazzaga abin cikin kwalbar akan hankicin ya nufo Yusuf yana huci " kai mai taurin kai ko? Gaka jarumi! In mun je can ka gwada jaruntar taka a can." Ya fada yana kokarin shakawa Yusuf a hanci, kauda fuskarsa yayi tayi, daya dake bayansu ya daga gariyo ya bugawa Yusuf a keya " wan nan balaraben dan banzan taurin kai ne dashi, gashi da alama zamuja kaya so ba wasa." Ya fada bayan ya sauke masa gariyon. " lailaha illallah, muham.....ko kafin Yusuf yakai ga karasawa dayan ya shaka masa hankicin. Salis ne cikin karfin hali yake kaiwa mai shakawa Yusuf hankicin duka a kafa.

Kallon salis yayi yana murmushin mugunta. Still duk da jikin Yusuf ya sake alamar he is uncountious bai sa ya dage hankicin ba. Ya ci gaba da kallon salis da murmushi a kan fuskarsa.

Harbi suka fara jiyowa ta ko ina da sawun tafiya, na tunka rosu. Tuni suka tsorata. Ganin tabbas suka tsaya bata lokaci, zaa cin masu. Sake Yusuf sukayi suka tasa sauran jamaar dake tare da su a gaba. Basu bi takan salis ba da shima ya ke yashe cikin jini, yana sauke numfashi da kyar. Sun San daukar Yusuf da salis a halin da suke ciki barazana ce a garesu.

Operation shaf shaf. Tun lokacin da aka tare motocin su Yusuf, wani bawan Allah dake aikin neman magunguna a cikin jejin ya gansu. Kuma dama yana da number na operation shaf shaf, saboda irin haka, tun da shi maa bocin hurda da dazuzzuka ne, suna ganin abun za suyi reporting. So ba bata lokaci ya kirasu ya shaida musu. Wannan shine

So ko da suka isa dasu Yusuf abuja general hospital, dan danan aka fara attending dinsu. Still Yusuf na unconscious. Isowar ta wagar ango, da da Alhaji Jamil kusan a tare hankalinsu duk a tashe. Lokacin an gama dressing din ciwon salis Allah ya taimakeshi yankan bai shiga ciki sosai ba, musamman na bayan. Karfe uku dai dai doctor din dake kan Yusuf ya fito fuska ba annuri, da sauri Alhaji Jamil da Engr Sahabi suka nufeshi.

Kallonsu yayi yana mai furzar da iskar bakinsa " I'm sorry Allah ya masa cikawa, saka makon over dose na...... Da bugun da aka masa a keya ya hana jijiyoyin dake sadar da jini ga kwakwalwa sun samu matsala.

Tun kafin doctor ya karasa bayani, tuni Alhaji Jamil yayi cikin dakin su Yusuf ango da gaba daya baka gane hakan saboda tashin hankalin da suka samu Kansu ciki. Suka rufawa Alhaji Jamil baya zuwa gadon da Yusuf ke kwance.

Tabbas mutuwa ba karya bace, nan danan suka fara hawaye Alhaji Jamil kam zubewa yayi a wurin a sume.

Imran ne yayi karfin halin kiran waya ya shaidawa Ahmad halin da ake ciki.

                 ***************
A kwana a tashi asarar mai rai. inji bahaushe. Yau hubby ke fita daga takaba. Daukacin kannen Yusuf mata da kawayenta, da yan'uwa sun zo tayata murnar kammala takaba lafiya .

Ta bangaren hubby har lokacin tana cikin damuwa, gaba daya ta rame kamar ba hubby ba. Dan yawan faraar nan ma yanzu duk babu, duk surutun hubby yanzu tana zaune za asha hira, amma ko uffan dinta baza kaji ba. Wannan Abu na matukar damun su Hajiya, tayi fadan, tayi nasihar duk a banza.

Ga yawan kukan da ta lura hubby ta mai dashi ibada. kullun ta farka da daddare sai ta sameta ko tana ibada ko tana aikin kuka. Don haka suka yanke shawarar da zarar ta kammala  takabarta, ta tafi wurin gwaggo a kankiya. Don sun San ita kadai ce zata iya da hubby a wannan gabar.

Haka ko akayi, hubby na kammala takaba, jafar ya dauketa zuwa kankiya.............

   
Yau gidan gwaggo cike yake. Alhaji Munir da iyalansa. Alhaji Kawu ma yau bai samu fita ba.

Alhaji Munir na tare da mahaifinsa Alhaji kawu, sun lume a falonsa suna tattaunawa kamar yadda suka saba duk lokacin da suka kadaita da juna.

A falon gwaggo kuwa mommy Hauwa da gwaggo sai jafar da hubby,Jabir. " gaskiya tsohuwar nan ta iya girki, dole in nayi aure in daukeki ki zauna a can kina dafa min beta. Shi kuma Alhaji Kawu mu nemo masa wata yar duma duma haka" hararar jafar gwaggo tayi " Allah ya sittiri bukwui, ni kam nayi ma nisa yaro, garama jafaru zan iya da rantamemen kan nasa. Amma kai kam ga dan Karen yanga, ga lalaci ina!!!! Bada ni ba."

Dariya suka yi " da tsohuwar Zuma dai ake magani, kafin ki samu jabir jafar kika samu. Don ma zan rufa miki asiri, da wannan rigimar taki wa zai iya dake? In ba ni  din ba?"

" ka ji cika baki? Kalleni da kyau na wuce alfarmarka. Karka manta har kujerar umra aka bani cin hanci."

Dariya suka yi gaba daya. Mommy Hauwa ta ce " Kwarai kuwa, autana ya kwace mata kuna nan zaune."

" wane shi mommy, aurena da gwaggo baya mutuwa. Takalmin kaza ne, mutu ka raba. Munci kujerar umra a awuf." Jabir ya fada yana kara danna lomar sakwara.

" kayya dai!!! Ni na fara jiyo kamshin gidan junaid, ina ga zanyi na ywnmatan zamani nima. " gwaggo ta fada tana murmushi tare da turo dankwali gaban goshi.

" kai kai kai!!! Wallahi baki isa ba, kin gama more min, sannan ki canza? Duk wahalar zuwa ungwuwar da nake kaiki? Dan goro na da kika cinye, dan turarena duka?"

Harararsa gwaggo tayi cikin wasa, ta kara  tura dan kwalinta gaban goshi.
" sai kayi lissafi junaid zai biyaka, har da kari. nifa ba mai min dole heh!!!!!!"

" mai idon cin naira kenan?" Sai lokacin hubby ta sa musu baki.

Mommy Hauwa kam tun dazu bin hubby da kallo take, cike da tausayawa. Yanzu kam tayi kyan gani, sai rashin walwala. Ta koma wata shiru shiru.

" ganemin hanya sis "

" kasan koda mukaje umra duk adduarta a kan junaid ne? Har da Allah yaja da ran mai halin tsoho, ko sau daya banji ta ambaci jabir ba, balle jafar." Hubby ta fada tana kallon jabir dake faman zaro ido cikin wasa.

" lallema tsohuwar nan, watan kinci moriyar ganga ko?"

" takwara akwai  sharri, kina ina nai ma kowanne dawafi na musamman. Kaji megidan kyaleta so take ta hadamu."

Mommy Hauwa ta yi murmushi " aiko dai alkawari bai ce haka ba. Ke kikawa auta alkawarin duk randa ya kaiki hajj ko umra, to baki da miji sai shi, kin ga ko kyan alkawari cikawa. Ya kuma cika nasa. Mun shaida aure ya dauru ke da auta."

Dariya gwaggo tayi tunowa da yarje jeniyarta da junaid wani Hutu daya zo mata, kusan shekaru Tara da suka wuce.

" ai shi kenan. Yanzu dai shiga ki debo mana namu tsarabar umran. "  jabir ya fada

" oh!!oh!! Ni banyi tsaraba ba, na dai muku addua. Kudina kuwa munci kaji, kayan marmari, da laban."

Dariya sukayi ganin yadda take yi da baki da hannu don kwatan tawa.

" lallai tsohuwar nan. Kije har kasa mai tsarki ki dawo, babu tsaraba?"

" kullun ne ake kwana a gado? Wannan karon ban yi ba, dadin kudina naji, sai Ku jira zuwa na gaba, in Allah ya mana yawan rai."

" sister kema bakiyi tsara barba?" Jafar ya tambayi  hubby

Kai ta kada mishi, tana murmushi.

" Allah ya kyauta, zanje next time don't expecte anything kuma."

" ga zam zam can, dauka kasha. Ina laifi." Gwaggo ta fada tana nuna masa jarkar zam zam 5liter dake can gefe.

Jabir ne ya kalli hubby cike da tausayawa. " sister menene plan Dinki? Kin ga zaman gida bazai miki ba, at least you have to fine some thing da zai kipping naki busy."

Duk Kansu ido suka zuba mata suji amsar da zata basu, don jabir kamar ya sosama mommy Hauwa in da ke mata kai kayi ne, amma ta rasa ta inda zata faro.

Shiru tayi tana wasa da yatsunta.

" yo!! Mace kam ai da zaman gida aka Santa, fatana Allah ya fito mata da miji tayi aurenta,."

Da sauri hubby ta kalli gwaggo. Cike da fushi ta ce " na ce kibar min irin wannan maganar, nida aure har abada, Nayi na gama."

Rike baki gwaggo tayi " aa lallai, da kuruciyarki da komai ki ce kin gama aure? Wasa kike yarinya. Gara ki farka tun kan dare ya miki, don bazamu ajiyeki muna kallo ba kamar photo."

Ganin hawayen dake bin fuskar hubby yasa jikin su jabir yin sanyi.

" kiyi hakuri, naga an fara registration na JAM ne, in kina da shaawa sai kiyi, at least karatun zai debe miki kewa."

Kada kai tayi tana share hawayenta tare da Jan hanci.

" haka zaki zauna ba karatu? Ko dai ta bakin gwaggon ne, aure kike so?"

Harararsa tayi " ina zuwa islamiyya Saturday and Sundays. Sannan akwai kankiya woman association committee da zan shiga, don tai makawa gajiyayyu, da marasa galihu, da Samar musu da sanaoi."

Shiru sukayi suna kallonta. Jabir ya kada kai ya CE " har yanzu kina  nufin baki da interest a kan karatu? Haba sister u have to wake up. Lokaci ya wuce da mutun zai zauna ba tare da ya nemi ilmi ba. Ilmin addini yafi komai muhimmanci ga rayuwa, duniya da lahira, ammafa ki Sani shima ilmin zamanin yanada nashi anfanin. Don shi giahirine na rayuwa. My advice to u shine ki daure ki yi jam in yaso sai ki karanta Islamic studies, ko Arabic ,tunda kinfi son fannin addini, ga Islamic low ma duk u can do it."

Jafar ne ya tare tare da ci gaba da cewa. " in da son samu ne, zan so ko midwifery ki yi, is good. "

" wai ina dalili ne? Yarinya ta ce bata so, basai a gyaleta ba, Ku waya matsa muku kukayi karatun? Ina raayinku ne? To ita ma ku barta tayi abunda ta ke so. Haba tun kan yarinyar nan tai auren farko ta nuna bata raayi, don haka kar wanda ya takura mata, ku barta. Ku dai ku tayata da adduar Allah ya bata miji na gari tayi aurenta. Ba gararanbar gantalin karatu ba."

" wai sau nawa kike son in gayamiki ki daina min maganar wani abu can aure? Nayi na farko nayi na karshe, in kika matsamin tattare kayana zanyi in yi gaba." Hubby ta fada cikin fushi tana share hawaye. Daga karshe ma tashi tayi ta shige bedroom din gwaggo tana faman mita.

Da harara gwaggo ta bita " bansan ranki ya baci ba, sai naji duka. Aure kam ya zama wajibi, in da baa aure a haigoki? In sha Allah sai naga yayanki takwara. Don haka yanzu na fara miki maganar aure, kin dade baki tattara kin tafi ba. Don can din ma ba bakona bane ehee!!!"

Mommy Hauwa dai nata ido, duk da zuciyarta tana cikin damuwa, da takaicin decision din hubby, amma tasan bata da ikon tofa nata, a gaban gwaggo,.

Haka dai sukayi ta hira har yamma kafin sukayi sallama dasu, suka nufi Kaduna.

                *****************

Hubby ce da gwaggo suna fitowa daga wani special hospital kankiya. Dubo wani makwafcinsu da aka kwantar.

Wurin parking suka nufa, don hubby ce ta tukosu. Sallamar da sukaji yasa su juyowa. Gwaggo ta amsa. Ganin mai sallamar yasa ta washe baki " aa doctor bokan turai, yaushe a gari?"

Murmushi yayi tare da rusinawa ya fara gaisheta. " dazun nan na iso Umma take gayamin rashin lafiyan Alhaji, shine nace bari in zo in dubashi."

" aiko ka kyauta. Jiki kam alhamdulillah ya fara samun sauki. Ya kishiyata da kannenta?"

Cike da faraa ya amsa " sunanan lafiya, sun ce a gaisheku"

" muna amsawa,."

Sai lokacin hubby ta samu damar gaisheshi.

Cike da kulawa ya amsa, yana tambayarta kannenta.

Gwaggo ce tai karaf ta ce " suna can Kaduna, kasan ita tun da ta gama takabarta muna tare"

" ayya haka ne, Allah ya ji kansa da gafara." Ya fada duk da yaje har Kaduna ya musu gaisuwa.

Ran hubby ya baci. Fadi baa tambaye kiba, ta fada under her breadth. Juyawa tayi ta shige mota tana mai amsawa da " amin" da kallo ya bita yana murmushi, sai da ya daina ganinta kafin ya maida kallonsa kan gwaggo dake gaisawa da wasu yan mata da suke gaisheta. Sosa kansa yayi da key din motarsa yama gwaggo sallama da alkawarin zaizo kafin ya koma.

Shiya budewa gwaggo kofar motar sai da ya tabbatar ta zauna kafin ya mata sallama. Kallon hubby yayi yana murmushi " kanwata sai anjima ko " hannu kawai ta daga mishi ta figi motarta tayi gaba.

Yana tsaye a wurin fuskarsa dauke da murmushi har ta bacewa ganinsa, kafin ya kada kai tare da shigewa cikin hospital din.

Kallon hubby gwaggo tayi, ganin yadda taketa kunbure kunbure, tana cika. Gwaggo ta ce " ke ko lafiyarki kike hawa kaman farashi?"

Shiru ta mata, sai can ta kalli gwaggo " daga tambaya, meye naki na wani tsayawa kina masa dogon sharhi?"

Haba gwaggo ta rike " too!!!!! Hashimu ne fa! Ko baki gane shibane? Dan gidan hausi"

Haushine ya kara cika hubby. " ya zanyi in manta da mugu irinsa?"

" aa takwara, hashimun ne mugu?"

" eh!! Mana. ban manta muguntar da yayi ta min ba lokacin ina primary,."

Dariya gwaggo tayi " mugunta ko gyara? Lokacin maganar wa kike ji? Daga Alhaji Kawu sai shi. Ai ni ko don yadda ya samin ido a kanki yasa nake son yaron."

Tunowa hubby tayi da yadda yake tasata a gaba zuwa makaranta. Tana kuka tana komai, wani lokacin har da bulalarsa yana tsula mata in yaga tana son yawo da hankalinsa. In tayi tsokana ko rashin ji, shi yake hukuntata. Tun gwaggo na jin haushi har ta hakura. Wani lokacin ma da kanta take kai karar hubby wurinsa.

Tsaki hubby tayi. Tunowa da alwashin da sukaci ita da kawarta dija, na  Duk randa Allah ya sa ya haihu, sai sun rama a jikin dansa. 

Tabe baki gwaggo tayi, ta ci gaba da kalle kallenta, har suka iso gida.

                 *****************
Kamar yadda Hashim yama gwaggo alkawari, ko sai gashi da yamma. Hubby na tsakar gida tana shara, gwaggo na daga falonta, ta daga labule suna magana da hubby kan community da aka kafa wanda zai yattauna da chairman din kankiya local government da kansiloli, don tattauna hannoyin magance matsalolin rashin aikin yi ga matasa da Samar musu da abubuwan yi. Mu samman mata.

Sallamar shine ta katse musu hirar.
Da sauri ta yayibi hijab dake jikin igya ta zunbula.  A hankali yake takowa idonsa a kanta har ya zo daf da ita.

Idonta akan tsintsiyar duk da jikinta ya bata ita yake kallo, bata dago ba. Jin takunsa da kamshin tururensa yasa tasan yazo gaf da ita.

" ina wuni " ta fada a takaice ba tare data kalleshi ba.

Cike da faraa ya amsata. Tare da shigewa falon gwaggo dake faman masa sannu da zuwa.

Tsaki hubby taja ta ci gaba da shararta.

Hira sosai sike shida gwaggo, dan game da aikinsa, da iyali.

" baka kyautawa hashimu, yanzu shekara nawa rabon yaranka da garin nan? Ko ba komai ka kawosu suga yan uwa, don su sansu, su saba dasu, ba in an haduba a zama bakin juna. Ku yan boko Sam rayuwarku ba tsari. Zumunci ya wuce komai. In baka sabawa yaranka shiga cikin yan uwanka ba sai yaushe? Kai kanka yaushe rabonka da garin nan? Kullun zancen mahaifiyarka ke nan. Kai baka damu kazo ba, ballan tana iyalanka. Su kuma in sun je maka ba dadi. Wace irin rayuwace wannan? Ina rokonka don Allah kayi kokari ka gyara. Ko duk wata ne kazo ka duba iyayenka, in anyi hutu ko kwana uku ne ka kawo yaranka suga gida. Ta haka ne sai kaga zumunci da shakuwa ya wanzu a tsakaninsu. Dama wannan ne yasa nake son ganinka."

Kanshi a kasa, tabbas duk abinda gwaggo ta fada gaskiya ne. Shi kansa abun na damunsa, amma ba yadda ya iya.

" in sha Allahu zan gyara. Na gode sosai."

Murmushi gwaggo tayi, tare da kwalawa hubby kira " ki kawo ma hashimu ruwa mana"

" Habiba ta koma makaranta ne? Ko har yanzu hali nanan na kin makaranta?" Ya tambaya

Nisawa gwaggo tayi " wane makaranta kuma banda Wanda tayi. Islamiyya dai take zuwa."

Girgixa kai yayi yana murmushi " ilmi yana da amfani da ta daure ta koma ko diploma tayi yafi zaman haka."
Dai dai lokacin hubby ta kawo masa ruwa, da 5 alive.

Tabe baki gwaggo tayi " Ku barmin ita tayi abin da take so. Suma kannenta da iyayenta maganar kenan. Tun da bata da raayi, ina dalilin tursa sawar bayan mun samu ta dawo hayyacinta da kyar. Shiyasa na ce kar Wanda ya kara takura mata kan maganar makaranta. Fatana Allah ya bata miji na gari tayi aurenta. Duk da shi din ma na lura zaayi yaki da ita, don ba aure a rayuwarta. Yarinya karama kuwa kamarta ba yadda zamu ajiyeta gida muna kallo."

murmushi yayi don yasan tsakanin gwaggo da hubby " Allah ya zaba abinda yafi alkhairi." Ya fada

" amin ya Allah"

Alhaji Kawu ne yayi sallama. Shima Cike da faraa ya ce " aa Hashim ne yau a gidan?"

Dariya gwaggo tayi " aiko dai gashi nan."

Murmushi Hashim yayi yana shafa keya. Tare da gaisheda Alhaji Kawu.

Hira sosai suka sha, sai gaf da magriba ya musu sallama ya fito. Har lokacin hubby na zaune a tsakar gida kan kujera yar tsugunno tana gyara busasshen zogale.

Muryarsa da kamshin turarensa taji a kanta. " sister can I have your phone number. "

Dago fararen idonta tayi ta sauke a kansa. Wanda ya kara sakarma da Hashim wani irin yanayi a tattare dashi.

" bani da phone. " ta fada tana ci gaba da gyaran zogalenta.

" really? I can believe baki da phone. Sai dai kice bazaki bani ba kawai."

Ba tare data dago ba ta ce " da gaske nake, don bani da bukatarsa."

Murmushi yayi tare da Sosa kansa.
" can I buy u are one ?"

Cikin sauri da kosawa tace " no, I don't need it."

" OK " ya fada cikin sanyin murya

Har ya juya zai tafi, ya dawo " zan iya kiranki a phone din gwaggo? Don akwai magana mai muhimmanci da nake son mu tattauna."

Dago kanta tayi, alamar ranta ya fara baci, don ya hango zallar bacin rai a idonta. " please Yaya Hashim don Call me." Ta fada tare da tashi ta shige falon gwaggo. Da kallo ya bita kafin ya girgiza kai, yana murmushi ya bar gidan.

             **********************

Hashimu Adam kankiya, shine asalin sunansa. Da ga Alhaji Adam da Hajiya hafsatu, wadda su gwaggo ke kira da hausi. Makota ne, tsakaninsu gida biyu. Su biyar ne a wurin iyayensu, shine babba. Yayi karatunsa primary da secondary anan kankiya, kafin ya tafi ABU, in da ya karanci medicine. Yanzu haka cikakken doctor ne mai zaman kansa. Wanda ya mallaki hospital na kashin kansa a garin abuja.

Hashim baki ne, amma ba wuluk ba, mai matsakaicin tsawo, mai kyan sura da cikar kamala, shi baza a kirasa kyakyawa ba, bakuma ya cikin sawun munana. Dan kimanin shekaru 47 amma saboda jin dadi, da gogewa yasa baza ka dauka yakai hakan ba. Yanada mata daya da yara hudu. Biyu maza biyu mata. Mutun ne mai nagarta da halin dattako, sai dai baiyi Saar abokiyar rayuwa ba. Fatima irin matan nan ne masu son kansu. Sun fi son mijinsu ya zamana daga su sai yayansu da yan uwansu. Hakan ne yasa bata zauna ba. Wurin Neman asirce asirce don ya zama nata. Tako yi nasara don sai ya shafe fiye da 3month bai waiwayi iyayensa ba. Dama ita ba zuwa take ba. Sai da babban dalili, haka yaran bata yadda su rabi dangin uban ko kadan, sai danginta. Suma dangin nasa basa zuwa, saboda kalolin wulakanci da cin zarafi da suke fuskanta a wurin Matar gidan da yaranta. Hatta yan aikin gidan basa girmamasu, shi yasa suka dauke kafarsu Suma. Abin na matukar damun Hashim amma ba yadda ya iya,."

Tun hubby na karama take burgeshi, Abu daya ke hadasu bata son karatu ko kadan, shi kuwa bashi da buri irin yaga kannensa sun yi ilmi sosai, lokacin tana primary 2 shi kuma yana 3ooL. So haka yake fama da ita kan rashin son zuwa makaranta, tare da kanwarsa Khadija wadda take kawa ga hubby, sai dai ita Khadija tana kokari sosai a school, ta riga hubby gama primary da 2years, repeating din da aka musu na farko a tare, da yazo ya musu dukan mutuwa, tun daga nan Khadija ta shiga hankalinta. Duk da da yawa tare suke rashin jin su.

Zumunci ne sosai tsakanin gidan Alhaji Kawu da gidan Alhaji Adam. Duk da Alhaji Kawu ya girmema Alhaji Adam sosai anma bai hana amin takarsu karfi ba. Haka hausi da gwaggo, don ta dauki gwaggo kamar Yaya, kuma yar uwa, mai bata shawara.

              ********************

Parking dinta kenan a dai dai hole din da suke metting, ko training. Sanye take da doguwar riga ta atamfa, light blue sai dogon hijab mai hannu purple kalan design din atamfar. Ba wani makeup a fuskarta, daga powder, kwalli, sai wet lips. Tayi matukar kyau fuskar nan sai daukan ido take don glowing.

Tana kokarin fitowa, wata mota kirar landcruser 2018 baka mai bakin tilted tayi parking kusa da ita.

Sai da ta mika hannunta gefe ta dauko handbag dinta, ta bude bayan ta dauki wani jaka madai daici, sannan ta rufe motar da remote.

Juyowa tayi don nufan cikin hole din, ganin mutun tayi tsaye jingine jikin karshen motarta ya mikar da kafarsa, yanda bazata samu damar wucewa ba matukar bata kan kafafun zata bi ta wuce ba.

A hankali ta dago don ganin wannan mai karfin halin, da rainin hankali......


 
[02/03, 12:33] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 10 · 0% Book details