← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 28

                            Part 6

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 22 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau

Duk yadda taso ya barta tayi wankan da kanta ki yayi, tana noke noke ga hawaye shabe shabe, tana ji tana gani ya zaunar da ita cikin bap din wankan.

" naga alama yau dinnan hawayenki zai Kare, kuka tun jiya yaki karewa " ya fada yana murmushi

Harararsa tayi, zuciyarta cike da jin haushinsa.

" kika sake hararata, zamu hadu yanzun nan " ya fada yana kafeta da mayun idonsa, masu rikitata.  Sunkuyar da kanta tayi, tana Jan hanci.

Da kansa ya mata wanka, ya nadota a towel kamar wata baby. Futowarsu a toilet din yaji kamar door bell na ringing.  Ajiyeta yayi, saman kujerar dressing  mirror. " I'm coming princess " ya fada yana barin dakin.

Ganin gwaggo tsaye bakin Kofa, ya cika da mamaki, cikin girmamawa ya bata hanya ta shigo, tare da karbar basket din hannunta.

Cike da kunya da jin nauyinta yake gaisheta.  Itam ma cikin sakin fuska ta amsa tare da tambayarsa hubby.

Yana gaba tana baya, har dakin hubby da tun fitar yusuf ta kifa kanta kan dresser din, tana sauke ajiyar zuciya. Sallamar gwaggo yasa ta dago da sauri.  Mikewa tayi ta fada jikin gwaggo tare da sake sabon kuka.

Sum sum sum yusuf yayi waje, yana murmushi, tare da jin jina shakuwar hubby da gwaggo.  Yau kam ya yadda da son jiki irin na hubby. Hirar su Hajiya ce ta fado masa a rai. Inda suke hirar halayyan yaran family dinsu.  Hajiya ke cewa " ai ni kinga habiba da Aisha ba mai sani rakasu labour room, sai dai ke, tana nufin Mmn samira, kuje tare.  Yara sai son jiki, basa son komai ya taba lafiyar jikinsu?  Dazu da naje gidan gaba daya Habiba ta hargitsasu da koke koke, wai ta yanke a hannu.  Na dauka zanga wani katon yanka, sai naga yan kan ma ba wai ya shiga bane, jinin da ta gani ne, duk ta rudasu da kuka, kamar yadda Aisha ke wannan iskancin a gidan nan. " murmushi ya Kara yi, tare da shigewa wanka.

" ai ni kin ban tsoro takwara!!  Mutuwa fa kika ambata min, kin sani fitowa ba shiri "

Baki ta tura cikin shagwaba, ga hawaye ta ce " numfashine fa kawai ajikina,  gara kizo in ganki Kafin na mutu. "

Dariya gwaggo tayi " baza ki mutu ba  Sai kin santalo min kyawawan tattaba kunne. Allah ya miki albarka da kika tsare mana mutuncinmu, kika kawo budurcinki dakin aure, ni kam kin gama min komai. "

" kafata kafarki, bazan yadda a kashe miki niba.  Dama ke kika zugani in ce aure nake so, na dauka auren dadi ne ai?  Ashe anani burdade ake ci. Kuma a haka kice kina sona? " ta fada cike da shagwaba

" gatan kenan takwara, da kin warke shi kenan, na dan lokaci ne. Yan zu dai Bari kiga " ta nufi toilet

Harararta hubby tayi " kiji mata wai na Dan lokaci,  bayan duk ke kika jamin ina zaman zamana. In da nasan dawan garin ai da sai dai mu karaci soyayyarmu a gida, in da ko hannu na bazai iya rikewa ba, balle.

" tashi muje ki gani " " wayyo Allah na yanzu fah na fito daga wanka "

" ke dalla rufamin baki, muje " ta hade rai. Dole hubby tabi bayanta tana dana sanin kiranta.

Ruwa ta hada mata, da wasu itatuwa. Sai da ta tabbatar ta zauna Kafin ta fito. Ta barta a toilet din.

Dube duben inda zata ga kasko take, bata gani ba, ta koma ta tambayi hubby.

Gawayin kanti ta hada a kaskon,  ta dauko kujerar dorot ta daura a kai, hubby na fitowa ta zuba wani gari a ciki mai azabar kamshi, Tasa hubby zama a kai.

" da nasan kema izayar da zakimin ke nan da ban kira ki ba " hubby ta fada tana kunbure kumbure.

Murmushi gwaggo tayi " yanzu ya kikaji jikin naki? "

Shiru ta mata, amma har ga Allah taji dadin jikinta, zata iya cewa ma ta daina jin ciwon da take ji a kasanta.  Sai abunda baa rasa ba.

" tashi ki shirya, kwalliya nake son kiyi sosai. Bari in dauko abincin da nazo miki dashi.

Baki hubby ta washe jin harda abinci gwaggo ta kawo mata, duk da bata jin yunwa.

Super exclusive mai launin brawn and black, Sai shade din light yellow. Dinkin Riga da skeet 8 pierces dinkin ya zauna cas a jikinta, kamar wata yar tsana don kyau.  Jelar kitsonta da suka sakko har kafadunta ta tattara ta daure da ribbon.  Simple daurin Dan kwali tayi. Da simple makeup,  tayi kyau sosai, ga kamshin turaruka da humra dake tashi a jikinta.

Washe baki tayi " Masha Allah,  in ce ko kina gode Allah bisa wannan sura da ya miki " kallon gwaggo tayi tana murmushi

Gwaggo ta Kara da cewa " abinda nake so dake shine,  hakuri da juriya, duk mace da kika ganta a gidan mijinta ta kwashe shekara da shekaru to ba komai ya Kawo hakan ba Illa hakuri, juriya da jajircewa. Yanzu ne zaki natsu ki gane me dame mijinki yafi bukata a tare dake, don ki Kara in ganta zamanku.  Tsafta kula da jiki, kula da muhalli, tsaftar kitchen dinki da duk abinda zaa sarrafa a cikinsa. Tsaftar ban daki, da uwa uba turakar miji. A kalla kina samun wanka Kamar sau uku, zuwa biyar a Rana, na safe Kafin ya fita daban, na rana daban, sannan na dare watau na tarbar megida. Don Allah takwara ban da son jiki, nasan baki da kazanta, ki Kara dagewa, San nan kar ki yadda ki nunawa miji gazawarki ta wurin daukar nauyin bukatarsa. Ki zama me juriya.  Ki dage ki koyi girki nasan wannan uwar taki bata koya miki komai ba. Kin dai san gidan da mijinki ya fito. Kowa yasan akwai cima Mai kyau a gidan Jamal,. Karki biyo uwarki da komai Sai masu aiki zasuyi.  Don in baki dace da suruka Irina ba, tuni zata auro masa wadda zata kula mata da danta da kyau. Ko ta tasa min ke a gaba da rashin mutunci. "

Murmushi hubby tayi " nifa ban son kishiya, naga kema baa miki ba, kike min fatan amin" ta fada tana tura baki

"ba fata na miki ba, amma kika sake kikayi halin hauwa, kin hadu da kishiya kin gama yarinya. Ki zauna gidan mijinki ki kula da mijinki da yayan da Allah zai azurtaku dasu. Mijinki Nada halin da zai kula da duk bukatunki, in ma kina bukatar wani abun ne, GA Sana oi nan da zaki iya yi a gida, sun isa basai kin wahalar da kanki ba. "

Shigowar yusuf ya katse musu hirar.  Sanye yake da lallausan voil fari kar da hula wadda ta dace da kayan sosai.  Kana ganinsa kaga balarabe sak, haskensa ya Kara fita sosai, ga wani kamshi Mai dadi da San Yaya rai na tashi.

"Yau wa, zo kaci abinci " gwaggo ta fada tana janyo masa basket din.

Murmushi yayi, tare da zama a bakin gadon,  hada ido sukayi da hubby dake kwasar farfesun Kayan ciki.  Murmushi suka aikawa juna, yayi mata blowing kiss.  Sunkuyar dakai tayi ta ci gaba da cin farfesunta.  Ya mata matukar kyau da kwarjini,  wani Karin son shi taji ya na bin jinin jikinta.

Shi din ma haka, ya kasa dauke idonsa a kanta.  Duk da kokarin saita kansa da yake, tayi kyau sosai, komai Masha Allah. Beyond what he expected.

Nasiha gwaggo ta musu mai shiga rai, Kari kan Wanda aka musu.

Mika masa wayar tayi " Kira min wannan mai ranta memen kan" mirmushi yayi don yasan Wanda take nufi.  Saida ya Kira sau biyu tukunna aka daga, ya Mika mata.

" to dan nema, zaka zo ka dauko nine ko  na Kira tsohonka shi yazo? "

Hararar wayar yayi kamar gwaggon na gabansa.

" kirashi man, sai me? "

"au!!!  Haka kace?  To shi ke nan " ta kashe wayar.

" Dani kake magana, ta fara lalubar number daddy su hubby.  Kira ne ya shigo wayar, yasa kiran daddy katsewa.

Dagawa tayi, muryar jabir ne " gani nan zuwa " ya fada Kamar zai fashe da kuka

" Dan nema, da karka zo man "
" da baki kirashi ba, muje in mai dake "

" aa,  barshi yazo, Dani yake magana ai. Ina ni ina fitar da ango daga gidansa. " ta fada tana kokarin tattara wormers din.  Da sauri hubby ta karbeta ta jera mata su.

"ina kika samo wormers masu kyau haka? "  hubby ta tambaya tana juya karamin.

" abincin ubankine nayo gaba dashi " daga hubby har yusuf tsayawa sukai suna kallon gwaggo.  Cike da mamaki

" to shi kuma yaci me?  Hubby ta tambaya

" wan nan ruwansu kuma " tayi ficewarta daga dakin

Da kuka suka rabu da hubby, Sai da ta mata alkhawarin sake zuwa dubata Kafin ta koma tukunna,.

                ******************

Gaba daya ranar a  cikin baki suka yishi, masu zuwa Ganin dakin Amarya.  Tun daga ranar hubby ta San akwai babbar matsala tsakaninta da dangin  Mmn yusuf, don da yawansu sun kasa danne kishinsu gareta.

Sai yamma can, su yusuf suka tafi bangajiyar surukai, yabar su yusra suna taya hubby gyaran gida.

Nocking sukaji, suna tsaka da gyaran falo.  Asiya ce taje ta bude.

Hayder, junaid, alim, amir, Hafiz da Hafiz omer. Kayayyakin cefane sukai ta shigo dashi da su bottle water, drinks, juices.

A kitchen suka jibge musu.  " a taimaka a shigar dasu store mana " Aisha ta fada tana kallonsu, sunyi dai dai a falon.

"aikin me kuke dabaza ku shiryasu da kan kuba?  Mu kam munyi namu, ya rage naku kuma, in kun so ku barsu a wurin " Hafiz ya fada yana kallon ta

Harararsa tayi " dadin abun ba kutare muke ba "

" na dauka ai kutarene "

" ina wuni yayarmu, suka fada a tare, banda haydar dake danne danne a wayarsa.

Suka fara gaishe da hubby data fito daga daki.

Amsawa tayi tana murmushi, tare da tambayarsu gajiya.

" Asiya kawo musu ruwa " ta fada tana kokarin zama a daya daga cikin kujerar dinning din.

" barshi kawai yayarmu, Sai mun sake zagayowa, sauri muke, dama Yaya ne yace mu kawo sako " Hafiz omer ya ce yana mikewa.

" na gode, sosai " ta fada tana hararar haydar da suka hada ido.  Kauda kansa yayi, yay gaba abinsa. Dublan alkaki, nakiya cin cin da sauransu tasa aka kulla musu Leda guda Asiya ta Kai musu har mota.

" yayarmu za tayi kirki, yaushe zamu koma? " Hafiz omer ya fada yana cika baki da cin cin.

" dole mu dinga zagowa, don nasan Anty Da kwadayi, zamufi maida komada da wuri. " amir ya fada

Haka sukaita hirar, a tsakaninsu har suka isa inda zasu.

                   ****************
Amarci sosai hubby da oga yusuf suka sha, na tsawon sati biyu ba tare da ya fita ko ina ba, daga masallaci, Sai mein house da yake zuwa every 2days ya gaishe da iyayensa.

Wani kyau ta Kara, da murjewar jiki, na ban mamaki. Ita kanta bata gajiya da kallon kanta, balle yusuf daya Kara susucewa a kanta.

                ****************
Turaren ta karba tana fesa masa, kallon yake yana faman murmushi, ganin yadda ta turbune fuska, kamar zatayi kuka.  Hannunsa duka biyu ya daura a kafadarta. 

" kiyi hakuri, it's just 2 days zanyi in dawo, in sha Allah.  Ke kanki kin San yanzu bazan iya yin nesa da keba na tsawon lokaci.  So please ki kwantar da hankalinki,  ki kulamin da kanki,  yanzu zan sa hayder ya kawo miki su Aisha su tayaki zama, Kafin in dawo. Rungumeshi tayi, tare da sake masa kuka, Mai cike da shagwaba, tana dan bubbuga kafa. Tuni ya Kara rudewa, tausayinta ya kamasa. Rungumeta yayi sosai,  yana bubbuga bayanta a hankali.

Cikin murya Mai zaki, cike da shagwaba " how can princess survive without her king? 2 days it's like 2weeks to me "

Dago kanta yayi, yana murmushi, tare da kada mata kai, alamar tabar kukan.  Bakinta takai kan nashi ta fara aika mai da hot kissing,  sun kai 10min suna abu daya. Dakyar ya samu yayi controlling din kansa, don ya san plan tayi don ta hanashi tafiya. Da gyar ya zameta daga jikinsa, tana Kara narkemasa. 

Har mota ta rakoshi, Sai da taga fitar su daga get din, ta juya, cike da kewar mijin nata. 

Hubby na zaune a falo, ita da yarinyar da take mata aikace aikace.  Ladi.  Suna kallon Hausa Film.  Su Aisha sukayi sallama.  Amsawa tayi cike da murnar ganin aminiyar tata.  Da sauri ta Mike suka rungume juna, suna ihe ihen murnar ganin juna.

" ke kam baki da kirki, ban ma san me yasa na wani tare ki ba?  A ce tun washe garin ranar da aka kawoni, da kika zo, ban sake ganin kafarki a gidan nan ba, yan zuma nasan da badan yayanki ba, da yau ma banga ko keyarki ba "

Dariya Aisha tayi " tuba nake matar yaya.  Dama nayi niyyar xuwa miki weekend,  ki tambayi yusra ma kiji, in baki yadda ba. "

Harararta hubby tayi " daga ke har itan ina nan daku,  Sai na shuka muku rashin mutunci.  Tunda baku da kirki"

" kiyi hakuri dama tare mukayi niyyar zuwa miki wuni "

Sai lokacin hubby ta Lura da abida, dake zaune kan kujera ta daura kafa daya kan daya, tana kadawa a hankali,  idonta na kansu, tana harararsu, cike da jin haushinsu.

" kiyi hakuri Anty abida.  Ban Lura tare kuke ba,  kwana biyu banga mutuniyar ba "  ta fada tana Kara sawa kusa da abidan fuskarta cike da faraa.

Kallon uku kwabo abida ta bita dashi, ta kwabe baki.  " naga alama ai " ta fada a ya tsine.  Hubby bata damu da yadda abida ke yatsine yatsine ba. Don zuwa lokacin tasan matsayinta a wurinta. Tun last zuwan abidan 5 days ago taga take takenta.  Murmushi hubby tayi tana gaisheta tare da tambayarta mutan gidan.  Kamar an mata dole take amsata, tare da jin haushin hubby ganin yadda tayi kyau cikin lokaci kadan.

" ina haydar din?  Kar ace a waje kuka barshi? " hubby ta tambaya tana kallon Aisha da suke magana da ladi.

" kema kin fi kowa sanin halin mutuminki, yana ajiyemu ya juya abinsa.  Dama da kyar ya yadda ya kawo mu"

Murmushi hubby tayi " Allah ya shiryi haydar da bakin hali,  na rasa inda ya samo bakar zuciya"

" jininku ne, kawai bai hadu ba, amma kowa yasan he's good boy" Aisha ta fada tana dariya

" arrogant boy dai " ta fada tana kin kimar jakar kayansu zuwa dakinta.

               *****************
"Yau wa, make some things delicious, kin san ina koyon girki ne, yanzu "  hubby ta fada tana kallon Aisha.  Dariya Aisha tayi " yafi miki ai, ina can ina tunanin yadda zaki Kare, don nasan banda indomie, farar shinkafa, sai supergettie, kika iya. Ina tausayin yayana, ya Saba da kwasar delicious food. "

Dukanta hubby tayi, "kin san yanzu na fara iyawa, yayanki na koyamin, next week zan fara zuwa catering school"

" so dama duk wannan kadifirin da fiffika da ake, baa iya girki ba!!   Amma dai anji kunya wallahi "  duk kansu suka juya suna kallon abida dake tsaye a bakin kofar kitchen din.

" haba ke kuwa, wane irin magana ce wannan.  " hararar Aisha tayi " ke Waya kasa dake? "

Hubby tayi murmushi, tare da ma Aisha alamar tayi shiru.

" Anty abida ke ya kamata ma kina zuwa kina koyamin wasu abubuwan please"

Tabe baki tayi da Jan dan guntun tsaki  " ki nemi mai koya miki, tun dare bai miki ba,  da can me ya hanaki ki tsaya ki koya?  Muddin dai mukaga Yaya na rama, mataki zamu dauka, Wanda ba zai ma yarinya dadi ba wallahi.  Meye anfanin macen da bata iya girkiba? "tayi tsaki tare da barin kitchen din. Tana kada jiki. Suka bita da ido, cike da mamakinta😶😶😶..........
"Don't mind her" Aisha ta fada tana kallon hubby. Murmushi hubby tayi , tare da kada kai. "Me zamu girka Ne?"

"Ehmmm!!! Fray rice, chicken deise, natural mango juice."

"Good idea" hubby ta fada tana murmushi. " ni fa zanyi kawai ki dinga nuna min yadda zanyi"

"Lallai Matar Yaya a serious, hakan ya Nuna min yadda ake ji da yayana, I'm so happy about that."

" I will do any thing for My king "

Dariya Aisha tayi " su King many a, Allah ya bamu masoya na Kwarai muma muji yadda ake ji, ko ma huta da iyayin hubby "

Murmushi hubby tayi, " amin dai in da gaske kike. Kuda kuka CE sai kunga karshen Biro, tukunna"

" in sha Allah  kam, sai na zama doctor Aisha Jamal Yusuf Oregon."

" Allah yasa"

" ya labarin karatu? Ko har yanzu kina nan akan bakanki?"

Tabe baki hubby tayi " Ku dai da kuka kwallafa ranku, kuyi tayi. Hubby kam aure bautar ubangiji ta zaba,."

" ilmi Nada dadi , ki daure ki ko ma school ko Kettering kiyi, zai anfaneki sosai a rayuwa. Ki daina bin zugar gwaggo don nasan duk hudubarta CE kike bi."

" in muna magana ki daina sako gwoggona a ciki, raayina ne ba ruwan gwaggo. Zan dai ko ma islamiyya, don inji dadin Neman Aljan'nata"

Haka Aisha taita nuna mata yadda zatayi, suna hirarsu gwanin shaawa. Har suka gama girki.

" uhmm!!!! Gaskiya randa hannunki ya fada a girki, yayana zai kwashi gara. kinji yadda girkin yayi dadi?"

Dariya hubby tayi " bar zugani yar uwa, a dai ci da hakuri kawai."

" da gaske nake, ba wasa ba "

" thanks, irin shi zan Ma king ranar da zai dawo "

" good idea "

                  ****************
Suna zaune a falo bayan sun gama kwasar girki. Abida na dakin hubby, don tun da suka mata tayin abinci, ba Wanda ya kara bi ta kanta.

Kallon kallo aka fara tsakanin hubby da Aisha. Abida CE ta fito daga dakin Yusuf daure da towel, ta Shiga dakin hubby minti kadan ta sake fitowa ta koma dakin Yusuf.

Mamakine ya cika hubby, tabbas dakin a kulle yake ,ta Yaya abida ta samu keys din har ta bude? Ke nan bincike ta mata a daki? Dole ne ta taka mata burki don taga alamar in ta ci gaba da yi mata kawaici, ba karamin takata za tayi ba."

Mikewa tayi ta nufi dakin Yusuf din, ranta na zafi,.

Zaune ta sameta kan stool din gaban madubi tana kwalliya, kallonta tayi cike da raini ta ci gaba da abinda take yi.

" duk dakunan dake gidan nan ki rasa India zaki baje hajarki sai nan? Bayan na tabbatar kin San hakan bai dace ba"

Kallon sama da kasa tawa hubby " au!! haba? Ashe bai dace kanwa ta shiga dakin yayanta ba? A wace mashabar kenan? Don bani da masaniya"

" ki Sani yanzu ba da bace, dakinsa sirrinmu ne, baya halatta gareki shigansa ba tare da iznin daya daga cikinmu ba. Wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaki shigomin dakin miji kai tsaye, zan day komai amma ba zan yadda da tozarci ba"

" ke har kin isa ki hanani shiga dakin Dan uwana? Da har kike gindaya min sharudda. Kin yi kadan wallahi"

" kar ki yadda Dan sauran mutuncinki da nake gani ya zube, tun nuna shaida juna ki fita a dakin nan in ba haka ba, abun bazai mana kyau ba."

Duk da abida ta tsorata da yanayin hubby, amma taurin rai ya hanata koda motsi daga in da take.

Basu ji shigowar Aisha ba, sai maganarta da suka ji duk suka juya suna kallonta. Cikin harshen larabci ta farama abida magana " me yasa zakiyi haka? Kin San cewar hakan bai dace ba, Yaya ko lokacin yana gida baya yadda mu shiga masa daki balle yanzu. Kin manta fadan mom kenan? Duk gargadinmu da tayi amma na lura tun da suka zo kike nemanta da magana, bakya ko tsoron bacin ran Yaya, don muddin kika batama matarsa kamar kin bata nasa ran ne. Ina rokonki da kiyiwa Allah ki rufa mana asiri mubar gidan nan lafiya. "

Jikin abida yayi sanyi, musamman data tuno irin farin cikin da ta gani a fuskar Yusuf lokacin da race itama zata biyo Aisha suzo tare, har alkhawarin sabiwar waya ya masu. Tabbas ko lokacin da take gida tun da suka fara tasowa ya hanasu shiga dakunan samarin gidan. Amma ya zatayi da dunbin haushin hubby da take ji? Hakika batason yarinyar ko dama can balle da ta zama sanadin rashin auren kawarta, yar uwarta da Yusuf.

Kayanta dake kan madubin ta tattara, cikin jin haushi,. Ban gaje hubby tayi tare da Jan tsaki ta fice a dakin. Jingina hubby tayi da bangon dakin ta runtse idonta tana ambaton sunan Allah. " kin ci daraja daya, yau da kin gane ko wacece hubby, gobe ko an ce kiyi min iskanci bazakiyiba" ta fada a ranta tana Jan numfashi.

Aisha CE ta dafa kafadarta " I'm very sorry, Anty abida bata kyauta ba, amma don Allah kiyi hakuri"

Murmushi tayi " it's OK "

Bayan fitar Aisha tabi dakin da kallon. Tsaki taja, iskancin abida har gadonsu sai da ta hau, ga alamar zama nan, gyara dakin ta karayi, ta nufi toilet anan ranta ya kara baci ganin kunfa ko Ina ga ruwa duk an zubar a kasan tails din, kamar ba bap a toilet din. Sai da ta tabbatar ta gyara ko Ina, ta saka turaren wuta, ta kulle dakin.

A falo ta samesu, Aisha da Ladi na ci gaba da kallo, abida na kan dinning sai lokacin take cin Nata abincin. Direct wurinsu Aisha ta nufa, suka ci gaba da shaaninsu, like notting happen. 

              ***************

" wai me kuke nufi ne? Bafa zata sabuba, in ci abinci da rana in sake ci da daddare." Da kallo suka bita, tana kwance a kan 3 sitter rike da wayarta.

Aisha ce ta bata amsa da cewa " a kawai sauran abincin da zai ishesu, ba sai sun yi west din abinciba,"

Harararta tayi " bashi nake son ci ba, don kinsan ko a gida, bancin abinci sau biyu, naci da rana, ya isa Ku tashi Ku nema min abinda zanci."

" ki dai ce in tashi, ita kam ai yanzu Matar Yaya ce, sai dai mu mu girka mata, ba Musa ta girka mana ba."

Cikin larabci abinda ta fara masife Aisha " kefa naga wani raini kike son kawo min tunda muka zo, ki shiga hankalinki dani, ita har ta isa in shiga kitchen in mata girki? "

" Allah baki hakuri, me zan dafa mini?"
" tsaki taja, barshi banso aikin banza kawai , baa iya komaiba sai kadifirin tsiya" ta fito da wayarta tayi searching number tare da barin falon tana harararsu.

Hubby da tunda suka fara ta dauke kanta kamar bata  falon. Don gaba daya tun da taga take taken abida, ta fita hanyarta, duk da Dama itama ba wani shiga harkarsu take yiba.

" me kikaga ya kamata a dafa mata? "

Kallon hubby Aisha tayi " rabu da ita kawai, in yunwar ta kwakule cikin ta nemi abinda zataci, Neman maganane kawai, ko a gida ba wani abinci take ci da daddare suya

Suna nan zaune abida tazo ta wuce su.

" Anty abida ina zuwa?" Aisha ta tambaya tana gaf da fita kofar da zai sadata da waje.

" in da kika aikeni " ta fice a Bin ta.

" Allah ya kyauta, nasan wannan Dan iskan saurayin Nata ne yazo, shi yasa ta nace ta biyoni, tasan in a gida ne bai isa ya taka kafarsaba."

Hubby kam shiru tayi abinta, don bata son shiga hurumin da ba nata ba. Kusan 30 min sai gata ta dawo dauke da ledoji farare masu dauke da tambarin special suya.

Ladi ta kalla cike da raini " ke maza ki hadomin tie, sauran kimin kazanta."

Duk Kansu ba Wanda yabi ta kanta. Wayar hubby ce ta fara ringing, ganin mai kiran yasa ta daga, tare da nufar dakinta, don ta samu dama da sakewa tayi hira da King dinta. Wanda take cike da kewarsa.

" hello princess, how's your day? "

Tura baki tayi kamar yana kallonta cikin muryar shagwaba da Jan hankali " boring!!! I miss my King so much, how are you "

" how can I be fine, without u by my side"

Murmushi tayi cike dakin dadin kalamansa.

" ya sokoto? Bayan kasha fura, kaci bula, da kilishi, ina zaka ita tunawa dani? Tun dazu nake expecting call dinka shiru, na kira ka yaki shiga."

Dariya yayi, cike da jin dadin ya ce " very sorry tunda na shigo garin nan, sai yanzu na samu natsuwa, ga network ba kyau.

Hira sukayi sosai, mai cike da nuna so da kauna, ko wanne yana kokarin nuna yan da yayi missing din dan uwansa.

                *****************

Yanzu nan da ku ka baje ina zan kwanta? Aisha ta kalleta tare da kara matsawa kusa da hubby. " wannan wurin ai ya isheki " tsaki tayi Allah yasa akwai mai banzan bacci a cikinku in koya mata hankali wallahi."

Shiru suka mata, don sun San duk neman magana takeyi. Hubby ce ta musu sai da safe....

               ******************

Yau 1 year ke nan da auren hubby da Yusuf, abubuwa da yawa na dadi, da akasinsu sun faru. Zama lafiya da kwanciyar hankali tare da tsantsar so da kaunar juna, kamar sa hadiya juna.ke tsakanin hubby da Yusuf, har lokacin hubby ko batan wata bata yi ba. Wanda ya kara hura wutar kiyayyarta a zuciyar dangin Mmn Yusuf. Hatta Mmn Yusuf din da take sassaucinta wasu lokutan, itama yanzu ta fara nuna damuwarta. Ganin duk Wanda sukayi aure a tare duk ko wanne nada dansa.

Su haidar sun tsufa a Cyprus, in da suke karatu a Cyprus International University ( CIU ) shida friends dinsa. Inda yake karantar Computer science.
Shida junaid, sai Alim da Hafiz health science, Hafiz omer da Ashir Jamil medicine.

Aisha na Kaduna state university ( KSU) tana karantar health science, yusra na karantar geography.

Hubby dai an samu da kyar anyi training na Kettering na 3 months. Yusuf yaso tayi joining dinsu Aisha tunda result dinta yayi kyau, amma ta nuna bata shaawa. Ganin hakan yasa ya rabu da ita.

Islamiyya dake unguwarsu ta shiga daga 10 to 12. Mummy ta tayi fada sosai kan kin ci gaba da karatunta amma ko a jikinta. Don harga Allah karatun boko baya gabanta, tunda ta samu na karatu da rubutu and she can speak very well ai shi kenan.  

               ******************

Gaba daya hankalinta a tashe yake, hada Maya kawai take tana tunanin yadda zata kwashe tsakaninta da yan uwan Mmn Yusuf, a Nigeria ma ya ta kare dasu balle kuma ta bisu har Niger. Niger din Ma bikin wadda itace tushen tsanar tata da sukayi. Babban damuwarta kasan cewar ba tare zasu wuce da Yusuf ba, Mmn Yusuf ta kasa ta tsare lallai sai ta bisu su wuce tare. Shikuma sai ana gobe daurin aure zasu iso da daddynsu.

Aisha ma bazata samu damar zuwa ba, don suna tsakiyar semester. Abu ya hade mata goma da shirin. At lest da da Aisha zatafi jin dadi da sakewa. Don duk sauran matan dakin su Yusuf ba shiri suke yi dasu ba.

Gin gine yake a jikin kofar dakin yana rungume da hannu idonsa na kan duk kan movement dinta. Ita kanta bata San da shigowarsa ba. Kallonta yake cike da tausayawa, ya lura tun da magana tafiyar nan ta taso, bata da walwala. Duk da tana kokarin boyewa karya gane halin da take ciki, wani sonta yaji ya kara mamaye zuciyarsa. Duk halin da take ciki da yan uwansa ba Wanda bai Sani ba, hatta da danben da suka kusa kwasa ita da abida, a gidan Ahmad yana da labari, amma dai dai da rana daya bata taba kawo mai kara ko korafin duk abunda zaa mata ba.

Shi kansa zai so su tafi tare, amma ya ya ita dole yabi umurnin mummynsa, sai gargadi da Jan kunne da yama kannen nasa. Daga baya ya hada da lallashin su kula masa da ita sosai.

Murmushi ta sake mai, lokacin da idonta yakai kansa, da gudu tazo ta dafeshi, bai yi wata wata ba ya cabeta sama ya fara juyi da ita kamar yadda ya saba, suna dariya...........

   
Not Edited.......
 [01/03, 10:38] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 6 · 0% Book details