← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 26 OF 28

                            Part 24

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 17 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau
   
Not Edited.......

Kallonta suke cike da gamsuwa da jawabinta. Hannunta dake cikin na hubby Asiya ta kara rikewa da kyau. murmushi tayi mai karawa fuskarta kyau da kwarjini. Asima zatayi magana Asiya ta dakatar da ita, da alama da hannu.

" I agree with every word u say. Amma da gaske nake na hakura, shawara daya zan baki, no matter how the situation is karki kara cewa wata ta auri mijinki, at the end u regret it. Baki san kishiya ba!! My be don baki ganta a gidanku ba. Shiyasa. Mu da muka tashi muka ganta munsan illarta, da alkhairinta. Bana ma kaina fatan ta, in dai ba kaddara ba, wadda baka wuceta. Nasan ko baki son hayder yanzu, na lokaci kadan ne, tun da har kika so Yaya Yusuf, na tabbata in no time zaki samu zuciyarki cikin kaunar hayder.
A halitta suna matukar kama, in kin dauke tsayi, da suffar karfi da hayder ya fi Yaya Yusuf. Sai ban bancin ido. Na Yaya Yusuf manya, na hayder madai daita. Sai dimples da Yaya Yusuf bashi dashi. Amma hatta muryarsu, da tafiyarsu kusan iri daya ne. Ta Yaya zaki iya kin son hayder bayan kamman nin da ke akwai tsakaninsa da Yaya Yusuf? Ga kuma jini da kuka hada! Halayyarsu wani zaki iya samu iri daya, wani kuma sabanin hakan. Hayder yana da zafi, sabanin Yaya Yusuf mai sanyin hali. Ki nutsu, ki rungume mijinki, ki rike aurenki. Kar kiba kowacce shegiya shigowa cikin rayuwarku."

" abin harda zagi?" Hubby ta fada tana murmushi

" baki san yan matan yanzu  bane shi yasa, bamu da dadi ko kadan. In mun shiga kokari muke mu fitar data ciki. Don haka ki rike wuta, ko wannan kodaddiyar kiyi kokarin mantar dashi ita."

Dariya sukayi baki daya. " baki da kirki Asiya, Nasrin din ce kodaddiya? Bari ya jiki kina kiran Sweet heart dinsa da kodaddiya" Hubby ta fada tana dariya

" ai ba karya nayi ba. Ke na lurama Sam baki kishi, bayan ansan mata da kishi, koda ko basa son abu, sukan nuna kishinsu." Asiya ta fada tana rike baki.

Asima dake sauraronsu tana murmushi ta ce " ki barta very soon zakiji Anty hubby ta saka gajeren wando."

Dariya sukayi gaba daya. " Allah ya kyauta." Hubby ta fada tana nufan kitchen.

" kin san dama duk soyayya mai tsafta daga kiyayya ake farata, mun ji labarin naku mafarin, zamuga how u end up. " Asima ta fada tana dariya

Asiya ta kalli Asima tana murmushi " na gode da shawararki uhtee, jhazhakallahu bi jannah."

" ba komai, amfanin yan' uwantakan kenan. Muba juna shawarar da zata anfane shi, lokacin da yake cikin matsala. Allah yasa haka shine mafi alkhairi a gareku baki daya. Amma menene anfanin son maso wani?"

" koshin wahala kam. Allah ka hadamu da masoyanmu na gaskiya." Asiya ta fada.

" Amen uhtee!.." Asima ta fada dai dai lokacin da hubby da Mariya ke shigowa da wormers din abinci. A dinning suka jera komai kafin hubby ta kallesu tana murmushi " bisimillah "

Mikewa asima tayi " kamar kin san kamshin abincin nan ya gama cika min hanci, Allah Allah nake a gama. Sam bana juriya yunwa yanzu." Asiya ma bayan Asima tabi suka zauna. Asiya ce tayi serving dinsu. Suna ci suna hira da dariya, gwanin sha'awa.

" ban labarin new catch!! " hubby ta fada tana kallon Asiya

Murmushi tayi " ba yanzu ba, sai komai yayi normal zakiji." Bata rai hubby tayi. Dariya Asiya tasa " bafa abinda kike tunani bane!! Na fi son sai komai ya dai daita, zanzo da kaina na baki labari, ba sai a waya ba. Nasan kuma zakiji dadi sosai!"

Kada kai hubby tayi " Allah ya sa! Ya zaba mafi alkhairi."

" Amen." Suka fada baki daya

" kira junaid, ya kamata mu leka gidan Yaya Ahmed. " Asima ta fada tana kallon Asiya

Tashi tayi, ta nufi jakarta, ta dau waya ta kirashi.

" dama shi ya kawoku, amma bai shigo ba?" Hubby ta tambaya

" eh! Sauri yake, su hayder na jiransa."

Kada kai hubby tayi. Sun gama suka tattara wurin, tare da wanke kayan da sukayi anfani dashi, sunayi suna hira.

Dakin hubby suka shiga, don gabatar da sallar la'asar. Sun sakko kenan junaid na sallama daga bakin Kofa.

" yasu mommy? " hubby ta tambayi junaid cike da kewar iyayayen nata.

" lafiya kalau, dady ne bai ji dadi ba kwana biyu, amma yaji sauki."

Cikin damuwa ta ce " amma shine aka rasa wanda zai gayamin?"

Murmushi junaid yayi " kiyi hakuri, kin san daddy in bashi da lafiya ba son a fada yake yiba."

" duk da haka, ai ni ba bare bace, balle a kasa gayamin." Ta fada cike dajin haushi

Ganin ranta ya baci, ya shiga bata hakuri. " it OK, ka gaishesu sai nazo!" Ta fada tana rakosu wurin motarsa.

Ledar dake hannunta ta mikawa Asima dake baya. " godiya sukayi mata, junaid yaja motar suka tafi.

              *********************
Hayder ta kira, tana son zuwa gida. Bai hanata ba, ya ce ta jirashi, zai zo sai su dawo tare. 5pm ta nufi gidansu cike da jin dadin yau zataga daddy dinta, don sun dade basu haduba sai a waya.

             ***********************

Ta fito wanka kenan idonta ya sauka a kan wata kyakyakyar traveling bag, pink a kan gadonta. Wurin ta nufa, tare da zage zip din, ajiyar zuciya tayi, don ta dan tsorata, tunda bata san da ita ba.
Laffaya less ne masu kama da saree kusan guda 5, sai irin rigunan India da ake hadasu da jeans 3 masu matukar kyau. 2 set na Indian gold, sai Indian fashion, yankunnaye warwaro, besleet, zobuna, Indian perfumes, Sai riga da wando set 2. Murmushi tayi tasan aikin hayder ne, don shine ya dawo daga India kwanan nan. Zip din taja ta rufe ta dauke bag din ta mata wuri a woodruff dinta.

Taji dadin kyautar don kayan sun burgeta matuka.

Sai da ta gama shirin baccinta tsaf ta nufi dakin hayder. Kamshi mai dadine ya bugi hancinta, ga sanyin AC. Ba kowa a dakin, jikin mirror dinsa ta nufa tana kallon kayan shafansa masu matukar tsada. Idonta ne yakai kan turaren da Nasrin ta masa kyautarsa a Cyprus. Dagawa tayi tana juya kwalbar, tare da zare murfin tana shin shinawa. Da sauri ta zareshi a hancinta. " ouch!!!." Ta fada tana maidashi. Don ji tayi ya balain hawa mata kai, sabanin farkon ganinshi da kamshin ya mata dadi.

"What are u doing with my special perfume?" Ya fada yana takowa inda take tsaye, sanye da rigar wanka, fara Sol.  Wai gowa tayi tana kallonsa tare da tabe baki. " turaren da yake wari!" Ta fada a shagwabe

Ido ya zaro " turaren nawa ke wari.?" Daga ido tayi tana yamutsa hanci.

Hannunsa ya kai ya dau turaren." Kinsan yadda nake sonshi kuwa?" Ya fada yana sashi a kan kirjinshi, dake bude. "Ina son shi sosai." Ya fada yana kashe mata ido daya, Tare da daga mata gira daya.

Shiru ta masa tare da daukar wani turaren, Bufewa yayi zai fesa. Da sauri ta kwace a hannunsa. Mika mata hannun yayi ta bashi, ta makale kafada, tare da maida hannnta baya. " ban son warinsa." Ta fada a hankali cikin siririyar muryarta.

Hannunsa duka biyu ya daga sama, kamar mai kiran sallah. " sorry!!!! Na manta fah! Yanzu kin zama tabani kaga sarki."

Body lotion dinsa ya dauka, hannunta ya kamo ya danka mata. Kallonsa tayi, ta kalli lotion din. Gira ya daga mata ya zauna a chair din mirror.

Murmushi tayi ta fara shafa mishi, cike da natsuwa, Lumshe ido. Mikewa yayi tare da  rungumota ta baya,

ji numfashin shi na sauka kan wuyanta, tana juyawa kaman predator ya Kama bakinta da nashi bakin,  idanu hubby ta lumshe. hannunshi biyu yasa ya riko waist dinta tare da danneta da kirjinshi giving the access of her chest pressing he's chest then he's hand on her well shaped hips,  hannu biyu tasa ta zagaye west dinsa dasu.  baya baya ya dingayi har saida ya kai bakin gadonsa ya zauna, ya Kama bakinta gan kaman cikin nasa ba tare da ya Saketa ba,  he was pushing he's tongue deep that jikinta ya saki  bayan kanta ya rike da hannu daya sannan ya dora dayan hannu kan chest dinta not massag dinsu a hankali, cikin kwarewa. kaman ya samu sweet haka ya dinga shan bakinta, sakin bakinta yayi, ya zare bakinshi, cikin nata,  idanuwansu cikin na juna,   wani kiss ya Dan dora a kan lips dinta.

A shagwabe hubby tace " please hayder let me sleep, jikina ba karfi."

A kunnenta ya rada mata cikin husky voice dinsa.  " bari in baki maganin karin karfi, da kuzari." Kafada ta makale. " please mana!!!" Shima kwaikwayon muryarta da yadda tayi maganar yayi " please habiba.!!!!" Dan harararsa tayi " banson habiban nan, ka kuma san haka!." Hancinta ya lakace " I call u Habiba because it your name. "

" call me Ummi kamar yadda su mommy ke kirana, in bazaka kirani da hubby ba." Ta fada

Smacking yayi, " nafi jin dadin Habiba."

Duka ta kai masa a kirji " ka gama rainani completely! Koda yake ba laifinka bane."

Gira ya daga mata " who's fault? " tura baki tayi, cikin shagwaba " it's my fault."

Still fuskarsa na dauke da smacking " u amazed me some time,!" Ya fada yana kara rungumeta a jikinsa.

Ido ta lumshe cike da  kunya ta fara shafa sajensa daya kwanta gwanin shaawa. Ganin hakan ya kara lafewa cikin jikinta, ya fara aika mata da samun ninsa masu wuyar fassaruwa. Gaba daya kowa na kokarin faranta ran daya, na dogon lokaci, kafin suka sararawa juna, bayan kowan nensu ya samu cikakken gamsuwa. A kunnenta ya rada mata "Allah ya miki albarka, Rabbi ya cika miki rayuwarki da farin ciki."

Lafewa tayi a kan faffadan kirjinsa, tanajin bugun zuciyarsa na harbawa kan nata, a haka suka dau lokaci kafin suka mike don tsarkake jikinsu. Daukanta yayi bridal style zuwa toilet din.

A toilet dinma sun dade suna romancing juna, kafin sukayi wanka suka fito.

Kwanciya tayi tana " wash Allah nah!!". Tana yamutsa fuska da tura baki.

" wayyo jikina duk ciwo yake." Ya fada yana kwaikwayon maganarta, yana rike baya.

Harararsa tayi, ta dau filo ta wurgeshi dashi. Chabewa yayi ya jefa mata kan fuskarta " lazy Bone's. " ya fada yana saka kayan baccinsa.

Kwafa tayi " zaka dawo ne." Ta fada cikin dan jin haushin lazy Bone's din daya kirata dashi.

Kunnensa duka biyu ya rike " afwan!!! Amin ko wanne horo amma banda wannan!! " yana murmushin gefen baki.

" zaka ga lazy ganin idonka." Ta fada tana kara gyara kwanciyarta. Kusa da ita yazo ya kwanta, tare da janyota jikinsa. " I say I'm sorry ko.?"

Kirjinshi ta fara shafawa a hankali. " naga kaya a bedroom dina?"

Kiss ya manna mata a goshi," its for u"

" na gode, Allah ya saka da alkhairi. " ta fada still tana shafa kirjinsa a hankali.

Yaji dadin adduarta sosai. Mannata ya karayi a jikinsa, kafin sukayi adduar bacci,. A haka suna dan wasa da juna har bacci ya kwashesu.

           **********************

Sun gama break fast, hayder ya mikawa hubby ticket. Amsa tayi tana dubawa, Dagowa tayi ta kalleshi. Yana jingine jikin kujera yana shafa sajensa. Fuskarsa dauke da smacking.

Hade fuska hubby tayi, " no way?" Ta fada tana mikewa...........

Kallonta yakeyi fuskarsa dauke da smacking, Ticket din ta ajiye a gabansa. Tare da zuba masa harara, baki ya tabe ya dauki ticket din yana kara dubawa.

" gobe zamu tafi, pack your bag and get ready." Ya fada in husky voice dinsa

" sai ka dawo!! Ba inda zani." Ta fada tana tura baki.

" kar muyi haka dake! Kefa kika ban wannan shawarar to meye laifi don kin tayani na gyara kuskiren da kike ganin nayi?"

" Allah kama gama rainamin hankali. Gotai gotai dani, zan rakaka zance? Bama a nan ba har Egypt, saboda bani da aikin yi? Ko ce maka akayi cewa tayi inje na gani?"

Murmushi yayi mai sauti, " we shall see to it." mikewa yayi ya dau ticket dinsa, sama ya haura cikin gudu -gudu, sauri -sauri.

Da harara ta rakashi, kafin tayi kwafa.

               *******************
Yau gaba daya gidan bai mata dadi ba, daga ita sai Mariya, yau ko bakin ma da suka saba zuwa yau babu. Hayder kam tunda ya fita da safe har zuwa lokacin to 5 bai shigo ba. Dole haka hubby ta sallami Mariya ta tafi gida, don lokacin tafiyarta yayi.

Tana kwance a kan sallayarta data idar da sallar isha'i. Tunani ne fal zuciyarta na rayuwa, sai lokacin ta fara tunanin magan ganun Asiya. Tabbas gaskiya ta fada mata. Don tasan ada ba wacce tafita kin kishiya. Tunowa da kishinta kan Yusuf, wanda ko kallon mace wadda ba muharramarsa ba, bata kauna taga yayi, balle magana. Yan matansa na family da wanda ta sani, gaba daya bata Shiga shirginsu, bata basu fuskama balle su kawo mata wargi.

Tsaki taja, tunowa da yadda hayder ya dage maganar zuwa Egypt. Ita bawai kishin Nasrin takeyi ba, don tare ta gansu. Amma ta yaya don ya raina mata wayau, wadda bata san abinda  takeyi ba, ta rakashi zance. Ita a tarihima bata taba ganin inda mata take raka miji zance ba, ba kuma zaa fara a kanta ba.

Lokaci yayi da zata kama mutuncinta. Tabbas ko bata sonsa, mijinta ne, uban yayanta. Duk wadda zai auro, ko tanason ko bata so, dole ya shafeta, ya kumayi tasiri a rayuwarta data yaranta. Sai ma tafi tasiri a kanta sama da yadda zatayi akansa shida ya aurota. Ya zama wajibinta ta sa su a adduarta, in alkhairi ne shigowarta rayuwarsu Allah ya tabbatar in ba alkhairi Allah ya masu canji na alkhairi.

Cikinta ta shafo, da har lokacin ba alamar tasowarsa, sai tauri da wurin yayi. Wani dadi da natsuwa taji suna ratsata for the fist time.

Tunowa da yadda Yusuf ya kwallafa ransa don ganin kwansa, A duniya. Kana naka Allah na nashi.wane irin farin ciki zaiyi in da ta samu ciki dashi? Wane irin so da tattali zata gani? Ta tabbata ko sarauniyar England bazata fita samun kulawa da tattaliba.

Hakika soyayya wani jigone, a rayuwar aure, duk auren da babu soyayya, dole zaka samu akwai tawaya a tattare dashi. Duk jin dadi da kulawar dake cikinsa.

Yanzu take jin son cikin jikinta, koba komai ta samu abunda zai sata farin ciki, da debe kewar masoyinta. Allah yasa namiji zata Haifa, ta nemi alfarmar koda hayder beyi niyya ba, yasa mata sunan masoyinta, balle a yadda shakuwar dake tsakaninsu ta San zai yi wuya ya kasa sa sunan."

Kuka sosai yazo mata,. Bataji shigowarsa ba, sai kamshin turarensa. A hankali ya tako zuwa inda take kwance saman daddumar sallah tana kuka, don gaba daya zuciyarta ta karye. Zama yayi kan lallausan carpet din dakin, tare da daddagota, ya daurata a kan cinyarsa, yana tare da rungumota jikinsa. Kara shigewa jikinsa tayi. A hankali ya dinga lallashinta, cike dajin tausayinta. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana lafe a jikinsa.

Sai da ya tabbatar ta samu natsuwa tukun.

" are u OK." Ya fada cike da kulawa. Kai ta kada masa.

Dagata yayi suka shiga toilet. Dayake shigowarsa kenan yaji zuciyarsa ta kasa natsuwa, yayi dakinta, sabanin da da bedroom dinsa direct yake wucewa. A tare sukayi wanka, shiya taimaka mata ta shirya cikin kayan baccinta, masu kyau da laushi. Dakinsa ya wuce daure da towel dinta don ya shirya.

Kitchen ya nufa don samawa cikinsa wani Abu don yunwa yakeji. Da yake bata cika ajiye masa abincin dare ba, saboda baya dawowa dawuri, in ma ya dawo baya bin takan abinci. Sau da yawa a main house yake cin abincin darensa, kafin ya wuce daukan karatu.

Dakinta ya nufa da trey dinsa. Tana kwance a kan bed, still fuskarta akwai damuwa, da rashin walwala.

Kujera ya jawo ya daura trey din a kai, ya zauna kusa da ita.

chicken salad, sai natural fruits juice, Kallonta yayi, da yanayin data kasa fassarashi. Dagota yayi, ta zauna sosai, salad din ya diba, yakai bakinta. Kauda kanta tayi, tare da kada masa kai.

Murmushin gefen baki yayi " ki ci, basai kin biya ba, tunda da kaina na baki."

Kada kai tayi " na koshi." Ta fada

" na dauka tsoro kikeji, kar ince sai kin biyani." Ya fada still da murmushi a fuskarsa.

" da can ma da naci ban biya ba, balle yanzu!! In ina so ci zanyi, ba yadda ka iya dani." Ta fada tana gyara kwanciyarta.

" kin dai manta, anma ba abincina da kikaci da baki biya ba." Ya fada yana cin salad din.

" sai ka tunamin ai!!"

" na school, kin biya da chocolate da sweet dinki. Food dinki dana friends dinki." Ya fada yana daga mata gira daya " right. ". Harararsa tayi. " ka biyani chocolate dina ai!! Tunda gasu nan a kitchen sai wanda nakeso in sha." Ta fada tana murmushi

" kifina da kika ci, da chips, suma kin biya With high price. " ya fada yana smacking

" ni ban biya ba! In don girkin da nake maka ne, bawai don in biyaka nakeyi ba malan." Ta fada cikin shagwabarta

" really!!!! Ke adole kin dauka bulus kika ci? I keep it they intentionally. Its a trap!" Ya fada

Tashi tayi ta zauna, Kallonsa take tana mamakin maganarsa. " why do u say that?" Ta fada tana rike habarta tare da daga masa gira duka biyu.

Sagensa ya shafa yana Kallonta, smacking yayi " Allah ne ya soki, da mage ta koromin ke!! Amma da trap dina ya kamaki?" Kada kai yayi tare da hadiye sauran maganar yana dari ya kasa -kasa.

Ido ta zaro cike da mamakin maganarsa. " hayder wane muguntar ka shirya min?" Ta fada tana tsareshi da ido.

Tabe baki yayi " ki dauka dama kazar da kowanne ango ke kaiwa amaryasa ranar da zai tare da ita, Kikaci. Koda mage bata koroki ba, nayi niyyar amsar hakkina a ranar, Your under my plan, Allah ya kwaceki. Kika kawo kanki cikin salama."

Rasa abinda zatace masa tayi, har ya gama ya fita da kayan binsatake da kallo.

Dakinsa ya wuce, ya tsaftace bakinsa tare da kara fesa turare, na baki dana jiki. Ya nufi dakinta. Har lokacin tana inda ya barta.

" please hayder me ka shirya yimin a ranar?" Ta fada

" forget about it," ya fada yana yarfe hannu daya.

"Amma kace ba kai ka turo min mage ba?"

" yes!"" Ya fada yana kallon kwayar idonta.

" ki gode ma Allah magen taimakonki tayi." Ya fada yana kwanciya kusa da ita. Hannu yasa zai rungumota ta bige hannun.

" uchh!!! " ya fada yana yarfe hannu. " don't u dare touch me, again." Ta fada cikin fushi.

" OK." Ya fada yana smacking tare da gyara kwanciyarsa sosai, kanshi na kallon sama, hannayensa duka biyu a hade kansa na tsakiyarsu.

Kallonsa tayi, tana jin kamar ta mari fuskarsa, saboda haushin murmushi rainin hankalin dake kan fuskarsa. Kwanciya tayi ta juya masa baya. "Amma kinsan ba kyau juyawa miji baya ko?" Ya fada in husky voice banza tayi dashi.

Tafiyar tsutsa ya fara mata a bayan. Hannunta tasa ta buge hannun again.

" gobe flight din  rana zamubi ki tabbatar kin shirya kafin 11, don ta abuja zamubi.

" sau nawa zan gaya maka, bazan jeba."

" yes u tell me. But look!!! Bana son gardama do as i say." Ya fada in high tone.

Shiru tayi, tana jin hawaye na kara cika mata idonta.

" kar dai maganar tafiyan ce ta saki kuka dazu?" Ya fada still in high tone

"Na tuno da masoyina ne, mai son farin cikina." Ta fada cike da takaici.

" good for u!! Amma ki Sani kin aikata haram, da aurenki, kike tunani fast love life Dinki?" Ya fada in his husky voice

" har kanada bakin da zaka fadi haka? Kai yanzu abinda kake shirinyi, a ina ka taba ganin anyi haka? Ina matarka ka rasa wanda zai rakaka neman aure sai ni? A ina ka taba jin anyi haka?" Ta fada still tana kallon gefe, ba tare data juyo ba.

" its not a big deal!! Zaa fara a kanmu."

" sai ka nemo Janeway ka jani ai!!!" Ta fada

" no need for that, da kafarki biyu zamu tafi. A u jealous of her ? "

" never." Ta fada

"U love me, bakya son ganina da wata, zuciyarki zata buga, bazata iya dauka ba. Is that your reason?" Juyowa tayi tana harararsa " Allah ya kiyaye, in tsaya ina kishinka! Kawai I don't want to go with u."

Tabe baki yayi, yana Kallonta. Murmushi ne ya kufce masa ganin yadda ta daure fuska, wai ita ranta ya baci.

" just sleep! I don't want your trouble, bayan ina cikin farin cikin ganin sweet heart tomorrow. "

Ya fada yana jawota jikinsa, tare da lushe idonsa. Kokari take ta kwace daga jikinsa ta kasa, dole ta hakura. Hannunsa na kan cikinta yana shafawa a hankali, har bacci yayi awan gaba dasu.

             *********************

Duk yadda hubby taso kaucewa binsa Egypt abin ya ki yiyuwa. Hayder akwai naci da tsayawa kan maganarsa. Dole tana ji tana gani suka nufi Abuja daga nan jirginsu ya daga zuwa Egypt. Su mommy Hauwa sai a waya ta musu sallama, don daga gidan Hajiya direct suka wuce abuja.

Da mamakin hubby tunda suka isa Egypt, yana tare da ita, in basa room dinsu a hotel din da suka sauka, to sun fita ganin wuraren tarihine, ko shopping. Shiru shiru taji ya mata maganar zuwa wurin nasrin taji shiru. Har ta kasa yin shiru, ta tambayeshi.

Bai ce mata komai ba, in banda murmushi da yayi mata, ya share zancen

Iya murzuwa hubby ta murzu a wurin hayder cikin kwanaki 14 da sukayi. In ka gansu gwanin shaawa baka taba cewa ba soyayya a tsakaninsu. Don wani kulawa da tattali suke ba juna na musamman.
Satinsu biyu suka tattaro zuwa kasa Nigeria, kowa yabar gida - gida ta barshi. A dade anayi sai naija...........

 [12/03, 12:42] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 26 · 0% Book details