← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 24 OF 28

                            Part 22

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 21 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau
   
Not Edited.......

Shiru kake ji, sai kira'ar sudais dake tashi a redion motar. Mariya na baya, tana faman kalle kalle. Sai hubby dake WhatsApp da Aisha, gaba daya hankalinta na kan wayarta.

Jin tsayawar motar, yasata saurin dagowa, kallon kofar gidan da sukai parking tayi, sannan ta maida kallonta ga hayder cike da Neman Karin bayani. Kauda kansa yayi, ba tare da yace mata komai ba. Garar rufe kofar motar da taji, yasa tai saurin kai kallonta ga Mariya da already ta fita a motar. Zagowa tayi tanama su hubby sai gobe in tazo.

Cikin sanyin jiki, hubby ta daga mata hannu, ba tare da ta samu ko kalma daya da zata furta ba. Allah - Allah take suje gida ta aiki mariyan ta siyo mata P-Test, ta samu tayi pregnancy test, ko ta samu natsuwar zuciya. Amma lokaci kadan hayder ya rushe mata plan dinta. Ajiyar zuciya tayi, jin ya harba motar a titi. " a kwai gobe" ta fada a kasan ranta, duk da ba haka taso ba.

Suna gaf da shiga unguwarsu, wayarsa tayi kara. Dagawa yayi, cikin husky voice dinsa yayi sallama Shiru yayi yana sauraron mai maganar. Kafin taji yana cewa. " koma menene Ku bari sai da yamma." Shiru yayi can kuma ya danyi tsaki " i say in the evening. " -- " OK."

Yana Karya kwanar layinsu, malan idi da gurgu na zaune a waje. Suna hira. Hango motar na zuwa gurgun ya washe baki. Malan idi, kakarmu ta yanke zaka, uwar dakinmu ta dawo." Da sauri malan idi ya mike, shima yana washe baki. " ai kuwa, sune, dama tun da naga yau ana share share, nasan su oga na hanya." Da sauri ya wangale get, tun kafin ma su iso.

A bakin get din Hayder ya tsaya suka gaisa da malan idi, tare da tambayarsu ya hanya? Hayder ya tambayeshi lafiyarshi da kuma gidan. " komai lafiya, yallabai. Sai rashinku na kwana da yawa." Murmushi hayder yayi tare da amsa gaisuwar gurgun mutumin dake ta washe baki.

Shiga yayi, yayi parking. Malan idi ya shiga musu da jakun kunansu.

Dakinta direct ta wuce, komai tsaf a gyare sai kamshi ke tashi.

Kayanta ta shirya ko wanne ta maida shi, inda ya dace. Sannan ta nufo kitchen don daura abincin.

Cook Book, ta dauko tana dubawa. Kamshin turarensa ya tabbatar mata da dosowarsa kitchen din. A bakin Kofa ya jingina tare da dafe kofar da daya hannunsa. Juyowa tayi, tana kallonsa, " me kake son a dafa?."  Shafa sajensa yayi da daya hannun still yana kallonta, Ba tare daya ce komai ba. Haushi ne ya kama hubby, yana daya daga cikin abinda ke hadata dashi, sai kayi magana yasan dashi ake, amma sai yayi maka banza.

Tukunya ta dauka ta zuba ruwa. Ta daura a kan cooker gas, tana kokarin kunna a shana, bataji takowarsa ba, sai dai taji an rike mata hannu. Hannun ta kalla, kafin takai kallonta kanshi. A shanar ya amsa, ya ajiye a gefe.

" an hutashsheki." Ya fada yana shinshina wuyanta.

" please hayder, kasan dai baza a zauna baa ci abinci ba, ko don su malan idi. " ta fada muryarta na rawa

Juyo da ita yayi, ya ci gaba da romancing dinta. Ta bude baki zata yi magana. Ya daura yatsanshi a bakinshi alamar tayi shiru. " ta rasa wane irin fitinan nen yaro ne, wannan. Ya dawo kenan, yanzu zai hanata sakat da fitinarsa.

" kina son ki batawa Hajiya yaronta." Ya fada in his husky voice.  Yana kara rungumota jikinsa.

" dama can, tasan halin yaronta, shi yasa ta masa aure kafin ya fara tsince yaran jamaa." 

" banda sharri!!! Ke kika gayyatoni, ni kuma na amsa, meye lefina?"

" da yaushe na kiraka?" Ta fada tana dago kanta yanda zata ga fuskarsa sosai.

" Hajiya kanta, ta yaba kwalliyar da aka min, shine naga ya kamata na bada tukuici. Kin ga ke kika bani goron gayyata." Ya fada yana smacking

" banyi don kai ba, da har kanka zai na fasuwa. Nayi don radin kaina ne? Ta fada tana harararsa.

" really. " ya fada yana daga mata gira.

" really!!! Ka jira Nasrin ta shigo, na tabbata zatayi don kai, amma banda hubby."

" kina son Nasrin din nan, naga a lama." Ya fada

" yes!! I like her, she is a nace girl." Murmushi yayi cike da jin dadi. " thanks. " ya fada

" amma kaman baka damu da ita ba? Do you really love her? " ta tambayeshi

" why do u ask?."

" gani nayi tunda kuka rabu, har yau baka taba daukar kafarka kaje ka ganta ba. Bayan an ce garin masoyi baya nisa, in har son da kake mata na gaskiya ne, yaka mata at least by now kaje ka kai mata ziyara."

Smacking yayi tare da tabe baki. " kika Sani ko irin namu tsarin kenan?" Ya fada yana shafa gashin kanta.

" ba wani nan, _a kwai katon question mark a kan son da kake mata.? Ta fada

" zaki rakani.?" Ya fada yana daga mata gira

" no." Ta fada tana kada kai.

" why." Ya fada

" ask one of your friend. "

" ke nake son ki rakani." Ya fada cikin very low voice

" no, in capital NO "

" u are jealous of her."

Harararsa tayi. " Allah ya kiyaye, da ina kishi bazan ce ya kamata kaje ba."

" OK." Ya fada yana tabe baki.

" kinsan yanzu zance ba sai kaje wurin budurwa ba, true phone and you're system, u communicate and see each other. I'm not like your stalking boyfriend's, every ware u go, the followe u."

" that how its suppose to be." Ta fada

" in my case is different. In ina son ganinta I just tell her, in no time zaki ganta a Nigeria. To tell u the true, ban taba daukar kafata naje wurin mace ba."

Tabe baki tayi. " there love u, more than you love them. Amma hakan bashi zai hana ka kula da mai kula da kaiba. Koda yake laifinsu Ne, da zasu tsaya zubar da darajarsu da Allah ya musu, saboda so. Nama rasa me suka gani da basu gani a sauran maza ba, suke wani makale maka? Farin ko dogon hancin? "

Murmushi yayi har tana jin sautinsa " ke da kike ikirarin bakya son Aliyu hayder bakya iya resisting dina, how do you expect them to resists me?"

Nocking suka fara ji, sai lokacin hubby ta tuna a inda suke. Da sauri ta mike, gyara kwanciyarsa yayi, ya daura kansa a kan hannayensa biyu, fuskarsa na kallon sama. Ta gafen ido, yake kallonta tana kokarin sa riga, cikin sauri. Still nocking din aka ci gaba dayi.

" wait. " ya fada yana mikewa, ganin tana kokarin fita. Kauda kanta tayi, smacking yayi, tare da zura jallabiyyarsa da short nicker. Sai da yazo zai fita, ya rada mata a kunne " go and cherk your self in the mirror. "

Haushi ne, ya kamata, kamar ta mangare keyarsa. Dama a cike take da maganarsa ta dazu.

Bai dade ba, sai gashi da manyan ledoji, masu tamarin Eat More restaurant. Still tana tsaye a inda ya barta, sai cika take. Tabe baki yayi. Ya wuce cikin kitchen din. Ya ajiye ledojin. Sauran kayansu dake watse a tiles din kitchen din ya tattara. Hannunta ya kamo, ya damka mata.
Da gudu- gudu, ta haura sama.

Dariya yayi, yana shafa tattausan sumar kansa. Don yasan ya tsokano rigima yau.

Toilet ta wuce, madubi ta kalla, yadda gashinta ya wani baje, tare da wargajewa. wanka ta fara, tana tuno maganar hayder, hawaye ne suka fara bin kumatunta. Ita kanta ta rasa wannan fitinar. Kamar wani magnet haka take rasa duk kan kuzarinta, matukar zai bukaceta, bata iya resisting, ya san weak point dinta, wannan wani sabon babi ne na  rayuwarta, da 'da bata San da shiba. Tana kokarin fitowa yana shigowa. Ta gefensa tabi zata wuce. Rukota yayi da sauri. Masifa ta fara masa, don abun ya fara isarta, duk makullan dakinta, da toilet duk ya kwashe, bata da wani privacy a gidan.

Dagata yayi cak, zuwa cikin barf da hannu daya ya riketa, ya kunna shower. Kokarin kwacewa take, don tayi alkawarin ta daina biye masa, tunda abun harda gori. Amma baa je ko ina ba, ya sakata a saiti. Midik kakeji

Harararsa tayi, " ban yafe ba wallahi, mugun yaro." Ta fada tana nufar woodruff.

Dariya yayi, yana ci gaba da goge kanshi da karamin trowel. Lotion dinta ya dauka ya fara shafawa. Duk harare -hararen da hubby ke binsa dasu yana kallonta. Shi dariya ma take bashi.

Sai da ya gama, tare da fesa turarukanta. Still tana gaban woodruff, ta rasa kayan da zata sa, don ta kubutar da kanta, tun kafin yaga bayanta. Duk kayan data dauko sai taga bai yi ba. Tsaki tayi, tana jin haushin Aisha da ta sata yin irin wannan banzan dunkunan. Tasan har dasu ke ja mata murxuwa a wurin hayder.

Wata tsohuwar rigar material dinta ta hango, mai zuwa da hijabinta. Musamman ta siyesu zuwanta umra, don zuwa masallaci.

"Ban wuri," ta fada cikin siririyar muryarta, tana harararsa. " let me help u." Ya fada yana matsa lotion din a hannunsa. " na rokeka don Allah ka barni in shirya a tsanake." Ta fada tana kwace lotion din a hannunsa.

Tabe baki yayi, tare da dage kafada, ya fita a dakin. Da harara ta rakashi.

                 *****************
3 cutter da armless shirt na kamfanin NIKE farare, sun masa kyau, kitchen ya wuce ya dauki Leda biyu, ya nufi waje. Malan idi ya samu yana alwala. Ya mika masa tare da juyawa ciki.

Godiya malan idi yayi, yana Allah Allah ya idar da alwala yaga abinda ke cikin ledar din. Saboda kamshi daya cika hancinsa.

Sai da ta idar da sallah, sannan ta sakko. A falonta na kasa ta sameshi, ya baje a carpet, yana kwasar girki.

  Ledar din ta fara bubbudewa, shawarma taci karo da shi, a wani Small paper bag. Zama tayi tare da yin bisimillah ta fara ci. Idonta ta lumshe, saboda dadin daya ratsa mata kwanya.

Tunda ta sauko, idonsa na kanta, ganinta da hijab, tabe baki yayi, ganin yadda take cin shawarma tana faman lumshe ido. Wunin ranar gaba daya haka hayder ya takura hubby, da fitina iri iri, sai yamma ta samu kanta, da su junaid suka kawo musu ziyara.

           **********************
Ya dawo daga main house kenan, sun dan tsaya da malan idi. Bayan sun gama magana wayarsa ya zaro daga aljihun Jens dinsa. Kan bike dinsa ya zauna yana waya.

Ledar din hannunta, take shillawa, tare da rere wakar film din Mariya. Ganin hayder a zaune saman bike dinsa. Jikinta ya dau rawa, mu samman da ta tuna da gar'gadin hubby. Ledar din data shilla take kokarin dawo da ita ta boye cikin hijab. Batai aune ba, sai ji tayi ta harde, dan dogon takalmin dake kafarta, ya turgude, sai gata a kasa, ledar tayi can gefe. Ko motsi beyi ba, yana ci gaba da wayarsa. Kallonta yayi, ya kalli leader din. Ya kauda kansa. Da sauri ya kara kai idonsa kan ledar din. P-Test  ya hango daya ya fito daga ledar din. Daga inda yake, yana iya karanta jikin dan dogon searchet din.

Da sauri ta mike, ta dau leader din. Tare da dauke wanda suka zubo din. Gaishe shi tayi, ta wuce da sauri kamar munafuka. Kai kawai ya daga mata.

Gaba daya hankalinsa ya kasu kashi biyu, ganin ya ma daina gane me nasrin ke fada, yasa ya mata sallama.

              ********************

"Kin tabbatar ba Wanda ya gani ko?" Hubby ta fada tana tsare Mariya da ido.

Kai Mariya ta daga mata. Da sauri hubby ta dauki leader din tayi sama.

Har washe garin ranar hayder na jira yaji hubby tace masa wani Abu, amma shiru. Bayan ya tabbatarwa kansa she is pregnant. Ganin tsinkayen datayi anfani dasu har hudu, amma suna nuna she is pregnant, Duk da boyon data musu bai hanashi bin ciko su a kasan dustbin din toilet dinta ba.

Farin ciki a wurin hayder baa magana, ranar ko bacci bai iya yi ba. Sai mika godiyarsa ga Allah tare da nemama yayansa gafara da rahamar Allah.

Hubby kam ranar tasha kuka, da tunanin mafita, rashin zuwan hayder gareta a ranar ya mata dadi, don ya bata damar nazarin abinda zatayi next.

11 dai- dai, hayder ya fito daga dakinsa. Hubby na zaune a gaban mirror. Kanta ta kifa, tana faman saka da war wara. Kamshinsa ta jiyo, tai saurin dago kanta.

" ki shirya ki sameni a waje, zamu je wani wuri." Ya fada yana juyawa, ba tare da ya jira mai zata ce ba.

Cikin sanyin jiki, ta dauko hijab dinta, kalan da zai shiga da atamfar dake jikinta. Ta saka, tare da daukar jakarta, Already dama shiryawarta kenan.

Yakai 5min a cikin motarta, sai gata ta fito. Gaba ta bude ta shiga, yaja suka tafi. Ba Wanda ya tankawa dan uwansa.

Kallonsa tayi, sannan takai kallonta kan ginin da suke tsaye a gabansa.
Sultana specialist hospital. Kallonsa ta kara yi, bai ce mata komai ba, bai kuma kalleta ba, balle ta sa ran samun karin bayani. Hasalima fuskarsa ba annurin da zata samu damar tambayarsa dalilin zuwansu hospital. Don haka tasa a ranta halan a cikin yan uwane wani ba lafiya, suka zo dubiya.

Fita tayi ta bishi a baya, yana gaba, tana biye dashi suka shiga cikin hospital din.......

Afwan. Rayuwa ba kai kake tsarawa kanka yadda kaso ba, sai yadda Allah ya so kuma ya tsara. Tafiya ce un expected ta kamani, shi yasa kuka jini shiru. Yau na dawo, ga gajiya, amma dunbin comments dinku yasa bazan iya shareku ba, kodon kauna da kulawarku. Shiyasa na daure na muku typing at leas in nuna muku how happy I'm. Na gode da kauna, da kulawarku. Love u all, thanks.
Kujera ya nuna mata a Reception din, ba tare da yace mata komai ba. Bata da zabin daya wuce ta zauna. Zama tayi tana binsa da kallo. Ya koma mata kamar ba hayder data sani ba. Wani kwarjini na ban mamaki taga ya kara mata a idonta.

Wayarsa ya Ciro, ya kira wata number. Minti kadan sai ga wani balaraben doctor ya fito daga wani corridor, wuyansa rataye da abun auna numfashi. Rungume juna sukayi, tare da hade kumatu, as usually gaisuwarsu.

Sun danyi magana kafin, suka dawo da kallonsu kan hubby, da rabin hankalinta na Kansu, rabi na kan yan matan dake gefenta. Tun shigowarsu gaba daya hankalin yan matan, yayi kan hayder.

" I known this guy." Dayar ta fada.

" kai guy din nan ya hadu karshe, I like this guy." Dayar ta fada Still idonta a kan hayder

" natuna!! You known Hafiz? Dayar ta tambaya.

" wane Hafiz kenan."

" our nebour."

" na ganeshi, Wanda ya dawo daga Cyprus ko?"

" yauwa shi. Friend dinsa ne, ina yawan ganinsu tare." Dayar ta fada. Ganin hubby na magana da doctor din da suke tare da hayder yasa sukayi shiru.

Gai sawa hubby sukayi da Doctor sabir. Jagora ya musu har office dinshi.

Katon office ne, mai kyau da tsari. Kujeru biyun dake gaban table dinsa ya nuna musu, cike da faraa.

Sun dan dau lokaci, suna hirarsu da hayder, kafin wata nurse ta shigo, dauke da file a hannunta. Cikin girmamawa ta gaisheda su hubby kafin ta mikawa doctor file din ta fita.

Doctor din ya dago yana kallon hubby cike da faraa a kan fuskarsa. Tambayoyi ya fara jerowa hubby, kallon hayder tayi, taga gaba daya hankalinsa na kan wayarsa. Gabanta ne ya fadi, cikin karfin hali, da rawar murya ta ke amsawa doctor din.

Waya ya dauka ya kira wata nurse din. Minti kadan sai gata. Wasu fararen takardu, da yayi rubutu a kai ya mika mata. Tare da kallon hubby ya ce " madam kuje tare, akwai wasu test da za su miki yanxu."

Jiki a sanyaye hubby tabi bayan nurse din.

Zaune take, bayan ta dawo daga wurin da aka dauki jini, da fitsarinta. Tana kallon hayder da yayi balance a kujera suna hira, sama- sama da Doctor din. Duk yadda taso su hada ko ido ne abu ya faskara.

Jikinta yayi sanyi, Bata so hayder yasan tana da ciki ba. Don ta gama yankewa kanta hukuncin zubar dashi, don da kunya a ganta da cikin hayder a jikinta. Bata san ya zata iya shiga jama'a da wannan abun kunyar ba. Ta rasa yadda akayi ya gane, tunda ita ba wani laulayi take yi ba, Aisha ce ta fado mata a rai, ta wani gefen kuma tana ganin Aisha bazata taba fallasa sirrinta ga hayder ba, tun da har ta shaida mata bata son ta gayawa kowa.

Nurse din dazu ce ta shigo da envelope a hannunta. Doctor din ta mikawa, ta fita. Zaro farar takardar yayi ya kalla, yana murmushi. " congratulation ahehh!!!! She is 2month 2 weeks pregnant. Rungume juna sukayi ya na ce masa " thanks. "

Hubby doctor ya kalla cike da faraa " congratulation uhtee!!!" Yake tayi tare da sunkuyar da kanta, cike dajin kunya.

" zaki zo every month, don tabbatar da lafiyarki, dana beby din mu." Doctor sabir ya fada lokacin da ya rakosu har mota.

Kai kawai hubby ta kada, tare da bude kofar motar ta shiga. Sallama sukayi da hayder sannan ya juya ya koma cikin hospital din, su kuma suka kama hanyar gida. Har suka iso gida, ba wanda ya tankawa dan uwansa.

*******************
10 o'clock dai dai, ya shigo dakin hubby, cikin shigar kayan baccinsa, sai kamshin turare ke tashi.

Yau idonta biyu, fargaba da rashin sanin matakin da hayder zai dauka a kanta, da makomar cikin dake jikinta, wanda ta tabbatar yanzu zubar dashi, tamkar yakin duniya na biyu ne a gareta.

Tana zaune a bakin gadonta, wani book din adduoi take dubawa. Ya shigo. Kallo daya ta masa, ta kauda kanta. Har lokacin fuskarsa ba walwala. Kusa da ita ya zauna tare da jingina da jikin gadon.

Nazarinta ya tsaya yi, ganin har lokacin taki dago idonta ta kalleshi. Shi mamakinta ne ya isheshi. A tunaninsa murna zatayi a duk lokacin da ta samu wannan kyakyawan labarin. Amma ga mamakinsa sai yaga sabanin hakan. Tun ranar da tayi anfani da P- test din nan, ya lura gaba daya bata cikin walwala, da natsuwa.

" me yasa baki gaya min kina da ciki ba?" Ya fada in his low voice, da ita kanta ba don tana kusa dashi sosai ba, bazata jiba.

Shiru ta masa, ba tare data ce komai ba, tana kokarin maida kwallar data cika mata ido.

" don't Tell me, u are not happy about it?" Ya fada yana tsareta da ido.

Hawaye ne suka fara bin kumatunta. Dafe kanshi yayi tare da anbaton " ya Allah.'"

sai kawai ta saki kuka mai cin rai, wani irin kunya ya rufeta shike nan yanzu ta tabbata matar hayder harda cikin shi a jikinta sannan kowa ya ganta yasan abinda hayder ya mata kafin ta samu cikin ace k'anin ta wai yau shine mijin ta kuma harda cikin shi a jikinta, ita duk a haukanta bata taba tunanin zata iya daukar ciki ba, da tayiwa kanta dabara, duk da baa wa Allah wayau. Yakan zartar da abinda yaso a lokacin da yaso.

Cikin kukan ta matsa kusa dashi, idonta na zubda kallah tace
"Dan Allah kayi hak'uri kar ka gayawa kowa please Na tuba, kasa ya zubar min da cikin ni banson haihuwa wallahi ni dai a zubar da cikin tun da ba wanda ya sani"

Smacking ne kwance a kan fuskarsa, sajensa yake shafawa, yana kallonta. jawota yayi jikinshi cikin lallashi ya hada bakinshi da nata kissing dinta ya fara, jikinta gaba daya tayi sanyi, so bata yi wani yunkurin hanashi yin hakan ba. Tama san in yayi niyya ba yadda ta iya dashi. Sai da ya gaji don kansa, ya zare harshensa tare da gyara mata zama ya kwanto da ita kadan a jikinsa. Fuskarta ya dago ya tsare ta da ido cikin husky voice dinsa yace. " Kin san sanda cikin ya shiga ne? kinsan me zaki haifa ne? kinsan rayuwar da zaiyi? Ke kika halicce shi?
Ko kyau tar da Allahu S. W. A ya mana kika raina? ki nitsu Habiba cikina fa kike cewa wai ince a zubar ciki da a da da kudima kin nema amma baki samu ba. Sai yanzu da Allah yaji kanki, ya tausaya miki, ya baki, kike neman yi masa butulci.
May child!!! My own flesh and blood kike son in sa a zubar? kinsan wahalar dana sha kafin na sameshi, kin san irin tashin hankalin da na shiga, daga ranar da aurenki ya fado kaina, har ranar da kika shigo gidan nan a matsayin matata ta sunna? Kin san yaki da zuciyata da nayi don kawai in karbeki a matsayin abokiyar rayuwa? U have no idea. My blood my halal kike cewa a zubar me zaki gayawa mahalliccin mu? Ranar da bayi ke girbar ayyukansu?" Ya fada still idonsa a kanta.

Idonta a rufe, don bazata juri kallon kwayar idonsa ba. kauda kanta tayi tare da cewa. "Bana so wallahi ko zan Haihu ba da kai ba, na yadda in haihu da koma waye da na haihu da kai, nace kanina ne mijina ko nace kaninah ne uban yarana?".

Sosai zantu kanta suka bata mai rai, tureta yayi daga jikinsa. Idonsa cikin nata ya nunata da yatsa jikin shi har rawa yake yana fidda numfashi da karfi yace.

" kar kiga Ina binki ina lallaba ki, saboda ke macece mai rauni da tawayan tunani, Ku mata akan biku a hankali dan a fahimtar daku amman na lura abin naki rainine, dan haka ya zama dole na gyara miki tunanin ki, zuwa yanzu, yaci ace na fi karfin ki kirani da yaro, tunda nayi abinda manyan mazan basu yi miki ba. Naga alamar baki tsoron Allah, sai tsoro da gudun surutun jama'a, da bazai anfaneki da komai ba. Sadaki aka biya, shaidu suka shaida. Ko kin dauka kowama sakarai ne, da zaiyi tunanin zan ajiyeki a gidana ina kallonki ba tare da wani abu ya faru a tsakaninmu ba? ki bude kunnenki da kyau. wallahi kar bakin ki ya kuma furta Kalmar zubda ciki a gidan nan. in kuwa kikayi gagganci furtawa, ko yunkurin aikata ba dai dai ba, akan cikina wallahi zaki gane kuskurenki, lokacin zaki san waye Aliyu hayder. Zan iya karawa da kowa akan cikina. Don shine farin cikina, cikar burin dan' uwana."

Mikewa yayi ya fice a dakin, cikin bacin rai, da jin haushin hubby.

Jikinta yayi mugun sanyi da kalamansa. " tabbas wannan babban butulci ne, ga niimar Allah a gareta. Sunje kasa yakai 6 duk don neman haihuwa. Bakar magana, wulakanci, cin mutunci, wanne ne bata fuskanta ba akan haihuwa? To meye nata na daukar zafi kan haihuwa da hayder? Surutun jama'a? A duniya ka isa ka hana jama'a surutu a kanka? Komai kayi abin magana ne, wani yaga kayi dai dai, wani yaga kayi kuskure. Baka taba burge jama'a. Tabbas farin ciki ya kamata tayi, yanzu ta tabbatar da kanta a matsayin cikakkiyar mace, mai haihuwa. Sabanin da da wasu ke lakaba mata juya, har ake kin aurenta don hakan. Tunowa tayi da Abdul Karim da Abdul fatta, wanda duk dalilinta na zamowa bata haihu da yayansu ba, yasa iyayensu mata kin yadda su aureta. Wanda ya zama sanadin aurenta da hayder.

Tabbas yayi kokari, kuma yayi sadaukarwa. A matsayinsa na yaro mai jini a jiki, wanda yanmata ke rubibinsa, amma ya hakura ya amsheta a matsayin mata. Duk da shekaru 5¹/² years dake tsakaninsu. Sannan a matsayin bazawara, ba budurwa ba. Batayi tunani ba, Allah S.W.A ya mata gata, ya mata canji da hayder wanda a yan watan nin da tayi dashi, ba abinda ta nema ta rasa, abinci, sutura, kudin kashewa, duk wani abu na more rayuwa dai dai karfinsa yana yi. Komai nashi enough zai yi batare da gajiyawa ba. Kamar yadda ya dauke mata dukkan bukatunta na ya mace. Wanda a zamanin nan yana da wuya mutun ya samu wannan.

Jiki a sanyaye ta tashi ta nufi toilet ta wanke idonta. Kara gyara jikinta tayi, tare da fesa turare mai kamshi ta nufi dakin hayder, don ta bashi hakuri. for the fist time. Don tun daga fist night dinsu, sai dai shi yazo dakinta, ko kuma ya dauketa zuwa dakinsa, amma badai da kafarta ta taka zuwa dakinsa ba. Ga mamakinta kamar yasan zata zo, dakin a kulle. Nocking tayi- tayi yaki bude mata, dole ta juya ta koma dakinta. Ran maza ya baci!!

Kwance yake yayi rigin gine, kansa a kan hannayensa yana kallon ruffing din bedroom din. Tasbihi yake da istigfar. Ko zuciyarsa tayi sanyi. Don gaba daya ransa ya gama baci da hubby. " Ashe bawa zai iya zama mai butulci haka? Allah ya maka Niima ka butulce masa, wasu na nema ido rufe basu samu ba. Amma kai ka samu ka butulce! Bayan da da kudinka ka nema baka samu ba! Tabbas hubby bata sonshi, ko kadan. Yau ya kara tabbatar da hakan, Tunda har bata son hada jini dashi. Don karfin hali da rashin kunya har tana iya bude baki tace data haihu dashi gara ta haihu da wani. Wannan maganar ta masa ciwo fiye da sauran magan ganunta. Ta manta shima bafa sonta yake ba. Ba yadda ya iya, shi yasa ya rungumi kaddara. Duk da wasiyyar Yusuf na ya aureta, Sam bai yi niyyar aurenta ba, don yasan baya sonta, shi yasa ma yaja bakinsa yayi shiru, bai taba furtawa kowa ba, daga shi sai Allah, sai kuma dan uwansa. Don dama koda Yusuf din ya bukata bai amsa masa ba. Don yasan abun da kamar wuya. Kaddara tazo ta hadasu hakan yasa ya amsa da hannu bibbiyu duk da yana jin ciwon abun a ransa. Amma ya kudurta zai zauna da ita don Allah, zai kula da ita ya sata a farin ciki, don Allah, sannan ya cika muradin yayansa na ganin hubby cikin farin ciki ko bayan rayuwarsa.

Yanaji ana nocking, yasan ita ce, amma bashi da muradin ganinta a lokacin. Tsaki yayi tare da gyara kwanciyarsa.

Ranar gaba daya baccinsu ragaggene. Hubby kam tsabar nadama da danasani su suke nukur kusarta. Nafila ta kwana yi tana neman gafarar Allah, tare da ma Yusuf addua. Sannan ta nema musu zaman lafiya ita da hayder. Koba komai yanzu dole ta yadda ta amince. Shine miji kuma uban yayanta. Allah ne ya bashi girman, dole ta saukar da kanta ta nemi aljannarta.

Ga hayder ma kusan hakan ce, sai dai shi addua yama yayan nasa, tare da adduar Allah ya sauki hubby lafiya, ya azurtasu da zuria masu albarka.

*******************
Yau kwalliya sosai hubby ta zage tayi, musamman don oga hayder. Tayi kyau sosai. His favorite tayi masa break fast.

Sai 10 ya shigo gidan. Sai da ya shirya cikin kananun kaya, ya sakko zuwa kitchen. Mariya ya samu tana goge goge. Da sauri ta durkusa tana gaisheshi. Rai ya hade kamar bai taba dariya ba, wanda yasa cikin Mariya kadawa don tsoro.

" meye aikinki a gidan nan?" Ya tambayeta cikin kakkausar murya.

Jikinta da zuciyarta gaba daya suka hau rawa. " wanke - wanke, shara, mopping, sai taya Anty aikin girki." Ta fada muryarta na rawa

" good!! Daga yau ta kara aikenki dai- dai da wajen get, kika je sai na kakkarya kafafunki." Ya fada in warning tone

Jiki na rawa Mariya ta amsa, tare da bashi hakuri.

" bace min a nan." Ai kafin ma ya rufe baki tayi waje da gudunta..........

 
 [10/03, 13:05] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA
Chapter 24 · 0% Book details