← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 15 OF 28

                            Part 14

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 21 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau

" amma gaskiya mutanen nan basu da mutunci. Yanzu duk yadda kuke da Hajiya Amina, da abunda zasu saka miki kenan." Hajiya Fatima ta fada bayan sun koma falon Hajiya.

Hajiya Balkisu ta karba, bayan ta rike haba irin na mutun yaga abun mamaki. " ai ni kam jikina yayi sanyi, dama an ce baa ba kishiya amana, ko ba dade ko ba jima, sai ta dagaki sama ta nana da kasa, ki ganta sumi sumi, da ita kamar bata yiba. Shiyasa kullun nake gayawa Hajiya ta yi taka tsantsan, amma sai tace ai anzama daya. Mutanen yanzu baka taba sanin zuciyarsu. sai abu ya sameka."

Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke " tun da dama Alhaji yayi maganar nan, na lura da take taken su, amma ban dauka abun yayi zafi haka ba. Ni a tunanina koda Habiba kwantai tayi, ita mai rufamin asiri ce, Ashe ni ban Sani ba, burun burun ake min. Allah na gani alkhairi nake nufin dukkansu dashi, ya rage nasu yanzu."

" to ke da kika ci alwashi, ba tare da dogon nazariba, abun fah da kamar wuya!!! kina ganin hakan zai yiyu?" Hajiya Fatima ta fada

" nima abinda na gani kenan, kin San a girme Habiba ta girma hayder tayaya zakiyi, wannan hadin. Da kin barta kawai baki amsata ba."

Murmushi Hajiya ta yi " she karu ba komai bane face numbers. Hayder dai ni na haifi abuna, in sha Allah ba niba har su sai sunyi alfahari da auren hubby da hayder. Alhaji yaso su da alkhairi sun bujire, ni kam zan amsheshe da hannu bubbiyu. Ko ba komai tuwona maina kamar yadda suka fada. Ina son Habib tamkar yadda nake son yayan cikina,. Kamar yadda duk duniya a yanzu, banda mijina, bani da kamar Hauwa. Nasan kuma in sha Allah hayder yayi mata, irin Matar da nake masa fatan samu, zuwa gaba  in sha Allah zaiyi alfahari da zamowarta mata a gareshi, kamar yadda itama zatayi alfahari da zamowarsa miji gareta."

" Allah yasa albarka ya kade fitina."

"Amin" Hajiya da Hajiya Fatima suka amsa.

" bamuga ta zama ba!!! Auren auta." Hajiya Fatima ta fada tana murmushi

" ba zama kam, yanzu meye abun yi?" Hajiya Balkisu ta tambaya

" eh!!! To!!! Maganar neman gidane zai zama matsala, saboda kurewar lokaci, don so nake a hada bikin gaba daya a wuce wurin. "

" wannan ba matsala bane, yanzun nan zan kira kanin megidana, harkar gine gine, yake yana bada haya. In ji ko akwai available. " Hajiya Balkisu ta fada tana lalubo wayarta.

Murmushi Hajiya Fatima ta yi tare da rike baki " ammafa ya kamata kafin mu fara gudanar da komai, aji ta bakin maza, tukunna."

" haka ne kam, amma dai buga muji maganar gidan, don in sha Allah ba fashi auren nan." Hajiya ta fada tana kallon Hajiya Balkisu.

                ******************
A tare suka sauke ajiyar zuciya, kada kai Alhaji Jamal yayi ya juya zuwa part dinsa.

Hayder da kansa ke faman juyawa, ga wani bugu da zuciyarsa keyi kamar zata faso waje. Bakin ciki, da takaicin magan ganun da  Hajiya kaka ke yi. Wanda duk akan kunnensu shida Alhaji Jamal. Suna tsaye suna magana, suka fara jin hayaniya, da sauri suka nufo part din matan, jin muryar Hajiya kaka yasa Alhaji Jamal Jan birki, ganin haka shima hayder din ya kasa shiga.

Ba abunda ya kara daga hankalin hayder irin furucin Hajiya. " in sha Allah gobe iwar haka Habiba ta zama Matar Aliyu hayder. " me hakan ke nufi? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, allahumma ajirji fi musibayi wakhlufli khairan minha. Ya furta a saman labbansa. Da kyar yake daga kafarsa, ya nufi part din su Abdul Karim, yayi sa'a ba kowa a dakin. kwanciya yayi dafe da kansa, dake barazanar tarwatsewa. Yana jero adduai a saman labbansa.

Alhaji Jamal na shiga part dinsa ya kira Hajiya Amina (Mmn samira) a wayarsa. Zama yayi Yana huci cike da bacin rai da damuwa.

A hankali ta tako zuwa cikin dakin, daya daga cikin kujerun dake kusa dashi, tama kanta masauki. Tare da gaishe shi. Shiru ya mata ba tare daya amsa gaisuwar tata ba. Ido ya zuba mata, wanda ta kasa jure kallon da yake mata ta maida kallonta gefe. " meke faruwa a gidan.?" Ya jeho mata tambaya

Cikin alamun rashin gaskiya ta kalleshi tare da kauda idonta " ba abinda ke faruwa, ko wani ya fada maka wani abu ya faru ne?." Takaici ne ya cika Alhaji Jamal ganin yadda take son raina masa hankali

" ba gayamin akayi ba, da kunnena naji duk abinda Hajiya kaka ke fada."

Tabe baki tayi " meye laifi to don ta fadi gaskiya?"

Baki sake Alhaji Jamal yabi Mmn samira dashi cikin tsananin mamaki. He can believed Mmn samira ce da kanta.  " kin ban mamaki, ban taba tsammanin haka daga gareki ba, ko don kusancin dake tsakaninki da Hajiya. Sannan da dai nawa ne? Koyana so ko bayaso jibi in sha Allah zaa hada danasu Aisha, kun dade baku daga hankalinku ba."

Wani kallo Mmn samira ta zuba masa, da tun aurensa da ita bata taba masa ko makaman cin saba.

" kamar yadda yake danka, haka zalika yake dana, haka kurun bazan zauna a ci gaba da cutata ba, abin baima tsaya kaina ba, sai an hada da yarana? Abdul da kansa ya ce baya sonta, banga dalilin da za'a masa dole ba, shima a barshi ya zabi abinda yake so kamar sauran yaran. Tayaya za'a jona masa bazawara?, bazawarar ma juya? Sannan a ce kar in yi magana?, ina kallo a cukeni a cuci dana. Naga in da namijin ne itama tana dashi, in gaskiya ne, shi ya aureta man. Za'a zo a kitsa maka abu ka hau ka zauna, Nasan duk ita ce mai wannan kinbibin hadin, don haka ta hada da danta badai dana ba."

Alhaji Jamal mamaki gaba daya ya cika shi. Tabbas abin ya wuce inda yake zatonsa. Mmn samira zai ce tunda ya aureta bata taba daga masa murya ba irin yau. Don haka mamaki da bacin rai yasa ya kafeta da ido.

Kin kallonsa tayi sai data kai inda taso kaiwa sannan ta yi shiru tana huci da huhhura hanci.

" shi Abdul Karim din da bakinsa ya ce miki baya sonta?" Ya tambayeta

" so sai ma, kaima ya kamata kasan baya sonta tun ranar daka taramu a nan. Don da yana sonta nan take zai amsa maka."

Kada kai Alhaji Jamal yayi " shi kenan tashi kije." Haka ta fice a dakin tana faman hura hanci. Da ido ya bita yana mamakin mutanen duniya, Tabbas in da ranka kasha kallo.

Fita yayi, ya nufi gidan Alhaji babba.

                    ****************

So koda Abdul Karim ya iso gida, bai samu shiga wurin Mmn samira ba. Don ya samu compound din gidan cike da abokan Ahmad sai engrn Sahabi da salis. Gefe kadan kuma su Hafiz omer, junaid, amir, alim, da Hafiz ne suma jikin motar amir suna nasu hirar.

Direct wurin su Ahmad ya nufa, bayan bayan ya paka tashi motar. an gaggaisa ya dale motar salis dake kusa data Ahmad in da wasu na jingine a jiki, wasu na kan kujerun roba. Kasan cewar Abdul Karim ya saba da yawancinsu, kusan duk ana tare, yasa shima ya shiga aka ci gaba da hirar dashi. Duk da deep down his heart tunanin hubby ne dankare a ransa, da son sake sakata a idonsa.

A hankali get man ya wangale kofar get din. Motoci ne suka fara shigowa dan kare da mata. A hankali ta sawo kan motarta cikin compound din. Wanda gaba daya hankalinsu Ahmad yana Kansu. Ita da yusra ne a gaba, sai mutun biyu, kawayenta na islamiyya, da suka mata kara, sai humaira ta uku. Hira suke sha da dariya don akwai daya mammy mai ban dariya a cikinsu.

A kusa da motar ummu khulsum ta faka tata motar.

" dadina da zuwa gidan nan akwai hadaddun samari, mai powder ta dan miko min in dan murza, kafin na fita ko nayi ciniki."  Dariya suka kwashe dashi suna kallon mammy data hakikance sai sun bata powder.

Yusra ta mika mata " gashi Allah ya kawo kasuwa, musha biki."

Murmushi tayi ta amsa tana " amin."

Tsaki hubby ta ja, hango su Engr da suka kafe motarsu da ido.
Kallonta yusra tayi, tare da kallon su Engr tayi dariya " gafa muta nenki?"

" na gansu, ban son gaishesu wallahi, dana San suna gidan nan ba abunda zai shigo dani yanzu." Hubby ta fara

" gaisuwa ai dole, ko baku gaishe suba ni sai na gaishesu
don na hango new catch dina." Mammy ta fada tana murmushi

" wanne a ciki?" Dayar ta tambayeta

" anki gaya miki, salon amin snatching. " dariya sukasa jin salon data amsa din.

" wannan shine riga malan masallaci, tun kan catch din yazo hannu, ana tsoron snatchers. " yusra ta fada, tana balle murfin motar ta fita. Hubby ta Gyara zaman gyalen after dress dinta tayi da kyau. Kamar ta sani ana gama lunch zaa taho ta dora after dress dinta a kan kayan.

Fitowarta yayi dai dai da isowar su junaid, gaisheta sukayi, cikin mutunci tare da tambayar kayan lunch. Key ta mikawa hafiz, akwai abubuwa a but, in kun kwashe a kawo min key dina.

"Sai Anty!! Allah ya bar mana ke." Hafiz omer ya fada yana murmushi.

Dole ta inda su Ahmad da tawagarsa zasu wuce, zuwa part din su Hajiya. Tun suka doso idon salis, engrn da Abdul Karim na kan hubby, harta iso. Yaya Ahmad ta fara gaisarwa, kafin ta musu jam'u cikin sitiriyar miryarta mai zaki, da dadin sauraro. Sauran ma gaishesu sukayi, suka wuce ciki.

A jiyar zuciya dukan su suka sauke a tare.

" engr wai ya maganarku da hubby ne ta kwana?" Daya daga cikin abokansu ya tambaya

Murmushi Engr Sahabi yayi " Ku tayani da addua, yarinyar akwai kafiya wallahi, ina nan ina kokarin shawo kanta, sai dai lamarin suraj kangiwa dake nemanta yasa jikina ya fara sanyi."

" haba faduwar gaba, asarar namiji, sai dai in dama ba sonta kake yi ba." Daya daga ciki ya fada

" kasan irin son da nake mata kuwa? Ina sonta fiye da yadda labbana zasu iya misaltawa, ina sonta, ina son halayyarta, after all duk Wanda ya samu wannan ya gama dace da mata tagari, I known how happy she made my friend, when they are together. Ya fada yana smiling

" gaskiya kam ta hadu ba karya. Amma ya kamata kai da salis daya ya hakura ya marama daya baya, ta haka zakufi saurin shawo kanta, akan dukkan Ku kuce kuna sonta at the same time. "

Kallonsa Engr Sahabi yayi " do'sen matter, an ce kasowa dan uwanka abinda kake sowa kanka, duk kanmu muna da reasons da yasa muke son aurenta, Duk Wanda ya samu a cikinmu we are happy. Abinda kawai zai bakanta mana shine, wani can daga waje yazo ya aureta."

" haka ne kam. Amma ina ganin kamar da wuya ta amincewa dayanku." Dayan ya fada

" we keep on trying." Salis da sai lokacin ya samu bakin tofa nashi ya fada.

" ammafa duk laifin Ahmad ne! Naga suna mutunci sosai, da zai shiga maganar da komai yazo da sauki." Daya ya fada

Harararsa Ahmad yayi " ka rufa min asirina, kai da bakinka kace muna mutunci? Hubby duk Wanda zai mata maganar aure yan zunnan duk mutuncin da kukeyi zaku bata. Ni kuma I don't want that."

" nifa ban gane maka ba? Ina da question mark da yawa a kanka? Anya!!" Salis ya fada yana tsare Ahmad da kallo

Murmushi Ahmad yayi. " koma dai menene kowa tashi ta fishshe shi."
Kowa dake wurin ido ya zubama Ahmad da yake ci gaba da danna wayarsa, kamar bai San abunda suke yi ba.

Engr ya kalli salis " dama na fada maka ai! Ko ban fada ba?"

Salis ya sauke ajiyar zuciya " ka fada kam" ya fada a takai ce.

" kai amma yarinyar nan tayi kasuwa, kana ganin yadda kangiwa ya haukace a kanta? Kusan a sati in bai zo garin nan ba yazo sau biyu, da da sai ya kwashe fiye da 2month bai shigo garin Kaduna ba, duk da iyayensa na cikinta." Daya ya fada yana jin jina kai

" shawara!!; Ku samu manyanta da maganar don kowa yasan matsayarsa, tunda ta wurinta ba nasara, nasan in sha Allah su za suyi nazari sosai kan abun." Daya ya fada

" ka kawo shawara mai kyau, nima nayi tunanin haka." Salis ya fada

Abdul Karim kam ya zama photo,sai kallonsu yake one after the other. Shi a tunaninsa hubby rasa mai aurenta tayi, yasa daddy son hadashi da ita. Yanzu ya gane manufar daddyn akan son dayansu ya auri hubby. In har abokan Yusuf zasu so su maye gurbin Yusuf saboda sanin kyawawan halin hubby, ina ga su kannensa. Shi duk zaman Yusuf da hubby bai da wani cikakken labari a kai, don lokacin da akayi yana Malaysia, in yazo Hutu yawanci yana Lego's gidan uncle omer zuwanshi gidan Yusuf sau daya, zuwansa bayan auren, da yaje ganin daki, tare dama yayansa Allah yasa albarka. Saboda bai samu damar zuwa lokacin bikin ba.

Sai lokacin yake tuna tarba ta karamci da hubby ta musu a lokacin, shida arif fist born din Alhaji omer. Da yadda sukai tayiwa yayan nasu dariyar ya auro Small girl, gashi da alamar bata waye ba, saboda zunbulelen hijab data sako har yana Jan kasa, "ga gida har gida, amma ba mata" kalaman arif ya tuna a lokacin.

Kalaman yaya Ahmad ne suka dawo masa bayan fitowarsu daga part din Alhaji Jamal " a matsayina na dan uwanka, shawara daya zan baka. Karka kuskura ka bijirewa wannan auren, ka karbeshi da hannu bibbiyu, na tabbata zakayi alfahari dashi. Karka biyewa kyale kyale, kyawun zuciya da addini shine abun lura. Hakika daddy ya maka zabe mai nagarta, wanda duk cikinmu ba wanda ya dace da hakan. Damarka ce wannan, in kayi wasa ta kufce maka, na tabbata zakayi dana Sani mara iyaka, lokacin da ba zai maka anfani ba."

Amsar daya bashi a lokacin ta dawo masa. " in haka ne mai zai hana kai ka aureta, naga kana da space na mutun uku, a gidanka. Ko ba komai kai ka taba aure, kaga bazawari da bazawara kenan. Kunfi mach ma,."

Murmushi Ahmad yayi masa " kai din saurayine? Karka dauka bansan duk sharholiyar da kake yi a abuja da Lego's ba? Gara ita ta hanyar auren sunna ta rasa budurcinta, kuma ga jininka. Kai fa? Allah kadai yasan yawan matan da kayi tarayya dasu. Kaga kenan kai ne baka dace da ita ba. Da kake fadin in aureta, Wait and see ka ce baka so ka gani."

Kunyar Ahmad ce ta kamashi a lokacin, bai taba tsammanin yasan abinda yake aikatawa a boye ba,no wonder ko waya sukayi ya dinga masa waazin yaji tsoron Allah, ya tsare dokokinsa, kar yaga ba idon yan'uwa, ya aikata duk abinda yaso, yasan Allah na kallonsa, kuma yana jiran dukkan bayi a mada kata. Ba abunda yake boye a gareshi game da bawa, don haka ka yawaita tuba, tare da nisantar miyagun ayyuka.

Kallon sa yakai kan Ahmad dake faman daddanna wayarsa. So da kaunar dan uwan nasa yaji ya kara ratsa zuciyarsa. In sha Allah zai karbi auren hubby da hannu bibbiyu, sannan zaiyi iya kokarinsa ya kyara tsakaninsa da mahaliccinsa. Ya tabbatar Ahmad na son hubby sosai, sai dai ya kasa gane abunda yasa ya zabi ya hakura, don ya tabbata daya gayawa daddy yana sonta ba wanda zai sakosu a ciki.

Kamar Ahmad yasan shi Abdul Karim ke kallo, ya dago suka hada ido, murmushi ya masa da kallo mai nuni da kaga maganata ko?" Lumshe ido Abdul Karim yayi tare da jin son hubby na kara ratsa zuciyarsa. Allah Allah yake dare yayi ya samu Daddy ya shaida masa ya amince da auren hubby, don bazai iya jira har nan da 5days ba, kamar yadda daddy ya diba masa, don yayi shawara ba.......
har yanzu guy din nan bai daga waya ba fah!!?" Hafiz ya fada bayan ya sauke wayarsa daga kunne.

Tsaki ashir yaja, bayan ya share bakinsa da tissue, yana ture plate din gabansa. " Ina kuke tunanin ya shiga?"

Kafada Hafiz ya daga " I don't known, tun dazu dai da muka rabu dashi a gidansu alim, kan daddy na nemansa, bamu sake ganinsa ba. Gashi  ko picking calls din ma bayayi. "

" duk rainin hankalin hayder, baya kin daga waya. Maybe daddy ya aikeshi ne." Inji Hafiz omer

" kai I don't think so. I'm filling some thing is wrong " junaid ya fada

" kun tambayi su Yaya Ahmad? Ko sun San inda yake?"

" they don't known where he is."

" let me trace his number. " junaid ya fada yana fito da wayarsa a pocket.

" a kwai dan iska, da kasan da tracing din ka barmu cikin damuwa." Amin ya fada

" I totally forget, sorry. "

For some second junaid ya dago yana kalonsu. " I can believed yana cikin gidan nan." 

" are u sure? " kai ya kada.

" OK Le's cheek Abdul part. Don nan ne kawai bamu duba ba." Ashir ya fada yana mikewa tsaye.

Dai dai lokacin hayder ya fito daga part dinsu Abdul. Da kallo suka bishi, kallo daya sukawa juna suka tabbatar some thing is wrong with him.

Wurinsu Ahmad ya isa, suka gaggaisa, ganin yanayinsa duk suka shiga tambayarsa lafiya? Murmushin karfin hali yayi " I'm not filling fine. " ya fada cikin muryarsa mai dadin sauraro da Jan aji.

Rungumeshi Ahmad yayi, yana tambayar abinda ke damunsa. Kansa ya nuna masa,. " kasha magani ko muje hospital? " ta tambaya cikin nuna tsantsar kulawa.  " no I'm ok. I take a drug. Fatan samun sauki sukai ta masa. Kafin ya nufi cikin friends dinshi.

" what is wrong with u?" Junaid daya tareshi tun kan ya iso, ya fara tambayarsa. Kamar yadda ya fadawa su Ahmad haka suma ya gaya musu. Duk da junaid bai yadda da abunda ya fada ba, amma ya bashshi a hakan.

Kayan ciye ciye ne burjik a wurin, don duk abinda aka ci a wurin sai da ta diba musu, a kyawawan containers. Ba suba har su Ahmad ma sun samu.

Cake din daya hango a gefe, ya janyo. Cake din ya burgeshi da gani zai yi dadi. Duk da cake ba cimarsa ba ce, musamman cup cake, amma wannan ya bashi shaawa. Sai da yakai daya bakinsa ya gutsura bayan yayi bismillah. Ya kalli Hafiz omer da tun dazu yake kallon hayder yana karantar yanayinsa. " ina cuka samu wannan delicious cake din?"

Amir ne ya amsa shi da " Anty hubby, kasan jiya da muka rabu dakai gidan mommy Hauwa muka je, so mun samu tana aikin cake din, kamshi ya ishemu, kasan hali, ta hanamu dandane, wai na lunch ne, baa ce taba kowa ba. She promise us, zata ajiye mana namu after lunch, she keep her promise." Ai kafin amir yakai aya hayder ya furzar da cake din bakinsa, ruwan dake hannun Hafiz ya fige, ya fara kuskure bakinsa dashi. Kallonsa suka tsaya yi baki bude, cike da mamaki, duk da sun San ba shiri tsakanin hubby da hayder amma sun San abun bai kai haka ba.

Dariya Hafiz yayi " na banza, don na tabbata wani ya wuce ciki."

" Allah ya kyauta. Naga ranar da zaku daina wannan abu kai da Anty. Ko ba komai ai you have to respect her, she is elder, and aur friend sister." Hafiz ya fada

" a kwai abunda ke damun kwakwalwar yaron nan, Ku barshi kawai." Hafiz omer ya ce

" waye yaron?" Hayder ya fada yana kallon Hafiz omer

Dariya Hafiz omer yayi tare da daga hannun serenader " sorry. "

Junaid dai na daga gefen hayder yana kallon ikon Allah. Duk da bai ji dadin yadda hayder yayi ba, amma ko a fuska bazaka gane hakan ba.

Kiraye kirayen sallar da suka jiyo, yasa suka nufi masallaci don gudanar da alwala da sallar magrib.

               *******************
Da sallama suka shigo, su Anty samira da munaya, sai sauran yan uwansu da suka dawo daga wurin lunching, basu kai ga shiga part din Mmn samira ba. Suna tsaye a harabar wurin ana maida yadda akayi, a wurin lunching, Su hubby suka shigo. Kadan daga cikinsu suka amsa musu sallamar.

Ganin yadda suka kuresu da ido, yasa su hubby suka gaishesu in jam'u. Har sun wuce samira ta ce " kai Allah mun gode maka, yanzufa yan matama kwantai suke, balle zawarawa, shiyasa sai kiga ana neman likawa jamaa dole." Ta fada da karfi yadda su hubby zasu jiyota.

" oho!!! Kuma!! In ta wuce kan mijina, ta fada kan kowama, bai daman ba." Munaya ta fada tana hararar bayan hubby.

Basu kai ga jin karashen maganar ba, suka shige, duk da su yusra basu San kan zancen ba, sun dauka hira kawai suke, amma ita hubby ta San da ita suke. Ranta ya baci amma bata da lokacin batawa a Kansu. Koma mai zasu ce, sun dade basu fada ba.

                *****************
Alhaji Jamal bai shigo gidan ba sai to 12am. Allah yasa Hajiya ranar ita keda girki. Hakan ya bata damar tattaunawa da mijin nata, a tsanake.

Abdul Karim kam bai samu shiga wurin Mmn samira ba, ana idar da sallar isha'i, suka fita da arif daya iso daga legos, lokacin da suka shigo gidan already late. Anty samira ma data kirashi hakuri kawai ya bata, kan zasu hadu da safe.

Hayder ranar raba dare yayi yana addua. Tare da kai kukansa ga mahaliccinsa. Don har ga Allah baya jin son hubby ko digo a zuciyarsa. To yarinyar da ko soyayyar yan uwantaka bata hadasu ba, ina ga soyayyar aure? Hankalinsa ya dan kwanta, ganin har ya bar gida, zuwa in da suke kwana, saboda baki, Hajiya bata masa maganarba. Yana fatan Allah yasa kunnensa ne bai jiyo masa dai dai ba.

                *******************
Tagumi mommy Hauwa ta zabga bayan ta gama jin bayanin bakin Alhaji Munir. Gaba daya lamarin ya isheta ya daya, amma kullun a kazo maganar aure sai ran kowa ya tashi, mu samman wannan karon.

Ajiyar zuciya mommy Hauwa tayi tare da kallon maigidan nata. " da kamar wuya, wai hurguwa da auren nesa!!! Wannan hadin gaskiya bayyi ba, kowa yasan tsakanin hubby da hayder kamar masu ganin hanjin juna, tun tasowarsu, har zuwa yanzu. Sannan hubby ita take gaba dashi a haife, ta ina zaa fara wannan danyen aikin? Kudai canza dabara gaskiya, kar azo ayi abinda za ayi dana sani."

Zama Alhaji Munir ya gyara, tare da fuskantar mommy Hauwa da kyau. " kin ban mamaki, ban taba tunanin wannan magana zata fito daga bakin kiba. Har kin manta da halaccin yar uwarki gareki? A tunanina ko yayayyen yaro Hajiya ta bukaci hada Ummi dashi bazaki ja da ita ba, balle danta na cikinta. Meye sharuddan da ya can -can-ci a ba namiji aure? Wannene hayder bai cika ba? Ban zama butulu ba, bazan taba manta alkhairi Hajiya da mijinta ba, kai harda su Alhaji babba, irin karamci da mutunci, da soyayya da suka nuna min, tun haduwata da omer, har zuwa jajur cewa da sukayi wurin ganin na aureki, har zuwa yanzu. Ni ko mai zan musu in biyasu? Babu!!! Na dade ina rokon Allah ya bani ikon saka musu da abunda suma zasuji dadi  komai kankantarsa. Auren Ummi da Yusuf ba karamin dadi ya min ba, duk da kalubalen da ni kaina nasan dasu. Haka ma yanzu ina son ki Sani, daga ke har Ummi ba shawararku nake nema ma. Umurni nane dana mahaifina, gobe in sha Allah bayan sallar jumaa zaa daura auren Ummi da hayder. Don haka duk abunda ake bukata ki natsu ki rubuta, gobe in Allah ya kaimu aje a siya. Don Sunday zata tare dakin mijinta, kamar sauran yan uwanta."

" bana kin hadin nan, kamar yadda kake fada, hasalima nafi kowa murna. Abu daya zuwa biyu ke damuna. Sanin halinsu, sai nake ganin zaman nasu kamar da wuya a samu yadda ake so." Mommy Hauwa ta fada tana sauke ajiyar zuciya

" addua zaki bisu dashi, ita suke bukata. Lokacin da zasu shirya kina ina? Karki manta ko ba komai yan uwan juna ne! Aure ya wuce duk inda kike zato. In sha Allah sai kin ce gara da akayi. Hakika nayi dacen suruki daya tamkar da dubu., hayder yarone, amma mai halin manya. Ke kanki abunda kika sani ne, ba yarinta a tare dashi, sai kamala, da mutunci, da sanin ciwon kai,da sanin ya kamata, Ga kamewa." Murmushi mommy Hauwa tayi " hakane kam, sai dai yarinyar taka fa zaa sha fama."

" don't mind her, barni da ita. Su gwaggo da tawagarta na nan isowa gobe, a gyara part din can su sauka a ciki, don gayya zatayi, kamar yadda ta fada min a waya. Tayi farin ciki sosai da jin wannan maganar."

" ai fa? Bikin mutuniyarta, don ma lokacin yazo a kure."

" haka ne!!; Ummi da gwaggo kam ai sai Allah, don ma ba kiji yadda take murna ba, ke kyace an mata albishir da gidan aljannah. "

" mutuminta ne Hayder, abun ya zama mata biyu. Takwara da balarabenta." Mommy Hauwa ta fada tana murmushi

Murmushi Alhaji Munir yayi, tuno drama din gwaggo da hayder. Gwaggo akwai son hira, ga jininsu ya hadu sosai da hayder, hayder ba Hausa sosai, gwaggo ba larabci, so in kaji hirar dole kayi dariya, mu samman yadda yake takar karewa sai yayi Hausa, in ya kakare gwaggo na dariya zata murda nata larabcin ta masa bayani yanda zai gane. In kana kusa, ba kayi wasa ba har fitsari sai kayi a wando, don dariya."

Hayder daga turanci, French, sai larabci sune manyan yaren da yake ji in yanayi kamar a bakinsa aka kirkiro. Hausa yana jin duk abinda zaka fada, mayar wane sai a slow. Don gidansu gaba daya baa wani yare banda arabic. Friend da sauran yan uwa da basa ji, sai dai suyi turanci. A school nema ya samu ya ji hausar don a gida ko iyayensu mata basu isa suyi musu Hausa ba, dokar Alhaji Jamal ce, dole a kiyaye a zauna lafiya.

            **********************

Yauma tun daga sallar asuba, Alhaji Jamal bai dawo gidansa ba. Hakan yasa basu hadu da Abdul Karim ba.

Koda ya shiga cikin gida, Hajiya kaka bata samu damar mayar masa da yadda akayi ba, saboda yana tare dasu arif. Anty samira kuma suna part din yara matan gidan. Ko da sukaje gaishe da Hajiya ita ma bata nuna masa komai ba. She act normal kamar yadda ta saba, duk da taji zafin jin cewa baya son hubby.

                  *****************
Chapter 15 · 0% Book details