Part 12
Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 31 min read
Written By Zulaihat Aliyu Misau
Wattpad@zulaihatualiyumisau
Not Edited.......
Tattaunawa akan daya daga cikin wannan mau'du'in. Muhimmancin ilmin da namiji, da ya'mace, sai muhimmancin auratayya tsakanin maban banta kabilu. Da harshen larabci
Tsaki hubby ta yi ta jerowa daya bayan daya. Ba wai larabcin bane bata iya ba, yanda zata jera point din. Sannan tana da matsala har yanzu wurin jera wasula.
"Alhamdulillah" ta fada lokacin da aka fara raba abinci, don tana bukatar sake nazari, duk point din data dade da tanada sun watse.
Hankalinta kwance ta dibi girki yadda ya kamata, ta kora da coca cola mai sanyi. Hayder ta kalla da ke shan tea. Ta tabe baki
Book dinta ta dauko ta ci gaba. Takaici ne ya ishi hayder, yadda hubby ta cika masa kunne da tsakinta
Littafin ya kalla don ganin me take rubutawa. Dariya ce ta kusa kamashi. " zero head, aikin yan kananan yara, amma ta kasa ta ishi mutane da tsaki." Ya fada a ransa
Kallonta yayi yadda ta takar kare kamar gaske.
Biron ya fige a hannunta, da sauri ta bishi da kallo, book din ya janyo ba tare daya ce mata komai ba, ya daura kan abin cin abinci, da zaka janyo mai kama da table ya fara rubutu.
" ban son rashin mutunci, taya zaka wani fige Abu a hannuna, kana shigamin hanci da kudun dune fah."
Ko kulata bai yiba, kallon rubutun take mai matukar kyau, a tsare. Kamar ingin ke rubutawa. " komai sai an masa yanga, rubutun ma ji yadda yake, kamar baya son yi."
Sai da ya gama, ya ajiyemata a gabanta da biron. " please leat me sleep in peace. " ya fada yana tsareta da ido.
" da yake na rike maka ido ba?" Kai ya kada tare da lumshe idanuwansa.
Taji dadi sosai, yanda ya tsara mata bayanan dalla dallah. In gan taccen Arabic. A Jakarta ta tura book din " shishshigi kawai, ko an gaya maka na kasa ne?"
Ya jita sarai, ya shareta. Don yasan albarkacin Yusuf take ci. Da ba dan haka ba da ko kusa bazata kara wargin shiga harkarsa ba. Yana respecting dinta ne saboda sanin matsayinta a zuciyar yayan nasa, da irin kyakykyawan zaman da sukayi, da duk lokacin da zaka zauna da Yusuf Ku dan dade sai kasan yadda ya damu da ita, haka ita ma. ta wani gefen kuma yana tausaya mata saboda rashin da tayi, Wanda maye gurbinsa zai mata wuya a rayuwa. Shi duk da jinin da suka hada da ita, kwata kwata baya jinta a ransa. Har mantawa ma yake da ita.
*******************
Dawowarsu da one week aka shirya wasu hayder hadaden get together and babaque. A harabar gidan Alhaji Jamal.
Abun ya kayatar sosai, yan uwa da abokan arziki duk sun hallara. Sir omer, da iyalansa, Jamil ma da nasa iyalan, Alhaji babba, shima da friends dinsa. Gidan ba masaka tsinke, kamar ana wani gagarumin biki.
Mommy Hauwa da friend dinta Hajiya salwa suna zaune a falon mommy Hauwa, yan aikinta na faman hada gifts din da already anyi packaging dinsu a manyan buhu, suna fita dasu mota.
Hubby ce ta shigo kamar an korota. Kallo daya mommy Hauwa ta mata taji gabanta ya fadi.
Batayi tsammanin samun mommy a gida ba. So ganinsu a zaune yasa tayi kokarin saita kanta, tare da share hawayen da suka wanke mata fuska.
" sannunku da gida." Ta fada tana wucewa dakinta da sauri, gudu gudu.
Dukkansu da kallo suka bita. Mommy Hauwa ta ja ajiyar zuciya ganin ta shige.
Hajiya salwa ta kalli mommy Hauwa dake kokarin yafa mayafinta. Bayan sammani ya fita da buhun karshe. " kina nufin tafiya zakiyi ba tare da kin je kinga halin da yarinyar nan take cikiba? Wai ke me yasa kike haka ne? Kina ganin ta shigo da irin wannan damuwar, ai kya je kiji abinda ya fusatata haka? In baki jata a jikinki ba kin san matsalarta,wa kike son ya miki wannan aikin. Bayan keda kike uwarta kina nuna ko in kula kan lamurranta. Shiyasa ta zabi zama da gwaggo sama da ke da kika haifeta."
Murmushi mommy Hauwa tayi, mai kama da yake " bazaki gane lamarin Ummi ba ne."
" ta ya zaki gane kuwa? Tunda baki jata a jikinki ba." Hajiya salwa ta fada tana nufan dakin hubby cikin jin haushin kawartata.
Tana jikin Woodruff kayanta take fito dasu, ga akwatunana har biyu manya ta bude tana jefa kayan a ciki. Hawayene wani na bin wani a fuskarta. Sai Jan hanci take. Tausayinta ne ya kama Hajiya salwa. Hannunta ta kamo suka nufi bakin gadon hubby. Kuka mai karfi hubby ta fashe dashi ta daura kanta a cinyar Hajiya salwa. Hajiya salwa bata ce mata komai ba, sai shafa kanta da takeyi alamar lallashi. Ta bata damar tayi kukan ko taji saukin damuwarta.
Mommy Hauwa ce ta leko, don taji shirun yayi yawa, gashi ana can ana jiranta. Kallonta Hajiya salwa ta yi " ki tafi kawai, zan isoki" juyawa mommy Hauwa tayi ba tare data ce komai ba. Amma ita kadai tasan damuwar da zuciyarta ke ciki. Mawuyacin Abu ne kaga kukan hubby, don ita sha yanzu ne, maganin yanzu. Kana gaya mata cuta ta gayama mutuwa, shike nan ya wuce a wurinta. Amma muddin kaga tana ma Abu kuka to ba karamin Abu aka mata ba.
Sai da tayi kukanta mai isarta. Sannan tayi shiru, tana Jan ajiyar zuciya. " komai yayi zafi maganinsa Allah. Ki daina sama kanki damuwa irin haka, duk da bansan dalilin kukan ba na tabbata ba karamin Abu bane zai saki kukaba." Hajiya salwa ta fada tana mai mata kallon tausayawa. Kanta ta sunkuyar tana wasa da yatsunta. Don duk a kawayen mommy Hauwa tafi jin nauyin ta da ganin girmanta. Don Matar tanada mutunci sosai. Ga sanin ya kamata.
" ki gaya min waye ya taba min ke?"
Shiru tayi ta kara sunkuyar da kanta. Duk yadda Hajiya salwa ta so hubby ta gaya mata damuwarta amma ta kasa. Saboda nauyinta da takeji. " shi ke nan, ni zan tafi tunda ban kai matsayin da zaki gayamin damuwarki ba."
Hannunta hubby ta riko " kiyi hakuri wallahi ba haka bane."
" I understand. But waannan kayan fa da kika fara hadawa?"
Kallon kayan hubby ta yi sannan ta sunkuyar da kanta " gobe zan koma kankiya."
Kada kai tayi, tana jin jina sakaci irin mommy Hauwa.
" ita matsala in ta samu ba guje mata ya kamata a yiba, fuskantarta za ayi don a maganceta, saboda guje mata kamar barin baya da kura ne." Ta fada tana mikewa.
" na gode sosai, ki gaishe min dasu Faisal." Hubby ta fada cikin girmamawa
" zasuji." Ta fada Tate da ficewa a dakin. A harabar gidan sukayi karo da Ummul khair da ummu sulaim suna shigowa. Gaisheta sukayi cikin girmamawa, sannan suka wuce ciki.
A gogo hubby ta kalla 9:43 na dare. Tsaki tayi ta tashi ta ci gaba da hada kayanta.
Kai tsaye dakin hubby suka nufa. Da sallama suka shigo. Dagowa tayi daga jera kayan da take cikin akwatin ta bisu da kallo. Tare da amsa sallamar." Me zan gani haka?" Ummul khair ta fada tana zama a bakin gadon. Ummu sulaim kam kujerar madubi taja ta zauna tana bin kayan dake wargaje da kallo.
" abinda idonki ya gane miki." Hubby ta bata amsa
" kar dai maganar waannan sakarkarun ne? yasaki kike son tafiya?"
Tabe baki hubby tayi tana ci gaba da ninke kayanta. " ko kadan, lokacin tafiyar tawa ne yayi."
" be kamata ki damu kanki ba, kan wannan maganganun shirmen, tun da kin San ba gaskiya bane. Ba komai yake damun munaya ba illah kishi da zugan su Anty samira." Ummu sulaim ta fada cikin takaici
Hawaye ne suka fara bin kuncin hubby " ta Yaya bazan damu ba? Kina jin irin sunayen data dinga kirana dasu a cikin jamaa. Tun da nake baa taba min tozarcin da ya bakanta min rai ba irin na yau. In kece ya zakiji?"
Kada kai ummu sulaim ta yi, cikin jin zafin abinda akawa yar uwarta. " a kwai ciwo kam, shi yasa na tsaya na basu nawa piece of mind din."
" na rasa abin da ya kawo wannan maganar. Naga da safe har gaisawa kukayi da ita lafiyar Allah." Ummul khair ta fada
" ki kyale abu, in har aka ce da munafurci a ciki. Anty samira yar uwata ce, amma Sam halayyarta basu min ba. Ta cika kananun magana da son hada wuri. Ina wurin munaya ke bamu labarin Ahmad ya kaiwa hubby su Arafat sun mata wuni. Da irin yadda yaran suketa labarin yadda ta kula dasu har basu so komawa ba. Munaya na ba su Anty samira labarin yadda take jin dadi, da yadda take son hubby saboda tana son yaranta. So na barsu suna ta hirar kin San munaya in kanason ka gama da ita to ki nuna kina son yaranta. Yanzu zaki ga mutunci. So ina ganin bayan na bar wurin ne suka zugeta."
" in banda dabbanci tayaya zatayi tunanin ni hubby in rasa Wanda zan so sai Ahmad? Tsakanina da Ahmad mutunci ne, da ganin darajar juna. Duk cikin yan uwan Yusuf ba Wanda yake bibiyar rayuwata sama da shi. Su suna ganin kaman zuwan da yake yi kankiya wani abun ke kaishi. Wanda kuma wallahi ba haka bane. Ko da wasa ban taba ganin wani alama ko kadan sabanin zumunci da mutuncin dake tsakaninmu ba. Shi yasa nima nake mutuntashi nake ganin girmansa."
" that's it. Wannan shine yasa suke ganin soyayya kukeyi. Don ni Anty samira ta so ta bugi ruwan cikina don taji wani Abu a bakina. Amma na nuna mata ban taba ji bama, har nake ce mata wannan ai tatsuniyar yara ce, ina hubby ina Yaya Ahmad. " Ummul khair ta fada cike da takaici.
" amma dai kin San baki mana adalci ba in har kika ce tafiya zakiyi, bayan kin San biki nan ba wani lokaci aka sa da yawa ba, just 3weeks." Ummu sulaim ta fada tana kallon hubby
" kiyi hakuri, gaba daya garin ya fita a raina. Kin San jiya salis har gidan nan yazo, ni na dauka abin arziki ya kawoshi,ba kunya ba tsoron Allah wai sona yake yi.
Ido suka zaro a tare " wane salis din? Yaya salis?" Ummul khair ta tambaya harda sassarfar magana.
" shifa!!!! Bama shi yafi ban haushi ba irin Engr Sahabi, harda wani shi ya dace ya maye gurbin marigayi. Mu rufawa juna asiri." Dariya su ummu sulaim suka sa. Haushi da takaici ya kara cika hubby.
Cikin dariya Ummul khair ta ce " sai kika ce masa me to?"
" bar dan iska, an gaya masa kwantai nayi? Ko kwantan nayi nafi karfinsa wallahi. In ba rashin kunya da rashin tunani ba tayaya yana abokin mijina, kawai don ya rasu ya wani zagayo. Sai ma kunji yadda yake wani kashe murya kamar in sanu muciya in ta dukan banza don haushi."
Har lokacin su ummu sulaim dariya suke ma hubby. " kin San dama an ce da budurwa da bazawara, kamar kasuwa ce, da mai brush da Mara brush kowa ya gani ya gyasa sai ya lallabo, sai in yaga no go no go sai ya kara mai. So kadan ma kika gani. Shiyasa gara mutun yayi aurensa ya huta. " Ummul khair ta fada
Harararta hubby ta yi " dama ke kam gara da aka hada dake, don naga kin fiye son aure da yawa. Ni kam ban shirya ba, ba kuma rana."
" ai kuwa yanzu kika fara ganin irinsu Engr masu son rufa miki asiri." Ummu sulaim ta fada tana dariya.
" zan kara ganin kafarsa a nan gidan, sai na tata masa rashin mutunci. Yanda gobe ko mai kama dani bazai kuma marmarin tunkara ba."
" kar kiyi haka, tunda bakya son sa just find a way da zaku rabu a mutunce, yaci albarkacin Yaya Yusuf kodan mutunci da zumuncin dake tsakaninsu." Ummu sulaim ta fada
" ya labarin hot guy?" Kallonta hubby tayi. " waye kuma hot guy? "
Harararta Ummul khair ta yi " karki raina min hankali man. Bayan naji labarin komai."
Tsaki hubby ta yi "sai ki je ki tambayi Wanda ya baki labarin. Kinfa fara raina ni, kar kiga ansa miki ranar aure ki shiga hankalinki dani."
" Allah baki hakuri. Don Allah dan ban labarinsa mana? Yaushe ze zo, na kosa in ganshi"
" ban Sani ba." Hubby ta fada
Sun dade suna hira, har 11 na dare, sannan sukayi sallama da hubby ta rakosu har jikin mota. Sannan ta koma. Already lokacin an tashi daga get together da babaque din su hayder.
Hubby na shirin kwanciya su mommy Hauwa dasu jabir duka dawo. Tana jin hayaniyarsu a falo taki fitowa, adduar bacci tayi ta gyara kwanciyarta.
Sai da kowa ya kwanta, sannan mommy Hauwa ta nufi dakin hubby.
Da akwatunan hubby ta fara karo. Kafin ta nufi gadon da hubby ke kwance. Bubbuga kafarta tayi, Wanda yasa hubby bude idonta, ganin mommy Hauwa yasa ta tashi ta zauna. Itama zama tayi a bakin gadon tare da kamo hannun hubby cikin nata. Cikin murya mai taushi " me ya faru kika dawo, dazu ba tare da an kammala abin da ya kai ki ba? Rai a bace? Ke da wa?" Ta jero mata tambayoyin a tare.
Cikin damuwa ta fara zayyanowa mommy Hauwa yadda sukayi da munaya. Dasu Anty samira. Ajiyar zuciya mommy Hauwa tayi ranta ya baci sosai amma bata nuna ba.
" wannan kayan fa?" Ta tambaya tana kallon kayan
" gobe zan koma."
Kada kai mommy Hauwa tayi " ki cire maganar komawa kankiya a ranki, don babu. Lokaci yayi da zaki tsaya ki zaba ma kanki mafita. Tunda kin nuna baki son karatu, to ki fito da miji mu aurad dake, don bazai yiwu ba karatu ba aure ba. Wannan yaron in har da gaske yake, to ki shaida masa ya fito."
" bafa soyayya muke ba, just friend dina ne." Hubby ta fada da saurinta.
Kallon ta mommy Hauwa tayi na dan lokaci kafin ta ce " shi kenan dama Hajiya salwa ta dade damun maganar tana son hada ki da Husain, ni na dakatar da ita, saboda sanin halinki, but zan gaya mata ta turoshi Ku dai dai ta. Hankalina dama bai kwanta da wan can yaron ba."
Da sauri hubby ta diro daga gadon, " mommy wane Hussain din?"
Harararta mommy Hauwa tayi " daya da kika Sani. Ki zama a cikin shiri daga gobe zuwa jibi zaki iya ganinsa a gidan nan. Ki natsu banda rashin hankali, kin dai San yadda muke da Hajiya salwa." Ta fada tana kokarin barin dakin.
" don Allah mommy kiyi hakuri, wallahi ni dai bai min ba."
Kallonta mommy Hauwa ta tsaya yi kafin ta kada kai ta fita.
" innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Meke faruwa da rayuwata ne? Daga wannan sai wannan. Ina ita ina Hussain miskilin mutun number daya hatta ita hanta Hajiya salwa kullun cikin korafin miskilancinsa take, gashi da murdadden hali ya hadu da zamowarsa soja. Tun da suke haduwa dai dai da rana daya bata taba ganin dariyarsa ba, magana ma wannan ko gaishe shi sukayi sai dai ya daga maka kannu kawai. Bata manta hutun data taba zuwa gidansu lokacin tana SS 1 irin dukan da sukaci ita da kanwarsa salma kafin ta rasu. Saboda surutunsu,.
Akwai ranar da har tsallen kwado ya sasu. Kwanansu biyu suna jinyar kafafu. Ita kanta Hajiya salwa shakkarsa take yi.
Ta kasa barci, saboda damuwa da nema ma kanta mafita. At last ta gama tunanin abinyi. Ajiyar zuciya tayi. Tana Allah Allah gari ya waye taje ta samu daddynta.......... Sunday, tun da sassafe hubby ta tashi. Ta gama saka kayanta a mota. Sannan ta kira malan iro. Don ta shaida masa ya zama cikin shiri by 11 zasu wuce zuwa kankiya. Saboda daddy dinta baya yadda tayi driving zuwa wani gari.
Sai 10 sannan mommy ta fito daga side din daddy. Dama hubby ta dade da shiryawa tana jiran tashin daddyn nata. Don tasan weekdays baya tashi da wuri.
With full confidence ta nufi part din daddy tare da sallama. A falo ta sameshi yana kallon tashar CNN. Cike da faraa da jin dadi yake kallon tilon yar tasa. " ummina an har tashi?" Murmushi tayi tare da gaisheshi tana zama kasan carpet cike da ladabi. Kallonta yayi yana murmushi " sai inah? Da safen nan?" Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta. " ina son komawa kankiya yau. Kayi hakuri da ban sanar maka da wuriba." Kallonta yake yi yana karantar yanayinta.
" mun riga mun gama magana da Alhaji. Zaki ci gaba da zama damu a nan. Har Allah ya fito miki da miji kiyi aure. So ba maganar komawarki kankiya, u stay with us."
Lokaci daya hawaye suka fara bin kuncin hubby. " please daddy kayi hakuri ka barni in tafi, nafi son zama a can don Allah. "
Ajiyar zuciya Alhaji Munir yayi. " me muke miki da kike gudun zama damu Ummi?" Kar ta kada cikin muryar kuka ta ce "ba komai, bakumin komai ba."
" so kamar yadda na fada ne, ba komawa kankiya. Sannan ki fito da miji cikin masu sonki Wanda hankalinki ya kwanta dashi. Don so nake a hada dana jafar tunda Allah yasa ya fito da yarinyar da yake so.
Kuka ta fashe dashi tana ba daddy hakuri, ita wallahi ba Wanda take so.
" shi kenan dama mommynki tamin bayanin dan wurin Hajiya salwa. So in yazo naji yanda kukayi."
" wallahi ni ban sonshi, don Allah daddy ka taimakeni ka gayawa mommy karta ce musu yazo."
Tausayi hubby ta bashi, ganin yadda take ta risgar kuka, amma ba yadda ya iya dole a matsayinsa na uba ya sauke nauyin da Allah ya dora masa. Ya tuno da maganganun da sukayi da Alhaji kawu.
Gyara murya yayi. " shi kenan zan gaya mata, amma bisa sharadi daya."
Da sauri hubby ta rarrafo hannunta ta daura kan gwuiwowin Daddy tare da kwantar da kanta. " na yadda da koma wane sharadi ne. Matukar mommy baza ta turo min wannan monster din ba." Ta fada tana Jan hanci saboda kuka.
" na baki nan da 2weeks ki fito da miji, don gaskiya na gaji da ganinki ke ba aure ba, ke ba karatu ba. Sai gararanbar association"
Da sauri ta dago cike da firgici da tsoron kalaman daddy. " kaji tausayina daddy don Allah. " ta fada cikin marairaice murya, baki na rawa ga hawaye nabin fuskarta.
Tausayi sosai ya kara kama Alhaji Munir. Gyara zama yayi. " Ummi hakan shine soyayyar, kowanne uba yayin da yarsa takai munzali fatansa ya aurad da ita. Don shine mutuncinsa kuma mutuncinta, ballan tana ke da kin taba yin auren, kin San dadinsa da rashin dadinsa. Don wata kaddara ta gitta, baya yuwuwa ki yankewa kanki kin sake wani auren. Hakan na nuni da kina fushi kenan da hukuncin Allah. Bayan sanin kanki ne duk abun da ya samu bawa to kaddararsa kenan, ya kamata ya rungumeta hannu bibbiyu, yayi fatan ta zamo masa alkhairi duniya da kiyama. Wannan shine daya daga cikin alamomin musulmi na kwarai. Yadda da kaddara mai kyau ko akasinta. A yan kananan shekarunki bai yiyuwa mu ajiyeki muna kallo, ba muyi miki adalci ba, bamuyi wa kanmu ba. Don haka ki kwantar da hankalinki, ki natsu cikin masu sonki in akwai Wanda ya kwanta miki, ki shaida masa ya fito, kiyi aurenki, shine cikar kamalarki, in kinyi haka muma kin tsare mana namu mutuncin."
Cikin kika " in sha Allah zan yi yadda kuke so."
" Allah ya miki albarka, ya baki miji na gari, da Yaya masu albarka wa' anda zasuji kanki kema. In sha Allah bazaki taba dana sanin biyayyar da kikai mana ba. Ina alfahari da zamowarki ya a gareni. Na gode."
Rungume mahaofin nata tayi. " na gode daddy da adduarku garemu. Ina alfahari da zamowarki iyaye na gari a garemu."
Murmushi mommy Hauwa tayi ta dade tsaye a bakin kofar, amma basu kula da shigowarta ba. " in an gama tattaunawar tsakanin uba da yarsa, sai muje a ba ciki nashi hakkin." Murmushi hubby ta kakalo tare da ficewa daga dakin.
Da kallo iyayen suka bita cikin tausayawa. " akwai rikici fa!!! Sai kinayi kina bata baki."
Murmushi mommy Hauwa tayi " ummin ce wani lokaci Zuma ce, sai da wuta. Kasan tun sassafe har ta sa kayanta a mota? Gani kawai take data zo ta kallalameka zaka barta ta tafi."
Ajiyar zuciya Alhaji Munir yayi " kema da naki laifin ai. Ban son ki kara mata maganar Hussain tunda ta furta bata son sa shike nan."
" Allah ya zaba mata miji na gari, amma gaskiya naso wannan hadin. "
" mata kenan, kibar yarinya ta zabi wanda ranta keso. Kedai naki ki bita da addua."
" ai shi kenan, na farko ma ya akayi, balle na biyu. Allah ya mana jagora."
" amin" Alhaji Munir ya fada, a tare suka nufo part din mommy Hauwa don yin break fast kamar yadda suka saba.
Already su jafar, jabir, junaid sun halkara saman dinning table suna jiran iyayen nasu.
Toilet direct hubby ta wuce ta wanke fuskarta. Sannan ta nufo dinning din.
*******************
Kwance take saman gadonta, sai sakawa da kwancewa take. Lallai ta yadda da maganar da hausawa ke cewa mutuwa mai tonon asiri, tabbas haka maganar take, dabadon mutuwa da yanzu tana tare da mosoyinta, wata kilama harda da ko ya. Tunanin yadda zata iya zama da wani mijin ba Yusuf ba take. "Yanzufa dole in auri wani? Dole yadda Yusuf ya sanni shima haka." Runtse idonta tayi hawaye mai zafi na bin kuncinta. Don ba abun dayafi daga mata hankali irin hada shinfida da wani ba Yusuf ba. To ita yanzu waye zata fitar? Hashim, suraj ko Munir.
Kai no!!! Ba dai Munir ba, yaron da suka taso tare tasan kuruciyarsa yasan nata. After all ya mata yaro da yawa. Hashim kuma gaskiya tana tsoron zama da kishiya, don bata tashi ta ganta a gidansu ba. Balle yadda ake fadin hatsabibancin matarsa, gaskiya bazata sa kanta a shiga uku ba. Suraj yes!!! Zata iya aurensa don ta lura yana matukar sonta, sai dai tana ganin kamar ajinsu ba daya ba, zai yi wuya aurenta dashi. Don difference din is Claire.
Agogon dakinta ta duba 1:6 pm mikewa tayi ta dauro alwala, bayan ta idar da sallar azhahar ta dora da salatul istikhara, 2 rakaat. Rakaar farko fatiha da suratul khafirun, rakaa ta biyu fatiha da ikhlas. don neman zabin Allah
Bayan ta idar tayi tasbihi, da istigfar ta karanta adduar istikhara.
Allâhumma inni astakhiruka bi ilmika wa astaqdiruka biqudratika wa as’aluka min fadlikal-azimi, fa innaka taqdiru walâ aqdiru wa ta’lamu walâ a’lamu wa anta allamul ghuyubi. Allâhumma in kunta ta’lamu anna hâdhal amra ( bukata ) khayrun li fi dini wa ma-ashi wa aqibati amri faqdir-hu li wa yassir-hu li thumma barik li fihi wa in kunta ta’lamu anna hâdhal amra( bukata ) sharrun li fi dini wa maâshi wa aqibati amri fasrifhu anni wasrifni anhu waqdir liyal-khayra haythu kâna thumma ardini.
Wani natsuwa taji yana ratsata. Tana cikin ninke sallayar Aisha tayi sallama. Yar da sallayar tayi da gudu ta rungumeta tana mai matukar farin cikin ganinta.
Cike da farin cikin ganin juna kamar ba jiya suka rabuba. Aisha ta kalli hubby " sis meya faru? Kar dai maganar jiya ce, tasa kikayi zuru zuru haka? Kamar wadda ta kwanta cuta."
Tabe baki hubby ta yi " abubuwa sun kwabe, dama na rasa abokin shawara. Na gode Allah da kika zo at right time "
" tare da Yaya Ahmad muke, yazo ya baki hakuri, baiji dadi yadda kukayi dasu munaya ba. Muje in mun dawo sai mu tattauna."
Tsaki hubby ta yi " wallahi ban son ko ganinshi. Da zaki taomakeni ki ce masa bananan."
Harararta Aisha ta yi " laifin wani dai baya shafar wani. Meye laifinsa a cikin rikicinku? Ki tashi muje don sauri yake, mu samman yabar aikinsa don yazo ya baki hakuri, muje."
Ba yadda hubby ta iya, haka ta zunbulo hijab dinta har kasa. Don Ahmad ya wuce ta masa wulakanci, saboda girma da mutuncinsa da take gani. Tabbas laifin wani baya shafar wani.
Sosai ya nuna rashin jin dadinsa, tare da bata hakuri. "Ba komai, yariga ya wuce" ta ce masa. Ya mata godiya sannan sukayi sallama ya tafi.
****************
Shiru sukayi kowa da abunda yake sakawa, bayan hubby ta gama zayyanowa Aisha matsalarta.
Nisawa Aisha ta yi " maganar su daddy gaskiya ne, lokaci yayi da zaki yi settling. Ni ina ga ki ba suraj dama ya turo. Gayen ya hadu, kuma yana sonki.after all da ganin alamunsa zai yi riko da addini."
" kayya dai!!! Baka ganewa a fuska"
"Haba ke kuwa, kina ganin tabon sallah a goshinsa, ai kinsan ko ba komai yana yinta."
" Allah yasa." Hubby ta fada
" naga alama kamar hankalinki yafi kwanciya da Dr Hashim. " Aisha ta fada tana dariya.
Harararta hubby tayi tare da Jan tsaki. " ni kam duk cikinsu ba wanda nake jin wani Abu a kansa. Sai dai kawai zan iya cewa na danfi ganin dama damar suraj, duk da dinbin matsalolin da nake hangowa."
" in haka ne, mai zai hana ki ba Hussain dama, wata kila in kin fahimce sa, kiga sabanin zatoki, kin San duk muskilancin mutun yakan dagawa matarsa kafa. Sai ki sha mamaki irinsu. Musamman akayi dacen yana sonki. Kuma kamar mommy hankalinta yafi kwanciya dashi."
" ina!!!!! Bada ni ba. Auren soja sa mutun ya shirya."
Dariya Aisha ta yi " nifa kike zagi da wayau."
" kinga zaki iya ne ai." Hubby ta bata amsa tana murmushi
" to koda Engr Sahabi za ayi." Duka hubby ta kai mata " Allah ya kyauta."
" maganar gaskiya dai ko suraj ko kuma salis. Don salis yayi gaskiya bashi da aibu."
" ke a tunaninki zan iya auren abokin Yusuf? Ko kadan don haka ki saka zancen wani salis a dustbin. "
" halacci ke nan aboki in ya mutu ko ya saki matarsa ka aura."
" Allah ko? To baa kaina ba. Don ni ko Wanda ya San Yusuf ban iya aura, don ina ganin kamar naci fuskarsa ne. Gara min bare inyi maneji."
" Allah ya zaba miki mafi alkhairi"
" amin."
Hirar bikin su Aisha suka fara, da yadda ya kamata komai ya kasance.
Sai 5pm Aisha ta masu mommy sallama, hubby ta rakota compound dinsu, in da driver gidansu Aisha ke jiranta.
Tsayawa sukayi jikin motar, suna maganar fita da zasuyi gobe saboda wasu shirye shirye daza su fara.
Wata hadaddiyar fox jeep ce ta shigo compound din. Baka wuluk sai daukar ido take, gashi tasha tilted da bazaka iya ganin wanda ke ciki ba.
Da kallo su hubby suka bi motar. Aisha ta kalli hubby, hubby ma aishan ta kalla. Suka sake maida hankalinsu kan motar data parka kusa da motar su Aisha..........
Toh!!pa!!!! Suraj, ko Dr Hashim, Munir, ko Engr Sahabi, ko kuma salis...
Wani hadadden half cover shoe army green ya fara musu sallama, bayan kamshin da ya cika hancinansu, da kofar driver ta bude. Sanye yake da shadda mai matukar daukar ido, light green, kanshi na sanye da hula damanga, army green. Yayi matukar kyau ga kamshi, kamar ya fito daga shagon turare.
Aisha ta kalli hubby " wannan hadadden guy din fah!!!" Da yake bata taba ganin shiba sai labarinsa da take ji.
Tabe baki hubby ta yi " suraj" ta fada a takaice, a hankali yadda bazai jiyo suba.
Fuskarsa cike da faraa ya nufo in da suke tsaye, Cikin takunsa na kasaita.
" u are lucky sis. Please don't let him go." Aisha ta rada mata kasa kasa.
Sallama ya musu, Aisha ce ta amsa masa fuskarta dauke da murmushi.
" what a lucky day. " ya fada yana kallon hubby da kanta ke sunkuye. Yau daya tun haduwarsu dataji nauyinsa.
Aisha ce ta gaisheshi, cikin mutunci suka gaisa. Sannan hubby ta gaishe shi.
Murmushi yayi yana karewa hubby dake sanye da dogon hijab har kasa brown kallo. Ta masa kyau sosai duk da ba wani kwalliya ce a fuskarta ba.
" to hubby sai goben in mun hadu." Aisha ta fada tana kokarin shigewa mota.
Kallon hubby yayi yana murmushi " baki gabatar min da kawar tamu ba, har zata tafi."
Hannun Aisha hubby ta kamo. " Aisha Jamal Yusuf zubair Oregon, sister din su hayder, my Best friend and also sister. "
" masha Allah, best friend ya kike, ya hidimomi."
Murmushi Aisha ta yi " lafiya kalau, kazo lafiya."
Nan fa hira ya barke tsakanin Aisha da suraj, don shi mutunne mai saurin sabo, da alama yana da son hira.
Hubby dai yar kallo ta zama, sai mamakin Aisha take yadda ta sake dashi kamar sun dade da sanin juna.
" I have to go, nice to meet u." Aisha ta fada tana murmushi
Shima murmushin yayi " nice to meet u too friend. " sallama sukayi da Aisha ta shige mota suka yi gaba.
" bismillah." Hubby ta fada tana yin gaba. Binta yayi da sauri suka jera.
Shuke shuke ne na fruit, sai kujeru singles kusan guda biyar. Wurin hirar su jabir ne da abokansu. Wurin yayi kyau. Daga wurin kana hango duk abin da ake a conpound din, kamar yadda kaima ana shigowa zaa hangoka.
Sai da ta tabbatar ya zauna computable,. " bari in shiga gida 2 min, kar suga na dade."
Murmushi yayi " no problems, ko kwana kika ce inyi, ai an gama balle 2min."
Takunta mai matukar burgewa da daukan ido, duk da dogon hijab din amma yakan iya ganin yadda take yi, cikin natsuwa, da yanga, wanda yasan is naturally. Har ta bacewa kallonsa murmushi yayi tare da sauke ajiyar zuciya. Allah ya sani yana matukar son yarinyar. Akwai hankali da natsuwa. Ba irin rawar kan nan na matan zamani. Shi da badan ma yaji ta taba aure ba, a bakin da baya karya. Da ba zai taba yaddaba. Tanada karamin jiki, kuma jikinta nada kyau sosai. Don shi a yadda yake bata bazata wuce 20 zuwa 21 years ba.
Wayarsa dake faman ringing ya duba tare da answering.
A cikin natsuwa take takowa, dauke da wani kyakyakyawan trey golden. Ruwan faro, sai 7live da cups, sai wani bowl mai dauke da danbun nama. Anyi celling din shi da leader
Da sauri ya tashi ya amshi trey din. Kujerar kusa dashi ta jawo zuwa gabansa, ya daura trey din a kai. " thanks. " ya fada yana Mata murmushi mai kayatarwa.
Shiru sukayi na dan wani lokaci. Shi ya katse shirun " naje kankiya jiya baki koma ba.?"
Cike da natsuwa, " I won't back to kankiya. "
Murmushi yayi " I known, Alhaji kawu ya min bayani. "
Ido ta zaro tana kallonsa cike da mamaki. " meya fada maka?"
Juice din ya tsiyaya, sai da ya yi sipping tukunna, idonsa a kanta, fuskarsa cike da annuri. " Notting much, ya tambayeni yadda mukayi dake, I tell him kinyi accepting dina as a friend. So murmushi yayi irin nasu na manya." Ya fada yana daga mata gira daya. " then he told me in turo magabatana nan da 2 weeks."
" what." Ta fada da dan karfi, idonta a waje. That means kenan duk abin da yake faruwa da saninsu.
Dariya ya yi " am so happy, jiya ko bacci ban iya ba, saboda dadi. Kamar yasan na matsu Kwarai in ga na ajiye iyali. Wannan shine dalilin zuwana don in ji naki raayin. " do u really accept me as your husband? "
Kanta ta sunkuyar tana wasa da tsinken dake hannunta. Zuciyarta na faman bugun uku uku. wannan shi ake kira abun yazo, in ji mai tsoron wanka.
" please ina son ji daga bakinki,. Kin yadda kin amince, zaki zama uwar yayan suraj kangiwa?"
Sai da taja numfashi tukunna, kanta a kasa " if that is what they wanted, it's OK by me."
" ba abunda suke soba, ke meye naki raayin? Zanfi farin ciki, ace ke kikayi accepting dina da kanki, ba wai under pressure from you're parent ba."
" I accept. " ta fada tana kara sunkuyar da kanta.
Farin ciki wurin suraj baa magana. " Alhamdulillah, in sha Allah bazaki taba yin dana Sani,da zamowa ta miji, kuma uban yayanki ba. Zan baki farin ciki, iyakar iyawata, In sha Allah. Na gode sosai da kika bani dama in shigo rayuwarki."
Hira sukeyi cikin natsuwa, duk da yawancin maganar shi yake bata labarin daya dangan ce shi, da family dinshi. Yaji dadin yadda ta fara sakin jikinta dashi, duk da ya lura tana da kunya sosai,. Yau ma kamar yafi na ko yaushe.
Shigowar motar Alhaji Munir, yasa gaba daya hamkalinsu ya koma kansa. Mikewa yayi. " bari in je in kwashi gaisuwa." Ya fada yana nufar motar Alhaji Munir. Da driver ke kokarin bude masa Kofa. Tun shigowarsu ya lura dasu.
Sallama ya masa, tare da kokarin durkusawa don gaisheshi. Da sauri Alhaji Munir ya tareshi, tare da mika masa hannu. Cikin jin kunya, da nauyinsa ya mika masa nashi, sukayi MusaBaha.
Suraj yaji dadin yadda Alhaji Munir ya tarbeshi,cikin mutunci. Duk da haduwarsu ke nan ta farko ba,. Already sun San juna, sun sha haduwa a maban- banta wurare.
Ajiyar zuciya hubby ta sauke, lokacin da suraj ya isa wurin daddynta. Sai yau ta kare masa kallo. Tabbas bashi da makusa, ya hadu. Sai dai tasan bai kama kafar Yusuf dinta ba.
" madam bari in kama hanyar kauyen mu." Suraj ya fada yana murmushi.
Tashi tayi ta rakoshi har jikin mota. Tare da masa fatan sauka lafiya. Har ta juya zata tafi. " ji mana." Ya fada yana bude kofar motar. Dawowa tayi ta tsaya.
Wata hadaddiyar leader ya mika mata " please ba don ni ba, don Allah ki yi anfani da ita, bana jin dadin rashin waya a hannunki, ko ba komai zanji muryarki, wani abun ma zakifi sake jiki, ki min magana. Next week Saturday in sha Allah parents dina zasu zo."
Gadiya ta mishi, da alkawarin zatayi anfani da ita kamar yadda ya bukata. cike da farin ciki suraj ya bar gidansu hubby.
Sai bayan da ta idar da sallar magrib ta dauki leader din ta nufi dakin mommy Hauwa. A zaune ta sameta tana jan tasbaha. Sai da ta jira ta gama sannan ta mika mata leader din. " meye wannan." Mommy Hauwa ta tambaya
" nima ban Sani ba, shi ya bani." Ta fada kanta a sunkuye.
Kada kai mommy Hauwa tayi tare da bude leader. Kwalin waya ne ta fara cin karo dashi. A hankali ta fito da kwalin ta bude. Ido mummy Hauwa ta zaro, baki a sake tana juya wayar, tare da kara karanta sunan waya.

Goldvish (18 carat white gold & 120carat of vvs---1 graded diamond)

Mommy Hauwa ta kalli hubby da itama idonta na kan wayar. Tana ganin kyawawan waya bata taba ganin wayar data burgeta ba, kamar wannan. Gata yar dai dai, so cute.
" Ummi wannan ai customize phone ne?" Mummy Hauwa ta fada tana juya phone din.
Junaid ne ya shigo da sallama. " evening Anty. " ya fada yana zama kusa da hubby. " evening brother, daga ina?"
" hayders house. "
" aikin ke nan." Hubby ta fada
"Mommy Hajiya na gaisheki, wai ya taji shiru."
" or I totally forget. I call her."
Mommy Hauwa ta kalli hubby, tare da mika mata phone din. " kin tabbatar dai kina son shi ko?" Kai hubby ta sunkuyar cike da jin nauyin mommy Hauwa.
" naso Kwarai Ku dai daita da hassan, amma tunda kin ga bai miki ba, shi kenan, Allah ya musu zabi na alkhairi."
Junaid ya amsa da " amin."
Shima ya yaba phone din. Leader ya bude wani kwalayen ya fito dashi. Daya smart watch, da yan perfumes ne different colours. Kananan kwalabe masu kyau.
"Woow!!! This is our collection." Junaid ya fada yana murmushi. Mommy da idonta ke kan set din perfume din ta ce " kamar Yaya?"
Sunan ya nuna mata. ( 7 friends for ever collection) sai ainihin sunan turaren caron poivre.

" kai junaid ban son karya, yaushe kuka fara kasuwancin da har zaku fara collection na kanku.?" Mommy Hauwa ta fada tana harararsa.
Dariya yayi " da gaske mommy wannan turaren mu mukayi, design dinsu, sannan mu muka zabi ingredients din da muke son a hada mana dashi. Mu muka yi exporting dinsu to Nigeria. Its our oder"
" yaran nan kun fara bani tsoro fah!!" Mommy Hauwa ta fada tana tsare junaid da ido.
Dariya yayi " kar kiji komai mommy. Neman halas dinmu fa muke yi. Kin ga waannan ko wanne da kamshinsa da ban. Its made from expensive ingredients, zakiji dadin su sosai."
Harararsa hubby ta yi " in mommy ta yadda ka dauka nima yadda zanyi. Please stop lieying. Luke at is very care full its expensive perfumes. How do you people have that kind of money to do all this in short time. ?"
Kada kai mommy Hauwa tayi alamar gamsuwa da maganar hubby.
Murmushi junaid yayi. " it's OK. Amma kar Ku manta muna da irin su don Harris da business tycoon Alhaji omer Yusuf zubair, har kwa tambayemu in da muka samo manyan kudi?"
" haka nefa!!!." Mummy Hauwa ta fada tana kallonsa.
" dama na shigo in gaya muku amaryata ta iso." Ya fada yana murmushi
" Amarya kuma?" Hubby ta tambaya
"Mai kafa hudu ba." Ya fada yana dariya ganin kallon da mommy Hauwa ta masa.
Murmushi suka yi tare da masa Allah ya sanya alkhairi. Tare suka fito compound din. A jikin motar suka samu jafar da jabir, suma suna kallon new car din kanin nasu.
Cike da mamaki mommy Hauwa ta ke bin motar dake gabanta da kallo

2008 BMW 7 Series.
" masha Allah brother, mota tayi kyau, Allah ya sa alkhairi, ya sa daka da alkhairin dake tattate da ita, ya kare ka daga sharrin dake tattare da ita." Su jafar suka fada, suna rungume dan uwan nasu, cikin farin ciki.
" ameen, na gode." Ya fada yana murmushin jin dadi.
Su mommy Hauwa ma sun tayashi murna da addua. Duk da zuciyarta na cike da tambayoyi.
" yarona fah?!" Mommy Hauwa ta tambaya
" power bike, da safe ya ce min zaizo ya nuna miki, da tare zamu taho, Alhaji babba ya kirashi."
Tabe baki hubby ta yi
" Allah ya kyauta, banda shirmen hayder me zaiyi da power bike." Mommy Hauwa ta fada
" ra ayi." Jafar ya fada yana dariya
"Sai kin ga power bike din yayi kyau sosai." In ji Junaid
" mako dai!!! Me mutun zaiyi da wani mashin in ba mako ba." Hubby ta fada tana hararar junaid
Ido ya zaro " kin San kudin bike din nan, kike cewa mako? Yafi kudin motar nan da kike gani nesa ba kusa ba."
Dariya hubby tayi " Haba yaro karka raina min hankali mana."
Kallon jabir junaid yayi " gaya mata brother. "
" is true bike akwai masu tsada sosai, duk da bansan irin wanda ya siya ba, amma zai iya kasan cewa yafi motar tsada." Jafar ya fada

"Aprilla ( Italian motorcycle brand )"
daga jafar har jabir kallon junaid suka yi cike da mamaki. " wow!!! Har kasa na kosa inga bike dinnan, kwanan nan friends dina na musu tsakanin aprillia da kasawaki."
Murmushi junaid yayi " zakuwa ka ganshi yayi kyau sosai,"
Mommy Hauwa dake saurarensu murmushi tayi " ina ruwan yarona, komai nashi daban."
Jabir ne ya amsa da " I love the boy, he have a taste, komai nashi unique. Kam"
" gobe zaa bani Amarya in dana." Hubby ta fada
Murmushi junaid yayi, tare da amsar key din a hannun jafar ya mika mata. " it all yours sis."
" thanks u are the best. " ido su jafar suka zaro cikin wasa " what about us." Dariya su hubby suka yi
" jealousy. " junaid ya fada yana dariya
" I love u all. " hubby ta fada tana shigewa ciki da gudu, kamar wata karamar yarinya.
Da kallo suka bita. Mommy Hauwa ta kada kai " Allah ka shirya, naga ranar da Ummi zata San ta girma."
Murmushi dukan su suka yi cike da son yayar tasu..........
[04/03, 18:15] Zulaihatu Aliyu: DA KAMAR WUYA