← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 28 OF 28

                            Part 28

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 33 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau
   
Not Edited.......

Gaba daya haka suka gama break fast, ba armashi tamkar kurame, dama ita ce mai yawan kawo hira to itanma brain dinta ya dau caji. Shikuma nazarinta ya tsaya yi, jikinsa yayi sanyi, anma baya jin zata samu abinda take so.

Sai da ya ajiyeta sannan ya nufi nashi
Wurin daukar karatun.

Zainab da Hafsat kawayene ga hubby. Tare suke karatu, duk kansu yan nigeria ne, zainab yar jahar kebbi, sai hafsat gombe, ta samu har sun rigata isowa. " ummu ama, yau kam kin buga latti." Hafsat ta fada bayan sun gama gaisawa.

" yau da gobe kenan, ballantana kar Ku manta sai na sauke Amatullah a day care, kafin na karaso, amma kullun ni nake rigaku isowa, sai yau aka samu akasi."

" shi yasa nake sara miki, mu kuwa ba cas- ba -as, shirya kanmu kawai sai kiga lokaci ya tafi." Zainab ta fada dai dai lokacin da lecturer dinsu ya shigo.

Gaba daya yau hayder kasa gane kansa yayi, karatun ma baya shiga yadda ya kamata, Hankalinsa na kan hubby. Yau ya kara tabbatar da son hubby da ya gama mamaye ransa. Duk da bai furtawa kowa ba, amma alamu sun gama nuna kansu. Tunda rashin walwalarta kawai na rana daya da ya gani ya hanashi sukuni. Tunanin abinda zai mata, ya sata farin ciki ta manta da damuwarta ya fara, duk abinda yazo ransa sai yaga kamar bai yi ba. He is not a romantic person, yan matan suke binsa, balle yasan yadda ake lallashi, ya kira hafiz omer ya tambaya, yana jin tsoron iskancin hafiz din. bai taba jin son wata kwata kwacin yadda yake ji akan hubby ba a yanzu. Yana son Nasrin, amma jigon soyayyar tausayi da kyawawan halayyarta. Sabanin hubby da sonta ya fara shigansa a hankali, har yayi girman da yanzu yake ganin bazai iya ci gaba da adanashi, a cikin ziyararsa ba. Hubby na sonsa he is 100% sure of that, kamar yadda bai furta ba itama ta adanashi a nata zuciyar. Sai dai action din kowanne na fallasa sirrin zuciyarsa ga dan 'uwansa.

Kyawawan halayyarta, rikon addini, tsafta, son jamaa, biyayya, da kawici. Kadan daga cikin halayyarta dake burgeshi.

Ta bangaren hubby kam, tunanin yadda zata samu damar zuwa hospital ba tare da sanin hayder ba, shiya tsaya mata a rai.

Sun fito daga day care kenan, ita da Zainab, don shayar da Amatullah kamar yadda ta saba in ta samu free time.

" please umm ama, yunwa nakeji, mu dan biya cafeteria ko snacks in siya. " Zainab ta fada tana yamutsa fuska kadan.

Dariya hubby tayi mata, suka nufi hanyar cafeteria.

Pizza suka yi order sai coca- cola. Suna ci suna dan taba hira kan abinda ya shafi karatunsu, da exams din dake gabatowa.

Wasu yanmatane su uku suka shigo. Sun sha kananun kaya, kamar yayan turawa, saboda tsabar belching ga uban Brazilian heir da suka sha kai ka rantse nasu ne, Ba laifi kowaccensu nada kyanta dai -dai kwargwado. Sai dai kallo daya zaka masu kasan kudi da duniyanci ya samu wuri.

" mutuniyarki!" Zainab ta fada tana murmushi

Tabe baki hubby tayi, tare da jan dan karamin tsaki. Kallo daya ta musu ta dauke kanta, tare da fatan musu shiriya, da sauran daukakin musulmi da sukabi hanyar da suka dauka.

A table din kusa dasu hubby suka zauna. Bayan sunyi oder din abinda suke bukata. Dayar ta kalli ta kusa da ita. " ina mamakin yadda zakiga mace tana cika, tana wani fadi, ita a dole kasaitacciya, amma at long last sai abun ya baki mamaki in kinji wani abu daya dangan ceta. A lokacin sai ta baki tausayi, kiga Ashe a isar ma bata isaba."

Tabe baki ta kusa da ita tayi, tana wani yamutsa fuska, cikin yauki " wannan zancen naki haka yake Merry. "

Wadda aka kira da Merry, wanda asalin sunan maryam ne. Tayi murmushi tana kallon su hubby cikin kallon da suka kasa gane ko na menene.

" duk wannan kafafar Ashe matar cushe ce, yaro nada wadda yake so, iyayensu suka aura masa ita. Kin san me? She is divorcee, his late brother wife. "

" don Allah Merry? " dayar ta fada cikin mamaki tana kallon Merry

Gira Merry ta daga mata,tare da yin fari da idanuwanta. " kin san jiya da idona na ganshi da yarinyar da yakeso, kamar zasu cinye juna don so da kauna. U know the sad of the story? "

" what!! " dayar ta fada cikin gaguwa da son jin karashen zancen.

" harda cute and beautiful angel dinshi. Kai jiya naga love, abun yamin dadi, tunda mu an toshe mana damarmu, wata ta samu ba kuma yadda mutun ya iya, matar cushe da bata da daraja, ina tausaya mata ranar da sweet heart dinsa zata shiga gidan nan. Don da ganinta gara namu duniyancin akan nata."

" meye matsalanki, can su karata." Dayar ta fada in I don't care manner

" ni ko nakeda matsala! Kinsan irin son da nake masa? Love at first site. Amma fa har yanzu ban hakura ba, sai  naga abinda ya turewa buxu nadi."

" sai kiyi tayi ai, kamar shine autan maza? Let them be." Inji dayar

" ko don abinda akamin, bazan taba bariba, ko ban shigaba, sai na tabbatar da wata ta shiga. I want to see her supper." Ta fada cike da mugunta da kyashi.

Zainab ta kalli hubby da ranta ke a bace, amma tayi iyakar kokarinta wurin saita kanta, she can give them the room to insult her. Da ido Zainab ke mata alamar tayi cool down, and take heart.

Har suka gama su Merry na kan zancensu.

Dai dai wurin Merry hubby ta isa fuskarta dauke da killer smile " wow!! Kinfa burge, meye ban bancin naki da matar cushe? Gara ma ita iyaye suka cusata, kefa? I promise u no matter how u try u never enter that house, it belongs to hubby and her children. About that lady da kika ce kin gansu tare. I know every think about her, I don't have any problem with it. So ki kwantar da hankalinki. Bazaki  taba samun hayder ba, in sha Allah, har gaban abadan. Yaso kowa, ya auri kowa amma banda ke, bai daman ba."

Cike da mamaki Merry ke kallon hubby, don a tunaninta hubby bata san da zaman Nasrin ba.

"Husband snatcher!" Zainab ta fada tana Jan hannun hubby suka bar wurin.

Da ido su Merry suka bisu, har suka fice.

" wannan yarinyar yar rainin hankali ce, ki daina biye mata." Zainab ta fada tana Jan tsaki

" ba yadda zaayi ka bugi mutun ka hanashi kuka, sai dai ni bana barin ta kwana, shan yanzu maganin yanzu."

Dafata Zainab tayi " har yanzu baki gayamin abinda ya hadaki da ita ba."

Tabe fuska hubby tayi, ta fara ba Zainab labari kamar haka " farkon zuwana school din nan da ita na fara karo. Ganinta bahaushiya yar Nigeria yasa na dan saki jiki da ita, don na ganta cikin shiga ta kamala, a lokacin. Ita ta nunamin wurare da dama a cikin school din nan. Kasan cewar ta rigani zuwa, a wurinta na samu bayanan topic din da akayi bananan. In zaki tuna ko lokacin da kuka zo tare muke da ita, lokacin bata hadu dasu sintia ba.

Ranar da suka fara haduwa da hayder a ranar na fara ganin changes a tare da ita, na yawan tambayana shi, ko in ta rakani wurin shayar da Amatullah ta dinga yabonta, tana abu kazanta ma irin na babanta, kaza na babanta and so on. Abin na damuna amma ban taba nuna mata ba. Sai ya zama kullun ita ke jirana a parking space, bayan dan uban kwalliya da zataci, haka zata gaisheda hayder tana wani karairaya, da kakkashe ido.

Satina biyu da fara zuwa, hayder ya gargadeni bani ba wannan yarinyar, baya son alakata da ita. Hakan yamun dadi, amma ta ya zan zame kaina bayan na bari ta shiga jikina da yawa?

Abu na farko dana lura dashi, shine yar burun- burun taso shirya min. Idonta a bude suke tar, mission dinta ta samu kyawawa, wanda zasu kawo mata haske cikin sha'aninta. At first ta dauka banida aure sai daga baya, duk da haka tana ganin zata iya brain worshing dina, sai taga sabanin haka, don sau da yawa nakan zauna namata waazi kan abunda nagani tanayi ba dai -dai ba. Musamman ta fannin addini, dana lura tana amsa sunan musulman ne kawai. Ganin hayder ya kara tabbatar mata da zanyi wuyar damuwa, yanda take tunani, don mai irin mijina baya bukatar kowa a rayuwarsa. Sauda yawa zakiji tana kokarin bugar ruwan cikina taji how he is, in our multimonial bed?. " auzubillah!! This is haram, maryam. Its between me and him, no body eals. Zakiga ta cika kamar ta fashe.

So tunda hayder ya gargadeni a kanta, na fara ja baya da ita. Abun bai mata dadi ba, don na lura gaba daya yanzu attension dinta ya koma kan mijina. Wannan ya kara sa na tsaneta, naji ta fita a raina kwata- kwata, ga halinta na rashin kamun kai, dana fara ganowa a lokacin. Rana daya na dauke mata wuta. Kusan sati tana bina ina shareta, cikin ikon Allah sai gashi mun hadu daku a cafeteria, Allah ya hada jininmu, ganina tare daku yasa ta kara daukan zafi. Washe gari na ganta tare da su sintia, tun daga lokacin muka fara yar tsama da ita. Hayder yasha cemin wai ta bishi har school, ranar dai na sameta har hostel na mata wankin babban bargo, to tun daga nan in ba a lectures ba bama haduwa, sai yau."

" anyi yar iskar yarinya! " Zainab ta fada tana jin jina kai.

" Allah ya shiryeta yasa ta gane, kina yar musulmai ki maida kanki tamkar taxi no gari, da sunan wayewa"

" ta amma wacece yarinyar da tace taga mijinki da ita? Har kike ikirarin kin santa." Zainab ta fada cike da son jin karin bayani.

" itace yarinyar daya kamata ya aura, kafin kaddarar  aurenmu aurenmu. Tana karatu a nan, suna tare  kusan 4years kenan." Hubby ta fada

" very sorry! Is not easy kasan mijinka na soyayya da wata, koda ko baka son shi. Ta dauka baki sani bane ta kunna miki wuta a gida. Duk da bansan dangan takar aurenku da mijinki ba, zan baki shawara! Ki zage damtse ki rike gidanki da kyau. Don irinsu maryam ba karaman shaidanu bane. Ki dage da addua."

" insha Allah, Thanks. "

" ina kuka shigane tun dazu na dawo ina ta faman nemanku? Ga wayar ma bata shiga" Hafsat ta fada cikin jin haushi

Murmushi sukayi " very sorry, muna daga day care muka wuce cafeteria," Zainab ta fada tana mika mata pizza da suka mata take away.

" kun kyauta, kamar kunsan ina jin yunwa sosai."

" ya jikin Islam din?" Hubby ta tambaya

" taji sauki, sunma dawo da ita clinic din cikin school din nan. "

" ya ka mata gobe muje mu dubata." Inji Zainab

" haka ne kam! Allah ya kaimu goben." Inji hubby

" amin." Suka amsa baki daya.

               **************"*"****

Ranar hayder ya shirya musu romantic dinner, a wani 5star hotel dake kusa dasu. Don faranta ran hubby.

Mariya da Amatullah suka saukesu a gidan friend dinsa.

Hakan ba karamin dadi yayiwa hubby ba, don tun a Egypt rabon da su share din moment irin haka.

Sai  past 11 suka koma gida, bayan sun dauki su Amatullah.

Haka suka raya daren cikin so da kauna, duk da baki ya hanasu furtawa juna, sai zuciya da gabbai dake nasu aikin.

Suna rungume da juna, cike da farin ciki, bacci yayi gaba dasu.

              ******************
Zuwan hubby da su Zainab dubo Islam school clinic, yaba hubby damar nazarin clinic din. Ya hadu, ga kayan aiki irin na zamani, mamaki ta fara da yasa tun farko basu kawo Islam nan ba.

Bayan 2days, daga school sun samu interval, ta wuce clinic din. Cikin 1hour 3omin result dinta a hannu, ta koma lectures ba tare data bude ba, don bata shirya gani yanzu ba, tafi son sai ta natsu tukun.

Maryam Kabir kamba, yarinya ce yar shekara 21 a duniya. Haifaffiyar garin Abuja, mahaifinta Alhaji Kabir kamba dan majalisan dattawa ne, wanda ya dade ana damawa dashi a gomnatoci da dama dasuka shude. Maryam ita ce auta a yayansa. Sun shagwabata, shagwaba na karshe. Hajiya tumba mahaifiyar maryam mace ce mai son abun duniya, wanda neman kudinta yafi mata tsayawa kulada rayuwar yayanta. Kusan duka yaran tarbiyyan yan aiki ne. Maryam tun daga secondary sch idonta ya bude da bin maza, ga son kudi. Duk da kudin da ubanta ke sake mata.

Shekararta 4 a kwakwalada amma ta kasa achieve din komai, makarantar ma sai ayi fiye da 2weeks bata leka ba, ganin hakan yasa mahaifinta yanke shawarar ta fita waje tayi karatun, a tunaninsa ko don tun farko ya hana ta yin karatu a wajene yasa bata maida hankali.

Taji dadin hakan, don zata samu damar barje tsiyarta ba tare da an sa mata ido ba. Tare suka taho da Best friend dinta Regina. Ranar data fara haduwa da hubby taji hubby ta kwanta mata, tana son kulla alaka da ita, duk da ta lura hubby ba irin su bace, amma with time, sunyi irin hakan yafi a kirga, so wannan ma bazaiyi wuya ba. So koda suka hadu da Regina ta mata bayani, tare da setting plan dinsu a kan hubby.

Zamanta da hubby na dan lokaci, ta gano tana da aure har da beby, amma hakan bai sanyaya gwuiwarta ba. Abu daya daya fara cimata tuwo a kwarya kan hubby shine, ta lura addini ya shigi yarinyar sosai, da zatayi wuyar samuwa.

Yawan waazi da Jan hankalin da hubby ke mata, kusan ko yaushe ya kara sa ta fara kwakekwanto kan hubby. Ganin hayder ya rikita duniyar maryam don duk dunya ji tayi ba wanda ya kwanta mata, ya dace da rayuwarta sama dashi, ta gefe daya kuma ga hubby. Zata jefi tsuntsu biyu da dutse daya.

Babban tashin hankalinta da hubby ta fita hanyarta lokaci daya. Hakan wani kalubale ne ga nasararta kan kudirinta a kansu.

Sannan ta gefen hayder Sam ba sassauci. Ita a yanda ma ta samu labarinsa abun tsoro ya fara bata, sai dai tadau kudiri da babu komawa baya. Ganinsa da Nasrin yafi komai daga mata hankali, nan da nan ta koma neman karin bayani, alhamdulillah ta samu dai -dai abinda take bukata.

Kalaman hubby sun sata, canza akalan plan dinta.  Dare nayi ta kira kawarta dake gida Nigeria ta labarta mata komai da taimakon da take bukata daga gareta.

Dariya Nancy tayi " ki kwantar da hankalinki an gama, ki turomin da cikakken sunansa, sunan babansa da mahaifiyarsa, angama.".........
Saida tayi sallar isha'i, tayi wanka ta shirya cikin wasu hadaddun English wares, riga da wando masu matukar kyau. Tama Amatullah wanka ta shiryata cikin kayan baccinta. Roll- on red.

Reports dinta ta dauko ta warware, ta fara karantawa, tana jijjigata Amatullah dake goye a bayanta. positive, 4month pregnant. Ido tadan zaro cike da tsoro da mamaki, 4month ta maimaita. " no it can be." Ta fada tana ninke report din.

Kenan tana komawa gidanta ta samu cikin, in tayi lissafi dai- dai, yanzu watan Amatullah 5 tana cikin na 6. " ya Allah!!! " ta fada tana sauke ajiyar zuciya, tare da tausayin kanta dana Amatullah. Tana maganar planning Ashe aikin gama ya dade da gamuwa. Duka 1 month kenan data fara jin changes a tare da ita, da yasa ta fara zargin kanta.

Dakin Mariya ta nufa, don dubata, tun dawowarta school ta dawo da ciwon kai. Ta samu tasha magani har tayi bacci. Saita mata Ac din dakin tayi, ta kashe mata wutar dakin ta fita.

A falo suka ci karo da hayder dake kokarin shigowa. Da sauri ta nufi she hannayensa ya bude ta shige, ya rungumesu daga ita har Amatullah dake bayanta. Kissing bakin juna duka fara kamar life defend on it. Kafin suka janye daga juna. Ta karbi jakar laptop dinsa. Kiss ya mannama Amatullah a goshinta, ai kuwa kamar jira take ta bude ido, baki ta bangale masa, tare da juye -juye, tana don taje wurinsa, hubby ta shigar mata da hannun cikin goyo.

Showel din ta balle ya daga ta yana cillata suna dariya. " kaji dadi da ka tasar min ita!! Na samu na lallabata dakyar." Hubby ta fada cikin shagwaba, tana nufar dakinsa.

Murmushi yayi, yabi bayanta dauke da princess dinsa.

Ajiye bag din, ta wuce toilet ta hada masa ruwan wanka.

A kadonsa ta samesu sai wasa yake mata tana bangala dariya harda kyakyatawa, Tana mamakin hayder, bata taba tunanin yana son yara haka ba, sai yanzu. " ruwan wanka is ready."

*******************

Shiya kwantar da Amatullah tare da mata addua, kamar yadda suka saba ( A'uzu bi khalimatul lahi ta'matih min kulli shai'danin wa hammat wa min kulli ai'nuin lammat 3)

Gira ya dagawa hubby dake kwance tana kallonsu, tare da kashe mata ido. Murmushi tayi tare da ware masa hannayenta.

Hancinta ya hade da nasa, Ido suka lumshe a tare,Wani iri suke ji a jikinsu wanda bazai misaltu ba,kasa matsawa kowannensu yayi, a nutse ya daura lips dinsa saman nata tare da dorata a samansa shi yana kasa, bakinsu ya hade wuri daya ya kamo harshenta da nasa Yana tsotsa kamar zai cinye Mata Baki, hannunta ta kai kan sagensa da tafukan hannunta masu matukar taushi tana shafawa a hankali zuwa gemunsa tana Kara kissing dinsa sosai, Kirjinsu ya hade waje daya tare da gangarowa zuwa wuyanta Yana lasarta, a hankali ya zuge zip din rigarta, Jin hannayensa a saman a saman kirjinta yasa ta rudewa, tare da kaimasa nata sakonnin.
Harshensa taji saman kirjinta wani shidewa ta fara yi, tare da zagewa wurin gigitashi da natsa salon.

Bakajin komai sai nishinsu, da kurnani, sai kalamai na maabota shauki.

Tana kwance a saman kirjinsa, bayan komai ya lafa, suna maida numfashi, duk kansu fuskarsu cike da farin ciki da annuri. Kiss yama goshinta, tare da kwantar mata da gashin kanta daya gama hargitsewa. " meye sirrin ne?" Ya fada in husky voice. Dago kai tayi tana kallonsa cikin rashin fahimta. Gira ya daga mata murmushi tayi tare da kara shigewa jikinsa, " kai ne sirrin." Ta fada a shagwabe

" thanks. " ya fada yana smirk shafa lallausan fatar kirjinsa zuwa 6 pack dinsa take cikin salonta.

" kullun cikin godiya ga Allah nake daya kaddari aure na dake, yanzu nake ganin anfanin biyayya iyaye, dana bijere musu kamar yadda na bijircewa wasiyyar dan uwana, da na tabka babban kuskure a rayuwata." Ya fada cikin sanyin jiki, da raunin murya.

Da sauri ta dago, tana kallonsa. Jin ya ambaci wasiyyar dan'uwansa, me hakan ke nufi?. Tashi yayi ya zauna, tare da jingina da jikin bed din. Tana kwance a kan cinyarsa fuskokinsu na fuskantar juna. Kallo sukewa juna mai cike da ma'anoni masu yawa, Masu wuyar fassaruwa.

" me kake nufi da wasiyyar dan'uwanka?" Ta fada cike da raunin zuciya

Ajiyar zuciya yaja, tare da kamo hannayenta duka biyu cikin nashi, yana dan murzawa a hankali. " in zaki iya tunawa, 3 weeks before rasuwan ahee! Ya kawo min ziyara." Kai ta kada, don ta tuno, da tare ma zasu zo, haihuwar Anty samira a lokacin yasa bata bishi ba.

Numfashi yaja, tare da fesar dashi tunowa da moment din na matukar dawo masa da mutuwar tamkar lokacin abun ya faru.

" A ranar da yazo mun tattauna abubuwa da dama, sannan ya bammin wasiyyu guda 3, biyu kam na amsa masa, kuma Alhamdulillah ina iyaka kokarin ganin na sauke wannan alkawarin dana dauka. Dayan ne dai duk yadda yaso, ban amsa masa ba, don nasan da kamar wuya, wurin yiwuwarsa."

Jin yayi shiru, tare da lumshe idonsa, ita kuma ta kagu taji duk da sanyin da jikinta yayi. " meye abu daya daka ki amsa masa a lokacin?" Ta fada idonta a kansa

" aurenki." Ya fada tare da bude idonsa ya sauke a kanta. Tashi tayi ta zauna, taja bargon ta dan rufe jikinta dashi.

Baki na rawa tana nunashi ta nuna kanta " auuure niii daaa kai?"

Smirk ya mata " of course, ahee!!! Ya rokeni da na aureki, don ya tabbatar zan kula dake yadda ya kamata. Baya son bayan mutuwarsa rayuwarki ta tagayyara, yana fatan ki kasance cikin farin ciki da walwala, Amma gaskiya a lokacin ban amsa masa ba. Duk da abun na cikin raina yana damuna, amma a lokacin nasan bazan iya cika masa wannan kidirin nasa ba."

Cike da mamaki hubby ke kallonsa. Kara matse hannunsa yayi cikin nata " yanzu kin kara yadda aure na dake mukaddarine? don ban manta kalmarsa ta karshe a kan hakan, dana rakoshi airport zai wuce Oregon. Kafadata ya dafa yana murmushi " na rokeka alfarma kaki min, ka sani Allah na cika burin bayinsa ta inda baa zato, a lokacin da yaso. Bazan matsa maka kan abinda baka ra'ayi ba, don muma ba wanda ya matsa mana. Duk abun da kake gani da wuya, a wurin Allah mai sauki ne. Zuwa gaba zaka gane soyayya da gatan da nama. Karike a ranka Yusuf na sonka so mai girma." Ina hawaye yana hawaye haka muka rabu, ina tsaye ina kallonsa, har ya bacewa ganina."

Hawayene kebin kuncin hubby, ganin hakan yasa hayder shiga damuwa da tashin hankali. Lallashinta ya fara in romantic way. Duk da shi kansa daurewa yake, amma kewar dan' uwan nasa fil ta dawo masa, shi yasa bai taba maganar da kowa ba.

" me yasa baka taba gayamin hakan ba?" Ta fada cikin dasashshiyar murya " ko don babu digon kaunata a zuciyarka?" Ta sake furtawa tana kafeshi da idonta da suka kada sukayi ja. Lashe labbansa yayi, " ban taba maganar da kowa ba, tsakani na dashi ne, sai mahaliccinmu, sai ke yau dana furta miki."

" ajiyar zuciya taja, tare da mikewa ta nufi toilet don ta tsarkake kanta. Meye anfanin gaya matan da yayi? Tunda bai gaya mata a lokacin da ya dace ya gaya mata ba! Tabbas da tasan da wannan maganar ko ja bazatayi ba zata aureshi, kodon son cika muradin masoyinta. Amma shi da yake ikrarin yana sonshi, ya gagara cika masa. Wacce irin kiyayya yake matane har haka? Me ta taba masa mai zafi har haka? Tunanin da suka cika zuciyar hubby kenan.

Jiki a sanyaye yabi bayanta. Rungumeta yayi a jikinsa ganin kamar fushi take dashi. " I'm so sorry!! Abinda ya wuce ya wuce, nasan kuma bai wuce kiruciya da rashin fahimtar juna ba. Ina so ki sani a yanzu soyayyarki ta gama mamaye zuciyar hayder, kece duniyarsa wanda Allah ya sanya farin cikinsa a cikinta, ke kika zamo min tamkar Zara cikin dubban mata, U are my every thing. Don Allah kar kiyi fushi dani." Ya fada cikin husky voice dinsa
Tare da shagwabe fuska

Dagowa tayi tana kallonsa, zuciyarta na bugawa, a hankali. " I love u so much. " ya fada idonsa cikin nata.

Kallonsa take cike da so da kauna, wani dadi na ratsa zuciyarta. " I love u too." Ta fada cikin muryarta mai sanyi da dadin sauraro. Bakinsa ya kai kan nata, ya lalubo lallausan lips dinta suka fara aikawa jina hot romantic kissing, kamar zasu cinye juna.

******************
Bedroom din hubby ya shiga, dauke da Amatullah dake makale a kafadarsa. " habitty what take u so long eh!!!!" Ya fada in husky voice dinsa yana shigowa. Daskarewa yayi daga bakin kofa yana kallonta baki sake.

Dariya tayi, tare da hure masa ido, bayan tayi dage sosai. Kaftawa yayi, ya saki murmushi " is that u." Ya fada yana kai hancinsa kan gashinta da yasha gyara sai kanshi da daukar ido yake.

Juyawa ta fara a gabansa in romantic way. Runtse ido yayi jikinsa na tsuma yana kara godewa Allah bisa duk kan ni'imar da yayi masa.

" don't kill me please. " ya fada muryarsa na rawa. Dariya hubby tayi tana kara kashe masa ido da salonta na Jan hankali. Tuni goga hayder ya dane network, kwalliyar da hubby tayi na kananun kaya (English wares) robber skirt and top da sukai asalin kamata ko Brazer bata bukata ba, gasu nan a cike kamar sa tsone idon oga hayder. komai masha Allah, ga gyaran gashi, yau na musamman tayi da makeup.

" ba dama mutun yayi kwalliyarsa sai an bata masa." Ta fada tana tura baki, cike da shagwaba

Smirk ya mata " kema kinsan abinda kikayi ai? abinda kika nema aka baki, right? " ya fada yana kashe mata ido

Duka ta kaimasa a saman faffadan kirjinsa,. Ya rike hannun, tare da mirginawa ta koma kasansa. " u say u want to talk to me? " ya fada yana shinshina wuyanta.

Lumshe ido tayi, tana maida numfashi. " let me show u." Ta fada cikin rashin kwarin jiki.

Dagata yayi Ta mike, da ido ya bita tana takunta mai tafiya dashi.

Amsar takardar yayi ya bude. Ido waje yake kallonta, murmushi tayi tare da shafa cikinta, da yadan tasa kadan, don in baka lurabama bazaka ganeba.

Hamdala yayi tare da daga hannu yana godewa Allah. Ya tashi sai ji tayi ya sureta ya fara zagaya dakin da ita, cike da farin ciki.

Dariya take, tana ya sauketa. Kukan Amatullah da suka farkar da ita da hayaniyarsu ya dawo dasu hankalinsu. Sauketa yayi, ya dauki princess dinsa ya fara mata rawa, suna celebrating sun kusa samun new beby.

Ranar hubby taga so da tattali, sosai yake nuna farin cikinsa mara misaltuwa, a kan cikin hubby. Da yamma ya dauketa zuwa wani special clinic don neman shawar -warin yadda zasu kula da Amatullah, da abubuwan da ya dace taci. Sun yanke shawarar Jan bakinsu suyi shiru. They want to surprise there family.

Koda suka yi waya da Aisha take tambayarta maganar family planing, ce mata tayi, tayi babban. Daga karshe ta shashantar da maganar.

Kula sosai hubby ke samu, a wurin hayder, haka ya hadata da wata doctor musamman take zuwa har gida ta dubata tare da bata shawarwari. Ta ci gaba da shayar da Amatullah yarinyar tayi girma da wayau abunta. Watanta tara ta fara takawa. Ta bangaren karatun hubby abin masha Allah, ta dage tare da taimakon Allah duk sakamakonta na 2 section din da sukayi sunyi kyau.

Maryam kam tana nan sai faman tura kudi ma Nancy take, kan hayder amma shiru ba nasara. Gashi zuwa lokacin soyayyar hayder ta kara nunkuwa a ranta. Haka zata bishi school ta tsaya daga nesa tana kallonsa kamar photo, don bata da ikon zuwa inda yake, tun tanar da ya sauke mata tagwayen maruka, da warning take tsoronsa.
Nancy kam kasuwa ta bude, sai tatsar maryam take, da sunan zuwa wurin malan alhali harkar gabanta kawai takeyi. Sai in maryam ta kirata kan aiki bai ciba har yanzu. Sai tace zata canza wurin wani malamin ko zaa dace. Haka zatayi ta mata bill na abubuwan da malan yace a siya na kayan aiki. Ita kuwa wawiyar jiki na rawa duk inda kudi suke zata nemo ta tura mata. A na haka list din Wanda aka kora saboda rashin maida hankali, da rashin samun makin da ya dace ya fito. Sunan maryam na daga ciki, hakan ya balain daga mata hankali. Dole tana ji tana gani, ta tattaro zuwa kasa Nigeria, da niyyar sake komawa Cyprus koba the same school ba.

Tama dawowa, hajiyanta ta hadata da wani dan ambassador na kasar France, ganin kudi yasata saurin amincewa da maganar aurensa, ba tare da bata lokaci ko bincike ba.

Ranar wata Monday su hubby suna lectures ciwon nakuda ya kamata, daga nan aka wuce da ita school clinic. Zainab ce ta kira hayder ta shaida masa. In no time sai gashi ya iso.

Wannan karon ma tare suka shiga labour room, da yake su sunma fi son mijin mace na wurin.

Tun 4 na yamma sai 11 na dare hubby ta santalo beby girl dinta again. Mai kama da hayder tamkar Amatullah. Murna a wurin hayder baa magana. Hada hubby da beby din yayi ya rungume a jikinsa, yana jin sonsu da kaunarsu na ratsa duk wata gaba ta jikinsa.

Hajiya na tsaka da baccinta, taji wayarta na ringing, ganin auta, yasa gabanta ya fadi, don bai taba kiranta a wannan time din ba. " lafiya auta?" Ta fada murya irinta mai bacci daya shiga fargaba.

Dariya yayi " mun samu karuwa!" Ya fada still yana dariya

Ajiyar zuciya Hajiya tayi " Wane irin karuwa? Kar ka cemin Ummi keda ciki ka kirani a wannan tsohon daren?"

" ta haihu dazun nan! Mun samu Amatulrahman." Ya fada cike da jin dadi.

Ai tuni bacci yayi kaura a idon Hajiya, ta gyara zama " an gaya maka haihuwar wasa ce? Ban son rainin hankali meya faru ka kirani?"

" Allah da gaske nake, gata ki tambayeta. " ya mikawa hubby dake kwance wayar yana murmushi

Ko gaisawa basuyi ba Hajiya ta katse hubby dake kokarin gaisheta " da gaskene abinda auta ya fada min?"

Kada kai hubby tayi cike da kunya, kamar Hajiya na kallonta, sai da ta kara tambayarta sannan ta iya ce mata "eh!" Ta mika masa wayar.

" amma yaran nan bakuda hankali, har ayi cikin ya kai haihuwa amma Ku kasa gayawa kowa, sai bayan an haihu?" Hajiya ta fada cikin fada da jin haushin abunda sukayi. Don bataji dadi ba kiba ko basu gayawa kowa ba sa gaya mata.

Hakuri hayder ya fara bata, cike da damuwa, bai dauka abun zai mata zafi haka ba.

Cikin daren Hajiya ta fara kiran jamaa tana shaida musu haihuwar hubby.

Hubby na zaune tana shan tea, kiran Aisha ya shigo wayarta. " hello besty." Ta fada tana murmushi

" ba wani besty! Ai ni kin gama ban mamaki, wannan kyakyawan labarin, amma sai injishi daga sama." Ta fada cikin jin haushi

" Allah ya huci ran besty." Ta fada tana murmushi

" yar rainin sense, shiyasa da muke maganar da Ummul khair kan maganar babban planning, tayi dariya ta ce " yanzu haka in kin bibiya Anty hubby ta kuma kunsan wani cikin ne, ta fake miki da babban tayi" ina cewa ina ba haka bane."

" tuba nake! Ya yarona?"

" gayi can, yanzu na senda shi wurin nanny dinsa. ina bebymu?" Ta fada tana washe baki, kamar ba ita ta gama korafi ba

" gata nan, tana bacci. Na tura muku da pictures in kin kunna data zaki ganta."

" ok. ina beby Amatullah? " Aisha ta tambaya

" tana wurin daddy dinta."

" na kosa inga new beby, how she look? " ta fada cikin kaguwa.

" like u." Hubby ta fada tana murmushi

" sai munyi waya, bari inga picture din bebynmu, I hope kin hado dana beby Amatullah?"

" yes!" Hubby ta fada tana sauke wayar a kunnenta

Kafin su hubby su iso gida, daga hospital, harsu Mariya da hafsa,Zainab sun gyara mata gidanta tsaf, sun saka turare, ko ina na tashin kamshi, dakin hayder ne kawai basu shiga ba. Hatta girki sun kammala.

Hubby taji dadin abunda suka mata. "Madallah da aminan kwarai" hubby ta fada tana murmushi

" dont meantion, we are know sisters right? " inji Hafsat

Kai ta kada tana murmushi " right. "

8:41 sai gasu Hajiya da gwaggo, Anty samira sun iso. Basu kira kowaba, don haka su hubby basu san da zuwansu ba, sai ganinsu sukayi. Zo kaga murna wurin waannan bayin Allah.

" da kungaya min inzo in daukoku daga airport. " hayder ya fada yana gefen Hajiya dake rike da Amatullah

" Abinda kuka mana, muka muku, kuji in da dadi." Gwaggo ta fada tana harararsu.

" mun bada hakuri fah!" Inji hayder

" ko don wannan zukekiyar bebyn kwayi hakuri, Ku yafa musu." Anty samira dake rike da bebyn ta fada tana murmushi

Ranar haka suka kwana cikin farin ciki, hubby na makale jikin gwaggo.

Haka duk nisan Cyprus bai hana yanuwa da abokan arziki zuwa duba hubby da beby dinta ba. Haka su junaid duk kansu sunzo kusan a tare, kwanansu biyu suka koma. Satin hubby biyu da haihuwa su gwaggo sukayi haramar komawa gida. Anty samira dai dama kwananta biyu ta koma tare dasu ummu sulaim.

Hubby taso gwaggo ta zauna mata, rike baki gwaggo tayi " kafata kafar Hajiya, ina zan iya da rashin kunyarku ta yaran zamani, wancan karon ma ya muka kare, balle yanzu da abun naku ya kara shahara? Ma dawo shekara mai zuwa ganin wani bebyn."

" haba gwaggo, wannan wane irin fatane?" Ta fada cike da shagwaba tana tura baki.

" fata ko gaskiya!! Miji na nanike dake kamar cungum ta ina zaki kasa haihuwa duk shekara.? " gwaggo ta fada tana tabe baki

Dariya Hajiya tayi " keda takwarar taki?"

" yo!! Me nace? Zamane dai banyi, Allah miki albarka da kika dauke Amatullah, kafin shekara ma dawo wani sunan. Ban zama inga wannan fitsara, kina nan ma ya muka kare, balle bakyanan?"

Dariya kawai Hajiya tayi. Don itama bata bayan zaman gwaggon. Don hayder yanzu bata ido ce ta isheshiba. A gaban kowa yake nuna soyayyar matarsa. Garama ita tana dan kawaici da kunya, daba haka ba. Hajiya taji dadin hakan sosai.

Tafiya da Amatullah dasu Hajiya sukayi ba karamin daga hankalinsu hubby yayi ba, musamman hayder da Mariya. Don har hawaye hayder yayi, Mariya kam kuka riris.

Tafiyarsu gwaggo da kwana biyu, su mommy Hauwa da Alhaji Munir suka iso, ganin jika. Sunji dadin ganin yaran nasu. Albarka sosai Alhaji Munir ya dinga saka musu. Haka mommy Hauwa baki yaki rufuwa don farin ciki. Ummin tace wai da yara har biyu? Ikon Allah.

Haka suka maida hankali kan karatunsu da kula da Amatulrahnan. Soyayyar hubby da hayder sai dada bungasa take, suna kula da juna, da gudun bacin ran juna, da nunawa juna tsantsar soyayya.

Hayder ya riga hubby kammala nasa karatun, hakan yasa ya kara maida hankali wurin karatun Islam, da dama kusan a tare yake yin kayansa. Zuwa lokacin yayi nisa sosai a littatafan hadith, fighu, tafsir da sauransu.

Alhamdulillah, Beby Amatulrahman nada shekara daya da wata biyu, hubby ta kara samun wani cikin. Na wannan karon mai matukar laulayi. Allah ma yasa Mariya ta kammala secondary sch dinta, kula da Amatulrahman ya koma hannunta.

A wahalce haka hubby ta kammala nata karatun. Lokacin cikinta na cikin watana 7 amma har lokacin tana laulayi, sai dai bai kai farkon cikin ba.

After one month suka tattaro zuwa gida Nigeria. Hubby tasha mamakin ganin gidan da hayder ya tsantsara musu a lamido crescent, Unguwar rimi. Gidane na gani na fada. Suna Jere dana junaid, komai iri daya.

Zuwa wannan lokacin business dinsu hayder ya kara bunkasa, saboda sabon salo da suka zo dashi na dabarun kasuwanci. Zuwa lokacin kowa ya fara cin gashin kanshi. Sabanin da da sukeyi a tare.

Ansa ranar auren junaid da Asiya, abinda ya faranta ran hubby sosai, tare da dunbin mamaki, koda yake ta dade da fara ganin alamu daga garesu, sai dai bata zurfafa tunani ba. Wata uku masu zuwa

******************

"please tell me, what happen between u and Nasrin? I want to know." Hubby ta fada tana narkewa a jikin hayder

Hancinta ya lakace " its all your fault " " my fault? how?" Ta fada tana mikewa zaune

Smirk ya mata " by stolen my heart." Ya kashe mata ido

Murmushi ta masa tare da kiss a lips dinsa.

" parents dinta sunki amincewa tayi aure nesa dasu, she is the only child da suka haifa. She love me so much, sun yadda ta aureni but da sharadin zan koma Egypt da zama. Abunda bazai taba yiwuwa ba, I can live my parents because of her. So mun dade ana ta jayayya, at last suka ce lallai se dai ta auri dan uwanta, tunda naki amincewa da sharadinsu. She come to me, so I advice her tayi hakuri ta musu biyayya tunda sun kafe kan hakan. Ni kuma bazan taba yin abinda suke so ba. Nasha wuya sosai kafin ta hakura zata aureshi. Yanzu haka 6 months kenan da akayi bikinta."

" baka kyauta ba, da sai ka dinga zuwa kana dawowa ai!" Hubby ta fada

Harararta yayi " kina dona kuwa?" Ya tambaya in husky voice

Dafe saitin zuciyarta tayi " sosai ma" tana kashe mishi ido

" ta ina zan iya yanke wannan danyen hukuncin, bayan kin bararraje a cikin zuciyar, baki bar space ko kadan ba." Ya fada yana smirk

" kar kasa kaina yayi kato fah?" Ta fada cike da shagwaba

"Kin riga kin gama da hayder Habiba, baya iya kallon ko wacce mace sai ke. A sonki bana ji bana gani. Don haka ki kwantar da hankalinki, zuciyar hayder taki ce da yaranmu. Haka gidan hayder belongs to u and our children's, sai kaddara da baa fata."

Rungumeshi tayi tana kissing nasa every ware " haka zuciyar Habiba taka ce only u, no one but u, till my last breath. "

Kara matseta yayi a jikinsa, cike da farin ciki, suka fara romancing juna daga nan suka wuce.....

******************
Wannan karon beby boy hubby ta santalo, mai kama da ubansa sak. Farin ciki baa magana, yaro yaci sunan Yusuf.

Hubby ta ci gaba da kula da yaranta, har lokacin Amatullah tana wurin Hajiya.

Anyi bikin junaid da Asiya. A lokacin akasa na Ashir da aina, Hafiz omer da Zainab kawar hubby.

Yusuf nada 3 month business Trip India ta kama hayder. Gidan Hajiya suka kai mata Amatulrahman, suka nufi kasar India.

Kwanansu biyar a kasar India, suna soyewa, a haka kuma yake samun time na abinda ya kaishi.

Hajiya ta kirasu, suje su duba Hajiya kaka, su Abdul Karim sun taho da ita ba lafiya. Abdul Karim ya kira, nan yake gaya masa hospital din da take, duka anan cikin Mumbai ne.

Bayan ya dawo daga meeting, suka shirya zuwa duba Hajiya kaka. Sun sha mamakin samunta ita kadai, sai rarraba ido take a gadon asibiti kamar agogo. Tana ganinsu ta fashe da kuka. Duk sun shiga damuwa bisa halinda take ciki.

Tun safe dasu Abdul Karim da matarsa sailuba, suka zo suka dubata har zuwa lokacin 7 na yamma basu kara lekota ba, tsawon 3 days daaka kawota haka suke mata, in sunzo da safe, sai gobe kuma su dawo dubata. Kasan cewar hospital din baa bukatar mai jinya, hatta abinci su suke ba majinyata. Shiyaba su Abdul damar banzatar da Hajiya kaka. Alhalin yawanci kowanne mai jinya, zaka samu akwai wani na kusa dashi a wurin, har zuwa lokacin bacci, kafin su tafi, su dawo da safe.

Ciwon zuciya ke damun Hajiya kakan, hakan yasa Mmn samira tattara yan kudadenta don samawa mahaifiyarta lafiya, ta turo Abdul Karim da matarsa don suyi jinyarta, don itama hawan jini yasata a gaba, yan kwanakin. Da ita zatazo da kanta.

Tunda suka zo kowa ya kama gabansa, in gari ya waye sun duba Hajiya kowa keyin hanyarsa. Don yanzu sosai halin Abdul Karim na muamala da mata ya shahara har kowa yanzu ya sani. Ita kanta sailuban abinda take yi kenan, kuma duka sun sani, har lokacin ko batan wata bata taba yiba, bata so ta tsufa da wuri, shiyasa take shan maganin planning. A cewarta

Hubby ce taci gaba da kula da Hajiya kaka, da safe kafin ta taho saita tana dar mata abinci na musamman wanda zai mata dadin ci, da saurin narkewa, ta taho mata dashi, haka zasu zauna susha hira har yamma, kafin hayder yazo ya dauketa su tafi. A haka har akama Hajiya kaka aiki, alhamdulillah an samu nasara duk da sai a hankali, tunda ya hada da girma. Hubby tunda take zuwa sau biyu suka hadu da sailuba, wadda takewa hubby kallon raini da kishi, don taji labarin komai, kuma har yanzu tasan akwai son hubby a zuciyar mijinta.

Sun hadu da Abdul Karim da dan dama, don tunda yasan hayder na zuwa, yake kokarin biyosa suzo, ko kuma lokacin da zasu tafi, shi kuma zai zo.

Saboda ciwon Hajiya kaka yasa suka kara kwanaki a India. Saida aka sallameta suka rankayo gida Nigeria gaba daya, suka bar Abdul Karim da matarsa a can, cewarsu akwai abunda suke, basu kammala ba.

Kuka sosai Hajiya kaka tayi, tana ba su hubby hakurin, abunda ta musu, tare da shi musu albarka da zuriarsu.
" nasan nayi kuskure, amma duk laifin samira ne data zugani, gashi ta kai dan uwanta ta baro, meye anfanin wannan aure na Abdul Karim? In banda takaici." Tabe baki hayder yayi " baki mana komai ba, illa ince abinda kika min banda kudin da zan biyaki dasu. Kin gama min komai, tunda kika zama sanadin aurena da Habiba. Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, ya baki lafiya. "

" amin! Allah ya riga ya kaddara Habiba matarka ce, Allah ya raya muku zuria." Ta fada tana share hawaye. Zuciyarta cike da dana sani da nadama

*******************
Sun dawo ba dadewa hubby ta fara aiki a hospital din doctor sabir. Lokacin arziki da budi kota ko ina haka suke bulbulowa a rayuwarsu hubby

Duk wani hidima na yan'uwa, da dangi kusan hayder ya dauke, kowa matsalarsa ta tashi hayder! Ya koma tamkar shine babba a gidan, duk abunda babban yaya yakamata yayi, shi yake gudanarwa.

Ta fannin taimako kuwa baa magana, don shi mutun ne mai matukar sirri, baka taba sanin ayyuka na alkhairi da yake gudanarwa. Yanzu haka yana da katafaren gida, mai kama da boarding school, inda yake ba tsofaffi mafaka, wanda basu taba haihuwaba, ga tsufa ya kamasu babu mataimaki. Wanda ya danka shi kalkashin kulawar malaminsa sheikh Ahmad al- kanawiy. Haka masallatai da rijiyoyi ya Samar ba adadi, sadakatul jariya, gareshi da dan' uwansa. Haka taimakon marayu, wanda hadin hannune shida abokanshi, sai hubby da tayi joining dinsu.

Shakuwa da kaunar juna, shine tsakanin hubby da yayyen mijinta, musamman ummu sulaim da Aisha, haka anintarta da yusra da humaira ya kara bunkasa, a gefe daya ga Zainab data shigo family duk ta sanadiyyarta. Sai Hafsat.

So da kauna sai abinda ya karu, tsakanin Hubby da oga hayder, kullun ka gansu kamar sabon aure. Rayuwa tamasu hubby dadi, sai dai duk yadda rayuwa take lallai tana zuwa da nata jarabawar iri iri,. Yusuf na wata 6 hubby ta sake samun wani cikin, fatan Allah ya sauki hubby lafiya, ya kara dankon kauna tsakaninta da oga hayder, ya raya su Amatullah da kannenta masu zuwa........

Anan na kawo karshen littafina mai suna DA KAMAR WUYA. Na gode da kauna da soyayyarku gareni, musamman masu kokarin yin comments da masu voting duka, Allah yasaka da alkhairi, ya bar kauna. Jhazhakallahu bi Janna to all of u. Sai mun hadu a littafina na gaba KYAN DAN MACIJI


 
 
Chapter 28 · 0% Book details