← Book details Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 1 OF 28

                            Part 1

Da Kamar Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

      Written By Zulaihat Aliyu Misau

       Wattpad@zulaihatualiyumisau
   
Not Edited.......
 
Bismillahir Rahmani Rahim

Dukkan yabo da godiya sun tabbata GA Allah, mamallakin duk kan komai da kowa. Ina rokon Allah da ya bani ikon fara wannan littafi, ya bani ikon kammalashi, ya bani ikon isar da dunbin sakon nin dake cikin sa. Ya bani ikon kammala daya littafina mai suna kuskurenmu, ya bamu ikon daukar darussan dake ciki.

Dedicated to all the one read my story.........

"Hubby please kar ki ci masa abinci, kin san yau full day ne, ya kike so yayi, kinsan baya cin abincin kowa a school din nan.

Harararta tayi " ai dama haka nake so, kinga jikinsa zai gaya masa kenan. Zai ji anani burdade yau.

"amma dai kin san abinda kikeyi bakya kyautawa ko? Koba komai ai ke babbace, bai kamata ki dinga cin zalin yaron mutaneba don kinga kawai baya shiga saugarki.

"Kinga yusra ya isheki haka!!! Ke bakya ganin irin rashin mutuncin da yake min ne. A matsayina na yayarsa ban isa ya gaisheni ba, sai wani ji da kansa yake kamar baya kashi. Ai ko don junaid ya dinga girmamani.

"Wow!!! Hubby ki rage son girma, kin San halinsa ba kowa yake kulawa ba, me yasa zaki damu kanki?

Banza hubby tayi da ita, ta ci gaba da cin jollop rice din da tasha hadi, ga kifi nan Manya Manya, yamafi rice din yawa. " dan banzan yaro, shiyasa kullun yake Kara kumatu. Dole yaki cin abincin jamaa, don shima kar aci nasa. Kin San kalar dadin abin cin nan? Ta fada tana gutsuran kifi, ko cokali bata bukata ba, don tunda taga abincin miyanta ya tsinke.

" kice dai yau kwadayinki ya motsa "

"Kema da kinsan kalan dadin abincin nan da baki ki ci ba. Dagaji girkin maman Aliyu ne, bana yan aiki bane. Dan Menan yaro yana wahalar min da innah.

"kyadai ji dashi, Allah yasa ya zo ya sameki, kina cinye masa abinci.

Dariya hubby tayi, da dai wani ne, ba wannan muskilin banzanba.

Ya kamata ki hakura haka, kija girmanki, kinga shi kwata kwata bakya gabansa.

Rufe curler din tayi, bayan ta cinye abincin tas, ko kwayar rice bata bari ba. Duk da ji da take cikinta kamar zai fashe, don koshi. Oya muje in wanke hannu Kafin a dawo class. Ta fada tana lashe hannu.

" naga ranar da zaki canza? Har yau halin yan kauye bai bar kiba. Yusra tace tana binta a baya.

" naga dai duk tsiyar mutun asalinsa kauye ne. Ke barima kiji, ni wallahi da zaa Mai Dani kauyen dana fi farin ciki. Inda zan sakata in wala, in tsula tsiyata yadda nakeso. Nayi missing kakus fiye da zatonki.

Har yajin aikin cin abinci nayi,  amma mutanen nan, ko a jikinsu. Sai da naga haza, in na mutu basu da asara  tunda bani kadai suka Haifa ba. Yasa na dawo aikin cin abinci. Don lokacin har na fara ganin kamar kowa ma farin kaya yasa a jikinsa. Kin ga alamar mutuwa ta matso kenan..

Dariya yusra keyi harda rike ciki. " ke din ce zaki iya wani yajin cin abinci?  Azumi ma da yaya kike kaiwa, balle ba'a azumi? 

Suna fita class din, su kuma suna shigowa. 

Wani hadadden matashi na gani, Wanda bazai wuce shekara sha biyar, zuwa sha shida ba, yana sanye da kayan kwallo na kamfanin NIKE farare,  kafarsa na sanye da farin canvas shima na kamfanin NIKE da farar safa. Fari ne sosai, yanada tsayi,  bayi da jiki. Amma da gani za'ayi hadadden guy mai kyan jiki,  da kira.

Kyakyawane na bugawa a jarida. Fiskarsa doguwa,  Mai dauke da dogon hanci,, ma-dai -dai tan ido,  masu matukar haske, sai Dan madai daicin baki , mai dauke da jerarrun hakora,  farare tas,  gasu sunada tsayi kwanin sha'awa. Yanada dimple both side din fiskarsa. Gashinsa bakine sidik, mai matukar laushi. Wanda yasha gyara. Yanada gashin gira baki Mai yalwa, ga baki, gashin idonsa kamar anyi piecing din su.

Shine a gaba, sai sauran tawagar student din. Ko wanne da kayan kwallo a jikinsa, duk sun hada zufa. Alamar daga field suke.

"Anty -Anty Allah ya bar mana Anty. Wasu daga cikinsu suka fara fada ganin hubby da ke fitowa a class din.

Hararar na gaban tayi,  Kafin ta wuce abinta,  yusra na binta a baya. Ko kallon inda take baiyi ba ya wuce locker dinsa.

Kayansa ya gani a bar baje, da sauri ya karasa wurin.  Da food placks dinsa ya fara cin Karo. Ganin ba komai a ciki,  yasashi mai da hankalinsa kan kayansa. A can gefe ya hango rigar uniform dinsa. Daukowa yayi. Dubawar da zai yi duk shatin mai da alamar da rigar aka goge hannu,  bayan an cinye masa abinci.

Wani bakin ciki da takaicine ya lullubeshi. Don yasan duk fadin school dinnan. Habiba (hubby) ya rasa mai ya tsare mata a rayuwa, ta takura masa. Shi ba shiga harkarta yake yi ba, duk da tana yar uwarsa. Zai iya cewa jinin sa bai hadu da nata ba. Shiyasa ko kallo bata ishe shiba. Don shi haka yake,  in ransa baya son mutun no matter how close they are. Ba ruwansa dashi. In ka girmeshi dai zai gaishe ka,  amma banda gaisuwa ba zai taba yadda wani Abu ya hada ku ba.

Ita din yayar sa ce, a kalla ta bashe good 6year's,  but amma yanayin childish behavior dinta yasa ko kallonta baya son yi. Don ba karamin haushi take bashi ba.

Kafadar sa da aka dafa,  yasa shi waigowa.  Daya daga cikin student din ne, " I'm very sorry broth " ya fada da yanayin damuwa a fuskarsa.

Murmushi ya kago " never mind, it's OK " ya fada, tare da tattara kayansa.

Wanda ya dafa shin ne ya miko masa shirt " take this. I were the one she spoil"

" no I will manage.

Zama yayi kan sit dinsa. Food Plack's student din ya ajiye akan table din,  tare da Jan yo kujera ya zauna.

" please haydar kar kace min bazakaci abincin nan ba.

Murmushi Wanda aka Kira da haydar yayi.  Junaid you know me very well, I'm not eat that food.

" so what do you eat?

Jakarsa ya dauko ya fito da dairy milk, Wanda ya tabbatar bata gan shiba da bai tsira ba. Ya fara ci. I will manage with this.

Girgiza Kai junaid yayi,  yana jinjina halin abokinshi kuma Dan uwansa, A ransa.

Duk yadda junaid ke jin yinwa, ganin Dan uwansa bai ci komai ba, yasa shima kasa cin nashi abincin.  "Have some" haydar ya fada yana Mika mishi chocolate din.

Tsaki junaid yayi,  tare da hararar chocolate din. " amma kasan you have a problem ko?

Murmushi yayi,  ya ci gaba da shan chocolate din shi.

Ransa ba dadi, har aka tashi daga school.

             *******************

Alhaji yusuf zubair Oregon. shine asalin sunan kakansu.  Dan a salin kasar Lebanon (Lebanese ) middle East. Wanda take boda da Syria, Israel da kuma Cyprus.

Aiki ya kawo yusuf garin kaduna. Wanda Allah ya kaddara zamansa a nan. Matarsa Hajiya Aisha Aliko. Haifaffiyar garin kaduna ( malali) sai yaransu uku: jamal,  jamil, omer.

Mutun ne na mutane. Yanada arziki dai dai misali.  Bayan ajiye aikinsa ya koma harkar restaurant Wanda dama tun yana aiki ya Fara bude su.

Kammala karatun Jamal na degree, yasa shima ya fan tsama sanaar mahaifin nasa.

A yanzu Alhaji jamal nada matan aure uku, : Hajiya Hadiza mai yara biyar.  Ummu kulsum, ummu Aiman,  ummu sulaim, ummul khair,  sai auta Aliyu haydar.  Sai Hajiya Amina mai yara uku : samirah, Ahmad, Abdulkharim . Sai Hajiya saadatu Mai yara biyar : yusuf,  Abdul majid,  Abida,  Aisha,  Airah.

Alhaji Jamal yanada arzkiki sosai, shine mamallakin gidajen abinci,  da ake ji dasu a jahohin Nigeria,  wato eat more restaurant.

Mutun ne mai son addini,  Wanda yakewa addini hidima da dukiyarsa, da karfinsa. Ya na son jamaa. Mutun ne mai jin kan iyaye, da kula da hakkokinsu,  mutun ne jajirtacce adali mai kyautatawa iyalansa. Sai dai fa in ka tabosa akwai fada 😎 akwai doka da oder sosai a rayuwar gidansa.

Alhaji jamil maaikacin currant affairs dake Abuja. Rikakken dan boko,  amma Wanda aka surka da ilmin addini 😊 yanada arziki dai dai misali. Yanada mata daya Hajiya maryam, da yara hudu : Aslam, Aaryan, Aashir,  Abdul Alim. Rayuwar gidansa rayuwace ta wayewa. Amma ba wadda ta kauce sharia ba.

Alhaji jamil nada kirki kamar Dan uwansa.

Sai Alhaji omer business tycoon.  Mazaunin Lego's duk ya fisu dukiya.
Yana da mata biyu Hajiya Zuwaira da yara hudu: Aisha (nana) Asima, Asiya, Asnah. Sai hajiya Bilkisu mai yara uku : Arif (omer), Abdul fatta, Abdul Hafiz.  Mommy Hauwa kanwace a wurin Hajiya Hadiza. Su biyu iyayensu suka Haifa, suna kanana Allah ya yi musu rasuwa.  Sun taso a hannun kanin babansu, Malan tsalha. sun samu tarbiyya  dai dai kwarkwado, da ilmi na addini dana boko. Duk da kalubalen da suka samu da maidakin nasa umma larai.

Bayan auren Hadiza da yan watannin ta dauke kanwarta,  ta ci gaba da kula da ita. Anan Allah ya hada Hauwa da Munir, abokin omer ne tare sukayi karatu a malesia. Shi dan ainihin katsina ne,  cikin kankiya local government. Yana zuwa Hutu kaduna wurin yayyen mahaifinsa da ke nan kaduna. Kasan cewarsa aboki na kut da kut ga omer,  yasa kowa ya sanshi a family din.

Ummu Habiba ita ce yarinyarsu ta farko,  sai jabir, jafar sai junaid Wanda yake sa an Aliyu.

Ummu habiba ta taso wurin kakarta,  wadda ta dauketa a nono. So ko bayan ta isa makaranta gwaggo kin dawo da ita tayi. Munir shi kadai suka Haifa,  daga kansa basu sake haihuwa ba. Wannan yasa ta ki mayar musu da habiba.

Rayuwar habiba a kankiya,  rayuwa ce ta ba sawa ba hanawa,  abinda take so shi gwaggo ke mata,  don ma Alhaji kawu na taka musu birki, in yaga abun yayi yawa.

Rashin kunya,  tsokanar fada,  Rashid son karatu,  kazanta, duk halin habiba ne. Batajin magana ko kadan,  ga dan banzan barna.

Tanada shekara goma,  amma har lokacin ajinta uku,  a primary school duk da kyan makarantar,  amma rashin maida hankali a karatu yasa ake mata repeating.

Ko kadan bata kaunar zuwa kaduna wurin iyayenta Hutu. A cewarta sun cika takura. Ganin haka gwaggo tace ba mai takura mata, tunda batason zuwa a gyaleta.

Wannan halayya na habiba na cin ran iyayenta. Musamman ta bangaren karatu. Habiba Nada shekara sha hudu sai lokacin ta gama primary school duk abokanta suna ss 1,  wasu na js3.

Ganin haka ya sa Alhaji kawu budewa gwaggo wuta, kan ta mayar da habiba, GA iyayenta, don ya Lura in ya ci gaba da zuba ido abun ba zaiyi kyau ba. Don habiba bata son Karatu ko kadan,  Sai tayi sati bataje school ba. Shi kuma ba mazaunin gida ba,  in ya fita Sai yamma can,  koma dare.

Da kansa ya dauki waya ya Kira Munir,  yazo ya dauki yarsa. Da kuka da birgima haka suka nufo kaduna. Suka bar gwaggo cikin matsar hawaye. Don ba kadan ba take son habiba. Har ciwo tayi na rashinta.

Lokacin jabir da jafar  sunyi exams din jsce.  Junaid na js1.  Dakyar suka samu aka dauketa a js1 saboda ko spelling mai kyau bata iya ba,  bata iya karatun Hausa ba ma balle English.  Sun amsheta da sharadin zaa nema mata lesson teacher. 
Aji daya aka sata da su junaid da Aliyu.

Son girma, mu samman da taga duk ajin ta fisu shekaru, duk da bata da girman jiki. Wannan yasa duk ta fitini kowa, musamman in zaka ganta kaki gaishta,  ko ta kamaka kana mata dariya,  in an tambayeta amsa bata sani ba,  To ka shiga uku. Kusan ko yaushe a cikin fada take,  ba maza ba mata. Dole yasa suke ce mata anty don gudun jarabarta.

Duk wannan abun da takeyi ko kallo bata ishi Aliyu ba, so da yawa har desk dinsa zata zo, ta duddungure shi,  tana masifa,  ko daga kansa bazai yi ba balle yasan tanayi. Wannan shi yake Kara bakanta mata rai,  baya ko kallonta,  balle ya gaisheta kamar yanda yan ajin keyi,  ko anty din ma bata samu arzikin sa ba.

Ko a gida suka hadu,  shi yazo ko ita taje, Ba ruwansa da ita. Tasha Kai kararsa wurin mommy da Haj amma ba abunda ya canza.

Wannan shi yasa tadau damarar yi masa rashin mutunci,. Tun daga lokacin ta maida rayuwarsa living he'll..
Sai dai abinda ke Kara bata haushi har yanzun nan da suke Shirye shiryen zana final exams dinsu, bai taba tanka duk abinda zatayi masa ba. Wanda ita ba haka ta so ba.

Aliyu najin zafin abinda take masa,  amma kullun maganar Haj in ya gaya mata, shine yayi hakuri,  ya rabu da ita, in ta gaji zata daina abinda take masa. Kuma yar uwarsa ce bai kamata ya biye mata suna fada ba. Duk da ta zubar da girmanta to shi ya dauki girman yayi hakuri.

             *********************

School bus dinsu na shigowa, bai tsaya baba ya Gama ko parking ba, ya Saba jakarsa ya balle murfin motar ya fito. Da kallo baba da sauran kannen nasa suka bishi.

"Shida mutuniyar ne ko?" baba ya tambayi su abida.

" kai ma kasan Sai ita,  don yaya bashi da abokin fada. Aisha ta ce tana Saba Jakarta.

"kai wannan yarinya,  Allah ya yi fitinanniya. Baba ya fada

Da Yaya Ahmad sukaci Karo,  yana fitowa. "Sweet broth well come "

" thanks " ya fada yana kokarin wucewa ciki,  ba tare da ya Kalli yayan nasa ba.

" what happened to you?  Ahmad ya fada yana juyo dashi. Ganin yadda yake faman huci,  yasan ran kanin nasa a bace yake.

" I'm sick and tired of that useless girl, I have to teach her a big lesson of her life.

Murmushi Ahmad ya yi,  don yasan yau ma an kuma. " me kuma tayi yau?

" she finish my food,  don wulakanci a jikin uniform dinsa ta goge filthy hands dinta.

Dariya Ahmad yayi, " lallai wannan yayar taku,  bata kyauta ba.

" Ba yayata ba. Allah ya kiyaye inyi yaya da wannan good for nothing din.

" don't say that.  Ni na rasa gane meye yake hadaku, ko kana mata wani Abu ne da bata so?

" me zan mata,  yarinyar da ko kamarta,  bazan iya tan tan cewa ba. Daga yanzu na daina kyaleta, zan gwada mata nawa rashin mutuncin. Dama hajiya ke cewa inyi hakuri, da tuni nayi maganinta.

" Aa Aliyu, ko Ba komai taci albarkacin mommy da junaid.  Zan sameta zamuyi magana.

Zuwan su Aisha yasa suka katse zancen,  ya shige part dinsu,  yabar Ahmad suna gaisawa da su Aisha.

A falo ya samu hajiya da mmn samira.  Suna duba wasu lessis da aka kawo na siyarwa.

Gaishesu yayi,  ya wuce dakinsa.  Mmn samira ta Kalli hajiya, yaya yau mutumin naki,  a sama yake.  Tabe baki hajiya tayi " nasan baya wuce shida habiba,  na rasa me yasa basa iya zama inuwa daya. ita son girma,  shi kuma kinsan halinsa sarai.

Murmushi mmn samira tayi " lamarin Aliyu sai shi. Na dauka yana girma abun na raguwa,  amma kullun gaba yake karawa.

" kedai bari,  nayi fadan,  nayi dukan duk a banza. Addua nake masa Allah ya yaye masa wannan halayya.

Fitowa yayi, ya wuce main kitchen. A nan ya tarar da mmn yusuf na kokarin daura abincin dare.

Gaisheta yayi cike da girmamawa.  Murmushi tayi " haydar an dawo? 

"Eh " ya fada yana bude fridge.

" ga abincinka nan,  yanzu nayi worming. Tana nuna masa microwave.

" thanks,  you are the best.  Ya fada bayan ya dauko bottle water da maltina.

Bude microwave din yayi ya fito da plate din.  Murmushi yayi saboda favorite dinsa da ya gani.

" Wow!!!!  Na gode sosai, kamar kinsan yunwa sosai nakeji, ina bukatar favorite,  don inji dadin ci.

Murmushi tayi. Shigowar hajiya ya sa ya dauki plate dinsa yayi gaba, da harara ta rakashi.  Kafin ta maida kallonta zuwa ga mmn yusuf da ta ci gaba da aikinta,  ba tare da tako Kalli hajiyar ba.

Tsaki taja, ta wuce fridge ta dauki abunda zata dauka ta fita..........
[29/02, 19:22] Zulaihatu Aliyu: 💐DA KAMAR WUYA💐
Chapter 1 · 0% Book details